Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
a cikin wani ayari take na fatake? Amsar da alkasim ya kasa baiwa kansa kenan haka dai alkasim yayi ta wannan hasashe da zulumi a cikin zuciyarsa har ya dawo cikin birnin misra da shigarsa cikin gidan sarautar sai ya wuce kai tsaye izuwa fadar sarki inda ya zube gabansa ya kwashi gaisuwa guyson sunana ko kuce Al amin Ahmed Dan misau Daga zauran labarai shikuwa sarki sai ya dubeshi cikin alamun matukar mamaki yace yakai dana abin alfaharina ya kai dodon maza zaki uban dawa kuma guguwa mai baje birane yau kuma me ya faru naga ka dawo daga farauta babu komai a tare dakai shin babu sauran dabbobine a cikin dajin namu ko kuwa ka fasa yin farautar ne ka juyo da baya? Lokacin da yarima Alkasim yaji wadannan tambayoyi guda biyu sai yayi ajiyar numfashi cikin alamun karayar zuciya nan take ya kwashe labarin duk da ya faru tsakaninsa da wannan bakuwar jaruma ya zayyane masa koda jin wannan labari sai sarki ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya yana mai tsananin farin ciki tamkar wanda aka yiwa albishir babba Al amarin da yayi matukar baiwa kowa mamaki kenan daga can sai sarki ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin dariyar sannan ya dubi yarima alkasim cikin murmushi yace wannan bakuwar jaruma itace matar da zaka aura har ka samu haihuwa da ita toh Guyson nake magana gobe ka sake yin shiri ka tafi daji ba don kayi farautar dabba ba sai domin farautar wannan mata taka duk wahalar da zaka sha da duk irin wulakancin da zaka fuskanta ka juresa yayin da alkasim yaji wannan batu sai shima fuskarsa ta fadada da murmushi ya mike tsaye ya dafa kirjinsa da hannu guda ya dubi sarki cikin dakakkiyar zuciya yace yakai abbana idan har na cika jininka nayi maka alkawari cewar duk irin gabar da zamu yi da wannan jaruma sai na siye zuciyarta ta kaunaceni'' typing by me Al amin Ahmed Guyson daga zauran labarai koda jin haka sai sarki ya sake kamuwa da matukar farin ciki ya mike tsaye daga kan karagarsa ya rungume alkasim yana mai cewa ina alfahari dakai yakai dana nasan zaka iya har dare ya raba alkasim bai rintsa ba domin da zarar ya rufe idanunsa baya ganin komai face fuskar wannan bakuwar jaruma a yinin gaba daya ka kasa ci da shan komai ko a zaune ko a tsaye sai yayi ta tuno da abubuwan da suka faru a tsakaninsa da bakuwar jarumar a daji dakyar dai alkasim ya samu yayi dan barcin amma alfijir na ketowa ya farka nan take yasa kuyangi suka shirya masa ruwan wanka da abincinsa na kalaci ya kimtsa kafin gari ya soma haske tuni ya gama shirin tafiya farauta ba tare da bata wani lokaci ba yarima ya hau dokinsa ya fice daga cikin gidan sarautar ya nausa izuwa cikin wannan daji wanda ya hadu da bakuwar jaruma a cikinsa jiya alkasim yaci gaba da nausawa cikin dajin yana ta dube dube da waige waige kai wani lokacin har saukowa yake daga kan dokinsa yana duba kasa ko zaiga sahul bil adama amma ko alamarsa bai gani ba sai da ya shafe sa a biyu da rabi yana ta kai kawo a cikin dajin banda dabbobi da tsuntsayebabu abinda yake gani da yake wannan karon ba tasu yake ba sai dai su wuce ya wuce abinsa babu mai tankawa wani hakanne yasa alkasim yaji ya kosa kuma zuciyarsa ta fara karaya da saran cewa zai sake haduwa da wannan bakuwar jaruma duk da mahaifinsa ya gaya masa cewa itace matar da zata zamo abokiyar rayuwarsa lokacin da rana ta kwale sai alkasim ya nufi wata katuwar bishiya mai yawan ganyaye domin yaje ya zauna a karkashinta ya huta da isarsa bakin bishiyar sai ya sauka daga kan dokin ya daure dokin a jikin bishiyar sannan ya zauna a lokacin da wata irin iska mai dadin sanyi ta fara kadawa hakan ne yasa ya kishingida yana mai jingina gadon bayansa a jikin bishiyar saboda gajiyar dake jikinsa sai kawai ya fara yin gyangyadi faruwar hakan keda wuya sai yaji wani abu na yawo a jikinsa tun daga kan kafafunsa a firgice alkasim ya yunkura domin zare takobinsa amma sai yaji an kanannade jikinsa gaba daya kafin yayi wani yunkuri tuni wannan bishiya ta dare saiga wata kofa ta bayyana nan take wata iska mai karfi ta fito daga cikin kofar ta zuke alkasim a lokacin da yaji wata irin kasala ta shigeshi yadda ko hannunsa ba zai iya motsawa ba ashe wata murtukekiyar macijiyace ta kanannade shi gaba dayan jikinsa kawai sai gani yayi an fyadashi da kasa a tsakiyar wata kasaitacciyar fada. Fadar ta kawatu ainun da kayan kyale kyale kai kace fadar birnin misra, Al amin Ahmed Guyson sunana' koda alkasim ya dago kansa cikin matukar karfin hali sai yaga ashe babu kowa a cikin fadar face mutum daya jal kuma ba kowa bane face wannan bakuwar jaruma ita kadai zaune aakan wata katuwar karagar mulki taci ado irin na 'ya 'yan sarakai. Koda yarima Alkasim yaga jarumar a cikin wannan hali sai ya kidime yaji ya kara kamuwa da tsananin sonta fiye da ko yaushe.. Don haka sai ya kura mata idanu yana murmushi ita kuwa saita murtuke fuskarta ta dubeshi a fusace tace mazaka bani amsar tambayar da zanyi maka yanzu in ba haka ba kuwa zan gana maka azabar da ba a taba yi maka irin taba koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace '' ina sauraronki me kike so kiji'' , kuma a nanne MUTUM DA ALJAN littafi na HUDU (4) Yazo karshe marubucin yace:- SHIN ME ZAI FARU A CIKIN TAFIYAR YARIMA ALKASIM DA JARUMA LUSLAIYA? . KAFIN SU KAMMALA GASARSU HAR TA KAMU DA SONSA SUYI AURE KUMA MENENE SANADIN AJALINTA? . IDAN AKA ISA GARIN SARKI MASARUL ANJANA ME ZAI FARU TSAKANIN GIMBIYA ZULFULAIFA DA YARIMA KAMSUS KUMA MAI ZAI FARU A TSAKANIN SARKI ALKASIM DA SARKI MASARUL ANJANA? . INA LABARIN JARUMI ZAIHAS DA YAR'UWARSA? . SHIN ZASU SAMU NASARAR DAUKAR FANSA A KAN SARKI ALKASIM? . mu hadu a littafi na Biyar domin jin cigaban wannan labari. Mutum Da Aljan Littafi Na Biyar (5) Part A. Ku ziyarci Shafin www.rumbunlabarai.com domin samun littattafai masu daɗi da debe kewa JARUMAR TA MIKE TSAYE DAGA KAN KARAGAR MULKIN, ta tako kafafunta tazo har daf da alkasim ta tsugunna fuskarrta na kallon tasa yadda har suna iya jin numfashin juna sannan ta dubeshi fuskarta a daure ta dubeshi fuskarta a daure tace wnene kai kuma me kake takama dashi har da zakayi kokarin zaluntata ka rabani da abinda na farauto a daji alhalin hannuna ya riga naka kaiwa kan dabbar? Sa adda yarima alkasim yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace bazan baki amsar wannan tambaya ba sai kin fara gabatar da kanki tukunna nasan ko ke wacece. Koda jin haka sai jarumar ta fusata ta mike tsaye zumbur ta koma da sauri zuwa kan karagarta ta zauna zamanta keda wuya sai ta yi nuni da hannunta zuwa kan alkasim take wannan murtukekiyar macijiya data kanannadeshi ta sauka daga jikinsa amma sai wadansu sarkokin karfe suka fito daka cikin bango kimanin guda dubu suka kanannadeshi har kansa suka janyeshi zuwa jikin bangon suka shiga matseshi yarima alkasim bai san sa adda ya fara kurma ihu da kururuwa ba sakamakon tsananin zafi da zugin da yake ji koda ganin haka sai jarumar ta fara kyalkyala dariyar mugunta tana cikin yin dariyar ne kwatsam taji alkasim ya daina yin ihu da kururuwan kuma nan take sarkokin suka karkatse suka zube kasa gutsungutsun sai gani tayi Alkasim ya baro jikin bangon ya durfafota yana tafiya da karfinsa tamkar wani abu bai taba samunsa ba Manya gatan wasa kenan sarki Alkasim. Cikin tsananin kaduwa da mamaki jarumar ta mike tsaye tana kallonsa kawai alkasim ya iso har daf da ita yadda suna iya jin numfashin juna kamar yadda tayi masa dazu ya dubeta cikin murmushi yace duk abinda kike takama dashi nima ina da irinsa ko ma wanda ya fishi akan wane dalili zaki dauki girman kai a gareni alhalin nine yakamata na zamo mai girman kai a gareki tun da na kasance da ga sarkin dake mulkin wannan kasa da kike cikinta. Koda jin wannan batu sai jarumar tayi murmushi sannan tace dama saboda kai nazo wannan kasa abinda yasa banje fada kai tsaye ba shine ina son na gabatar da abinda nazo yi a sirrance ya kasance a tsakaninmu ne kawai mu biyu sunana LUSLAIYA YA GA SARKIN MAFARAUTA NA BIRNIN TEHERAN tun ban fi shekara takwas ba a duniya mahaifina ya bani horon yaki wanda ina iya fuskantar zaratan mayaka guda dubu sannan ya bani horon gumurzu da manyan dabbobin daji baya ga hakan ya bani horon rayuwa a cikin daji gami da yin gudu na tsawon kwanaki tara ba tare da tsayawa ba sama da dakika arba in ba bugu da kari mahaifina ya tsumani a cikin tsumin tsafi irin wanda samun mai irinsa sai an tona lokacinda na samu shekaru goma sha takwas ina samun wannan horo ya zamana cewa na zama budurwa cikakkiya sai na kawai da dukkan yan fashin dake cikin dazuzzukan kasarmu ni kadai hakanne yasa yan fashin suka fusata suka nemo taimakon yan uwansu dake cikin kasashen ketare amma duk da hakan sai na zame musu alakakai na zamo tamkar shaidaniya a cikin bil adama akwai wata ranar da wadannnan yan fashi suka ritsani a daji adadinsu yakai miliyan shida amma ni kadai na kashe mutum miliyan uku da rabi daga cikinsu sauran suka tsere daga wannan rana ne na dinga jin kamar babu wani mayaki ko sadaukin da yafi ni jarumtaka amma sai mahaifina ya dubeni yace yake yata kada ki kuskura ki dorawa kanki girman kai bisa wannan jarumtaka da kika ga kin samu a halin yanzu ina mai tabbatar miki da cewa akwai wani dan sarki wanda karfinsa da jarumtakarsa har da karfin sihirinsa zasu iya zuwa dai dai da naki koma yafiki koda jin wannan batu saina kamu da tsananin mamaki na tuna irin karfiin da nake dashi amma ace wai har akwai wanda ya kaini koma ya fini bisa wannan daliline na yanke hukuncin nazo na hadu dakai domin muyi gasa guda mu banbance tsakanin aya da tsakuwa gasa ta farko itace gudun tseren da zamuyi tsawon kwana tara ba tare da tsayawa ba ta sama da dakika arba in ba gasa ta biyu itace akwai wani babban gari na arnan daji dake can kudancinmu na taheran ina son mu je mu sato gunkin da suke bautawa domin mu tsokano yaki dasu wadannan arnan daji suna da mugun yawanda ba asan iyakar adadinsuba ni dakai dai zamu yakesu domin mu tantance iyakar jarumtakarmu gasa ta uku wacce itace ta karshe zamu shiga daji kowannanmu yayi farautar dabbar da babu kamarta ya kasheta yazo da gawarta idan har dabbar da na kashe tafi taka hadari ka tabbata cewa nafika karfi da jarumtaka kenan Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai page nake typing nan take zamu rabu na koma kasata cikin farin cikin cewa nafi ka komai yayinda jaruma luslaiiya tazo nan a zancenta sai hankalin alkasizancenta sai hankalin alkasim ya dugunzuma ainun saboda zuciyarsa ta karaya akan wannan abu guda uku amma daya tuna cewa shifa mutum ne mai sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa sai yaji dukkan tsoro ya kau daga cikin ransa don haka bai san sa adda ya dubi jaruma luslaiya ba yace na yarda da duk wannan sharadi na gasar da kika shirya mana kuma saina tabbatar miki da cewa nafiki karfi da jarum taka wow nima Guyson saina tabbatar muku da cewa jarumi ne ni. Yanzu idan na lashe wannan gasa menene sakammenene sakamakona? Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya kama luslaiya tace inda dai ace kai ba dan sarki bane toda saina baka dukiyar da har ka mutu kai da danginka ba zaka yi talauci ba amma ai mahaifinka yafi mahaifina dukiya yanzu ban san dame zan iya biyanka ba koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace ai kuwa kece kike da abin da zaki iya biyana yake jarumar jarumai kuma tauraruwar taurari ba komai nake so a wajanki ba face soyayyarki da aurenki idan har na lashe wannan gasa akanki to na siyi soyayyata kenan kuma babu abinda zai hana aurenmu koda jin wannan batu sai jaruma luslaiya taji zuciyarta tayi baki kirin kuma nan take taji ta tsani yarima alkasim fiye da komai a duniya saboda tunanin cewa ya na so yayi mata dole ta soshi kuma ta aureshi cikin tsananin fushi ta dubeshi tace nayi maka alkawari zaka sha bakar wahala da baka taba sha ba a rayuwarka a cikin wannan gasa wacce zata kaika ga rasa lafiyarka ko rayuwarka gaba daya kuma ina tabbatar maka da cewa baka da jarumtakar da zata iya burgeni har zuciyata ta kamu da sonka don haka duk yadda zanyi naga ka fadi wannan gasa sai nayi ya kasance ne ne na lashe gasar ka sani cewa babu hada kai a cikin wannan gasa ni dakai sai dai kowa tasa ta fishsheshi kuma kowannanmu zai iya shiryawa dan uwansa tarkon mugunta domin ya hallaka iana son mu zamo tamkar abokan gaba masu farautar rayukagaba masu farautar rayukan juna lokacin da sarki alkasim yazo dai dai nan a labarin da yake baiwa yarima kamsus sai yaga idanun yarima sun ciko da kwalla kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tari numfashinsa yaana mai cewa daka ta yakai abbana yanzu kana bani labarin wata jaruma a matsayin itace mahaifiyata to ita kuma junaina wadda na taso nake ganinta a matsayin uwata wacece ita?? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki Alkasim yayi shiru kamar ba zaice komai ba daga can ya dago kai ya dubeshi cikin rawar murya yace yakai dana kayi hakuri zakaji amsawar wannan tambaya da kayi min a karshen wannan labari da nake baka kafin mu isa birnin masarul anjana Tabbas zaka tantance a tsakanin mahaifiyarka junaina da kuma mahaifiyarka jaruma luslaiya zaka san matsayin kowacce a wajenka koda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai zuciyarsa ta karaya ya fashe da matsanancin kuka al amarin da ya dugunzuma hankalin yarima kamsus kenan ya shiga rarrashin sarki a lokacin da yaji ya kamu da tsananin tausayin mahaifin nasa sarki Alkasim da kyar ya shawo kansa ya daina kukan sannan yarima kamsus ya dubeshi cikin zakuwa yace na rokeka dakaci gaba da bani wannan labari domin naji yadda karshen gasarkdomin naji yadda karshen gasarku da jaruma luslaiya zata kasance sannan kuna na gane banbancin dake tsakanin luslaiya da mahaifiyata junaina Al amin Ahmed Dan misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai nake magana tayaya zan karbi luslaiya a matsayin uwa ta alhalin ban san wata uwa ba face junaina gama fadin haka keda wuya sai hawaye ya kwararo bisa kumatun yarima kamsus take shima sarki alkasim yaji ya kamu da matukar tausayinsa don haka sai ya rungumeshi akan kirjinsa sannan yaci gaba da bashi labari yana mai cewa..... . LOKACIN DA NAJI ABINDA LUSLAIYA ta fadi cewar a cikin wannan gasa zamu zamo tamkar abokan gaba kuma zamu rinka shiryawa juna tarkon muguntar da zan iya hallaka sai hankalina ya tashi saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko shine na kamu da tsananin sonta dalilina biyu kuwa bazan iya shirya mata mugunta da zata hallaka ba nan take zuciyata ta gamsu cewar lallai zan sha bakar wahala a cikin wannan gasa musamman da na tuna cewa inda zamu je mu gabatar da wannan gasa acanne nahiyar su jaruma luslaiya don haka ban san sirrikan dazuzzukan dake can ba. Yayin da luslaiya taga na sunkuyar da kaina kasa ina tunani da nazari saita kyalkyale da dariyar mugunta sannan ta hade fuska tace yaro bai san wuta ba saiya taka ta yanzu saika tashi ka koma gida ka sanar da iyayenka duk abinda ya faru a tsakaninmu domin kayi musu sallama ka dawo mu tafi ka sani cewa tun daga nan gasar mu zata fara don haka kayi amfani da damarka ta kowa a gidansa sarkine duk yadda zakayi ka tabbatar kaga bayana kafin mu bar nahiyarku dajin wannan batu sai yarima Alkasim yayi murmushi ya mike tsaye ya juya mata baya har yayi taku uku gaba zai yi tafiyarsa sai ta kira sunansa ya waigo ya dubeta cikin mamaki ita kuma sai tace da sassafe zaka fito gobe ka sameni anan wurin idan ka baata min lokacin zanyi tafiyata sai kayi da gaske zaka riskeni alkasim yayi murmushi yace babu matsala zanzo akan lokaci yana gama fadin hakan sai ya juya yayi tafiyarsa har yarima alkasim ya isa gida jikinsa a sanyaye yake kuma hankalinsa a tashe yake domin guiwarsa tayi sanyi ainun bisa wannan gagarumar gasa dake gabansa da isar yarima Alkasim a lokacin da magariba ta gabato sai ya nufi kai Tsaye bisa mamaki sai ya hango kofar dakinsa a bude al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan domin babu wanda yake da ikon shiga dakinsa ba tare da izininsa ba face mutum biyu daga sarki sai mahaifiyarsa a fusace yarima Alkasim ya kunna kai da sauri cikin turakar tasa da nufin yaci mutuncin wanda ya bude ya shiga koda yayi arba da wanda ke zaune a cikin dakin sai zuciyarsa ta buga da karfi ba wani bane ba face mahaifiyarsa tana zaune bisa shimfidarsa kanta a sunkuye hawaye na diga daga idanunta cikin firgici ya karasa gareta da sauri ya durkusa a gabanta ya rike hannayanta biyu yana dubanta cikin tsananin damuwa yace yake ummina ina dalilin zubar wannan hawaye daga cikin idanunki sa adda taji wannan tambaya sai tasa hannunta na dama ta share hawayan nata sannan ta janyo yarima izuwa jikinta ta rungumeshi akan kirjinta tace ya kai dana yau shekara talatin da kadan kenan ina tare dakai bamu taba rabuwa ba amma yau sarki ya tabbatar min da cewa a wannan karon zaka nisanta dani kuma zaka yi wata tafiya mai hadari wacce zama ka iya rasa rayuwarka koda jin haka sai yarima alkasim yayi murmushi cikin nutsuwa yace haba yake ummina akan wane dalili zaki damu kanki alhalin kin san duk ahalin gidan nan yana da sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa ke da bakinki kin sha bani labarin irin gwagwarmayar da sarki yayi a rayuwarsa tamkar ba zai tsira da rayuwarsa ba wai shin ma me yasa kika shigo cikin turakata kika zauna kina ta kuka? Shin yanzu kina nufin ki ce dake za ayi wannan muguwar tafiya ne? Nayi murna da ganinki a yanzu domin dama akwai wani abu daya shige min duhu ina son kiyi min cikakken bayani kada ki boye min komai taji zuciyarta ta buga da karfi tsoro ya shigeta ta fara zargin anya kuwa sarki bai sanar dani sirrin da suka boye ba tsawon shekaru cikin karfin hali na budi baki nace yake umma ina sonki sanar dani matsayina kafin yarima alkasim ya karasa fadin abin dake bakinsa sai yaji motsi a bayansa don haka sai ya waigo da sauri sarkine tsaye a bayansa fuskarsa a murtuke yana mai kada kansa wato yana yi masa nuni da kada ya fada mata abindake bakinsa... Zidane kd Mutum Da Aljan Littafi Na Biyar (5) Part B. . Marubucin littafin Abdul aziz sani madakin gini typing by Al amin Ahmed Misau Guyson Call;- 08064594218 Doka;- Ban laminta ba ayi edit na post dina ba tare da sanina ba. . Labari ya isowa guyson cewa...... KAWAI SAI SARKI YA DUBI MAHAIFIYATA yace ina son nayi magana da dana shin zaki iya bamu dama? Ba tare da tace uffan ba sai ta mike tsaye ta fice daga cikin tantin a sannan ne sarki ya dubi alkasim a fusace yace shin baka da hankaline har da kake shirin tambayarta matsayinka a wajenta kana yin garaje a cikin al amarinka kuma ita gaggawa bata haifar da komai sai nadama kayi hakuri kaji karshen labarin da nake baka tukunna a sannan ne zaka san matsayinka a wajenta ba wai sai kaji daga bakin taba ni yanzu abinda ya kawoni wajenka ba komai bane face na sanar dakai cewa kada ka kuskura ka bar zuciyarka ta karaya bisa gasar da zakuyi kai da luslaiya yar sarkin mafarauta na birnin taheren duk irin masifar da zaka gani a cikin tafiyar taku duk irin tsananin wahalar da zaka sha kada ka karaya domin ba a samun komai a banza a cikin wannan duniya dolene sai an sha wuya sannan akansha dadi duk abinda ya faru a daji tsakaninka da luslaiya na gani a cikin madubin tsafina don haka kayi sammakon riskarta a dajin gobe da safe kamar yadda ta umarceka taimakon da zan baka a matsayin babban guzuri a cikin wannan gasa da zakayi shine ka rike abu uku wannan abubuwa uku ba komai bane ba face gaskiya hakuri da amana sune kadai abubuwan da zasu kubutar dakai daga sharrin luslaiya amma ba karfin damtsenka ba ko karfin sihirin tsafinka ba saboda duk a bin da kake takama dashi itama tana dashi ka sani cewa nima na taka irin wannan matsayin da kake kai yanzu kafin na mallaki mahaifiyarka wannan al adar gidannance babu wani sarki da ya taba auren matar da bata kasance basadaukiya ba Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan kuma jaruma abar kwatance a duniya an tsara hakanne domin dukkan zuri armu su rinka shan jarumtaka a nono da wannan furuci nake yi maka sallama kuma nasa maka albarka ka tafi abinka nasara na tare dakai koda gama fadin hakan sai sarki ya dora hannunsa na hagu akan tsakiyar kaina faruwar hakan keda wuya sai naji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikina kuma naji dukkan tsoro da fargaba sun kau daga cikin raina har ina jin kamar cewa ni kadai zan iya yakar duniya. Saboda farin ciki bansan sa adda na duka har kasa ba zan yiwa mahaifina sujjada amma saiya kamo kafaduna ya tasheni tsaye yace kwanta ka huta dana gobe akwai gagarumin aiki gabanka yana gama fadin haka sai ya juya ya fice daga cikin dakin ya barni ni kadai nan dai naje na kwanta a shimfidata na lumshe idanuna domin nayi barci amma saina kasa domin fuskar luslaiya naci gaba da gani ba sassauci har gari ya waye barcina rabi da rabine wato rabi tunani rabi barci kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya keto na gama shiri kuma nayi sallama ga mahaifiyata duk mu biyun muna kwalla muka rabu cikin gaggawa nayi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro na hau dokina na sukwaneshi da guda na fice daga cikin gari na naushi daji hakika masu iya magana sun yi gaskiya da sukace komai sammakonka wani a tafe ya kwana a iya tunanina sai dai naje wannan wuri inda mukayi alkawarin haduwa da luslaiya na jirata amma ina isa wajan na isketa a tsaye gaban wannan katuwar bishiya wacce ta zukeni waccen karon luslaiya ta ruke kugunta tana kai kawo alamar cewa har ta gaji da jiran isowarta koda ta hangoni na durfafota sai tayi dan guntun murmushi da isowata daf da ita sai ta dubeni tace in dai baso kake ka zalunci wannan doki naka ba zai fi kyau ka sake shi ya kama gabansa domin zaka ja shine izuwa hallaka kuma kada ka manta cewar daga nan ne zamu fara yin gasar gudu ta kwana tara kuma tabbas wannan doki ba zai jure hakan ba ba tare da wata gardama ba saina sauka daga kan dokin na bugeshi ai kuwa sai dokin ya juya da baya da gudu yana mai bin hanyar da muka fito nan da nan kuwa ya kule muka daina ganinshi a sannan ne na juyo na dubi jaruma luslaiya da kyau ai kuwa sai na rude kuma na kidime naji na kara kamuwa da tsananin sonta fiye da koyaushe a wannan lokaci luslaiya na sanye da riga da wando ne na fatar damisa wadanda suka kasance matsatstsu don haka gaba dayan surorin jikinta sun fito karara ni kam in dai tambayata za ayi to zance duk duniya babu wata ya mace mai kyan sura da kyan fuskar mahaifiyarka luslaiya luslaiya ta daure wadansu gajerun adduna guda biyu akan cinyoyinta dama da hagu a gadon bayanta kuwa tana rataye da wata sharbebiyar takobi dogon gashin kanta kuwa ta tattareshi a bayanta ta daureshi ya zuba har kan kasan kwankwasonta sai sheki da walwali yake duk da cewa nayi gagarumar shigar yaki sai da na raina kaina domin tata shigar tafi tawa kyau da kwarjini luslaiya ta sake dubana cikin wani irin murmushi mai kama da mugunta ko yaudara tace idan ka shirya yanzu zamu fara gasarmu ta farko ta gudun kwana tara babu tsayawa ta tsawon sama da dakika goma Al amin Ahmed Misau Guyson, Dajin haka sainayi murmushi nace ai tunda har na dawo gareki na gama shiri kafin na gama rufe bakina sai kawai naga luslaiya ta zabura ta falfala da azababben gudu izuwa cikin daji koda ganin haka sai nima na falfala nan da nan kuwa na risketa muka jera muna gudun tare da zarar naga ta rage karfin gudun nata sai nima na rage nawa ya dawo dai dai da nata koda ganin haka sai tayi murmushi na mugunta nima sai na maida mata da martanin murmushin muguntar saboda nasan cewa na fita sanin sirrin wannan daji da muke ciki kuma na tabbatar da cewa bata san irin hadarin dake gabanmu ba akan wannan hanya da muka biyo Abinda luslaiya bata sani ba shine anan gabanmu kadan akwai wani kogi na tabo wanda indai mutum ya fada cikinsa babu yadda zai iya kubuta sai dai ya nutse a cikinsa face wani ya taimakeshi koda ya rage saura baifi dakika dari ba mu iso inda wannan kogin tabo yake saina fara rage guduna ta hanyar nuna alamun cewa na fara gajiya koda ganin haka sai luslaiya ta fara murna kuma ta karawa kanta karfin gudu hakika rashin sani yafi dare duhu tabbas inda luslaiya tasan masifar dake gabanta da batayi wannan ganganci ba na kara karfin gudun nata shi dai wannan kogin tabo gaba da bayansa a lullube yake da tsirrai babu yadda mutum zai iya ganewa cewa kasan tsiran tabone sannan kuma tabon yana da zurfin gaske Al amin Ahmed Misau Guyson nake magana daga zauran labarai page. Da isowarmu daf da wannan kogin tabo luslaiya na kan gaba ina bayanta koda ta waigo taga na karo guduna ina son na risketa saita daka tsalle sama domin ta bani tazara mai yawa kawai saiji tayi ta fado cikin tabo ta makale da kasa gaba da baya nan fa ta fara amfani da karfin sihirinta na tsafi domin ta fito daga cikin tabon amma saita kasa kuma sai taji tana kara nutsewa kasa a hankali Al amarin da yayi matukar dugunzuma hankalinta kenan ta juyo bayanta da sauri ta dubeni kawai sai gani na tayi a tsaye nayi turjiya na zuba mata idanu ina mata murmushin mugunta luslaiya ta daka min tsawa tace meka tsaya kana jira ka ci gaba da gudunka ka barni a anan tawa ta fishsheni idan ma na mutu anan shi kenan ka lashe gasar koda jin wannan batu saina sake yin murmushi a karo na biyu nace tayaya zan iya tafiya na bar masoyiyata a inda zata hallaka ai dole ne na ceto rayuwarki luslaiya tace ai kuwa inka ceci rayuwata kayi babban kuskuren da saikayi nadamarsa da jin haka saina gyada kai nace har abada masoyi baya nadama akan taimakon masoyinsa koda na gama fadin haka saina kwance jakar guzurina dake rataye a kafadata na fiddo wata doguwar igiya na cillawa luslaiya ta cafe sannan na rinka janyota daga cikin tabon a wannan lokaci tabon ya shanye dukkan wuyanta don haka gaba daya jikinta ya baci da tabon da kyar na samu na fito da ita tana gama fitowa sai ta nufi cikin wata korama ta kama yin wanka ni dai ina tsaye a gefe daya ina kallonta kawai saita daka min tsawa tace shin tarbiyarka daka samu kenan ta kallon mata? Koda jin haka sai nayi sauri na juya mata baya ina mai cewa ki gafarceni nayi kuskure bayan luslaiya ta gama wanka gaba dayan tabon jikinta saita fito daga cikin kogin tazo kusa dani ta dubeni tace yanzu ta yaya zamu iya haye wannan kogin tabo muci gaba da yin tafiyarmu duk inda kika ga nasa kafata kema ki saka naki ina gama fadin hakan saina nufi kan karshen gefen kogin tabon naci

Chapter 6 of 9