Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MUTUM DA ALJAN!!! Littafi Na Daya (1) Complete book 1 Typing Suleiman Zidane Kd. Whatsapp 09064179602 A WANI ZAMANI CAN BAYA MAI TSAWO daya shude,anyi wani gawurtaccen sarkin Aljanu mai suna MASARUL ANJANA.Sarki Masarul Anjana yana mulkin wata babbar kasa ne mai suna DILHAR wacce ke can karshen birnin SIN.Duk wata daukaka ta duniya babu wacce sarki Sarki Masarul Anjana bai samu ba walau ta DUKIYA,KARFIN MULKI,JARUMTAKA,GIRMAN KASA DA TARIN 'YA'YA,yana da MATAN AURE guda DARI UKU DA SITTIN,'ya'ya kuwa sai da aka haifa masa guda DUBU DAYA DA DARI HUDU amma cikin iko na ALLAH sai ya zamana cewa duk shekara sai 'ya'yan nasa kimanin dari da wani abun sun mutu kuma basa yin wata doguwar jinya ta rashin lafiya sai rai yayi halinsa.Abu dai kamar wasa sai 'ya'yan nasa suka cigaba da mutuwa da daidai har saida ya zamana cewa saura guda daya jal wacce ta kasance itace 'YAR AUTANSU ana kiranta da suna ZULFULAIFA.Zulfulaifa ta kasance kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance domin tun tana jaririya da aka haifeta sai labarin ya bazu a ko ina a cikin duniya a kasashen bil'adama saboda tsananin kyawunta yafi gaban kwatance,tun a sannan ne sarki Masarul Anjana ya dauki son duniya ya dorawa Zulfulaifa ya zamana cewa dare da rana yana tare da ita baya yarda ta gusa daga kusa dashi kuma ko kuda baya son yaga ya sauka a jikinta,kai ko ciwon kai sarki Masarul Anjana yaga Zulfulaifa nayi tofa sai an tara gaba dayan likitocin garin a kanta,wanda duk ya bata maganin data samu sauki nan taje tofa shi kakarsa ta gama yanke saka,domin za'a bashi dukiyar da tattaba kunnensa ma basu isa su iya karar da ita ba.Idan kuwa likita yayi kuskure ya bata maganin daya wahalar da ita HUKUNCIN KISA ya tabbata a kansa har dama dukkan iyalansa.Bisa wannan dalili ne kowane likita yake yin taka tsantsan gami da yin baya baya a duk sa'adda Zulfulaifa ta kamu da rashin lafiya.Lokacin da Zulfulaifa ta cika shekara goma sha takwas da haihuwa sai sarki Masarul Anjana ya tara gaba dayan gwamnonin jihohin dake kasarsa a babbar fadarsa wadda girmanta ya ninka gaba dayan birnin sin sau uku ya dubesu yace,yaku shugabannin jihohin kasata,ku sani cewa saura wata uku 'yata Zulfulaifa ta cika shekara goma sha takwas da haihuwa,ni kuma zan cika shekara dubu uku da saba'in da uku a duniya saboda haka ina farin ciki mara misaltuwa.Bisa wannan dalili ne nake son na shirya gagarumar walima irin wacce ba'a taba yin kamarta ba a duniya,kuma za'ayi shagalin biki na tsawon kwanaki arba'in.Inason a tara mini gaba dayan mawaka da makada na duniya daga jinsin Mutane da Aljanu kuma inason a tara mini dukkan jaruman duniya na mutane da aljanu sannan a tara mini duk wanda zai iyasa 'yata Zulfulaifa tayi dariya.Tun Zulfulaifa tana jaririya kawo iyanzu data shekara goma sha takwas a duniya bata taba yin murmushi ba bare tayi dariya.Baby mahalukin daya taba ganin hakoranta saboda tsananin rashin dariyarta da maganarta,tana da tsananin fushi,dan kankanin abu na iya sata kuka.A kullum takan yi kuka kamar sau dari(Uhmm Sarauniyar Shagwaba),duk mahalukin daya sata dariya ko ya sauya mata yanayin rayuwarta daga yawan kuka ya koma murmushi da farin ciki zan mallaka masa duk abinda yake so a cikin wannan duniya indai akwai shi.Akwai sharadi guda daya,sharadin kuwa shine idan mutum ko aljan yasa Zulfulaifa tayi kuka a maimakon murmushi ko dariya a lokacin da yake kokarin sata walwala tofa zan kaishi kurkukuna ne na daureshi ba zai taba fitowa ba har sai ranar da Zulfulaifa tayi dariya.Idan kuwa kuwa zata shekara dubu arba'in nan gaba a duniya batayi dariya ba to saidai shima yayi ta zama a kurkukun tsawon wannan lokaci koda kiwa ya mutu ya rubde kashinsa ma ya zama kasa.Inason yanzu nan a rubuta wasikun gayyata aje a rarrabasu izuwa ga dukkan kasashen duniya da aljanu a cikin abinda bai wuce sa'a uku ba kuma a sanar da kowane sarki cewar idan bai tara jama'arsa ba ya amsa wannan gayyata zan turo dakaruna na yaki su baje kasarsa,gidajensu su zama turbaya.Koda jin wannan batu sai gwamnonin gaba dayansu suka amsa da angama ya shugaban.Nan take sarki Masarul Anjana ya sallami gwamnonin nasa kowannensu sai ya tashi sama tare da mukarrabansa suka luluka a cikin gajimare,kafin kiftawr idanu sun bace bat a cikin gajimare.A wannan lokaci a duk fadin duniya ana tsaron sarki Masarul Anjana saboda babu wata kasa mai karfin mayaka don haka duk inda yaje da bukatar ana rawar jiki za'ayi masa.A fagen arziki kuwa yayi fintinkau bashi dasa a sannan Allah yayi shi sadauki na gaban kwatance domin idan ya fusata shi kadai ma yana iya zuwa ya yaki kasa guda ya murkushe ta a cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba komai yawan al'ummar dake cikinta walau ta kasance kasar mutane ko ta aljanu.Wani abin mamaki a tare da sarki Masarul Anjana shine yana da matukar saukin kai,in dai za'a bashi girma kuma za'a bi umarninsa to za'a zauna lafiya ba zai taba zaluntar mutum ba ko aljan.Babban abinda ya tsana shine girman kai ko gardama,komai matsayin mutum ko aljan komai daukakarsa da mulkinsa indai ya yiwa sarki Masarul Anjana girma kai ko rashin kunya tofa tasa ta kare saidai a tuno dashi a tarihi.Abinda yake daurewa dukkan jama'ar aljanu da mutane kai dangane da halayen sarki Masarul Anjana shine ko kadan addini bai dameshi ba,a cikin kasarsa aljanu suna yin addinai kala kala sama da guda dubu kuma kowa yana da yancin yayi nasa a ko'ina babu mai hanashi ko tsangwamarsa.Shidai sarki Masarul Anjana yana bautar wani gunki ne mai siffar mari babban kifi wanda aka sassakashi da zinare aka sanya shi a cikin wata katuwar kwalba wacce ke cike da ruwa.Ita dai wannan kwalaba ba'a ★Abubakar Haleefah Physicist★ budeta kuma bata da murfi ko kofa.Duk wanda ya ganta sai yayi mamakin ta yadda aka zuba ruwan a cikinta.An anjiye wannan kwalaba ne a cikin wani daki na musamman dake cikin gidan sarautar kuma tafi shekara dubu goma a wajen domin tun iyaye da kakannin sarki Masarul Anjana akayi ta kuma kowane sarki a zamaninsa dole ne kullum ya ziyarci wannan gunki sau uku,safe da rana da daddare ya kwashi gaisuwa yayi sujjada sau uku a gaban gunkon sannan ya mike ya fita amma shi sarki Masarul Anjana a zamaninsa sai ya sauya yanayin bautar ta koma sau daya kawai a rana.Itama sujjadar saiya mayar da ita sau daya,lokacin da fadawansa sukayi masa magana akan sabon tsarin da yazo da shi sai ya dubesu yace ai sarki goma zamani goma,iyayena da kakannina a lokacinsu basu da aikin yi don haka suna bata lokacinsu ne a banza amma ni yanzu ko sauraron harkokin fada ya isheni don haka bani da lokacin da zan rinka batawa haka mai yawa a dakin bauta.Daga wannan rana kowa ya kunshe bakinsa ba'a sake yi masa wannan magana ba.Lokacin da gwamnonin jihohin dake cikin kasar Dilhal suka baro babban birni inda fadar sarki Masarul Anjana take basu zame ko ina ba sai kasar daya daga cikinsu wani gwamna wanda ake kira da suna Asmaru bin Aiyan suna sauka a fadarsa suka wuce izuwa dakin taro inda suka zauna suka fara tattaunawa akan wannan babban aiki wanda sarki Masarul Anjana ya basu.Bayan sun zauna kuyangi sun kawo musu dan abin sha kowa ya dan zuka sai shugaba Asmaru ya dubesu yace yaku yan'uwana gwamnoni ku sani cewa wannan aiki da sarki ya bamu bazai kammalu ba a cikin sa'a uku ba saboda duniya ta wuce wasa.Duk da kasancewarmu Aljanu kuma babu wani jinsi na aljanu daya fimu karfin gudu a cikin sararin samaniya ba zamu iya karade dukkan kasashen mutane da aljanu ba a cikin sa'a uku mu isar da wannan sako ga kowane sarki.A kowane nahiya sai mu kaiwa manyan sarakunansu in yaso su kuma sai mu dora musu alhakin kaiwa kananan sarakunansu.Tunda dai saura kwanaki ca'sain ranar walimar tazo,to kafin sannan zasu isar da sakon ga kowane sarki.Koda sauran gwamnonin sukaji wannan batu sai suka kamu da tsananin farin ciki saboda sun san cewa wannan itace kadai mafita a garesu.Ba tare da bata wani lokaci ba kuwa aka tara manzanni sama da guda miliyan dubu aka danka musu wasikun,rabin wadannan manzanni zasu kai wasikun ne izuwa ga kasashen aljanu,rabi kuma izuwa kasashen bil'adama.Duk manzon da aka turashi izuwa kasar bil'adama sai aka umarceshi daya kai sakon izuwa ga babban boka na birnin da yaje,shi kuwa bokan shine zai kai wasikar ga sarkinsu.Nan da nan kuwa cikin abinda bai kai sa'a uku ba kowane manzo ya cika aikinsa.A wannan lokaci a kasashen bil'adama babu wata kasa wacce tayi shaharar birnin Misra saboda daukakar ta,arzikinta da kuma girman masarautarta da karfin mulkinta,sarkin dake mulkin birnin Misra a sannan shine sarki Alkasim Bin Mas'ud.Kamar yadda Allah ya baiwa sarki Masarul Anjana komai da jin dadin duniya haka ya baiwa sarki Alkasin,bambancinsu kawai shine sarki Alkasim mutum ne shi kuma sarki Masarul Anjana Aljani ne.Baya ga haka kuma shi sarki Alkasim sau daya ya taba haihuwa kuma 'da Namiji,Allah ya bashi wani kyakkyawan saurayi mai suna KAMSUS.Yarima Kamsus ya zama daya tamkar dubu a cikin dukkanin samarin dake nahiyarsu domin shi tun yana da shekaru goma a duniya ya shahara ya zamo abin kwatance kuma abin misali,abin al'ajabi harma wasu nayi masa kirari da KYAUTAR ALLAH.Abu na farko daya ajiye na tarihi shine ba'a taba ganin ranar da yarima Kamsus yayi fushi ba saboda tsananin hakurinsa da kawaicinsa,kai ko zaginsa akayi ko a dokeshi fuskarsa ba zata sauya yanayi ba saidai kawai yayi murmushi kuma ya baiwa mutum hakuri koda kuwa zaluntarsa akayi.Yarima Kamsus ya kasance gawurtaccen sadauki mai jarumtaka ta ban al'ajabi domin komai yawan runduna ta abokan gaba baya tsoron ya shigesu ko shi daya ne,kuma duk irin bala'in da za'a yi saiya tsira,ko rauni ba'a taba yi masa ba a filin yaki.Duk wani mugun abu daya gagara a nahiyar yarima Kamsus ne ke zuwa ya kau dashi walau wani mugun dodo ko mugun aljani ko kuma wata muguwar dabba.Kamsus yana da matukar tausayi,taimako gami da jin kai,kuma tun yana jariri kawo izuwa girmansa mahaifiyarsa ta tabbatar da cewa banda kuka da yayi a ranar da aka haifeshi irin na jarirai bata sake jin kukansa ba,kuma bata taba ganin hawaye ya zuba daga cikin idanunsa ba.Wuya,farin ciki ko bakin ciki basa sashi kuka saidai murmushi da fara'a.Yana da tsananin sa'a bisa duk abinda yasa a gabansa bai taba samun akasi ba.Wannan baiwa da Allah ya baiwa Yarima Kamsus ce ta janyo masa FARIN JINI a wajen mutane maza da mata,musamman 'YAN MATA wadanda suka haukace kuma suka dimauce a cikin KOGIN SOYAYYArsa.Amma sai yayi biris dasu yaki karbar soyayyar kowa saboda yana da wani buri a cikin zuciyarsa wanda yayi alkawarin cewa saiya cikashi sannan zaiyi aure.Wannan buri na Yarima Kamsu babu wanda ya sanshi hatta sarki Alkasim kuwa. FADA RA CIKA MAKIL DA JAMA'A,duk inda mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan bil'adama fululu babu masakar tsinke.Sarki Alkasim tare da Yarima Kamsu na zaune bisa KARAGAR MULKI suna daf da juna ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba,ga fadawa sun kewayesu,A wannan lokaci ana cikin nishadi,wasu kyawawan yanmata sanye da korayen tufafi su hudu suna ta faman tika rawa a tsakiyar fadar a lokacin da wani kida mai taushi ke tashi irin nasu na larabawa.Kowa ka kalla a cikin fadar sai kaga yana dariya ko yana murmushi,wasu kuma suna fadin albarkacin bakinsu saboda suna jin dadin kallon wadannan yan ★Abubakar Haleefah Physicist★ yanmata dake debe musu kewa sakamakon cewa rawar tasu akwai burgewa da ban sha'awa.Kwatsam!Ana cikin wannan hali saiga boka Rausum ya shigo cikin fadar da sauri a hannunsa akwao wata fata mai daraja.Koda ganin boka Rausum a cikin wannan hali sai aka daina kida da rawa,fadar tayi tsit tamkar babu kowa a cikinta.Nan take aka budawa boka Rausum hanya ya wuce ta tsakiyar fadar ya nufi inda sarki Alkasin ke zauna.Koda daya rage saura baifi taku biyar ba tsakaninsa da karagar mulkin saiya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya dago kai ya dubi sarki Alkasim a lokacin da kowa ya kasa kunnuwansa domin yaji abinda zai fada saboda wasikae da aka gani a hannunsa ba'a taba ganin irinta ba.Boka Rausum yayi gyaran murya sannan yace ya shugabana yanzun nan manzo yazo daga birnin Dilhar ya kawo mini wasika daga hannun sarki Masarul Anjana.Koda jin wannan batu sai idanun gaba dayan jama'ar dake fadar ya zazzaro,aka firgice wasu ma nan take cikinsu ya duri ruwa,hantar cikinsu ta kama kadawa,amma banda sarki Alkasim da yarima Kamsus,maimakon ma yaji tsoro sai farin ciki ya turnuke shi ya kama murmushi da fara'a yana ta yake baki tamkar wanda akayi masa bushara ta samun duniyar duka.Shi kuwa sarki Alkasim sai ya turbune fuska tamkar wanda aka aiko masa da sakon mutuwa ya dubi boka Rausum cikin matukar fishi yace maza ka baiwa magatakarda wannan wasika ya karantata a fili muji abinda ke cikinta.Dajin haka sai Boka Rausum ya mikawa magatakarda wasikar da sauri ya karba hannunsa na karkarwa saboda tsoro ya budeta a hankali saboda gani yake kamar bakin kura zai bude.Ba wai hannayensa ba hatta kafafuwansa ma karkarwa sukeyi.Koda ganin haka sai sarki Alkasim ya dakawa magatakarda tsawa ya ka nutsu ka daina barin jiki,domin kana gaban SHUGABAN SARAKUNA wanda fushinsa ya ninka na mai wannan wasika sau dubu.Idan baka nutsu ba yanzun nan zan sare maka kai.Koda jin haka sai magatakarda ya nutsu a lokacin da gumi ya karyo masa amma gaba dayan jikinsa ya daina karkarwar.Lallai masifa ta zahiri tafi wacce ba zata zo ba.Nan yake magatakarda ya fara karantawa wasikar a fili kamar haka... -Takarda daga hannun SARKIN SARAKUNA,shugaban Attajiran duniya kuma SADAUKIN SADAUKI Sarki Masarul Anjana,zuwa ga Alkasim na birnin Misra,yakai wannan shugaba kayi sani cewa ni Sarki Masarul Anjana tare da yata Gimbiya Zulfulaifa zamuyi gagarumar walima ta murnar cikar shekarunmu sha takwas da dubu uku da saba'in da uku,saboda haka ina umartarka daka tara gaba dayan mawakan kasarka da makadanku da kuma jarumanku da duk wani ma'abocin barkwanci ko wata baiwa azo dashi birnina a wannan rana domin a debe mana kewa.Ka sani cewa yata bata taba yin dariya ba a rayuwarta kuma bata tabayin murmushi ba.Wanda duk yasata tayi dariya ko murmushi zan bashi duk abinda yake bukata idai akwai shi anan duniya.Wanda duk ya sata tayi kuka zai shiga kurkuku bazai fito ba sai ranar da wani yasata tayi dariya.Duk sarkin da baibi umarninmu ba zamu turo mayakanmu su baje birninsu su kashe duk wani abu mai numfashi a kasarsa.Koda magatakarda yazo nan a karatun wasikar sai sarki Alkasin ya mike tsaye zumbur cikin tsananin fushi har fuskarsa nayin gatsine ya bude baki cikin daga murya yace ba za'abi umarnin nasa ba.Waye shi dazai shiga cikin harkokin mulkinmu na bil'adama? Lallai ya tsaya iya matsayinsa da kuma jinsinsa.MUTUM DA ALJAN ba daya bane,suyi al'adarsu,Addininsu da mulkinsu a iya kasashensu da jama'arsu muma mu tsaya a iya matsayinmu,maza a rubuta masa wasikar raddi a baiwa Boka Rausum.Kafin sarki Alkasim ya gama wannan jawabi tuni fadawa da sauran jama'ar gari sun tsure kuma sun firgice saboda sanin masifar Sarki Masarul Anjana.Shi kuwa Yarima Kamsus saiya mike da sauri ya kama hannayen sarki yace yakai abbana ka sanyawa zuciyarka ruwan sanyi ka kwantar da hankalinka,ka sani cewa durkusawa wani ba gajiyawa bane,ina mai tabbatar mala da cewa wannan ce babbar damar dana samu wacce zan cika babban burina na duniya,burin daka matsanta mini akan na sanar dakai amma naki.To ka sani cewa kana daf da sanin ko menene wannan buri nawa amma sai idan ka amince mini na tafi birnin Dilhar a matsayin daya daga cikin wadanda zasu sa gimbiya Zulaifa dariya.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke kowa musamman sarki Alkasim ya dubi yarima Kamsus cikin tsananin damuwa yace ta yaya kana matsayin dan sarki guda zakaje wajen wata yar sarki a matsayin mai barkwanci,ka kaskantar da kanka?Ka sani cewa babu wani abu wanda Zulfulaifa tafika dashi face kawai ita Aljana ce kai kuwa mutum ne.Yarima Kamsus yayi murmushi yace nasan da haka yakai Abbana amma ka sani cewa daukaka bata zuwarwa mutum kawai dole ne ya sha wahala ko kuma ya kaskantar da kansa kafin ya sami matsayin da yake nema.Sa'adda Yarima Kamsu yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki Alkasim yayi sanyi kuma hankalinsa ya DUGUNZUMA yayi shiru yana tunani gami da nazari a cikin kwakwalwarsa har izuwa tsawon yan dakiku a lokacin da fadar tayi tsit kuma kowa ya zuba masa idanu ana sauraron a ji amsar da zai baiwa Yarima Kamsus.Kawai sai akaji ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan saiya dubi Yarima yace yakai dana na yarda da bukatarka.Zan barka ka tafi izuwa birnin sarki Masarul Anjana amma face idan ka amince zamu tafi tare.Nima zan batar da kamannina naje a matsayin mai baiwa gimbiya Zulfulaifa dariya kamar yadda kaima zaka bata dariya.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa dake fadar ya dugunzuma ainun musamman na yarima Kamsus,domin durkusa yayi a gaban sarki bisa gwiwoyinsa y kama rokonsa akan ya hakura kada ya bishi. Zidane Kd DUK DA CEWA KUWA MACEN TA RUFE FUSKARTA.Kai ba wai sarki Alkasim da yarima Kamsus ba hatta sauran baki da gaba dayan jama'ar gidan sarautar kallon wadannan matasa biyu suke suna mamakin yadda Allah ya halicce su da kyau gami da kamanni iri daya.Sarki da Yarima dai basu san sa'adda suka kurawa wadannan tagwaye idanu ba sukayi shiru ga barin hirar da sukeyi.Har Yarima ya yunkura zai sauko daga kan matattakar benen da suke tsaye domin yazo kasa ya karewa tagwayen kallo sosai kuma yayi magana dasu sai sarki yayi wuf ya riko hannunsa yace haba kada ka bayar dani mana,sai kace baka taba ganin abin da ya fi wadannan tagwaye ba al'ajabi.Ko kuwa kana so ne mutane suyi zargin cewa ka kami da son macen?Koda jin wannan batu sai kunya ta kama Yarima Kamsus ya dawo bayan sarki ya tsaya yace kayi gaskiya yakai Abbana,amma ban taba ganin tagwaye irin wadannan ba.Ni kawai so nake naji tarihinsu da kuma irin baiwar da suke da ita wacce ta sa suka yanke shawarar yin wannan tafiya.Koda jin wannan batu sai sarki Alkasim ya bushe da dariya sannan yace to in banda abinka me kake ci na baka na zuba?Ai duk irin guzurin da suke dauke dashi zamu gani a cikin wannan doguwar tafiya da zamuyi.Koda gama fadin haka sai sarki Alkasim ya kirawo sarkin Gida ya dubeshi yace aje a baiwa gaba dayan bakin nan masauki kowa ya kwanta ya hutu kuma a sanar da boka Rausum cewa sai gobe da yamma za'a dunguma abar birnin Misra.Koda jin wannan batu sai yarima Kamsus ya zazzaro idanu ya dubi sarki cikin alamun firgici da damuwa yace haba ya Abbana yaya zajace sai yamma za'ayi wannan tafiya alhalin Boka Rausum yace dole ne ayi gaggawar tafiya domin a isa can birnin Sin.Koda jin haka sai sarki Alkasim ya bushe da dariya sannan ya turbune fuska ya cakumi kwalar rigar Yarima Kamsus yace hakika kai yaro ne.Ka sani cewa babu abinda nake shakka a wannan duniya.Na rantse da girman iyaye na bazan bi dokar Sarki Masarul Anjana ba.Dole sarki Masarul Anjana ya gane cewa ni daban ne bana daga cikin jama'ar da suke tsoronsa ko shakkarsa.Ta haka ne kadai zamu iya nuna masa matsayinmu.Na umarceka da ka zamo kamar ni kada ka kuskura kayi biyayya ga Masarul Anjana.Ka sani cewa mutum yafi aljani daraja da kima.Tun farkon duniya mutum ne ke sarrafa aljan.Sune bayinmu mune iyayen gidansu.Kada ka kuskura ka kaskantar da kanka a garesu.koda sarki Alkasim yazo nan a zancensa sai yarima Kamsus yayi murmushi yace madalla da zaki uban dawa mai zuciyar karfe.Tabbas ka tunasar dani abinda na sani kuma nayi maka alkwarin cewar lallai zan kiyaye dukkan umarninka.Koda jin haka sai sarki ya saki kwalar Yarima Kamsus ya rungume shi cikin farin ciki sannan ya kama hannunsa suka kama saukowa daga kan wannan matattakalar bene.A daidai wannan lokaci ne wadannan tagwaye biyu mace da namiji suka zo giftawa ta gabansu yayin da tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku biyar ba.A wannnan lokaci gaba dayan bakin dake wucewa suna risinawa suna gaishe da sarki da yarima amma su wadannan tagwaye ko kallo kirki basu yi musu ba.Al'amarin daya fusata sarki Alkasim kenan har ya bude baki zai daka musu tsawa sai yarima Kamsus ya tari numfashin yace rabu dasu akwai abinda ya kamata mu fara sani a kan wadannan tagwaye.Kawai sai Kamsus ya kurawa macen idanu.Koda ganin haka sai macen tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa,saida sukayi dan nisa da wucewa sannan ta waigo sau daya tana hada idanu da Kamsus sai ta sake kawar da kanta da sauri.Nanfa Yarima Kamsus ya fara kokarin ya tuno inda ya taba ganin wannan idanu amma saiya kasa.Kawai sai yaja sarki suka wuce izuwa cikin gidan sarautar.Har suka isa turakar sarki yana lallaba shine yana tausarsa saboda a fusace yake bisa ganin yadda wadannan tagwaye suka ki gaishe su alhalin kowa a kasar yana girmamasu.Saida Yarima Kamsus ya zaunar da sarki a kan kujera a babban falonsa yasa aka kawo masa ruwan inibi mai sanyi yasha sannan ya dubeshi cikin murmushi yace yakai Abbana ka sani cewa wannan ne karo na farko da aka taba samun talakawanka wadanda suka ki risinawa a gareka su gaishe ka.Abinda yasa na hanaka ka dauki mataki a kansu shine da zarar kayi musu wani abu alkadarinka ya karye tunda duniya zataji cewa an sami wadanda suka zo maka da wargi har cikin fadarka alhalin hakan bata taba faruwa ba.Da gani sai ka luta da rashin da'arsu a wajen,kana tanka musu shike nan ka daukaka darajarsu.Da sannu zamu ga iyakar takamarsu kuma dole ne su kaskanta a gabanmu.Lokacin da yarima Kamsus yazo nan a zancensa sai murmushi ya subucewa sarki Alkasim ya dubeshi cikin murna yace hakika nayi babbar sa'a da ubangijina ya bani da mai basira da hangen nesa.Na karbi wannan shawara taka kuma nayi maka alkawarin cewar bazan taba yanke wani hukunci ba a kan wadannan tagwaye ba face bisa ra'ayinka.Koda jin haka sai Yarima Kamsus yayi farin ciki matuka kuma ya sumbaci sarki a goshi sannan yayi masa sallama ya fice daga cikin falon ya nufi tasa turakar.Har Yarima Kamsus ya isa cikin dakin baccinsa babu abinda yake tunani face kyawawan idanun wannan macen tagwayen.Tabbas ya taba haduwa da wannan mai idanu amma ya kasa tuno da inda suka hadun da kuma lokacin.Har Yarima ya isa kan gadonsa ya kwanta bai iya tuno komai ba.Koda yaga cewa yana bata lokacinsa a banza sai ya cire al'amarin daga cikin zuciyarsa yaja mayafinsa ya lullube jikinsa ya kama bacci abinsa.Kashe gari kuwa sarki Alkasim bai fito fada ba har saida rana ta take.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan musamman bisa sanin cewa yaune fa za'a tafi birnin Sarki Masarul Anjana.Nan take ★Abubakar Haleefah Physicist★ kowa ya gane cewa tsabar jin kai da IZZA ne yasa sarki yaki fitowa da wuri domin ya nunawa duniya cewa fa baya shakkar sarkin Aljanu Masarul Anjana.Shima Yarima Kamsus ko fitowa baiyi ba daga cikin turakarsa har saida kuyangi suka kawo masa abincinsa na rana yaci ya koshi.A sannan ne ma ya shiga kewate yayi wanka.Yana fitowa saiya tsala uban ado na kure adaka.Shi kansa yayi mamakin dalilin da yasa ya caba wannan ado,maimakon ace yayi gagarumar shigar yaki tunda tafiya ce mai hadari za'ayi.Nan take ya tuno da wannan kyakkyawan idanu na macen tagwaye.A karon farko a rayuwarsa sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi kuma yaji babu abinda yake so sama da ganin fuskar wannan mace.Koda gama ayyana hakan sai Yarima Kamsus ya dakawa kansa tsawa a cikin zuciyarsa yace a kul ka sanyawa zuciyarka son wata 'ya mace domin masu iya magana sunce somi somin Hauka zub da yawu ne.Ba zaka taba son wata ya mace ba face ra'ayinka yazo daidai da nata kuma sai ka yaba da halayenya.Yarima yana cikin yin wannan zancen zuci ne Boka Rausum ya shigo cikin falon nasa da sauri hankalinsa a tashe har yana tuntube.Da isowarsa daf da yarima saiya zube kasa bisa guiwoyinsa ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shugabana kayi mana rai nida sauran jama'ar da za'ayi wannan tafiya,kayi sani cewa kai ne kadai zaka iya zuwa ka fito da sarki yanzu muyi gaggawar barin garin nan.Rashin tafiyarmu yanzu zai janyo mu kasa hallara a fadar sarki Masarul Anjana a kan lokaci kuma zamu fuskanci horo mai tsananin.Koda Boka Rausum yazo nan a zancensa sai yarima Kamsus ya bushe da dariya.Al'amarin daya kara firgita Boka

Chapter 1 of 9