Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
dawo, Abdulmalik ya ji shigowarta babban falo dan haka sai ya ji wani farin ciki ya lullubeshi domin tuntuni ya matsu da ya ga ta dawo domin baya iya yin sama da sa'a biyar bai ganta ba Wani sa'in ko a makaranta yake sai ya yi ta bugo mata waya duk bayan sa'a guda dan kawai ya ji muryarta Don haka sa'ar da ya ji motsin dawowar Ummi sai ya ajiye takardun bokon da yake karantawa ya lumshe idanu yana jiran shigowarta domin ya san alkawari ne sai ta shigo dakin. Tsawon lokaci shiru babu motsin UmmiTSOHON ALKAWARI-12 . Domin ya san alkawari ne sai ta shigo dakin. Tsawon lokaci shiru, babu motsin Ummi sannu a hankali har mintuna talatin suka shude bata shigo dakin ba. Abdulmalik ya mike tsaye cikin tsananin damuwa da mamaki domin a iya saninsa da Ummi ko kayan jikinta ba zata sauya ba sai ta zo gare shi su yiwa juna Sallama Cikin sauri Abdulmalik ya fita daga dakinsa ya ratsa ta falo ya nufi dakin Ummi. Abdulmalik ya dan kwankwasa kofar dakin a tausashe sannan sai ya yi sallama ya shiga. Ummi na kwance akan gado, sanye da kayan da ta fita da su walimar, ko cire su bata yi ba, ta kurawa saman dakin idanu bata ko kiftawa kamar mai kallon allon sinima. Abdulmalik ya tsaya cak a tsakiyar dakin kamar an dasa shi, ya kurawa Ummi idanu cikin tsananin mamaki da kaduwa domin ya fahimci ashe Ummi bata san ma ya shigo dakin ba. "Ummi..." Ya sake maimaitawa a karo na biyu kamar mai biya karatu. Ummi ta juyo firgigit ta tashi zaune akan gadon. Ta dubi Abdulmalik. "Tunanin me ki ke yi haka?" Ummi ta dubeshi da murmushi. "Ka yi hakuri don Allah Abdulmalik wallahi ban san ka shigo ba." Abdulmalik ya matsa kusa da ita ya zauna daga can nesa da ita a bakin gadon ya kura mata idanu. "Na ji shigowarki, ina ta jira ko za ki zo, ba ki zo ba shi ne na ce bari ni nazo da kaina na gani ko lafiya." Ummi ta sunkuyar da kai sannan ta yi ajiyar zuciya kana ta dago kai da murmushi ta dubi Abdulmalik ta ce. "Lafiya lau Yaya Abdulmalik bala'in gajiya na yi." Tun kafin ta gama fada Abdulmalik ya san karya take yi, domin alamun damuwar dake fusakarta tamkar bakin rubutu ne akan farar takarda. Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta sosu, bai ji dadin abin da ta fada ba, domi a duk iya tsayin zamani, tun ranar da aka haifeta ya fara daukarta, har zuwa yau bata taba fada masa karya ba sai yanzu. Abdulmalik ya dubi Ummi cikin shakka, ya girgiza kai ya ce. "Kada ki ce haka Ummi, ba gajiya ba ce kawai ke damunki akwai matsala ta daban." Ummi ta dubeshi da wani fatalwan murmushi akwai alamun kunya a fuskarta ta ce. "Gaskiya ne Abdulmalik wallahi akwai abin dake damuna, ka kuma yafe min dan Allah ka san ban taba yi ma karya ba sai yau..." Ta dan yi shiru tana murmushi sannan sai ta dada da cewa. "Yau din ma kunya ce wallahi ta sa ni yin karya." Abdulmalik ya yi ajiyar zuciya kana ya dubeta cikin shauki ya ce. "Na yafe miki Ummi...ai kin san duk laifukanki a gurina yafaffune har ma da wanda ba ki yi ba." Ummi ta yi dariya ta sake sunkuyar da kai Abdulmalik ya sake nazarin fuskar Ummi cikin damuwa ya ce. "Fada min sirrin dake zuciyar ki Ummi me ke damun ki ne?" Ummi ta dauke kai gefe guda na tsawon lokaci, haka nan a duk iya tsayin wannan lokaci akwai alamun murmushi-murmus hi da kuma damuwa-damuwa a fuskarta. Shi dai Abdulmalik ya kura mata idanu cikin mamaki bai tari numfashinta ba. Tsawon lokaci, sannan Ummi ta juya ta dubeshui, ta ce bakinta na rawa. "Yaya.....Abdul malik...wallahi irin abin da nake yawan karantawa ne a cikin littattafan labarai na Hausa ya faru a kaina." Abdulmalik ya ji gabansa ya fadi ras! Ya dubi Ummi. "Me ki ke nufi." Ummi ta dauke kai gefe guda a kunyace ba tare da ta hada idanu da shi ba ta ce. "Wallahi...wani na gani a gurin liyafar nan naga ya burge ni." Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta harba. "Har yanzu ban fahimce ki ba Ummi, waye wani, kuma ya burge ki kamar ya ya." Ummi ta sake dariya ta ce. "Yaya Abdulmalik ji na yi wallahi ina masifar kaunarsa a zuciyata, a yanzu din nan haka ji nake yi kamar mun dade da sanin juna." Ta dan yi shiru ganin Abdulmalik bai ce wani abu ba sai ta dada da cewa "Za ka yi mamaki idan na ce da kai Mabaruka ce kawai ta turani na yi kiransa." Abdulmalik ya dago kai ya dubeta da murmushin karfin hali, amma a badini tuni har zazzabi ya rufe shi "Ummi kenan. To yanzu ya ya za ki yi kenan? Kin ga mutum kin ce kina sonshi amma ba ki san ko wane ne shi ba ba ki san inda yake ba baki san ko da sunan shi ba." Ummi ta matso kusa da Abdulmalik ta ce "Ma'aikacin otal din da aka yi liyafar ne, na ji Mabaruka ta kira shi da suna ANAS!" Abdulmalik ya sunkuyar da kai Ummi ta dubeshi cikin damuwa. A tunaninta halin da ta tsinci kanta ciki ne ke damun Abdulmalik domin ta san irin yadda yayan nata Abdulmalik ke matukar sonta don haka sai ta ce dashi a tausashe "Ka da ka dami kanka Yaya Abdulmalik na san duk abin da ya shafe ni kai ya shafa. Ni dai abin da nake so shi ne ka tayani don Allah mu same shi ka ga kaunarsa" Ta dan yi shiru sannan sai ta dubi Abdulmalik ta ce "Kana jin kuwa zai iya kaunata?"*** Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya dubeni da murmushi sannan ya dubi tubanin Tubanin dake gabansa cikin damuwa domin tuni ya hadiye sama da kashi uku bisa hudun tubanin A zuciya ta na ce kai wannan tsoho da cin tsiya yake domin na tabbata yawan tubanin da ya hadiya tun daga rana zuwa yanzu ya ishi katti goma su ci su koshi amma sai gashi shi kadai duk ya hadidiye su kamar rumbu "To Nas ka ga abin da nake fada maka tun farko ko? Sai da na ce da kai ni ne mai saka labari kamar injin saka, na hade ma shi guri guda, gashi kuwa sannu a hankali na nuna maka alakar zarurrukan labarin guda biyu." "Haka ne Baba Sidi." Na ce dashi Sidi mai jaka ya canko wani katon tubani mai kama da dankali ya gutsiri rabi, sauran ya fado a cikin kwanon Sidi mai jaka ya dubeni ya ce. "Nas, wannan shi ne karshen wannan dogon zaren labarin, yanzu abin da ya rage shi ne na gaggauta na daura ma bakin zarurrukan labaran guda biyu kafin nan da sallar magariba, domin bana son labarin ya kai mu har bayan sallar magariba." Na yi sauri na gyada kai na ce. "Ni ma ai na fi son haka." Sidi mai jaka ya gyada kai ya ce. "To Nas, bari yanzu ne zan koma kan wancan tsohon zaren labarin da muka bari lokacin da zamu tafi sallar azuhur, inda mauka baro Anas yana karatun wasikar da Ummi ta bashi." Ya dubeni ido da ido. "Ka tuna da gurin?" Na gyada kai na ce. "Kwarai kuwa, ba inda ka ce har ma yana jiyo kukan matarsa Mabaruka ba daga cikin bandakin?" Sidi Mai jaka ya fashe da dariya yace. "Nas kenan, da ace yadda kake rike labari a kwakwalwarka haka nan kake rike karatu da ba karamin malami za a yi ba wata rana, to sai dai kuma na fahimci kamar kwakwalwarka ta fi iya rike labari fiye da komai." Nima sai na fashe da dariya, na ce. "Baba Sidi kena." Sidi mai jaka ya yi gyaran murya sannan ya ce. "Nas, dauki zuciyarka cancakat ka mayar da ita cikin bandakin nan, inda muka baro Anas dazu yana karatun wasikar da Ummi ta bashi." "Na mayar." Na ce dashi. Yauwa Nas. Anas ya ci gaba da juya takardar a hannunsa, zuciyarsa dauke da abubuwa guda uku masu kama da kishiyar juna. Ka ga na farko dai akwai farin ciki, domin Anas bai san abin da zai iya kwatanta farin cikinsa da kalmar Ummi ba, inda tana kaunarsa da kanta. Na biyu akwai tsana mai tsanani cikin zuciyarsa, domin a yanzu duk duniya babu abin da ya tsana kamar matarsa Mabaruka. Domin tuni Anas ya riga ya san wannan mummunar gurguwa ita kadai ce katangar karfen dake tsakaninsa da babbar masoyiyarsa Ummi. Abu na uku kuwa dake dafe a zuciyar Anas shi ne tsananin fargaba, don Anas ya tabbata sai dai ya zabi tsakanin mummunan aski da sa kai a wuta, domin muddin ya ci gaba da mu'amula da Ummi, rabuwarsa da Mabaruka ta zo kenan, shi ko ya san a yanzu koma me yiwuwa har abada Mabaruka ita ce babbar rumfar da ta rufe kansa da inuwa ta yi masa katanga da zafin ranar talauci. Wadannan abubuwa guda uku su suka hadu suka cunkushe zuciyar Anas, don haka yana nan bandakin yana maimaita karatun wasikar Ummi har sai da ya karanta ta sau kusan talatin. Bai tashi komawa dakin kwanan su ba sai da ya tabbata a lokacin Mabaruka ta gama fushinta ta yi barci. Anas ya nufi dakin kwanansu cikin sanda, a lokacin kusan biyu da rabi ne na dare. Ko kusa ko alama baya son ya sami Mabaruka ido biyu bata yi barci ba, domin Anas ya gama gajiya da ita, kai hatta muryarta baya son ji. Murya daya ce kawai ke yawo cikin kwakwalwarsa muryar Ummi. Anas ya yi boyayyiyar ajiyar zuciya sa'ar da ya tura dakin kwanan nasu ya shiga. Domin ya ga a cikin duhu yake. Tabbas ta yi barci, Anas ya ce cikin zuciyarsa Sannu a hankali ya sauya kayan dake jikinsa sannan ya lallaba ya haye bisa gadon ba tare da ya yi wani kwakkwaran motsi ba ya kwanta haka nan bai ma yarda koda jikinsa ya taba jikinta ba Anas ya yi lamo kamar ya mutu gashi dai baya ko motsi amma idanunsa a bude yake garau Zuciyarsa dauke da hoton kyakkyawar surar Ummi Yana nan kwance zuciyarsa fari fat lokaci guda kuma yana tunanin hanyar da zai bi a gobe ya gujewa Mabaruka domin ya sami damar ganawa da Ummi Anas na nan cikin wannan haki can sai ya ji agogo ya buga karfe daya sannan ne fa ya ji abin da yasa gashin jikinsa mimmikewa tsaye "Anas." Muryar Mabaruka ta ratsa duhun dake dakin ta daki dodon kunnensa. Anas ya zabura cikin kaduwa Bai taba tsammanin Mabaruka ba barci take yi ba. "Mab...Mabaruka ...dama ba barci ki ke yi ba." Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce a sanyaye cikin karayar zuciya. "Ya zan iya barci Anas bayan kana fushi dani." Hakan kawai da ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta ya kamashi.TSOHON ALKAWARI-13 . "Ya zan iya barci Anas, bayan kana fushi dani." Hakan kawai da ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta ya kamashi. Don haka sai ya yi karfin hali ya ce. "Ki yi hakuri Mabaruka...wann an duk wani al'amari ne na rudin shaidan." Ga mamakin Anas sai ya ji Mabaruka ta yi wani irin nannauyan ajiyar zuciya, sannan sai ta juyo shi ta rungume shi ta kankameshi ta ce. "Ka yafe min Anas, ka kuma manta da duk abubuwan da na fada ma na bakaken maganganu, wallahi masifar kaunarka da kishinka ne suka sani..." Ta yi shiru tana numfashi sama-sama daga nan bata kara cewa komai ba, a haka barci ya dauke ta hannayenta kankame da jikin Anas babban masoyinta a duniya. Shi ko Anas, yadda ya ga rana haka ya ga dare bai runtsa ba. Ga dai Mabaruka rungume da shi cikin shaukin bege, amma shi ji yake yi kamar a rungume yake da kaya. Washe gari da safe suna karin kumallo sai Anas ya fuskanci duk da yake dai ba cikin fushi Mabaruka ta tashi ba amma babu alamar walwala sosai a fuskarta haka nan da kyar ta kai abinci sau biyu bakinta. Ka bi ta a hankali dan samari wannan gurguwa ita ce babbar inuwar rayuwar ka Wata zuciya ce ke baiwa Anas Shawara Wata zuciya ce ke baiwa Anas shawara. Anas, ya mike tsam daga inda ya ke ya koma kusa da Mabaruka ya zauna, sannan ya dauki yan siraran hannayenta ya rikesu a tausashe ya sa alamun damuwa na karya a fuskarsa, sannan sai ya matsa da bakinsa kusa da kunnen ta ya ce. "Mabaruka...me ke damunki ne, na ga duk kamar ba kya cikin walwala, ko har yanzu fushin ki ke yi dani? Ba na nemi afuwar ki yafe min ba?" Mabaruka ta langabe kai duk da yake dai bata yi masa murmushi ba, to amma fuskarta ta nuna alamun jin dadin tarairayar da ya yi mata. "Anas, wallahi zuciyata ce ke cikin fargaba." Anas ya dubeta cikin mamaki, sannan ya matse hannayenta a cikin nasa ya ce. "Fargabar me kuma, Mabaruka? Kina da kudi da duk wani jin dadin duniya da ki kebukata, tun da dai Allah ya hore miki dukiya, haka nan kuma kina da ni, ga ni kusa da ke, to mene ne kuma na fargaba?" Mabaruka ta dago kanta ta dubi Anas cikin mamaki ta ce a sanyaye. "Ina da kai fa ka ce?" Anas ya gyada kai ya ce. "Kwarai kuwa kina da ni, ni ba mijinki ba ne?" Mabaruka ta dan lumshe idanu sannan sai ta bude su ta dubi Anas. "Ka ga ni kuwa fargabar da nake yi gani nake yi kamar kwace min kai za a yi, rabuwarmu ta zo." A wannan dan takin lokacin da take kalamin sai Anas ya ji tausayinta ya sake kama shi a karo na biyu. Tabbas ya san batunta gaskiya ne, domin tuni ma in dai batun soyayya ne an riga an raba su, abinda ya rage tsakaninsa da ita a yanzu shi ne auren kaddara. "Ka da ki ce haka Mabaruka, bai kamata ba irin wadannan kalamai marasa dadi suna fitowa daga bakin ki." Anas ya dauke kai gefe guda fuskarsa cikin damuwa. Da ace za ka ga fusakarsa a lokacin, mutum sai ya rantse da Allah cewa abin da yake fada har zuciyarsa haka nan yake. Mabaruka ta yi wata kwakkwarar ajiyar zuciya ta dubi Anas. "Ba ni lemo na sha." Anas ya mike cikin sauri ya tsiyayo mata tacaccan lemo cikin kofin alfarma sannan ya zauna kusa da ita kana ya dan janyota jikinsa ya kara mata kofin a bakinta Cikin farin ciki mara misaltuwa Mabaruka ta fara shan lemon kadan-kadan har sai da ta shanye gaba daya. Abin ya baiwa Anas mamaki domin bai taba ganin ta yi haka ba. Amma ga Mabaruka hakan da ta yi akwai dalili mai karfi dalilin kuwa shi ne rabon da Anas ya yi mata irin wannan tarairaya tun daren amarcinsu na farko "Lemon ya ishe ki ko na karo miki?" Anas ya tambayi Mabaruka a tausashe Mabaruka ta dubeshi da murmushi a karo na farko ta girgiza kai "Ya ishe ni." Ta dan yi shiru sannan sai ta ce "Ina ma ace kullum haka muke da na fi kowa farin ciki a duniya" Anas ya sunkuyar da kai gami da murmushin yake shi kansa kunyar hada ido yake yi da ita domin a zuciyarsa cewa yake yi ina ma wannan tarairayar da yake yiwa Mabaruka ace Ummi ce Abin da Mabaruka ba ta sani ba shi ne duk wannan tarairaya da Anas ke yi mata kokari yake yi ya sami hanyar da zai bi ya sulle ya ziyarci Ummi "Daga yanzu zan manne ma kamar cingam duk inda za ni muna tare." Kalaman Mabaruka suka fado zuciyarsa Anas ya ji gumi ya fara tsiyaya ta bayansa duk kuwa da cwa wayewar gari kenan kuma koda ma babu sanyin iskar safiya akwai na na'urar sanyaya daki. "Tunanin me ka ke yi Anas?" Mabaruka ta tambayeshi babu zato babu tsammani ashe duk abin da yake yi tana lura da fuskarsa Adaida lokacin ne to wata dankareriyar karya ta darsu a zuciyar Anas ya riga ya san ita ce damar sa ta karshe ta samun damar zuwa gurin Ummi dan haka sai ya dubi Mabaruka ya ce a tausashe. "Kin san ina da abokai a cikin gari da yawa wadanda rabon da mu gana dasu tun kafin na aureki shi yasa ki ka ga na shiga cikin damuwa saboda ina fargabar kada su ga kamar dan na sami canjin rayuwa ne shi yasa na watsar da su." Mabaruka ta dan yi shiru na lokaci tana kallon kofin da ke gabanta. Zuciyar Anas ta fara harbawa da karfi, yana jiran ya ji abin da za ta ce, ya san idan ta ki amincewa bashi da damar ganin Ummi, haka nan kuma idan tare zasu fita nan ma bashi da damar zuwa gurin Ummi kenan. Tsawon lokaci, sannan Mabaruka ta dubeshi a tausashe ta ce cikin murmushi. "Kuma ka ki ka sanar dani tun dadewa ko tsorona ka ke ji?" Ta dan fashe da dariya. Jin haka shi ya sa Anas ya washe baki har kunne, zuciyarsa kamar ta fasa kirjinsa saboda doki. Anas ya dada rungumo Mabaruka. "Ya ya zan ji tsoron matata?" Wannan abu da ya fada shi ya kara narkar wa da Mabaruka zuciya, cikin sauri ta dubi Anas. "Yaushe za ka je ku gaggaisa da abokan naka?" Anas ya yi sauri har zai ce yau, sai wata zuciya ta ce dashi bi a hankali Anas, wannan nannadaddiyar matar ta fi ka wayewa. "Duk lokacin da ki ka ce Mabaruka haka za a yi, in ma kina ganin za ki iya jure shiga gargada da kwari da tudu irin na unguwanninmu na yan Allah baku mu samu sai mu tafi tare ki rakani, domin ba na son rabuwa da ke." Mabaruka ta dage kai cikin murmushi, sannan ta girgiza kai ta ce. "A'a ni ba zan iya shiga gargada ba, kana ganin ma so nake yi mu tafi london hutu, amma rashin doguwar tafiya a jirgi ya hanani" Ta dan yi shiru. Zuciyar Anas sai harbawa take yi yana jiran ya ji abin da za ta ce. "Anas." Ta kira sunansa a sanyaye. "Na'am, Mabaruka." Anas ya amsa cikin kwararren murmushinsa na mayaudara. Mabaruka ta ce. "Idan ka tafi kamar karfe hudu na yamma sai yaushe za ka dawo?" Anas ya dan yi jim sannan sai ya dube ta, ya ce. "In ba dan abokan nawa suna da yawa ba da sai in ce dake karfe takwas ma ina gida, to amma me yiwuwa na kai har wajen tara." Ya dubeta ido da ido. "Babu damuwa?" Mabaruka ta kama hannunsa cikin farin ciki ta gyada kai ta ce. "Na kara ma awa daya, amma kada ka wuce karfe goma, domin ko ruwa ba zan sha ba sai ka zo ka ba ni." Ta dan yi shiru tana duban Anas, suka yiwa juna murmushi. "Idan za ka fita sai ka dauki motata shudiyar lexus din nan, kada abokan ka su raina min kai!" *** Sidi mai jaka ya dubeni babu ko saurarawa ya ce. A can gidan su Ummi, Abdulmalik ya tsinci kansa cikin damuwar da bai taba shiga irinta ba, domin kwanansa guda cur) babu dare ba rana, yana ta faman rubutu ne. Na dubi Sidi mai jaka cikin mamaki. "Rubutun me kuma?" Sidi mai jaka ya ce. "Saurareni da kyau ka ji dalili." Ka ga Nas, tun ranar da Ummi ta halarci liyafar gidan Mabaruka, inda ta baiwa Anas yar rubutacciyar wasika, tana komawa gida sai ta wuce kai tsaye zuwa dakin dan uwanta Abdulmalik. "Yaya Abdulmalik." Ta kira sunansa tun daga kofar dakin cikin doki da farin ciki. Abdulmalik ya dago kai cikin damuwa ya dubi kyakkyawar fusakarta domin ya san labarin da ta zo dashi ba zai taba faranta masa ba. Daman tun da yamma kafin ta tafi sai da ta sameshi ta ce. "Yaya Abdulamalik...M abaruka ta gayyace ni liyafa a gidanta." Abdulmalik ya boye kunar zuciyarsa ya dubeta da murmushin da bai kai zuci ba. "Ki ce yau kin sami damar ganin mutumin na ki." Ummi ta sunkuyar da kai. "Uhm, shi da ma yake da mata, ni na san ma ai zai yi wuya in zai kulani." Abdulmalik ya ji zuciyarsa kamar za ta fashe. "Namiji ai na mace hudu ne." Ummi ta gyada kai ta ce. "Yanzu yaya Abdulmalik idan mun hadu da shi ya ya zan yi?" Abdulmalik ya dube ta ya ce. "Duk da yake dai nima ba sanin irin al'amuran soyayyar nan na yi sosai ba, to amma ina ganin tunda dai ke mace ce, ba za ki rasa dabarar da za ki bi ba wajen nuna masa cewa kina kaunarsa. Sai dai kuma ki bi a hankali kada babbar kawarki ta kamaki kina kokarin sace mata miji." Suka fashe da dariya, A haka suka rabu. Wannan shi ya sa lokacin da ta dawo sai ta shiga dakin cikin farin ciki ta zayyanawa Abdulmalik duk abin da ya gudana tsakaninta da Anas "Yaya Abdul kana jin zai zo gobe din kuwa?" Abdulmalik ya ji murmushinsa ya fara daukewa "Me zai hana, tun da dai idan aka yi la'akari da abin da ki ka ce shima ashe ya dade yana kaunar ki" Ummi ta yi tsalle a tsakar dakin ta dire cikin farin ciki ta ce. "Wallahi Yaya Abdul ba ka ga yadda na ruda shi ba jikinsa har rawa yake yi" Abdulmalik ya cije baki sannan ya dage kai. Ummi ta daina tsallen da take yi ta dube shi cikin damuwa. "Yaya Abdul...ba ka da lafiya ne na ga kana cije baki?" Abdulmalik ya dubeta. "Kaina ne ke sara min da ciwo tun da safe" Ummi ta dube shi cikin.TSOHON ALKAWARI-14 . "Kaina ne ke sara min da ciwo tun da safe" Ummi ta dube shi cikin damuwa. "Bari in dauko ma magani" Abdulmalik ya yi sauri ya girgiza kai. Sannan ya yi mika. "Ina tsammanin gajiya ce ta yi min yawa, na san idan na sami isasshen barci zan warware zuwa safe" Ummi ta kura masa idanu cikin damuwa na tsawon lokaci. "Bari to na tafi na barka ka huta, domin zuwa na yi mu yi bankwana, na kuma fada ma cewa gobe ne da daddare muka yi dashi zai zo...in dai zai zo din" Ta mike tsaye. Abdulmalik ya dubi kyakkyawar fuskarta. "Ina taya ki fatan alheri Allah ya sa ya zo din" Ummi ta yi murmushi ta ce. "Ameen Yaya Abdul, Allah ya karbi addu'arka, wallahi yau da kyar zan yi barci" "Ai ba ke kadai ba" Abdulmalik ya ce cikin zuciyarsa. "Sai da safe Yaya Abdulmalik." Ummi ta ce da faffadan murmushi. Sannan sai ta fice daga dakin. Tana fita sai Abdulmalik ya kifa kai akan cinyarsa, ga mamakinsa sai ya ji wani zazzafan hawaye ya fara kwaranya akan fuskarsa. Yana nan zaune har karfe biyun dare ta gota barci bai samu ba, domin Abdulmalik ya riga ya san cewa idan ya yi lako-lako yana ji yana gani kwado zai leko daga tafki ya yi masa kafa ya koma. Tabbas idan ya yi wasa yana ji yana gani Ummi, abin da ya fi kauna fiye da komai a duniya za ta sulale ta tsakanin yan yatsun ikonsa. A lokacin ne to dabarar ta fado zuciyar Abdulmalik. A kullum zuciyarsa kan fada masa cewa hanya daya ce kawai zai bi ya magance wannan bala'i dake kokarin afka masa. Ita ce ya kira Ummi ya yi mata bayanin cewa ita fa ba yar uwarsa ba ce ta jini, ya kuma yi mata bayanin irin yadda ta shige zuciyarsa. To amma kashedin mahaifinsa shi ke taka masa birki. Wata zuciyar ta kan ce dashi me zai hana ka sanar da mahaifiyarka halin da ake ciki. Kunya ba za ta bari ba. Ita ce amsar da Abdulmalik ke fadawa zuciyar tasa. Yana cikin hakan ne to ya kasa barci, kawai sai dabara ta fado masa Abdulmalik ya dauko littafin rubutu, mai shafi dari da sittin, ya dauki biro ya fara rubuta labarin tun farkon haduwarsa da marigayi Saifullahi mahaifin Ummi. Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi "Nas, wannan labari da Abdulmalik ya rubuta shi ne sanadiyyar duk wani labari da nake baka a halin yanzu." "Kamar ya ya kenan, ban fahimce ka ba Baba Sidi?" Na ce dashi. Sidi mai jaka ya ce. "Za ka fahimce ni ne, amma sai nan gaba, kai dai rabu dani na karasa labarin nan, na ga magriba ta karaso, bana son labarin nan ya kaimu har bayan isha." ya dauki tubani ya jefa a baki sannan ya ci gaba. Washe gari tun kafin magariba Ummi ta shiga wanka, ba ita ta fito ba sai karfe shida da rabi. Bayan ta yi sallah sai ta shiga kwalliya, sai da ta shafe sa'a guda tana kwalliya. Bayan ta gama shafe-shafe da feshe- feshen turare, sai ta wuce kai tsaye zuwa dakin Abdulmalik domin tun da safe suka yi dashi cewa shi ne zai rakata hirar, domin Ummi ta ce dashi ba ta son a san alakar a cikin gida har sai Anas ya zo a kalla sau uku. "Har kin shirya kenan?" Abdulmalik ya dubeta cikin karaya. Ummi ta yi murmushi ta dubeshi ta ce. "Dubanni da kyau Yaya Abdul...dan Allah na yi kyau? Idan ban yi ba fada min na yi sauri na sake shiga kada ya zo ban gama shiryawa ba." Abdulmalik ya kurawa kyakkyawar halittar idanu. Ba wai yana kallon Ummi bane don ya ba ta amsar tambayar da ta yi masa ba, yana kallonta ne da idanun bege da tsananin shaukin ina ma ace shi ya mallake zuciyar ta baki daya. Kai wannan Anas da sa'a yake a duniya. Abin da ya fi damun Abdulmalik da kuma bashi mamaki shi ne, wai shin shi wannan Anas din kamar ya ya yake, wane irin kyawun siffa ce dashi, ko kuma Ilimi, ko kuma dadin baki, da har wannan kyakkyawar ta mace da tsananin kaunarsa. "Ya ya ka ganni Abdulmalik, na yi kyau?" Zazzakar muryar Ummi ta sake ratsa kunnen Abdulmalik. Ya yi ajiyar zuciya ya ce. "Kin yi kyau wallahi sosai ma kuwa." Ummi ta yi tsalle cikin murna ta ce. "Har na ji dadi wallahi, tashi to mu tafi." Abdulmalik ya mike tsaye da kyar kamar ya hadiyi tabarya sannan ya ce. "Idan momi ta tambaye kin inda za mu ki ce da ita kanti zamu je siyayya." *** Karfe takwas saura kwata na yamma Anas ya shigo titin a cikin katuwar motar shudiya kirar Lexus yana tafe yana bin wakar kidan turawa abinsa cikin farin ciki da wannan rana. Tun da ya auri Mabaruka bai taba samun yanci irin na wannan rana ba. Ga shi dai daman tun ranar da ya aureta ya yi tsalle ya fice daga kurkukun talauci ga motocin hawa sai wacce ya zaba ga sutura Kusan kullum sai ya sa sabon kaya na yamma daban na safe daban. Ga aljihunsa a cike taf da mikakkun takardun kudi na kashewa, amma duk a banza bai jin dadinsu ba don kome ba kuwa sai dan wannan nacacciyar gurguwa kamar yadda ya kirata, wacce ke manne da shi kullum kamar cingam. Dan haka a yanzu da ya shigo cikin titin sai ya dubi kujerar motar dake hannun damansa cikin farin ciki domin yau Allah ya raba shi da cingam, lokaci guda kuma sai ya dubi takardar da ke hannunsa na dama, yayin da hannunsa na hagun kuma yake sarrafa matukin motar. Tabbas titin ne. Anas ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai ya dada kallon takardar kwatancen da Ummi ta bashi, kana ya sake dago kai yana nazarin jerin gidajen dake gurin yana kokarin hangen mai lamba ashirin daga cikin su. A daidai lokacin ne to hasken fitilar motarsa ta hasko masa abin da ya sa yar autar hantar cikinsa kadawa. Sannan sai ya fara musu da zuciyarsa, kai wannan ba ita ba ce, ya ce da kansa, sa'ar da ya hangi kyakkyawar hallitar tsaye a jikin katangar wani sabon gida da ba a gama ginin sa ba. Ita da wani saurayi ne kyakkyawa dogo fari mai dogon saje da dogon hanci mai doro daga tsakiya sai ka ce hancin Larabawa. Anas ya ji wani bakin kishi ya turnuke zuciyarsa sa'ar da ya tabbata lallai Ummi ce ba wata ba. Abin da ya fi bata masa rai shi ne saurayin da ke tsaye da ita shima kyakkyawa ne, duk da yake dai Anas bai ga alamun saurayin ya zo da mota ba, to amma a yanayinsa babu alamar talauci ko kankani a jikinsa. Sannu a hankali ya ja birki ya tsaya a daf da su kana sai ya rage hasken fitilar motar kadan ya dada nazarin fuskar Ummi. Abin ya bashi mamaki, domin ya lura da cewa sun juyo inda yake, sun zubawa motar idanu. Sidi mai jaka ya yi shiru, kana ya sheka wata uwar hamma ya dubeni a yatsine ya ce. "wato Nas, tubani na da dadi, amma tsiyata da shi saurin sa mutum barci, ga shi da sa cikin mutum ya yi nauyi wata sa'ar sai in ji kamar na hadiyi duwatsu." "Dan ma ka saba cin sa." Na ce dashi a kagauce domin na matsu na ji yadda za a yi. Sidi mai jaka

Chapter 5 of 7