Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
itama ta huta da baqin ciki da wahalar rayuwa. Kuka ta rushe dashi har tana shi'dewa hannu na rawa ta karbi robar batareda ta 'dagoba dan bata fatar sake ganin fuskarsa. 'Dagawa tayi ta 'dora abaki xatasha aka fixge robar da qarfi Atare suka kai kallonsu gareta nafisace tsaye cikin tsantsar takaici tamaida kallonta ga nazli datake faman sheshshekar kuka ahankali kamar ranta zai fita Cikin babbar murya tace, Nazli lokaci yayi dazan daina kallon wannan masifar, Me kike tunani xai faru idan kikasha wannan gubar kika mutu? Me kike tunanin wa inda kikayi shekaru kina wahala sbd su zasuyi da rayuwarsu bayan sun gano ko ke wacece arayuwarsu? Bakya tunanin ya rayuwar waleed xata kasance bayan kin mutu baki ha'dasa da mahaifinsaba. Shin nazli meyasa bazaki daina wahala akan wa'inda basusan kinayiba? Nazli lokaci yayi da sir ta...... Da sauri ta miqe da gudu ta nufi qofa tana wani irin jan numfashi sbd tsabar kukan datake. Caraf ya riko hannunta batareda yakalletaba idanunsa nakan nafisa dake watso kalaman dasuka kusan tarwatsa masa tunani da qwaqwalwa. Kukanta ke qara sauti kuma ahakan nafisa taci gaba da zancenta batareda ta tsayaba. Nazli idan har kinasonsa kinason kare rayuwarsa to tabbas lokaci yayi dazaisan koke wacece. Fixge hannunta tayi da gudu tana kuka sosai ta fice. Jiri ya xubar dashi a kujera kansa na juyawa. Qara hargitsewa tunaninsa yayi sbd bai gane komai na xancen nafisa ba amma ya gane abu 'daya shine zancensu nada alaqa dashi. Duk yanda yaso tashi yabi bayansu jiri hanasa yayi sbd tashin hankali. Da gudu ta isa 'dakin ta 'dibi kudin albashinta ka'dan ta fice gidan da gudu tana wani irin kuka mai tsima rai. Tana fita tasamu taxi ta fa'da sai tasha kuma cikin sa'a mutun 'daya ake jira tana shiga suka tashi suka wuce har alokacin kuka take kamar ranta zai fita sbd ta rabu da tameer rabuwa tahar abada. Tana shiga taga bata 'dakin ta duba toilet bata gantaba. Fitowa tayi tafara dudduba ko ina amma babu nazli Nan take hankalnta ya tashi tuni hawayen takaicin tameer da tausayin nazli ya tsinke mata sbd tana hango tsantsan masifa agaba muddin nazli tace ta tafi kenan kuma itama wallahi tafiyarta xatayi. A ru'de ya sauko zashi 'dakinsu dan gaba 'daya yau idan basan komaiba komai xai iya faruwa dashi dan wata irin rashin nutsuwa yakeji kamar xaiyi hauka. A firgice ta fito 'dakin tana hawaye suka ha'de bakin qofar ya wuceta xai shige cikin muryar kuka da takaici tace batanan ta gudu ta tafiyarta sbd kai, Kaine sanadin komai na wahalarta arayuwa, Meyasa ka kasa tsayawa ka fahimceta kayi mata wannan hukuncin harda baraxanar shayar da ita guba, Shin ko kasan sbd kaine xatasha gubar tabar duniya duk dan sbd kai uban 'dan..... Kasa qarasawa tayi sbd kukan dayaci qarfinta tace nima nasan koban tafiba xamana ya qare a gidannan dan haka tafiya xanyi. Ido rufe ya daka mata wata mahaukaciyar tsawar dabaimasan yayiba ya bu'de ido jajir yace, Har abada bazaki bar gidan nanba harsaikin fadamun abunda yake faruwa sbd xuciyata na gab da tarwatsewa sbd ru'du. Cikin rashin tsoro tana sharce hawaye tace, Ni 'yar aikice banida dama ko matsayin dazan fadi wani abu amma alh da haj da aminanta sunada dama harmada dr ibrhm. Tana fadar haka ta shige 'dakinta ta sulale qasa tana kuka amma tasan allah bazai bari su cutatar da itaba tunda qarshen wahalar alamarin ne takawo idan har tameer yasan komai. A zafafe yake kaida kawo apalon, Banda sarawa ba abunda kansa keyi ga fuskarnan tayi ja abinka ga farin mutum. Zama yayi a 'daya daga cikin kujerun palon yana jiran dawowar kowa daga gurin event 'din dan ayau yakeson jin komai basai gobe ba. Sallamar dad ne da driver 'dinsa janye da 'yar jakarsa yasashi miqewa tsaye cikin godewa allah da dad 'din ya iso yau kuma a daidai lokacin dayake buqatarsa. Kallon mamaki dad yake masa sbd ganinsa a yamutse hankali duk atashe idanunsa jajir. Subhanallah tameer meyene naganka haka hnkli atashe? Fitowarsu haj xeenat da aminan natane yayi daidai da fa'dar maganar dake bakinsa... πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰ mamuh geee [8:55pm, 15/01/2017] β“‚amuh geee: πŸŒ• ⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 181β†’185 WACECE NAZLI A RAYUWAR NAN GIDAN? alokaci 'daya jakunkunan hannuwansu su duka ukun suka kufce musu cikin wani irin mugun tashin hankali. Kallonsu yayi yakaranto tashin hankalinsu tsaf a fili kafin ya maido kallonsa ga dad 'dinsa dashi kuma mamakine xalla afuskarsa na yanda akayi tameer yasan sunan nazli. Murya a sanyaye yace, My son ina kaji sunan nan? 'Yar aikin gidan nance me sunan...fannah ta fa'di haka tana shigowa palon dan dawowarta kenan taji abunda ake fada. Mamakin dad ya qaru muryarsa har rawa take yace, Me aiki anan gidan? Akiramun ita yanxu nan inason ganinta. Wata wawar murdawa cikin haj xeenat yayi ta diro tsakiyarsu da qarfi tana rawar murya tace, Alh ba nazli 'dinsa bace wannan watace dabam. 😳😳 zaro ido su haj kareema sukayi sbd jin 6arin bakin datayi na cewa nazli 'dinsa. Gogan kuwa qara 'daukar zafi kansa yayi jin ta danganta nazli dacewa tasa. Fannah kallon rashin fahimtar komai take musu Dad kuwa rashin gaskiya ya hango tsantsa a tattare da haj xeenat wadda ita sai daga baya ta gane ru'du yasa tasaki layi saita fara kame kame amma ina tuni alh zaid ya nufi hanyar kicin da kansa sbd shi ka'dai yasan irin qaunar dayakewa nazli. Cikin wata wahalalliyar murya yace, dad ta tafiyarta tabar gidan sbd nakamata zata kashe fannah ta hanyar xuba mata guba tasha. Ai mutanen naku najin haka ko wacce saidata kusan tsirgo fitsari suka fice palon da mugun sauri suka bar gidan dan yau qila rana ta 6atar musu. Fannah jikin yayan nata ta isa da sauri ta jirgixashi tace, B pls dnt say that nazli baxatayi hakaba i knw her for sum month amma na karanci halayenta she cant d.... Da qarfi yana tureta daga jikinsa yace, Just shut up. I saw her and she...... Shut up. Shima dad ya katsesa da qarfi sbd ganin abunfa da gaskene akwai gagarumar matsala dabai sanda ita a gidansaba. A fusace yakalli haj xeenat yakalli tameer 'din yace, Weda nazli 'din ce ko kuma wata daban inason tabbas ku nemota sbd koma meyene kune kukasa ta tafi. And as for u dakakeson sanin komai to zan fada maka amma saika nemota duk inda ta tafi. Fadar halinda yashiga abune mai wuya dan kuwa idanunsa har wasu ruwa suka tara Shima cikin mazewa yace, Nikuma na fasa auren meenah saina san ko wacece nazli. A razane dukkaninsu suka maida kallonsu kansa dad kuwa hayewa samansa yayi cikin wani irin yanayi. Da rawar jiki haj xeenat ta juyo xata fara roqonsa ya juya rai abace da sauri ya haywarsa samansa. Juyowa tayi gurin fannah dake hawayen ganin abundake shirin faruwa dasu yau harb 'dinta na tureta da gudu tabar palon tana kuka tayi 'dakinta ta rufe. Gumi ta sharce kafin ta ruga 'daki tadauki wayarta jiki na rawa tana qara hada wani gumin takira kareema ta fada mata wata sabuwar masifar fasa auren meenah da tameer yace yayi. Kaf 'dinsu a daren babu wanda ya rintsa sbd kowa nacikin nasa kalar tashin hankalin bama kamar SIR TAMEER. Washe gari kowa da damuwa yatashi fal danko breakfast babu wanda yayi. Haka take agidansu haj kareema dan kuwa aure dai ya fasu sai ranar dayace iya tashin hankali kam suna ciki. Hardai meenah da haj kareema ta zayyane mata komai hankalinta yayi mummunan tashi jin cewar nazli matar tameer ce. Wata muguwar tsanar nazli ta mamayeta nan take ta'dau waya takira megadi mijin sa'adah tace ta koresu maza maza subar gidan ayau basai gobeba. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Da asuba suka isa kano Idanunta sun kumbura sunyi jajir ko gani batayi sosai tsabar kuka ga ciwon kai kamar kanta da zuciyarta xasu tarwatse. Mashin yakaita har qofar gate 'din gidan ta qwanqwasa kofa abu mai gadi mijin sa'adah ya bu'de gate 'din yana ganinta ya saki fara yana mata sannu da hanya duk da fara'ar qarfin halice yakeyi sbd ya lura da yanayinta. Tana shiga suka ha'da ido da sa'adah data tashi sallar asuba. Kawai saita saki wani sabon kuka tana shesheka kamar me asma tsabar kukan yacita. A rude sa'ada ta rungumeta tana lallashinta har suka samu daqyar sukayi sallah. Har gari ya waye yayi ras suna zaune takasa magana sai kuka takeyi. Waleed natashi daga bacci yaga antynsa da gudu yafada jikinta ta qanqameshi tanajin maseefar sonsa sbd tayiwa kanta alqawarin ta rabu da tameer da rayuwarsa har abada. Sunan xaune ne saiga kiran meenah ta koresu nan wani sabon tashin hnkali ya samesu wanda nazli kukanta ta qaru sbd ta dangana hakan da itace sanadi dan haka zata 'dauki 'danta su tafiyarsu. Nasiha abu yayi mata sisai kafin ta tsaya suka tattara 'yan kayansu sukabar gidan Sai wata babbar unguwar masu ku'di a wani babban gida da aka 'dade da ba abu cigiyar yasamo musu me gadi sai kawai yakai kansa babu 'bata lokaci kuwa aka basu 'dan qaramin boys quaters 'din gidan duk da gidan gidane babba. ********** Duk yanda kowa ya tsammaci abun yawuce nan dan sosai gidan yakoma kamar gidan mutuwa sbd kowa nacikin muguwar damuwa bama kamarsa da tunani da damuwa sufara yi masa yawa har ciwo nason yashigo ciki. Ku'di yasakarwa p'a 'dinsa sosai ana nemanta amma ba wani lbr. Kwance yake apalonsa idanuwansa a lumshe yayi nisa cikin tunani. 'Dayar wayarsace tayi ringin ya bu'de idanu ahankali sai yaga p.a ne akasalance ya 'daga wayar sai yaji yace, Sir dama alh ne yasani 'dauko masa wasu takardunsa acan tsohon gida gashi yanxu nakawo amma bayanan ya fita kuma naga takardun nada mahimmancin da bazan iyaba kowaba saikai. Siririn tsaki yaja tareda kashe wayar ya miqe yasauka palon qasa saiyaga takardun da 'dan yawa ya watsawa p.a kallon wane irin takardune wa'inan. Yayi saurin cewa, Eh dama takardun gidan yace mu 'dauko ta sai muka samesu da wasu sauran takardun daban sai kawai na kwaso masa gaba 'daya. Hannu yasa ya kar6ba tareda hayewa saman. Fannah dake tsaye qofar 'dakinta tana kallon yayanta taga muguwar damuwa tattare dashi ta share hawayen dasuka gangaro mata takira nafisa tace taje takaiwa tameer abinci yanxu ita xata yanka masa fruit tazo dasu. Yana shiga palon yayi wurgi da takardun a kujera suka watse kansa na sarawa yajuya zai shige 'daki ya tsaya cak tareda juyowa da mugun qarfi sbd hotunan dasuka watse daga cikin takardun. Raruma yakaiwa hotunan nan take jikinsa ya 'dau rawa sakamon kansa daya gani tareda wata kyakkawar yarinya kamar balaraba daya sake dubawa saiyaga tabbas nazli ce. Hotunane birjik duk suna dariya da wasa ta daukesu hotunan ga tsantsar so da qaunar junansu dayake bayyane afuskarsu Hotunane datake daukarsu awaya lokacin tana turawa dad sune yasa aka wanko masa tun da dadewa. Baraxanar 'daukewa numfashinsa yayi lokacin daya 'dago hoto na qarshe wanda ashe ba hoto bane katin 'daurin aurene na TAMEER ZAID OMAR DA NAZLI ADO TAKAI. Da akayi shekaru biyar dasuka gabata. A haukace ya 'daga takardar qarshe ta gidace da dad yasaka sunan nazli yabata gidansa dasuka taso. Qoqarin xubewa yake nafisa tashigo tayi saurin aje tray tayo kansa da sauri.. TO FAH YANXU AKE. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 186β†’190 Da gudu ta iso gurinsa tana kiran sunansa. A kujerar ya zube yana dafe kansa dake neman bugawa, Hotunan da katin ya qanqame cikin tashin hnkli yanajin zuciyarsa na wata irin bugawa da qarfi. Manyan idanuwansa dasuka koma jajir ya warowa nafisa saidatayi saurin ja da baya cikin tsananin tsoro sbd gaba 'daya ya birkice yakoma kamar wani jan xaki. Jada baya tafara ganin ya miqe yana jefa mata wani mugun kallo da jajayen idanunsa. Cak ta tsaya tana ha'de yawu a dan tsorace. Gabanta ya tsaya yana mata kallon dayake qara razanata. Hotunan hannunsa da katin 'daurin auren ya 'daga da qarfi ya watsa mata da qarfi jikinsa har rawa yake yace, Waye nazli aguna? Wannan auren, Wannan hotunan, Da wannan.... Just tell me everytin now I want to know every single thing akan auren nan. Zufa ya fara fesowa nafisa tako ina jikinta na 'dan rawa. Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata data mugun razanata batasan sanda tace, KANA CIKIN HAUKA AKAYI AUREN. hawayen dake cikin idanunsa na 6acin rai suka gangaro ya qura mata ido kamar bai fahimci mai tace ba sbd qwaqwalwarsa ta gaza 'daukar xancen. Hauka? Ni? Nayi hauka? Har akayimin aure Dakuma harkar? Sanyi muryarsa tayi sosai kamar yaro yafara roqonta kamar itace boss 'din. Nafisa pls am begging you ki fadamun abunda nakeson ji kada kiyi wasa da tunani ki fadamun gaskia. Ka kamu da lalurar ciwon juyewar qwaqwalwa shekara biyar dasuka wuce, A farkon ciwon alh yayita yawo dakai a qasashe amma babu Wani cigaba saima tsanani da abun yake, Bayan andawo dakai nan ne akayita 'daukar masu kula dakai amma dasun zauna kwana biyu saisu gudu daga qarshe aka kira malami yazo ya tabbatarda aikin sihirine malam yabada shawarar ayi maka aure dan zakafi samun kulawa daga matar datasan kai mijintane. Nazli marainiyace bata uwa batada uba ita aka auro maka. Fa'dar irin baqar wuyar datasha kafi gurin kula dakai zaiyi wuya, Ahaka ta samu..... Shiru tayi tana ha'de wasu yawu sbd tsoron fa'da. Jikinsa ya mutu iya mutuwa saiya bude baki daqyar yace, Kada kiji tsoro fadamun komai pls. Naz....naz..nazli ta...ta samu ci.. Ciki alokacin. Saurin dafa bango yayi sbd wawan jirin daya kwashesa. Sannu ahankali tafara fayyace masa komai na irin baqar wuyar da naxli tasha akansa harda rayuwarsu a takai da kuma gidan innah asmah da waleed da aka haifa masa. Komai bata 6oyeba saidata bayyana masa illah abu 'daya shine mugayen ayyukan da haj xeenat ke aikatawa.... πŸŒ•βšœAM REALLY SORRY FANS DAJINA SHIRU DA KUKAYI TWO DAYS I WAS VERY BUSY NE AMMA INSHA ALLAH YANXU XAKU RIQA JINA. πŸŒ•βšœ LUV U ALL😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘 πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰ mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 191β†’195 Luu ya tafi xai kife fannah dake tsaye bayansu tana wasu irin axababbin hawaye sbd tun fara zancensu tazo kuma taji komai. Wurgi tayi da tray 'din hannunta tayi kansa da mugun gudu yana ganinta ya sulale zaune itama ta zauna yayi saurin fa'dawa jikinta tareda sakin wani irin kuka mai ciwo kamar qaramin yaro. Rungumesa tayi tana gargiza masa kai tana cewa, No b pls dnt cry Kada kayi kuka, Ure breaking my heart. Cikin kuka yake fadin, Fannah i have a son Who is out there yana wulaqantacciyar rayuwa, And she's my wife,my sons mother but babu wanda yadamu da afadamun qarshema a me aiki take acikin gidanta gidan mijinta. Meyasa aka bari matata tazama me aiki anan gidan aftr knowing d fact shes my wife the mother of my son. Why why. I even try to kill her wit my own hands ta hanyar bata poison tasha. Fannah i wnt to see her i wnt to see my son I wnt them both.... Fan fannah i..i..i..... Toshe masa baki tayi tana kuka mai tsanani sbd tsananin tausayin halinda yake ciki dan kuka yake sosai yana sambatun kamar ma ciwon nasa na haukane yataso. Nafisa duqe take agefe tana nata kukan ahankali sbd ganin yanda tameer 'din ya birkice sai sambatu yake cikin kuka fanna na jawasa jiknta tana goge masa hawaye amma sam kamar zugasa sukeyi. Abu kamar wasa tameer ya birkice sosai fannah tun tana kuka kamar ranta zai fita tadawo itama kamar wata zararra gurin lallashinsa amma sam shi ba abunda yakeso sai ganin matarsa da 'dansa. Nafisa tadataga abin yayi tsanani saita 'daga wayar fannah jiki na qyarma takira dad. Yana 'dauka cikin tsabar ru'dewa sai kawai tace masa Daddy sir tameer ya qara hauka..... Bata qarasa fadaba yayi wurgi da wayarsa yayo saman tameer 'din dan yadawo ko minti goma baiyiba da dawowarba saiga kiran. A gigice yashigo palon saiya tsaya turus ciwon xuciyarsa na neman tashi sbd ganin 'ya'yansa zaune a qasa tameer na risgar kuka fannah ta rungume kansa itama kukan tausayin 'dan uwanta take duk sunyi wani iri dasu. Fannah na ganin dad ta 'dan rage kukanta Ya qaraso cikin fargabar idan da gaske 'dan nasa ya qara haukacewa. A tsorace yace, Fannah fadamun abinda yasamu 'dana tun ciwona bai tashiba. Saidata 'dan goge hawayen fuskarta Tace, Dad nazli da ciki ta tafi and..... Kuka yaxo mata Dad ma baisan sanda yajawo tameer jikinsaba yana fadin, Kufadamun ta haihu kadaku cemun na rasa rasa grandson. Lafewa tameer yayi jikin dad murya a dashe yace, Dad ta haifamun 'dana Ur grandson, And natashi da 'dana tun yana jariri, Nayi wasa da 'dana infact he was my friend alokacin, We played as frnds Dad inason ganina tareda shi da nazli, Dad do sumtin I wnt to see them now pls. My heart is beatin faster dad ta6a kaji i cnt breath pls dad i want to see th..... Bai qarasaba yafara wani irin tari Ai nan suka qara rikicewa dad yakira dr da sauri. Dr ibrhm nazuwa yaga halinda yake ciki bai tsaya wata wataba yayi masa allura nan take ya xube yana baccin wahala. 'Daki dad da dr suka kaisa suka kwantar fannah ta lullubesa tana hawaye tareda shafa gashin kansa da ku'din gyaransa dabanne amma yau tashin hankali yasa duk ya hargitse. Bayan fitar dr da dad ta qura masa idanu tana tunano fuskar nazli. 'Dan naxli dataxo dashi suna kano kafin sudawo was her own son amma rashin sani yasa batamayi tunanin dasukazo tace tanason ganinsaba qilama datun anan zata ga wani alamar cewa shi'din jininsune. Allah sarki my b yanada 'da, Ni aunt ce bansaniba. Wani mugun son yaron yashigeta tun bata gansaba tana tunanin irin gatan dazai samu daga gareta kawai kafinsu dad da ubansa gaba 'daya wato b 'dinta sbd ta hango wani irin tsananin son nazli atake dayayiwa b muguwar shiga LOVE AT FIRST SIGHT, To bare abunda ta haifamasa,jininsa,me sunan dad 'dinsu. Data tuno irin baqar wuyar da akace sunsha sai hawaye suka sake 'balle mata. ********* Bai farkaba sai washe gari da allurar data sakesa Kowa gidan cikin tashin hnkali yake banda haj xeenat da itama sam saura ka'dan ta haukace sbd jin nazli ta haihu kuma namiji. Yanda tashin hankalunta yafito filine yasa dad qura mata ido amma sai baice komaiba. Qarshe dai itama allurar akayi mata sbd jininta daya hau lokaci 'daya. Qarfe tara ya farka amma da tashin hnkali dan kuwa wani irin jijjiga yakeyi datasa akayi asibiti dashi hankali tashe. Kwantar dashi akayi asibitin sbd dr ya tabbatar musuda zancen daki xuciyar sosai wanda yaso taba qwaqwalwarsa amma bai ta6a 'din ba saidai kuma fa dole anemo masa matarsa da 'dan nasa. shiru sukayi cikin damuwa hardai fannah da kullum saita kira wayar data siyawa nazli amma batashiga abunda bata saniba shine agidan nazli tabar wayar yashe akashe tun lokacin da tameer ya damqeta da guba ahannu. Kano suka shirya ta jirgi sukaje amma cikin rashin sa'a koda sukaje babusu sa'adah a gidan an koresu. Hankalinsu bai tashiba saida suka kwana biyu akano ana xagayen nemansu harda hotunan nazli ake nunawa a gidan talabijin dakuma kyautar maqudan kudi amma babu wani alamun za'a samesu. Komawa sukayi jiki asalube da damuwa. Sannu ahankali ciwo ke cinsa amma sbd yanason yaje nemansu da kansa yasa ya nuna ya warke dan yanda yakeji aransa idan babusu arayuwarsa xuciyarsa bugawa zatayi ya mutu dan ko ayanxu 'din daurewa kawai yake amma yana cikin tsananin tafasar xuciya. Tunda yadawo gida da hotonta yake kwana wanda fannah tasaka masa a 'dan frame ta dora masa kan bedside drower dake gefen gadonsa. Duk iya yanda yaso sakewa kasawa yayi dan gabaki 'daya farin ciki yabar gidan kowa cijin damuwa yake sbd damuwar son aga su nazli 'din dakuma uwar damuwar da tameer 'din yake ciki. Abinci ma dainaci yayi sai ruwan lipton kawai yakesha shima kullum sai fannah tayi masa kuka tace "B nazli 'dinka babu abinda takeso kaman tameer 'dinta dan haka duk inda take xataji ajikinta meer 'dinta yaqi cin abinci so zata shiga damu... Bata qarasawa yake shanyewa ya miqa mata cup. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰ mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 196β†’200 Haj xeenat al'amura sun tsananta gareta sbd tana cikin tsananintashin hnkli na neman nazli da 'danta da akeyi kullum sai dukiya alh zaid ke sakarwa jamian tsaro gashi ta fara samun matsala da haj kareema sbd auren meenah da tameer 'din da'aka fasa kuma haj bilki bayan kareema tabi abun yana ca6e musu. Hankalinta bai qara tashiba saida taji alh zaid yace angama zuba komai a katafaren gidansa na kano daya maida sunan waleed akan takardun gidan zasu koma kano harsai yaga surukarsa da grandson 'dinsa da tuni an maida sunansa ga wasu daga cikin takardun dukiyarsa. ********* KANO Yau sun tare a gidansu na kanon wansa yake babba sosai shima kuma tsarinsa 'daya dana abj dan haka kamar abj kowa irin 'dakinsa nacan ya 'dauka. Tunda suka iso bai zaunaba kullum yana tareda manyan jami'an tsaron gari ana masa bayani akan binciken. Yau tun safe yayi order 'din masu gyara sukazo 'dakinsa 'daya dake cikin palonsa aka cire komai aka zuna kayan wasan yara kamar hauka da gado da komai na 'dakin na yara ne gar stickers 'din bango na spiders da ben10 komaidai mota,mashin da sauran tarkace. Wardrop 'din 'dakin kuwa kayan da aka xuba sunfi kala hamsin duka masu shegiyar tsada hatta takalmi saidana gaji da qirgawa. Duk na waleed ne his own son and his bst friend.kaman yanda take cewa kenan. A 'dakinsa ma abun haka yake domin kaya na fitar hankali ya siya yacika wardrope 'dinsa dasu duk na nazli 'dinsa dayake cewa she is his savior. Duk abunda yake su dad na lure dashi sbd mugun tausayinsa sukeji dan gaba 'daya kamar a 'dan xauce yake ga ciwo dayake dannewa tsabar qarfin hali. ******** Satin su uku agarin ya 'daga hankalin dad akan saiya kaisa gurin wa'inda aka nemi auran nazli tun farko. Sai alokacin dad yama tuna dasu suka kwasa sukaje su duka har haj xeenat daketa shiryeshiryen cimma burinta dan tayi alqawarin kobata aikasu duka lahiraba ta wlh saita aika koda 'daya tsakanin TAMEER,NAZLI,WALEED,FANNAH KO DAD. (readers wa kuke tsammanin xata kashe batareda xuciyoyinmu sun karayaba ) Koda suka isa gidan haj salamatu tana ganin haj xeenat tahau rawar jiki ba 6ata tym sukace gidansu nazli na takai sukeson akaisu. Mijin haj salamatu yanajin haka yasan kudi zasu samu yace aiba matsala haj salamatu ta tashi suje. Suna isa qofar gidansu nazli na takai nan take guri yacika ana kallonsu sbd anga larabawa. Qofar gidan ya qurawa ido xuciyarsa na harbawa sbd muguwar tausayin wainda ke rayuwa acikin gidan. Savior 'dina anan tayi rayuwa taredani cikin so harta haifi bbynah anan.hw i wish zanganki my savior dazan xa6i rayuwa a inda yafinan muni idan har tareda kene. Hw i wish kin haifamun babys da yawa ba waleed ka'daiba. Fannah ta katse tunaninsa ta hanyar dafasa sbd ta lurada yayi nisa tunani. Su haj xeenat ne suka fito tareda ladingo da jummai sai wani rawar jiki suke har qasa suka xube kamar zasu kwanta suka gaida alhaji zaid. Tameer kuwa kallonsu yake kamar wasu halittu sbd a koma'de suke sai tsami ke tashi tunda suka fito. Suma kallonsa suke ko qyaftawa basayi sbd tunanin kamarsa da shegen mahaukacin nan mijin nazli. Haj xeenat ta katse musu tunaninsu ta hanyar miqa musu bandir 'din dubu ashirin tace su wuce an gode. Kallon rashin fahimta suka aika mata tace, Alh sunce nazli tun 'danta na jinjiri tabar garin tareda tameer kuma basusan qauyen da innah asma take bare su fada. Cikin 6acin rai tameer yace, Dad zai iya yiyuwa qarya suke tunda basa santa ni xan saka police su kamaminsu ayita horonsu saisun fadamin inda my savior take. Da sauri dad ya dafasa yana fadin, Calm down son bazasuyi qaryaba sbd sunga kudi dan dasun san inda take dasun fada sbd kudi. Muje my son ka qara hkr ankusa ganinsu. Jiki asanyaye suka koma kano bayan sun sallami haj salamatu da 'dubu hamsin. ********** CAIRO lokacin da dad yayi waya da haj nurat ya zyyane mata komai itama kukan tasa masa tana fadin a kashe konawa xa'a kashe koma duka dukiyarne a nemo mata nazli da jikanta 'dan tameer 'dinta. Su ammah ma dasukaji 'yar tsohuwar rikice musu tayi jin cewar harda 'da a alamarin kuma ba abunda takeson gani kamar yarinyar dataso tameer 'dinsu alokacin hauka lkcn da bashida kowa. Saurin dangi kuwa banda waleed ba abunda sukeson gani daji. Qarshe dai haj nurat kasa xama tayi ta tarraro tayo nigeria dan sam hnklinta yakasa kwanciya idan basu aka ganiba. Lokacin data iso taga yanda tameer 'dinta yakoma rungumesa tayi tana hawaye shima lafewa yayi ajikin umminsa yanajin wani sabon radadin rashin matarsa da magajinsa. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ NAZLI(mai fans da yawaπŸ˜ƒ) Rayuwa a sabon gidan da mijin anty sa'adah take aiki ba laifi saidai kam ita tuni tayi bankwana da farin ciki sbd rashin meer 'dinta ba qaramar illace ba. Ciwon datake fama dashi a zuciyarta shiya tabbatar mata da ciwon xuciyane yakamata sbd azaba takeji sosai amma haka take rayuwarta sbd bata tunanin akwai ciwon dayakai mata rayuwa babu meer 'dinta. Waleed kuwa ya sake suna zuwa wata makarantar gwamnati dake 'dan kusa dasu kullum mijin sa'adah ke kaisu da qafa yadawo. Ta rame sosai kullum cikin yimata nasiha anty saadah take harta gaji ta bari ta zura mata ido saidai addua. ******* Wayarsace tayi qara yana kwance 'dakin umminsa kansa nakan qafarta tana shafawa ahankali alamar rarrashi kamar shine waleed 'din😑. Ganin yaqi ko kallon wayar yasa haj nurat kallonsa cikin muryar lallashi tace, My boy ka 'daga wayar mana tunda kasan a nema muke zai iya zama cikin masu neman ne wani yagan..... Bata qarasaba ya 'daga da sauri kamar ance masa nazli 'din ce. Hey mr tameer ne kuwa? Yes,yes nine. Hahhhhhhh tameer hameed lamido ne. Duk da yana cikin damuwa hakan bai hanasa farin cikiba sbd jin babban aminsa 'dan govnr din kano dasuka 'dibi shekaru basu haduba sbd kasancewarsu basa zama su duka. Hameed yace 'dazu naga p.a 'dinka a bank yacemun kuna kano ku duka dasu dad. Ajiyar xuciya yasaki tareda cewa Hameed matana da only son 'din sun 6ata anan kano. Wat. Hameed yafada da qarfi cikin shock Tameer ur wife and ur son? To mekayi akan hakan kaga muhadu yanxu kawai dan nima ina kanon. Ok hameed send me ur address xanxo yanxu. Bayan hameed ya turo masa address din ya miqe yafita dan xuwa. Dakansa yake tuqin fannah data biyosa tanagefensa xaune tana waya ammah tana kwantar mata da hankali. Sun shigo anguwar gidan hameed 'din dai dai saura qadan su isa qofar gida wani yaro yafito aguje da 'yar ball 'dinsa kadin tameer yayi wani motsi tuni ya ka'desa. A gigice suka fito motar basu tsaya wata wataba suka 'daukesa sai asibiti. Kunasn waye fans? WALEED NE. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee

Chapter 6 of 9