Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fini dacen miji a fadin duniyar nan.Saidai kash tun bayan auren mu dashi ban taSa samun kwanciyar hankali a wajen dangin mijina ba kannen sa harma da mahaifiyar shi baki Wayan su suka tsaneni kullin banda bankaWa da tsina ba abinda nike sha a wajen kannen mijina harda wasu daga cikin DANGINMU haka suka shiga suka fita wajen haddasa musiba da bala'i a rayuwar aurena saidai duk abin nan Ya Nizam baisan abinda ake ba saboda aiki da yakeyi a kasar America wannan dalilin yasa mijina baida cikakkar masaniya akan abinda ke faruwa.Akwai wata rana da bazan taSa mantawa da itaba ranar da mijina ya tafi aiki bayan mun dawo daga rakiyar shi muka wuto gidan su,lokacin ina fama da kwaikwan ciki banda lafiya,ina cikin bacci naji surukata ta she?a mani ruwan sanyi a jikina haka ruwan ya zubo mani har cikin kunnuwa na,a firgice natashi duk na ruWe kamar wata zautatta dandanan sanyi ya rufe ni,nakama kyarma mai tsanani,ban aune ba naji kannensa sun hau dukana suna zagi na kamar wata baiwa,daga bisani muryar suruka tace ta maido ni cikin hayyacina jin abinda take cewa."Ke dan uban ki har kinada damar da zaki kwanta ki mike kafa ki a bacci a cikin gidan nan tunda mijin ki ya tafi bake ba wani baccin jin dadi tashi zakiyi ki girka mana abinci sannan ga wanki can naji ranki saura kiyi wankin banza,idan kingama ki tabbatar kin gyarama su Aisha Wakin su kina jina."?jikina na rawa nace."Toh Mommy."munafukar banza munafukar wofi auraka jakar mata."tabbas maganar ta taSaman zuciya amman ban nuna na damuba saboda nasan mutuqar mijina ya koma aiki ina shiga cikin iftila'i har sai ya dawo nike samun sassauci,haka naje nagama aikin data tasani tas,da kyal na samu waje na zauna ga inada karamin ciki bansan kanshin komai,amman a haka na girka masu abincin da zasuci,ranar ban samu na huta ba har saida aka kira magrib sannan na gama komai." Hawayen da suka ziraro mata tasa hannu ta share taci gaba dacewa."Duk wannan wahalar da nayi bata kareba koda dare yayi kanwar mahaifiya ta, tazo gidan ta iskeni ina shara,jikina na rawa na dukawa na gaida ta,sai ta hau zagina tana tsinata harda duka,cikin kankanin lokaci DANGINMU dangin mu ssukai ta shigowa suna tsinata,mai dungurina nayi mai dukana nayi wasu na ceman shegiya yar iska,kuka nafara ina basu hakuri amatsayin su na 'yan uwana amma basu raga mani ba kuma bansan laifin da mayi masu ba tsabar dukan dana sha ko maganata da kyal take fita ga cikina ya kulle mani kamr zan mutu da kyal na riko hannun surukata nace."Dan Allah kuyi mani hakuri minayi maku kuka tsaneni,kada ku manta nima ?arku ce daga cikin ku nike dan Allah ku yafeman komi nai maku,dan Allah ku faWa mani abinda baku so wlh zan daina na tuba dan Allah kudaina dukana zan mutu...."ban karasa maganar da nike ba naji an wanke ni da marika har sau hudu frgici da azaba yasa ni sakin fitsarin wahala,kafa Fadila tasa ta halbani har saida kaina ya fashe,duk da haka ban fasa basu hakuri ba nagama tsorata da lamarin DANGINMU!har nike7ma kaina tambaya kodai ba daga cikin su aka haife ni ba."Kuka ta kece dashi na mintoci tanajan majina dake neman zubo mata ga jijiyoyin kanta sunyi raWo raWo banda sautin kukan ta ba abinda ke tashi a cikin Kotu saboda kowa yayi tsit dayawan su tausayin ta ya kamasu yayin da wasu kuma kejin haushin ta musamman wasu daga cikin dangin su..."Ke Kotu ke saurare Hajiya Nazima."cewar Barr Nakowa Wago kanta tayi ta daura mashi rinannun idanuwan ta taci gaba da cewa."Ranar wata juma'a ina zaune a Wakin da aka bani a gidan su Ya Nizam wanda baida banbanci da gidan Yari a wajena tunda basu bari in koma gidana idan mijina bai nan basu bari in koma Wakina sai ana gobe zai dawo nike samun yan'ci na har in koma Wakina ina cikin nazarin duniya bansan surukata takirani ba kuma yayar mahaifiya,ashe kirana tayi,tana shigowa tahau yimin masifa dandanan jikina yahau Sari take nafara kuka ina bata hakuri dan nasan yanzun ya'yanta zasuzo su fara dukana,ina cikin bata hakuri naji ta hau dukana da bulala duk yanda naso guduwa nakasa ina mikewa tasa kafa ta taWeni na faWi ruf da ciki wata uwar kara na kwaWa ban kuma sanin inda kaina yake ba,nafi awa hudu a sume,ta kira family doctor ya dubani koda na falko ashe cikin jikina ya zube saida akasa mani drip kwana na hudu sannan na samu kaina."numfashi mai zafi ta fesar tace."Kasan abinda yafi bani mamaki a wannan lokacin Barrister."? Kallan ta Barrister yayi yace."Aa saikin faWa."numafashi taja taci gaba da cewa."koda Doctor ya gama treatment dina,naso su maidani gidan mu,amma mahaifiya ta tace in zauna wajen iyayen mijina ba yanda na iya haka na zauna dasu a Warare saidai abin dayai bala'in daure mani kai sun daina takuraman suka fara bani kulawa ta musamman,ashe duk kulawar da suke bani ta riya ce,mijina ne zai dawo,ba karamin dadi naji ba tunda Mommy ta sanar mani niketa murna har nafi kowa zakuwar dawowar shi,saboda Mommy bata bari ko waya inyi dashi koda kirana yayi zata amshe wayar ta kasheta,sai taga dama take bani mu gaisa shima ta wayarta,duk ranar da nace mashi banjin dadin jikina ranar sai nasha dukan tsiya shiyasa bani iya fada mashi damuwata saidai inyi shiru,ko abincin bata bani inci in koshi asalima mijina zai bada kudi a dinga sayen abinda nikeso na kwalam kasancewar ina yawan kwaikwai ba komai nikeci ba sai tace ko zan mutu ba zanci abinda nikeso ba asalima saidai su cinye ita da ya'yanta ya zama haramiya ta,abinda surukata ta tsira bata tashi kuntata mani sai taga abinda banso ci ko kamshin sa sai tace sai naci shi koda zan mutu haka taita gallaza min azaba banda dukan yau daban na gobe daban,wannan dalilin yasa zuciyata ta shiga kokonto danaga suna bani kulawa kodan sunyi silar zubewar cikima ne shiyasa suke mani haka oho?ashe saboda mijina zai dawo shiyasa na kasance cikin farin ciki marar misaltuwa ranar ko bacci kasayi nayi washe gari ya dawo naita murnar ganin shi,shima haka sai jindadi yakeyi sai dare muka muntafi gidan mu muka cigaba da zamammu cikeda so da kaunar juna bayan kwana biyu, nafara ganin banbanci a wajen mijina sai yafara kyara ta dandanan na shiga matsananciyar damuwa nafara tambayar shi ko lafiya cikeda fada yace."Miyasa zakiyi mani ganganci da ciki,akan mi ba zaki kulaba har cikina ya zube."?bantaba ganin fushin sa ba kamar ranar na shiga rudani saidai nasan tuggu ne aka hada mani amma bam fada mashi sune silar zubewar cikin nawa ba."kayi hakuri bazan kuma yin ganganci da nayi ba."barin gidan yayi yana fada ko magana ya daina yimin kowa ya haWe mani kai gwara Salma ita ke bani kulawa da hakuri a koda yaushe saita kasance ko hidima ban son ta samu a cikin dangin mu,da an haWu hidima za'a dinga yadamani habaici ana zagina ana musguna mani saidai yan uwana suke shigarmani ko mahaifiya ta saidai tace inyi hakuri da kaddara ta saboda haka DANGINMU suke,saina kara jajircewa abinda taje yawan cemani kenan,haka naita hakuri da rayuwa harna samu kan mijina ya dinga kulani har lokacin komawar shi yayi nayi kuka saboda nasan kwanan zancen,haka ya dinga kwantar min da hankali har na dangana washe gari ya koma wajen aiki a yinin ranar saida Fadila,Nafisa da sauran yan matan familyn mu sukayi mani wulakanci suna kirana da karya wai in rabi da Ya Nizam na nace mashi...kowa da abinda yakeyi banda damar tankasu gudun kada mommy taji labari nasan kashina ya bushe shiuasa bantaba rama abinda suke mani ba,bayan kwana biyu ana sunan diyar Ya Hafiz WanWan kanin Abban mu ne,ana cikin suna ina zaune nida Salma muna fira,bansan hawa bansan sauka ba naji sun watsa mani miya a jiki,duk abin nan agaban dangin mu suka watsamin miyar suka hauni da duka suna cemani"maiya kin samu jar miya sai haWama kikeyi munafuka bake ba Ya Nizam dole sai kinbar gidan shi ni Fadila nice matar Ya Nizam."ta ida maganar tana dungurina a ranar ne DANGINMU suka rabu kashi biyu wasu suka shigar mani aka dinga fada,har Hafsat kanwar mijina ta kamani da rigima bansan sadda nai mata maruka har biyu ba.yayyan mu maza suka raba faWan take tsoro ya kamani hakan yasa naki komawa gidan iyayen mijina ga gidan mijina sun rufe shi kuma key na hannun su, nasan muddin na koma gidan mu zan haWu da fushin mahaifina haka nakama laSe har akai isha'i karshe Isah mai magi ya rakani cikin gida tun a kitchen na hadu da Mommy,tun kan intashi daga du?iyar da nayi na gaida ta tafara duka na a gaban mai gadi,ranar saida sukai mani liqis wai na mari yarta Hafsat ranar ko abinci hanani sukayi haka na kwana ina kuka."tsaigaitawa tayi ta share hawayen fuskar ta tace."shin Barrister ko wannan dalilan bazai sa in nemi takardar saki a wajen mijina ba?ba dole naji ban son shiba?kuma dan nace ban kaunar shi nakishi saboda DANGINMU!nasan ko waWannan hujjojin zasu saa tausayama ni asa mijina ya sakeni."ta ida maganar tana kuka mai tsuma rai,shiko Nizam kamar gawa haka ya keta aikin kallan ta ko motsi ya kasayi tsabar mamaki da firgici. Barrister Nafi'u yace."Hakane saidai a wajen ki yake hujja a wajen mu wannan aiba wani abu bane da zaki tursasa mijin ki ya sake ki duba dashi yan sonki."sake mikewa barister Mukhtar yayi yace."Objection my lord yana da kyau lauyan wanda ake kara ya daina karyama mai kara guiwa dan ta fadi hujjojin ta duba da kalar kalubalen d ta fuskan ta dole ta bukaci saki wajen mijin ta,wannan kamar shiga hurumin shari'a ne da hukuncin Alkali,thank you my lord."Cikeda gamsuwa Alkali ya ce. "Ka kiyaye hakan Barr Nakowa,zaka iya cigaba da aikin ka."thank you my lord,sannan yaba Nazima damar zama banda shu'umin kallo ba abinda suke aikama juna musamman Rukayya shiko Nizam idan shi sunkaWa sai kallan Nazima yakeyi kamar wata bakuwa ta koma mashi,jin kiran da Barrister Nafi'u yai mashi yasa shi dawowa duniyar zahiri daga barin duniyar ruWani a hankali ya tashi yaje gaban Barr ya tsaya."Doctor Nizam kaji abinda matarka tace ko kayarda da abinda ta faWa."?Ajiyar zuciya ya sauke yace."naji komai saidai bazan ce ban yarda ba duba da duk abinda akeyi banda masaniya akai nayi takaicin jin wannan labarin."murmushi Barr yayi yace. "Zaka iya tsakinta kenan."Bazan iya rabuwa da matata ba nidai Allah yasani ina son ta kuma ina iyakar kokarina dan ganin na bata kulawar data dace matsalar dangi daban Barr ni da matata bamu da wata matsala Allah ne shaidana kuma ina sonta."jinjina kai yayi yace."kowama ya shaida haka Dr zaka iya komawa ka zauna."maida kallan sa yay ga Alkali yayi yace."Ya mai girma mai shari'a ko da waWannan hujjar ta Nizamuddeen nasan Kotu zatayi nazari akan abinda yace bai zaune duk abinda ya faru baida labarin shi bare har ya dauki mataki,sannan har mai kara zata samu damar hujjar da zatayi dogaro dashi bare har mijinta ya sake ta,dan haka nasan wannan Kotu mai adalci zata duba wannan hujjojina nagode." Komawa yayi ya zauna Alqali yace."Barrister Mukhtar ko kanada abin cewai."?.."banda wata tambaya a hankalin yazun saidai ina so Kotu takara mani mako Waya dan sake wani bin cike a kan wannan shari'ar." Shiru Alkali yayi sai kuma yace."duba da binciken da aka gabatar da yanda akaji daga bakin masu kara da wanda ake kara Kotu ta dage wannan zama nan da kwana bakwai dan kammala binciken da Barrister Mukhtar zaiyi kamar yanda ya buka ta."Buga court stick yayi ya mikeda haka kowa ya tashi saidai kowa da abinda suke cewa wasu najin tausayin Nazima da haka kowa ya kama gaban shi....... *Sdeendtm* I'm sell data to all Nigeria network Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I'm selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp 08066268951 _____________ _Akwai ingantaccan maganin?p? *Sdeendtm* I'm sell data to all Nigeria network Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I'm selling MTN data with

Chapter 6 of 14