Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
ya suri yan tsaki yayi jifa dasu izuwa cikin wata korama dake can gefe daya.Ai kuwa sai Sarki Alkasim ya soki kasa da makaman nasa maimakon ya sami nasarar soke cikinsu.Koda Namrita da Zaihas suka fada cikin wannan fadama ruwa ya jikasu sai nan da nan suka farfado daga suman da sukayi suna bude idanuwansu sai suka hango sarki Alkasim ya nufo su da gudu a sama tamkar ya kasance kibiyar da aka harbo daga cikin baka saboda karfin gudun nasa.Saura baifi taku uku ba kacal ya sake samun nasarar soke su sai yaga sun daidance sun zama kamar kwayar zarra sun shige cikin karkashin kasa sun bace bat. ★MUTUM DA ALJAN★!!! Littafi Na Biyu (2) Part C . ★A-Haleefah Physicist★ SUN SHIGE CIKIN KARKASHIN KASA SUN BACE BAT.Sarki Alkasim ya diro kasa bisa kafafuwansa fuskarsa cike da kaduwa gami da mamaki yana dube dube amma ko alamun tsagwayen bai gani ba.Duk irin ilmin tsafin da sarki Alkasim ke dashi bai taba sanin irin wannan lakani dasu Namrita sukayi ba.Nanfa ya shiga amfani da karfin Sihirin nasa na tsafi domin ya gano inda suke amma sai abu ya faskara.Al'amarin da yayi matukar fusatashi kenan ya juyo ya dubi Yarima yana mai daka masa harara irin wacce bai taba yi masa ba har saida Yarima yaji ya firgita hantar cikinsa ta kada.Kawai sai sarki Alkasim ya daka masa tsawa yana mai cewa akan wane dalili ka tserar da rayuwar makiyana?Shin ka gaji da ganina ne ka kosa na mutu ka haye kan karagata?Koda jin wannan tambaya sai nan da nan idanun Yarima suka kada sukayi jawur har hawaye ya zubo masa,kawai sai ya durkusa bisa guiwoyinsa biyu yana mai sunkuyar da kansa kasa ya bude baki cikin sanyin murya yace tabbas na aikata babban kuskure kuma babban laifi wanda ya zame mini abin nadama a halin yanzu.Ya kai Abbana maza ka takobinka ka sare kaina.Idan zubar da jinina zai sa zuciyarka ta huce daga zafin dana aikata Maka.Koda yarima Kamsus yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki Alkasim yayi sanyi bai san sa'adda ya mayar da makamansa cikin kufe ba sannan yazo gaban yarima ya kama kafadunsa ya tashe shi tsaye suka dubi juna ido da ido sannan yace yakai dana hakika ka aikata mini babban laifin da bazan iya yafe maka ba.Ka sani cewa bazan iya kasheka ba a matsayinka na dana guda daya jal tilo wanda nake tsananin SO da KAUNA fiye da komai amma ya zama wajibi nayi maka horo bisa wannan laifi daka aikata mini domin ya zamo izina a kan dukkan jama'ar dake karkashina su san cewa babu wanda yafi karfin fuskantar hukuncina muddin ya aikata laifi tunda gashi na hukunta dana na cikina.Zaka fuskanci horo na dauri a cikin rana na tsawon yini uku ba ci ba sha.Koda gama fadin hakan sai sarki Alkasim ya juyawa yarima baya sannan ya fiddo wani karamin kaho daga cikin aljihunsa ya busa.Faruwar hakan keda wuya saiga shugaban dakaru Uzaila tare da dukkan yaransa da kuma hadiman sarki sun rugo da gudu izuwa cikin sansanin.Da zuwansu sai sarki ya bayar da umarnin a gyara masa tantinsa kuma a dawo da sauran abokan tafiya.Ba tare da bata lokaci ba aka cika wannan umarni kuma aka sanya tsaro mai tsauri a sansanin irin na farko.Da yake sauran abokan tafiyar basu san abinda ya faru ba sai sukayi ta mamakin abin da yasa sarki ya sauya shawara haka nan da nan. *Al'amarin jaruma Namrita da dan uwanta Jarumi Zaihas kuwa lokacin da suka tsira da rayuwarsu daga sharrin sarki Alkasim ya zamana cewa sun zama kwayoyin zarra sun shige cikin karkashin kasa basu bayyana a ko ina ba sai a can cikin wani daji dake can bayan wanda su sarki Alkasim suke.Tazarar dake tsakaninsu takai tafiyar sa'a uku.A galabaice suka baje a kan kasa suna numfarfashi kamar ransu zai fita.Saida suka shafe yan dakiku suna hutawa sannan suka mike zaune a lokacin da suka dawo cikin hayyacinsu sosai.A wannan lokaci ne kowannensu ya fada cikin sabon kogin tunani.Shidai jarumi Zaihas ba komai yake tunani ba face mamaki irin tsantsar jarumtakar sarki Alkasim gami da bajintarsa ta iya yaki.A zatonsu shekaru bakwai da suka shafe shi da yar uwarsa suna neman ilmin tsafi gami da karbar horon yaki a wajen jarumai kala kala sun sami damar da zasu iya kashe sarki Alkasim amma sai gashi sun kasa don haka lallai aikin dake gabansu bana wasa bane dole ne su sake yin sabon shiri gami da sabon tunani.Ita kuwa Jaruma Namrita ba komai ta fara tunowa ba face fuskar yarima Kamsus a lokacin da ya ceci rayuwarsu sa'adda sarki Alkasim ya fado kansu zai tsire cikinsu da makamansa.Wai shin a kan wane dalili yarima Kamsus ya ceci rayuwarmu?Alhalin yasan cewa mu makiyan mahaifinsa ne?Wane irin kallo ne yayi mini a lokacin?Shin ya kamu da SO na ne shi yasa ya ceci rayuwata data dan uwana?Amma dai ya cika SAUNA idan har saboda SOYAYYA ya tserar da rayuwar MAKIYANSA.Koda Namrita tazo nan a zancenta na zuci sai taji zuciyarta ta ta buga da karfi a karon farko a rayuwarta.Kawai kuma sai taji babu abinda take so sama data sami damar da zata sake saduwa da yarima Kamsus har su zauna suyi yar hira domin tasan gaskiyar abinda yake cikin ransa.Ayyana hakan keda wuya sai hankalinta ya dugunzuma ainun saboda ta fahimci cewar akwai alamun itama ta dan kamu da son Yarima Kamsus.Tana cikin wannan tunani ne Zaihas ya dubeta yana mai katse mata hanzari yace yanzu wane mataki ya kamata mu dauka tunda dai munyi gumurzu da sarki Alkasim gaba da gaba babu nasara?Koda jin wannan tambaya sai Namrita ta kawo gwauron numfashi ta ajiye sannan tace ai komai ya dagule a halin yanzu,tabbas ba zamu iya kashe sarki Alkasim ba a cikin wannan tafiya.Dole mu hakura har a isa can birnin Sarki Masarul Anjana.A can ne kadai zamu iya kashe shi kuma sai mun hada kai da masanin sirrinsa.Koda jin wannan batu sai Zaihas ya murtuke fuskarsa ya dubi Namrita cikin alamun tsananin fushi yace wannan kuma wace irin maganar banza ki keyi haka?Kina nufin kice ba zamu sake jarraba sa'armu ba a kansa?To kiyi sani cewa abinda muka kasa yi anan ba zamu iya yinsa a cikin birnin sarki Masarul Anjana ba,saboda birninsa ne birnin da yafi ko ina a duniya tsaro.Ke dai kawai ki gaya mini gaskiya idan kin sauya shawara ne a cikin zuciyarki domin na fuskanci kin yaba da abinda yarima yayi mana.Koda jin wannan batu sai Namrita tayi farat tace ni babu wani abu dana sauya a cikin zuciyata kuma ni Yarima Kamsu bai ★Abubakar Haleefah Physicist★ burgeni ba amma ya bani mamaki,shi yasa kaga ina kallonsa domin banga dalilin da zaisa ya ceci rayuwarmu ba alhalin yasan cewa so muke mu kashe mahaifinsa.Sa'adda Zaihas yaji wannan batu sai yayi murmushi yace nima nayi mamaki amma kuma ta wani fannin banyi mamaki ba,tunda inda zaki iya tunowa tun muna yara lokacin da sarki Alkasim ya kashe mahaifinmu Yarima Kamsus ne kadai ya tausaya mana harma saida ya zubar da hawaye,kinga kenan shi yafi mahaifinsa adalci da tausayin talakawa,don haka baya goyon bayan irin abubuwan da yake aikatawa.Ina miki gargadin cewa kada ki kuskura ki bari zuciyarki ta sami rauni akan wannan gagarumin buri dake gabanmu na daukar fansar ran mahaifinmu domin ko yaya son yarima ya darsu a cikin zuciyarki to ba zamu taba samun nasara ba.Sa'adda Jaruma Namrita taji wannan batu sai jikinta yayi sanyi ainun tayi shiru tana mai sunkuyar da kanta kas kuma tayi shiru har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai ta dago kai ta dubi Zaihas cikin murmushi tace ka kwantar da hankalinka yakai dan uwana,kayi sani cewa babu wani mahaluki walau MUTUM ko ALJAN wanda zaisa na fasa aiwatar da wannan babban aiki dake gabanmu.Ko mutuwa nayi ruhina ba zai kwanta ba a cikin kabari face ya dauki wannan fansa,tunda zaluntar mahaifinmu akayi aka kashe shi ba bisa laifinsa ba sai bisa kuskure da rashin sani.Koda gama fadin hakan sai zuciyar Namrita ta karaya idanunta suka ciko da kwallah bata san sa'adda ta fashe da kuka ba.Koda ganin haka sai shima Zaihas zuciyarsa ta karaya don haka sai ya kamo Namrita ya rungume ta uana mai rarrashinta a lokacin da shima idanunsa suka ciko da kwallah. *A can sansanin su Yarima Kamsus kuwa lokacin da sarki Alkasim ya shiga cikin tantinsa ya kwanta domin yayi bacci sai ya kasa sakamakon takaici bisa ganin yadda Zaihas da Namrita suka iya guje masa suka bace masa da gani ya neme su sama da kasa ya rasa.Abinda ya daure masa kai kenan ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace yanzu kenan akwai kalar sihirin da bani dashi a cikin wannan duniya alhalin ina ganin cewa babu wani boka wanda ya fini ilmin tsafi ko kuwa wannan bacewa dasu Namrita sukayi bada sihirin tsafi bane?Ai kuwa idan haka ne yanzu za'a iya samun wanda ya fini karfin sihirin tsafi anan cikin duniyarmu ta bil'adama,ashe idan muka isa birnin Sarki Masarul Anjana zan iya jin kunya ko kuma na raina.Haka dai sarki Alkasim ya cigaba da wannan tunani da zulumi daga karshe sai kawai ya manta da komai yayi kwanciyarsa yaja mayafi ya lullube jikinsa sakamakon sanyin da ake busawa.Lokacin da gari ya waye sai aka kawowa sarki Alkasim abincin buda baki,maimakon ya zauna yaci abincin sai ya fito daga cikin tantin nasa da sauri a fusace ya kwalawa shugaban dakaru Uzaila kira.Nan da nan sai ga Uzaila ya iso da gudu.Da zuwansa sai ya zube a kasa gaban sarki ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shugabana me kake da bukata?Koda jin wannan tambaya sai sarki ya dubi Uzaima a fusace yace maza ka debo dakaru kuje tantin Yarima ku kamo shi da karfin tsiya ku kai shi tsakiyar sansanin nan ku daure shi a jikin Dirka yadda rana zata kare a kansa kuma duk wanda ya bashi ruwa makwarwa daya ko abinci kwatankwacin kwaya guda ni da kaina zansa takobina na sare shi.Koda jin wannan umarni sai mamaki ya turnuke Uzaila da dukkan dakarun dake kusa dashi amma sai Uzaila ya mike tsaye da sauri yana mai cewa an gama ya shugabana.Nan take Uzaila ya zabo karti shida majiya karfi daga cikin yaransa suka durfafi tantin Yarima. ★MUTUM DA ALJAN★!!! Littafi Na Biyu (2) Part D ★A-Haleefah Physicist★. SUKA DURFAFI TANTIN YARIMA.Da shigarsu cikin tantin sai suka iske Yarima a zaune yayi tagumi yana mai hada kansa da guiwa kuma yana rike da takobinsa da hannunsa guda.Koda ganin yarima a cikin wannan hali sai hankalin su Uzaila ya dugunzuma ainun suka firgita domin a zatonsu Yarima yakarsu zaiyi kuma sun san cewa a cikin dakiku kadan zai hallakasu su duka.Bisa wannan dalili ne jikinsu ya kama karkarwa aka rasa wanda zai kusance shi bare yayi yunkurin kamashi.Kwatsam sai sukaga Yarima Kamsus ya dago kai ya dube su cikin murmushi sannan yace yakai Uzaila ku kwantar da hankalinku kuyi sani cewa babu yadda za'ayi na yake ku.Ina mai umartarku daku cigaba da aikinku.Inason ku kamani a wulakance kuna jana a kasa tamkar bawa ku kaini har can tsakiyar sansanin kuyi duk yadda aka baku umarni don kada fushin sarki ya tabbata a kanku.Koda jin wannan batu sai Uzaila yaji ya kamu da tausayin yarima amma sai ya dubeshi yace ka gafarceni ya shugabana ba'a son raina haka zata faru ba.Yana gama fadin hakan sai ya dubi wadannan karti shida yayi musu inkiya.Nan take suka make yarima ya fadi kasa har lebansa ya dan dare jini ya zubo,kawai sai suka kama shi suka rinka jansa a kasa tamkar tsumma suka fice dashi daga cikin tantin.Uzaila na biye dasu har zuwa tsakiyar sansanin.Da zuwa sai aka haka rami aka binne wata dirka mai gwafa sannan aka daga Yarima Kamsus aka daure shi tamau da murtukekiyar igiya a jikin dirkar.Kawai sai aka bar shi anan kowa ya cigaba da harkokinsa.A gaban Yarima akayi kalaci aka ci abincin rana dana dare amma ko digon ruwa ba'a sanya masa a cikin bakinsa ba.Har ma saida sarki yazo gabansa yasa aka gasa masa barewa ya rinka ci yana shan ruwan inibi a gefe daya kuma ga wadansu kuyangi suna tika rawa sarki Alkasim nata faman kyakyata dariya abinsa ko kallon yarima sau daya baiyi ba.Har saida aka dauki lokaci mai dan tsawo anayin wannan bidiri ya zamana cewa gari ya soma duhu.A wannan lokaci yarima ya galabaita ainun,lebansa ya bushe saboda kishirwa kuma idanunsa har lumshewa sukeyi saboda yunwa da jigata.Kawai sai akaga sarki Alkasim ya mike tsaye ya juya ya nufi inda tantinsa yake.Koda gamin haka sai Uzaila ya ruga gareshi ya risina yace ya shugabana zaka tafi kuma baka bayar da umarnin a kwance Yarima ba a bashi abinci da ruwa ba.Koda jin wannan batu sai sarki Alkasim yayi murmushi yace ku kyale shi sai nan da cikar sa'a guda tukunna.Dajin haka sai Uzaila ya dubi sarki cikin kaduwa da firgici yace haba ya shugabana shin so kake lafiyar yarima ta tabu ne?Bai kamata kayi masa horo da yunwa ba ko kishirwa.Koda jin haka sai sarki ya turbune fuska ya dakawa Zaihar tsawa yace ka fini sonsa ne?Dana ne fa kuma shi kadai gareni a wannan duniya.Laifi yayi mini kuma sai dana gargade shi a kan kada ya aikata laifin amma yabi son zuciyarsa.Ta wannan hanyar ce kadai zansa ya gane kuskurensa kuma ya kori gaba.Kowa ya tafi yabar shi a wannan wuri sai bayan sa'a guda ka aika kuyangi su kwance shi sukai shi cikin tantinsa.Sarki Alkasim na gama fadin hakan sai ya juya ya nufin cikin tantinsa yaje ya kwanta,shima shugaban dakaru Uzaila ya gyada kai ya tafi izuwa inda nasa tantin yake. * A can dajin dasu Jarumi Zaihas suke kuwa lokacin da gari ya soma duhu bayan sun bude jakar guzurinsu sun dauko abinci sunci sai Namrita ta dubi Zaihas tace amma fa ya kamata muje sansanin su sarki Alkasim muyi LEKEN ASIRI domin musan halin da suke ciki saboda babu mamaki ya kasance suma suna shirin kawo ma harin bazato kamar yadda muka kaiwa sarki.Sa'adda Zaihas yaji wannan batu sai yayi ajiyar numfashi gami da gyada kai yace tabbas maganarki gaskiya ce amma kuma akwai hadarin gaske mu sake kai kanmu sansanin sarki Alkasim a yanzu domin babu mamaki sunyi mana mugun tanadi bisa tunanin cewa zamu sake kai wani hari.Namrita tace hakan zai iya faruwa amma ai tunda kasan cewa na kware ainun a iya leken asiri fiye da kai babu wani tarko wanda dakarun sarki Alkasim zasu iya dana mini ya kama ni.Rashin sanin shirin da sukeyi a kanmu yanzu yafi komai hadari a garemu.Ka kwantar da hankalinka ka barni naje nayi wannan leken asiri nayi maka alkawarin cewa babu abinda zai sameni kuma zan dawo gareka lafiya lau cikin koshin lafiya.Lokacin da Namrita tazo nan a zancenta sai dan uwanta Zaihas yayi shiru yana tunani gami da nazarin abinda ta fada har izuwa lokaci mai dan tsawo daga can kuma sai ya dago kai ya dubeta yace shi kenan yar uwata na amince ki tashi kije kiyi wannan aiki amma ki sani cewa idan sa'a hudu ta wuce banga kin dawo ba zan biyo bayanki domin zanyi zaton cewa kin fada tarkon makiya.Koda jin haka sai fuskar Namrita ta fadada da murmushu tace na yarda da hakan.Tana gama fadin hakan sai ta mike tsaye zumbur ta dauki MAKAMANTA na YAKI ta dauresu a jikinta kuma ta rufe fuskarta da wata bakar hula yadda idanunta,hancinta da bakinta kadai ake gani,kawai saita rungume Zaihas tana mai yi masa sallama sannan ta juya ta falfala da azababben gudu izuwa cikin daji.Wani irin gudu ne na ban al'ajabi Namrita keyi wanda saidai a kwatantashi da gudun tauraruwa mai wutsiya a cikin gajimare.Nan da nan kuwa cikin kankanin lokaci Namrita ta iso sansanin su sarki Alkasim,nan take tayi girgiza ta zama wahainiya ta cigaba da tafiya a kasa tana giftawa ta gaban dakarun sarki Alkasim ba tare da kowa ya ganta ba saboda kalar jikinta ta saje da ciyawar kasa.Kwatsam ba zato ba tsammani Namrita na cikin kalle kalle da dube dube a cikin sansanin tana nazarin komai da kowa dake wajen sai ta hango yarima Kamsus tsaye ★Abubakar Haleefah Physicist★ kuma a daure jikin dirka a tsakiyar sansanin.Al'amarin da yayi matukar daure mata kai kenan ta tsaya cak a inda take tana tunani inda tace a cikin ranta anya kuwa wannan ba wani tarkon bane ba aka dana mini?A daidai wannan lokaci ne ta hango yadda bakin Yarima Kamsus ya bushe kuma ta lura da irin mugun daurin da aka yiwa hannayensa da kafafuwansa.Take ta gane cewa tabbas abin da gaske ne.To waishin akan wane dalili sarki Alkasim zai yiwa dansa irin wannan danyen hukunci?Kafin Namrita ta baiwa kanta amsar wannan tambaya sai ta cigaba da tafiya da sauri akan ciyawa a cikin siffarta ta hawainiya ta nufi inda yarima Kamsus ke daure.Da zuwa sai ta daka tsalle ta dira akan kafarsa ta cigaba da tafiya a kan kafar tasa har ta iso kan kafadarsa.Tun sa'adda yarima yaji alamun tafiyar wani abu a jikinsa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda yasan cewa koma mene ne abinda ke hawa jikinsa zai iya cutar dashi tunda ba zai iya kare kansa ba sakamakon cewa hannayensa da kafafuwansa a daure suke tamau.Koda Yarima yayi arba da hawainiyar data taho kan kafadarsa sai yaji tsigar jikinsa ta tashi gaba daya kuma tsoro ya kama shi domin yaji a jikinsa cewar wannan ba kwaro bace saidai MUTUM KO ALJAN.Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga hawainiyar ta rikide ta zama jaruma Namrita zaune akan kafadarsa ta kura masa idanu tanayi masa murmushi.Kafin ya bude baki yace wani abu sai ta dafa kansa da hannunta na hagu.Take igiyar data daureshi ta kwance kanta suka bace tare daga sansanin.Basu bayyana a ko'ina ba sai a can wani bangaren daban na dajin.Kawai sai ta cire battar ruwa a jikinta ta mika masa tace maza kasha wannan ruwa idan ba so kake kishirwa ta kasheka ba. ME ZAI FARU A YANZU TSAKANIN YARIMA KAMSUS DA JARUMA NAMRITA? SHIN SU JARUMI ZAIHAS ZASU SAMI NASARAR DAUKAR FANSA A KAN SARKI ALKASIM? YAUSHE NE ZA'A ISA BIRNIN SARKI MASARUL ANJANA? WADANNE ABUBUWAN MAMAKI NE ZASU FARU A FADAR SARKI MASARUL ANJANA?KUMA WANE IRIN DAUKI BA DADI ZA'AYI? WAYE ZAI DACE YASA GIMBIYA ZULFULAIFA DARIYA KUMA WANE LADA ZAI SAMU? Mu Hadu A Mutum Da Aljan. Littafi Na Uku Don Jin Cigaban Wannan Labari. Mene Hasashen ku game da wadannan tambayoyi? .MUTUM DA ALJAN Littafi Na Uku (3) Part B. Author: Abdul aziz M Gini Rubutawa : Al amin Ahmed Misau Nickname: Guyson ko shagala Contack me: 08064594218 Gargadi: Ban yarda wani yayi edit na wannan post ba ba tare da izinina ba.. . Labari ya isowa Guyson cewa Face mutum biyo, wato sarki da yarima kamsus tsawon yan dakiku suna tsaye suna kallon yadda ake ta shirye shiryen tafiyar dayansu bai ce uffan ba daga can sai sarki yayi gyaran murya ya dubeshi a cikin murmushi yace'' hakika ka baiwa namrita shawara mai kyau dakace da ita su manta da batun daukar fansa a kaina'' koda jin wannan batu sai zuciyar yarima kamsus ta buga da karfin gaske ya firgita ainun kuma ya kamu da tsananin mamaki kuma yayi shiru baice komai ba sarki ya sake yin murmushi a karo na biyu yace idan namrita da dan uwanta zaihas sun dauki shawararka sun daina farautar rayuwata nima zan kyalesu amma nayi maka alkawarin duk ranar da suka sake yin gangancin kawo min hari a wannan lokaci zan zare musu ruhin numfashinsu wannan shine kashedi na karshe kuma sakone nake baka yanzu ka isar dashi. Alfarma daya zan iya yi musu idan har suka zo gareni bisa lumana zan rokesu gafara bisa abinda na yi na kashe musu mahaifi ba akan laifinsa ba ka sani cewa a ka idar sarauta kisa a wajan sarki ba laifi bane saidai a kirashi kuskure saboda duk harkace ta mulki duk sarki na gari mai cikakken iko da isa gami da kamala baya durkusawa wani ko da kuwa dan uwansa sarki ne' koda sarki Alkasim yazo nan a zancensa sai ya kwalawa wani hadiminsa mai suna kailub kira yace maza ka janyo min dokina nan take kailub ya ruga zuwa inda dokin sarki yake kafin yazo da dokin tuni sauran hadimai sunkimtsa sarki sun daura masa damararsa an kawo masa takalmansa an ajiye a gabansa ya sanya kuma an shirya masa kayan yakinsa a jikinsa koda ganin haka sai shima yarima kamsus ya ruga zuwa nasa tantin ya shiga kimtsawa da sauri nasa hadimin na taimaka masa. Lokacin da sarki Alkasim ya gama shiri ya hau bisa ingarman dokinsa mai launin ruwan kasa ya zauna saiya wuce kan gaba gaba daya miliyoyin jama ar dake cikin tawagar sai suka biyoshi a baya duuuu.... Kai kace mutanen duniyar ne kaf sukayi hijira zasu koma wata nahiyar daban'' wohoho'' hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace dole ne ace da mijin iya BABA. domin duk wanda yaga sarki Alkasim a wannan lokaci saboda kwarjininsa cika idonsa da kuma irin gagarumar shigar yakin da ya yi dolene ya tsorata da al amarinsa saboda ya zama tamkar zaki Uban dawa kallo daya mutum zaiyiwa sarki Alkasim yaji zuciyarsa ta buga da karfi saboda kirarsa gaba daya irin ta zakice kaida gani kasan cewa dolene ya kasance masifaffen kakkarfa hm Guyson nake magana sarki Alkasim ya kasance dogon mutum mai murdadden jiki cike da kwanji gami da jijiyoyi yana da yalwataccen kirji cike da gashi kuma a fuska ya kasance kyakkyawa abin kwatance amma kusan ko yaushe fuskar tasa a murtuke take tamkar bai taba yin dariya ba tabbas barewa bata gudu danta yayi rarrafe yarima kamsus ya gado mahaifinsa a sura da cikar zati sai dai zuciyarsa bata da tauri irin ta mahaifinsa ma ana yafi sarki Alkasim walwala da annurin fuska kuma ya fishi tausayi gami da jin kai, sai dai suna tsananin kama da junansu tamkar hassan da usaini kawai shekaru ne ya banbantasu gami da tsohon kashi shidai sarki yana da saje mai kauri gemu mai tsawo da gashin baki mai yawa shi kuwa yarima kamsus bash da saje da gemu sai dan siririn gashin baki wanda ya yiwa lebensa da habarsa kawanya abin gwanin ban sha awa kuma ko yaushe yana tattare dogon gashin kansa ya tattareshi ya daure su zube bisa gadon bayansa yan matan kasar birnin misra da yawa sun dimauce a cikin soyayyar yarima kamsus saboda kwarjininsa kyawunsa da kuma baiwarsa ta jarumtaka kai wasu ma saida suka zama kamar zautattu saboda yawan begensa da ambatonsa amma ba a taba samun wacce ta burgeshi ba bare ma yayi soyayya shi kansa a halin yanzu da yaji zuciyarsa na begen jaruma namrita kamuwa yayi da tsananin mamaki har yana tambayar kansa a cikin zuci yana mai cewa akan wane dalili nake tunanin namrita alhalin na sha haduwa da matan da suka fita kyau matsayi da daukaka amsar da ya kasa baiwa kansa kenan a duk lokacin da wannan tunani ya bijiro masa to wai shin yadda naji na kamu da son namrita haka itama al amarin yake a ranta kuwa? Ta yaya zan gane hakan alhalin har yanzu bamu fito kuru kuru mun bayyanawa junanmu komai ba ai ita ce ya kamata ace ta fara bayyana min sirrin zuciyarta tunda ni dan sarkine ita kuwa ba yar kowa bace haka dai yarima kamsus yake ta irin wannan tunani da wasu wasun zuci mara kan gado a duk sa adda tunanin namrita ya bijiro masa. Kamar yadda sarki Alkasim ya fada haka al amarin ya kasance wato tunda aka fara wannan tafiya babu sassauci ba ayada zango sai bayan kwanaki uku uku kuma dare da rana a cikin tafiyar ake hatta abinci akan ababan hawa ake ci kuma ko bukatace ta kama mutum ba a tsayawa a jirashi saidai a barshi a baya ya kawai da bukatar idan ya kammala ya ruga da gudu ya riski tawagar kai ko barci ne ya kama mutum sai dai yayi akan dokinsa ko rakuminsa ko alfadaransa sau tari sai dai kaji tum mutum ya fado kasa daga kan abin hawansa saboda magagin barcin sai dai ya mike tsaye zumbur a firgice ya sake dane abin hawan nasa hm Al amin Ahmed Misau Guyson.. Wani babban abin mamaki shine babu wanda yake jin gajiyar tafiyar a jikinsu har sai an yada zango bayan cikar kwanaki ukun . Haka dai darare suka ci gaba da shudewa har ya zamana cewa saura kwanaki uku kacan a iso birnin sarki masarul anjana wanda ke nahiyar kasar Sin inda aka yada zango a cikin wani babban daji wanda ake kira da suna DARUL SAMJUL. Shidai wannan daji na darul samjul masana matafiya da masu bincike sun tabbatar da cewa babu wani daji mai girmansa tarin ni imominsa da kuma yawan dabbobi babu tamkarsa a duk fadin duniyar nan don haka yana da hadarin gaske saboda babu irin kalar mugayen halittun da babu a cikinsa kai sai mafarauci ya cika babban barde yake iya shiga cikinsa yayi farauta inba haka ba kuwa sai dai a dauko gawarsa a ciki koda aka iso farkon wannan daji sai sarki Alkasim dake kan gaba ya ga dokinsa yayi turjiya yana mai haniniya gami da daga kafafunsa na gaba sama kuma yaja da baya kadan cikin alamun firgici tamkar wanda ya hango wani mugun abu a gabansa ai kuwa nan take sauran dawakai da sauran alfadarai da rakuma sukayi koyi da wannan doki na sarki aka rasa dayansu wanda zai kara gaba koda taku daya ne koda ganin abinda ya faru sai farin ciki ya lullube sarki Alkasim ya bushe da dariyar farin ciki a lokacinda kowa ke firgici aka yi tsit ana kallonsa kawai cikin al ajabi kawai kuma sai aka ga sarki Alkasim ya sauko daga kan dokinsa ya tsuguna kasa bisa gwiwarsa guda ya debi kasa ya shinshina cikin hanzari da murna ya juyo ya dubi sarkin yaki da yarima kamsus yace tabbas mun iso dajin darul samjul dajin da na dade ina burin son zuwansa domin nayi farauta a cikinsa maza mu yada zango a nan a kafa tantuna tunda dare ya soma sai gobe da safe saimuyi shirin shiga farauta cikinsa yakai sarkin yaki ka zabo manyan jarumai a cikinmu guda arba in ka shirya mana gasar farauta a cikin wannan daji na darul samjul lallai ka sa kanka da yarima a cikin wannan gasar koda jin wannan batu sai mamaki da tsoro ya kama gaba dayan jama ar dake cikin wannan tawaga sarkin yaki da yarima kamsus ne kadaibasu yi wani gezau ba Saikuma Ni Al amin Guyson. Wanda na kasance Jarumi. Ba komai ne ya firgita jama ar ba face kowa ya dade yaana jin wannan dajin darul samjul ana cewa komai hatsabibancin boka ko mafarauci ko kuma jarumi yana shakkarsa akwai abubuwa masu tsananin wahalar gaske wadanda ba a samunsu sai a dajin darul samjul kuma mutane da yawa sun hallaka a kokarin nemo wadannan abubuwa a cikin dajin kai ance ma komai yawan ayari kona fatake idan sukazo giftawa ta cikin dajin darul samjul to sai kaso biyu cikin ukunsu sun zama gawa kaso dayan ma sai sun kasance zakwakuran mayaka matsafa da jarumtaka sannan zasu tsira kuma duk da hakan ma sai da yawansu sun samu mugayen raunuka a jikinsu ba tare da bata wani lokaci ba aka yada sansani a bakin wannan daji na darul samjul aka shiga kafa tantuna aka shirya kayayyaki sai dai mutane da yawa a firgice suke musamman mata hadiman da aka taho dasu saboda jiyo sautin kukan mugayen dabbobi da tsuntsayen dajin duk da cewa suna can nesa dasu saboda kukane mai irin wani bakon sauti wanda kunnuwa basu saba ji ba bayan an gama kafa tantuna anci abinci ana zaune ana hutawa kowa ya samu nutsuwa yarima kamsus na zaune a cikin tantinsa tare da wadansu kuyangi guda uku suna debe masa kewa daya

Chapter 3 of 9