Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
gaba da tafiya akan kogin hankali kwance tamkar ba akan kogin tabo nake ba ita kanta luslaiya sai abin ya daure mata kai ta kamu da tsananin mamaki sai da na fara taka inda nake takawa sannan na gane cewa ashe bushashshen tabone a wajan ba danye ba duk da haka luslaiya bata yadda taci gaba da yin gudu ba akan busashshen tabon a hankali ta rinka tafiya har muka tsallake kogin tabon gaba daya muna fita saita sake falfalawa da gudun gaske nima saina rufa mata baya sai da muka yini muna gudu ba tare da mun tsaya ba ko mun hadu da wata matsala ba ko kishirwa ta kama daya daga cikinmu sai dai ya daga battar ruwansa yana cikin gudun ya dan sha kadan yaci gaba da gudu a binsa A wannan lokacine nayi tunani na gane cewa zamu gane kuskurenmu anan gaba tunda bamuyi guzurin abinci ba sai guzurin ruwan sha shi kansa ruwan shan ba zai ishemu ba a cikin tsawon kwanaki taran da zamu yi muna wannan gudu to wai shin idan yunwa da barci suka kamamu a cikin wannan gudu ya zamuyi? Amsar da na kasa baiwa kaina kenan haka muka ci gaba da gudu har gari ya soma duhu koda luslaiya taga gari ya soma duhu bata ganin gabanta sosai saita daga hannunta na hagu sama nan take fitilar ice ta bayyana a hannunta nima sai nayi irin tsafin da tayi na samu fitilar Wohoho ! Ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare kuma ba a sanin jimrau sai idan ba a san karshen wuya ba haka dai muka ci gaba da gudu a cikin dajin ba sassauci tamkar jikinmu bana jini da tsoka bane domin babu alamar cewa zamu sare ba wai gajiyar bace babu a jikinmu tsabar juriyace kawai da sabo, sai dare ya soma yi sannan yunwa da barci suka fara damunmu amma saboda naci muki yarda mu sare ko mu tsaya hutawa ko yada zango Al amin Ahmed Misau Guyson Lokacin da luslaiya taji cikinta ya fara murdewa saboda yunwa saita fara tunanin mafita nima a wannan lokaci na fara shiga irin wannan hali da ta shiga don haka burina kawai shine naga ta sare na fadi kasa nima sai kawai na zube kasan don haka dolenemu yada zango a wajan ba zato ba tsammani sai kawai naga luslaiya ta daka tsalle sama izuwa kan wata bishiya ta cafko wani tsuntsu tana dirowa kasa taci gaba dagudunta tana cikin gudun ta kafawa tsuntsun hakoranta akan makoshinsa ta cisge masa wuya kawai sai ta kama shan jininsa bayan ta gama tsotse jinin saita kama fige gashin tsuntsun tana gama figeshi ta kama cinsa danye a haka ta gama cinyeshi Koda ganin abinda luslaiya tayi sa nayi koyi da ita amma fa sai dana ji kamar zanyi kumallo domin ban taba cin danyen nama ba a rayuwata sai a sannan. Zidane Mutum Da Aljan Littafi na biyar (5) Part C. . Marubucin littafin: Abdul aziz sani madakin gini Typing by' Al amin Ahmed Misau Guyson Contack: 08064594218 for more Doka' ban yarda a sarrafa wannan post ba inbada izinina ba. ! Labari ya isowa guyson cewa... Hakika dole kanwar naki ce domin inda banci wannan danyen tsuntsun ba da tabbas yunwa zata iya min lahani hakika a cikin wadannan kwanaki tara naga abubuwan al ajabi a tare da jaruma luslaiya babban abin da yafi burgeni da ita shine yadda take iya yin barci a lokacinda take cikin yin gudu ba tare da tayi karo da bishiya ba ko dutse da zarar ta tunkari bishiya ko dutse saitazo daf da su saikaga ta goce musu ta wuce lafiya lau ni kuwa sai da na rinka yin karo da bishiyoyi da duwatsu ina jin ciwo da faduwa tsabar naci da juriya ce tasa ban sare ba naci gaba da gudu a hakan a wannan lokacine na tabbatar da cewa luslaiya ta samu horo da ni bani dashi hakika munsha bakar wahala a cikin wadannan kwanaki tara tamkar zamu rasa rayukanmu amma har lokacin ya cika ban sare ba a ranar kwana na taran ma a jere muka iso farkon wani daji wanda ke cikin nahiyar kasar teheren da yammaci ne muka iso farkon dajin kawai sai naga luslaiya ta zube kasa bisa guiwoyinta tana haki nima sainazo na zube kasa daf da ita kawai saita dubeni tace tabbas na yarda kai jarumine na gaske domin kaine mutum na farko daya jure irin wannan wahala tare dani tsawon kwana tara ba tare da ya rasa rayuwarsa ba yanzu ka tsallake matakin farko na gasarmu amma ina mai tabbatar maka da cewa babu yadda zaka iya tsallake mataki na biyu bare har ka kai kan mataki na uku yanzu ne zamu yada zango mu huta kuma mu kwana sai gobe da safe zamu ci gaba da tafiyarmu koda gama fadin hakan sai luslaiya ta zare addarta guda dake kan cinyarta ta hagu ta yunkura zata wuce ta gabana a zatona ni zata kawowa hari don haka nima saina yunkura na zare takobina amma sai naga kawai ta wuce ta nufi inda wata bishiya take mai dogayen rass ta fara saranta da yake masu iya magana sunce idan kaje gari kaga kowa da bindi kaima saika daurawa kanka sai kawai nima naje na taya luslaiya aikin da takeyi nan da nan muka saro rassan bishiyoyin da yawa muka tarasu a waje guda daga nan kuma sai naga taje ta kama yanko wadansu busassun jijiyoyi na bishiya masu kwari gami da wadansu irin manyan ganyaye na wata bishiya ta musamman masu fadi nidai sai naci gaba da yin koyi da ita bayan mun gama tara wadannan kyayyakin sai luslaiya ta shiga gina daki kawai saina tayata muka kammala ginin har da kofa da rufi kai kace kwararrun magina ne suka yi aikin abin gwanin ban sha awa saiga kyakkyawan karamin gida a tsakiyar dokar daji tunda muka fara wannan aiki da yammacin bamu kammala aikin ba sai da dare ya soma a sannan ne wata irin matsananciyar gajiya ta riskemu kuma kwasam sai hadari ya gangamo aka fara tsawa da walkiya nan take luslaiya ta shige cikin wannan daki da muka gina ta turo kofa zata rufe saina kare da hannuna nace ya ya zaki shige kuma ki rufe min kofa koda jin wannan tambaya sai luslaiya tayi min. Wani irin kallo mai nuna tsantsar kiyayya tace wane ne kai a gareni har da kake tunanin zamu kwanta tare a cikin daki guda hm Guyson sunana wannan abun ya ban mamaki.. Ni ba kowa bane a gareki kuma bazan taba kusantarki ba amma ina da ikon kwana a cikin wannan daki tunda dani aka ginashi luslaiya ta sake hade fuska tace gani kayi ina aikin ginin wannan daki ka tayani amma ban gayyaceka ba don haka daki nawane ba naka ba idan ka matsa saika shigo saidai muyi yaki mu baje dakin gaba daya tana gama fadin haka saita bangajeni nayi baya taga taga kuma ta banko kofar dakin ta kulle abinta faruwar hakan keda wuya aka fara yin wata irin iska mai karfin gaske sannan kuma aka kece da ruwan sama tamkar da bakin kwarya nan take na jike sharkaf, kawai sai naga luslaiya tana lekena ta cikin tagar dakin nata tana yi min murmushin mugunta haka dai ruwa yaci gaba da dukana inaji ina gani ga inda zan fake amma babu dama ba komai ne yasa naki matsawa akan saina shiga dakin ba face nasan cewa ruguza dakin zamuyi a banza alhalin mun sha wahalar gaske wajan ginashi baya ga haka ni har a cikin zuciyata bana son abinda zai sa luslaiya ta sha wuya ko zuciyarta ta sosu saboda soyayyata a gareta ta gaskiyace hm So kenan ' lokacin da ruwan saman yaci gaba da dukana ga iska mai dan karan sanyi na kadawa sai nan da nan zazzabi ya rufeni jikina ya kama karkarwa nan fa na fara tunanin neman mafaka kawai sai na ruga izuwa gabas da yamma kudu da arewacin dajin ina neman inda zanga wani kogon dutse na shige cikinsa amma ko alamunsa ban gani ba nan take na gane cewa luslaiya mugunta ta shirya min dama tasan cewa babu mafaka a ko ina cikin dajin kawai sai naji raina ya baci zuciyata ta fara ayyana min cewa kawai na koma wajan luslaiya na fasa kofar dakin na shiga da karfin tsiya in yaso kome zai faru ya faru har na yunkura zanje na aiwatar da hakan sai na tuno da nasihar mahaifina cewa na jure duk irin wahalar da zan sha a cikin wannan tafiya tawa tare da luslaiya don haka Haka saina fasa kawai na dawo kusa da dakin nata na haye kan wata bishiya na kwanta ina mai takure jikina a lokacin da ruwan saman yaci gaba da zaneni ina ta karkarwar jiki saida aka shafe kusan sa a hudu ana tafka wannan ruwan sama sannan aka dauke dif A sannan ne zazzabin jikin nawa ya kara zafi ainun gashi kayan jikina a jike suke sharkaf kuma gashi duk itatuwan dajin sun jike babu damar na kunna wuta naji dumi A wannan lokaci alfijir ya keto don haka har gari ya waye sosai ina cikin mugun yanayi na rashin lafiya sannan ga tsananin yunwar dake damuna domin rabonmu da abinci tun jiya da rana sa adda muke gasar tseren gudu na tsawon kwana tara sa adda kowannenmu yaci danyen naman tsuntsu kwatsam saiga luslaiya ta fito daga cikin wannan daki a shirye cikin nutsuwa da cikar lafiya a hannunta akwai cinyar wani katon tsuntsu gashashshiya tana ci Al amarin dayayi matukar daure min kai kenan na cika da tsananin mamaki na tambayi kaina a cikin zuciyata nace yaushe ne luslaiya ta farauto tsuntsu har ta gasashi ban sani ba koda nayi tunani mai dan zurfi saina gane cewa lallai yaudarata tayi dama can ta tanadi wannan nama a cikin jakar guzurinta ban sani ba kuma tana sane taci naman danyen tsuntsu don kada nasan tana da wani guzuri a boye kawai sai naji wani irin takaici ya rufeni na sake tambayar kaina nace akan wane dalili luslaiya ta tsaneni haka har take son ta cutar dani matuka ga ya Alhalin ni ban taba zama abokin gabarta ba amsar dana kasa baiwa kaina kenan luslaiya ta taho gareni a lokacin da nake bisa wannan bishiya cikin halin rashin lafiya jikina nata tsuma kawai saita dago kai ta dubeni cikin murmushin mugunta tace lokacin gabatar da gasarmu ta biyu yayi sai ka sauko domin mu kama hanyar zuwa birnin Arnan daji inda zamu sato gunkin da suke bautawa koda jin wannan batu sai hankalina ya dugunzuma ainun na dubeta cikin mamaki da fushi nace Shin bakya ganin halin da nake ciki ne na rashin lafiya da matsananciyar yunwa? Ta yaya zan iya ci gaba da yin wannan gasa a haka kodajin wannan batu sai luslaiya ta bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ta hade fuska tace ashe kenan ka yarda na lashe wannan gasa tabbas baka cika jarumi ba wannan ya nuna cewa na fika karfi da jarumtaka kafin luslaiya ta gama rufe bakinta tuni na duro kasa daga kan bishiyar da nake kwance na duro bisa kfafuwana na tsaya cak a gabanta nace har abada namiji yana gaba da mace yunwa da rashin lafiya ba zasu saki lashe wannan gasaba mujezuwa mahaukaci ya hau kura zamuga inda zata kaishi. Koda jin wannan batu sai luslaiya tayi min murmushin mugunta ba tare da ta sake cewa dani uppan ba saita juya ta falfala da gudu izuwa cikin daji ai kuwa nima saina ware na bita a guje muka kasa tsere tamkar babu wata lalura a tare dani amma ni nasan abin da nakeji tabbas nasan cewa ba karamin ganganci nayi ba domin idan har yaki ya balle a tsakaninmu da Arnan dajin da zamujewa ina cikin wannan hali komai zai iya faruwa a gareni tun da babu cikakken karfi da kuzari a jikina. Kash! Tabbas rashin sani yafi dare duhu ashe wani babban tarkon mugunta luslaiya ta shirya min wanda ta tabbatar da cewa indai na fada cikinsa babu makawa saina hallaka ni kuwa gogan naka sai naci gaba da tsala gudu kokarina kawai na risketa mu jera tare in yaso duk masifar da zan shiga mu shiga tare sai da muka shafe sa a daya da rabi muna ta tsala azababben gudu a cikin dajin tamkar zamu tashi sama a wannan lokacine naji jiri ya fara dibata saboda muguwar yunwar da nakeji gami da rashin lafiyar dake addabata amma saboda bakin naci irin nawa gami da juriya irin ta manyan mazaje sai naki sarewa. Ita kanta luslaiya tayi tsananin mamaki bisa ganin yadda nake iya yin wannan gudu da dukkan karfina tamkar bani da wata lalura muna cikin yin wannan gudu ne ba zato ba tsammani naga wani wawakeken rami a gabanmu mai tsananin fadi da zurfi gashi babu damar muyi turjiya mu hana kanmu fadawa cikin ramin, kawai sai naga luslaiya tayi wuf ta zaro wata doguwar igiya daga cikin jakar guzurinta mai kugiya a karshenta tana sama ta cilla igiyar izuwa can karshen ramin ta sakalo dutse sai gani nayi ta tsallake ramin da dire can samansa ni kuwa saina fada can kasan ramin ina mai kwala uban ihu saboda na tabbatar da cewa mutuwace tazo da sauri luslaiya ta rugo izuwa bakin ramin ta leko lasansa amma saboda tsananin zurfin ramin ko hangoni batayi kawai saitayi murmushin farin ciki saboda ta tabbatar da cewa na halaka ita kuwa ta lashe wannan gasa cikin murna ta juya tayi gaba ta kule cikin daji Al amarina kuwa lokacin dana fada kasan wannan mugun rami mai tsananin zurfin gaske ina kwala ihu cikin karayar zuciyar saina fara kokarin ceton ratuwata ta hanyar amfani da karfin sihirin tsafi amma sai tsafin nawa yaki tasiri Al amarin daya kara tabbatar min da cewa lallai ajalina ne yazo ban isa karshen wannan rami ba sai bayan kimanin dakiku dubu daya da dari shida saboda mugun zurfinsa. Nidinne Dai Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan First Admin na zauran labarai page 2017 Zidane Mutum Da Aljan Littafi na biyar (5) Part D. . Marubucin littafin Abdul aziz sani madakin gini typing by Al amin Ahmed Misau Guyson contack: 08064594218 for more Doka' banyarjeba a yi edit na post dina.... . Labari ya isowa guyson cewa.. Ashe acan karshen ramin kasusuwane na matattun dabbobi, tsuntsaye da mutane bisa rashin sa'a kuwa sai na fado akan kashin wata dabba mai tsini take kashin ya sokeni a gefen cikina ya faso ta gadon bayana nidai kawai naji ganina dajina sun dauke duf, ban sake tuno da komai ba sai bayan wadansu sa'o'i sannan na farfado daga dogon suman da nayi koda na bude idona naga katon kashin dabba a cikin cikina har ya bullo ta gadon bayana kuma ga jinina ya zuba da yawa a kasa sai na kamu da tsananin mamakin abinda ya hanani mutuwa cikin tsananin juriya da karfin hali na yunkura ina mikewa sama kashin na fita daga cikin cikina a sannanne na rinka kwarara uban ihu gami da kururuwa mai ban tsoro saka makon mugun zafi da radadin da nake ji a cikina aikuwa ina gama zare kashin daga cikin cikin nawa na sulale kasa mutuwa nayi ko suma ban sani ba lokacin da jaruma luslaiya ta barni a cikin wannan rami wanda ta tabbatar da cewa na gama halaka sai ta nufi wata hanyar daban wacce zata kaita can birninsu na taheren a maimakon ta nufi birnin Arnan daji inda zamu yi gasarmu ta biyu har tayi nisan zango Arba'in a cikin tafiyar tata sai wani tunani ya fado mata a rai ta tsaya cak a inda take ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tace yanzu idan na isa gida da wacce hujja zan gamsar da mahaifina cewar nice na lashe wannan gasa wacce mukayi nida yarima Alkasim lallai idan ina son ya gamsu dolene na koma can bakin ramin nasan dabarar da zanyi na shiga cikinsa na dauko gawar Alkasim na tafi da ita gama ayyana hakan keda wuya sai luslaiya ta juya da baya da gudu ta nufi inda ta baroni bata iso ba sai bayan sa'o'i da isowarta bakin katon ramin sai tayi turjiya koda ta leko kasan ramin a karo na biyu taga baata iya hango karshensa ba saboda tsananin zurfinsa sai hankalinta ya dugunzuma kuma zuciyarta ta buga da karfi tace kai kada nima fa naje na hallaka a banza a kokarin shiga wannan rami tunda kowanne irin tsautsayi zai iya faruwa a gareni wata zuciyar kuma sai tace da ita to ai baki da wani zabi wanda yafi ki shiga cikin wannan rami ki dauko gawar sarki alkasim inba haka ba kuwa duk wannan wahalar da kika sha a baya ta zama ta banza domin baki da hujjar da zaki tabbatar da cewar kece kika lashe wannan gasa taku a wajen mahaifinki sarkin mafarauta na birnin taheren koda gama ayyana hakan sai ta fara tunanin irin dabarar daya kamata tayi don shiga kasan wannan mugun rami ai kuwa bata dade tana tunanin ba dabara ta zo mata wannan igiyar tata mai kugiya ta sake fiddowa ta sakalata a jikin wata bishiya mai kauri ta sulala izuwa kasan ramin sannan ta runtse idanunta ta fara yin wani irin sihirin tsafitake igiyar ta ringa karawa kanta tsawo tana sauka izuwa kasan ramin nan fa luslaiya ta rinka ganin zurfin ramin a cikin idanunta ai kuwa igiyar bata isa can karshen ramin ba sai bayan sa a uku al amarin daya yi matukar dugunzuma hankalin luslaiya kenan amma da yake bata da wani zabi dole ta kama igiyar ta fara sauka kasan ramin kafin luslaiya ta isa kasan ramin saida ta shafe tsawon sa a ukun ta sha bakar wahala kuma babu yadda bata yi ba ta isa kasan ramin da sauri bisa karfin tsafi amma abu ya gagara koda ta dira a karshen ramin sai tayi arba da gawata a kwance cikin rub da ciki ga ramin da kashin dabba yayi min a gadon bayana cikin farin ciki ta matso daf dani ta tsugunna tana haki sakamakon muguwar gajiyar da tayi don haka dolene ta huta tsawon lokaci sannan ta dauke gawata ta saba a kafadarta ta kama igiyar ta hau tayi sama wannan tunani da tayine hankalinta ya dugunzuma ta tuno da wahalar da tasha ita kadai bare kuma yanzu ga dakon gawa sai da luslaiya ta shafe sa aguda tana huce gajiya dake jikinta sannan ta mike tsaye ta kama gawata da nufin ta dorata akan kafadarta kwasam ba zato ba tsammani sai taji nasa hannuna na tunkudeta ta fadi can gefe daya cikin tsananin juriya da zafin nama na kama rigar jikina na yageta sannan na daure ramin raunin jikin nawa kuma na mike tsaye bisa kafafuna na dubeta tana daga zaune a kasa dirshan gaban kwarangwalolin dabbobi da mutane nace har yanzu ban mutu ba don haka gasa bata kare ba saimu ci gaba saboda tsananin kaduwa da mamaki luslaiya kasa yin magana tayi da motsi kawai saita bude bakinta tana kallona kawai daga can saita bushe baki tace kai mutun ne ko Aljan? Yaya akayi ka rayu baka mutu ba alhalin ga wannan mugun rauni a cikinka mazajen kwarai basa faduwa a banza domin ransu tamkar na karfe ne Ina gama fadin hakan sainayi wuf na finciko jakar guzurinta na budeta na fiddo ragowar wannan gasasshshen tsuntsu data boye na kama ci har saida na koshi ina gamawa na zura hannuna a cikin aljihuna na fiddo wani kullin garin magani na zazzagashi akan raunin cikin nawa take wajen ya kama turon da hayaki tamkar wuta aka zuba masa na rinka ihu da kururuwa saboda tsananin zafi da Radadin da naji har saida raunin yayi baki kirin kuma ramin ya toshe tamkar wajan bai taba hujewa ba sannan na daina ihu da kururuwa kawai saina dubi luslaiya nace tare zamu hau wannan igiya taki mu fice daga cikin wannan rami don bazan yarda ki rigani fita ba koda sarki Alkasim yazo nan a cikin labarin da yake baiwa yarima kamsus sai ya daga masa hannu yana mai dakatar dashi yace tsaya haka yakai Abbana nifa gaba daya kaina ya daure da jin abubuwan da suka faru a cikin wannan labari naka Wai shin kana son kace dani sai da kuka kammala wannan gasa kenan? Anya kuwa zaka gama bani wannan labari kafin mu isa birnin sarki Masarul Anjana? . SHIN ME ZAI FARU A CIKIN TAFIYAR YARIMA ALKASIM DA JARUMA LUSLAIYA? KAFIN SU KAMMALA GASARSU HAR TA KAMU DA SONSA SUYI AURE KUMA MENENE SANADIN AJALINTA? IDAN AKA ISA GARIN SARKI MASARUL ANJANA ME ZAI FARU TSAKANIN GIMBIYA ZULFULAIFA DA YARIMA KAMSUS KUMA MAI ZAI FARU A TSAKANIN SARKI ALKASIM DA SARKI MASARUL ANJANA? INA LABARIN JARUMI ZAIHADA DA YAR'UWARSA? SHIN ZASU SAMU NASARAR DAUKAR FANSA AKAN SARKI ALKASIM??? Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents Mutum Da Aljan Littafi Na Shida (6) Complete . Al amin Ahmed Misau Suleiman zidane kd Whatsapp 0861272634 post:Abubakar Ahmad # Adon_masoya Labari ya isowa guyson cewa... . Lokacin da sarki Alkasim yaji tambayar da yarima kamsus yayi masa sai yayi murmushi yace ni kuwa dadina dakai gajen hakuri ai a cikin kankanin lokaci zan gama baka wannan labari kuma zaka sha mamaki idan kaji yadda karshen gasarmu yake kasancewa ni kaina yanzu bana son na tsaya akan wannan labari da nake baka face na je karshensa ko muna kan hanyane zan cigaba da bakashi yanzu dai tunda mun kammala cin abincin zaifi kyau mu tashi mu kimtsa tunda mu kadai ake jira ba tare da wata gardama ba sai yarima kamsus ya mike tsaye nan da nan shida sarki suka gama kimtsawa suka hau bisa dawakansu suka jagoranci dubunnan daruruwan jama'ar dake cikin wannan tawaga tasu suka durfafi hanyar da zata kaisu birnin sarki masarul anjana ana fara wannan tafiya sai yarima kamsus ya jera da sarkin yaki ya ki yarda wani abu ya shiga tsakaninsu burinsa kawai shine sarki ya cigaba da bashi wannan labari na gasarsa da jaruma luslaiya bisa mamaki sai yaji sarki yayi shiru har ya zamana cewa tafiyar tasu ta fara dan nisa don haka takai tsawon rabin sa'a Al'amarin da ya jefa yarima cikin tsananin damuwa kenan yayi kamar ya yiwa sarki magana amma sai yayi shiru A dai dai wannan lokaci ne suka iso wani kauye na Aljanu dake cikin nahiyar kasar sarki Masarul Anjana nan fa gaba dayan jama'ar dake cikin tawagar suka cika da tsananin mamaki dukkaninsu suka zama kamar 'yan kauye domin basu san sa adda suka wangame bakunansu ba suka kama kalle kalle saboda gani sukayi kamar mafarki sukeyi ba a zahiri suke ba gaba dayan gidajen dake wannan kauye sunkai kimanin guda dubu uku da doriya kuma dukkaninsu iri dayane kuma an ginasu ne da tubalin zinare ko ina a cikin kauyen babu inda mutum zaiga wata kazanta an shimfide ko ina da dutsen jauhar Abinda yafi daurewa kowa kai shine babu kura ko wata iska mai karfi dazata dami mutum a garin face wani irin yanayi mai dadin gaske wanda babu zafi kuma babu sanyi irin wannan yanayine yake sawa fatar jikin mutum ta rinka sheki laushi da haske tamkar jariri gaba dayan Al'ummar wannan kauye suna ta kai kawo suna tafiyar da harkokinsu babu wanda ya kula su sarki Alkasim sai dai kaga suna ratsawa ta cikin jikkunansu suna wucewa abinsu Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan daga zauran Labarai. Sarki Alkasim bai san sa'adda ya ja linzamin dokinsa ba ya tsaya a kofar wani katafaren gida mafi girma da kawatuwa a garin kai da gani kasan cewa wannan gida mallakar shugaban kauyen ne koda ganin tsayuwar sarki sai kowa ma ya tsaya faruwar hakan keda wuya saiga wani narkeken Aljani ya fito daga cikin wannan gida a cikin shiga irin ta masu mulki, fadawansa a biye dashi, da isowarsa daf da sarki Alkasim sai ya risina kamar zaiyi masa sujjada sannan ya dago kai ya dubeshi yace '' Lale marhaban da sadaukin sadaukai , sarki Alkasim na birnin misra inayi maka barka da zuwa kauyen LAUSAS sunana DAMZURUL MASWAD nine shugaban mazauna wannan kauye na lusas daga nan zuwa babban birnin kasarmu wato DILHAR inda maigirma Sarki masarul Anjana yake tafiyace ta kwana goma sha uku kacal Kayi sani cewa sarakunanku na bil adama guda dubu dari takwas da saba in da ukune suka rigaka isa fadar sarkinmu kuma akwai wasu da yawa a bayanka idan kana so zaka iya hutawa a cikin garina har tsawona Sa'a uku sannan kuci gaba da yin tafiyarku koda shugaba damzurul maswad yazo nan a jawabinsa sai fuskarsarki Alkasim ta fadada da murmushi yace zanyi farin ciki da hakan nan take wasu hadiman Aljanu suda yawa suka baiyana tsulum ! Suka kamawa kowa abin hawansa aka sauka nan dai aka tafi da ababan hawan izuwa wani wuri daban sannan aka wangame katuwar kofar wannan babban gida take shugaban damzurul Maswad da fadawansa suka yiwa su sarki Alkasim jagora izuwa cikin gidan saboda zurfin wannan gida da fadinsa da kuma kayan kawar da aka shirya masa hatta sarki Alkasim da yarima kamsus dimaucewa sukayi suka zama cikakkun 'yan kauye cikin kankanin lokaci aka kai kowa masaukinsa kuma aka basu abinci da abin sha nasu na biladama kuma na alfarma harda irin wanda shima kansa sarki Alkasim bai taba dandanarsa ba Abin da yafi baiwa kowa mamaki shine ganin yadda a cikin dakiku kadan aka kai dukkan tawagar izuwa cikin dakunansu kuma mutum bibbiyu aka rinka hadasu wadansu kyawawan yan matan Aljanu ne wadanda kamar su sukayi kansu don kyau suka rinka yi musu hidima da yawa daga cikin mutanan wannan tawaga ta sarki Alkasim basu san sa adda suka kama sambatu ba suna cewa aisu inda sun san cewa akwai irin wannan aljannar duniya da tuni sun baro komai da kowa nasu sun dawo wannan gari da zama koda kuwa zasu yi aikin bautane a cikinsa wasu kuwa sai suka kama kuka saboda bakin cikin sanin cewa babu aure a tsakanin MUTUM DA ALJAN inda daga cikin inda da halin hakan da kowa ya auri daya daga cikin wadannan kyawawan kuyangi masu yi masa hidima lokacin da yarima kamsus yaga an hadasu tare da shi da sarki a cikin wannan kasaitaccen babban daki mai dauke da shimfidu kujeru da gidaje na alfarma sai ya kamu da tsananin farin ciki da shigarsu cikin dakin sai sarki Alkasim ya nufi wani luntsumemen gado ya fada kansa ya baje saboda tsananin taushin gadon take ya fara lumshe idanu alamar cewa barci na son satarsa koda ganin hakan sai yarima kamsus ya tasheshi zaune sannan ya dubeshi cikin alamun matukar damuwa yace haba yakai abbana yanzu ashe duk barcin da ka keyi jiya a cikin dare bai ishekaba? Kada ka bamu kunya fa tun yanzu nan kauyene kawai a cikin garuruwan kasar sarki masarul anjana'' koda jin wannan batu sai sarki Alkasim yayi zumbur ya mike tsaye yana mai mitsitstsike idanunsa sannan ya nufi kan wata doguwar kujera yana rike da hannun yarima suka zauna tare suna masu fuskantar juna sarki Alkasim yayi gyaran murya sannan yace yakai dana hakika wannan duniya fadi gareta kuma abin cikinta yawa gareshi tabbas na daina raina kowa da komai domin komai na iya faruwa cikin bazato amma duk da haka na yarda da kaina nayi imani cewa ni zakine abin tsoro zan iya jada duk wani mai ji da kansa don haka har abada zuciyata ba zata karaya ba akan mutum da Aljan domin sai an buga sannan ake sanin na kwarai. Inaji a jikina cewa a tsakaninmu ni dakai dayanmu zai cika burin sarki masarul anjana na sauya rayuwar 'yarsa lokacin da sarki Alkasim yazo nan a jawabinsa sai yarima kamsus ya bushe da dariyar

Chapter 7 of 9