Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
wannan busasshiyar otal din da kake aiki a ciki, in sa a rugujeta a sake gina ma ita, in ya so sai ka zabi sunan da ka ga ya dace ka sa mata." Aliya ta yi shiru tana numfasawa, sannan sai ta mike tsaye ta dubi Anas ta ce. "Ka yarda zaka aure ta?" Anas ya ji kamar katanga ta fado masa a tsakiyar baya. Abu daya da ya tabbatarwa kansa shi ne in duk za a bashi duniyar nan domin ya kaunaci wannan mummunar gurguwa ba zai taba iyawa ba, to amma da albashin naiura dubu dari biyu a wata, da naira dubu dari a sama da kuma kyautar otal din da za a bashi, ya tabbatar ko da Mabaruka kuturwa ce sai ya aureta. Cak! Yau na zama miloniya cikin sa'a guda... Ya ce cikin zuciyarsa, koda ya tuna da cewa lagwada otal za ta zama tasa sai ya ji wani zazzafar gumi na farin ciki ya zubo masa tuntuni ya dade yana addu'ar Allah ya bashi damar da zai rama wulakancin da manajan otal din ke yi musu, sai gashi a banza yanzu dama ta samu a bagas. Wani busasshen murmushin mugunta ya subucewa Anas nan da nan ya dauki alkawarin cewa duk ranar da ya mallaki ota din sai ya tikawa dan dukurkushin manajan dundu a tsakiyar baya. "Anas!" Aliya ta katse masa tunani "Tunanin me kake... Baka amince bane?" Anas ya girgiza kai cikin sauri sannan ya ce. "Kin ce cikin sati za a daura auren ni ko yanzu naira dubu takwas ce daidai a aljihuna ita ma ta albashin da aka biyani ce dazu da yamma." Aliya ta yi murmushi sannan ta ce "Tun da ka amince ina kai ina fargabar kudi, nan gidansu ka zo." Ta dan yi shiru sannan sai ta ce. "Kana jin naira miliyan goma zata isheka fara shirye-shirye kafin zuwa jibi". Anas ya ji yawun bakinsa ya kafe ya dube ta a rude. "Miliyan goma kika ce ko kuwa dubu goma." Aliya ta fashe da dariya sannan ta dubi yarta Mabaruka wacce ke gefe ta yi tagumi tana sauraronsu ta ce "Miliyan goma na ce ko sun yi ma kadan a kara ma?"**** Sidi mai jaka ya yi ajiyar zuciya sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa cikin takaici duk yawan tubanin nan ya hadiyesu baki daya saura kwaya uku kacal cikin kwanon. "Nas ga labari ya dauko dadi gashi kuma tubanina ya zo Gangara. Irin wannan abin shi yakansa wani lokacin na ji duk na tsani bada labari domin tubanin nan tamkar mota ce da man fetur idan babu shi ka san ban cika abin kirki ba". Sidi mai jaka ya yi shiru yana kallon cikin kwanon tubanin sannan ya dubeni fuskarsa a murtuke. "Kamata ya yi ka karasa min zuwa sallar Azuhur, idan na koma gida sai na sa kakata ta sake yi ma wani tubanin." Nan da nan fuskar Sidi mai kaja ta washe. "shi yasa nake son ka NAS. Domin daga na yi motsi sai ka gane abin da nake nufi." ya dan yi shiru, sannan sai ya ce, bari a gurguje na kulla maka wani sabon zaren labarin da wannan, domin naga kamar lokacin sallah ya kusa." Sidi Mai Jaka ya tsikari tubani na ukun karshe ya jefa a baki sannan ya dubeni. Nas, ina son ka dauka cewa tuni har an daura auren Anas da Mabaruka gurguwa." "Na dauka." Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dubeni, sannan ya ci gaba. Wato Nas, watanni biyun da suka biyo bayan bikin Anas sun yi matukar jefa Anas a cikin sabon yanayi. Lokacin da Anas ya bar gidan su Mabaruka bai tsaya ko ina ba sai wurin iyayensa, jikinsa na rawa ya ce da su aure zai yi. Lokacin da labarin auren nasa ya watsu a cikin dangi sai aka yi ta zuwa ana taya mahaifansa murna, domin duk garin babu wanda bai san ko wacece Mabaruka ba. Da yawa daga cikin mahassada suka yi ta zunde, tsegungumi da gulma, suna cewa wai in ba lalacewa ba ina kyakkyawa kamar Anas ina auren gurguwa mummuna. Wasu daga cikin masoyansa sun taya shi murna, domin sun san duk da dai bai yi dacen mata ba, to amma ya yi bankwana da talauci har abada, wannan a gurinsu ya isa abin farin ciki, domin a tunaninsu Anas ya gama samin kwanciyar hankali da nutsuwa. To kamar yadda suke tunani NAS hakanan ta kasance a cikin watanni biyun da suka biyo bayan bikinsu, domin Anas ya sami hutun da bai taba tsammani ba a iya tsawon rayuwarsa. Da farko dai da yake daman shi ba damuwa ya yi ba da wani addini ba kullum kwanan duniya Anas baya tashi daga barci sai karfe goma sha daya na safe, sannan ne zai tashi ya yi wanka, sannan ya nufi wurin aiki. Zamantakewarsa da Mabaruka ta bashi mamaki, domin ya sami Mabaruka macece mai iya dadin magana, da tarairaya, duk kuwa da cewa gurguwa ce, wani sa'in sai su tafi bakin (Swimming pool) su yi ta wasa da katuwar bal marar nauyi, Mabaruka na zaune akan kujerarta a bakin ramin ruwan, shi ko yana ciki, idan ya jefo mata, sai ta cafe ta jefa masa. Wani sa'in kuwa sai Anas ya dauketa a mota su yi ta yawo a cikin gari suna bin guraren shakatawa abinsu da yake Anas gwanin ban dariya ne, sai ya yi ta yi Mabaruka tana dariya. Wannan ita tasa sau biyu ko uku kawai Anas ke zuwa gurin aiki a sati. "Kada ka dami kanka Anas da yawan zuwa wurin aikin nan kudi ne, muna dashi albashinka kuma ko kaje ko baka je ba dole ne a baka." Mabaruka ce ke cewa Anas haka a wata safiya suna karin kumallo. "Anas, zamanka kusa dani ya fi min zuwanka aiki, domin ni har kullum idan na dubeka sai na ji zuciyata ta yi fari tas, dan haka ne bana son rabuwa da kai koda dai dai da kankani...domin ..." Ta dan yi shiru tana duban Anas. Anas ya dube ta sa'ar da ya ji tayi shiru. "Domin muma me...?" Mabaruka ta dube shi. "Domin bana son wata mace ta mallaki zuciyarka a duniya idan bani ba, shi yasa ka ga na ce ma sau biyu kawai za ka ke zuwa aiki a sati." Anas ya ji zuciyarsa ta harba, ko a lokacin da yake yawon banzan sa, babu abin da ya tsana a rayuwarsa irin mace mai naci, wacce zata makale masa kamar cingam ta hanashi shan iska. Sidi mai jaka ya dago kai ya dubeni da murmushi sannan ya ce "Nas, wata uku su Mabaruka suka yi cikin farin ciki, daga wannan kuma basu kara samun koda dai dai da sa'a daya ba ta farin ciki, domin a safiyar wata rana ne Mabaruka ita da kanta ta yi sanadiyar kawo karshen duk wani farin ciki nasu! Wata rana da safe aka yi sa'a Anas ya farka tun da asussuba, koda yake ba farkawar Allah da Annabi bace. Anas na kwance kawai sai ya ji idanunsa sun bude. Abin ya ba shi mamaki dan haka sai ya dubi agogo. Karfe hudu na asuba agogon ya nuna. Anas ya tashi zaune cikin mamaki, ya dubi Mabaruka gurguwa kwance a kusa da shi a takure kamar kunkuru tana ta barci abinta, mummunar fuskarta a yatsune. Anas ya dauke kai zuciyarsa na wasi-wasin dalilin da ya sashi farkawa a wannan lokaci. Tsawon lokaci yan zaune akan gadon, sannan ne to maganar Mabaruka ta fado masa. "...bana son wata mace ta mallakeka a duniya idan bani ba..." Wani zazzafan gumi ya barkowa Anas, sa'ar da ya tuno da wannan kalami nan da nan ya sake duban mummunar fuskar Mabaruka. A zuciyarsa ya ce cab! Ba zata yiwu ba duk kyawawan matan dake duniyar nan na rasa wacce zan kare rayuwata da ita sai wannan! Anas ya share gumi sannan ya dada kallon Mabaruka tsigar jikinsa ta dauki rawa....TSOHON ALKAWARI-7 . Sannan ya dada kallon Mabaruka, tsigar jikinsa ta dauki rawa. Dole ne na sami hanyar da zan rika zagayawa gari ni kadai, ya ce cikin zuciyarsa, wani abu da ya fi baiwa Anas tsoro da al'amarin Mabaruka shi ne ya fahimci tana da bala'in Kishi. Sau da yawa idan suna tafiya a mota da taga ya dauke idanunsa gefe guda ya kalli inda mata suke sai ta kalleshi ta ce. "Me kake kallo?" Anas ya kan ji zuciyarsa kamar za ta fashe saboda haushi. Me take nufi ne da zata hana shi kallon kyawawa bayan duk da tarin miliyoyin kudin nan nata yar karamar yarinyar dake talla a gefen tituna ta fita fasali Bayan da wannan kuma akwai wata rana da yamma wata kawar Mabaruka wai ita Amal ta ziyarci Mabaruka Lokacin da ta samesu zaune suke cikin tangamemen lambun shakatawar gidan Anas yana karantawa Mabaruka wani littafi na hausa wai shi SIRRINSU. Tun kafin Mabaruka ta gama gaisawa da Amal ta kura masa idanu. Anas ya lura da irin kallon da take yi masa, dan haka sai ya yi sauri ya sunkuyar da kansa kamar yana kallon littafin da yake karantawa duk kuwa da cewa a fakaice kallon kyawawan kafafunta yake yi ta kasan littafin. "Tashi ka koma daga ciki kadan bamu guri zamu gana, idan mun gama zan sa a kirawoka." Mabaruka ta ce dashi, Anas ya mike tsaye simi-simi kamar tunkiya ya wuce cikin gidan zuciyarsa na kuna. Kalmar ta yi matukar kona masa rai, to amma tunda dai an saye shi ya yarda ya amince babu abinda zai iya domin kowa ya sayi rariya ai ya san ta zub da ruwa. Idan har akwai abu daya da Anas ya tabbatarwa da zuciyarsa shi ne ba zai taba yarda ya batawa Mabaruka rai ba, domin ya san hakan na nufin rabuwa da ita, shi ko ya san a yanzu ya gama sabo da jin dadi kum... "Anas." Ya juyo firgigit sa'ar da muryar Mabaruka dake kwance kusa da shi ta katse tunaninsa. Mabaruka ta dubi agogo, sannan ta yi mika ta dubi Anas cikin mamaki ta ce. "Lafiya na ganka a zaune haka tunda asussuba." Ta dan yi shiru sannan sai ta miko siraran hannunta ta shafi bayan Anas. "Ko ba ka da lafiya ne?" Ta rikoshi ta mike zaune, nannadaddun kafafun da Anas ya tsana fiye da komai a jikinta suka fito fili. Anas ya girgiza kai. "Kaina ne ya ke dan sara min...amma na san nan da dan lokaci zai bari daman lokaci- lokaci yakan yi min haka." Mabaruka ta dubeshi cikin shakka da mamaki ta ce. "Ina jin rashin yawan motsa jiki ne..." Ta dan yi shiru, sannan sai ta ce ya kamata na hada mana wata hadaddiyar liyafa ta shakatawa a gidan nan, ina ganin haka zai sa ka dan warware, kuma kamata ya yi bayan liyafar mu tafi kasashen turai hutu, domin tuntuni ya kamata ace mun tafi mun yi (honey moon) dinmu a can, dadin da bana ji sosai ne ya hana." Ta dan yi shiru tana duban fuskar Anas "Ko kuwa ya ka gani." Anas ya ji wani dadi ya lullubeshi domin tabbas ya san irin liyafar miloniya me take nufi ko shakka ba ya yi za a tara zuka- zukan mata kyawawa, abin da idanunsa suka fi kaunar gani fiye da komai a duniya. Don haka sai Anas ya dubeta cikin sauri ya ce. "Kwarai kuwa haka za a yi liyafa ba lallai kin zo da dabara." Suka fashe da dariya, sannan Mabaruka ta dora kanta bisa cinyarsa ta rungumoshi fuskarsa kusa da tata, abin da Anas ya yi matukar tsana, ta ce. "Anas wai don Allah me ka fi kauna fiye da komai a duniya?" Anas ya dubeta cikin mamaki domin tambayar ta zo masa a bazata, kadan ya rage ya ce da ita kyawawan mata, to amma da yake tsohon kwararre ne a sanin tarkon mata ya fahimceta don haka sai ya dubeta da tattausan murmushin yaudara ya dada rungumota a kirjinsa ya ce. "Abin da na fi kauna a duniya ki ke son ki sani?" Mabaruka ta gyada kai cikin murmushi. Anas ya dubeta a tausashe duk kuwa da cewa zuciyarsa kamar ta tsage saboda haushi ya ce. "Ke na fi kauna fiye da komai a duniya." Mabaruka ta lumshe idanu cikin tsananin farin ciki Tun da take a duniya bata taba jin kalamin da ya faranta mata rai kamar wannan ba. Wani zazzafan hawaye na farin ciki ya yi sartu akan fuskarta. *** Sidi mai jaka ya dauki dunkulallen tubanin karshe ya jefa a bakinsa, ya dubi kwanon cikin takaici, sannan ya dubeni ya ce. "Nas, ranar liyafa ta zo. Kamar yadda Anas ya yi tsammanin tun farko haka ta kasance domin duk kusan kala-kala ta kyawu na mata babu wadda ba a hada a wurin ba. Liyafar ta sami halarta mata kyawawa ashirin da uku, maza goma kacal wadanda mafi yawa ma daga cikinsu duk Anas ya girmesu. Aka yi ciye-ciye da shaye-shaye a tangamemen lambun shakatawar, aka saki kidan dujal yan mata da samari masu karancin kunya suka fara tikar rawa. A can gefe guda gindin wata katuwar lema fara, Mabaruka gurguwa ce da angonta Anas, ta caba kwalliya ta gani ta fada, to amma a wurin Anas kukun dake rabon abinci ma a wurin tafi Mabaruka kyawun fasali. . A daidai lokacin da liyafa ta yi liyafa ne to zazzakar murya mai kama da sarewa ta daki dodon kunnen Anas Nan da nan ya ji numfashin sa ya dauke ko shakka ba ya yi ya san mai muryar. "Yaya Mabaruka ki yi hakuri don Allah wallahi unguwa muka je sai yanzu na sami damar karasowa." Mai zazzakar muryar ce ke magana sa'ar da ta matso kusa da su cikin sauri. Anas ya kura mata idanu cikin tsananin shauki, zuciyarsa na harbawa, rabonsa da ganinta tun ranar da ya fara haduwa da ita. In ba dan muryar ba da zai yi wuya ma ya ganeta domin ta dada tsayi kadan ta dan kara kauri haka nan kyawunta ya dada bayyana a fili har daukar idanu fuskarta ta ke yi. Anas ya yi mamakin ganinta matuka. Budurwar mai zazzakar murya ba wata bace da ta wuce Ummi, budurwar da ta kirawo wa Mabaruka Anas a ranar da suka fara haduwa a wurin liyafar bikin haihuwar Mabaruka. Sidi Mai jaka ya dan yi shiru sannan ya dubeni ya ce. "Nas, ina fata ka tuna ta?" Na gyada kai cikin kaguwa domin na fahimci kamar ma yanzu ne labarin tsohon zai fara dadi. Sidi mai jaka ya ce "Yawwa Nas, sannan ya ci gaba. Mabaruka ta dubi budurwar cikin farin ciki sannan ta ce. "Ba ki da kirki Ummi kada ma ki yi kokarin wani kare kanki, idan yanzu kin zo a makare, to me ya hana ki zuwa liyafar aurena?" Ummi ta rufe fuska cikin dariya, sannan a karo na farko sai ta dubi Anas da tausasshen murmushi ta matsa kusa da shi ta durkusa ta ce. "Yaya Anas ina wuni..." Anas ya ji wani dadi marar misaltuwa ya kwarara cikin zuciyarsa. Cikin sauri ya tausasa murya ya ce. "Lafiya lau...Ummi!" Idan ya yi kuskurensa na farko kenan kiran sunan nata da ya yi. Ummi ta dubeshi cikin mamaki ta ce. "Ashe ba ka manta suna na ba." Murmushin Anas ya fadada. "Ai...tun...tun ..." Ya yi shiru sanda ya lura Mabaruka ta sunkuyar da kai ta mance dasu. Anas ya mike tsaye jikinsa na rawa ya dubi Mabaruka ya ce. "Darling bari in dan zagaya na barku ku gana." Nan da nan fuskar Mabaruka ta washe domin zamansa da Ummi shi take tsoro. "Kwarai kuwa gara ka bamu wurin domin muna son mu yi sirrinmu na mata." Anas ya mike ya nufi cikin farfajiyar lambu inda samari da yan mata ke ta sheke ayarsu, babu wanda ya kula dashi, domin ba a sanshi ba matar aka sani, sai yan tsirarun da suka sami damar halartar liyafar aurensa ne ke gane shi, suma shekeke suke gayar dashi, domin sun san shi ba kowan kowa bane ya dillalin kashi. Anas bai iya tsayawa cikin jama'a ba, sai ya zagaya can bayan lambun ya nemi karkashin wata inuwa mai yawan bishiya ya zauna. Bayansa jingine da bishiyar, daga inda yake zaune yana iya jiyo kida na tashi gami da hayaniyar samari da yan mata. Anas ya lumshe idanunsa, sannan wutar kauna da bege ta fara kona cikin zuciyarsa. Ko shakka ba ya yi kaunar Ummi ta fada zuciyarsa, tun sa'ar da ya fara ganinta irin begenta ya shuka kansa cikin zuciyarsa, a yanzu irin ya girma ya fito fili. Abin da ya fi damun Anas shi ne bai san yadda za a yi ya girbi bishiyar kaunar dake cikin zuciyarsa ba. Mabaruka! Ya kira sunanta a sanyaye, ita ce kadai babbar katangar dake tsakaninsa da Ummi haka nan... "Anas." Zazzakar muryar ta katse tunaninsa. Ya juyo firgigit, ya ce bakinsa na rawa. "Ummi." Ummi ta dubeshi da murmushi ta ce. "Ashe nan ka dawo Mabaruka na can tana jiranka." Anas ya dubeta ya sunkuyar da kai ya ce a sanyaye. "Har kun gama tattaunawar?" Ummi ta gyada kai da murmushi sannan sai ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran yan yatsunta Tsawon lokaci matasan biyu suna nan tsaye suna duban juna Wutar bege ta dada ruruwa cikin zuciyar Anas musamman sa'ar da iska ta buga kamshin turaren dake jikinta zuwa hancinsa. "Ummi." Anas ya kirawo sunanta a sanyaye. Ummi ta matsa kusa dashi sannan ta dago kai ta dubeshi ido da ido ta ce "Anas." Anas ya yi sororo jiki na rawa ya kasa cewa da ita komai akwai wani irin kwarjini a jikinta da ya karya zuciyar Anas duk kuwa da kwarewarsa a harkar mata. To amma duk da haka sai ya sake ta yan maza ya ce. "Ummi..wani abu ne ke damuna wallahi na rasa yadda.." Ummi ta katseshi ta hanyar dora hannu a bakinta ta ce "Ba sai ka fada ba, na san abin dake damunka sai dai nan ba wurin da ya dace a yi irin wannan magana ba ce." Ta yi shiru sannan sai ta mika masa wata yar takarda ta ce. Gashi nan sai mun hadu, ka yi sauri ka koma tana can tana jiranka ka santa da zargi." Tana gama fadin haka sai ta juya da sauri ta bar shi anan tsaye. Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran.TSOHON ALKAWARI-8 . Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran farin ciki a duniya da ya wuce Ummi, to sai dai kuma wani bangare na hadamammiyar zuciyarsa na cewa "Uhum-uhm Anas ka bi a hankali yanzu fa zabinka biyu ne ya rage a rayuwarka ta duniya, ko dai ka zabi kudi da tashin hankali ka bar Ummi, ko kuma ka zabi Ummi ka bar kudi. *** Karfe goma sha daya saura minti uku na dare, Mabaruka da Anas suka shiga dakin kwanansu. Tun daga sa'ar da ya koma wurin. Mabaruka a farfajiyar lambun ya lura da cewa lallai yau akwai masifa domin ta cika ta yi fal har wani kumbura take yi. "Ina ka tafi ka zauna ina ta nemanka?" Mabaruka ta tambayeshi a fusace sa'ar da Anas ya dawo ya zauna a kusanta. Bi a hankali dan samari wata zuciya ta ce dashi. "Ina can baya a zaune muna gaisawa da bakin ki." Mabaruka ta dubeshi a yatsine cikin tsananin zargi sannan ta dauke kai gefe guna. Har bayan da suka gama sallamar baki suka shiga dakin kwanan nasu Mabaruka bata kara cewa dashi uffan ba. Anas ya lura saboda tsabar fushi bakinta har wata kumfa-kumfa yake fitarwa, haka nan duk illahirin jikinta rawa yake yi kamar kamun zazzabi. Anas ya tura Mabaruka akan kujerarta daf da jikin gadon kamar yadda suka saba, sannan ya yi yunkurin daukanta ya daura akan gado. Ga mamakinsa sai ya ji ta buge hannunsa a fusace. "Ka da ka taba ni!...Na ce da kai kada kabani munafuki...!" Anas ya ja baya cikin kaduwa a tsorace. "Me na yi miki?" Mabaruka ta kifa fuskarta akan cinyarta, sannan sai ta fashe da kuka mai karfi jikinta sai rawa yake yi kamar zata fado daga kan kujerar. Tsohon lokaci sai ta dago kai ta ce. "Me ye...hadinka da Ummi?!" Anas ya yi kokari ya sa alamun rudewa akan fuskarsa ya ce. "Ummi kuma...ba kawarki ba ce ni ban ma taba ganinta ba sai sau biyu kuma duk a dalilin ki." Mabaruka ta ci gaba da shisshikar kuka sannan ta nuna shi da dan yatsa ta ce. "Anas, ina son ka sani cewa na aureka ne don ni kadai ba don ka samar min kishiya ba. Na yi maka abin da duk duniya babu wanda ya isa ya yi ma haka ba don komai ba sai don cikar farin cikina." Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. "Tun farko sai da na ce sayenka zan yi Anas ban fada maka ba? Idan kuwa haka ne to kai nawa ne ba na kowa ba, don haka daga yau sai yau zan gargade ka, babu kai babu Ummi, koda ta zo gidan nan bana son ka kara ko da kallonta ko gaisawa ban yarda ku yi ba, kai ba ma Ummi ba duk wata mace a duniya in ta wuce kanwarka ta jini ko mahaifiyarka ban yarda ku gaisa da ita ba, kuma daga yau ka daina zuwa wurin aiki, zan ci gaba da biyanka albashinka na fi son daga yanzu kullum kana tare dani kana faranta min, duk inda zaka daga yanzu tare zamu ke tafiya, dare da rana safe da yamma, ruwa da iska kai ko bala'ine bai isa ya rabamu ba, domin muna tare zan manne ma kamar cingam domin sayenka na yi." Mabaruka ta yi ajiyar zuciya sannan ta daga dan yatsa ta nuna shi ta ce. "Idan kuma kana ganin da takura, to ina shawartarka da ka rubuta min takardar sakina yanzun nan, sai ka hada naka ya naka ka bar min gidana, amma ka tuna daga lokacin ka daina karbar albashin naira dubu dari biyu ka daina karbar kudin da mahaifiyata ta ke baka duk wata ka kuma daina hawa motocina kai hatta kayan da ka saya da kudin mahaifiyata sai ka ajiye min kayana kuma sai ka yi sallama da fita wata kasa a duniya domin na san a rashin zuciya da lalaci irin naka da wahala in zaka yi arziki a duniya mutumin da ko sallah baya iya yi!" Anas ya yi tsaye sororo cikin tsananin kaduwar da bai taba irinsa a duniya ba. Wani abu mai kamar gare-gare ya fara yawo a cikin kwakwalwarsa, nan da nan ya ji cikinsa ya murda kamar zai yi amai Cikin sauri ya dubi Mabaruka baki na rawa ya ce "Ki yi hakuri Mabaruka abin duk bai kai da zafin haka ba." Anas ya dada dafe ciki sannan ya dubi Mabaruka. Mabaruka ta sake fashewa da kuka. Anas ya ji ba zai iya daurewa kukanta ba dan haka sai ya ruga bandaki a guje yana zuwa sai ya fara keta amai. Bayan tsawon lokaci ya gama zubar da abincin da ya ci a wurin liyafar. Daga bandakin yana iya jiyo shisshikar kukan Mabaruka hakan shi ya tuna masa da guntuwar takardar da Ummi ta bashi cikin sauri ya laluba aljihunsa ya dauko takardar sannan sai ya warwareta ya fara karantawa...... . Anas Tun da nake a duniya ban taba sanin mene ne so ba domin ni ko zance ma bana fita wurin samari To amma tun ranar da na dora idanuna a kanka sai na ji duk duniya bani da abin so kamar ka. Na yi matukar farin ciki sa'ar da na dubi cikin kwayar idanunka, sai na tabbata kai ma kana kaunata. Haka nan na yi bakin ciki da ya kasance wannan gurguwa ta yi min shigar sauri ta aureka. Wannan shi ya sa na yi amfani da damar wannan liyafa domin na isar da sakon zuciyata zuwa gareka Na gode, zan tsaya anan, idan har abin da nake zargi gaskiya ne, na san zaka so mu hadu. Ga adireshina nan a kasa, zan jiraka gobe gida tun daga karfe bakwai na dare har zuwa goma na dare...sai na ganka mai... Ummai. Anas ya kankame takardar a kirjinsa cikin farin ciki sannan kuma cikin tsananin rudewa. "Daga yanzu duk inda za ka muna tare zan manne maka kamar cingam!" Ya tuna da kalaman Mabaruka. "Ina jiranka gobe a gida..." ya kuma tuna da kalaman Ummi na karshe. Anas ya lumshe idanunsa, sannan ya kara takardar wasikar akan hancinsa, ya shaki kamshin turaren jikin Ummi dake jikin wasikar, cikin jin dadi. Daga can falo ya jiyo gurnanin kukan Mabaruka. Anas ya yi sauri ya toshe kunnensa domin baya son kukan ya bata masa farin cikin da yake, kai da zai yiwu ya gwammace ya kwana cikin bandakin rungume da wasikar Ummi! Sidi mai jaka ya yi shiru lokaci guda. Na dubeshi cikin kaduwa na ce bakina na rawa. "To mana Baba Sidi...ci gaba mana ya ka tsaya bayan labarin ya gama daukar dadi." Sidi mai Jaka ya dubi kwanon tubanin dake gabansa cikin takaici, sannan ya dubeni da kyau ya ce. "Kada ka bari dadin labari ya dauke ka, saurara da kyau ka ji kiran sallah ake yi. Tashi ka je ka yi sallah idan an idar da sallar sai mu sako wani sabon zaren labarin." Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya dauki tsohuwar butarsa ta karfe mai kwarin tsiya ina tsammanin butar tafi shekaru arba'in. Na mike tsaye cikin sauri na ce. "Baba Sidi dan Allah...da na gama sallah fa zan dawo." Baba Sidi ya dubeni da murmushi ya ce. "Idan za ka dawo ka tabbata ka dawo min da karin tubani, domin idan babu shi, to babu labari Nas, na riga na fada ma ni da tubani tamkar tsohuwar mota ce da man fetur. Ya juya cikin sauri da butarsa a hannu ya nufi waje zai yi alwala. *** Ban sami damar dawowa wajen Sidi mai jaka ba sai bayan sallar La'asar sakamakon tsayawa da na yi a sake dafa min sabon tubani. "Kai dan nema, bana son shakiyancin banza, me kuma zaka sake yi da tubani. Na dauka dazu-dazun nan na yi ma cikin kwano guda?" Kakata ce ke fadin haka. Na dubeta da dariya. "Kin ga in za ki dafa min ki dafa, in kuma ba haka ba yanzun nan in baki takardar saki akan tubani." Ta fashe da dariya. "Amma kuwa da ka yi abin kunya wallahi ka saki matarka saboda tubani?" Daga karshe bayan mun sha cacar baki kusan mintuna bakwai, na shawo kanta da kyar, ta sake cika min kwano da tubani, a wannan karon har sun fi wadancan girma domin ba a son ranta ta yi su ba. Na riski Baba Sidi mai jaka zaune akan tsohuwar kujerar katakonsa yana jan carbi, tun kafin na gama yi masa sallama ya dago kai ya dubi kwanon dake hannuna cikin fara'a, kamar karamin yaron da ya yi ido biyu da alewa mai tsinke. "Tsohon alkawari a karo na biyu, lallai Nas ka kyauta min." Ya ce sa'annan ya mika hannu ya karbe kwanon daga hannuna tun ma kafin na ajiye shi da kaina. Sidi mai jaka bai jira komai ba, sai kawai ya bude kwanon tubanin ya fara juya tubanin da yan yatsunsa bayan wani dan lokaci ya tabbata da cewa sun juyu yadda ya ke so don haka sai ya can ku wani kato ya jefa cikin bakinsa sannan ya dubeni. "Nas, ina fatan dazu kana biye dani a labarin da na fara baka." Cikin sauri na gyada kaina. "Kwarai kuwa ka tsaya inda Anas ya shiga bandaki ya fara karanta wasikar Ummi harma take cewa dashi tana son ganinsa a daren washe garin ranar Sidi mai jaka ya gyada kai da murmushi. "Wani lokaci ina son mutum mai saurin rike al'amura a cikin kwakwalwa nan da nan ba tare da mantuwa ba." Na dubeshi da murmushi a karo na farko na ce. "Ai kuwa in ka dauke labarai babu abin da kwakwalwata ke iya rikewa domin koda sunan mutane in ba dadewa muka yi da kai ba sai ka yi ta zuwa ina kiranka da kai!" Sidi mai jaka ya fashe da dariya sannan ya canko wani katon tubani ya sha ya ji jajur dashi ga girma kamar dankali ya miko min. "Ungo wannan Nas jefa a bakin ka." Na yi saurin girgiza kai cikin kaduwa. "Allah kuwa karbi baka jiba yadda tubanin nan ya yi dadi...TSOHON ALKAWARI-9 . "Ungo wannan Nas jefa a bakin ka." Na yi saurin girgiza kai cikin kaduwa. "Allah kuwa karbi baka jiba yadda tubanin nan ya yi dadi har ya fi na dazu." Na dada girgiza kai. Sidi mai jaka ya zunkuda kafada, "Ka cuci kanka Nas, ni duk abincin duniya ban ga abin da zai zo a na biyun tubani ba a gare ni. Ya sake tsikaro guda ya jefa a bakin salatinsa sannan ya juya ya dubeni idanunsa na zubar hawaye kamar kuturu. "Nas, zaren labarin dana fara baka labari dazu ya kare iyakarsa kenan." Na dubi Sidi mai jaka cikin kaduwa. "Haba Baba Sidi, kai fa ka ce

Chapter 3 of 7