Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
ya ji a bayansa ta ce. "Ka zo wai tana kira". Anas ya juya firgigit domin ganin mai zazzakar muryar. Daya daga cikin kyawawan matan nan ce ke tsaye a kansa. Da yake ita kadai ce a wurin sai Anas ya sami damar kare mata Kallo sosai. Budurwar dake tsaye a kansa doguwa ce fara, kyakkyawar gaske mai hasken fata. Budurwar za ta yi kimanin shekaru goma sha takwas, ko sha tara me yiyuwa ma ashirin, abu ne mai wuya ka iya fadin shekarunta kai tsaye, domin kyawun fuskarta ma'abociyar annuri da kwarjini sun isa su sa duk wani mai iya hasashen shekaru cikin rudani. Budurwar tana da manyan idanu farare tas! Wadanda duhun dare bai hana Anas ganin fararen idanun ba, wani abu da ya so tsayarwa Anas numfashi shi ne kundukukinta mai annuri gami da shafaffiyar mararta wacce ta bayyana a fili sakamakon tsukakken dinkin bakar shaddar dake jikinta. Kafarta fara sol gwanin sha'awa cikin bakin takalmi. Anas a zuciyarsa ya ce da za a barshi ko da daidai da na dakika guda ne ya sumbaci kafarta da babu abin da zai hana shi ya bada albashinsa na wata guda. . "Tana ina?" Anas ya tambaya cikin karfin hali zuciyarsa na harbawa, lokaci guda kuma ya mike tsaye. "Zo mu je na kai ka inda take." Budurwar ta ce dashi. Babu alamun bakin ko farin ciki a fuskarta. Budurwar ta juya tana rausaya. Anas ya bi ta a baya kamar tunkiya. Sannu a hankali suna tafe har ta kawo shi filin da ake fakin da motoci na ota din. Anas ya godewa Allah, domin har suka isa wurin bai hadu da ko ma'aikacin otal din kwaya daya ba, domin sun dade da yi masa muguwar lambar yawan mu'amala da mata. To amma duk da haka sai da Anas ya raya a zuciyarsa cewa inama su hadu da Sabi'u, domin abin alfahari ne ya ganshi da wannan zukekiyar. Sa'ar da suka kawo farfajiyar sai Anas ya lura duk kusan tarin motocin nan sun baje, sauran da suka rage basu fi guda ashirin ba kawai. Anas na bin dudurwar a baya har ta zo dashi jikin wata mota katuwar (Jeep) Shudiya. Tun kafin su karasa kofar motar ta bude sannan sai muryar Mabaruka ta ratsa kunnensa. "Sannu da zuwa lallai ka cika alkawarinan mabaruka ce zaune a bayan motar ita kadai, sannan a gidan gaba akwai direba wani dogo ne, fari bafulatani. Mabaruka ta dubi kyakkyawar budurwar ta ce. "Na gode Ummi, sai goben kenan idan kin zo. Budurwar ta yi murmushi a karo na farko ta dubi Mabaruka ta ce. "To Mabaruka, Allah maimaita mana, sai da safen, bari in yi sauri ga su fati can a mota suna jirana." Sannan ga mamakin Anas sai ta juya gare shi ta haske shi da murmushi ta ce. "Malam sai da safe." Ta juya cikin sauri ta bar wurin. Anas ya bi ta da kallo, a zuciyarsa yana cewa kai lallai kudi ma dai wallahi banzaye ne domin basu san inda ya kamata su je ba. Koda ya kwatanta kyawun Mabaruka Miloniya da budurwar, sai ya ga tamkar ka kwatanta alli da bakin gawayi ne. "Ga shi har dare ya fara yi." Muryar Mabaruka ta katsewa Anas tunaninsa. Anas ya juya firgigit sannan ya saki wani fatalwar murmushi ya ce. "Ranki ya dade gani." Mubaruka ta kura masa idanu na tsawon lokaci, akwai murmushi a fuskarta. "Da za ka kirani da sunana Mabaruka ina gani zai fi" Anas ya dan rankwafa cikin girmamawa to amma ba ita yake girmamawa ba, miliyoyin kudin da ya ji labarin ta mallaka yake girmamawa. "To ranki...Mabaruk a." Mabaruka ta fashe da yar dariya. "Ka kuwa iya fadar sunan" Anas ya ji wani daddadan kamshi sai hurowa yake daga cikin motar. A iya tsawon lokacin da ya yi yana aiki a otal din ya sha jin kamshi iri-iri daga jikin yan birni da masu hannu da shuni da yan kwalisa masu kunan bakin wake da yan kuru, amma a duk cikin su bai taba jin kamshin da ya kai koda rabin wanda ke hurowa daga motar Mabaruka ba. "Idan ba za ka damu ba, ba zan kuma takura maka ba, zan so ka shigo motar nan mu tafi tare da kai." Mabaruka ta ce da Anas tana duban fuskarsa. Anas ya dubeta cikin tsananin kaduwa ya ce baki na rawa. "Mu tafi...ina?" Mabaruka ta dubeshi da murmushi. "Gidana nake son mu tafi tare da kai domin akwai maganganun da nake son mu tattauna da kai masu muhimmanci" Anas ya dubi nannadadun kafafunta kana ya dago kai ya ce. "Har yanzu ban fahimce ki ba" Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce. "Duk abin da zan fada ma anan ba zai gamsar da kai ba, shi yasa nake so na tafi gidana da kai inda zamu samu damar tattaunawa sosai" Ta dan yi shiru tana nazarin fuskarsa ganin cewa har yanzu a rude yake sai ta ce. "In kuma har yanzu ba ka gamsu ba bari in fito fili in fada ma abin da zamu tattauna. So nake na saye ka!" Anas ya ji gabansa ya fadi ya dubi Mabaruka a rude. Mabaruka ta dubi Anas ta fashe da dariya ta ce "Me ye na ga ka hada fuska kana jin ba zan iya sayen naka bane?" Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya dubeni "Nas wannan shi ne karshen wannan dogon zaren labarin" Na dubeshi cikin kaguwa "Haba Baba ya ya sai da labarin ya dauko dadi za ka katse ni anan?" Sidi mai jaka ya tsikari katon tubani daya ya jefa a baki kana ya dube ni ya ce. "Nas kenan, har kullum ba ka fahimtata in ban da abin ka ai sauran zararrukan labarin da ke gaba sun fi wannan ma dadi nesa ba kusa ba. Ka yi min afuwa Nas zan koma da kai can baya shekaru ashirin da takwas da suka wuce kada ka damu sannu a hankali zan dawo da kai kan tsohon zaren labarin da na gama yanzun nan na hada maka bakinsu in kulle guri guda" Na gyara zama sannan na ce dashi. "To Baba Sidi, ina sauraronka" Abin da yake bani mamaki ga lamarin Sidi mai jaka shi ne irin yadda yake bada labarin ko sarkewa ba yayi. . SIDI MAI JAKA ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya dubeni cikin murmushi, sannan sai ya tura tsinke ya tsikari wani dankareren tubani ya tura a baki. "Nas duk duniya babu abin da na fi so kamar tubani" "Haka ne" Na ce dashi. Sidi mai jaka ya dubeni. "Me yiwuwa ka yi mamakin irin yadda nake ta zubo maka labari bana ko tsayawa" Na gyada kai. "Kwarai kuwa" Na ce dashi "Domin a wancan karon da na zo duk kusan mintuna goma sai ka tsaya" Sidi mai jaka ya fashe da dariya. Sannan ya sunkuyar da kai ya ce. TSOHON ALKAWARIN da ka cika min ne ya sa nake ta kwararo labarin nan ba wakafi balle aya" Na dubeshi cikin mamaki. "Wane tsohon alkawari kuma?" Sidi Mai jaka ya dubi kwanon dake gabansa ya ce. "Tubanin da ka yi min alkawari shekaru biyu da suka wuce shi nake nufi da tsohon alkawari. Domin ba duka mutum bane a wannan zamanin kan iya cika alkawari" Sidi mai jaka ya dan yi shiru sannan sai ya dubeni ya ce. "Nas, ina son ka dauki zuciyarka cancak ka mayar da ita shekaru ashirin da takwas da suka wuce a lokacin ma ba a haifi Mabaruka ba" Na dago da kai cikin kaduwa. "Shekaru ashirin da takwas?" Sidi mai jaka ya gyada kai. "Kwarai kuwa, domin shi ne zaren labarin mu na biyu." Ya dan yi shiru kana ya tsikari tubani ya jefa baki sannan ya dubeni. "Nas, shekaru ashirin da takwas da suka wuce, wasu ma'aurata guda biyu wadanda ke cikin tsananin shauki na kaunar junansu sun kasance zaune a wani fankadeden falo na alfarma wanda a takure zai iya cin mutune sittin ba tare da wani ya shaki numfashin dan uwansa ba. A zaune a daya daga cikin kujerun wani mutum ne dogo, baki, sanye da farar riga suwaita da shudin wanda na shadda, kansa babu hula, hakan shi ya bayyana matashin sankonsa a fili, da yawa daga cikin wadanda suka sanshi a lokacin, sun riga sun yi imani da cewa mutumin ba zai dade da gashi a kansa ba, domin gashi dai a lokacin bai fi shekara talatin da biyar ba a duniya, amma dogon sankon ya gama cinye rabin gashin kansa. Wannan dogon sanko dake kan mutumin bai hana matarsa Aliya mutuwar kaunarsa ba, duk kuwa da cewa a lokacin ma tana da cikin dan wata takwas Wannan mutum mai dogon sankon sunansa A. Faruk. Ba karamin mutum bane, domin a fagen kudi biloniya ne, mamallakin kamfanoni ashirin da takwas a nan kasar. Jita-jita kuma na cewa wai yana da kamfanunnuka sama da goma a kasar Amurka, da kuma wani katon asibiti a kasar Birtaniya. Lokacin da ya auri matarsa Aliya tana yar shekaru ashirin daidai. In ban da yawan maganganu n yan uwa da babu abin da zai sa ya yi aure a lokacin. Domin tun yana dan saurayi kafin ya yi arziki ya taba neman wata yarinya Murja, wani direban mota ya kasa shi, tun daga wannan bai kara sha'awar ya nemi wata mace ba a duniya sai da ya hadu da Aliya. Da farko sa'ar da aka yi bikinsu da Aliya bai taba tsammanin auren zai sami wata kyakkyawar nasara ba. To amma kwanaki uku kacal da yin auren sai ya fuskanci ashe Aliya mace ce ta gari mai iya kissa da soyayyar janyo hankalin maza. Wannan ita ta sa a yanzu A. Faruk yake mutuwar kaunar matarsa Aliya. Duk inda zashi koda kasashen ketare ne tare suke tafiya, to amma yanzu da yake cikinta ya tsufa sun fi wata uku a gida Najeriya suna renon cikin. Aliya ta muskuta akan kujerar ta shafa cikinta ta ce. "Kwanta Mabaruka yar gata." A. Faruk ya ajiye jaridar dake hannunsa kana ya shafi dogon sankonsa ya dubi matarsa Aliya cikin murmushi. "Aliya, ke fa wallahi ba kya rabuwa da rigima in ban da abin ki wa ya ce dake mace za ki haifa da har ki ke sanya mata suna Mabaruka?" Aliya ta harareshi, sannan ta mike da kyar, ta nufo inda yake, tana zuwa sai ta kwanta akan cinyarsa a rigingine kana ta shafo cikin nata ta dubeshi ta ce a tausashe. "Ni na san mace ma zan haifa in Allah ya yarda." Faruk ya fashe da dariya ya dubeta. "To yanzu da har ki ka sa mata suna Mabaruka idan kika haifi namiji kuma me za ki sa masa? Kamata ya yi ki zabi sunaye biyu, na mace da na namiji, ina ganin zai fi kyau idan namiji ne mu sa masa suna Mabaruki." Aliya ta fashe da dariya. "Kai (darling) don Allah ka daina sa ni dariya, kar ka sa cikina ya yi ciwo." Faruk ya dubeta. "A'a, to ke kin ga laifina? Tun da dai kin ce idan mace ce za ki sa mata Mabaruka ni kuwa idan namiji ne sai in sa masa Mabaruki." Aliya ta kamo wuyansa cikin dariya ta matso da fuskarsa kusa da tata, ta dora bakinta akan kunnensa ta ce. "Kai a tunaninka idan na haifi mace da wa za ta yi kama?" Faruk ya dan dago kansa sama ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya, sannanTSOHON ALKAWARI-5 . Faruk ya dan dago kansa sama ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya sannan ya tuna da dogon sankonsa, gami da tababben hancinsa wanda sau da yawa, shi yake hana shi ganin madubi, sai ya dubeta da murmushi ya ce. "Ina fatan ko mace, ko namiji za ki haifa Allah ya sa ya yi kama da ke Aliya. Aliya ta rungumo shi cikin farin ciki domin ita kanta ta san kyakkyawa ce. Anan, sai Sidi Mai Jaka ya yi shiru, sannan ya sa hannu ya goge gumin da ke sartu akan goshinsa. Me yiwuwa zafi ne, babu mamaki kuma zazzafan yajin tubanin ne ya sashi gumi. Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce. "Nas, wani sa'in matasan mata sukan bani mamaki, da zarar sun sami ciki sai kaga suna ta zaben, wai sun fi son su haifi mace, ko namiji ko kuma mai kama da su, ko kyakkyawa...hak a dai za ka ji suna ta kawo tsarabobi iri daban-daban kai ka ce su ke da ikon halitta. Ni a ganina Nas, gara a bar wa Allah zabi domin shi ne gwani akan komai ko kuwa me ka gani?" Na gyada kai cikin sauri. "Haka ne. Ci gaba baba." Sidi mai jaka ya dubi kwanon tubanin dake gabansa kana ya girgizaq kai cikin takaici, domin duk yawan tubanin nan dake ciki ya nhadidiyesu kamar zakara wadanda suka rage basu fi kwaya goma ba. Sidi Mai jaka ya canki na goman karshen ya jefa baki kana ya ci ga. "Nas, wata guda da yan kwanaki, da faruwar wannan hira da na baka labari dazu tsakanin ma'auratan biyu, sai Aliya ta haihu. Ta wani bangaren haihuwar ta zo musu kamar yadda suka zata tun farko to sai dai kuma ta wani bangaren haihuwar ta zo musu a murde, musamman ma Aliya. Lokacin da Aliya ta haihu bata san inda hankalinta yake ba, sai bayan kusan sa'a guda da haihuwar ne sannan likita ta zo gabanta da murmushi ta ce. "Ina taya ki murna kin haifi mace." Aliya ta yi matukar farin ciki da jin cewa mace ta haifa, amma sa'ar da likitan ta miko mata jaririyar da ta haifa sai duniyar jin dadin Aliya ta birkice lokaci guda. Aliya ta dubi jaririyar cikin kaduwa, ko kusa ko alama jaririyar bata yi kama da ita ba, gashi dai lafiyayyace sosai to amma irin tabebben hancin mahaifinta ya mamaye kusan rabin fuskarta, bugu da karin bakin ciki ga Aliya kuma jaririyar ba ta da kafafu domin duk a shanye suke sili-sili kamar maburgi. "Wannan...kafaf un nata ba za su gyaru ba?" Aliya ta tambayi likitan muryata na rawa. Likitan ta girgiza kai cikin jimami. "Babu wani likita a duniya da ya isa ya gyara kafafun nan nata. Ki godewa Allah da ya kawota duniya cikin koshin lafiya, ba kya ganin idan ki ka dauke shanyayyun kafafun lafiyarta kalau." A daidai lokacin da likitar ta yi shiru sai jaririyar ta bude idanu. Aliya ta dubeta tayi kamar za ta fashe da kuka Ga mamakinta sai jaririyar ta dubeta ta washe baki cikin murmushi Aliya ta rungume yar jaririyarta cikin kuka ya ce. "Ina son ki Mabaruka, ina son ki haka nan domin haka Allah ya so ya gan ki." Shekaru ashirin suka shude kamar wasa, a cikin shekaru ashirin din nan babu irin gatan duniyar da Mabaruka bata gani ba. Anan Najeriya ta yi makarantar firamare dinta, amma duk sauran karatunta a Burtaniya ta yi. Duk da kasancewar Mabaruka gurguwa kuma mummuna, iyayenta basu ki nuna mata tsananin soyayya ba. Wani Ikon Allah kuma tun daga kan Mabaruka, Aliya ba ta sake haihuwa ba, wannan shi ya kara tsananin kaunarsu a gare ta. Mabaruka ta tashi cikin jin dadi, da gata marar misaltuwa, ga ta dai gurguwa amma duk satin duniya sai ta hada hadaddiyar liyafa, wani sa'in kuwa sai ta tara guragu irinta, ta sa su bi layi a kofar gida, ita ko a yi ta turata akan keken guragu na musamman tana raba musu kudi, tufa, ko abinci. Kudi ba matsalar Mabaruka bane, domin mahaifinta Alhaji Faruk biloniya ne, ya gama tara mata su gashi kuma ita kadai ce bata da ko kani guda daya. Wata rana Mahaifinta ya taba cewa da ita. "Mabaruka, duk abin da ki ke so ki yi da kudi ki yi kawai kar ki ji tsoron komai ki yi ta kashewa tun da dai naki ne. Ki godewa Allah da ya yi ki gurguwa da uba biloniya." Mahaifin Mabaruka ya mutu tana da shekaru ashirin da hudu a duniya, sakamakon wani mummunan hadarin jirgin kasa da ya ritsa da shi a kasar Indiya. Mahaifin nata Faruk ya bar duniya da bakin cikin har Allah ya karbi ransa bai ga mijin yar sa abar kaunarsa Mabaruka ba. Sau da yawa ya kan so ya tambaye ta shin ko ta sami saurayi To amma idan ya tuna da yadda take ita ba kyau ba a fuska hakan nan ga ta gurguwa sai ya yi shiru domin ko kadan bai san ya yi abin da zai sosa mata rai Duk da haka nan sau da yawa ya kan yi alfahari da ita domin ta yi matukar kama dashi musamman ma tababben hancinsa mai kamar begila. Sa'ar da mahaifinta ya rasu, sai duk kusan kamfanunnukansa da makudan kudinsa gami da sauran muhimman kadarorinsa suka koma karkashinta. Cikin kankanin lokaci ta zamo tabani ka ga sarki, ga ta dai gurguwa kuma mummuna, amma fuskarta ta fi komai kyau ga duk wanda ya santa a zahiri da badini ba don komai ba kuwa sai don dimbin arzikinta. Lokacin da mahaifin Mabaruka ya cika shekaru hudu da rasuwa, sai mahaifiyarta Aliya ta yi kiranta wata rana da yamma ta ce da ita. "Mabaruka kina tunanin aure kuwa?" Mabaruka ta sunkuyar da kai cikin taraddadi, domin ta san tun da take wani saurayi bai taba dubanta a matsayin ta burgeshi ba, sai dai ya dubeta a matsayinta na macen da ta fi kowa arziki a cikin matan Afirka. "Ina yi." Ta ce da mahaifiyarta kanta a sunkuye. Aliya ta dubeta cikin tausayi, domin ta san ko ita da ta sha miya a duniya ta fi Mabaruka kyan gani a fuska. "In dai kin sami wanda ki ke so sai ki sanar dani, kin ga ke kadai nake da ita a duniya, shi yasa nake matukar son na ga jikokina a duniya tun ina da sauran numfashina." Mabaruka ta yi shiru tana sauraren mahaifiyarta, yanayin fuskarta a birkice. Ita kanta ta san mummuna ce, sau da yawa in ta kalli madubi sau daya ba ta son ta kuma kallo a karo na biyu, amma ta kan gode Allah da ya yi mata dimbin dukiya. Aliya ta yi nazarin fuskar yar ta na tsawon lokacin sai ta ga duk hankalinta ya tashi. Ta san abin da ke damunta dan haka sai ta dubeta da murmushin karfafa gwiwa ta ce. "Kada ki damu da yadda Allah ya yi ki Mabaruka, abin da nake so ki kula shine kina da dukiya, kin san kuwa a wannan zamanin ba ta da na biyu." Ta dan yi shiru tana nazarin fuskar Mabaruka. "Ina fatan kuna fahimta ta?" Aliya ta ce da ita tana dubanta ido da ido. Mabaruka ta girgiza kai a sanyaye. Akwai alamun kwalla a idanunta. To amma bata bari mahaifiyarta ta gane ba domin ta san hakan na iya tayar mata da hankali. "Abin da nake so da ke Mabaruka shi ne ki duba ki waiga, ki hanga da idanunki, duk fadin garin nan, idan kin hango namijin da ki ke so, ki ka ga ya kwanta miki a rai ko wane ne shi ki yi kokarin ki shawo kansa ya zo nan gida gurina!" Mabaruka ta dubi mahaifiyarta cikin kaduwa ta ce. "Mama...ya ya za a yi na iya kawo shi har gida? Sai dai in shi ne ya ganni ya zo ya ce yana sona." Aliya ta dubeta gami da dariya. "Mabaruka kenan. Na fahimci har yanzu ba ki san irin yadda mutane suka dauke ki bane. To bari in fada miki duk kasar nan ke ake labari saboda tsabar kudin da ki ka gada. Duk da yadda ki ke ganin ki din nan ki ke raina kanki kin fi karfin raini, domin kudinki ya wanke duk wani nakasu naki. Saboda haka ina son ki sani cewa babu wani da namiji da za ki kirawo a girin nan ya ki zuwa gare ki ko shi wane ne, domin kina da babban makamin da ya fi nukiliya tasiri, dan in ba kudi babu zancen nukiliya balle aikinsa." Aliya ta dan yi shiru tana duban fuskar Mabaruka sannan sai ta daga hannu ta nuna fuskarta ta ce. "Na baki daga nan zuwa sati guda duk namijin da ki ka gani ya yi miki ki yi kokarin ki kawo min shi nan.. Nan da rana ya ta yau kenan.... Ranar da ta yi daidai da cikarta shekaru ashirin da takwas a duniya! Mabaruka ta ji wani zazzafan gumi ya fara lullubeta. Tambayar da ta fi damun zuciyarta shi ne, shin a cikin mako guda ya ya za a yi ta sami saurayin da ta ke so, ta kuma iya jawoshi har gida! Sidi Mai jaka ya yi shiru anan, sannan ya dubeni da murmushi ya ce. "Nas, ka ga abin da nake fada ma ko? Ai daman sai da na ce da kai kayi hakuri da sannu zan hade ma bakin zaren labarin biyu na daure. Gashi kuwa na daure ma su kamar yadda na yi maka alkawari." Na dago kaina gami da ajiyar zuciya "Haka ne." Na ce dashi "To ya ya kuma bayanin can inda muka baro, inda Mabaruka ta ce da Anas ya shiga mota su tafi." Sidi mai jaka ya dubeni ya yi murmushi ya ce. "Nas kenan, na dai fuskanci ka fi son can daya bangaren labarin ban yi mamaki ba a matsayin ka na saurayi dole ne labarin soyayya da kudi ya burge ka." Sidi Mai jaka ya yi shiru kana ya tsikari tubani guda ya jefa a baki ya dubeni idanunsa na zubar da ruwa kamar kuturu saboda masifaffen yajin dake cikin tubanin "Nas, ina son ka kaddara a cikin zuciyarka cewa ga Mabaruka da Anas nan zaune a cikin tangamemen falon gidansu Mabaruka suna fuskantar mahaifiyarta Aliya "Na kaddara." Na ce dashi cikin sauri domin na gama kaguwa na ji yadda za ta kasance. Sidi mai Jaka ya goge hawayen dake zuba daga idanunsa sannan ya ci gaba. Daga lokacin da katuwar (Jeep) din ta ajiye su Anas da Mabaruka a farfajiyar gidan zuwa lokacin da suka ratsa akalla Falo Bakwai ANAS YA GAMA FITA DAGA HAYYACINSA domin a iya tunaninsa bai taba imani da cewa akwai gidan da ya kai na su Mabaruka tsaruwa ba a duk fadin garin. Gashi dai Anas ma'aikacin otal ne, haka nan otal din ita ce uwa ga duk wata otal dake fadin garin wajen kayatuwa, amma sa'ar da ya ga irin tsari da ni'imar da aka shirya a gidansu Mabaruka sai ya ga duk darajar otal din ta zube a gurinsa, ta koma tamkar kango a zuciyarsa. A tunanin Anas ya dauka irin kayatattun gidajen nan da ya kan gani a finafinan Turawa, ba za a iya taba samunsu anan ba sai a kasashen turawan, domin abu ne mai wuya ace irin yadda almajirai ke cika tituna taf da barace-barace da kuma tarkacen marasa aikin yi da talakawan dake ta sintirin neman abinci sau daya a rana a titunan Najeriya, wai za a sami mai arzikin da har zai iya gina irin wannan! Hakika Anas ya yi masifar kaduwa sa'ar da ya shiga gidansu Mabaruka domin bashi da maraba da irin wadanda yake gani a finafinan turawa. Anas ya yi imani da cewa da ace za a dauke shi a cikin barci bai sani ba a jefashi a gidan, idan ya farka ya ganshi ciki babu abin da zai hana ya ce aljannu ne suka dauko shi suka kawo shi London. Lokacin da suka isa babban falon gidan karfe takwas da yan mintuna. Sa'ar da Aliya ta shigo dakin tuni har Anas ya zabi bangare guda na daga tarin kujerun dake dakin ya lume a ciki, to sai dai kuma duk wanda ya ganshi ya san a bala'in tsorace yake, domin a rabe yake a gefe guda ya yi fakare baya ko kwakkwaran numfashi kamar jikakken zakara. Aliya ta matso zuwa tsakiyar falon, ta dubi Anas da tattusan murmushi. "Ina son ka saki jikinka Anas ka dauka a zuciyarka cewa nan gidan ku ne." Anas ya ji gabansa ya fadi ras! Rabon da da wani ya ce dashi nan gidansu ne, tun ziyarar sa gidan wata budurwarsa Safiya wadda iyayenta suka so su makala masa ita, da kyar Anas ya samu ya tsere, domin a duk fadin duniya abokan gabarsa guda biyu ne, talauci da aure! Aliya ta nemi kujera ta zauna. Daga inda take zaune tana fuskantar su Anas, hakan nan ta lura da cewa Anas duk a rude yake tuni har ya faera zubar da gumi duk kuwa da ni'imar rabar dake kwararowa dakin. A zuciyarta, Aliya na cewa lallai abin ma zai zo da sauki tunda ma ya gama tsorata dani, don haka sai ta kalli Anas kai tsaye ta ce. "Ina fatan ta fada ma dalilin da ya sa ta kawo ka gidan nan?" Anas ya dubi Mabaruka a rude, Mabaruka ta yi masa murmushin yake, sannan ta sunkuyar da kai a kunyace a zuciyarta tana cewa, oh! Yau na shiga uku za a tursasa mutum ya aure ni ba tare da yana kaunata ba. Ganin Anas ya yi shiru sai Aliya ta dube shi ta ce. "Bawan Allah mene ne sunanka?" "Sunana Anas...." Ya ce bakinsa na rawa. Aliya ta sake duban kyakkyawar fuskarsa ta ce, "Ina son ka dubi yarinyar nan da kyau ya ta ce." Anas ya dago kai cikin kaduwa ya dubi mummunar fuskar Mabaruka na dakika uku sannan ya sunkuyar da kansa. "Na...kalleta.. ." Aliya ta yi murmushi "Anas, abin da ya sa na ce ka dube ta shi ne, domin ka ajiye hotonta a cikin zuciyar ka, domin ita ce matar da za ka aura." Anas ya dago kai cikin tsananin kaduwa, "Hajiya...ban fahimce ki ba?" Aliya ta dubeshi da murmushi. "Sannu a hankali za ka fahimce ni ka kuma fahimci dalilin da ya sa na ce da kai ita za ka aura." Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. "Da farko dai ina son ka sani cewa ni ce na sa Mabaruka na ce da ita duk namijin da ta gani ta ji ya kwanta mata a rai ta kawo min shi.....TSOHON ALKAWARI-6 . "Abu na biyu kuma shi ne tun da aka haifi Mabaruka bata taba neman wani abu ta rasa ba, shi yasa to na ce da kai ita za ka aura, domin kaunarka ce ta sa ta kawo min kai." Anas ya ji kamar an dora masa buhun alhaki a tsakiyar kansa, domin ko mosti baya iya yi zaune yake ya yi mutuwar tsohuwa sai idanunsa ne ke ta kifkiftawa kamar idanun barawon akuya, to amma zuciyarsa na kai kawo. Cab! Na auri gurguwa mummuna! Ai da na auri wannan ma gara na auri uwar domin ta fita komai da komai.Anas ya share gumi sa'ar da zuciyarsa ta tuno masa da cewa wannan mummunar gurguwar fa da ake kokarin cusa masa, sunanta KUDI! "Anas." Aliya ta katse tunanin sa. Anas ya dago kai ya dubeta. "Ina son ka bani hankalin ka nan." Anas ya dube ta ido da ido ya ce. "Ina jin ki." "Idan ba ka san wannan yarinyar dake gabana ba bari in fada ma. Ka ga duk fadin kasar nan babu wata mace da ta mallaki kashi daya bisa hudun dukiyar da ta mallaka haka nan ita ce mace ta biyu a kudi a cikin duk matan Afirka Da mun biya ta mutane da tuni an aure ta ko dan a amfani kudin da take dashi, to amma kuma ni na fi son ta zabi wanda take so da kanta." Aliya ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. "A yanzu kai ta gani ta ke so shi ya sa ta kirawo ka gare ni. Anas ina so ka auri Mabaruka domin auren ta alheri ne a gare ka." Ta sake yin shiru a karo na biyu sannan sai ta dubeshi ta ce. "Nawa ake biyanka a wannan busasshiyar otal din da kake aiki?" Anas ya hadiyi yawu da kyar kwakwalwarsa sai juyawa take yi cikin kokon kansa. "Du...dubu takwas!" Aliya ta dubeshi ta fashe da dariya ta ce. "Dubu takwas! Kyakkyawan saurayi kamarka a dubu takwas? Ko kuwa kullum ne ake biyanka dubu takwas din? Anas ya girgiza kai. "Wata-wata ake biyana." Idanun Aliya suka zazzaro waje cikin tsananin kaduwa. "Wata guda a dubu takwas." Cab! Allah rufa asiri." Ta yi shiru na dan lokaci sannan ta sake duban Anas. "Idan yanzu na baka manajan daya daga cikin kamfanunnukanta albashin naira dubu dari biyu ya yi ma...a wata guda nake nufi." Anas ya ji zuciyarsa ta harbo da karfi kamar kibiya tana kokarin fasa masa kirji, dubu dari biyu! Tun da yake bai taba tsammanin zai sami dubu hamsin ma ba a duniya lokaci guda. "Ya...yi min." Ya ce da kyar domin makogwaronsa ya bushe. Aliya ta yi murmushi sannan ta ci gaba da cewa. "Ka je gida ka turo iyayenka domin nan da sati guda za a daura muku aure. Ina son kuma ka sani cewa daga yanzu duk inda kake so a duniya za ka iya sa kafar ka, haka nan ban da albashinka, duk karshen wata na yi maka alkawarin naira dubu dari daga cikin ribar da nake samu karshen wata a kamfanina na atamfa, sannan a matsayin kyauta ta musamman da zan yi ma a matsayin ka na angon yata zan saya ma

Chapter 2 of 7