Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TSOHON ALKAWARI 1 . Nazir Adam Salih (Nas) . A ranar ashirin da takwas ga watan Afrilu na shekarar Milladiyya ta dubu biyu da guda hudu wacce ta yi daidai da ranar Laraba na tashi a rude, kwakwalwata a cunkushe domin sama ko kasa na nemi sabuwar basirar da zan yi rubutu na rasa. Tun misalin karfe goma nake zaune na sa littafin a gaba ina kallo har zuwa karfe goma sha biyu na rana kwakwalwata ba ta zo min da komai ba sai tunane- tunane marasa amfani. Ina nan dai zaune cikin akurkin dakina ni kadai da biro a hannu sai jujjuyashi nake yi kamar sigari daga karshe dai na tabbata ta kare min dan haka sai na ajiye biron na mike tsaye gami da mika kuma cikin damuwa. "Me ke damuna ne?" Na tambayi kaina ko da idanuna suka kai ga shafin littafi na ga ko alif ban rubuta ba sai na yiwa kaina murmushi, maganar makaranta littattafaina ta fado min sa'ar da suke cewa wai ta qare min, lokacin da na kasa fito musu da cigaban ALJANI YA TAKA WUTA da kuma BINDIGAR KWALI NA BIYU lallai ga dukkan alamu suma da gaskiyarsu tabbas ta kare min tunda dai gashi na sa littafi a gaba na kasa rubuta komai tsawon sa'o'i biyu. . Na gama hakura, na fito kofar gida kenan sai na hango wata yarinya dauke da fanteka da kwanuka a samanta abin tsautsayi ta zo tsallaka kwata kenan sai kafarta ta zame, fantekar a cike take da danwake, wannan shi ne ya yi sanadiyyar barkowar wani zazzafan gumi a kan goshina, zuciyata ta fara harbawa, sakamakon abin da na tuna, tabbas na san inda zan je na samo labari. Na sake duban dunkule-dunkulen dan wake burjuk a kasa sai ta tuno min da TUBANI ina tuno da tubani sai na tuno da dattijo SIDI MAI JAKA A cikin sauri na nufi gidan wata kakata, na yi sa'a kuwa na sameta a gida. Bayan mun gaisa sai na ce da ita. "Tubani nake son ki yi min." Ta dubeni cikin dariya ta ce "Ka ci gidanku ja'iri dan nema, kai a zamaninku ana yin tubani ne? Sai dai jefi-jefi." Na dubeta gami da sa alamun nutsuwa a fuskata na ce. "Dan Allah ki yi min wallahi da gaske na ke yi, fada min duk abubuwan da za a saya sai na baki kudin..." . Bata sami damar suturta tubanin nan ba sai bayan karfe biyu. Bayan na gama sallar Azuhur sai na ga ta bade tubanin da yaji sosai, domin na riga na san Sidi Mai Jaka zai yi matukar farin ciki da hakan, na sa ta dada kwarara masa mai, sannan aka zuba min shi a cikin kwano. Karfe biyu da kwata na isa gidan Sidi Mai Jaka dake bakin kasuwa. Abin da ya fi damuna shi ne tun sa'ar da muka rabu da shi shekara biyu da suka wuce ban kara zuwa wurinsa ba. . Ina isa kofar gidan sai na leka zauren cikin doki, gabana na ta faduwa domin kada na yi zuwan banza ko baya nan. Ga mamakina Sidi Mai Jaka na nan zaune akan kujerar katakonsa, carbi a hannunsa, haka nan akwai lofe a gefensa a ajiye bisa wani farin buzu. Sidi Mai Jaka ya dago kai muka yi ido biyu, ko dakika biyu ba a yi ba ya shaida ni. . "A'aha, yaushe a gari inji ma ki bako Nas, ashe daman kuna duniya?" Na dubeshi da dariya. "Baba Sidi kuma tsofaffi ba ku bar duniya ba ballantana mu." Sidi Mai jaka ya fashe da wata shakakkiyar dariya. Na dubi Sidi Mai jaka kallon tsaf, kana idanuna suka yo nazarin zauren. Ko kusa ko alama babu wani canji a kamannin Sidi Mai jaka ko kuma zauren gidan. Wani abin dadin mamaki kuma shi ne, tsohuwar rigar nan dake jikinsa mai kamar rariya, ita ce dai har yanzu bai sake wata ba, na yi mamakin karfin hali irin na wannan rigar, domin sa'ar da na fara ganinta shekaru biyu da suka wuce ban taba tsammanin zata sake wata guda a duniya ba ta fatattake ba. Har yanzu katon farin tabaron nan nasa na nan daraf akan hancinsa. . Jikinsa kuwa sa'ar da na dubeshi sai na fara tunanin me yiwuwa tun bayan rabuwata dashi a shekara biyu wankansa bai fi sau uku ba, me yiwuwa ma sai dai ko alwala. Amma fa duk da wannan al'amari na Sidi Mai jaka ina matukar girmamashi. Shekaru biyu da suka wuce, wannan tsoho Sidi mai jaka dogo fari yankwanannen tsoho, kansa fari fat, da furfura, farin gemu da fuska ma'abociyar fadin goshi ya taba bani labarin wata malamar asibiti TANI da wasu yan fashi. . Sidi mai jaka ya dubi kwanon dake hannuna cikin farin ciki yace. "Ko shakka ba na yi wannan alkawarina ne na TUBANI ko?" Na ajiye kwanon a gabansa lokaci guda kuma na matsar da lofen dake kan farin buzun na zauna na dubeshi cikin murmushi. "Tabbas ka canka tubaninka ne." . Fuskar Sidi Mai jaka ta washe, cikin nutsuwa ya mika hannu ya dauko wata butar roba, ya guntsi ruwa a bakinsa ya kuskure bakinsa ya fesar a jikin bango. Kana ya janyo kwanon tubanin nan ya bude ya fara kallonsa cikin nutsuwa. "Nas, ina me yi maka albishir da cewa wannan kyauta ta tubani da ka kawo mini tamkar wani dan mukullin labari ne da na dade ina son na baka to sai dai kuma shekaru biyu kenan yau rabonka da nan sai yau Allah a kawoka." "Haka ne." Na ce dashi, sannan na dada gyara zama domin na san sabon labari ya riga ya zo.... .TSOHON ALKAWARI--> 2 . Shekaru biyu kenan yau rabonka da nan sai yau Allah a kawoka." "Haka ne." Na ce dashi, sannan na dada gyara zama domin na san sabon labari ya riga ya zo.... Sidi Mai jaka ya birkita manya- manyan tubanin, sannan ya dauki tsinke, ya tsiraki wani kato ya tura a baki, nan da nan idanunsa suka fara zubar da hawaye saboda yaji.Ko wace ce ta yi ma tubanin nan, ba karamin kwarewa ta yi ba Nas." Sidi mai jaka ya ce dani. Na gyada kai. Sidi mai jaka ya cire farin tabaron dake idanunsa ya sa hannun rigarsa ya goge idanunsa sannan ya dubeni ya ce."Nas kune samari yanzu idan aka ce ka yi auren jari za ka yi?" Na dubeshi cikin mamaki na girgiza kai na ce."Ya danganta da irin macen...koda yake dai ni a gaskiya baya bani sha'awa, ni na fi son auren da muke kaunar juna don Allah." Sidi mai jaka ya dubeni ya kyalkyale da dariya ya ce.Abin da Anas mijin Mabaruka gurguwa kenan ya kasa fahimta." Na dubeshi a karo na biyu "Wa yekuma Anas mijin Mabaruka gurguwa?" Sidi mai jaka ya tsikari katon tubani ya jefa a bakinsa."Shi ne labarin da nake son na baka Nas ban saniba ko kana da sha'awar irin wadannan labarai na irin wadannan mata masu matukar son kansu a duniya fiye da kowa?" Na yi shiru na dan lokaci ina juya, abin da ya ce cikin zuciyata. A gaskiya ni a son zuciyata na fi son a bani labarin yan ta'adda irin wanda ya bani shekaru biyu da suka wuce, to amma da yake ni yanzu ta riga ta kare min dole ne na saurari komai domin bani da zabi. Wa ya sani ma ko wannan ma ya fi wancan labarin dadi."Zan so kuwa na ji labarin wannan gurguwa, wace ce ita'" Na tambayeshi, Sidi mai jaka ya yi dariya ce."Bi ni a hankali Nas dadina da kai gaggawa sannu a hankali zan fara saka ma zararrukan labarin ina kulla maka su kamar yanda gizo-gizo ke sakar gidansa" Sidi mai jaka ya dan yi shiru sannan ya ci gaba."Ita wannan gurguwa mai suna Mabaruka ba a taba samun wata mace a zamanin ta mai arzikinta ba, miloniya ce a fagen kudi, to sai dai kuma wani ragin jin dadi da ta samu shi ne gurguwa aka haife ta" Sidi mai jaka ya juyo ya dubeni."Nas, domin ka fahimci zaren labarin nan da kyau, dole ne na ajiyar zaren labarin gurguwa mabaruka, na koma na dauko ma hoton Anas" Na dago kai a kagauce na kalle shi."Ka ce kuma da labarin gurguwa za ka ba ni." Sidi Mai jaka ya gyara tabaronsa kana ya tsikari tubani guda ya jefa a bakin salatinsa."Dole ne mu fara da zaren labarin Anas, in kuwaba haka ba Nas, ba za ka taba fahimtar labarin nan ba" Na gyada kai cikin fahimta."Yauwa Nas, ina son ka dauki zuciyarka ka mayarda ita cikin wata mashahuriyar otal." Na dubi Sidi mai jaka cikin kaguwa na ce dashi "Na mayar""Yauwa" Ya ce dani sannan ya fara.**** "To Nas ga Anas nan a cikin dakin karbar baki na otal din yana zagayawa cikin farin ciki da annashuwa domin aljihunsa a cike yake da albashinsa na wannan watan"Sidi mai jaka ya yi yar atishawa sannan ya ce."Kafin na ci gaba bari na baka hoton Anas. Ka ga Nas Anas dogo ne wankan tarwada mai kyawun fuska na ban mamaki. Domin an ce ba mata kawai ba hatta maza idan Anas ya zo wucewa sai sun kalleshi sun yaba da halittar Ubangiji. Wani karin abin burgewa kuma gareshi shi ne duk irinsuturar da ya sa sai ta karbeshi cif-cif kamar daman da ita aka haifeshi. Wannan da kuma iya zancensa da tarairaya shi ya sa dimbin mata suke kaunar Anas kamar su hadiyeshi. Wani abu da zai baka mamaki Nas, shi ne Anan ba wai yan mata bane kawai ke son sa, hatta dattijan mata ma suna kaunarsa sau da yawa masu budurwar zuciya daga cikinsu kan yi kokarin su kaiwa Anas cafka musamman ma dattijan zawarawa attajirai. Wani sa'in Anas ya kan kula su ba don komai ba kuwa sai don dan abin hasafin da sukan bashi.Daya daga cikin abin da Anas ya fi kauna a rayuwarsa shi ne hira da kyawawan mata, sau dayawa Anas ya kan tsinewa talauci sau daruruwa cikin zuciyarsa, domin a cewarsa shi ne ya shiga tsakaninsa da kyawawan mata masu aji. Duk da yake dai kyawunsa kan janyo ra'ayin kyawawan mata, to amma Anas bai taba gamsuwa ba domin shi ya riga ya sani, akwai irin kyawawan matan da kyawunsa bai isa ya janyo su ba. Wannan ita ta sa Anas ya yi kurda-kurda ya sami aiki a Lagwada Hotel. Duk da yake dai shi ba kowan kowa bane a otal din domin aikinsa ya fi karfi a rabon abinci, wani sa'in kuma ya kan nunawa baki dakunansu su ta hanyar daukar dakon yan jakunkunansu, to amma wannan bata dami Anas ba domin shi burinsa ya cika. Dan wannan ita ce hanya daya jal da zai yi ta ganin kyawawan mata iri-iri, yanda yake so duk kuwa da cewa bashi da ko kwabo. Babban abin farin cikin Anas shi ne ya ga ana liyafa a otal din, musamman ma ta bakin aure, domin tana bashi damar gani kyawawan mata wani sa'in ma har yazanta da su. Anas yana daya daga cikin irin samarin nan marasa zuciyar nema, wadanda harkullum kwanan duniya burinsu su ci BULUS ba tare da sun sha wahala ba. Dan haka...... .TSOHON ALKAWARI--> 3 . Wadanda harkullum kwanan duniya burinsu su ci bulus ba tare da sun sha wahala ba. . Dan haka Naira dubu takwas din da ake biyan Anas a wata sun isa su sashi farin ciki, tun da dai ba zai iya kokarin samun abin da ya fi haka ba.Anan, sai Sidi mai jaka ya yi shiru ya dago kai ya dube ni."Nas, ina fatan kana fahimtar hoton Anas da nake ta kokarin zana ma" Na gyada kai na ce."Ina fahimta" Sidi mai jaka ya gyara zama sannansai ya ce."Bari to in koma da kai can baya kadan inda nake cewa Anas yana zagaya wa a otal din cikin farin ciki, lokaci- lokaci ya kan shafi aljihunsa a fakaice domin baya son mutane su fahimci cewar dan albashin Naira dubu takwas din aljihunsa yake tabawa. Haka nan shi kuma bashi da imanin da zai iya jurewa daidai da minti gudabai taba aljihunsa ba domin ji yake yi kamar kudin za su zube.Anas ya ci gaba da zagaya wa a dakin karbar bakina otal din ya gaisa da wancan ya yiwa wannan wasa har dai ya kawo daidai kan kanta inda Balaraba mai bada dan mukullan dakuna ke zaune. Anas ya matsa kusa da kantar ya dora hannunsa sannan ya dubi Balaraba da kyakkyawar fuskarsa ya hasketa da murmushi fararen hakoransa suka fito fili."Hajiya Balaraba ya ya garin ne?"Balaraba ta dubeshi da murmushi sannan ta turo biron dake hannunta cikin kunne ta fara juya shi, tana kanne ido."Lafiya lau Anas. Har ka tashi ne?"Anas ya dubi agogo sannan ya dube ta."Da saura dai Balaraba." ya dan yi shiru sannan sai ya ce."Balaraba ba ki ga motsin Halima ba ne?" Balaraba ta girgiza kai."Ban ganta ba, rabona da ita tun jiya da yamma kamar ya yanzu da ta zo neman ka." Balaraba ta ci gaba da susa da biron cikin kunnenta."Anas, wai don Allah yaushe za ka daina yaudarar yayan mutane ne?" Anas ya dubeta da murmushi ya ce."Sai kin shirya Balaraba." Balaraba ta harareshi."Me kake nufi da sai na shirya?"Anas ya shafi kyakkyawar fuskarsa."In har kin yarda za ki aure ni, me zai sa na ci gaba da yaudara? Daman ke ce ai ki ka ki da tuntuni kin amince dani da tuni na yi aure na huta." Balaraba ta kyalkyale da dariya."Oh! Anas Allah ya rufa asiri wallahi wadda bata san ka ba ka cuce ta." Ta dan yi shiru ta sunkuyarda kai.Balaraba bazawara ce, sau uku tana aure tana fitowa. Da yake tana da sakamakon diflomarta a hannu kuma basira ta bace mata maimakon ta yizamanta a dakin miji sai ta nemi aiki a otal, a lokacin watanta takwas kenan da fara aiki. Tun sa'ar da ta fara dora idanu akan Anas ta ji duk duniya babu wanda take kauna sai shi. Balaraba kyakkyawa ce daidai misali, to sai dai kuma bata cikin irin tsarin matan da Anas ke so, domin a cewar Anas duk macen da ta fiye gajarta bata cika kyakkyawa ba ko da kuwa tana da kyawun fuska. Balaraba ta so ta cusa kanta a wurin Anas,to amma irin jeri-jerin matan da kan zo neman Anas tun daga cikin gari har otal din, shi ya gargadi Balaraba ta hadiye maitarta ta yi shiru. To sai gashi kuma yanzu Anas da kansa yana zolayarta da zancen soyayya. Duk da yake Balaraba ta tabbata karya yake sai da kalaman nasa ya faranta mata rai."Balaraba." Anas ya kira sunanta. Balaraba ta juyo frgigit."Tunani n me ki ke yi?" Balaraba ta dago kai ta dubeshi na dan tsawon lokaci sannan sai ta ce."Kana da labarin kayatacciyar liyafar da za a yi yau a otal din nan?" Anas ya dubeta cikin mamaki."Tun jiya na sami labari a wurin Sabi'u amma ni bai ce dani ta hadu ba." Balaraba ta dube shi."Ai kuwa tun..." Kalamanta suka makale a fatar bakinta ba ta karasa ba. Anas ya dubeta cikin mamaki sai ya ga bashi take kallo ba bayansa take kallo. Can wajen kofar shigowa. Anas ya yi mamaki domin duk kusan lokaci guda jama'ar dake cikin dakin tarbar bakin suna surutai suka yi shiru na dan lokaci. Anas ya juyo sosai domin ya ga abin da ke faruwa. A daidai lokacin ne to ya hangesu.Wasu kyawawan mata ne suka shigo kowaccen suta ci kwalliya ta gani ta fada. Anas ya ji yawun bakinsa ya kafe, sannan sai ya lura daya daga cikin yan matan tana tura kujerar guragu ta farinkarfe akan kujerar a zaune sanye da kayan alfarma masu tsadar gaske, wata budurwa ce gurguwa, za ta yi kimanin shekaru ashirin da bakwai.Koda Anas ya ci gaba da kallon gurguwar da yan matan ke turawa, sai ya yi ajiyar zuciya."Kai amma fa an yi asarar kayan kwalliya." Balaraba ta dubeshi da dan murmushi ta ce."Me ya sa ka ce haka?" Anas ya dan yi shiru sannan ya dada waigawa a karo na biyu ya kalli gurguwar, sannan ya juya ga Balaraba."Kin san ni ban cika shiri da munanan mata ba.Dube ta fa gurguwa mummuna amma kayan jikinta sun fi na kowa tsada, ai dole in ce an yi asarar kayan kwalliya." Balaraba ta fashe da dariya."Kai dai Anas wallahi ba ka da kaico, me ya sa kake son muzanta munana? Suma fa Allah ne ya haliccesu kamar yadda ya halicceka kyakkyawa kuma idan ya so yana iya sa wa ka aure ta......TSOHON ALKAWARI-4 . Me ya sa kake son muzanta munana? Suma fa Allah ne ya haliccesu kamar yadda ya halicceka kyakkyawa, kuma idan ya so yana iya sa wa KA AURE TA." Anasya harare ta."Allah sawwake, kin ga Balaraba ni fa bana son mugun fata, tun da abin na ki haka ne ma ni kin ga tafiya ta." Anas ya juya cikin sauri ya nufi cikin otal din a daidai lokacin ne to ya hango Sabi'u cikin sauri ya matsa gareshi."Sabi'u ka ga wata mummuna da alamun kudi." Sabi'u ya dubi Anas ido da ido, akwai wani yanayi a irin kallon da yake yi da ya sa Anas ya jigwiwarsa ta yi sanyi."Ya ya na ga kana yi min wani kallon uku ahu?" Sabi'u dan lukuti, gajere ma'aboin son sa kayan turawa duk kuwa da cewa ba wani kyau suke yi masa ba, ya gyara tsayuwa sannan ya dubi Anas "Ka san inda kake wage bakinka, in kuwa ba hakaba wata ran za ka kwana a ciki. Shin ka san waccan gurguwa ko wace ce kuwa?" Anas ya girgiza kai ya ce."Fahimtar dani." Sabi'u ya gyara wandonsa wanda ke kokarin sullubewa ya fado."Ni na san ba ka santa ba shi yasa kake kokarin muzantata. To bari in fada ma, ka ga duk munin nan nata, wallahi ba muni bane a gurina, kuma ka ga dai gurguwa ce to ni a gurina kafafunta sunfi naka sau dubu amfani." Sabi'u ya dan yi shiru sannan sai ya dago hannunsa ya dan daki kirjin Anas ya ce."Wannan gurguwa da kake gani ita ce Mabaruka S. Faruk, daya daga cikin matan da suka fi kowacce arziki a matan Afirka." Sabi'u ya ya balligoro ya jefa a bakinsa sannan ya dubi kyakkyawar fuskar Anas da murmushi."Na san ka sha jin labarinta, me yiyuwa a zahiri ma baka taba ganinta ba, to yau gata a otal din ka, bikin cika shekarunta ashirin da takwas a duniya za a yi. Mu kanmu nan otal din ba karamar sa'a muka yi ba, domin da liyafar a Landan za a yi sai Mabaruka ta ce ba za ta iya doguwar tafiya a cikin jirgi ba domin wai juwa kedamunta wannan shi ya sa su zuwa nan, ina fatan ka fahimce ni? Dan haka Anas ina son ka yishiru da bakinka domin otal din nan ta yi muguwar cin riba da liyafar nan da za a yi, idan ka sake manaja ya ji kalamanka akan Mabaruka, na rantse ma har da gemun tsohona ba za ka sake awa guda a gidan nan ba za a sallame ka daga aiki." Anas fuska na tsiyayar da gumi ya dubi Sabi'u a tsorace. Ya mari bakinsa da hannu"Shegen baki yau ya kusan ya janyo min tsiya." Sabi'u ya fashe da dariya ya ce."Zo mu je mu fara shirye- shiryen abubuwan da za su bukata, ka san fa muke da alhakin kula dasu." Sabi'u ya juya cikin sauri Anas ya bi shi a baya da sassarfa kamar doki. A zuciyarsa yana tunani, Mabaruka! Cab! Ai kuwa ya sha jin labarinta ba tun yau ba. Wani abokinsa ya taba cewa dashi. "Anas duk matan kasar nan babu mai arzikin Mabaruka gurguwa, kai bar ma ta kasar nan duk Afirka sai an tona. To amma a tsammanin Anas da ya ji an ce tafi kowacce mace kudi a Afirka ya dauka zai ganta wata kyakkyawa ajin farko, irin matan nan masu shekia fuska kamar madubi irin wadanda duk tsananin duhun dare sai kaga surar fuskarsu saboda tsabar kyau. Abin da Anas ya gani ya sashi kaduwa musamman ma yanzu da aka ce dashi wannan yankwananniyar matar mai tababben hanci kamar begila ita ce Mabaruka gurguwa uwar kudi! Allah mai yadda ya so. Anas ya ce cikin zuciyarsa.Tun karfe biyar na yamma aka fara liyafar farfajiyar otal din babu masaka tsinke duk inda ka duba motoci ne manya-manya masu bawo. Da yawa daga cikin bakin basu sami damar shigowa da motocinsu ba saboda cunkuso.Anas da sauran ma'aikatan dake bangaren girke- girke suka yi ta rabon kayan lashe-lashe da makulashe. Dakin da ake liyafar tangamemen gaske ne, wanda aka gina shi da zummar ya dauki mutum dari uku ba tare da wani ya shaki numafshin dan uwansa ba, Anas ya fara waige-waige yana kokarin ya karewa Mabaruka kallo.Ya ce gaba da zagaya wa lokaci guda kuma cikin jama,a yana yin abin da ya kamata sai dai kuma akwai wani abu da ke damun Anas sa'ar da ya kawo kusa da inda su Mabaruka suke zaune da manyan kawayenta. Jikinsa na bashi cewa kamar kallonsa ake yi a baya. Wannan ita ta sa Anas juyawa a wayance ya dubi bayansa. Gabansa ya fadi ras! Sa'ar da suka hada idanu da Mabaruka, ko shakka ba ya yi shi take kallo, haka nan har da murmushi a fatar bakinta. Anas ya ji bugun zuciyarsa ya karu lokacin da yaga kamar mabaruka ta daga hannu ta yafato shi. Anas ya shiga cikin rudani domin yana fargabar kada ya je wurin kuma ya kasance ba shi take kira ba.Anas ya waiga bayansa domin ya ga koda wani take sannan ya sake juyowa, sai ya ga ta sake yafuto shi da hannunta. Cikin rawar jiki ya nufi inda take zaune tare da sauran kyawawan matannan. Anas ya ji duk gwiwarsa ta yi rauni kamar ba za ta iya daukarsa ba domin kyawun matan da suka kura masa idanu ya yi yawa, ko kusa ko alama basu yi kama da irin yan matan da yake mu'amala da su a baya ba.Anas ya ratsa a hankali ta tsakanin kyawawan tebura ya karasa gaban Mabaruka. Yana zuwa saiya rankwafa a gabanta ya ce."Gani ranki ya dade ko bani ki ke kira ba?" Mabaruka ta dubeshi da mummunar fuskarta ta saki wani abu da take tsammanin wai tattausan murmushi ne."Kai nake kira mana" Ta dan yi shiru, sannan ta ci gaba."Daman so nake na fada ma don Allah ku yi sauri ku gama shirye-shiryen mana, ka ga kamata ya yi ace tun da wurwuri kun gama komai kafin mu zo" Anas bai iya dago kai ya kallisauran yan matan da ke bayanta ba, to amma yatabbata duk kallonsa suke."To ranki ya dade" Anas ya amsa. Ya yi kamar yamike tsaye ya koma kan aikinsa to amma sai ya ga alamun bata gama bayaninta ba. Mabaruka tadubeshi ido da ido, kana sai ta yi kasa-kasa da muryarta ta ce dashi."Ka bar aikin haka nan ka tafi ka gyara jikinka sosai, ka jirani a waje idan an tashi ina son ganinka. "Kasa-kasa da murya, Ehemm.. Anas ya dubeta cikin mamaki, lokaci guda kuma ya godewa hayaniyar al'ummar dake wurin liyafar domin ya tabbata hatta kyawawan matan dake jere a bayanta ma ba su ji abin da ta ce dashi ba ballantana sauran jama'a. Shi kansa yasan ba dan yana kallon motsin fatar bakinta ba da ba zai taba fahimtar abin da ta ce ba. To amma duk da haka yana shakkar abin da ta ce dashi. Dan haka sai ya ya dubeta a rude ya ce. "Ban fahimce ki ba ranki ya dade?" Mabaruka ta yi masa murmushi ta maimaita. "Ka je ka sake kayan dake jikinka ka kuma jirani a waje, idan an tashi zan turo a yi min kiranka ina son magana da kai." Kusan awa daya da rabi ya shafe zaune karkashin wata dukurkusar bishiya mai kama da ta dabino dake farfajiyar otal din yana jiran tsammani zuciyarsa cike da tambayoyi sama da guda dari. Amma manya-manyan tambayoyin da suka fi damun zuciyarsa sune; shin mene ne dalilin ganawa dashi? Shin laifi ya yi mata? To ai kuwa har murmushi take yi masa sa'ar da take bayanin. To mene ne dalilin da zai sa ta ce ya sake kayan dake jikinsa? Babu mamaki ji ta yi kamar jikina yana wari. Anas ya ce da kansa. Duk da yake dai sa'ar da ya baro wurin liyafar sai da ya yi ta shinshina jikinsa domin ya ji ko wari yake yi, to amma har zuwa wannan lokacin da yake sake kayan dake jikin nasa Anas bai gamsu ba, lokaci- lokaci sai ya sunsuna hannun rigarsa kana ya duba agogon. Sa'a daya da rabi kenan yana zaune a gurin yana jira. Tab! Anas ya yamutse fuska cikin damuwa. A karo na farko a rayuwarsa ta harkar mata sai ya ji ya fadi babu nauyi domin a tarihinsa wata mace bata taba sashi ya yi jiranta daidai da na mintuna biyar ba, sai dai ita ta jirashi. Amma sai gashi yau tarihin ya sauya, wai Anas da kansa ne yake zaman jiran wata nannadaddiyar gurguwa mummuna mai dogon hanci da fadi kamar nakiya, lallai duniya juyi-juyi! Wannan tunani shi ya sa Anas ya saki wani tattausan murmushi a cikin duhun daren da ya fara shigowa sannan ya dada jingina bayansa a jikin bishiyar da yake zaune, ya share gumi daga goshinsa a zuciyarsa ya ce. "Kada ka damu Anas, a da can kyawawan mata sun yi jiranka, a yanzu kuwa kai ne kake jiran mummuna da kudi, ko ba komai dai ba talaka kake jira ba. Abin ya kan baiwa Anas mamaki, wata sa'ar ma har dariya idan ya tuna da cewa wai daya daga cikin matan da ta fi kowace kudi a Afirka yake jira! Anas na nan a zaune yana ta sake-sake bai ji zuwanta ba sai muryarta

Chapter 1 of 7