Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
zauna akan gadonsa ta fara karanta wani abu mai kama da almara..labarin wadansu mutane da yaki ya korosu suke gudun hijira. Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi ya ce "Ina fatan dai kana biye dani Nas?" "Kwarai kuwa Baba". "Yawwa Nas, to bari mu koma kan wancan tsohon zaren labarinmu inda muka bar Anas a durkushe a gaban matarsa Mabaruka gurguwa. Sidi mai jaka ya yi shiru sannan sai ya sake zarar wani katon tubani ya jefa a bakinsa ya dubeni ya ce. "Ba zan iya hakura da cin tubani ba Nas, sai dai tumbina ya fashe Tsawon dakika talatin Nas, Anas yana durkushe a gaban Mabaruka cikin tsananin kaduwa yaya ma za ta bari ta yi ciki? Anas ya tambayi kansa, wani bakin ciki ya lullube zuciyarsa. A haukan Anas ya gama imani da cewa babu makawa Mabaruka mummunan jariri ko jaririya za ta haifa masa a matsayin dansa. Wannan tunani shi ya sa wani zazzafan gumi barkowa akan goshin Anas. Cikin karfin hali Anas ya ciccibi Mabaruka ya kwantar da ita akan gado sannan ya kwanta a kusa da ita ya yi shiru, domin kwakwalwarsa lokacin ba za ta iya tunanin komai ba sai na Ummi. A zuciyarsa yana cewa, ina ma ace cikin nan Ummi ce ta yi shi a matsayin matarsa. Tsawon lokaci suna nan haka a kwance ba sa ko motsi cikin bacin rai, can sai Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce a tausashe. "Anas..." "Na'am." Anas ya amasa bayan jinkirin kusan minti guda. "Ban ji ka ce komai ba ko ba ka farin ciki da dan da zan haifa ma" Anas ya ji kamar Mabaruka ta soka masa kibiya a tsakiyar zuciya. Shiru na yan dakiku, Anas bai amsa ba. "Anas...ba ka ce komai ba!" Mabaruka ta ce cikin wata irin shakakkiyar murya tana shirin fashewa da kuka. "Me ki ke so in ce dake?" Anas ya ce da ita a fusace. Hakika tuni ya gama yankewa zuciyarsa shawara shi fa ya gaji da wannan daurin talala da mulkin mallaka. Cikin kaduwa da jin abinda ya ce Mabaruka ta turar da hannunsa ta dan dago kai ta dubi fuskarsa a cikin dan hasken fitilar dakin dake ajiye akan wani teburi na alfarma. "Anas...ba ka kaunata ko?..." Anas ya yi shiru na yan dakiku bai amsa ba sannan sai ya tashi zaune ya ce. "Mabaruka ya kamata mu fuskanci gaskiya, sanin kanki ne tsakani da Allah cusa min ke aka yi...ba wai bana kaunarki bane amma..." "Ya isa haka!" Mabaruka ta daka masa tsawa cikin wata karyayyiyar murya. "Ba sai ka karasa ba Anas, na yarda tabbas ba ka kaunata." "Ka da ki zarge ni, ki zargi mahaifiyarki Mabaruka da kuma ke kanki." Aka sake yin shiru na yan mintuna. "Ummi ce ko?" Mabaruka ta bata shirun da wannan tambaya. "Ba zan boye miki ba Mabaruka...wall ahi duk duniya babu wacce nake kauna kamar ta. Mabaruka ta ji kamar ya watsa mata wuta a doron zuciya. Wani abu mai kamar amai ya zo ya toshe mata makogwaro. "Anas...mu sawwake wa juna ina ganin shi zai fi ko?" "Kwarai kuwa...nima da niyyar da na zo kenan." Cikin sauri kamar da wasa sai Anas ya lalubi aljihunsa ya zaro takardar da tun a cikin mota ya rubuta a lokacin da zai yi fakin da ita a gareji. Hannunsa na rawa ya mika mata ya ce baki na rawa. "Na sake ki saki biyu." Mabaruka ta karbi takardar ta karata a kirjinta, kana ta lumshe idanu, ga mamakin Anas, sai ya ga ta dubeshi ta ce. "Don Allah taimaka ka kaini falo." Anas ya ciccibeta, cikin damuwa domin tausayinta ya gama lullube zuciyarsa, to amma babu abin da zai iya akan hakan. Lokacin da ya ajiyeta, sai ta dube shi ta kuma cewa. "Dan Allah koma daki ka jirani." Ta dan yi shiru sannan sai ta kuma cewa "Za ka bari gari ya waye ko yanzu za ka fita?" Anas ya dubeta a rude sannan ne to fa dimbin asarar da zai dibga ya darsu a zuciyarsa, tabbas ya san ya rabu da masifa ya fada masifa. Domin a gurinsa Mabaruka masifa ce, haka kuma rabuwa da ita ma na nufin sake shiga cikin masifar talauci Koda yake dai ai ina da yan kudi a banki da gida da mota da kuma otal din da mahaifiyarta ta bani Anas ya fadawa kansa "Duk abin da ki ka ce haka za a yi in ba kya son ganina yanzu ma sai in tafi" Mabaruka ta danne kukan dake kokarin kufcewa daga makogwaronta. "Dan jirani a dakin to ina zuwa" Anas ya koma cikin dakin ya zauna gami da ajiyar zuciya Ga mamakinsa sai ya ji tamkar an dauke masa wani katon kaya mai nauyin tsiya daga doron bayansa Sannan ne to ya jiyo sautin muryar Mabruka daga cikin falon tana yiwa Mahaifiyarta waya Tsawon mintuna talatin Anas na nan zaune yana jran dawowar Mabruka gurguwa lokacin ne ya juyo sautin injin mota an shigo farfajiyar gidan Cikin sauri Anas ya mike a rude ya nufi taga ya leka. Tun kafin ya gama bude labulen tagar ya hangi dogon direban gidansu Mabaruka ya budewa Hajiya Aliya kofar katuwar (Jeep) din nan baka ta fito jikinsa na rawa Anas ya nufi falon inda Mabaruka take Anas ya sameta zaune akan kilishin dake mamaye da tsakar dakin kan talfon din rike a hannunta ta kwantar da kanta akan kujerar dake daf da ita gaban rigarta sharkaf da hawaye "Me ya kawo mahaifiyarki kuma cikin wannan maganar? Don me ba ki fada min ita za ki kirawo ba?" Mabaruka ba ta dago kai ba balle ma ta kalleshi sai ta ce a sanyaye "A GABANTA MUKA FARA AGABANTA NAKE SON MU ƘARE."TSOHON ALKAWARI-18 . "A GABANTA MUKA FARA AGABANTA NAKE SON MU KARE." Kofar babban falon ta bude Hajiya Aliya ta shigo a fusace bata ko damu da ta zauna ba sai ta dubi Anas ta ce "Tun da ka sake ta me kuma ka ke jira sai ka fice ka bar mata gidanta." Babu kunya, babu tsoro sai Anas ya dubeta ya ce "Gidanta ko gidana? Na dauka ke ki ka fada da bakinki kin bani gidan nan?" Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke ta ce Duba bayan ka wannan shine Yarima Gangariya na mallaka masa wan nan gida kuma daga zarar ta haihu za'a daura musu aure Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke ta ce "Kai dai jahili ne wallahi Anas kai ka taba gani inda aka baiwa mutum kyautar gida babu shaidu kuma babu takardu? Ko ka taba ganin inda aka baiwa mutum kyautar otal babu shaidu kuma babu takardu?" Anas ya ji wani zazzafan gumi ya karyo masa Hajiya Aliya ta dubeshi ido da ido ta ce "Ka yiwa kanka matsiyaci sai ka koma cikin talaucin ka motar da na baka na kwace kayata domin daman duk takardunta yana hannuna haka ma gidan da kuma otal din da na baka duk na kwace su. Daga yanzu ba kai babu karbar ko kwabo daga kamfanunnukanmu matsiyaci." "Bai kamata ki yi min haka ba?" Anas ya ce cikin kaduwa domin a shashancinsa bai taba tunanin haka ba. "Ba ka da hankali Anas tashi ka fice min daga gida. Rufeshi zamu yi a cikin daren nan in koma da yata gida ka yi ma sa'a wallahi da yan kudin da suke bankinka ma sai na yi hanyar da za su salwanta...amma ka yi sa'ar ta." Ta dan yi shiru tana duban Mabruka. "Ita ce ta ce na kyale ma kudin da ke cikin ma'adanin ka. Sai ka fice Allah ya bamu alheri." Anas ya dubi Mabruka a rude sannan sai ya juya zuwa cikin dakin. Ba a dade ba ya hado kayan sawarsa a cikin jakunkuna guda uku ya ratayo su da kyar sannan ya dubi Mabruka ya ce. "Na gode Mabruka." Sannan sai ya fice daga dakin. Wani abin mamaki shi ne tun da Mabruka take da Anas, bai taba fada mata kalmar da ta amince da ita har zuciyarta ba sai wannan godiyar da ya yi mata. Koda Anas ya nufi farfajiyar gidan sai dogon direban nan ya tare shi, ya karbi biyu daga cikin jakunkunan uku ya ce. "Mabruka ce ta ce duk inda ka ke son zuwa na kai ka." Anas bai san menene mutunci ko so ba sai yanzu. Abin mamaki sai ya ji hawaye ya yi sartu akan kuncinsa. Koda direban motar ya fara tafiya da su sai Anas ya yi ajiyar zuciya. A kalla dai ko da na rasa arziki ina da wacce na fi kauna da so a duniya Ummi! Anas ya ce da kansa. "Yallabai ina zan kai ka?" Anas ya dubi direban a rude sannan yace. "Bari in tuna"**** Ummi ta ji hawaye ya yi sartu akan kundukukinta sa'ar da ta gama karanta takardun. Hawayen da ke zuba a yanzu hawayen bakin ciki ne da farin ciki. Bakin cikin shi ne ya ya ma za a ce wai wadannan mutane da tun da ta fara budar ido su take gani a ce wai ba mahaifanta bane yayin da kuma farin cikin shi ne yanzu ta fahimci tana da damar mallakar abin da ta dade tana kauna tun da ta zo duniya. Haba gaskiya fa ta ji ba ta san rabuwa da shi tana bege da shaukin son zama da shi ashe ba dan uwanta ba ne na jini. Ba ta ji shigowarsa ba sai inuwarsa ta gani a kanta. Ta juya a razane, sai suka yi ido biyu da Abdulmalik. Nan da nan sai ya yi murmushi sannan ya mika mata wani farin kyalle ya ce a tausashe. "Goge hawayen ki." Ummi ta ji kunyarsa ta rufe ta, ta kasa hada ido da shi, kanta a sunkuye ta karbi kyallen gami da ajiyar zuciya. "Abdulmalik, me ya sa baka fada min ba tuntuni...kuma dan Allah wannan abin da ka rubuta min gaskiya ne?" Abdulmalik ya dubeta da murmushi ya ce. "Na taba fada miki karya?" Ummi ta yi sauri ta girgiza kai. "Kuma na ji kin kira sunana kai tsaye na dauka ni yayanki ne ko kin fasa yayan da ni?" Ummi ta rufe idanu a kunya ce ta ce "Ni na isa, ai har abada kai Yayana ne kuma..." Ta yi shiru ba ta karasa ba. Abdulmalik ya zo kusa da ita ya zauna da murmushi ya ce. "Karasa mana kuma me?" Ummi ta fara wata sassanyar dariya. "Ni ba zan karasa ba." "Allah sai kin karasa." Abdulmalik ya ce cikin dariya. Uimmi ta dago kanta ba tare da ta kalli fuskarsa ba, ta dubi hotonta dake manne a jikin bangon dakin sannan ta ce. "Rufe idanunka, ka miko hannunka na rubuta maka abin da na ki karasawa." Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya rufe idanunsa, sannan ya mika mata tafin hannunsa. Cikin sauri Ummi ta yi rubutu akan tafin hannunsa, sannan sai ta dauki takardun da ya bar mata ta karanta ta rike a hannunta sannan sai ta ruga a guje ta fice daga dakin. . Abdulmalik ya zo kusa da ita ya zauna da murmushi ya ce "Karasa mana kuma me?" Ummi ta fara wata sassanyar dariya. "Ni ba zan karasa ba." "Allah sai kin karasa." Abdulmalik ya ce cikin dariya Uimmi ta dago kanta ba tare da ta kalli fuskarsa ba ta dubi hotonta dake manne a jikin bangon dakin sannan ta ce "Rufe idanunka, ka miko hannunka na rubuta maka abin da na ki karasawa." Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya rufe idanunsa sannan ya mika mata tafin hannunsa. Cikin sauri Ummi ta yi rubutu akan tafin hannunsa sannan sai ta dauki takardun da ya bar mata ta karanta, ta rike a hannunta sannan sai ta ruga a guje ta fice daga dakin ta nufi dakin mahaifiyar Abdulmalik domin ta fasa kwai. Abdulmalik ya bude idanu a daidai lokacin da Ummi ta fice daga dakin kana ya dubi tafin hannunsa sai ya ga Ummi ta rubuta YAYANA MIJINA ! . Sidi mai jaka ya ja doguwar hamma ya kuma karawa sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya ce "Nas na fa gaji." Na dube shi cikin kasuwa na ce "Ka da dai ka ce min karshen labarin kenan?" Sidi mai jaka ya girgiza kai ya ce "Ba karshensa ba kenan amma saura dan kadan saurara na karasa maka sai mu watse" Na ce to, Sidi mai jaka ya dube ni kana ya ci gaba. Washe garin ranar karfe takwas daidai dan kabu-kabu ya sauke Anas a kofar gidan su Ummi idanunsa sai zubar da ruwa suke kamar tsohon kuturu domin rabonsa da ya hau kabu-kabu tun kafin satin da zai hadu da Mabruka Anas ya aika yaro zuciyarsa cike da farin ciki duk kuwa da sauyin rayuwa da ya same shi na gaggawa cikin sa'a ashirin da hudu kacal A daren jiya bai yi barci ba duk kuwa da cewa a dakin otal ya kwana amma dakin bai kai ko da rabin dakin kwanansu da Mabruka ba * A can cikin gida Ummi ta dubi Abdulmalik ta ce. "Mutumin ka ne, don Allah zo mu je ka labe daga bakin kofa ka ji yadda za mu kare da shi." Cikin murmushi Abdulmalik ya dube ta ya ce. "A'a, kada mu koma kamar yara kanana mana, ke dai je ki ku gama da shi ina nan." Ummi ta dube shi da dariyar zolaya ta ce. "Kai dai tsoro ka ke kada su Mama su ganmu tare, to mene ne kuma bayan sun san komai." "Sun san me?" Abdulmalik ya tambaya a tsora ce. "Takardun da ka rubuta suna gurin mama..." Ta fashe da dariya, da haka ta fice ta bar shi anan baki bude. Anas ya ji wani farin ciki marar misaltuwa ya lullube shi, sa'ar da ya hango kyakkyawar fuskar Ummi ta leka kofar gidan cikin sauri ya tareta da faffadan murmushi. "Hajiya Ummita." Ummi ta dube shi shekeke ta ce. "Ranka ya dade...yau a kasa ka zo ina motar?" Anan ne to Anas ya gama karkade dan sauran abin da ya rage na kaunarsa dake zuciyarta. "Wannan marar mutuncin gurguwarce ta kwace motar...kin san fa mun rabu da ita jiya da daddare saboda ke." Ummi ta dube shi cikin takaici ta ce "Kana nufin ka saki Mabaruka?" Anas ya gyada kai "Mene ne to amfanin zama da nacacciya. Matar da za ta hanaka walawa." Ummi ta kura masa idanu, yanzu kam ta tabbata duk abin da Hasiya ta fada akan wannan saurayi mai kyawun dan maciji gaskiya ne. Ummi ta dubeshi ido da ido ta ce. "Amma bai kamata ba ace ka saki Mabruka, dubi fa son da na ga tana yi maka Anas yanzu kai ko tausayinta ba ka ji?" Anas ya fashe da tattausar dariyar da ya sha satar zuciyar yan mata da ita ya ce. "Don me zan tausaya mata bayan tana son ta raba ni da ke." Ummi ta sake dubansa ta ce "Anas, wai me ya sa ka ke kaunata?" "Saboda kina da masifar kyau Ummi, ko ke ba kya ganin kanki ne." "Shi kenan abin da ya sa ka ke kaunata?" Anas ya gyada kai sannan ya dube ta ya ce "Ke fa me ya sa ki ke kaunata?" Ummi ta dube shi na tsawon lokaci kana sai ta dauke kai gefe guda ta ce "A da dai saboda kana burge ni ne kawai idan na dubeka shi yasa nake sonka." Anas ya dubeta cikin mamaki ya ce "A yanzu fa?" Ummi ta girgiza kai ta ce "Ka daina burge ni Anas, kai bari in fada maka ma infact na tsaneka domin ka fiye son kanka." Anas ya ji wani abu kamar tafasasshen ruwa ya fara wanke masa fuska. "Ummi in wasa ne wannan ki ke yi dan Allah ki bari Ummi domin yana iya sa ni hauhawar jini." Ummi ta girgiza kai ta ce "Ban taba yin wasa da kai ba, wadanda suka sha wasan da kai dai sun yi, irin su wadannan." Ta zaro hoton da Hasiya ta ba ta, ta mika masa. Anas ya karba hannu na rawa, nan da nan sai ya ji kwalla na kokarin kwace masa. "Haba Ummi, yanzu wannan yar iska ce za ta rabani da ke'" Ummi ta kuma girgiza kai ta ce "Ka da ka sake daukar alhakin baiwar Allah wanda ka dauka a da ma ya ishe ka wallahi babu ruwanta a cikin wannan zance." Anas ya yaga hoton dake hannunsa gida biyu a fusace yace. "To idan ba ita ba ce me ya sa za ki ce kin tsaneni Ummi? Me ya sa! Na dauka ke ki ka rubuto min a takarda kina kaunata ??"TSOHON ALKAWARI-19 KARSHE . Na dauka ke ki ka rubuto min a takarda kina kaunata?" "Wannan da ke nan Anas jiya na sake shawara ka san duniya juyi- juyi kullum da irin abin da take zuwa" Anas ya matso kusa da Ummi cikin kaduwa ya ce cikin karyayyiyar murya "Na ji na yarda Ummi kin tsane ni amma ina son don Allah ki taimaka ki fada min mene ne dalilin da ya sauya miki ra'ayi a kaina?" "Yanzu ka yi tambaya?" Ummi ta ce tana ja da baya cikin shirin shigewa gida "Abin da ya bani tsoro da kai Anas guda daya ne jal shi yasa na tsaneka akan dole" "Mene ne." Anas ya tambaya kusan cikin kuka. "Ka da ka bada yan maza Anas yanzun nan zan fada maka" Ta dan yi shiru tana gyara lullubin koren gyalen mai shara-shara da yake kanta sannan ta dube shi ta ce "Ga ni na yi Anas aurenka yana da hadari" "Saboda me Ummi? Saboda me ki tuna fa ni mai kaunar ki ne" "Na yarda Anas kana kaunata" Ummi ta ce cikin murmushi "Amma abin da na yi tunani shi ne, duk mutumin da bai tausaya wa zuciyar gurguwa abin Allah sarki ba to kuwa ba zai taba tausayawa mai kafafu kamata ba" Ta juya cikin sauri ta shige gida ta bar Anas sororo a tsaye yana lissafin irin asarar da ya yi . Sidi mai jaka ya mike tsaye ya yi doguwar mika ya ce "Nas labarin nan fa ya kare in kuma ba so ka ke in shiga yi maka karya ba ka san kuwa karya LINZAMIN SHAIDAN CE" . "Haba Baba Sidi ai ba ka fada min yadda Mabruka ta kare da cikin ba" Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi ya ce "Nas kenan daman da gangan na kyaleka na dauka za ka mance da sauran bakin zaren labarin da muka bari bamu dinke ba amma tunda ka tuna bari in dinke ma shi a gurguje Sidi mai jaka ya gyara tsayuwa ya ce "Nas watanni shida sun shude kamar wasa an daura auren Abdulmalik da Ummi har ma tana da ciki wata dayashi kuwa Anas ya koma matsiyacinsa yan kudin ma da suka rage a asusunsa duk ya kashesu a banza domin dan zaman da ya yi da mabruka ya yi sabo da jin dadi Haka nan ma Mabruka ta haifarwa Anas wata kyakkyawar ya mace amma kwanakinta bakwai a duniya ta rasu. Anas ya yi ta rusa kuka shi kadai a daki domin ya so a ce ta rayu don ko banza dai in Mabruka ta mutu yar ce za ta gaji duk dukiyar shi ko yana iya zuwa ya karbe yarsa da dukiyarta ka ga ya zama miloniya kenan . Sidi mai jaka ya dubeni cikin murmushi ya ce Nas wato mutum dai sai dai ka bar shi da halinsa amma hali zanen dutse ne" "To yanzu ina Anas din yake?" Na tambaye shi "Nas kenan kai dai ka cika son jin kwakkwafin labari na dai fahimci so ka ke ka sa dattijo ya shiga karya" Anan sai na fashe da dariya Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi ya ce "Na ji an ce wai Anas din ma ya samu tabin hankali tun da yar jaririya da aka haifa masa ta mutu amma fa labarin wai ne har yanzu bani da tabbacinsa" Sidi mai jaka ya dubeni kana sai ya juya ya ce "To Nas Allah ya dada sada mu da alheri sai wata rana" . Dattijon ya shige cikin gida abinsa ya bar ni nan tsaye ina kokarin hada zarurrukan labarin . KARSHE . An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7