Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
Zaunawa tayi tana murmushin 'keta saiga haj nurat 'din tafito sbd ansanar da ita tanada bakuwa. Kallon mamaki takebin xeenat dashi kafin tadan saki fuska tana mata sannu suka gaisa aka kawo mata drinks. Ruwan sanyi ta kurba tareda crossing legs tana girgixawa tace, Sunana haj xeenat zaid omar. Kallonta haj nurat tayi dakyau amma bataga alamun hauka atareda itaba saita 'dan saki murmushin ya'ke tace, Allah sarki wane zaid omar 'din? Zaid omar 'kaninki Ni matarsane tsawon shekara uku kenan ina zaune a abuja nigeria. 'Kuri tayiwa haj xeenat tanason tayi tunani 'kwakwalwarta takasa dan ita takasa ma tuno me xeenat 'din tace tsabar rudani. Kafin tace wani abu saiga alh zaid sun shigo shida matarsa dasu tameer Tasaki ajiyar zuciya tana kallonsa dan bakaramin dadin ganinsa tayiba alokacin. Idanunwansa na sauka kan xeenat ya washe baki duk da ya razana sosai da ganinta. Ganin yanda yasaki fara'a be yasa suka kalli juna cikeda mamaki. Haj nurat ta'dan ha'de fuska tace, Zauna ka fadama wacece ita. Zama yayi yana kallon fuskar nyssa dan makaramin so yake mataba Yamaida kallonsa ga yayarsa murya a'dan tsarge yace, Kuyi hakuri naso na bayyana mukune yanda xaku fahinta amma kuma sai abun yazo ahaka Xeenat matata ce, Munyi aure shekara uku yanxu. Kallonsa suke dakyau ba alamar wasa axancensa bari makamancin hakan. Iya 'kuluwa sun 'kulu Nyssa ta mike tareda sa'ba fannah akafada ta fice afalon batareda ko gefensa ta sake kalloba. Haj nurat ma mikewa tayi tashigewarta tabarsu. Mikewa yayi yabi bayanta ta dakata da tafiya ta juyo ba 'bata lkc tace, Tabbas bani bakai idan har kana tareda waccar matar. Zaro ido haj zeenat tayi dan tana labe tana jinsu. Lallai zanyi maganin wannan matar tafada tana 'kafa. Tashin hnkli akayi sosai amma aikin asiri yaki bari yasaketa ga nyssa tuni tafara ciwo sbd mugun 'kullin da haj xeenat tazo dashi ta barbada mata a palo sbd 'karfi da yaji suke zaune gida 'daya. Tameer bayanan yana paris karatu Kwanciyar hankali ta 'kauracewa familyn dan nyssa ciwo ya munana ga xeenat taki komawa Shikansa alh ya susuce gaba 'daya ganin masoyiyarsa kwance rigis. Mahaifiyar nyssa ita takarbi fannah tadawo hannunta kafin nyssa ta warke. Shekara 'daya tana jinya allah yakarbi ranta wanda kuma gurin xuwa gaisuwar munafincine su haj bilki suka zomata da wani mugun aikin daya haddasa fitina gaba 'daya a familyn dan kuwa 'kiyayya mai zafi ta shiga tsakanin dangin nyssa dashi dan gani suke shine sanadi. Hakama 'yar uwarsa haj nurat tayi mummunan fushi dashi tanajin wata irin tsanarsa shima haka yakejin duk tsanarsu dansun tsani matarsa haj zeenat. Da haka ya tattara yabaro cairo yakoma paris gurin 'dansa dan yanda yakejin tsanarsu ko fannah dake gurinsu bazai iya zuwa ya kar'ba ba. Rayuwa tayiwa haj xeenat yanda takeso dan tuni tazama haj babba ga hutu da dukiya dasuka mufun ratsata. Matsalar farko dasuka fara samu itace 'dansa tameer ya girma yazama saurayi yafara 'dorasa adukiyarsa sai abun yafara damunta sbd yanda ta tsani yaron dan ya'dau son duniya dana nyssa ya 'dora masa. Tameer saurayine bamai wasu shekaruba dan duka duka shekarsa ashirin da biyar xuwa da bakwai, Yarone 'dan gata fiye da tsammani, Balarabene sak dan mum 'dinsa ya 'dauko akomai. Dad 'dinsa baya boye sonsa agaban kowa. Ganin 'kiyayya ta ginu tsakanin haj zeenat da tameer yasa ya tattarata yamaidota nigeria dan yanxu babu wani sauran sonta aransa kawai dai zaman ake hakama 'kiyayyar 'yan uwansa ta ragu aransa. Barinta 'kasar yasa tameer yakoma cairo dan kula da kamfunan dad 'din nacan wanda wata sabuwar 'kauna da gata yatashi acan dan kuwa dan lelensu yazama wanda hakan ne yasa yake asangarce duk da ya girma amma idan ka gansa a waje ya iya ha'de gira ba wasa. Zamansa a cairo yasa komai ya cahanxa masu rayuwarsu suke a nutse sai lokaci lokaci yakanje nigeria gurin dad 'dinsa duk da shima bai cika zama a nigeria 'dinba. Wani zuwane dayayi meenah 'yar haj kareema tagansa tace ita duk duniya shi takeso Shikuwa harya koma baimasan dazamantaba. Awata dawowar ne suka aikata masa mummunan aikin tunanan yafara 'dan ciwon kai kafin ya tattara yakoma Aiko yana komawa ciwo ya tabbata hauka. Sannu ahankali abu yaki sauki 'Karshe dai dad 'dinsa yazo yadau 'dansa yafara yawon 'kasa 'kasa dashi amma an tabbatar masa da kwakwalwarsa ta juye. Nijeria ya dawo ya damka kula da 'dansa ga dr sufyan wanda ya budewa babbar asibiti yana sakar masa dukiya. Ahakane wani malami ya tabbatar musu da sammune. Anyi neman maganin sammun har angaji ba wani sauki ga masu kula dashi sai guduwa suke sbd wahalar kula dashi shinefa karshe akayi masa aure dan asamu akula dashi dakyau kafin ya warke ya za'bi zama da matar ko rabuwa da ita. TOFAH..... πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 86β†’90 TASHA...... kiran sallar asuba yasa ta'dan 'dago kanta tana kallon masallacin cikin tashar Bata gani sosai sbd kumburin da idanuwanta sukayi dan tsabar kukan datake sharba har asuba 'din. Maida kallonta inda tameer ke kwance tayi tana kallon yanda sanyi ke ka'da jikinsa yatakure yana fidda numfashi da sauri da sauri. Duddubawa tayi taga inda ake diban ruwa taje ta 'debo tadawo tayi alwala ta tada tameer da 'kyar tayi masa alawa sukayi sallah. Gari na'dan fara haske taga anfara gyar motoci zasu fara lodi ta mike tareda kamosa ta'dau jakar kayansu suka nufi motocin. Da sauri wani yayo gurinsu yace ina zasu murya adashe tace kano. Karbar kayansu yayi yasaka a mota suka shiga atsorace sai rabon idanu take sbd kallon da aketa binsu dashi dan ganinsu kamar larabawa ita buxuwa da zuriar hausawa shima larabe da xuriar hausawa. Tameer gaba 'daya afirgice yake duk da baida lafiya Ganin ana kallonsu saiya 'kankame nazli yana lafewa ajikinta Mutane mezasuyi inba dariyaba ganin 'katon saurayi dashi yana boyewa bayan mace Gashi a fuska kamar jarumi. Dariya ake musu sosai harda tsokanarsu aka fara tana hawaye tayi saurin jansa suka fada motar suka xauna yana 'kankameta. Hawaye take sosai har motar tacika suka tashi bayan ankarbi kudin motarsu. Lafewa tameer yayi ajikinta yana kallon kyakkyawar fuskarta data kumbura Ta'dan kallesa cikeda fargabar abunda zasu tarar atakai dakuma tsoron kada cimar can tayi masa mummunar illah akan wadda yake ciki. Da rana tsaka suka isa kano ta fito rikeda hannunsa tashin hankalinta na tsananta ganin sun kusa isa kenan. Motar 'kauyen takai suka shiga daga cikin tashar Ga yunwa da 'kishirwa dake damunsu su duka hardai ita me juna biyu da duk kaganta kasan cikine da ita. Karfe hudu suka isa takai ana saukesu ta rushe da kuka jikinta na mazari dan tun bata isaba takejin wani irin tsoro na shigarta musamman na cikin jikinta dabatasan yaza'ayiba. Da 'kafa suka isa 'kofar gidan taja ta tsaya cak shikuwa tameer sai shige mata yake sbd tsoron yaran dake biyarsu tun a hanya suna cewa lah buxaye. Hawayen idonta suka gangaro ahankali tasaka hannu na rawa ta shafesu tareda doka shahada tashiga tsakar gidan. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Zaune suke a tsakar gidan sunacin gyada suna rangada fira itada aminiyarta ta kullum wato iya jummai sai karima 'yar iya jummai dake 'dakin babah ladingo itada bubah suna firar soyayya cewar su babah ladingo amma kuma banda tumurmuxarta ba abunda yake a'dikin kuma sarai suna jiyosu amma sai firarsu suke cikin nishadi. Ganin larabawa a gidan yasa suka mi'ke atare suna kallonsu Babah ladingo tayi saurin juyawa zata 'dauko tabarma tana fadin, Sannunku ba'ki kushigo. 'Ko'karin shinfida tabarma takeyi iya jummai data 'kurawa nazli dake hawaye ido tana mata kallon 'kurulla ta waro ido da 'karfi tace, NAZLI Kallon iya jummai tayi murya 'kasa 'kasa tace, Jummai wace nazli kuma salon ki kore manasu 'kila ba'kin arzikine. Da 'karfi taja bushashshen hannun ladingo takaita gabansu tana duba kigan...... Bata 'karasaba sbd cikin jikin nazlin data gani. Tattakewa babah ladingo tayi ta zuba ihu tana kiran jamaa suzo su tayata ganin ankoro nazli da cikin shege datayo da aurenta. A kidime su bubah suka fito yana gyara zaman wandonsa suma a firgice suke kallonta sai alokacin suka lurada balaraben dake bayanta nan take suka rufeta da duka har ita harshi Ma'kabta suka taru ana kallo tareda yin tir da halin nazli datayo cikin shegen aka korota 'karshema cewa sukayi mai gadin gidanne buzu irinta yayi mata ciki aka korosu tare. Labari yakai kunnen me gari ya aiko 'dan aike da wuri akan adaina dukansu akawo masasu yanxu yanason ganinsu dan bazasu zauna agarinsaba. Koda sa'ko ya isa tuni dukkaninsu sun jima da suma tsabar duka. Ruwa aka kelaya musu suka fara motsi Ta bude idanuwanta dakyar tanajin wani irin ciwo tako ina ajikinta. Cikin wata irin dauriya ta daddafa ta tashi zaune tareda jan jiki ta isa inda yake zube ko yatsa bai iya 'dagawa bakinsa da hancinsa na jini haka itama Kuka tafashe dashi tana kiran sunansa agalabaice. Ciccibarsa sukayi itama su iya jummai suka jata kawar kaya akayi fadar me gari dan ladingo ta gwammace ta kashesu data zauna dasu. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 91β†’95 Gaban me gari aka xubesu kamar kayan wanki ko motsi dakyar sukeyi anyi musu raunika bakyan gani. Kallonsu yayi saiyaji wani tausayinsu yashigesa hardai na nazli dayasan mahaifinta sosai da mahaifiyarta kuma yana sane da ukubar datake ciki hartayi aure. Gyara xama yayi yana kallonsu yace, Dukan dakukayi musu bazai bari nayi wani hukunci ayanxuba dan haka abarta ta zauna gidan mahaifinta harta samu sauki sai adawo. Yana fadar haka ya sallami kowa su babah ladingo kamar zata fashe tsabar ba'kin ciki tana fadin, Ni yaushe wannen 'bakar zuri'ar zasu barni naji da'din rayuwata. Da taimako suka iso gidan ladingo naxabga musu harara kamar idonta zasu fado Zuciyarta na tafarfasa kaman ta 'kone jitake kamar ya sha'kesu su mutu ta huta Ta shige 'daki da 'karfi tana huci tareda mukarabanta. Da bin bango ta isa kofar tsohon 'dakinta daya tsufa ya mutu duk ramukan cinnaku da 'beraye yacikashi sbd dama ba siminti ne dashiba. Jiri na 'dibarta ta share 'dakin ta fidda zaninta 'daya ta shimfida a'kasa takoma takamosa ta kwantar dashi akai itama ta sulale 'kasa ko shimfida babu Nan take suka fice hayyacinsu sbd zazzafan zazzabin dayayi musu mummunan kamu sbd azaba. Ruwan randa me sanyin aka antaya musu bokiti guda A firgice ta tashi zaune duk da ba 'karfi ajikinta ko kadan Shikuwa idanu kawai ya iya budewa awahalce dan ko motsi baya iyayi sbd arayuwarsa baisan wahalaba, Jikinsa banda hutu da gyara ba abunda yasani shiyasa yake cikin azaba sosai. Baba ladingo ce tsaye karima agefenta rikeda bokiti. Cikeda ba'kin cikinta takalli shegen buzun ta 'karbi bokitin 'karfen hannun karima xata buga masa akai Nazli tayi surin fadawa jikinsa bokitin yasameta a goshi tuni jini ya 'balle amma hakanan ta daure tana share hawaye. Shewa ladingo tayi tana cewa lallai naga alamar akan wannnan ko'dadden zaki 'dau komai to muzuba nidake dan wallh su buba da iro da idi zansa su jibgarmun shege kekuma ni zanji dake. Tashi nafasa korarku agidana aikin bauta zakuyimun koba komai nasamu bayi Tashi maza wanki zakimun yanxu. A ki'dime ta 'dago sbd tsakar darene gata tana cikin wani hali na ciwo da yunwa ina taga 'karfin wanki. Kan tameer tayi da bokitin a fusace zata rafka masa cikin sauri ta mike tana cewa xanyi wankin. Wata dariyar 'keta suka saki suna kallon wani sabon ikon allah. Tana kallo yana rawar sanyi kamar zai shide sbd sanyi ake ga ruwan da aka zuba musu ga 'dakin ko 'kofa baida Tana kallonsa ahaka ta fice tana hawayen ba'kin ciki. Wankine kamar sunyi shekara basuyi dan harda kayan iya jummai danasu buba dana karimar dana ita ladingo hardana iro da idi. Jikinta na rawa ta fara wankin ko gani batayi sosai ga hankalinta duk yanakan meer dake can kwance cikin ruwa da sanyi. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee. πŸŒ• ⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 96β†’100 Wankine mai yawan gaske na dukkaninsu hardana iya jummai da 'danta iro, Gana buba da idi hardana karima da ladingo. A wahalce take wankin jikinta na mazari sbd zazzabin datake ciki ga sanyi dake kadawa sosai Duk radadin datake ciki Gaba 'daya hankalinta nakan tameer data baro 'dakin kwance yana rawar sanyi cikin ruwa ga sanyi da ciwo. Saida gari yayi haske sosai ta gama wankin dakyar ta mi'ke a duddu'ke tana tafiya dan bazata iya mikewaba. 'Dakin ta nufa tana hawaye dakuma fargabar halinda zata samesa. Kukane tareda farin ciki sukaxo mata lokaci 'daya sbd a zaune tasamesa jingine da bango yana bude idanu dakyar sbd azaba. Da gudu ta fada jikinsa tareda sakin wani irin kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro. Saidata sha kukanta kafin ta mike tareda kamasa tana shirin canza masa kaya sbd ajike yake har alokacin. Jakar kayansu ta duba bataga komaiba. Ta sake dubawa da kyau ba kala ko 'daya aciki Hayaniya tajiyo a tsakar gidan tana saurarawa saita jiyo rabon kayane suke Da sauri ta fita tsakar gidan aiko kayansu kaf Su idi,da bubah, da iro suka rabe kayan tameer Nawa kuwa kaf karima aka ba. Ahankali hawayenta suka cigaba da gangarowa ta juya takoma 'dakin tareda zama kusada shi ta cusa kanta a tsakiyar gwiwowinta tana rero kuka sbd. Kiran tashin hankali ladingo tafara yo mata ta mike ahankali taje fuskarta duk ta kumbura sbd kuka. Aikin gidan tasata harda 'diban ruwa tana gamawa taje tasiyo tameer koko Tana basa yafara kelayo mata amai. Hankali tashe take kallonsa harya gama Ta goge masa jiki tareda gyare gurin. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Rayuwa ta zame musu u'kuba a 'kauyen Tun suna jiran kiran me gari harta daina dan yayi watsi da zancen. Ladingo kuwa duniya tadawo musu sabuwa dan tasamu bayi yanda takeso duk da itake duk aikin dazasu saka tameer 'din kasancewar yanxu agarin kowa yasan lalurarsa ta juyewar hankali. Itake aikin gidan kaf Tayi wankinsu kaf Tayi 'dibar ruwa da abincin saidawar ladingo komai yawansa duk da aikin yafi 'karfinta. Tun yana mata rakin cizon cinnaku harya daina yasaba Yunwa kuwa tasamu kyakkyawan mazauni ajikinsu dan sunyi wata muguwar rama. Fatarsu ta dafe ta lalace sbd sunma manta da wani sabulu ake wanka Sunyi wani furi furi dasu. Tameer yadaina ciwo sosai saidai haukarsa data fito muraran dan yanda idan zasu 'dibar ruwa suna tafiya yana tsince tsince Hakama idan sukaje rafi cewa yake saiya fada ruwan yayi wanka Ga yara da suke bibiyarsa suna masa wakar mahaukaci. Abun nadamunta amma ba yanda ta iya. Tun ana zaginsu da kyararsu har andaina anfara tausaya musu sbd ukubar dasuke ciki sosai. Suturar sawama basuda ita dan kayansu sun ko'de harsun fara yayyagewa. Ahaka Cikinta ya tsufa sosai kuma hakan take duk wahalar Ta bushe bayan kashi ba komai. Soyayyarta da kulawarta kullum akan tameer 'dinta suke, shi kadai ke kawo murmushi afiskarta dan duk takallesa takanyi murmushi hardai idan tana aiki yana damunta da shirmensa. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Zaune take tana wanke wanke cikin sanyin jiki sbd tun daren jiya takejin ciwo ahankali amma take daurewa dan kota nuna ba me taimakonta. Tana kallonsa yana wasa da ruwan wanke wanken amma takasa hanasa hartasamu ta gama dakyar. Gyare gurin tayi ta'dau bokiti tana rintse idanu suka fice zuwa 'dibar ruwa. Shike rikeda bokitin itakuma tana tafiya ahankali sbd ciwonta yafara tsananta. Wata mata data shigo 'kauyen rikeda 'yar ledarta harta giftasu saita 'dan dawo tana kallon nazli tace, Yarinya gidan malam adamu headmaster nake nema dan ya'dan 'bacemun. Lumshe idanu tayi ta budesu dakyar cikin 'dan kannewa tace, Ya rasu tunda dadewa. Salati matar tasaki cikin rawar murya tace, 'Yarsa fa tanan? Dan allah nunamun gidan. Cikin ciwonta daya fara fin karfinta tace, Ni..ni nice 'yarsa. 'Kara dam'ke hannun tameer tayi duk da tana cikin ciwo dan zai iyayi wani gurin. Akidime ta 'kurawa fuskar nazli ido Sai alokacin matar ta lura da halinda nazli take ciki πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 101β†’105 Kamota tayi tana kiran sunanta dan 'kokarin durkushewa take kuma har lkcin takasa sakin hannunsa Matar takalli tameer dakeson kwace hannunsa ya hango kara yanason yaje ya 'dauko. Kamata tace masa tana kamo nazli 'din Kallonta yayi yana son boyewa bayan nazli. Cikin azaba tace bashida lafiyar hnkli. Kamata tayi suka koma gidan dakyar Kai tsaye 'dakinsu suka shiga zuwa lkcn ciwo take sosai. Bakowa agidan dan basanan sunje wani 'kauye bikin suna. Kwantar da ita matar tayi dan dama itake karbar haihuwa garinsu. Cikin ikon allah babu 'bata lokaci ta haihu lafiya 'kalau. Ruwa matar ta 'dora tayiwa yaron data kirada balarabe sbd tsantsar kyawunsa data gani wanka. Kama nazli tayi tayi mata wanka tas kuma allah yasa bayau su ladingo zasu dawoba. Nade yaron sukayi axanin bakuwar dan babu kayan daza'a saka masa. Ido ta 'kurawa yaron tana hawaye dan tasan bazai samu rayuwar jin da'di kamar yanda taso masaba. Kuka take rerowa harda shesheka matar nakallonta harta gama ta matso kusada ita tace, Sunana INNAH ASMAH Tareda mahaifiyarki nataso akayi mana aure tare Tun rasuwar baffana data mahaifiyarki ban 'kara xuwa garinnanba sai yanxu naxo sbd na duba 'yar rahane ashe har malam yarasu an miki aure. Hakanan ta kwashe komai kaf tafada mata tana kuka sosai. Ita kanta innah asmah hawaye take tana sharce majina kafin ta mike tana cewa Nazli wahalarki insha allah takare dan bazan barkiba dake xan tafi. Mikewa tayi tafice afusace tana sharce hawaye. Sai alokacin tameer yashigo 'dakin kayansa sharkaf da ruwa dan tunda suka shigo yanacan tsakar gidan yana 'bata ruwan ladingo allah ma yasa basanan. Da sauri yazo kusa da ita yazauna yana kallon 'dan jaririn dake hannunta yana keta kuka ta rasa yazatayi sai kukan take itama. Washe hakora yayi yana 'kokarin tabashi saiga innah asmah tayi saurin karbar yaron tareda saka masa kayan dataje tasiyo yanxu. Duk wani abun bukata tayi musu dan kwananta biyu kafin su ladingo suka dawo sunyi mamakin ganin na haihu amma ganin innah asmah yasa sukayi biris damu dan tace sai bayan sati zata koma. Tameer kuwa wawa yakoma kan yaron dan rigima yakeyi sosai sai anbashi jaririn Tun innah asmah najin tsoro harta daina dan sosai yake nuna son yaron. Sati nayi suka radawa yaron suna ZAID Nazli nakiransa da WALEED Sun 'dan walwale cikin 'yan kwanakin sbd samun cima mai 'dan kyawu da kula da innah asmah ke musu. Kwananta goma cif ta ha'da kayanta zata tafi da niyyar zata dawo ta tafi dasu wani satin. Hawaye nazli keyi sosai bayan tafiyar innah dan tasan zasu komama wahalane Amma idan ta tuna daxata dawo ta tafi dasu saitaji wani sanyi aranta. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Ahankali dai sai gasu sunkomawa wahalarsu ladingo ga nauyi daya 'karar mata na waleed allah ma yasa tameer takebawashi su zauna 'daki tayita aikinta. Tun tana lissafin dawowar innah harta daina sbd fiyeda wata uku kenan amma babu ita. Wahalarsu ta yanzu hartafi tada dan tuni suka 'karmaje dukkansu hardai ita dake shayarwa. Kullum dare kwana take kuka, Ko aiki take hawaye takeyi sbd tausayin rayuwarsu. Kamannin waleed sun fito sosai da tameer dan kuwa kamar tasu hartayi yawa. Ga wata irin shakuwa dake tsakaninsu danko ita wani xubin yafison tameer da ita. Muguntar dasu bubah kewa waleed yasa bata bari suna fitowa tsakar gidan kullum suna 'kunshe adaki. Akwai ranar da waleed yayiwa ladingo 'barin gari aiko buba yayi ball dashi Ladingo kuwa ruwan talginta ta zuba masa ahannuwa harda sumewa yayi Ranar basuyi bacciba kwana sukayi zaune suka kuka harda tameer 'din sbd yanda yaron hannuwansa suka sale ga wani irin kuka dayake sbd zazzabi da azaba. Komai ya ida jagule musu wuya tayi wuya Ga waleed yagirma sosai harya iya magana Sunkoma suturama saida fadar mai gari taji tausayinsu aka basu kala biyu biyu wanda daga gani kayan sun jima da mutuwa amma haka suka karba suna sawa. Babbar damuwarta baifi waleed da bayajiba gasu sukuma sukamasa suyi masa dukan tsiya kamar wani 'kato 'dan uwansu. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Zaune take tana bawa tameer ruwa sbd ciwo dayake fama dashi tun daren jiya. Waleed ya shigo 'dakin da gudu yana haki yace, Anty kinga wata tana nemanki gatanan xuwa. Zaunar dashi tayi tana cewa, Waleed bana hanaka yawoba. Allah anty banje yawoba ina 'kofar gidafa. Sallamar innah asmah ya hanata yin magana ta mike da gudu ta rungumeta tareda fashewa da kuka. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 111β†’115 Wani wawan haushin kare yaji daga nesa baisan sanda ya juyo da gudu ya fa'da gonar wani wawan jiri da sarawar kai ya ziyarcesa amma baitsayaba saidaya kai tsakiyar titin wanda yayi daidai dakawowar wata mota aguje tayi sama dashi ya zube cikin jin. Akidime nacikin motar yafito yayo kansa yana salati sbd ganinsa cikin jini Juyosa yayi da sauri dan 'daukarsa yakaisa asibiti tunda shi likitane abun zaixo da sauki insha allah. Zabura yayi da 'karfi ya ware murya yace TAMEER Jikinsa har rawa yake yadaukesa yasa amotar ya figeta da wani irin speed sai kano. Asibiti ya wuce dashi kai tsaye aka shige dashi emrgency. Waya dr ibraheem ahmad ya fiddo wayarsa jiki na rawa ya lalubo wata number ya danna kira. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ABUJA Zaune yake cikin tangamemen palonsa Idanunsa sanyeda farin medicated glass Yayi xurfi cikin tunani da damuwa Yau tsawon wata shida kenan da allah yabasa sa'ar kubutowa daga 'yan ta'addan dasuka sacesa suka rufe Tunda yadawo yasamu bayanin 'bacewar 'dansa da nazli abakin matarsa datayita kukan munafuncin cewar ba'asan inda sukayiba anyi nema har angaji. Wannan mugun labarin saidaya haddasa masa kwanciya asibiti tsawon wata biyu a newyork kafin yadawo aka baza bincike tako ina. Wayarsace tayi ringin harta katse bai dubi inda takeba. Haj xeenat data shigo palon cikin ado tana she'ka 'kamshi takalli wayar dan ansake kira tamaida kallonta garesa tana zama kusa dashi tareda 'daukar wayar sbd sunan dr ibrhm data gani dan sam tana kasa nutsuwa a duk lkcn dataji yakira alh zaid sbd tsoron yafada masa komai gameda abunda yafaru. Arikece yake fadin, Alh...alh tameer....gashi nnan asibiti Wat ta fa'da da 'karfi tana mikewa cikin wani irin tashin hankali Jikinta nan take ya'dau rawa. Alh zaid kuwa wayar ya warta da 'karfi yana sauraron bayanin dr ibrhm aibai tsaya jin sauranba yafice palon baikobi takan haj xeenat dake daskare agurin tana aman xufa. Motoci uku na alh zaid da securites suka 'dau hanyar airport adaren dan xuwa kano. Wuraren asuba suka sauka kano kai tsaye asibitin suka wuce Alh zaid naganin yanda tilon 'dansa yakoma ya yanke jiki yafadi. Yana farfadowa ba'a tsaya komaiba ya ha'da 'dansa da dr ibrhm suka bar 'kasar zuwa germany. ******** Jinyarsa ake ana kula dashi sosai a garmany 'din dan tuni su haj nurat suka isa germany 'din suma. Watansa 'daya akwance kuma anasa ran farfa'dowarsa ko wane lokaci. Haj nurat ce da fannah zaune a'dakin. Haj nurat waya takeda ammah mahaifiyar nyssa tana fada mata yanayin jikin nasa Fannah kuwa chattin takeyi da tsadaddiyar wayarta. Ahankali yafara bu'de idanunwansa dasukayi masa nauyi sosai yana gani dishi dishi harsuka bu'de. UMMEE ya fa'da muryarsa bata fita amma cikin sa'a kuwa haj nurat taji hakama fannah. Rige rigen isa gurinsa suke cikin tsananin farin ciki wanda yayi daidai dashigowar alh zaid Farin cikin dasuke ciki baya misaltuwa dan kuwa tameer ya warke ras yadawo cikin cikakken hankalinsa kamar kowa. An sanar da 'yan cairo dabasu sabu xuwa kowa murna yakeyi anata farin cikin. HMMMMMNN WATA SABUWA KENAN. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 106β†’110 Zaunawa sukayi tana lallashinta tace, Nazli kiyi hkr rashin lafiya nayi sosai kuma maigidana ya rasu shiyasa ban dawoba amma yanxu gani nazo kuma ayau zamu wuce basai gobeba. Sharce hawaye tayi gabanta na faduwa hakanan taji gabanta yafa'di da tafiyar. Kallon tameer tayi kafin tamaida kallonta ga inna tace, Inna meer bashida lafiya yazamu iya tafiya dashi. Kadaki damu tunda zai iya tafiya muje damun shiga mota zai aishikenan. Ha'da 'yan tsummansu tayi tana share hawaye dan sam ta rasa nutsuwa batasan dalili ba. Kamo tameer tayi inna ta riko hannun waleed dake murnar zasuje yawo. A tsakar gida suka samu ladingo da iya jummai suna she'ka firarsu Suna ganinmu suka 'daure fuska suna harare harare. Inna ce tayi musu bayanin xata tafi damu har xuwa samun saukin tameer. Harara iya jummai ta watsowa inna tana fadin, Dan wa'innan dangin buxayen masu kama da figaggun kaji to tafi dasu ko aminiyata da 'yayanta sa huta da ba'kin iri. Ladingo kuwa ko kallo basu isheta ba sai ka'da kafarta take. Ficewa sukayi jiki asanyaye. Dakyar suka samu motar 'kauyensu inna. Tunda suka baro gida takasa tsaida hawayenta tana tunanin yaushene zata samu kyakkyawar rayuwa? Itakenan kullum garari yanxuma batasan wace rayuwa zasuyi acanba. Da maraice suka isa 'kauyen da 'kafa suka isa gidan inna. 'Dan 'karamin gidan 'kasane mai tsakar gida da 'dakuna biyu sai 'dan 'karamin ban'daki atsakar gidan. 'Daki 'daya tabasu suka share tsaf tabasu tabarma suka shimfida tareda aje 'yan kayansu. Sanwar abinci inna ta 'dora musu tana gamawa tabasu sukaci suka 'koshi nan waleed yafara wasarsa itakuwa share gidan tayi tas Ana kiran sallah sukayi sallarsu har lkcn kwanciya yayi suka kwanta. Washe garima da kanta ta gyare gidan tayi duk aikin gidan inna na yaba mata sosai sbd tayi 'kokari. Chanjin rayuwa yazo musu sosai sbd yanxu harsuna dariya su 'kyakyata Ga yunwa tuni ta gudu ajikinsu Sunyi 'danyi kyawun gani dan yanzuma kamannin tameer da waleed ke 'kara fita abun har tsoro yake bata Ga muguwar sha'kuwar dake tsakaninsu sbd waleed yasan tameer shine babansa. Hankalinsu yanxu akwance yake basuda matsala sbd inna asmah nada rufin asiri sosai sbd tanada dabbobi da yawa ga sanaar saida kayan 'kulle 'kulle datakeyi. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ 4 month later Tun jiya takejin jikinta asanyaye da faduwar gaba har saida inna ta tambayeta lafiyarta 'kalau kuwa Tace lafiyarta 'kalau. Zaune suke tsakar gidan inna na 'daura kuka datake saidawa nikuma ina wanke wanke. Waleed da tameer ke wasarsu suna dariya sai waleed ya 'dale bayan tameer ya goyasa yazagaya tsakar gidan dashi ya saukesa saiya juya waleed yana 'kokarin shima wai waleed 'din ya goyasa. Daria muka saki duk mu duka waleed ya gudo bayan inna yana cewa, Inna dubi wai saina goyasa babba dashi fa. Daria inna tayi tana cewa, Aini bana shiga tsakaninka da babanka nazo naji kunya anjima dan nasan shiryawa zakuyi. Da gudu waleed yabar bayan inna yana daria shima tameer dariyar yake Nazli ta 'kura masa ido sbd kyawun dataga yayi mata sosai wanda rabon datayi masa irin kallon harta manta Wani sabon sonsa takeji yana sake tsima azuciyarta. Waje sukayi dukkansu suna daria itakuwa taci gaba da aikinta inna ma hankali ta mayar anata aikin. 'Boyewa waleed yayi bayan bishiyar 'kofar gidan tameer yawucesa batareda yagansa ba Shikuwa yana ganin ya wuce fito ya zauna 'kafar gida yana wasar 'kasarsa. Tafiya yaketa famanyi shi ala dole saiya kamo waleed haryayi nisa sosai. 'Karyen 'kauyen yakai ammai bai tsayaba sai kawai yaci gaba da tafiya tun yana gani har duhun mangariba yasawo kai nan take tsoro yafara kamasa Yafara waiwaye yana tafiya da sauri sauri. Har duhu yayi sosai gudu yake ketawa adajin kamar

Chapter 3 of 9