Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
ya dafa cikinsa da busassun yan yatsunsa gami da dan runtse, idanu sannan sai ya dubeni ya ce. "Sannu a hankali Nas, Anas ya tuko motar zuwa inda suke ya tsaya, lokaci guda kuma ya sauke gilasan motar. Cikin sauri Ummi ta nufo gindin tagar motar, Abdulmalik na biye da ita a baya, a lokaci guda kuma ya ji wani matsanancin bakin ciki ya lullube shi Na shiga uku ya ce a cikin zuciyar sa, Ashe Anas din shima kyakkyawa ne." "Anas..." Mabaruka ta kira sunansa a kunya ce. "Ummi..." Shima ya kira sunanta, sai dai har yanzu zuciyarsa na bugawa domin bai fahimci matsayin saurayin dake biye da ita a baya ba. Ummi ta lura tun da ta zo gurin idanun Anas akan Abdulmalik suke don haka sai ta yi sauri ta dube shi ta ce. "Anas...ga Yayana Abdulmalik ba ku gaisa ba." Sannan sai ta juya ta dubi Abdulmalik da faffadan murmushi ta ce. "Yaya Abdul...ga Anas dina da nake baka labari yau dai Allah ya hada ku." Cikin sauri gami da ajiyar zuciyar jin dadi abin da ta ce, Anas ya bude kofar motar ya fito, sannan ya mikawa Abdulmalik hann. "Yaya barka da yamma." Samarin biyu suka cafke hannun juna, kana suka dubi juna ido da ido, Abdulmalik ya riga ya san matsayin Anas a gurin Ummi, to sai dai shi Anas bai san matsayin Abdulmalik ba a gurin Ummi, duk da yake dai ta ce dashi wai Yayanta ne, akwai wani abu a yanayin fuskar Abdulmalik da ya jefa shakka cikin zuciyar Anas, tabbas abin ya jefa shi cikin kaduwa, domin irin yanayin da yake gani a fuskar Abdulmalik, ya sha ganinsa a fuskokin gomomin samarin da ya sha kwace musu yan mata a baya, to amma da yake a yanzu bashi da wata kwakkwarar hujja abar dogaro, sai ya dubi Abdulmalik ya kuma cewa. "Ya ya ayyuka...ko kuma ya ya karatu zan ce..." "To, karatun dai...ai har yanzu yayan naka dalibi ne." Abdulmalik ya ce a karo na farko. Aka sake yin shiru na yan mintuna, Ummi na kallon Anas, shi kuma na kallon Abdulmalik, Ummi ce ta fara bata shirun. "Yaya...Abdulma lik yau dai Allah ya hadaku da Anas din da nake baka labari." Ba na fatan na kara haduwa da shi. Abdulmalik ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai ya ce a fili. "Malam...Anas, ta sha bani labarin ka...ga shi sai yau Allah ya hadamu." Ya dan yi shiru yana duban Ummi kana sai ya ce. "Daman zuwa na yi mu gaisa da wanda kanwata ke so...ni zan koma, gara na barku ku dan zanta." Yana gama fadin haka sai ya fara juyawa da baya. Ummi ta dubeshi cikin mamaki- mamaki kaduwa-kaduwa, domin ta fahimci lallai yana cikin damuwa. Na shiga uku. Ummi ta ce a ranta.TSOHON ALKAWARI-15 . Ummi ta dubeshi cikin mamaki- mamaki kaduwa-kaduwa, domin ta fahimci lallai yana cikin damuwa. Na shiga uku. Ummi ta ce a ranta. Yaya Abdulmalik jininsa bai hadu da na Anas ba. Ta kuma fadi cikin zuciyarta, sannan sai ta ce a fili. "Yaya Abdulmalik...ta fiya za ka yi tun yanzu?" "Eh mana, ai gara na ba ku waje ku yi hirar ku...na sa kannena a gaba?" Ya fadi gami da jeho wani takurarren murmushi. To sai dai kuma ba Anas ba wanda tuni daman ya gama fahimtar Abdulmalik, hatta Ummi ta gane cewa murmushin yake ne tabbas ta san yayanta yana cikin damuwa. "Sai an jimanku..." Abdulmalik ya kuma fada sannan cikin sauri ya juya ya nufi gidan su. Suka zuba masa idanu har sai da ya shige cikin gidan ba a samu wanda ya ce kala ba. Ummi ta yi ajiyar zuciya sannan ta sunkuyar da fuskarta akan kirjinta cikin yar damuwa. "Ya ku ke da shi?" Anas ya tambayi Ummi yana dubanta cikin zargi, wani bakin kishi na kokarin tsaga masa zuciya. "Yayana ne." Ummi ta bashi amsa kai tsaye lokaci guda kuma ta kalleshi ido da ido. Anas ya dubi fuskarta na tsawon lokaci yana nazari a cikin duhun daren, abin ya bashi mamaki domin a yadda ya ga tana kallonsa da karya take yi ba za ta taba iya hada idanu da shi ba. To amma me ya sa kyakkyawan saurayin mai hancin larabawa yake irin wannan dabi'a haka kamar wanda yake tsakiyar kogin begen Ummi? Tambayar kenan da Anas ya kasa amsawa kansa. "Kina nufin yayanki na uwa daya uba daya ko kuwa dai kawai yaya ne na yan uwa." A wannan karon Ummi ce ta dube shi da wani tattausan murmushi ta ce. "Oh...Anas kenan, lallai na fahimci kai ma kana da kishi kamata." Ta dan yi shiru lokaci guda kuma ta dafa kofar motar dake bude da hannunta na hagun ta dubi Anas ta ce. "Ka da ka bari kishi ya hana mana jin dadin hirarmu ta farko da kai." Cikin sauri Anas ya sassauta fuskarsa duk kuwa da cewa har yanzu zuciyarsa tafasa take yi. "Ki gafarce ni Ummi, masifar sonki ce ta yi min yawa a cikin zuciya, irin yadda nake kaunar ki ko kuda ya sauka a kanki sai na yi kishi da shi...to ballantana kuma wannan kyakkyawa da ki ka ce wai yayanki ne." Ummi ta fashe da wata zazzakar dariya, wacce sautinta ya sa wasu yan gajerun samar dake can gefe guda suna jiran fitowar tasu budurwar suka juyo cikin sauri suka kalli bangaren da su Ummi da Anas suke. "Kai Rabe...ka ji wata cika tana dariya kamar ana busa sarewa." "Ummi kenan." Daya saurayin ya ce da abokin sa "Duk unguwar nan babu cikar da ta kai haduwar ta, ba ka ganin gashinta daga nan har sheki yakeyi kamar madubi, to don ma da daddare ne da rana ce in ka kalli gashin kanta sai ya dauke maka idanu." "Allah mutumi na...to ko barin wannan kucakar zamu yi mu koma can mu gwada sa'ar mu." Daya saurayin ne yake fadawa Rabe haka. "Rufawa kanka asiri." Rabe ya ce da saurayin. "Ummi me shegen girman kai kamar ibilishiya tun da nake ban taba ganinta da wani saurayi ba sai yau...kuma in ban da rigimarka ma ina kai ina Ummi? Zoben dake danyatsanta guda daya fa sai ya yi ma dinkin sallah karama da sallah babba har sau uku, kuma ya bar ka da ya canjin kashewa...samar i yan hutu ma masu kafafu hudu da iya kwalisa ba ta sauraresu ba sai kai mai katon kai da fadi kamar faranti." "Ka ga bana son iskancin banza...kai din kyau ne da kai ko dan ba ka kallon madubi." Saurayin ya ce da Rabe a kufule. A daidai lokacin da Rabe ya fara kokarin mayar da martani ne to, kofar wani gida ta bude sannan wata yar gajeriyar budurwa fara ta fito cikin sauri ta nufi inda su Rabe suke, ko da ta zo giftawa ta kusan inda su Ummi suke, sai ta tsaya turus ta Kalli Anas sama da kasa sannan ta dauke kai ta dubi Ummi ta ce. "Yaya Ummi ina wuni." "Lafiya kalau Hasiya...ya ya ki ke?" "Lafiya nake." Shiru Hasiya ta dan yi sannan sai ta sake duban Fuskar Anas ta ce. "Lalatacce mayaudari nan kuma ka dawo?" Anas ya ji gabansa ya fadi sannan zuciyarsa ta harzuka ya dubi budurwar a kidime yana kokarin tuna inda ya san ta. "Ai ba za ka iya tunani ba mayaudari tun da muna da yawa a gaban ka." Tana gama fadin haka sai ta juyo ta dubi Ummi ta ce. "Ki bi a hankali Yaya Ummi kada ki sake dashi domin ba zan so ace kin fada tarkon sa ba." Tana gama fadin haka sai ta juya gami da cewa. "Bari in je in fatattaki wadancan yan iskan...duk sahunsu guda da wannan da yake gabanki, kar ki yarda da shi mai kyan dan maciji ne."***** . Ummi ta yi sororo a rude tana kallon Anas yayin da shi kuma Anas ya dubeta a tsorace baki na rawa ya ce. "Ummi...wannan kuma wacce mahaukaciya ce?" Ummi ta yi ajiyar zuciya a kidime kana ta ce. "A iya sani na dai tana da hankali." Ta dan yi shiru, sannan sai ta dauke hannunta daga kan kofar motar. "Daman kun dade da sanin juna ne kai da ita?" Cikin sauri Anas ya girgiza kai "Ko kusa ko alama ni ban ma taba ganinta ba wallahi sai yau." Ga mamakinsa sai ya ga Ummi ta zunkuda kafada sannan ta haskake shi da murmushi ta ce. "Me yiwuwa wani ne mai kama da kai ya taba yaudarar ta na san halin Hasiya wani sa'in rudaddiya ce." "Yauwa ko da na ji fa" Anas ya ce gami da ajiyar zuciya, sannan ya share gumi lokaci guda kuma ya yi sauri ya sauya zancen da cewa. "Ummi wai don Allah uwa daya uba daya ki ke da Abdulmalik." "Ummi ta fashe da wata sassanyar dariyar jin dadin ganin Anas yana kishi a kanta. "Har yanzu dai ba ka yarda ba kenan." "A'a ba wai ban yarda ba ne...amma ni abin ne yake bani mamaki, ni sai na ga kamar shima sonki yake." Ummi ta girgiza kai ta ce. "Anas, wallahi yayana ne, uwa daya uba daya, ni dai abin da nake tunani me yiyuwa wani abu ne daban yake damunsa ko kuma ganin zai tafi ya bar ni ni kadai ka san tun muna kanana bama rabuwa tare muke duk inda zamu tafi yawan lokuta ma barci ne ke rabamu to ka san ban taba yin saurayi ba sai a kanka ina jin abin da yake damunsa kenan." Anas ya karkada yan makullayen dake hannunsa ya ce, "Na yarda da ke Ummi." Sannan sai ya hango inda su Hasiya da samarinta suke tsaye gabansa na faduwa, haka nan wani zazzafan gumi ya fara sartu akan doron wuyansa tabbas sai yanzu ya tuno ta. A daidai lokacin ne to ya dubi agogo sai ya ga ashe har goma na dare ta wuce. Sannan ne to ya ji gaba daya duniyar nan ta yi masa bakinkkirin. Mabaruka ce ta fado a ransa kwata-kwata ganin kyakkyawar fuskar Ummi ya gama mantar da shi komai a wannan lokacin baya iya ganin komai sai Ummi. "Ummi ni zan tafi...sai yaushe kenan?" Ummi ta dubi fuskar Anas sai ta ga duk ta jike da gumi nan da nan ta fahimci halin da ya ke ciki. "Oh...na san fa ashe tana can tana jiranka ko?" Anas ya sunkuyar da kai "Ummi tun da na yi aure ban taba samun farin ciki kamar na yau ba...dan haka ina rokonki da ki yi shiru da bakin ki kada ki bata min farin cikina na wannan rana ta farin ciki." Yana gama fadin haka sai ya shiga motar ya rufe kofa sannan ya sako kansa ta tagar motar ya ce. "Ummi tun da nake ban taba kaunar wata mace a duniya da gaske har zuciyata ba sai a kanki." Ummi ta dan rankwafa kadan ta ce "Na yarda da kai Anas...sai yashe za ta sake bamu ranar haduwa?" "Wa ki ke nufi? ban fahimce ki ba." "Matarka mana Mabaruka na yi mamakin ma yadda aka yi ta barka kazo." Anas yaji kamar ta watsa masa wuta a fuska. "Ba ta isa ta juya ni ba Ummi duk lokacin da naga dama zan iya zuwa gurin ki." ya dan yi shiru sannan sai ya ce "Ki jira ni zan zo jibi" A haka ya tuka motar ya fice daga layin Ummi ta bi motar da kallo ga mamakinta sai ta ji gaba daya ma ta shiga cikin rudani domin a da kafin ya zo ta dauka idan ya zo ba za ta iya rabuwa dashi ba sai da kuka saboda tsabar kaunar da take yi masa amma a yanzu ta shiga wasi-wasin zuciya, bata san mene ne dalili ba. A can cikin motar Anas ya ji hawayen bakin ciki ya fara sartu akan kuncinsa Shin ya ya abubuwa zasu zama haka ne ya ya aka yi duk sa'a ta ta kwace min, don me yar iskar nan Hasiya za ta yi min haka. A da kafin Anas ya zo ya dauka zai bar gurin Ummi dauke da farin cikin da bai taba jin irinsa a duniya ba To amma a yanzu wani karamin digo na kalanzir ya riga ya fada a cikin kokon ruwan shan kaunarsa ya kuma ji a jikinsa cewa in ba wani abu daga Allah ba dan digon kalanzir din nan sai ya gurbata dukkan illahirin dandano na ruwan shan kaunarsa A karo na farko tun bayan da ya girma sai Anas ya fara kokarin yin addu'a to sai dai kuma har sa'ar da ya fara hangen fitulun lantarkin da ke makale a jikin katangar gidan Mabaruka gurguwa bai iya tuno koda addu'a daya ba *** Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya harari kwanon tubanin da ke gaban sa ya mika busassun yan yatsunsa guda uku ya cafko wani katon tubani mai siffar kwado ya dago shi sama yana nazarinsa sai da ya dade a haka sannan ga mamakina sai na ga ya mayar da tubanin cikin kwanon ya dubeni cikin nadama ya ce "Nas cikina ya gama cika amma har yanzu bakina na muradin ci gaba da taunar tubanin nan." "Haka ne" na ce da shi "Ci gaba Baba Sidi na matsu in ji karshen labarin nan...sai na ji duk ma ka dada ruda labarin." Sidi mai jaka ya saki wata kekasasshiyar dariya.TSOHON ALKAWARI-16 . "Ci gaba Baba Sidi, na matsu in ji karshen labarin nan...sai na ji duk ma ka dada ruda labarin." Sidi mai jaka ya saki wata kekasasshiyar dariya ya dubeni ya ce. "Ai Nas zararrukan labarin ma sun zo karshe...bari na yi sauri na saka maka na karshe sai mu hadasu da sauran zararrukan labarin mu daure." "Haka ne." Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dubi kwanon tubanin cikin takaici ya yi kamar zai dauki daya sai dai ya sauya shawara ya dubeni ya ce. Nas, tun karfe takwas na daren ranar da Anas ya tafi gurin Ummi, Mabaruka ta caba kwalliya, sannan ta sa hadiman gida suka shirya musu kayan shaye-shaye da tande-tande na musamman. Shiru-shiru karfe tara ta wuce babu Anas babu labarinsa, wannan shi ya sa Mabaruka gurguwa rarrafawa gaban dan gajeren madubin da aka yi mata na musamman ta dubi mummunar fuskarta a jiki sai ta ji kamar ta fashe da kuka, domin ta lura duk kwalliyar da ta yi ta damalmale. Cikin sauri ta rarrafa zuwa bandakinta na musamman ta kuma kwashe mintuna talatin tana wanka gami da shafe-shafe da goge-goge, fitowarta ke da wuya daga bandakin sai tangamemen agogon azurfa wanda mahaifiyarta ta bata ya dauki rurin karfe goma na dare. "Na shiga uku." Mabaruka ta fada a fili kai ka dauka tare suke da wani a dakin "Me ya tsayar da Anas ne har yanzu?" Mabaruka ta tambayi kanta, Nan da nan sai ta ji jikinta ya dauki rawa, zuciyarta ta fara harbawa sannan sai ta fara zargin kanta da wauta. Dan me zan bar shi ya tafi shi kadai? Ta kuma tambayar kanta to sai dai wannan karon Mabaruka na da amsar tambayar cikin zuciyar ta. Anan sai Sidi mai jaka ya dan yi shiru yana kallona, sannan sai ya ce. "Nas akwai wani sirri da Mabaruka take son sanar da Anas tun kusan kwanaki uku da suka shude amma yar rashin jituwar da suka samu a daren da aka yi liyafar nan shi ya sa ta boye masa. "Wanne sirri ne wannan?" Na tambayi Sidi mai jaka. "Bi ni a hankali Nas, ni ma zakin mazallako ne kawai da daga ciki yana rokon uba kwabo shi ya sani azarbabin fada ma, amma da sannu zan kawo ka kan zancen, kai dai bani aron hankalin ka mu koma kan zaren labarin da muke. "Na baka." Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dan faki idanuna sannan sai ya mika hannu ya zaro tubani guda ya jefa a bakinsa kana ya ci gaba da cewa. "Abin da ya sa Mabaruka ta bar Anas ya tafi shi kadai shi ne ta san cewa Anas fa ba kaunarta yake yi ba ko kankani, ita ce dai ke kaunar sa, haka nan ta tabbata muddin ta uzura da manne masa, to za ta sa ya kuma tsanarta a cikin zuciyarsa wanda hakan na iya kawo sanadiyyar rabuwarsu. Duk da irin kuri da cika baki da mabaruka ke masa cewa idan ba zai iya ba ya ajiye mata duk dukiyarta ya bar mata gidanta, babu abin da Mabarukan take tsoro da fargaba irin rabuwa da Anas, domin ta san idan ta rabu da shi tana iya haduwa da cutar da za ta kawo ajalinta a kusa, wannan dalili shi ya sa duk da tana zargin karya Anas yake yi ba gurin abokansa za shi kawai ba Mabaruka ta kyale shi ya tafi shi kadai, tare da fatan me yiwuwa idan ta bashi yana yan walawa shi kadai yana iya dan kaunar ta ko daidai da kwayar zarra ne, haka nan tare da karfin gwiwar cewa idan ya dawo zata fada masa abin me yiyuwa zai iya sa shi farin cikin da dole ne ma ya tarairayata ko da bai so ba. Wannan shi ya sa Mabaruka ci gaba da kwalliya tun magriba har zuwa karfe goman dare bata gama ba. "Bari in sa wannan shudiyar rigar me yiwuwa ta burgeshi, na ga ran nan da na sa irin ta kamar yana satar kallona." Mabarua ce ta ci gaba da zance da kanta sa'ar da take kokarin sa rigar. Bayan ta gama sai ta sake rarrafawa zuwa gaban madubi ta kuma duban kanta a karo na goma sha uku. Abin da ta gani ya dan faranta mata rai babu dai yabo babu fallasa, domin ba katon goshinta ba kawai, hatta dan tababben hancinta mai kamar kataura ya dan mike sakamakon matsar da ya sha a hannunta, haka nan fuskarta na dan sheki, to sai dai kuma ta fuskanci kamar hoda ta so ta yi mata yawa a fuskar Wannan ya sosa mata rai, dan haka a fusace sai ta mika hannunta zuwa kan gado ta janyo wani abu da take tsammanin me yiwu rigarta ce, da zummar ta yi sauri ta goge hodar dake fusakarta domin duk sosunan kwalliyar sun hade da kalolin hodoji iri-iri sun baci. Janyo abin ke da wuya sai ta ga ashe wandon Anas ne. Cikin farin ciki sai ta kara wandon mijin nata akan fuska, sannan ne fa kudundunnaniyar takardar fara ta fado daga cikin aljihun wandon. Mabaruka ta ji gabanta ya fadi ras, tun kafin ma ta dauki takardar. Hannunta na rawa ta dubi takardar cikin tsananin zargi sannan sai ta jefar da wandon gefe guda ta dauki takardar ta fara karantawa.... . ".....Ni ce Ummi." Mabaruka ba ta iya maimaita karatun takardar a karo na biyu ba, sai ta kifa kai a jikin gadon ta fashe da kuka mai karfin gaske wanda har rawar da gangar jikinta ke yi ta sa gadon shima ya dauki rawa Kofar dakin ta bude a hankali sannan Anas ya shigo fuska a turbune shigowarsa ke da wuya sai ya tsaya turus kamar wanda ya ji shi cikin fasassun duwatsu a cikin duhun dare. "Ku...kukan me ki ke yi Mabaruka ba gani na dawo ba." Mabaruka ta dago kai jiki na rawa cikin kuka ta ce. "Mene ne amfanin dawowar ka tsohon mayaudari! Ai sai ka koma can gidan su Ummin ka kwana a can...!" Ta kara fashewa da kuka. "Ban fahimci abin da ki ke nufi ba." Anas ya ce cikin shakka, domin bai san munafukin da ya fada mata daga gidan su Ummi yake ba. "Ya za a yi ka fahimce ni, tun da ka tsaneni! Ba ka kaunata!! So kake na mutu da bakin cikin kaunarka ko Anas?" Hakan da ta fada sai Anas ya ji tausayinta ya kamashi. Ga mamakinsa sai ya ga Mabaruka ta rarrafa inda ya ke tsaye ta rike kafafunsa cikin kuka ta ce. "Anas....don Allah ka yi min rai ka kaunace ni ko da daidai da na kwana daya ne... Haba Anas don ka ga ni mummuna ce...dan ka ga ni gurguwa ce....shi ne kake son kashe ni." Ta sake fashewa da kuka. Anas ya ji kwalla ta zo idanunsa, cikin sauri ya durkusa a gabanta ya dafe kanta. "Daina kuka Mabaruka bari in yi miki bayanin abin da ke zuciyata." "Ba sai ka yi ba Anas, na ri ga na sani...ni dai ina rokon don Allah ka kauna ce ni kada ka sa bakin ciki ya kashe ni, ni da danka da ke cikina!" Anas ya ji kamar an zunguri zuciyar sa da allura. "Wanne dana ki ke nufi a cikinki?" Ya tambayeta a rude. Mabaruka ta dada kankameshi sannan ta fashe da kuka ta ce. "Anas tun shekaran jiya na ke son fada ma likita na ya sanar da ni ina da ciki wata uku!"*** Na dubi Sidi mai jaka a rude nace "Haba Baba Sidi ya ya tun dazu ka ke labarin nan amma ba ka ce tana da ciki ba sai yanzu?" Sidi mai jaka ya dubeni da busasshen murmushinsa ya ce. "Nas ke nan, abin da ba ka sani ba shi ne idan na fada maka tun dazu cewa tana da ciki ai na ragewa labarin dadi, haba Nas kai sai ka ce ba marubuci ba. Bari in sako maka zaren labari na karshe sai in hadasu da wannan na kulla ko ma kai ga karshen labarin nan." "Haka ne." Na ce dashi ba musu. Yauwa Nas, ta yanzu ina son ka sa a zuciyar ka cewa ga Ummi nan ta fito daga dakinta a rude, wannan kuwa fitowa da ta yi a washe garin ranar da Anas ya zo mata zance ne. Ummi ta dubi dan karamin agogon da ke sanye a santalelen hannunta, karfe hudu da mintuna biyar agogon ya nuna. Cikin sauri sai ta nufi kofar dakin Abdulmalik ta kuma kwankwasawa, a karo na goma sha takwas a ranar. Shiru ba a amsa ba, Ummi ta dada rudewa. Shin ina Yaya Abdulmalik ya tafi ne tun da sassafe har yanzu bai dawo ba. Abin da ya dada tayar mata da hankali shi ne a daren jiya sa'ar da ta shigo gida bayan sun rabu da Anas, ba ta tsaya a ko ina ba sai dakin Abdulmalik, domin tana da tambayoyi masu yawan gaske da take bukatar amsarsu. Lokacin da ta isa kofar dakin sai ta hango wutar dakin a kunne take, to sai dai kuma kamardakin a rufe. Me yiyuwa har ya yi barci. Ummi ta ce a ranta, to amma sa'ar da ta matsa kusa da kofar dakin sosai, sai ta ji motsi a cikin dakin kamar ana taba takardu. "Salamu alaikum." Umma ta yi sallama lokaci guda kuma ta tura kofar dakin. Ga mamakinta sai ta ji kankam kofar dakin a rufe take. "Yaya Abdulmalik bude min na dawo" Ummi ta ce Shiru ba a amsa ba "Yaya Abdulmalik." Ta sake kiran sunan a karo na biyu "Ina jin ki Ummi..ki bari sai gobe ma hadu" Ummi ta ji gabanta ya fadi nan da nan ta ji jikinta ya dauki rawa kamar zazzabi zai rufe ta Wannan shi ne karo na farko da yayan nata ya fara fushi da ita amon muryarsa ya fadi sakon da ke zuciyarsa "Yaya Abdulmalik..me na yi maka? Ka bude min mana" "Babu abin da ki ka yi min Ummi ta fi dakinki kawai ma hadu gome...yanzu wasu yan rubuce- rubuce nake yi bana son a dame ni" ummi ta ji kamar ya watsa mata wuta Cikin kunan rai ta jingina bayanta a jikin kofar dakin idanunta suka fara ambaliyar kwalla na mintuna biyu sannan a hankali sai ta nufi dakinta domin ta tabbata ba zai bude mata kofar ba Tana zuwa dakinta sai ta fada akan gadonta ta fashe da kuka tabbas jinin Abdulmalik bai hadu da na Anas ba Ummi ta fada a ranta*** Na dubi Sidi mai jaka a rude na ce A wan nan lokacin ne to kalaman Hasiya suka fado mata "Ki bi a hankali Yaya Ummi kardai....TSOHON ALKAWARI-17 . A wan nan lokacin ne to kalaman Hasiya suka fado mata "Ki bi a hankali Yaya Ummi kada ki sake dashi domin ba zan so ace kin fada a tarkon sa ba" Shin ko abin da ta fada gaskiyar ne, shin ko Yaya Abdul Shima ya san halin Anas ne shi yasa yake fushi da ni. Ummi ta kuma tambayar kanta, sannan sai ta dada fashewa da kuka, a haka barci ya dauketa. To amma kafin barcin ya saceta sai da ta yiwa kanta alkawarin cewa in dai har alakarta da Anas ne ya batawa Abdulmalik rai, to babu mamaki za ta rabu da Anas duk kuwa da irin kaunarsa da take yi, domin da ta bakantawa yayanta Abdulmalik gara ta rabu da abin da take kauna. Washe gari da sassafe, tana idar da sallah sakamakon makara da ta yi da bata tashi da asuba ba, sai ta nufi dakin Abdulmalik cikin sauri ta tura kofar dakin babu ko sallama sai ta ji kofar a rufe. Cikin sauri ta juya da baya a kidime ta nufi dakin mahaifiyarsu. "Mama ina Yaya Ya tafi?" "Ya fita tun da duku-duku nima ban san ina za shi ba, ya dai ce dani ba zai dawo ba sai can yamma. Tun daga wannan lokaci Ummi ke ta faman safa da marwa daga dakinta zuwa dakin Abdulmalik har zuwa yanzu babu shi babu alamarsa. Hawayen bakin ciki ya yi sartu akan kumatunta. Ummi ta yi sauri ta goge sannan ta nufi dakinta ta zauna a bakin gado ta kurawa kofar dakin nata idanu cikin takaici. Wannan shi ne lokaci mafi tsayi a rayuwarta da ta taba zama ita kadai ba tare da dan uwanta Abdulmalik ba a kusa da ita. Tana nan zaune ta zubawa kofar dakin nata idanu tana jiran ta ga ta inda Abdulmalik zai bullo, sai aka yi sallama. Da farko muryar mahaifiyarta ta fara ji daga waje tana cewa. "Ki shiga tana ciki." Cikin sauri Ummi ta goge hawayen da ke kumatunta ta mike tsaye, a daidai lokacin da ta ji an sake cewa. "Salamu alaikum." Sannan sai ta ji an nufo kofar dakin. Ummi ta dubi Hasiya sa'ar da ta shigo dakin. "Sannu da zuwa Hasiya dama wallahi ina son ganin ki." "Ni ma son ganin naki ne ya kawo ni Yaya Ummi." Hasiya ta ce lokaci guda kuma ta zauna a bakin gadon ta dubi Ummi. "Ga ni me ki ke son yi min?" "Ke ma ai kin sani." Ummi ta ce tana dubanta "Wai dan Allah abin da ki ke fada min jiya a gaban wannan saurayin nawa gaskiya ne?" Hasiya ta fashe da dariya ta ce "Oh! Yaya Ummi kenan, ta wallahi kima daina kiransa da suna saurayin ki...don kin ga nima din nan babu irin abin da bai fada min ba amma daga karshe ya koma kan wata kawata Samira..wallahi sai da na yi rashin lafiya da kyar Allah ya yaye min masifar kaunar sa daga zuciyata na huta." "Wai ki na nufin ki ce saurayin ki ne da?" Ummi ta tambaya. Kina shakka kenan to bari ki ga zahiri." Hasiya ta bude cikin jakar da ke kan cinyarta sannan ta zaro wani hoto ta mikawa Ummi, "Kalli wannan." Ummi ta zurawa hoton idanu cikin kaduwa. Tabbas Anas din ta ne, shi da Hasiya a bakin otel din da suka yi liyafar bikin zagayowar ranar haihuwar Mabaruka gurguwa, abin da ya fi kona mata rai a hoton shi ne, hannun Anas na hagu dare-dare yake akan kafadar Hasiya. Hannun Ummi na rawa ta mikawa Hasiya hoton. "Ungo abin ki." Hasiya ta girgiza kai ta ce "Ki rike shi a gurinki, idan ya dawo ki nuna masa hoton ki tambaye shi me ya sa bai aure ni ba." Hasiya ta mike tsaye ta ce "Bari in karasa gida Yaya Ummi...daman daga unguwa nake shi ne na ce bari in biyo ta nan domin ba zan bari wannan kyakkyawan macijin ya sake saran yar uwata mace ba. Sai an jima." Da haka ta fice daga dakin ta bar Ummi cikin kaduwa dauke da hoton a hannunta, ba tare da ta iya yi mata ko da rakiya ba. Bayan ta kalli hoton na mintuna biyar sai ta mike tsaye, sannan ta daga karkashin matashin kanta ta jefa hoton, kana sai ta mike cikin sauri ta nufi dakin Abdulmalik domin ta sake dubawa ko ya dawo. Tana zuwa kofar dakin sai ta sake turawa babu sallama domin a tunanin ta idan ta yi sallama Abdulmalik ya ji muryarta me yiyuwa ba zai bude ba, zuciyarta na harbawa das! Das!! Das!!! Ta shiga dakin, tana shiga sai ta yi turus, Abdulmalik baya cikin dakin. Sannu a hankali ta shiga dakinta jikinta na rawa sannan ne to ta hangi tarin takardu farare an cikesu da rubutu akan wani dan teburin gilashi dake kusa da gadon Abdulmalik, sannan sai idanunta ya kai ga wata takarda fara kwaya daya jal akan gadon a jikinta an rubuta kamar haka;- Masoyiyata Ummi ki karanta takardun dake kan teburin nan domin amsoshinki duk suna cikin takardun..." Hannunta na rawa ta dauki takardar ta juyata a hannunta sannan sai ta dauki sauran takardun dake kan teburin jiki na rawa ta

Chapter 6 of 7