Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
ba mutumba. Daidai wata gona yakai ya tsaya cak kamar an tsaidashi. Gonar wani bawan allah ce dayayiwa wani kyakkyawan asiri sbd 'barayi duk wanda yashiga gonar indai yanada asiri ajikinsa to zai karye ko wane irine. Soyake ya keta gonar ya wuce yakasa dan tsananin tsoro sbd titin daya hanga motoci na wucewa da mugun gudu dazarar ka wuce gonar. Juyawa yayi da sauri dan komawa inda yafito. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 116β†’120 Gab da magrib ta le'ka 'kofar gidan taga waleed ka'dai tace, Waleed kudawo gida lkcn sallah yayi Ina meer 'din yake? Kwaso kayansa wasansa yayi yana cewa, Tun tuni fa yatafiyarsa yawo nika'dai nake wasana. Dam. Gabanta ya buga tareda ha'de wani yawu da'kyar tafito wajen gaba 'daya ko hijab babu ta riko waleed ta jijjigasa da 'karfi tace, Waleed ina yatafi? Kuma tun yaushe? Anty tunda muka fito baiko tsayaba fa yawuce yabi can. Yayi mata nuni da hanyarda tameer 'din yabi. Cikin gidan takoma a ki'dime jikinta na zuba wani irin 'bari tajawo hijab tasaka a birkice tana 'kokarin ficewa inna tayi saurin kiranta tana cewa, Lafiyarki kuwa inata tambayarki kina 'kokarin ficewa hijab ajuye? Hawaye suka tsinke mata cikin rudewa tace, Inna meer bayanan wai wai baya 'kofar gida ya..ya..y sai kawai ta juya ta fice da sauri Hijab inna tasaka tabi bayanta da sauri sukabi inda waleed yake nuna musu yabi. Yawon nemansa suka fara suna tambayar duk wanda suka hadu dashi har akayi magrib babu wata alamar ganinsa. Kuka take wanda ya gagara tsayawa jikinta Sai mazari yake saida inna ta ri'keta sbd ganin yanda take neman xubewa dan gaba 'daya a ki'dime take Waleed ma dayaga halinda antyn tasa take ciki saiya fara kuka. Har 'karfe goman dare suna yawo saida suka zagaye 'kauyen tas amma babu alamarsa. Da'kyar inna takamota dajan 'kafa suka dawo gidan suna shiga ta sulale 'kasa tareda sakin kuka da 'karfi tana kiran sunansa. Kuka sosai take tana kiran sunansa cikin wani irin ra'da'di da ciwo a xuciya, Yanda take kukan ne kamar ranta xai fita cikin wani irin hali yasa hawaye tsinkewa inna na tausayinta dakuma tunanin wane hali tameer 'din yake. Kamata inna tayi tana 'kokarin tadata sai kawai taga ta zube idanuwanta arufe. Salati tasaki tana yayyafa mata ruwa cikin ru'dewa dan yanda take ganin wani irin tashin hankali daga nazli 'din dan tasan tameer ya 'bata amma tasan nazli zata shiga mummunan halinda yafi wanda zaije yashiga sbd ganin idonta taga yanda naxli ke masifar sonsa fiyeda komai. Tana farfadowa tasaki siririn kuka ahankali inna takaita 'daki tana bata 'karin gwiwar zaa gansa insha allah. A daren ranar basuyi bacciba sbd halinda nazli tashiga dan kuka take babu alamar tsayawa har shi'dewa take Inna hankalinta ya tashi sosai dan tsoron kada wani abun yasamu nazli acikin wannan halin ga waleed ma saidaya sha kukan akaisa gurin tameer kafin inna ta lallabasa da'kyar yayi bacci wanda hakan ya 'kara 'daga hankalin nazli. ********* Duk iya yanda inna ta tsammaci abun ya wuce nan dan saida 'yarta tilo guda sa'adah dake aure a kano tazo dan taimakawa halinda ake ciki Dan ciwo rigis nazli ta kwanta bayan sun share kusan sati biyu kullum suna yawon nemansa har 'kauyukan kusa dasu sunje amma ba wani alamarsa. Tayi wata muguwar rama,kuka da tunaninsa sun zama abincinta, Inna tayi iya yinta amma babu wani sauki har ciwo yayi mata mugun kamu. Inna da sa'adah sosai suke kula da ita har saida tayi wasu sati biyun akwance kafin taji sauki amma ba'a zuciyaba dan kuwa batajin zata ta'ba iya cire tunaninsa aranta. Duk lokacin data tuna cewar bashida kowa ayanxu sai ita gashi tayi sakaci tabari ya 'bata. Al'kawarin datayi na kula dashi yatafi abanxa yakasa kula da tameer 'dinta, Tameer 'dinta datakejin rayuwa babusa batada amfani agareta. Duk wani so da 'kauna ta tattara ta 'dorawa waleed, Shikansa waleed kullum saiya musu rigimar abbansa saisun lallabasa. Ahaka har wata biyu suka shu'de musu kuma tana 'dan sakewa wani lokacin amma shikam kuka kullum daren allah saita sha'ki abinta. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ• ⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 121β†’125 TAMEERβ˜† Yaji sauki sosai ya warware kamar bashiba Kowa ji yake dashi kamarsu ha'desa. Cairo yayi zamansa dad kuwa suka koma tareda haj xeenat datazo dubasa itama. Dad dakansa yasa ayi masa binciken inda nazli take bayan yadawo sbd tameer sam baisan komai gameda ciwonsaba hasalima sun 'boye masa hauka yayi sun fada masa cewar kawai yasamu accident ne. Duk iya yadda dad yaso asamo masa inda nazli take ba'a samu ba haka ya hkr yana adduar allah ya bayyanota kodan auren 'dansa dake kanta. Watansa biyu a cairo yakoma asalin balarabensa yayi wani irin jajir dashi, Yakoma asalin tameer 'dinsa 'dan gaye da tsafta ga class ga nera tuni 'yar tsohuwa ammah(kakarsa mmn nyssa)tafara masa maganar ita aure takeso yayi. Hutawa yakesonyi sosai kafin ya koma office dan haka ya shirya ya wuce 'kasar america. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ 5month ltr Watansa biyar cif a america yana cikin kwanciyar hankali da hutu Ya xabga wani irin kyawu na ha'kika, Fatarsa ta 'kara kyawu na musamman sai she'ki take alamar hutu ya ratsata sosai. Duk wanda yagansa zai 'dauka mawa'kin nanne na larabawa me suna tameer housny. Wani kwarjini da annuri ke fita afuskarsa da duk wadda takallesa saita 'kara kallonsa komai haduwarta da ajinta. Jirgin cairo yabi yana sauka motocin kamfaninsu nanan akaxo 'daukarsa. Sanye yake cikin black jins da red shirt data maseefar yimasa kyawu,sai wasu ha'daddun takarma ba'kake da agogon diamond rolex dake 'daure ahannunsa. Fuskarnan sanye da gogls baki sai hakan yasa kyawun jajayen lips 'dinsa suka 'kara fitowa ga gashinsa dayasha gyara sai she'ki yake. Wani irin 'kamshi ke tashi ajikinsa na turaren signature designer na maza. Kai tsaye gida aka nufa dashi saidaya huta yayi wanka kafin yashirya ya tafi gidan umminsa wato haj nurat. Tana ganinsa farin ciki ya bayyana afuskarta yazo ya rungumeta yana cewa, I miss you so much my ummi. I miss you too tameer ta fada tana jan kumatunsa. Fannah ce ta fito 'daki rikeda waya tana magana da daddynsu aitana ganinsa ta katse kiran tareda fadawa jikinsa tana nurnar ganinsa. Rungumeta yayi shima yana murmushi ya 'dago fuskarta yaja dogon hancinta irin nasa yana cewa, My fannah has grown up but still acting like a bby. Turo baki tayi tana cewa, Pls B. Tafada cikin shagwaba. Ammi kallonsu take cikin tsananin 'kauna tana 'karajin sonsu aranta. Nandanan aka gyare dining cikeda abinci kala kala sbd shi kawai. Sam bai wani ci abincinba dan bayason abinci da yawa. Yana gamawa shida fannah suka fita zuwa gurinsu ammah. Dakansa yake tukin cikin nishadi sbd ganun 'yar little 'kanwarsa dayakeso fiyeda komai tana taredashi. A gidansu ammah suka kwana dan yanda tsohuwar ta rikice masa akan lallai aurensa takeson gani Dakyar ya lalla'bata hardai saida suka kwana agidan. Satinsa 'daya a cairo ya shirya yadawo nigeria dan sam ji yake kamar komai nasa farin cikinsa,ruhinsa,rayuwarsa duk jiyake kamar suna can. Tareda fannah suka taho dan hakanan yanxu bayajin zai iya rabuwa da 'yar 'kanwarshi bare yanxu dazai zauna nigeria gaba 'daya. Dad da kansa yazo 'daukarsu tareda direbansa Yana ganin 'yayan nasa ya rungumesu cikin farin ciki da tsananin 'kaunarsu. Kai tsaye sabon 'katon gidansa mai kamada mention dake asokoro. Babban gidane mai 'daukeda sashe biyu 'Daya na dad da haj xeenat sai 'dayan na sir tameer. GODIA ME TARIN YAWA DA RASHIN IYAKA GAREKU MASOYAN DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngπŸ™πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜ πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰ mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 126β†’130 Haj xeenat nacikin tashin hankali sosai sbd dawowar tameer harda 'karin 'kanwarsa fannah wadda ta gani 'baro 'baro daga dad 'din har tameer ji suke da ita kamarsu ha'diyeta. Babban tashin hankalinta baifi boka dayace aiki bazai 'kara kama 'daya daga cikinsu Sannan gasu liloh sun gudu sunbar 'kasar sbd alh zaid yasansu su suka kamasa dan haka itadasu haj bilki sun basu kudi masu yawa sunbar nan sbd kada akamasu su fa'di sunayensu amatsayin wa'inda ke sasu aiki. Yanxu batada wata sauran dabara data wuce tayi amfani da kissa tasamu yanda takeso dan ta tabbatar da baxata hutaba saitaga bayan tsinannun dangin larabawan. Gate biyune da gidan Na farko securitys ne xube agurin kuma anan duk wasu masu aiki ke tsayawa. Saina biyu idanka shege na farkon shikuma motar masu gidanne kawai keshiga dan duk ba'ki da sauran motacin tsaronsu duk a harabar gate 'din farko ake barinsu. Harabar gate na biyu kuwa duk motocinsune na musamman jere agurin parkin space. Fa'dar tsaruwar gidan tabbas zaicinye page 'din gaba 'daya amma ku kwatanta irin yadda gurin zai tsaru. Flowers ne masu kyau da tsada a harabar gurin ga fitilu masu ban sha'awa rufi da pentin gidan kawai abin kallone. Babbar 'kofar palon shiga palon gidance agurin sai 'kofar garden 'din gidan. Steps uku zaka taka kashiga ha'daddiyar babbar 'kofar palon. Palon ya hadu ya tsaru sosai da royal kushins brown sai komai na palon shima brown tun daga kan cuttons 'din da center crpt,dasu manyan frames daduk wani abun dake palon dan hatta splite a.c guda biyarne a palon. Opposite da dining area dake palon matattakar benene guda biyu suna kallon juna 'daya na hayewa palon tameer da two bedroms dinsa aciki, Sai 'dayan na hayewa 'bangarensu dad suma amma nasu palo da tree bedroms. Palon 'kasa 'din akwai wani palo ha'dadden palo da bedroom 'dinsa aciki wanda aka gyaresa tsaf da komai mai kyau da tsada sbd fannah. Kwanansu biyu da dawowa tameer yafara fita office Hakama haj xeenat ta maida hankali sosai gurin nuna musu so da kulawa na munafinci wanda ba 'bata lokaci ta siye xuciyar fannah tuni dan wani gata da ririta take nunawa fannah Itakuwa fannah dama 'yar tagace sai kawai rasaki jiki tana shagwabarta son ranta Kafin kace me tameer sbd son dayakewa fannarsa saiya fara girmama haj xeenat sosai hardai idan ana dining cin abinci ta kulawa kamar tabasu abaki. Hankalinsu ya kwanta sosai sai rayuwar jin dadi suke da mum kaman yanda suke kiran hj xeent. ********** Cikin nutsuwa yake saukowa daga stairs 'din yana sanye cikin black suit sai 'kamshi yake ya xuba kyawu iya kyau. Fannah tayi saurin mikewa ta tarosa tana cewa, Gud morning b. Morning my little, Daria tayi tana ce masa, B pls inason xanbi mum biki xuwa kano Pls kabarni nabita. Xama yayi kan dining table 'din yana gaida dad da haj xeenat Kafin cikin isa da class 'dinsa yace, Little ure not goin anywhr for now but kibari next mnth am goin there for some work sainaje dake. Shagwa'be fuska tayi tana kallonsa kamar xatayi kuka tace pls b. Haj xeenat tasaki murmushi tace, Alh kasa baki b yabarta taje mana. Aa kunfi kusa amma bari nataimaka muku. Kallon tameer dake kur6an black tea yana duba jaridar yau yayi yace, Son kabarta sutafi since bata ta6a zuwa kanon ba dama and its just a matter of 5 days. Kallon agogon diamond 'din dake hannunsa yayi yace, Shikenan dad since ka amince da tafiyar Mikewa yayi tareda kwasar wayoyinsa yafice dan yanada meeting 9 gashi har 9 'din tayi. B what tym xaka dawo yau sbd i wnt to spend sumtimes wit you cox all diz days bakada tym 'dina koyaushe busy. Kafin yabata amsa MEENAH tashigo harabar gurin cikin wani irin ado najan hankali tana sanyeda doguwar rigar pink lace ya kamata tasaka wasu heels masu shegen kyau sai 'kamshi ke tashi ajikinta. Tun kafin ta iso gurinsu zuciyarta ta buga da 'karfi Tunda allah ya halicceta bata ta'ba ganin ha'dadde,kyakkyawa,cikakke mai class kamarsaba. Wani gigitaccen sonsane ya daki xuciyarta nantake tayanke tasamu mijin aure. Shafo fuskar fannah yayi yace, Take care lttle Yafada motar direba yaja suka bar gidan. Kallon fannah meenah tayi tareda sakin murmushi dan sai yanzu tagano sune 'yayan mijin mummy xeenat 'kawar mummynta. Gaisawa sukayi fuska asake kafin suka shiga palon daidai nan dad yafito shima yabar gidan. Rungumesu haj xeenat tayi tana farin cikin ganin meenah kafin suka 'dunguma xuwa cikin palon. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 131β†’135 Agidan ranar meenah ta yini tanata faman jan fannah ajikinta harsaida suka saba sosai Ta girmi fannah da kusan shekera hudu amma haka dan tanada 24 fannah kuma nada 19. Kamar kadasu rabu haka meenah ta tafi da motarta Tana isa gida ta fada jikin mummynta cikin farin ciki tace, Mummy nasamu wanda nakeso zan aura tameer 'din gidan mummy xeenat. Wani farin ciki haj karima taji dan dama tundata 'kyalla ido akan tameer taga yanda dukiya da hutu tareda jin dadi suka kwanta masa taji tanason meenarta ta auresa dan zasu samu dukiyarda suke burin samu tuni. Kallon 'yarta tayi tana cewa, Bby ai kuwa kinyi miji dan idan har ni haj karima ina yawo saikin auri tameer kin haifamun larabawan jikoki. Cikin farin ciki ta rungume mummyn tana fadin i love you mum. Ta waya haj karima takira haj xeenat tayi mata bayanin komai haj xeenat harta kusan fin haj karima farin cikin hakan nan suka hure kunnan meenah suka koya mata kissoshin dazatabi ta mallakesa wadda ta farko itace ta siye zuciyar fannah wadda ita xata saka tameer yaso meenah tunda yana maseefar son 'kanwar tasa zai iya komai akanta. ************ Burin meenah yacika dan kuwa yanxu sun 'dinke da fannah sun zama aminan juna Kullum suna gurin yawon shopping ko gurin shakatawa Tameer kuwa ya maida hankali sosai akan aikinsa sai kudi dayake sakar musu dan tun yana 'daurewa meenah fuska harya 'dan fara sake mata ka'dan sbd shakuwarta da little 'dinsa. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ 'Karfe biyar jirginsu yasauka a airport 'din kano sbd bikin dasuka xo na 'yar 'kawarsu mummy. Fannah,meenah,mummy karima da mummy balki ne kawai sukaxo mummy xeenat bata samu zuwaba sbd wani uzuri. Daga airport gidan haj karima dake kanon suka dosa Babban gida mai kyau dashi ba kowa sai mai gadi da matarsa dake kula da gidan. Sa'adah 'yar inna asmah itace matar me gadin gidan kuma 'yar aikin haj karima ita ta gyare gidan tsaf tana musu barka da xuwa suka amsa fuska asake kafin kowa ya wuce daki dan hutawa ita kuma ta shiga kicin tafara ha'da musu lafiyayyen abinci. 'Kamshine yacika ko ina agidan na girkin datake tana gamawa ta jere a dining nan duk suka fito kowa yayo wanka yafito cikin shigar shan iska dan sai jibine ma xa'a fara bikin. Saida kowa yazauna dining kafin fannah ta fito daga bedroom cikin 3 quater jins pink da farar vest ta 'daure gashinta dakw lilo har kan bayanta tana waya da b 'dinta. Saura 'kiris sa'adah tasaki drinks 'din data dauko a tray zata kai dining 'din sbd ganin fannah. Ido takura mata tana ha'diye wasu yawu dakyar sbd fuskar waleed 'din nazli 'dinsu data gani sak a fuskar fannah hatta 'dan dimple 'dinsa da dariyarsu komaima sak gashinan illah hutun dake fatarsu ya banbanta. Dakyar ta iya kai tray 'din ta aje tana yiwa fannah data gama wayar ta zauna barka da fitowa Cikeda fara'a ta amsa tana cewa, Lallai xanji 'dadin abincin nan dan 'kamshinsa na da'di. Daria kowa yayi banda sa'adah data 'kara gigicewa sbd maganar da fannah tayi ya 'kara fiddo da tsantsan kamanninta da waleed. Suna gamawa ta tattara gurin takoma tana cigaba da aikinta. Kano tayi musu da'di dan kuwa shakatawarsu suke kafin afara biki sbd kullum suna yawon gari dan yanxu ba 'karamar dukiya suke samu ta gurin fannah ba dan kudi sosai tameer ke sakar mata. A 'bangare 'daya kuwa wata irin shakuwa tashiga tsakanin sa'adah da fannah dan sosai takeson aikin sa'adah sbd tsananin tsaftarta da iya girkinta ga barkwanci da saurin sabo. Jitakeyi badan sa'dah nada aureba da da ita xata tafi dan tanada bukatar 'yar aikin kanta acan sbd duka duka nafeesat ce kawai me aikin mummy dan haka tana bukatar me kula da tsaftar gurin b 'dinta dakuma nata gurin. Fira sa'adah take mata tana yanka mata fruit sukadai ne agidan dan su mummy sun fita meenah kuwa tana 'daki tana bacci. Kallon sa'adah tayi tace, Maman abdul bakida 'kanwa ko wata dakika san ta iya komai kamar ke kikawomin ina tsananin bukatar me aiki gaskia kuma xan bada ko nawa takeso indai har tanada tsafta kuma ta iya aiki. Babu wadda tafadowa sa'adah arai sai nazli dan tasan tama fita iya aiki da tsafta. To amma yazatayi da waleed dan tasan naxli bazata iya rabuwa da waleed ba daidai da minti 'daya bare taje har abuja tabarshi amma xata gwada tagani. Cikin jin dadi tace, Akwai 'kanwata kuwa tana gida ta ta'ba aure mijin ya 'bata tanada 'da 'daya kuma tanada tsafta fiye danima. Farin ciki fal fuskar fannah tace, Yauwa maman abdul kije gidan kijiyo idan zatayi aikin saiku taho tare sbd saura kwana biyar mu koma. Meenah data fito 'daki cikin wata 'bingilalliyar riga ta xauna tana tambayar firar me sukeyi. Fannah tayi mata bayani nan itama tayi naam da hakan tunda dan kula da 'bangaren rabin rantane wanda tuni fannah tasan son da meenah kewa tameer kuma tamata alkawarin ganin ya aureta insha allah. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰ πŸŒ• ⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 136β†’140 Zaune suke atsakar gidan inna na bubbuga 'dan redionta daya tsaya kwana biyu waleed na kwance jikinta yana wasa da zaren tabarma Ita kuwa tanka'den gari take ahankali tayi nisa cikin tunani. Sallamar sa'adah tasa dukkaninsu 'dagowa suna kallonta cikin farin ciki banda nazli datayi nisa cikin tunani. Harsuka gaisa ta zauna inna na tambayarsu abdl data baro nazli batasan me ake ciki ba. Cikin tausayi da jimami sa'ada takalleta tamaido da kallonta ga inna tayi mata bayanin aikin data samowa nazli ta 'dora da fadin, Inna ina ganin kodan asamu ta rage wannan damuwar datake ciki ta 'bacewar abban waleed kuma tasamu tasaka waleed makaranta kodan yanayin rayuwa. Jinjina kai inna tayi cikin gamsuwa da zancen sa'dah amma kuma zaiyi wuya ita nazli ta yarda sbd baxata taba 'yarda tabar waleed ba. Cikin jinjina kai tace, Kinsanfa nazli waleed da tameer sune rayuwarta To tarasa tameer yaya kike ganin xata iya barin waleed dan yanxu ko nan da 'kofar gida bata bari yafita wasa. Waleed ne yafada jikinta da 'karfi yana cewa, Anty ki goyani. Dawowa tayi daga dogon tunanin data fada sai kawai taga sa'adah zaune da inna Ta saki fuska tana cewa, Anty sa'adah yanxu kike tafe, Ya hanya? Inasu abdul? Cikin sakin fuska ta amsa tana cewa, Nazli bazaki hakura ki fawwalawa allah komaiba kullum sai 'karewa kike kinsa tunani aranki fiyeda shekara nawa. Murmushin 'karfin hali tasaki tana danne hawayenta. Inna ta gyara xama ta zayyanewa nazli abunda yakawo sa'adah. Shiru tayi cikin tsananin tashin hnkli amma kuma batajin zata iya watsawa inna da anty sa'adah ido sbd sun taimaketa fiyeda tunani To amma kuma waleed 'dinta fa? Anty sa'dah ce ta katse mata tunani da cewa, Nazli nasan waleed kike tunani To kadaki damu zamu dashi kanon saiki barsa agurina asakasa mkrntar dasu abdl keyi ta gwamnati. Shiru tayi tana 'boye hawayenta na tsananin tausayin kanta da 'danta. Inna tace, Nazli kadaki saka damuwa aranki wannan ba abun damuwa bane idan bakyason zuwa baida matsala munsan halinda kikeji. Share hawayenta tayi tareda rintse ido tace, Inna tunda har anty ta tunada ni ta nuna kulawarta akaina ta taso tazo bazanji dadi ba idan har nayi mata haka dan haka inna inkinyi na'am zanje. Aa nazli kiyi tunani ba abun takura bane. Bakomai inna aitunda aikin na 'dan lokacine tace kuma idan naje naga ba matsala aisaina dawo natafi da waleed 'din kuma aiba tabbata zanyi ba. Sosai suka jinjinawa yanda ta daure tayi musu bazata dan basuyi tunanin zata yarda haka da wuri ba. Harta gama aikinta dare yayi suka kwanta akan gobe zasu wuce hawaye take tanajin wani irin sabon ciwon 'batan tameer 'dinta dakuma jin cewar abj za'a da ita Garin da takejin tsanar shigarsa ayanxu sbd ba tameer 'dinta. Har gari ya waye tayi sallah goge hawaye take. Saida rana suka fito dan tafiya sai alokacin tasaki siririn kuka Inna da itama takejin damuwar kewarsu dazasuyi ta lallasheta suka wuce. Da maraice suka isa gidan me gidanta dake zaune bakin gate na ganinsu yataso yana musu sannu harsuka shige boys quatrs inda anan suke zaune. Sallah sukayi sukaci abinci nan waleed yafara wasa dasu abdl duk da sun girmesa. Sai bayan sallar magrib taja nazli 'din suka nufi sashen mutanen gidan dan gabatarda naxli ga fannah. Zaune suke dukkaninsu a palon suna fira idan kacire fannah dake 'daki tana waya dasu ammah daga cairo. Cikin ladabi sa'adah ta gaidasu Amsawa sukayi suna kallon nazli dake tsaye gefenta sunne dakai. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰ mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 141β†’145 Haj wanannan ita 'kanwata da haj fannah tace nasamo mata yar aiki. Kai sunkuye nazli ta gaidasu suka amsa batareda sun 'kara kallon gefentaba. 'Dakinda fannah take can sa'adah ta nufa nazli na bayanta jiki duk amace. Tura 'kofar 'dakin tayi tareda sallama tashiga suka tsaya nazli na bayanta har lokacin kanta aduke yake. Ganinsu yasa tacewa ammah dasuke waya, granny i will call you later inada ba'ki. Kallon sa'adah tayi tana murmushi tace, Maman abdul sannu da dawowa wanban itace 'kanwar taki? Tafa'da tana kallon nazli. Eh itace gatanan nace muzo ki ganta. 'Dagowa nazli tayi zasu gaisa wani mahaukacin bugu xuciyarta tayi Tari mai 'karfi ya sar'keta su duka sukayo kanta fannah tayi saurin bata ruwan swan dake kan bedside drower. Kasa karbar ruwan tayi ta dafe zuciyarta dake bugawa da 'karfi kamar xata faso ta watse. Kallon tashin hankali takebin fannah dashi Saida sa'adah ta jijjigata da 'karfi ta'dan sauke idanunta 'kasa. Tameer,waleed dakuma wannan budurwar yarinyar komai nasu zak babu banbanci kamar 'yan uku. Tabbas datasan tameer 'dinta nada 'kanwa to da saitace wannan 'kanwarsace, Hakama dah ba ita ta haifi waleed ba to dah tabbas saitace wannan itace ta haifesa. Yawu ta hade dakyar ta gaidata Fannah tasaki ajiyar zuciya tana cewa, Ohh wlh ni harna tsorata. Kallon nazli tayi tsaf taga tabbas babu alamar 'kazanta atareda ita saidai talauci daya koma'data. Gata budurwa kamarta kamar bata haihuba dan badan sa'adah dakanta tace mata ta haihuba da vazata yardaba. Gata Kyakkyawa sosai kamar itama balarabiyarce duk da ta dafe ta 'kanjame hakan hana fannah gano hakanba dan tayi mamakin sam ba xubinsu 'daya da maman abdl ba. Shikenan maman abdl tayi ba matsala saikuje tun anan ki kokkoya mata wasu abubuwan kafin jibi xamu wuce kuma zan ringa bata dubu talatin a wata. 😳zaro ido sa'adah tayi itakuwa nazli bata wani damuba dan babu wani abu dayake burgeta ko aikin zatayine kawai sbd zuciyarta dake ingixata takuma rasa gane meyasa. Godiya sukayi suka fice suka koma can gurinsu sa'adah. ********* Washe gari duk aikin gidan tare sukayisa sa'adah na bata shawarar iya xama da mutane. Sam su haj karima da haj bilki babu wanda yagane nazli ko kusa sbd muguwar canxawar datayi sannan kuma dama can ba wani cika ganinta sukayiba tunda kullum tana sama. Sun fara hidimar bikin daya kawosu dan gobene xaa daura aure amarya ta tare kowa ya watse. Sosai fannah ta fara yabawa da halin nazli sbd yarinyar akwai nutsuwa da tsafta ga wani irin class datake dashi duk da tana 'yar aiki dan bata shiga lamarin kowa saina ita data 'dauketa aiki. Murmushi tayi tana cewa, B nasan zakaji dadin wannan abun danayi mana tunda nasan sarai kana bu'katar mai kulada tsaftar part 'dinka dan nafisat aikin yayi mata yawa da bazata iyayinsa yanda kakesoba. Ranar dazasu wuce kuka take wiwi akan rabuwa da waleed amma haka tayi masa wayo suka fice. Aharabar gidan ta tarar dasu sun fito suka shiga mota akayi airport dasu. Jirgi suka shiga babu bata lokaci suka 'daga xuwa abuja. Da maraice suka isa motar gidan haj bilki tazo 'daukarta Itama haj karima direbanta yazo 'daukarta. Suma motarce tameer ya aiko 'daukarta airport. Suna isa gidan kai tsaye 'dakinta ta wuce nazli na biye da ita sbd babu kowa a gidan Dad baya 'kasar yayi tafiya, Tameer ma bayanan yaje lagos meeting hakama mum tana cikin gari sai dare zata dawo. Akwatinta da nazli ta jawo mata tayi mata nuni data shigar dashi bedroom. Kaiwa tayi tadawo ta tsaya gefe atsaye bakomai hannunta dan fannah tace kada tadauko kayanta zata siya mata kaya idan sunzo nan 'din dan idan b 'dinta yaganta a yamutse zai iya cewa bayason aikinta dan bayason 'kazanta ko ka'dan. Nafisa fannah takira da landline 'din palonta tace tazo yanxu tana nemanta. MUCH LOVE😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘 πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 146β†’150 Turo 'kofar palon fannah 'din tayi tareda sallama ta 'karaso kusada nazli ta tsaya tareda cewa, Gani. Hankalinta nakan wayarta Tana 'kakarin kiran b 'dinta tace, Nafisa wannan wadda zata ringa kula da tsaftar dakina da palona dana b ce kuma ni takewa aiki ba kowa ba atakaice komai nawa dana b Is her responsibility ta kula dashi. Daidai nan tameer yadau wayar ta mike tayi 'daki tana waya dashi. Atsanake suka juyo dan gaisawa da juna Lokaci 'daya kamar wa inda wutar lantarki taja kowanne yaja baya da sauri cikin mugun tsananin ki'dima. Nafisa ce tayi 'karfin halin 'daga hannu tana nunin nazli 'din tana cewa, Nazli kece? Ko kuwa idanuna ne? Nazli datafi firgita sosai dan nan take tafara tunanin kaddai fannah 'yar uwar tameer ce takawota gidan aiki? Idan kuwa hakane kiketa zasuyi saita kaisu gurin tameer Tameer 'din dabatasan inda yakeba Yanacan 'kilama cikin mugun garari. Girgixata nafisa tayi da 'karfi jikinta na rawa ganin sai zubar hawaye take ba magana. Murya na rawa cikeda damuwa da tsoro tace, Nafisa inane nan? Ina haj xeenat? Wacece wannan fannah 'din? Wane gidane nan? Duk arude take watsowa nafisa tambayoyin Itama nafisar arude take Kawai saita damki hannun nazli tajata sukabar palon. 'Dakinta dake gurin 'kofar kicin tajata ciki ta dannawa 'kofar key har alokacin duka hankalinsu atashe yake su duka. Jiyowa nafisa tayi a kidime take cewa, Nazli nan ba gidan kowa bane face gidan alh zaid da iyalansa, Haj zeenat nanan acikin gidan, Sun baro can gidan sun dawo nan ne tun bayan da alh zaid yadawo yatarar da 'bacewarku yakasa zama awancen gidan, Fannah 'kanwar sir tameer ce daya dawo da ita nan tun bayan dawowarsa daya samu lapiya. Tunda nafisa tafara koro mata bayanan hankalinta da nutsuwarta suka fara barin jikinta amma Kalmar nafisa ta 'karshe ita tafi dukan zuciyarta ta razanar da ita fiyeda tunani. Kamar bebiya tafara nuni da hannu tana cewa, Meer...meer...a..a...ina Meer...ya...ya... Ganin takasa 'karasawa dan a birkice take yasa nafisa ta gya'da kai tace, Tabbas nazli sir tameer ya warke yanzu yana cikin cikiakkiyar nutsuwarsa. Dr ibrhm yakira alhaji yace ya bugesa da mota can hanyar wani 'kauye a kano Akayi kasar waje dashi kuma yana farfadowa cikin hankalinsa yatashi wanda kowa yayi mamakin hakan. Nazli babban abun ba'kin cikin dazan fada miki yanxu shine SIR TAMEER BAISAN KOMAI DAYA FARU LOKACIN RASHIN LAFIYARSA

Chapter 4 of 9