Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
Rausum kenan hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe.Nan take yarima Kamsus ya kama kafadun boka Rausum ya tashe shi tsaye sannan ya dubeshi cikin murmushi yace yakai dirkar Birnina kayi sani cewa idan giwaye biyu na fada to dukkan namun daji saidai suyi kallo.Kai dan kallo ne kawai,bai kamata ka tashi hankalonka ba.Sarki Masarul Anjana da mahaifina manyan giwaye ne biyu,sauran sarakunan duniya da sauran jama'ar mutane da aljanu sune namun daji.Kawai ka zuba idanu kaga yanda karshen rigimar zata kasance.Tuni a yanzu labari ya riski Sarki Masarul Anjana bisa taurin kan Abbana da rashin tsoronsa,me yasa bai dauki mataki ba a kansa?Kar ta san kar kuma sai an gwada sannan ake sanin na kwarai.Muje can turakar ta sarki,yanzun nan zamu tafi.Koda jin haka sai murna ta kama boka Rausum ya juya da sauri suka fice daga cikin turakar yarima suka tunkari ta sarki.Da shigarsu cikin harabar turakar ta sarki sai suka iske sarki Alkasim a cikin rafinsa na wanka yana nishadi abinsa,ko kadan babu alamar cewa yana sauri ko shirin tafiyar dake gabansa.Koda sarki Alkasim ya hango Boka Rausum tare da yarima Kamsus saiya kyalkyale da dariya yace me kukazo yi wajena yanzu.Ashe tun jiya ba na gaya muku cewa sai yamma zamu bar garin nan ba?Kafin sarki ya gama rufe bakinsa tuni Yarima ya tari numfashinsa yana mai cewa ai na sauya tsarin tafiyar saboda wadansu dalilai masu mahimmanci.Koda jin haka sai sarki ya turbune fuska kuma yayi tsaki.Nan take ya fito daga cikin rafin babu komai a jikinsa face wani gajeran wando.Wohoho duk wanda ya kalli sarki Alkasim a wannan lokaci yaga irin kirar karfin da Allah yayi masa ta manyan sadaukai dole ne ya sallama kuma ya firgita saboda kirjinsa kai ya kasance tamkar na zaki cike da gashi,ga tudu da fadi.Gaba dayan jikinsa a murde yake cike da kwanji gami da tarin jijiyoyi tamkar ba kashi da tsoka bane,sai kace dutse aka jajjera. Zidane Kd SAI KACE DUTSE AKA JEJJARA.Nan take wata kuyanga tazo da sauri ta gogewa sarki Alkasim danshin ruwan dake jikinsa gaba daya.Kafin cikar yan dakiku an kawo tufafi iri daya dana jikin Yarima Kamsus an sanyawa sarki Alkasim sai gashi shima yayi kyau sosai.Kai in ba don sarki Alkasim yana da saje da kasumba ba da shima za'a iya cewa matashine kamar dansa Yarima Kamsus.Ba tare da bata wani lokaci ba aka gama kimtsa sarki suka tafi izuwa babbar fada su ukun.Dakaru da kuyangi na take musu baya.Da isarsu cikin fadar kuwa sai suka iske gaba dayan fadawa a tsaitsaye a bayan KARAGAR MULKI.Abokan tafiya kuwa wato,MAWAKA,MAKADA,JARUMAI da masu BARKWANCI na tsaitsaye a tsakiyar fadar suna fuskantar karagar mulkin.Koda shigowarsu sai yarima ya kurawa abokan tafiyar idanu yana kallonsu daya bayan daya yana kokarin yaga wadannan bakin tagwaye amma wayam.Ko Alamarsu bai gani ba.Ashe shima sarki ya lura da hakan.Abinda basu sani ba shine a yau tagwayen basuyi shiga iri daya ba,kuma basa tare a waje guda kuma ita macen bata rufe fuskarta ba,amma tayi wata irin shiga ta batar da kamanninta.Su dai wadanann tagwaye basu kasance yan kasar Misra ba kuma ba komai ne yasa suka shiga wannan tafiya ba sai domin su dauki fansa a kan sarki Alkasim bisa mahaifinsu daya kashe akan wani laifi daya aika bisa rashin sani a matsayinsa na bako.Wannan abu ya faru ne kimanin shekaru bakwai da suka gabata.Akwai wata shekara da akayi fari na ruwan sha a birnin Misra saboda gurbatar magudanar ruwan garin sakamakon wani mugun boka da yazo ya lalata ruwan garin ya zuba matattun tsuntsaye a cikin ruwan don gabatar da aikinsa na sihiri.Nan take sarki Alkasim yasa aka kamo bokan aka tsire shi a bainar kasuwa kuma ka kafa dokar cewa duk mutumin da aka sake gani yayi ta'ammali da magudanar ruwa kisa ne hukuncinsa.Bayan shekara daya da faruwar wannan abu ne wani matafiyi yazo giftawa ta bakin magudanar ruwan birnin Misra tare da iyalinsa,matarsa da 'ya'yansa guda biyu mace da namiji wadanda shekarunsu sun kai goma sha daidai.Koda wannan mutum tare da iyalansa sukazo giftawa ta gefen wannan magudanr ruwa sai santsi ya kwashi dawakansu suka fada cikin wani tabo gaba dayansu duk jikinsu da jikin dawakan ya turbune da tabo.Abinka da rashin sani sai suka mike tsaye suka shiga cikin wannan magudanar ruwa tare da dawakan nasu suka kama wanke tabon jikin nasu.Suna cikin hakane dakaru sukazo suka kewayesu aka kamasu aka kaisu fada gaban sarki aka gurfanar dasu aka fadi laifinsu.A wannan lokaci Yarima Kamsus na zaune daf da sarki kuma shima baifi shekara goma sha daya ba a duniya.Ba tare da sarki Alkasim yayi wani bincike ba sai kawai yace aje a kashe wannan mutum.Nan take yarima Kamsus ya kama rokon sarki Alkasim akan ya yiwa mutumin afuwa amma sai ya ki.Iyalin mutumin na kuka suna ihu gami da rukunkume shi amma sai aka fincike shi daga jikinsu da karfin tsiya.Suna ji suna gani aka tafi dashi ana jansa a kasa har aka isa tsakiyar kasuwa,anan aka bankare shi akayi masa KISAN GILLAH.Anan ne matar mutumin da yayan nasa sukayi ta rusa kuka kamar ba zasu daina ba amma babu wanda ya tausaya musu.Yarima Kamsus ne kadai ya tsaya a gabansu yana kallonsu cikin matukar tausayawa har yana zubar da hawaye.A lokacin ne uwar yaran ta dauke su suka kama hanya suka fice daga cikin birnin amma kafin su kule saida macen ta waigo ta kurawa Kamsus idanu ita dashi duk suna zubar da hawaye.Idanun wannan macen sune abinda yarima Kamsus yake ta kokarin ya tuno amma ya kasa.Lokacin da sarki Alkasim da Yarima Kamsus suka iso gaban karagar mulki suka tsaya suka fuskanci jama'a sai yarima yayu wuf ya yiwa sarki rada a kunne yace akwai matsala yakai Abbana,banga wadannan tagwayen ba biyu kuma lallai ya kamata mu san ko su waye su kafin a fita daga cikin birnin nan domin zasu iya zama daya daga cikin makiyanmu.Koda jin haka sai sarki yayi murmushi sannan yayiwa yarima rada a kunne yace to waishin wa kake tsoro ne tsakanin MUTUM DA ALJAN? SHIN SU YARIMA KAMSUS ZASU GANO WADANNAN TAGWAYE KAFIN A BAR BIRNIN MISRA? ME ZAI FARU A CIKIN WANNAN GAGARUMAR TAFIYA DA ZA'AYI ZUWA BIRNIN SIN? TSAKANIN SARKI MASARUL ANJANA DA SARKI ALKASIM WAYE ZAI FIFITA AKAN WANI? WACE CE ZATA ZAMO MASOYIYAR YARIMA KAMSUS? WADANNE ABUBUWAN AL'AJABI NE ZASU FARU A BIRNIN SARKI MASARUL ANJANA? Mu Hadu A MUTUM DA ALJAN Littafi Na Biyu (2) Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen Labari. Daga Mai Debe Muku Kewa A Koda Yaushe. Abdul'Aziz Sani Madakin Gini Suleiman Zidane Kd 09064179602 MUTUM DA ALJAN 1 By Abdul'aziz Sani M/Gini.txt Displaying MUTUM DA ALJAN 1 By Abdul'aziz Sani M/Gini.txt. ★MUTUM DA ALJAN★!!! Littafi Na Biyu (2). Part [A] . ★A-Haleefah Physicist★. LOKACIN DA YARIMA KAMSUS YAJI SARKI ALKASIM YAYI MASA wannan tambaya yace waishin me kake tsoro ne tsakanin MUTUM da ALJAN?Hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda yasan cewa ko kadan sarki bazai damu da batun wadannan tagwaye guda biyu ba.Shi kuwa ya san cewa dan hakin daka raina shike tsoka ne maka idanu.Duk da cewar Yarima Kamsus ya yarda da jarumtakarsu,karfin damtsensu da iya yakinsu gami da karfin sihirinsu na tsafi yasan cewa makiyi abin tsoro ne tunda baka san nasa shirin ba da kuma irin mugun tanadin daya dade yana yi a kanka.Hakan ne yasa yarima Kamsus ya kudiri niya a cikin ransa cewa lallai shi bazai yi sakaci ba wajen kula da rayuwarsa data mahaifin nasa kuma zai ci gaba da zuba ido har ya gano wadannan tagwaye biyu da kuma dalilin daya sa suka shigo cikin wannan tawaga wacce zata je birnin Dilhar don amsa gayyatar sarki Masarul Anjana.Sarki Alkasim ya fuskanci gaba dayan jama'ar dake cikin fadar cikin izza yana murmushi yace,yaku jama'ar birnin Misra,kuyi sani cewa yanzu ne zamu kama hanya mu durfafi birnin Dilhar don amsa gayyatar sarki Masarul Anjana ba don muna tsoronsa ba kamar yadda sauran sarakunan duniya ke tsoronsa kuma ba don muna neman wani abu ba a wajensa,domin mu mawadata ne sai domin mu nunawa duniya cewa karfinmu yakai kuma mun isa muyi gwagwarmaya da kowa walau MUTUM KO ALJAN.Koda sarki Alkasim yazo nan a zancensa sai fadar ta rude da shewa aka kama yiwa sarki Alkasim jinjina gami da kirari akayi ta kodashi yana ihu yana daga takobinsa sama.Shi kuwa yarima Kamsus adaidai wannan lokaci nutsuwa yayi ya kurawa gaba dayan abokan tafiyarsu idanu dake tsaitsaye a gabansu yana nazarin kowa daya bayan daya.Kwatsam sai ya hango wani JARUMI a cikin tsakiyar jama'ar ya sunkuyar da kansa kasa.Har tsawon lokaci wannan jarumi bai dago da kansa sama ba ya kallo kowa,koda ganin haka sai yarima kamsus ya baro inda sarki ke tsaye ya kutso cikin abokan tafiyar ya nufi inda wannan jarumi yake amma kafin ya isa daidai inda jarumin yake sai ya neme shi kasa da sama ya rasa tamkar wanda ya latsa layar zana.Al'amarin da yayi matukar girgiza yarima Kamsus kenan ya cigaba da dube dube a cikin dandazon jama'ar.Kwatsam kuma sai ya hango wannan macen tagwayen a can gefe daya,kafin ya isa inda take sai itama ta bace bat!Nanfa hankalin yarima ya sake dugunzuma ainun fiye da koyaushe don haka sai ya koma da sauri izuwa inda sarki ke tsaye ya tsaya a bayansa yana muzurai da kalle kallen kowace kusurwa don tabbatar da tsaro,ma'ana sai ya zamo mai tsaron sarki na musamman.Nan dai sarki Alkasim ya gama jawabi akan wannan gagarumar tafiya.Ba tare da bata wani lokaci ba aka janyo dawaka,rakuma da alfadarori dauke da guzuri kowa ya haye bisa abin hawansa.Sarki Alkasim tare da yarima Kamsus da dakarunsa na musamman suka tsaya a baya,jarumai,makada,mawaka,masu barkwanci da sauran masu baiwa iri iri sune suka wuce gaba.Nanfa wannan tawaga ta fice daga cikin birnin Misra duu...Kai kace gaba dayan mutanen duniya ne sukayi hijira saboda yawansu.Mata,yara da tsofaffi kuwa sai sukayi tsaitsaye a kofar gidajensu sunayi musu bankwana gami da fatan dawowa lafiya.Wasu ma saidai kaga suna kuka da bakin cikin rabuwa da iyalansu saboda sun san cewa basu da tabbacin isa birnin Sin a raye su dawo gida.Kafin cikar wadansu dakikai masu yawa wannan runduna tayi nisa ga barin cikin birnin Misra ta nausa izuwa cikin daji.Saida aka shafe sa'a bakwai ana ta kutsawa cikin daji ba tare da an fuskanci wata matsala ba,sannan sarki Alkasim ya bayar da umarnin a tsaya a yada zango domin a huta kuma a ci abinci.Nan take kuwa aka tsaya aka kafa tantuna.Ana cikin wannan aiki ne shugaban dakarun sarki Alkasim wanda ake kira da suna Uzaila bin Kaidas ya dubi gaba dayan abokan tafiyar yace yaku yan uwa kuyi sani cewa yarima ya bayar da umarnin cewa yana son duk sa'adda muka yada zango mu rabu izuwa kaso biyar,kaso na farko shine taron jarumai,saina mawaka,makada,barkwanci da kuma masu sauran abubuwan baiwa.Wanda duk yaki sanya kansa a cikin daya daga cikin wadannan rukunai zai fuskanci horo da bincike.Koda Uzaila yazo nan a jawabinsa sai sarki Alkasim ya kamu da farin ciki kuma yayi mamakin irin wannan hikima ta yarima saboda indai akayi hakan dole ne a gano makiyan da suke shigo cikin wannan AYARI. Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace maso abinka ya fika dabara.Ashe tun daga lokacin da sarki Alkasim ya bayar da umarnin a yada zango sai wadannan tagwaye guda biyu suka bace bat daga cikin ayarin su da dawakansu tamkar basu taba bayyana ba saboda karfin sihiri da tsafi.Bayan batan nasu ne suka bayyana a can baya kadan cikin wata duhuwa.Nan take suka sauko daga kan dawakansu suka zauna a kasa dirshan suna masu yin tagumi cikin alamun takaici da damuwa.Tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba sannan namijin yayi gyaran murya ya dubi macen yace yake NAMRITA yanzu yaya zamuyi kenan?Yarima Kamsus yana ta hanamu samun damar kashe mahaifinsa.In badon yana bashi kariya ba da tuni mun gama daukar fansar mahaifinmu.Wannan dabarar daya fito da ita a yanzu ta ware rukunai biyar a cikin ayarin wannan tafiya saita tona mana asiri,saidai mu hakura da batun cigaba da tafiya a cikinsu in yaso mu fara tunanin kai masa HARIN BAZATO.Koda jin wannan batu sai Namrita tayi kwafa cikin matsanancin bakin ciki tace ai idan anason asha zuma dole sai an kawar da uwarta.Kawai mu fara kashe Yarima tunda shine kadai yake hanamu cika babban burinmu.Sa'adda Jarumi Zaihas yaji wannan batu na 'yar'uwarsa Jaruma Namrita sai ya ★Abubakar Haleefah Physicist★ dubeta a fusace yana mai daka mata tsawa yace yanzu ashe har kin manta kenan da wasiyyar da mahaifiyarmu ta bar mana cewar kada mu kuskura mu ce zamu taba lafiyar 'da saboda kiyayyarmu akan ubansa.Burinmu shine kamar yadda ya maishemi marayu shima dan nasa ya zama maraya.Ki tuna cewa a lokacin da sarki Alkasim ya kashe mahaifinmu yarima Kamsus bai so hakan ba harma saida ya zubar da hawaye saboda tausayinmu.Ke da kanki kinga zubar hawayensa kamar yadda kika sha jaddada mini.Akan wane dalili yanzu zaki ce mu kashe yarima?Namrita najin wannan batu sai tayi tsaki tace aini idan bana son uwa dole ne naki yayanta.Bana son sarki Alkasim don haka babu yadda za'ayi nason jininsa.Na yarda cewa Kamsus bashi da wani laifi kuma tabbas ya tausaya mana a lokacin da aka zaluncemu aka kashe mana mahaifinmu,to amma ka tuna fa cewa yau shekara bakwai kenan muna baiwa kanmu horon yaki domin daukar wannan fansa kawai.a tsawon wadannan shekaru munyi yawo a duniya izuwa kasashe tara kuma munsha bakar wahala kafin mu sami sirrikan tsafin da muka samu tamkar zamu rasa rayukanmu.Shi kenan yanzu saboda mutum daya sai mu bari shirinmu na shekara bakwai ya tarwatse a banza? Ka sani cewa komai zanyi sai nayi shi muddin zan sami nasarar kashe sarki Alkasim koda kuwa zata kama cewa sai na kashe gaba dayan mutanen birnin Misra bawai yarima shi kadai ba.Lokacin da jaruma Namrita tazo nan a jawabinta sai hankalin dan uwanta Jarumi Zaihas ya dugunzuma yayi shiru yana nazari da tunani saboda yasan cewa tafi zafi kuma batayin magana biyu.Daga can sai ya dafa kafadunta da hannayensa biyu ya dubi cikin idanunta a lokacin da nasa idanun suka ciko da kwalla,yace yake yar uwata kin sani cewa a shirye nake na rasa rayuwata muddin wannan buri namu zai cika,amma ki sani cewa wannan sarki da muke son kashewa ba kanwar lasa bane,ba'a taba samun makiyin da ya sami nasara a kansa ba.Ansha kai masa hari sau ba adadi babu sa'a kuma komai yawan rundunar dakarun sumame basa iyawa dashi kadai,bare mu da muka kasance mu biyu rak.Ki tuna cewa duk shirinmu muna son mu kashe shine ta hanyar KISSA da SHAMMATA domin babu yadda za'ayi mu sami damar yin GABA DA GABA dashi.Ni a tawa shawarar shine mu jarraba kai masa harin bazato koda zai kai sau biyu ne ko sau uku.Idan ba muyi nasara ba sai mu fito muyi gaba da gaba dashi idan yaso ayi ta takare ko mu ko shi,tunda dai bamu san iyakar karfinsa da shirinsa ba shima kuma bai san namu ba.Sa'adda Zaihas yazo nan a jawabinsa sai jikin Namrita yayi dan sanyi ta sunkuyar da kanta kasa daga can kuma sai ta dago kan ta dubeshi a cikin murmushi tace yau dai a karon farko kayi galaba a kaina na amince da wannan shawara taka amma lallai ka hanzarta tunanin irin harin da zamu fara kaiwa Sarki Alkasim da kuma lokacin da zamu kai harin sannan ka tabbatar da cewar ba zamuyi kuskure ba kuma babu ta yadda zai iya tsallake sharrinmu.Dajin haka sai murna ta kamu Zaihas ya rungume Namrita yana mai cewa lallai a cikin wannan dare na yau zamu kai masa wannan hari kuma ina mai tabbatar miki da cewa babu yadda zaiyi ya iya tsira da rayuwarsa.Koda jin haka sai itama Namrita ta kamu da tsananin farin ciki.Wannan shine abinda ya faru tsakanin Jaruma Namrita da dan'uwanta jarumi Zaihas tagwayen da suke shafe shekara bakwai suna tarkon Sarki Alkasim domin daukar fansar ran mahaifinsu. *A Can Sansanin Su Sarki Alkasim Kuwa Kamar Yadda Yarima Kamsus ya bayar da umarni haka al'amarin ya kasance wato saida aka raba gaba dayan abokan tafiyar izuwa rukuni biyar,dakarun sarki da hadimansa ne kadai ba'a tarwatsa su ba ya zamana cewa duk suna cikin harabar da tantin sarki yake.Nan take aka sa dakaru suka kewaye sansanin gaba dayansa don tabbatar da tsaro.Kai bama sansanin ba har gaba da bayan dajin kimanin tafiyar zango ashirin-ashirn saida aka baza dakarun leken asiri kwararo domin su lura da dukkan mostin wani abu mai rai wanda ka iya kawo harin bazato.Bayan an gama dukkan wannan shiri ne sai Yarima Kamsus ya fara shigowa cikin rukunan biyar daya bayan daya yana karewa abokan tafiyar kallo.Bayan ya gama duba kowa ne rukuni sai kansa ya daure ya kamu da tsananin mamaki domin baiga tagwayen nan ba kuma duk binciken da yayi babu wanda ma ya taba ganinsa a cikin wannan tawaga bare yaga sa'adda suka sulale suka gudu.Babu takun sawayensu kona dawakansu.Wannan ce tasa yarima Kamsus yaji a jikinsa cewa lallai wadannan bakin tagwaye ba karamin shiri ne dasu ba don haka sun tabbata abin tsoro duk da cewa kuwa shi sarki baya shakkar kowa.Shi dai Yarima Kamsus a koda yaushe a cikin zuciyarsa baya raina makiyi,sannan kuma duk irin baiwar da yake da ita ta jarumtaka,sa'a da kuma karfin damtse dana sihiri yana sawa a cikin ransa cewa za'a iya samun mahalukin da yafishi duk wadannan abubuwa sabanin sarki Alkasim wanda shi gani yake kamar ma in duk duniya zasu taru a kansa shi kadai baza'a iya samun nasara a kansa ba.Sarki Alkasim na zaune cikin tantinsa bisa shimfidarsa ta alfarma,kuyangi na shayar dashi giya kuma suna ciyar dashi abinci sai nishadinsa yake tayi kawai tamkar babu wani abu dake damunsa a duniya.Kwatsam sai ga Yarima Kamsus ya shigo cikin tantin.Koda ganinsa sai kuyangin suka watse suka fice daga cikin tantin suka barsu su biyu rak.Nan take Yarima Kamsus ya zauna daf da sarki Alkasim suka fuskanci juna sannan ya dubeshi a cikin nutsuwa gami da gyaran murya yace yakai Abbana yanzu a iya tunaninka akwai ABOKAN GABArka wadanda zasu iya bin bayanka a cikin wannan tafiya namu?Koda jin wannan tambaya sai Sarki Alkasim yayi shiru kuma ya daga kansa sama yana tunani har izuwa. ★MUTUM DA ALJAN★!!! Littafi Na Biyu (2) Part B . ★A-Haleefah Physicist★. KUMA YA DAGA KANSA YANA TUNANI har izuwa tsawon yan dakiku daga can sai ya dubi Yarima yayi murmushi yace yakai dana kayi sani cewa sama da shekaru goma baya na firgita gaba dayan makiyana ya zamana cewa sun razana dani ainun.Da yawansu na turmushe su na kau dasu daga doron kasa,wasunsu kuwa hijira sukayi suka bar kasashen su,suka bazama izuwa sassan duniya nesa da inda nake.Ina mai tabbatar maka da cewa na kashe sama da sarakai arba'in a wannan lokaci,don haka ina da tabbacin cewa babu sauran irin makiyana a wannan nahiya tamu gaba daya.Lokacin da sarki Alkasim yazo nan a zancensa sai ya bushe da dariyar mugunta yace haba yakai dana wai shin me kake shakka ne har yanzu?Yanzu kai a tunaninka har akwai wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda zaiyi gangancin farautar rayuwata alhalin yasan cewa nine GUGUWAR ANNOBA mai baje birane kuma nine KOGIN JINI mai shanye ALKARYA.Sa'adda yarima Kamsus yaji wannan batu na mahaifinsa sai yayi ajiyar zuciya yace yakai Abbana ka yi sani cewa wannan duniya tana da fadi,haka kuma abubuwan cikinta yawa garesu kuma komai nisan gari akwai wani a gabansa.Tabbas na yarda cewa kai ZARTO ne abin tsoro kuma kai tauraro ne wanda ya haska duniya amma ka sani cewa ZAMANI RIGA CE.Dole ne mai laya ya kiyayi MAI ZAMANI.Kullum shekarunka tafiya sukeyi kuma kullum ana samun sauyin al'amara na cigaba.A halin yanzu a iya binciken da nayi na gano cewa akwai makiyanka a cikin wannan tawaga tamu,amma gashi ni da kai da dukkan dakarunmu mun kasa gano ko su waye wadannan makiya.Asalima mun kasa ganinsu a zahiri.Shin ba zaka iya tuno da makiyanka na karshe ba wadanda baka sami nasarar kawar dasu ba ko kuma akwai wadanda kake zargin cewa nan gaba zasu iya zama makiyanka?Koda sarki Alkasim yaji wannan tambaya sai yayi shiru kuma ya nutsu sosai,nan take ya fada cikin kogin tunani bisa abinda ya faru a baya.Bayan ya gama tunanin ne ya dubi yarima Kamsus yace shin zaka iya tunowa da al'amarin daya faru a birninmu kimanin shekaru bakwai baya sa'adda baka fi shekara goma sha daya ba a duniya?Koda jin wannan tambaya sai zuciyar yarima Kamsus ta buga da karfi.Sarki Alkasim ya cigaba da cewa akwai watarana da wani bakon boka ya sauka a birnin ya gurbata ruwan shanmu,na kafa doka mai tsauri akan duk mutumin daya sake bata mana ruwan sha Hukuncin kisa ne a kansa.Bayan shekara guda da faruwar al'amarin ne wani bakon bafatake tare da matarsa da 'ya'yansa guda biyu tagwaye suka zo suka sake gurbata mana wannan ruwan sha namu.Koda aka gurfanar dasu a gabana sai nan take na yankewa mutumin hukuncin kisa ba tare da nayi bincike naji dalilin laifinsa ba.Wannan shine kuskure na guda daya jal a rayuwata wanda har kwanan gobe nake yin nadamar aikatashi saboda nayi amfani da karfin mulkina ne don tsorata masu kawo wargi na tafka zalunci saboda wannan bakon bafatake ba'a kan laifi na hukunta shi ba.Yayi laifin ne bisa tsautsayi da rashin sani.A iya tunani yayan wannan bafatake zasu iya girma su zama abokan gabata tunda a gaban idanunsu nasa aka kashe mahaifin nasu suna kuka da ihu suna rokona gafara.Bazan taba mantawa ba a sannan saida kai ma ka roke ni akan nayiwa mahaifin nasu afuwa.Koda sarki Alkasim yazo daidai nan a labarinsa sai nan take yarima Kamsus ya tuno da lokacin da Jaruma Namrita ta waigo tana kallonsa,sa'adda mahaifiyarsu ta janyesu ita da dan uwanta lokacin da suke ficewa daga cikin birnin misra.Nan take Kamsus ya gane cewa wadannan idanu daya gani a shekaru bakwai baya sune ya sake gani a yanzu akan fuskar wannan macen tagwayen.Kawai sai hawaye ya zubowa yarima Kamsus ya dubi sarki Alkasim cikin alamun karayar zuciya yace tabbas wadanann yayan bafatake sune ke biye damu a cikin wannan tafiya tamu domin su dauki fansa a kanka kuma ina ji a jikina cewa suna nan a kusa kuma a koyaushe zasu iya kawo harin bazato.Koda jin wannan batu sai sarki Alkasim ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya ta mugunta.Al'amarin daya firgita gaba dayan jama'ar dake sansanin kenan har shugaban dakaru da sauran yaransa suka rugo da gudu izuwa gaban tantin sarki.Koda ganin haka sai sarki ya mike tsaye ya fito daga cikin tantin ya dubi shugaban dakaru Uzaila bin Kaidas yace dashi maza ka janye gaba dayan yaranka daga cikin sansanin nan da wajensa bana bukatar daya daga cikinku ya sake bani tsaro har sai na sake bukatarku da kaina.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma musamman na yarima Kamsus don haka sai ya dubi sarki cikin alamun matukar kaduwa gami da firgici yace haba ya Abbana ai wannan ba karamin ganganci bane kayi tamkar ka siyar da rayuwarka ne ga makiyanka.Sarki Alkasim ya dafa kafadar yarima yana maiyin murmushi a gareshi yace yau ne zan nuna maka cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane,kuma ni MURUCIN KAN DUTSE ne ban fito ba saida na shirya.Karo dani sai DUBU TA TARU.Wadannan tagwaye guda biyu na dade da saninsu kuma nasan da zuwansu kasata a wannan lokaci.Macen Sunanta Namrita shi kuma namijin sunansa Zaihas.Saida suka shekara bakwai suna yawo a duniya suna ziyartar manyan bokaye da manyan jarumai suna koyon fada,yaki da tsafi ba don komai ba sai domin su sami nasarar daukar fansa a kaina.A yanzu haka suna can gaba kadan cikin wani daji mai DUHUWA wanda ake kira SURFAL wanda tazararmu dashi bata wuce zira'i arba'in ba.A yau din nan idan dare ya raba zasu kawo mini harin bazato domin su hallaka ni don haka nake son kowa ya kauce daga kan hanyarsu banda yarima domin mu biyu ne kacal zamu iya tsira daga sharrinsu.Sa'adda sarki Alkasim yazo nan a... ★Abubakar Haleefah Physicist★ Jawabinsa sai Uzaila ya risina yace an gama ya shugabana.Nan take shugaban dakaru Uzaila ya tattaro gaba dayan dakarun sarki ya tafi dasu izuwa can gaban sansanin suka kafa nasu sansanin.Suma ragowar gaba dayan abokan tafiyar sai suka bi su Uzaila ya zamana cewa saura sarki da yarima Kamsus kadai a cikin sansanin suna kallon juna.Shidai Yarima Kamsus tsananin mamaki ne yasashi yayi shiru kawai yana mai kurawa sarki Idanu domin ya firgita da al'amarinsa,bai taba zaton cewa yasan komai ba haka akan wadannan makiya nasu.Kawai sai sarki ya dubi Yarima yace kai kuma me ka tsaya kake jira!Ai sai kabi sauran jama'ar kaima so nake a barni ni kadai.Koda jin haka sai Yarima Kamsus yayi wuf ya durkusa bisa guiwoyinsa ya kama kafar sarki yace ina mai rokonka daka barni naga yadda zata wakana tsakaninka da wadannan abokan gaba.Koda jin haka sai sarki yayi shiru yana tunani sannan yace shi kenan na amince zan barka ka tsaya tare dani amma bisa sharadi biyu.Kada ka tayani yakar wadannan makiya nawa kuma kada ka karesu.Sa'adda Yarima Kamsus yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun amma saiya kudurce a cikin ransa cewa saiya zartar da abinda ke cikin ransa koda ransa zai baci daga baya don haka sai ya dubi sarki cikin murmushi yace na amince da wannan sharadi naka.Lokacin da dare ya raba sai dajin gaba daya yayi tsit,ba'a jin sautin komai face na kadawar iska gami da kukan kananan kwari da tsuntsaye.A wannan lokaci tuni sarki Alkasim ya dade da fara yin bacci harda munshari abinsa,shi kuwa Yarima Kamsus yana zaune a gefe daya cikin tantin ya kurawa sarki Idanu kawai yana mamakinsa yana mai cewa a cikin ransa waishin sarki wane irin hatsabibin mutum ne shi haka?Yaya shi da yasan cewa za'a zo kashe a cikin wannan dare amma kuma saiya kwanta ya kama bacci abinsa ba tare da fargabar komai ba?Gama fadin hakan keda wuya sai kawai yaji saman tantin nasu ya dare gida biyu.Kafin ya daga kansa sama yaga abinda ke shirin faruwa tuni Jaruma Namrita da Jarumi Zaihas sun duro cikin tantin sun kaiwa sarki Alkasim suka a ciki da takubbansu.Cikin bakin zafin nama sarki Alkasim ya doki kasa da tafin hannayensa yayi sama tamkar da majajjawa aka janyeshi,sai takubban nasu suka soke a cikin kasa suka lume.Kafin su zaro takubban tuni sarki ya tale kafafunsa a sama ya doki kirazansu.Duk da karfin dukan kirjin nasu da yayi basu fadi kasa ba amma saida sukayi baya,nanfa aka kacame da azababben yaki mai tsananin ban tsoro da al'ajabi.Duk wannan abu dake faruwa Yarima Kamsus na zaune a inda yake ko motsawa baiyi ba kawai ya zubawa JARUMAN UKU idanu yana kallon masifaffen yakin da sukeyi na ban al'ajabi da ban tsoro.Saida aka shafe kusan rabin sa'a anayin wannan BAKIN ARTABU ba tare da tagwayen biyu sun sami nasarar koda kwarzanar jikin sarki Alkasim ba kuma tunda ka fara gumurzun sarki Alkasim bai mayar da martani ba kawai kare kansa yakeyi fuskarsa cike da murmushi tamkar wasa yakeyi ba yaki ba.Ashe so yake kawai ya fahimci iyakar jarumtakar wadannan tagwaye.Koda yaga tagwayen biyu sun kasa yi masa komai saiya daka tsalle sama ya luluka sama yana katantanwa tamkar an murza dan mazari,shi kansa yarima Kamsus bai taba ganin irin wannan jarumtaka ba don haka bai san sa'adda ya daga kansa sama ba yana kallon IKON ALLAH.Suma tagwayen biyu haka suka daga kawunansu sama suna mamaki.Koda sukaga sarki Alkasim ya cigaba da lulukawa sama yana neman kulewa a cikin gajimare sai suka dubi junansu nan take sukayi amfani da karfin sihirinsu na tsafi suma suka tashi sama kamar tsuntsaye suka bi bayan sarki Alkasim da nufin su cimmasa.Kwatsam ba zato ba tsammani sai ganin sarki Alkasim sukayi daf dasu tamkar zukoshi akayi.Kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni sarki Alkasim ya gabza musu wawan naushi akan kirazansu saboda karfin naushin sai suka rikito kasa suna aman jini duk su biyun suka fado kasa tim suka baje a cikin wani irin mugun hali mai kama da suma sun jirkitar hankali.Kawai sai sarki Alkasim ya nufosu daga saman yana mai saito cikin kowannensu da tsanin makami zai soke su.Koda Yarima Kamsus ya kyallara idanu yayi arba da fuskar macen tagwayen a wannan lokaci yaga irin tsananin kyawun da Allah ya bata wanda bai taba ganin irinsa ba kuma yaga cewa tabbas sarki kasheta zaiyi kuma ya kashe dan uwanta sai ya zabura cikin bakin zafin nama ya janyesu daga inda suke kwance tamkar shaho

Chapter 2 of 9