Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
dani Ummi ta ce tana son ganinsa washe garin ranar, kuma yanzu ka ce dani wai zaren labarin ya kare." Sidi Mai Jaka ya yi murmushi "Haba Nas kai fa yanzu mun zama jiki sai dai ka fadawa wani ni, sanin kanka ne idan na ce da kai zaren labari ya kare to ya kare din tabbas, dole ne sai na sako sabo sannan na jona ma shi da bakin wannan tsohon labarin da na saka. Ya dan yi shiru, sannan ya sunkuyar da kai. Nas ina son ka dauki zuciyarka cancak ka maishe da ita can wani lokaci, kuma wani zamani mai dan tsayi na a kalla shekaru ashirin da biyar da suka gabata. Na dubi Sidi mai Jaka cikin mamaki bani da abin cewa dan haka sai na gyada kai na ce dashi "Na mayar." Sidi Mai jaka ya ce "Yauwa Nas haka nake so da kai." * * Shekaru ashirin da biyar da suka wuce wani dogon mutum fari siriri buzu-buzu balarabe-balarabe, ya sauka a garin nan dauke da yar tabarmarsa ta kaba akai yana neman inda zai sauka. Ba don komai ba kuwa sai don lokacin da ya sauka a garin nan cikin dare ne tare suke da matarsa ita ma kusan irin kirar su daya to sai dai kuma kyakkyawa ce ta gani a fadawa sarki. Wannan mutum dogo fari siriri babu komai a cikinsa sai hanji domin rabonsa da abinci kwana biyu kenan haka ma matarsa. Haka nan kuma yadda cikinsa yake hakanan aljihunsa yake, karaf babu ko karfanfana. Mutanen guda biyu mace da mijinta suka shigo birni, mijin na gaba dauke da tabarmar kaba, ita ko matar na biye dashi a baya dauke da wasu tsummokarai da ita kanta bata san amfaninsu ba. Me yiwuwa dai tana dauke da tsummokaran ne don cika umarnin mijinta, babu mamaki kuma sabo da yi ne wai gawa da gatsine. To koma dai mene ne wannan mutane dauke suke da muguwar yunwa ga kishi ga gajiya, ga babu tabbacin gurin kwana, sannu a hankali suna yawo cikin birni tsakanin manya- manyan gine-gine na alfarma can sai matar ta jefar da kayan tsummokaran dake kanta ta durkusa, ta rike ciki. "Wallahi...mai gida ni na gaji." Ta ce cikin wata irin bakuwar Hausa. Mutumin ya ajiye tabarmar keson dake kansa sannan ya dubi dankareren gidan dake gabansu wanda ke ci reras da fitulu kamar rana. Ya dubi matarsa cikin tsananin tausayi. "Ban ga laifinki ba HINDATU, ai kin yi ma kokari." Ya dan yi shiru idanunsa akan katon gidan dake gabansu. "Gashi wannan gidan ma kamar babu kowa a cikinsa, da sai in karasa na barato mana dan abin da zamu sa a bakinmu." Matarsa Hindatu ba ta ce komai ba, maimakon hakan ma sai ta kwanta a kasa ta dora kanta akan kullin tsummokaran ta kurawa sararin subhanahu idanu. Hankalin mijinta ya dada tashi, ya san cewa dadin ta yunwa ce kawai, duk wannan mai sauki ne, domin sun riga sun saba da jin yunwa, tun sa'ar da yaki ya barke tsakanin buzaye yan tawaye da gwamnatin kasarsu basu kara samun damar wani jin dadin rayuwa ba. Koda yake can ma ba wani cikin kwakkwaran jin dadi suke yi ba, to amma akalla dai kafin barkewar yaki suna da kwanciyar hankali wannan da sauran matsalalo halayyar yaki marasa adadi su suka sa wadannan mutane sabo da duk wata irin wahala, a cikinsu har da ma jimirin yunwa. Dan haka abin da ya sa hankalin mijin matar nan Hindatu ya tashi shi ne, ya san tana da juna biyu, akalla zai kai wata uku. Tun sa'ar da ya ki ya barke suka fita gudun hijira mutumin ya fitar da ran cewa matarsa zata sami damar haife cikin, kullum kwanan duniya cikin zullumi yake, yana sauraron zubewar cikin, amma cikin ikon rabbana har zuwa wannan lokaci matar bata ko taba ciwon kai ba ballantana a yi zancen zubewar cikin sai yanzu da ta fadi a gabansa ta ce dashi ta gaji ga kuma muguwar yunwa. Dogon mutumin ya mike tsaye sannan ya sake duban matarsa cikin damuwa kana ya dubi sararin samaniya sai ya ga tuni ya hade da gajimare an kuma fara rugugin aradu haka nan Walkiya sai haskawa take yi wal- wal kamar tana daukar hotonsu. "Sannu Hindatu dan jirani kadan na karasa kofar gidan can me yiwuwa idan nayi sa'a ko masamu wani ya taimakomu da abin da za mu sa a bakinmu." Hindatu ta runtse idanu sannan ta budesu cikin karfin hali ta dubi mai gidanta ta ce. "Kada ka damu je ka gani, Allah baka sa'a." Cikin sauri na ban mamaki idan aka yi la'akari da rama da kuma bakar wahalar dake jikinsa mutumin ya nufi kofar gidan kai tsaye kirjinsa na harbawa. Har sa'ar da ya kai ga tangamemiyar kofar me kamar kofar gari bai ga motsin ko da halitta daya ba a duk tsawon kwararo sai wasu karnuka guda uku dake can karshen kwararon suna ta faman haushin babu gaira babu dalilin kamar sun yi ido biyu da aljan. Mutumin ya matsa kusa da kofar ya tsaya cikin shakka, domin bai san abin da ya kamata ya yi ba Shin buga kofar zai yi ko kuwa sallama zai yi. To idan ma ya yi sallama wa zai ji shi? Ya tambayi kansa. Yana nan tsaye cikinsa na kugi kamar tukunyar talge, sai ya ji kamar dagacan sashen hagu na katuwar kofar ana tabata. Mutumin ya yi sauri ya dan ja da baya lokaci guda kuma ya dubi bangaren hagu na jikin kofar. A lokacin ne to ya fahimci ashe a jikin katuwar kofar akwai wata yar karamar kofa daga hannun hagu wacce akalla mutum guda zai iya wucewa ta ciki, wannan yar karamar kofa ita ce ake motsawa ba a ko dade ba sai ta bude. Wani dan matashin yaro fari kyakkyawa ma'abocin kyawun sutura da cikar hallita ya fito daga cikin gidan sannan ya kurawa dogon mutumin idanu baya ko kiftawa. Dogon mutumin ya dubi yaron, sai ya rasa ma me zai ce masa. Domin da ido mutum na iya tsammanin dan saurayin yaron ya kai shekara goma sha uku ko sha hudu, to amma a gaskiyar al'amari yaron shekarunsa goma cif-cif da kwana biyu, domin shekaran jiya-jiya din nan aka yi bikin cikar shekarunsa goma da haihuwa. "Sannu Malam." Yaron ya ce da mutumin cikin ladabi. "Yauwa dana, sannunka dai." Ya dan yi shiru sannan sai ya dubi yaron ya ce. "Da Allah dan samari idan da hali taimakon abinci nake nema duk kankantarsa, wallahi mu baki ne bamu san kowa ba, ga matata can kwance akan titi, yunwa ce ta hanata tafiya" Yaron ya dubi mutumin na dan tsawon lokaci, a zuciyarsa yana tunanin ja da baya a guje ya rufe gida domin me yiwuwa mutumin nan dake tsaye a gabansa mahaukacine, dubi fa kayan dake jikinsa, koda yake dai irin kayan da yake gani ne jikin buzayen dake gadin gidansu, to amma shi wannan nasa sun ji jiki da yawa. "Ka ce abinci kake so?" Yaron ya tambaya. Mutumin ya gyada masa kai sannan ya dada da cewa. "Ko da kadan ne wanda zan bawa matata da Allah a taimaka min, so nake na bata ta dan ci mu yi gaba" Yaron ya daga kai ya dubi hadarin da ya mamaye sararin samaniya, sannan sai ya dubi mutumin cikin tausayi ya ce. "Ina zuwa" Cikin sauri ya shiga cikin gida. Ba a dade ba sai ga yaron tare da masu gadin gidansu mutum uku biyu buzaye daya tsohon soja, hakanan kuma da wani mutum dogo kakkaura wankan tarwada sanye da babbar riga amma kansa babu hula, ko shakka babu shi ne ya yi kama da mamalakin dankareren gida. Dogon mutumin dake tsaye, ya dubi mutumin a tsorace, domin ya tabbata kashinsa ya bushe a tsammaninsa kamashi zasu yi a matsayin barawo ko mahaukaci. Tun kafin su karaso gurin mutumin sai ya ji maigidan nan na cewa sauran masu gadin. "Wai wani mutum ne da matarsa anan kofar gidan suke neman taimakon abinci a gurin Abdulmalik shi ne na fito da kaina gara mu je mu gani ko wane irin mutum ne, duniyar nan yanzu ba abin yarda ba ce." Dogon mutumin ya zube gaban mai gidan ya gaida shi. Maigidan ya dubi dogon mutumin ya ce. "Malam kaine me neman taimakon abinci?" Mutumin ya gyada kai ya ce. "Ni ne ranka ya dade, wallahi zuwan mu kenan garin nan ni da matata, ga ta can a bayan yunwa ce ta kayar da ita ta kasa tafiya kuma tana da ciki wata uku, wannan shi ya takurani nake neman wannan abinci kafin Allah ya bani masauki, domin mu ba mutanen wannan kasa ba ne yaki ne ya koromu gudun hijira." Kalamin dogon mutumin ya karya zuciyar maigidan, nan da nan sai ya ji tausayinsa ya kamashi, musamman ma daya ji tare suke da matarsa kuma tana da ciki wata uku. Wannan shi ya fi tayar masa da hankali. Domin yau shekarunsa ashirin da yin aure, tun daya auro matarsa Hajiya Sa'adatu basu sami damar haihuwa ba sai bayan shekaru goma suka haifi Abdulmalik, tun daga kansa kuwa basu kara samun koda batan wata ba har zuwa wannan lokaci. "Yanzu ina matar taka take?" Dogon mutumin ya nuna can bayansa ya ce. "Ga ta can yallabai" Mai gidan ya dubi masu gadinsa guda uku ya ce. "Ku je dashi ku taho da matar, ku sameni a tsakar gida." Sannan sai ya kama hannun Abdulmalik suka shige farfajiyar gidan ma'abociyar shuke-shuken da kamshin furanni. Ba'a dade ba, masu gadin suka shigo farfajiyar gida tare da.TSOHON ALKAWARI-10 . Ba'a dade ba, masu gadin suka shigo farfajiyar gida tare da dogon mutumin da kuma matarsa Hindatu. Suna isowa sai mutumin da matar tasa suka zube gaban alhaji suka sake gaidashi. Mai gidan ya dubi tsohon sojan nan mai gadinsa ya ce. "A kaisu dakin nan na kusa da injin bada wuta su kwana a ciki yanzu zan sa a kawo musu abinci ina son kuma a lura dasu kaji ko?" Tsohon sojan ya rusuna ya ce "An gama alhaji" Sannan sai ya dubi dogon mutumin da matarsa ya ce. "Ku biyoni mu tafi." Ramammun mutanen guda biyu kyawawa suka bishi a baya, gami da godiya. Mai gidan ya bisu da kallo cikin tausayi yana tunanin abin da ya kamata ya yi domin taimakonsu. "Wallahi baba mutanen abin tausayi ne dubi matarsa da kyar take tafiya" Mutumin ya dubi dansa Abdulmalik ya gyada kai, bai ce komai ba. Sidi mai Jaka ya yi shiru sannan ya dubeni ya ce. "Nas, ina fatan kana biye dani akan wannan dogon zaren labari" Na gyada kai cikin kaguwa na ce. "Ina biye da kai baba Sidi, sai dai kuma ni wannan labarin duk jinsa na ke yi kamar sabo daman har yanzu ban ji alakarsa da wannan ba" Sidi Mai Jaka ya dubeni da murmushi sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya cafka daya ya jefa abakinsa ya dube ni. "Nas kenan, amma dai yanzu ai ka isa ka baiwa wani labari, sanin kanka ne in har na sako sabon zaren labari to ko shakka babu in Allah ya yarda sai na hade shi da wancan na baya, shi yasa ba ka gane alakarsu ba, to amma ka jira sannu a hankali lokacin da zaren labarin zai rikida ya koma kan wancan su hade da juna ba zama ka sani ba" "Haka ne, ina to sauraronka" Sidi Mai Jaka ya dada jefa tubani daya a baki ya ce "Dadina da kai kenan Nas, iya sauraron labari, ba ka gajiya da saurare" Na fashe da yar dariya. To ai labarin naka ne wani sa'in dole ma a saurareka domin sai kayi kamar kayi gabas da mutum sai an jima can sai a sameka a yamma" Baba Sidi ya fashe da dariya sannan ya dube ni ya ci gaba da cewa. "Nas, tun daga wannan rana da mai gidan ya sauki dogon mutumin nan da matarsa basu kara barin gidan ba, har sai da ta Allah ta kasance a kansu." Na dago kaina na dubi Sidi mai jaka cikin sauri na ce dashi. "Kada kace na tari numfashinka baba Sidi, ina da tambaya." Sidi mai jaka ya dubeni cikin mamaki. "Me kake son tambaya." Na dubeshi na ce. "Ni tun da ka fara bada sabon zaren labarin, kake ta ambaton wani dogon mutum, da kuma mai gidan daya sauke su, gashi dai ka siffanta su, kace sunan matarsa Hindatu, sunan dan mai gidan daya sauke su Abdulmalik, to shi dogom mutumin da mai gidan ya ya sunansu?" Baba Sidi ya dan yi shiru na dan lokaci sannan sai ya dubeni da murmushi ya ce. "Wani lokacin mutane kan bani mamaki, wai idan kana basu labari dole ne sai ka fadi sunan mutunen," Sidi mai jaka ya danyi shiru sannan sai ya ce. "Sunan dogon mutumin Saifullahi, mai gidan kuma Alhaji Kabiru. Nas ina fatan ka gamsu." Na gyada kai na ce "Eh, ci gaba" Sidi mai jaka ya dora daga inda ya tsaya. Washegarin ranar da Alhaji Kabir ya sauki bakin, tayi mutukar faran tawa bakin rai, domin yasa masu gadin gidansa sun bincikesu daga karshe suka gane cewa lallai da gaske yan gudun hijira ne kuma ya ki ne ya koro su. Dan haka sai Alhaji Kabiru ya ce a ci gaba da basu abinci, daga nan har zuwa ranar da matar Saifullahi zata haihu. To amma duk da haka sai da alhaji Kabir ya gana da masu gadinsa a sirrance ya ce suna fa kula da bakin nan, domin mutum na yau ba abin yarda bane domin sai ka dauko mutum daga rana ka sashi a inuwa, shi ko ya tura ka cikin wuta Sidi mai jaka ya dubeni cikin mamaki A haka Saifullahi da matarsa Hindatu suka zauna cikin farin ciki, a karshen watan da suka sauka a gidan ne to wasu sangartattun yan fashi suka ziyarci gidan alhaji Kabir A ranar da yan fashin suka zo tun karfe hudu na yamma ake tafka ruwan sama haka nan yan fashin basu tashi zuwa ba sai ana daf da fara sallar asuba lokacin suka karaso ko shakka babu sun rigaya sun gama sanin abin da za su yi dan haka cikin ruwan sanyi barayin su goma sha tara kamar tururuwa suka cafke masu gadin buzaye cikin ruwan sanyi yayin da tsohon sojan nan ya yi kokarin kawo musu turjiya hakan shi yasa cikin ruwan sanyi suka danne shi suka yi masa yankan rago kai tsaye kuma suka wuce inda Alhaji Kabir yake shi da iyalinsa. "A can bangaren hadiman gidan Saifullahi ya ji idanunsa sun bude ya farka daga nannauyan barci sannan sai ya ji jikinsa ya fara rawa babu gaira babu dalili cikin sauri ya taba matarsa Hindatu. . Matar ta mike zaune cikin firigice, ta dube shi a tsorace da yake har yanzu razanar ya ki bata gama saketa ba. "Me...nene?" Saifullahi ya dubi matarsa ya ce. "Ji na yi haka kawai idanuna sun bude, duk yadda aka yi wani mugun abu ne ke shirin faruwa a gidan nan." Ya dan yi shiru yana saurare kamar zakara. "Dauko min damarar layuna da guraye na." Cikin sauri na mamaki ga macen dake da ciki wata uku da kuma magagin barci jikinta, ta mike ta nufi inda tsummokaransu suke ta mika masa jakar gurayen. Cikin yan mintuna Saifullahi ya daura gurayen, sannan ya mike tsaye. "Bari in je in gani." Hindatu ta dubeshi da murmushin karfafa gwiwa ta ce. "To, Allah kiyaye bacin rana Allah bada sa'a." Saifullahi ya juya cikin sauri ya fice daga dan dakin. Hindatu ta bishi da kallo, ko kusa ko alama bata fargabar komai, domin ta yi imani da cewa in dai ba karfin kaddarar karar kwana ba, babu abin da zai sami maigidanta, ta riga ta san sirrin dake tattare da gurayen, ta ga yadda suka ratsa ta tsakanin sojojin yan adawa akan iyakar kasarsu, suka tsallako ba a gansu ba, ba a kuma samesu koda da alburushin bindiga guda daya ba duk kuwa da irin barin wutar da ake yi. Saifullahi ya matsa wata katuwar laya mai kamar makami da ke kwibinsa na hannun dama. Sannan ya nufi cikin gidan, ya tabbata a lokacin in ba Allah ba, ko ifiritu bai isa ya ganshi ba. Saifullahi ya hangi barayin daya bayan daya har su goma sha tara sun mammakale a loko-loko guda biyar daga cikinsu tsaye a kofar babban dakin shakatawar gidam. Saifullahi ya zaro wani bakin guru daga kugunsa wani dogo mai kamar maciji ya zagaya barayin dashi har sau biyu, nan da nan barayin suka sankare a gurin basa ko motsi kamar itatuwa. Saifullahi ya barsu a gurin, sannan ya ringa bin barayin daya bayan daya yana zagaya su da gurun ba tare da sun ganshi ba har sai da ya kamar dasu baki daya, sannan sai ya nufi kofar falon, ya zagaye barayin ya kwankwasa kofar dakin shakatawar a hankali. Shiru-shiru bai ji motsin komai ba, Saifullahi ya dada kwankwasa kofar da karfi, har sau goma. Tswon lokaci, sai ya ji kamar motsi an nufo kofar a hankali kamar a tsorace. "Alhaji ni ne...Sanifullah i." Saifullahi ya ce cikin tattausar muruya. "Saifullahi...l afiya ina masu gadin?" Saifullahi ya tausasa murya ya ce. "Yan fashi ne suka kama su, sun kuma kashe tsohon soja." Alhaji Kabir ya rike numfashi a tsorace. "Yanzu ina barayin?" Ya tambaya a tsorace. "Gasu anan waje duk na kama maka su." "Kai kadai Saifullah?" "Kwarai kuwa ai ikon Allah ya fi da haka." Tsawon lokaci, bai fito ba, can sai ya leko a hankali a tsorace sannan sai ya ja da baya saboda mutanen da ya gani guda biyar duk a sankare kamar itatuwa. "Kada ka ji tsoro Alhaji, kana iya fitowa, babu abin da zasu iya har sai idan na ga dama da ikon Allah, sannan zasu yi motsi." Alhaji Kabir ya dubi Saifullahi cikin kaduwa. "Jirani to ina zuwa, bari na bugawa yan sanda waya." Mintuna goma bayan haka gidan ya cika da jami'an tsoro. An kame barayin gaba dayansu, tun daga wannan rana sai Saifullahi ya sami cikakken yanci, Alhaji Kabir ya gama yarda dashi, ya kuma bashi shugabancin masu gadin gidansa. Sannu a hankali watanni suka shude, har cikin Hindatu matar Saifullahi ya isa haihuwa, ran nan da safe sai ta fara nakuda, Alhaji Kabir da kansa ya bada mota a kaita asibiti. Kusan sa'o'i biyu suna jiran labarin haihuwa, a cikin masu jiran akwai Alhaji Kabir, matarsa Hajiya Sa'adatu, Abdulmalik da kuma Saifullahi. A cikin wannan sa'ar ne abubuwa biyu suka faru, farin ciki da bakin ciki, domin Hindatu ta haifi wata kyakkyawar budurwa, mai kyawu na ban mamaki, ita kuwa Hindatu Allah ya yi mata cikawa. Tun daga wannan rana Saifullahi bai sake samun lafiya ba. A ranar da za a radawa jaririyar suna, jikin mahaifinta Saifullahi ya matsa, tun da sassafe ya sa masu gadi suka roki Alhaji da ya zo yana son ganawa da shi domin ba zai iya zuwa da kansa ba. Alhaji kabir ya zo dakin mai gadin cikin gaggawa, Saifullahi ya dago kansa da kyar ya dubeshi ya ce bakinsa na rawa.......TSOHON ALKAWARI-11 . "Alhaji, jikina ya tsananta min, haka nan kuma bana jin zan warke daga wannan rashin lafiya tawa." Alhaji Kabir ya matsa kusa da mutumin cikin tausayawa ya ce. "Ka da ka ce haka Saifullahi, ai ita cuta ba mutuwa ba ce" Saifullahi ya girgiza kai ya ce. "Ba zan rayu ba Alhaji, domin na ji a jikina, Shi yasa na kiraka domin na baka abu daya da na mallaka a duniya wanda da shi ne kadai zan iya saka maka abin da ka yi min a duniya" Ya dan yi shiru yana mayar da numfashi. "Alhaji a duniya bani da wanda ya fi ka, na dauke ka a matsayin dan uwa, amini, ka mutunta ni, ka taimakeni a lokacin da nake matukar bukatar taimako" Saifullahi ya tura hannunsa cikin wasu tsummokara dake gefensa ya dauko wata tsohuwar jaka ta bakin yadi ya mikawa Alhaji Kabir. "Wannan shi ne kyautar da zan yi maka ta musamman, guru ne, da layu guda uku. Sirri ne na tsarin kai da mahassada, da su ne Allah ya taimakeni na kama barayin nan" Ya dan yi shiru sannan ya ci gaba. "Ga Yata nan jaririya, na baka ita, ka taimake ni dan Allah ka rike min ita, idan an jima in za a sa mata suna, ka sa mata suna Nana firdausi, domin sunan mahaifiya ta ne" Ya fara tari, sannan sai ya yi karfin hali ya dago ya dubi Alhaji Kabir idanunsa na zubar da kwalla. "Alhaji wannan ita ce alfarmar da nake nema, za ka yi min..?" Cikin sauri Alhaji Kabir ya amsa masa. "Na amince Saifullahi, in Allah ya yarda zan rike ta kamar yar da na haifa a cikina kuma ina fatan ma Allah ya baka lafiya" Washe gari da aka yi sunan Firdausi mahaifinta Saifullahi ya bar duniya, a lokacin kwananta takwas kawai a duniya. Bayan an binne Saifullahi, sai Hajiya Sa'adaru ta fito dauke da kyakkyawar jaririyar ta sami maigidanta zaune a falo shi da dansa Abdulmalik, ta zauna kusa da maigidanta, sannan ta kurawa jaririyar idanu ta ce. "Oh, Allah mai yadda ya so, Allah gwanin iya halitta, ka dubi wannan kyakkyawar halitta, kai wallahi Alhaji ina bala'in son jaririyar nan, ba don komai ba. Sai don irin maraicinta, da kuma kasancewar sunan mahaifiyata ne nima aka sa mata" Alhaji Kabir ya dubi matarsa ya ce. "Ki riketa da kyau cikin aminci da kulawa kamar yadda za ki rike danki Abdulmalik." Hajiya Sa'adatu ta rungume jaririyar ta dubi maigidanta, sannan sai ta dubi kyakkyawar fuskar jaririyar ta ce. "Daga yau kin zama yata, Allah ya raya ki UMMI na" Tun daga wannan rana ne sunan Ummi ya bi wannan jaririya. Sidi mai jaka ya juyo da murmushi ya dubeni. Ni kuma na dubeshi cikin bazata. "Baba Sidi, kana nufin ka ce min wannan jaririyar ita ce Ummi din da Anas ya kamu da ciwon Kauna?" Sidi Mai Jaka ya fashe da dariya ya ce. "Nas kenan, ai daman sai da na fada ma sai na baka mamaki, sannu a hankali zan dawo da kai na jone ma bakin zaren labarin, gashi kuwa tun ma kafin na jone shi din har ka fara ganin alakarsu da wancen tsohon zaren labarin da muka saka" Na dubi Sidi mai jaka cikin kaduwa. "Wai Baba Sidi kana nufin ka ce ita wannan kyakkyawar Ummi din iyayenta ba ma wata tsiya ba ce a garin nan" Sidi mai jaka ya gyada kai ya ce. "Kwarai kuwa Nas, dan ma ka tari numfashina, domin har yanzu zaren labarin bai kare ba, bari in gama saka ma shi, idan na gama zaka fahimci rudanin dake cikin wannan labari" Na gyara zama na dubi Sidi mai jaka cikin doki na ce "Ci gaba, ina saurare" Sidi mai jaka ya jefa tubani daya a baki ya ci gaba.**** Sannu a hankali Nas Ummi ta fara girma kullum ta Allah kyawunta karuwa yake yi. Ba mutumin dake ganinta a waje ba lokaci-lokaci hatta Alhaji Kabir da matarsa Sa'adatu dake ganinta kullum suna mamakin kyawu irin na Ummi Wani abin ban mamaki shi ne tun ranar da aka haifi Ummi kullum a hannun Abdulmalik take wuni yana yi mata wasa. Gashi dai shi ba mace ba amma kullum yana makale da jaririyar dan haka har sa'ar da Ummi ta kai shekaru goma a duniya, duk inda zasu tare suke da Abdulmalik a lokacin nan shi yana da shekaru ashirin a duniya Amma duk da haka kusan tsayin sa daya da Ummi Wani sa'in sai Abdulmalik ya dauki Ummi a mota su yi ta yawo kantuna-kantuna inda ake sayar da kayan lashe-lashe da makulashe idan sun je sai Abdulmalik ya juyo ya kalli Ummi cikin fara'a a tausashe ya ce "Ummi, dauki duk abin da ki ke so" Cikin farin ciki da kauna irin ta dan uwa sai ta dubeshi ta ce "Abdulmalik kana shagwaba ni!" A duk lokacin da ta ce haka sai Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta dada narkewa da begenta domin tun ranar da aka haifi Ummi Abdulmalik ya fara sonta tun ma bai san mene ne kauna ba. Don haka sannu a hankali shekaru na shudewa har wannan son ya juye zuwa kauna. To sai dai kuma abin da Abdulmalik ya kasa fahimta shi ne a duk tsawon zamanin nan Ummi a matsayin dan uwanta na jini ta daukeshi domin bata taba sanin cewa ba uwarsu daya ba ubansu daya ba. Abdulmalik ya riga ya fi kowa sanin cewa Ummi ba yar uwarsa ba ce ta jini Domin shi ne ma ya yi sanadiyyar haihuwarta a gidan, to amma daidai da rana daya bai taba nuna mata alamu ba A bangaren iyayen Abdulmalik kuwa sun dade suna kallon irin alakar mai karfi dake kulluwa tsakanin yaran guda biyu, koda yake ga zuciyar Alhaji Kabir bai taba daukar alakar yaran a bakin komai ba face kawai sabo da kuma yan uwantaka. . To amma ranar wata laraba da yamma sai matarsa Sa'adatu ta dubeshi ta ce. "Alhaji, wai kuwa kana lura da al'amarin yaran nan?" Maigidanta Kabir ya dubeta cikin mamaki. "Kamar ya ya ina lura dasu? Wannan ai dole ne domin kuwa yayana ne." Sa'adatu ta dubeshi cikin yar damuwa ta ce. "Ba abin da nake nufi kenan ba." "To me ki ke nufi?" Sa'adatu ta gyara zama ta ce. "Wato ni gani na ke yi kamar Abdulmalik kaunarta ya ke yi." Alhaji Kabir ya dubeta baki bude cikin mamaki ya ce. "Yau ga ikon Allah, to daman mutum ba dole ne ya kaunaci dan uwansa ba." Sa'adatu ta girgiza kai. "Abin ya wuce da haka ina tsammanin begenta ya ke yi." Alhaji Kabir ya kura wa matarsa idanu na tsawon lokaci, sannan sai ya yi kasa-kasa da murya ya ce. "Kada fa ki manta cewa, har yanzun nan Ummi ba ta san cewa ba mune iyayenta ba." Sa'adatu ta yi murmushi. "Idan ita ba ta sani ba, ai shi Abdulmalik ya san ba yar uwarsa ba ce ta jini. Kuma abin da ya sa ka ji na fada ma haka shi ne, yanzu da ka leka cikin dakinsa za ka ga duk ya zagaye shi da hotunan Ummi, kowannensu ya rubuta (My love) Alhaji Kabir ya dada duban matarsa na tsawon lokaci, akwai alamun tunani a fuskarsa, can sai ya yi ajiyar zuciya ya ce. "To, sai mu bar wa Allah komai, ya yi ikonsa, Allah zaba musu abin da ya fi alkairi." . A bangaren Abdulmalik, sannu a hankali har Ummi ta kai shekaru goma sha bakwai. Kullum wutar begenta sai dada ruruwa cikin zuciyarsa take yi, ita ko in ka dauke soyayya irin ta yan uwantaka bata dauke shi a bakin komai ba. Amma duk da haka nan dai kullum suna tare basa rabuwa. Wata rana da yamma Ummi ta shiga dakin Abdulmalik ta ci kwalliya, fes,fes, hakan shi ya sa zuciyar Abdulmalik harbawa. A ranar ne to Abdulmalik ya ji kamar ya amayar mata da boyayyen sirrin zuciyarsa, to amma sai ya tuna kashedin da mahaifinsa ya yiwa duk wani mutum dake gidan inda yake cewa. "Kada wani daga cikinku ya sake ko da da wasa ya fadawa Ummi cewa mu ba iyayenta ba ne." Wannan shi ya sa Abdulmalik hadiye maitarsa. Zuciyarsa na harbawa ya dago kai ya dubeta cikin yabawa da abin da ya gani ya ce. "Kai, amma fa kin kara kyau Ummi." Ummi ta dube shi cikin dariya ta ce "Na gode yaya Abdul." Ta dan yi shiru tana kallon jeren hotunanta ko ina a cikin dakin sannan ta dubi Abdulmalik ta ce. "Duk duniya babu yan uwan dake kaunar juna kamar mu, dubi fa Yaya Abdulmalik duk ka bi ka wani shagwaba hotunana kamar wata budurwarka. Wannan ko budurwa ce ai ba karamin kaunarta kake yi ba." Abdulmalik ya sunkuyar da kai da dan murmushi, wata zuciya na cewa da shi, fada mata kawai cewa ita fa ba yar uwarka ba ce ta jini. To amma sai gargadin mahaifinsa ya sake dawowa zuciyarsa dan haka sai ya dago kai ya dubi Ummi da Murmushi ya ce. "Ummi kenan. Ina za ki ne na ga kin caba kwalliya haka?" Ummi ta dube shi da murmushi sannan ta ce. "Ina zani, ko dai ina zamu, bikin taya murnar ranar haihuwar wata kawata zaka rakani." Abdulmalik ya dubeta cikin mamaki ya ce. "Kin manta ne cewa ina da jarrabawa ta karshe a makaranta, kin san ina bukatar karatu." Ummi ta yi sauri ta rufe fuska cikin dariya. "Oh! Dan Allah Yaya Abdulmalik ka yi hakuri, wallahi mantawa na yi ashe kana da jarrabawa gobe." Abdulmalik ya mike tsaye. "Mu je na raka ki sai na dawo." Ummi ta mike tsaye ta dube shi ta ce. "Wallahi nima dan muna bala'in mutunci ne da MABRUKA da ba zan je ba tun da kaima ba za ka ba." Abdulmalik ya yi murmushi. "Ai ba komai. Yaushe zaki dawo?" Ummi ta lumshe idanu ta dan daga kai sama. Abdulmalik ya kurawa wasu siraran zane guda uku da suka yiwa kyakkyawan wuyanta kawanya. "Nan da karfe tara na dare zamu dawo."*** . Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce ina fatan kana fuskantar inda labarin ya dosa da kyau? Na gyada kai cikin sauri. "Ina fuskanta." Sidi Mai Jaka ya ci gaba. A daren ranar da Ummi ta dawo daga walimar bikin zagayowar haihuwar Mabaruka ne to Abdulmalik ya fara ganin canjin yanayin karara a fuskar Ummi Karfe tara na dare da yan mintuna ta

Chapter 4 of 7