Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
yayi wanka ya huta nafisa nacan takai abinci can samanku din. Miqewa sukayi bako kunya hannunsa na riqe da nata harsuka haye. 🌕🌕👉mamuh geee [2/4, 9:25 PM] +234 703 962 5239: 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE ¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo 235~236 Suna shiga palon yasakawa qofar key tareda jawota jikinsa yana jifanta da wani shu'umin kallo daya sakata sadda kai tana murmushi. Gani baida shirin motsawa yasa takamo hannunsa suka nufi bedroom ta dauko towel ta miqa masa yaqi kaba yakuma qi dauke kallonsa akanta. Da kanta ta tubesa tajasa toilet ta hada ruwan dumi a bathtub zata juya ya jawota jikinsa yana qoqarin tubeta ta qwace da sauri ta fice tana dariya. Murmushi yasaki tareda daukar brush. Ko ina nafisa ta gyare sai qamshe da sanyin ac ke tashi dan haka babu abinda zatayi sai kawai ta fitar masa da kayan shan iska takoma palo tazauna tareda qurawa tv ido murmushi da zallar farin ciki na fita a fuskarta. Yana fitowa wanka ya shafa mai tareda saka kayan data fidda masa ya fesa turarukansa masu tsada yafara gabatar da sallolinsa. Tashi tayi tayi dayan bedroom din wanda na waleed ne tayi wanka cikeda farin ciki dan yau sam bakinta yakasa rufuwa. Tana fitowa 'daureda towel sai ganinsa tayi a dakin ta tsaya tana kallonsa shima ita yake kallo jiki amace Dan duk ta kallesa jikinsa mutuwa yake. Ficewa tayi tashige dayan dakin ta xauna gaban mirrow tana murmushi. Riga da skirt tasa na supa red me kwalliyar black dinkin ya xauna daram a jikinta. Daure gashin kanta tayi a tsakar kai da red band me yar kwalliya ta fesa turare yashigo dakin ya jawota jikinsa yana shinshinata. Qwacewa takesonyi ya dago fuskarta yana kallon tsakiyar idanunta aikuwa nan take ya kashe jikinta ta rasa duk wani kuxarinta. Murmushi yayi tareda hade fuskrsu guri daya yana ha'de yawu kafin ya isa cikin bakin nata. Atare suka saki ajiar xuciya yafara kissing dinta cikin sanyi. Yanda suke kissing din ne zai tabbatar da yanda suke tsananin son junansu sbd cikin nutsuwa sukeyi yana shafarta. Hannu yasa ya zuge zip din rigarta tayi sauri juyawa tana fidda numfashi Yajawota ta baya bayan ya xame rigar ya jefar ya birkitota tareda daukarta tayi saurin rintse idanu tana tura kanta a qirjinsa. A gado ya kwantar da ita tareda hawayewa yana aika mata da tsimin son dayake mata. Basu sauko palon qasaba sai lokacin cin abincin dare suka taru duka gidan akaci dinner cikin farin ciki Waleed kuwa kasa taqamaiman me basa abinci akayi sbd kowa basa yakeyi tun daga dad ummi fannah da daddynsa nazli dasu inna iyakacinsu murmushi. Kwanansu biyar suka tattara suka koma abj bayan antura haj bilki gidan yari daurin rai da rai. Sun koma abuja da sati daya suka tattara gabaki dayansu suka wuce cairo inna da nafisa da abdl da ahmd 'yayan saadah kawai aka bari dan har ita saadah aka tafi sbd wani irin janta ajiki da ummin keyi. Ranar dasuka isa cairo taga qauna da gata agurin dangin uwar mijinta marigayiya nyssa. Waleed kuwa sam ita batamasan inda yakeba bare waleed din akwai rashin ji shiyasa yakeda saurin sabo. Duk yanda tameer yaso qin barinta akayi ta kwana gurinsa tanayi masa dariya ya wuce yanajin wani zazzabin dole daya saukar masa. Wasa wasa saida suka share sati tana 'dakin tsohuwa amma ganin da gaske suke ya shirya musu tafiya zuwa greece da uk gurin aminisa EMRAAN da matarsa AYEESHA. Ba yanda sukaso haka yadau matarsa suka tafiyarsu. 🌕🌕👉mamuh geee [2/4, 9:25 PM] +234 703 962 5239: 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE ¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo 237~238 Sabon babin rayuwa suka bude a qasar dan tuni sun manta da nigeria sai luv sukeci abinsu, Sun canza sunyi jajir dasu kullum suna manne da juna dan wani irin so sukewa junansu mai wuyar fassarawa. Dad da fannah da anty saadah sun koma dan waleed dai anbarwa ummi shi a cairo zai zauna. A nigeria dai aure ya tabbata tsakanin dad da anty sa'adah dan andaura inna kuwa qin zama tayi agidan saidai takoma gidansu na kano aka zuba mata yan aikinta qauye dai kuma sai lbr. Duk yanda taso yakice alamarin hameed abin ya gagara sbd ya nace yakoma kalar tausayi dole ta sauke komai ta bada kai bori yahau dan dama tanason abinta. Ba 6ata lokaci suma suka fara zuba luv dinsu danma ta hanasa turowa sai b dinta yadawo. *********** Kwance take tana bacci cikin kwanciyar hnkali tayi wani irin haske ta ciko. Tsayawa yayi akant yana kallonta cikin yar rigar data sa me kama da babu tana baccinta. Komai takeyi kyau take masa hardai yanxu data qara cikowa. Zama yayi bakin gadon tareda shafo fuskarta tayi wani irin juyi tana rungumo hannunsa. Murmushi yayi kafin ya sunkuya daidai kunnanta yace, Missty zamuyi missing flight fa. Bude idanu tayi tana turo baki cikin shagwaba tace, Bacci fa nakeji sosai my meer. Hawa gadon yayi tareda jawota jikinsa yana kallon 'dan bakinta yace, Missty tashi kifadamun wannan sleeping sickness na menene. Kallon fuskarsa tayi sonsa na qara hudata ta shafo fuskarsa tareda kai bakinta cikin nasa. Saidaya kuma wani wankan dan wancan tuni yabi ruwa. Tare sukayi wanka suka shirya tana jikinsa har airport. Suna isa uk emran da kansa tareda ayeesharsa sukaxo daukarsu daga airport din. Kallon juna suke kowacce na maqale jikin mijinta tana tunani to acikinsu wayafi son mijinsa suma mazan tunaninsu kenan na wayafison matarsa acikinsu. Babban hotel din garin suka sauka sbd tameer yaqi yadda su sauka gidan emran din. Abu kamar wasa nazli ta langabe masa gaba daya duk inda zasu tana langabe aikinsa ga yawan bacci da shagwaba. Ba yanda ya iya banda yabiye mata yayita lallaba abarsa. Nanma saida suka share sati biyu suna shiririta kafin suka dawo cairo. Tunda suka dawo yaga yanda umminsa da amma na kula da ita sai okacin yagane cikine da missty dinsa. Nan wata sabuwar rayuwa ta tashi dan qara dauketa yayi sukayi tafiya. Basu dawoba saida cikinta yakai wata biyar harya dan fito kafin suka wuce nigeria sbd takurawar da hameed yayi masa awaya akan fannah taqi bari ayi komai saisun dawo. 🌕🌕👉mamuh geee [2/4, 9:26 PM] +234 703 962 5239: 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE ¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo 239~240 Lokacin da suka iso fannah naganin cikin nazli rungumeta tayi tana murna hameed yadan duqo kunnenta cikin rada yace, Dakin yarda anyi komai da yanxu namiki irin wannan din. Hararar luv ta aika masa tana murmushi. A gidama dai dad da anty sa'adah data canza takoma wata babbar haj murna sukeyi sosai. ********** Tunda suka dawo saiya lallabata take bacci sbd cikin wata muguwar shagwaba yasakar mata da son jiki Jikinma nasa Shikuwa haka yafiso dama. Duk wanda ke gidan lalla6ata yakeyi abu kuwa idan tace shi takeso to anty sa'adah da fannah da nafisa suke taruwa a kicin ayi mata shikuwa boss din shine me bata abaki dan aikin office ma dad ganin haka yabasa hutu har missty din 'dan nasa ta haihu danko yaje yasan ba abinda zaiyi. Rayuwa dai allah ya canzawa nazli ita sbd kaf gidan har cairo itace abinson kowa dukiya kuwa dad yabata kadarori sunfi a qirga sbd itace farin cikin iyalinsa da nasa. ******* Gadan gadan aka fara bikin fannah da hameed wanda sam tameer kasa barin missty dinsa yayi ta sake sosai sbd bbynsa sakuma rashinta da baya iyawa. Ahadai har akayi daurin aure amarya ta tare a gidanta. Kwance take cikin jikinsa yana bata fruitshake abaki tana sha yace, Missty, Yes my meer. I love you. I love u too my meer. Tell me sumtin missty do u.... Washhh ta fada kafin yaqarasa zancensa. A rude ya aje cup din yana tallafota jikinsa. ********* 5yrs later. Missty kinga waccar tanata kallona harda murmushi take aikomin. Ha'de fuska tayi har zatayi maganasaita fasa tasaki murmushin daya qara fiddo da kyawunta aikuwa sai gogan ya ha'de rai yana kallonta Tace, Ya akayine my meer? Missty yazaayi kiyi murmushi agurin nan tunda kinga akwai maza. Dariya tayi tace, Eyya my meer ainayi ne sbd tunowa danayi babu filin ko wace mace azuciyar meer dina. Kamota yayi jikinsa tareda miqewa yana cewa, Muje gida kawai mungama bikin kuma. Miqewa tayi suka fice daga babban qayataccen hall din dake cikin babban hotel na qasar australia dasukazo bikin auren 'dan kanwar mahaifiyarsa nyssa. Mota suka shiga yana tsokanarta tun bata kulasa harta 'bata fuska kamar zata fashe. Suna isowa gidansu na qasar ta fito motar da sauri tayi cikin yayi saurin riqo hannunta yana kiran sunayen 'yayansu dake 'daki tareda nanny dinsu. Da gudu suka fito su biyu suka fada jikinsa suna cewa, We miss u daddy. Kiss yabasu a kumatu yana cewa, I miss u too my angels. Kallon nazli yayi yace musu, Abrar and nyssa oya kuzo kubawa mummy hakuri dad yayi mata laifi. Shida su suka kama kunnuwansu tareda cewa, Sorry mummy. Dariya tasaki tareda rungumosu hardashi suna dariya.. ALHAMDULILLAH. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Nagode allah daya nunamin nagama wannan novel din lpia. Sannan ina miqa godiyata ga masoyana dasuka ringa tayani da addua, Godiya ta musamman ga members na grp din, Mamuh geee fans 1 Mamuh geee fans 2 Sauyin lamari fans Masoyan mamuh geee Novels only Taurarin mamuh geee Da duk masoyana tared writers yan uwana. Wannan takuce ta musamman👉 Husnah bbchoudiallo Maryam matasa Subee umar Zee gummy Fammah gummy Jameela gummy Sis rahamat na lele Amina jaji Xinnie Maman khalid Fain Sis jamila muhd ali Maryam aliya Da duk sauranma daban xayyanoba. Sai mun hade a cigaban auren raba gardama da zuciyarmu daya. 🌕🌕👉 mamuh geee An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9