Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
BA ma'ana BAISAN DAKEBA BAZAI TINAKI BA. Sulalewa tayi 'kasa tana neman shi'dewa komai na duniyar na juya mata Jitake kamar zuciyarta zata buga Gaba 'daya zantukan nafisa sun hargitsata batamasan wane tunani zatayi ba. Sai alokacin wani irin kuka mai ciwo yazo mata ta 'kankame jikinta tanayi abunta sosai. Yanda take kukan ne ya masifar kashe jikin nafisa dan tana tunanin akwai abunda yafaru akan rabuwarsu. Zama tayi kusada ita tanason ta rarrasheta amma yanda nazli ke kukan tana bukatar abarta tayi abunta kodan samun saukin radadin zuciya sbd kalar kukanta ya bayyana zuciyarta tana cikin wani mugun hali. Tsoro nafisa tafaraji ganin nazli na neman sha'kewa ahalinda take ciki Ta dafata cikin tausayi tana shirin yin magana nazli ta gwalo mata manyan idanunta dasukayi jajir sbd kuka. Girgixa kai tayi murya ashake tace, Dan allah ki fitar dani agidan nan yanxu, Banason bayanke dakika ganni wani yaganni musamman haj xeenat Bakuma zan iya jurar ganin meer 'dina yaganni amma baisanniba, Bai tunaniba, 'Karshema yanamun kallon 'yar aiki Baxan iya jure wannan ba Gwara natafi nakoma nayi jinyar xuciyata dazata rayu da tsananin sonsa da damuwar rashinsa 'karshe ta mutu da sonsa. Nazli kece wadda duk masoyan alh da 'yayansa ke adduar su samu sbd nagani nakuma ji ajikina kece zaki kubutar dasu daga sharrin hajiya. Mikewa tayi tana nufar 'kofa nafisa tayi saurin shan gabanta tace, Nazli ina cikin jikinki dakika tafi dashi? Cikin kuka tace, Babushi ya xube. Garin yaya yazube? Bansaniba nima Tun yaushe? Bazan iya tunawaba Bazai yiyu ba sbd kinason tameer nasani fiyeda kanki dan haka joda cikinsa dake jikinki ya zube nasan bazaki taba manta ranar ba. Dan haka tun yaushe ne cikin ya zube? Shekara hudu. Tafada da 'karfi tana kuka dan duk tambayoyin na nafisa a jere take matasu duk sun rudata dan dama aruden take. Ja baya nafisa tayi tareda sakin ajiyar zuciya tace, Shekarar abunda kika haifa hudu kenan nazli Dan banyarda da cikin yafitaba. Rintse idanu tayi tana jingina da bango hawayenta naci gaba da ambaliya. Gidan takeson bari danji take makar zata 'kone tsabar ciwon zuciya. Cikin hawaye da sanyin murya tafadawa nafisa komai tun bayan barinsu gidan 'karshe ta 'dora da fadin, Rayuwata ba 'daya daga cikinsu wato meer ko waleed to tabbas batada amfani agareni. Inasonsu fiyeda kaina, Inason meer tun bansan soba, Inason duk wani abu daya dangaci meer 'dina shiyasa nakeson waleed fiyeda numfashi sbd duk nakallesa fuskar meer da jinin meee nake gani yana yawo ajikinsa. Inason meer 'dina, Inason meer 'dina kuma meer 'dina yana sona kaman yanda nake sonsa Amma wannan na yanzu ba meer 'dina bane sbd meer 'dina bazai mantani ba, Bazai daina sonaba, Meer 'dina ya mutu ya barni daga yanzu zanyi takabar meer 'dina Nida waleed 'dina munzama marayu mun rasa meer 'dinmu wannan tameer ne yafi 'karfinmu. Kukan tausayinta nafisa keyi tana lallashinta. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh gee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 151โ†’155 Kiranta fannah tayi ta hanyar landline 'din 'dakin nafisa Nafisa tafada mata suka mike gaba 'daya zuwa can 'din. Kaya dake gibge kan kujera ta nuna mata tareda cewa, Ki 'dauka ga kayanan zan siya miki wasuma sbd inaso ki ringa wanka biyu ayini tareda canza kaya dan ki kasance atsaftace koyaushe. Na yaba da tsaftarki amma inaso ki 'kara dan kiyaye duk abunda zai 'bata ran b 'dina. Ki gyara 'dakina yanzu bari ni nashiga wanka. Bedroom tashige tana tubewa tashige toilet. Nafisa ta kwasar mata kayan sta fice itakuma ta gyare gurin cikin sanyin jiki. Tana gamawa ta fito kenan yayi daidai dashigowar haj xeenata dasu haj karima harsun samu fitowa daga dawowarsu dan bata rahoton gurin boka dasukaje can kanon. Zabura tayi da 'karfi taja baya tana nuna nazli tareda ha'de wasu wahalallun miyau. Kallon rashin fahimta suke mata haj bilki takalli nazli tamaido da kallonta ga haj xeenat tace, Me aikin da fannah ce datasa aka samo mata tun akano fa. Afirgice takallesu tace, Kun kuwasan me kukayi barin wannan tsinanniyar tazo mana da wannan Ta nuna nazli a rude. Haj karima tace, Xeenatu kiyi mana gwari gwari mana munkasa gane me kike nufi. Karima nazli ce fa matar shegen tsinannen yaron nan. Meyasa kuka bari tazo da ita? Na shiga uku ni zeenatu meyasa abubuwa ke neman tabarbaremun ne? A kidime suke kallon nazli datati 'kasa da kai tana adduar allah yasa su koreta yanzu basai gobeba tabar gidan dan tabbas bazata iya rayuwa agida 'daya da tameer ba. Wata wawuyar dam'ka haj xeenat takai mata ta shaqota tana fadin, Zo tsinanniya munafuka kibar gidannan yanxu tun wani daga cikin alh ko tameer basu gankiba duk da nasan yanxu baisankiba ko kukuwa wlh nayi miki mummunar kisa. Janta tafara tanajin wata irin tsanarta kamar ta shaqeta ta mutu ta huta. Riqeta haj bilki tayi da sauri tana ha'da zufa tace, Aa wannan ba itace mafitaba agaremuba dan taga inda suke yanxu zata iya dawowa ta baya ta tona asirin komai ta gudu kuma kunga basanin inda takeba zamuyi bare mu 'dau fansa ko mataki akanta. A ru'de haj xeenat tace, To meye abinyi dan namatsu tun kafin shegiyar can ta fito taganmu ahaka tayi zargin wani abin. Haj kareema tace, Mafita 'dayace mu barta anan muna ganin duk wani motsinta da abunda takeyi duk ranar data gudu ko ta tona mana asiri wallahi saimun bashi guba ya mutu tunda shine abunda tafi so fiyeda komai tunda allah ma yasa babu shegen cikinta dayanzu masifar dazamu shiga saitafi haka. Jinjina kai sukayi cikin gamsuwa da bayaninta haj xeenat ta 'dora da fa'din, Kuma duk rintsi kadaki bari alh yaganki kuma kadaki bari tsautsayi yasa ki nuna kinta'ba ganinmu arayuwarki dan kuwa da kaina zan dama guba na basa kina kallo yasha, Bake bashi, Ki tsaya amatsayinki na me aikinsa da tsinanniyar qanwarsa. Idan kikayi ganganci to kisani da rayuwarsa kike wasa dan yanzu tana hannunki. Ficewa sukayi batareda sun tattauna abunda yakawosuba. Kukandata risga adaren bai fa'duwa sbd abun yazo mata ba yanda tasoba. Meyasa koyaushe tameer ne abunda kowa ke amfani dashi gurin quntatar da ita? Meyasa tameer yazama wanda zata iyayin komai akansa har ayanzu dasuka zama duniya daban daban? Tameer shine farin cikinta, Shine baqin cikinta, Shine damuwarta, Shine buqatarta. Kuma shine weak point 'dinta. Yanzu gashi once again zatayi rayuwar wulakanci acikinsu akansa duk da baimasan tanayiba. Amma koba komai zata zauna tayi gadin Koda garin haka zata rasa rantane. Koda garin ya waye fuskarta ta kumbura suntum ko gani sosai batayi amna haka taje tayi gyaran dakin fannah tsaf. ******** Sannu ahankali ta 'dan saba da fannah sbd tana janta ajiki sosai tana kula da ita kamarba 'yar aiki ba. Wasu lokutan kiranta take su zauna tana janta fira duk da ita bata sakewa sosai. Abunda ta lura dashi shine tana tsananin son yayanta sbd takanas ta 'dauketa takaita shago tayo mata siyayyar turaka masu kyau da qamshi da kaya sosai duk dan sbd kada yayanta shaki wari ko tsami idan tana masa aiki. Itadai damuwarta duk kayan yawancinsu dogayen rigunan kantine masu kyau da 'dan kama jiki. Amma haka take sakawa atakure tana aikin. 'Bangarensu haj xeenat kuwa ido sosai suka saka akanta. โšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœ Duk inda nutsuwarta take bata jikinta yau dan yau tameer zai dawo Tun safe aka bu'de mata sashensa amma takasa shiga ta gyara saida nafisa takama hannunta suka hau saman har cikin tsakiyar palonsa kafin ta juya ta fita. Lumshe idanu tayi tana tsiyayar hawaye. Komai na palon tsaf yake sai 'kamshi dake tashi duk da 'dakin ya kwana biyu bakowa. Daqyar ta lalla'ba kanta ta gyara palon da bedroom ta fesheshi da airfreshner masu da'di ta kukkuna ac ta rufo qofar ta fice. Girki na musamman sukayi hadda fannah 'din sai farin ciki take ga aminiyarta meenah tuni ta iso taci wani irin ado dan tarbar tavin ranta. Suna gamawa suka jere a dining fannah tayi gurin wanka bayan ta umarceta da itama taje tayi wankan dan driver yaje 'daukarsa daga airport. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 161โ†’165 Cikin rashin bawa xancen mahimmanci yace, Tunda kunaso zan duba nagani. Mikewa yayi yabar gurin yana xuba hannuwa a aljihun wandonsa. Dai dai xai shiga 'dakin ita kuma ta fito 'daukeda glass cup din fresh milk sukayi wani wawan karo Fresh milk 'din tazube ajikinsu gaba 'daya tayi baya da qarfi cikin tsoro aikuwa ta taka wadda ta xuba a qasa santsin tiles yayi mata mummunan ja ta tafi da qarfi zata xube Wata fixga yay mata ta fado masa da qarfi saikuma suka zube gaba 'daya. Fannah dake tsaye ta dariya ta kufce mata dan tun qarar faduwar cup 'din ta taso dan dubawa komai akan idonta yafaru. Dariya take sosai kamar 'yar bby sbd ganin yayanta kwance cikin madara har a fuskarsa ga nazli itama duk ta 6aci da madarar sai suka koma kamar wasu yara. Saurin tashi tayi daga jikinsa ta bar gurin da sauri idonta na qoqarin kawo ruwa dan haduwar jikinsu ya zaburo mata da tsimin sonsa datake neman dannewa. Mikewa yayi yana ha'de fuska yayi hanyar stairs dinsa. Gaban madubin bedroom 'dinsa ya tsaya sai kwai yasaki murmushi dan komawa yayi kamar yaron da yayi 'banna. Wanka yayi yayi sallar magrib yazauna palon yakira fannah. Da sallama tashigo palon itama ta canxa kaya tana 'daukeda tray 'din farfesun kifi da akayi masa fannah na bayanta. Ajewa tayi tana mikewa fannah tace, Nazli ki xuba masa saiki 'dauko ruwa da drinks ki kawo masa. Riko hannunsa tayi tace, B pls get married, I really want to see you happy kuma inason naga 'yan babys sun fara kirana aunt. B pls do dis for me qnd marry my friend meenah. Na yaba maka da ita and you knw i always choose wats best for you. She's very nice, Kind and gud..bayan wannan she really loves you. Kallon tv yake yana saurarenta jin muryarta ta fara rawa kaman xatayi kuka yasa ya juyo aikuwa hawayen take Jawota yayi jikinsa yana cewa, Little youre askin for sumtin dat i dnt really tink i can do for you. Marriage is not a joke or sumtin simple. Its abt my future,my happiness my..... Daz y i want you to get married b bcos i want to see u live a happy life.. Pls pls b do this for me, Do this for ur little sister. Zanyi tunani little but for now pls kibar xancen okey? Kai ta 'daga cikin tana murmushi. Miqewa tayi xuciyarta na bugawa da qarfi kamar zata fashe. Kishinsa takeji yana kona zuciyarta ta fice da sauri tabar palon ko ruwanma bata 'dauko masaba sai dai fannah ta kawo masa. Sosai ya lura da yanayin data shiga amma ya basar sbd baisan dalilin shigarta halinba. Kuka ta la6e ta risga a 'daki har saida taji kanta na sarawa kafin ta lallashi kanta ta fito. Da daddare harta kwanta fannah takira wayarta data siya mata dan irin haka. Nazli pls ki kaiwa b hot coffee yanxu yanacan yana jira. Kicin ta nufa ta 'dora yanayi ta juye tadauka ta nufi 'dakinsa. Apalo ta tarar dashi zaune da farar singlet da farin dogon wandon bacci mai taushi yana aiki da laptop. Duqawa tayi ta aje tray 'din akan center table 'din dake gabansa, Qamshin turarenta ya daki hancinsa ya lumshe ido batareda yakalli gefen datake ba. Mikewa tayi zata fice saitaji tanason kallon fuskarsa ta juyo ahankali idonta tab da hawaye. Juyowarta tayi daidai da 'dagowarsa idanunsu suka shiga cikin na juna. Qurawa juna idanu sukayi Tsantsar damuwa yake hangowa a idanunta yayinda ita kuma take hango rayuwarta a idanunsa. Hawayene suka gangaro mata ta juya da gudu ta fice tana toshe bakinta sbd kukan dayazo mata. Qofar yabi da ido cikeda mamaki Dan iya tunaninsa magana bata taba shiga tsakaninsu ba amma yanayin yanda ta kallesa kamar tasanshi yayi mata wani laifi. Shafo fuskarsa yayi yana ayyanawa aransa akwai wata damuwa atare da ita. ********** Bayan 'dan lokaci ya amince da maganar auren meenah badan yana sonta ba sai dan yanda fannah ta damu sosai akan zancen dan shi sam beyi wani tunanin xai iya samun lokacin kula mace bare soyayya ayyukan gabansa ma kawai sun ishesa arayuwa. Meenah,haj xeenat,haj kareema,haj bilki da fannah ji suke kamar su taka kan jariri sbd farin ciki, tuni aka fara shirin biki sbd har dad yazo ankai qarshen komai. meenah tuni ta dawo gudan da xama dan idan ba ita ta nemesaba baya bi takan zancenta saiya xama itake zuwa fira 'dakinsa. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 166โ†’170 Zaune suke a garden 'din gidan yana waya dasu ammah akan sha'anin bikin yace suyi zamansu basai sunxo ba bayan bikin zasuzo tareda meenah 'din. Meenah dake zaune taredashi tasaki wani murmushin farin cikin samun cikar burinta dan yanda takeji ko kisa xata iya akan tasamu tameer. Miqewa yayi sbd umminsa haj nurat data karbi wayar zasuyi magana kasancewar yasan batason auren da meenah yasa yatashi ya zagaya yana wayar 'dayan hannunsa na sanye cikin aljihun 3quater jins blue dake jikinsa da farar body hug. Yana cikin yin wayarne yaringa jiyo sheshshekar kuka natashi ahankali. Ignoring yayi yana cigaba da wayarsa. Sautin kukan yafara yawo a kunnuwansa har baya iya fahimtar me umminsa ke cewa, Ya rintse idanunsa yanason kukan yadaina damunsa amma ina saima qara shigarsa yake haryana dukan zuciyarsa. Bayan flowers 'din gurin ya nufa sbd daga can kukan ke fitowa. Duqe take tasaka kai atsakiyar qafafunta tana rero kukan. Bayanta ya kalla ya gane 'yar aikin nance. Juyawa yayi yana 'bata fuska yana jin haushinta aransa na yanda takeda damuwa takasa fa'da ataimaka mata tunda tasan fannah zata iya taimaka mata da koma nawane. Cak ya tsaya xuciyarsa na tantama sbd sunansa dayaji ta fa'da cikin kuka. Tameer,meer meyasa rayuwata take wahala haryanxu akanka? Meyasa zan zauna dan ganin wannan baqar rana agareni duk dakai farin cikine agurinka. Waleed 'dina zai tabbata a maraya kenan shima baqar rayuwar danayi ita xaiyi sbd rashin mahai.... Bata qarasaba kukanta yaci qarfinta duk da bata bari sautinsa yafuta ba. Xuru yayi qwaqwalwarsa a cunkushe dan baisan tunanin dazaiyiba. Baimasan me zancen nata yake nufiba, To amma meyasa sunansa yashiga zancen nata? Kodai bashi tameer 'din ba. And waleed? Who is that waleed she's talkin abt? Is he her hus... Juyawa yayi yabar gurin dan tuni kansa ya fara sara masa. Baikoma takan meenah ba yawuce 'daki kai tsaye. Da daddare data kawo masa fresh milk ko kallonta baiyiba sbd bayason yaringa damun kansa da abubuwan daba serious ba. Juyawa tayi ta fice jiki asanyaye kamar mara lafiya. Bayan ta fita saiyaji yana buqatar coffee sai bai nemi fannah ta turo masa ita ya miqe yasauko dakansa dan yasa nafisa tayi masa sbd ita 'din ya lura kaman tana cikin tough time. Ba kowa apalon dan haka ya nufi qofar 'dakin dan qwanqwasawa Hannu ya 'daga zai buga maganar nafisa ta daki kunnansa, Nazli pls kadaki bari ayi wannan auren ki fito ki fa'da komai Ki bayyana musu waleed da gaskia sbd da anyi wannan auren babu wata mafita dan kuwa burinsu yagama cika akansu. Kuma dolene sir yasan gaskia wata rana dan haka gwara ki sanar ma...... Cikin tsananin kuka tace, Nafisa babu gurina arayuwarsa yanxu, Yana cikin farin cikinsa bazan katse masashiba dan tarayyata dashi ba abunda yaja masa sai wahalar rayuwa da qasqantacciyar wahala. Kasa sauraron sauran yayi yajuya yabar qofar 'Daki yakoma yakasa zama ya kasa tsayuwa so yake ya gano me suke nufi amma bai ganoba qarshema ciwo kansa yafara saiya kwanta kawai. Tundaga lokacin yafara saka ido akanta sbd hankalinsa ya kasa kwanciya akan xancensu duk da yanada tabbacin wani tameer ne suke magana akai. ************** An fara shagalin biki sosai dan dukiya alh zaida da tameer suka sake musu anata shagali duk da dad bai dawoba sai saura kwana 'daya 'daura auren. Shagali sukeyi sosai duk da angon baida lokacinsu saisu ka'dai suke bidirinsu sudai suga an 'daura auren. Duk iya yanda ta kama kanta sosai ta danne xuciyarta hakan bata faruba sbd muguwar rama tayi sbd tsananin damuwa da tunani dan yanxu kukanma ya daina zuwa saidai idanuwanta su ka'da suyi jajir. Fannah da kanta tasata agaba tace nazli bakida lafiyane ko kinada damuwar zama damune? Kai kawai ta girgixa mata. Kula da abincinsa yana kanta dan tun fara biki fannah take jaddada mata hakan. Toilet 'dinsa take wankewa cikin cikin tsautsayi bakin taje kunna tab saita kunna shower aiko ruwan sukaxo da qarfi nan take suka jiqata jagab. Dan qaramin tsaki rana kallon yanda ta jiqe gaba 'daya har gashinta. Sanin bayanan bakuma kuma baya dawowa sai maraice yasa ta Xame hijab 'dinta ta shanya a toilet din hakama doguwar rigarta danso take kafin tagama sun 'dansha iska. Bra ce fara qal ajikinta da farin under skirt tsaf dasu kamar sabi sbd sosai fannah ke siya mata duk wani abun buqata. Zaune yake a sit 'din baya yana sanye da suit black masu red tie sai qamshi yake zubawa driver na tuqasa. Wayarsace tayi qara ya duba saiyaga p.a 'dinsane cikin qasaita ya 'daga wayar. P.a dinsa yace, Sir am sorry walh meeting 'dinnan sun aiko wai sunada babban uxuri an 'daga sai gobe kuma. Kasa magana yayi sbd haushi sai kawai ya datse kiran ya kashe wayoyinsa gaba 'daya yace driver yamaidashi gida yama fasa xuwa office 'din yau gaba 'daya. A gate 'din farko yace driver ya ajesa ya aikesa office shikuma ya taka ya 'karasa wanda hakan ya hana sam tasan da yadawo. Dai dai qofar shigowa palon yaci karo da fannah tana riqeda coke ahannunta tanasha zata fita cikin sauri dan xuwa gidansu meenah sbd yaune suke qunshi. Gaba 'daya coke 'din ta 6atasa Ya rintse idanu cikin takaici kafin ya wuce da sauri yana ce mata ta tafi kawai tunda yaga she's in hurry. Yana shiga palonsa yasawa qofar key dan bayason adamesa wanka kawai xaiyi ya huta. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 171โ†’175 Yana shiga bedroom 'din ya kalli jikinsa yana 'dan yamutsa fuska dan yaso yana dawowa ya kwanta ya huta amma yanxu saiya kuma wani wankan. Tu6ewa yayi ya 'daura farin towel a qugunsa kyakkyawan jikinsa da lafiyayyar fatarsa sai sheqi suke alamar hutu daya ratsasu. Kai tsaye ya bude qofar toilet 'din yashiga tareda rufowa. A firgice ta 'dago daga duqen datake tana canxa ruwan cikin bathtub. "Ohh my god" ya fa'da yana kare idanuwansa da hannunsa cikin wani irin tsoro da ganin dirinta daya kusan tafiya da numfashinsa dan nan take yaji wata sha'awa ta taso masa. Gabaki 'daya rikicewa tayi tama rasa yazatayi ta fito dan wani santsi ke janta yana maida ita tama kasa fitowa bare takai gurin kayanta. Jin tasaka fitowa sai zamewa take yasashi matsowa ya miqa mata hannunsa danshi amatse yake data fice dan ya rikitu sosai ga qamshin turarenta daya cika gurin. Qaf qaf tafara da idanu tana sake qoqarin fitowa batareda takama hannun nasaba. Zamewa tasakeyi shisaima tabashi daria ya saka hannuwansa biyu ya 'daukota gaba 'daya aiko bai qarasa fitowa da itaba santsi yajasu gaba 'daya suka fa'da cikin bathtub 'din hannunsa ya bugi shower saiko ta fara sako musu ruwa. Itace a qasa shine asamanta jikinsu ya ha'de sosai gashi babu me kaya ajiki acikinsu Nan take suka shiga wani yanayi sbd body contact dasuka samu. Qurawa juna idanu sukayi basako qyaftawa duk da ruwan shower dake xuba akansu. Hannu yasa ahankali ya matsar da dogon gashinta daya jiqe ya 'dan hawo gefen fuskarta. Cikin wani salo ya janye da gashin yana kallon tsakiyar idanunta. Shafo gefen fuskarta yayi har xuwa wuyanta cikin wani salo Taja numfashi ahankali tareda lumshe ido. Kasa bude idonta tayi sbd fuskarsa dataji tana matsowa xuwa tata. Da sauri numfashinta ke fita har qirjinta na 'dagawa yana komawa. Qirjin ya qurawa ido hankalinsa na qara ficewa daga jikinsa sbd ganinsu farare tas acike tsaye acikin bra 'dinta suna daqawa suna koma sbd numfashinta dake ja. Hannu yakai ahankali ya shafosu cikin wani salo ai 'dauke huta tayi ta bude baki numfashinta na fita ahankali ya maida kallonsa ga 'dan bakinta bai tsaya komaiba ya shigar da nasa cikin nata 'din. Ahankali yake kissing 'dinta yana qarajin wata fitinanniyar sha'awa na taso masa. Zare bra 'dinta yayi yana ya jefar yana qara cusa bakinsa anata. Sam basusan me sukeba dan kuwa tuni alamari yayi nisa. Qoqarin rabata da pant 'dun jikinta yake ta dawo hayyacinta A furgice ta zame tareda sakin kuka ahankali. Dafe kansa yayi cikin tsananin kunya da takaici Dan baisan meya hau kansa yatashi aikata hakaba. Dukkaninsu kasa motsi sukayi sbd rashin kuxari Ita kuwa harda kunyar tashi take yaganta tunda yayi wurgi da bra 'dinta. Saidaya tattaro 'dan guntun kuzari ya mike ya fito ruwan ya fita Saigashi da jallabiya fara tas ta maza da wani farin towel ya miqa mata ya juya dan idan ba haka yayiba taci gaba da zama gurin xai iyayin komai danko yanxu saidaya yaqi shai'dan sbd baita'ba jin sha'awa kamar yau 'dinba. Goge jikinta tayi tana rawar jiki kafin ta xura rigar daya bata batareda ta tsaya 'daukar bra dinta ko sauran kayanba ta fito kanta na qasa ta fice da sauri harta tuntu6e. Tunda take saukowa haj xeenay ta hangota amma ta kasa gasgata abunda idanunwanta suka hango mata. Murza idanuwa tayi taga tabbas rigar tameer ce ajikinta kuma ga kanta a jiqe sharkaf da ruwa. Wani rikitaccen gumi ta sharce tana jinjina kai har nazli ta shige 'daki. Lallai nayi sanyi tunda har nayi saken da irin haka tafara faruwa. Wlh babu tsinanniyar macen data isa ta haihu a zuriyar gidan nan tunda ban haihuba ko meenah bazan bari ta haihuba kozanyi yawo tsirara bare wannan shegiyar. zanyi maganin komai Kowama ya huta kona samu nutsuwar zuciya. Adaren kasa bacci yayi sai juyi yake dan baitaba tunanin shi 'din mai cikakkiyar lafiya bane sai yau dan gabaki 'daya ya birkice buqace yake. Ita kuwa zuru tayi akwance tana tunani me ciwo ko hawayen takasayi sai radadin zuciya. โšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœ Tunda wannan abun yafaru tafara 'boye masa. Bata shiga aiki saiya fice hakama abincinsa tun bai dawoba take kaiwa ta aje ta ficewarta dan ta tabbatar da sonda take masa zai iya rinjayarta duk da ita tasan ba haramun bane to shifa? Yazai 'dauki abun? *********** Yau gidan ba kowa saisu sbd yaune suke bridal night amma fir tameer yaqi xuwa dan sam kamai na auren baya kansa. Basusan dazai dawoba suka dawo gidan cikin isa da qasaita. Nafisa haj xeenat takira a waya tace tafa'da mata tana neman nazli yanxu. Fadawa nazli saqon haj xeenat tayi sukayi shiru cikeda tunanin me kuma zaifarune kaba komai yau batajin kanta daidai. A daidai stairs suka tsaya nafisa tace, Nazli duk abunda zasuyi miki kadaki yadda dasu dan zasuyita amfani dakene suna biyan buqatarsu. Sawo kai yayi apalon cikin qasaita kuma kunnuwansa sun 'debo mai zancen nafisa na qarshe datace " yadda dasu dan zasuyi amfani dakene gurin biyan buqatarsu" Komawa nafisa tayi ita kuwa ta haye stairs 'din cikin faduwar gaba. Tana shiga suka kalleta a wulaqance kafin haj xeenat tace, Ba 'bata lokaci xamuyi ba abunda zamu da'da miki yanxu shine an canxa shara'di. Ma'ana rayuwar fannah itace fansa ga rayuwar masoyinki. ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ ja da baya tayi cikin muguwar ki'dima tana kallon bakin haj xeenat datayi xancen. Haj kareema ta miqe tsaye tace, Bari kada mu barki a duhu.fannah mukeson kisawa guba taci ta mutu idan kuwa ba hakaba to tabbas a daren farkonsa zaisha guba ya mutu. Qwarai kuwa dan haka kiyi gaggawar xa'ba dan tafiya xamuyi. Bushewa xuciyarta tayi tafara tunanin yanxu lokaci yayi daya kamata ta ringa tunani irin wanda su basayi sbd ku'butar da masoyanta daga sharrinsu dan tanajin qaunar fannah kaman yanda meer ke qaunarta amma zatayi wasa da tunaninsu dan tsirar dasu fannah. Hawowa stairs 'din yayi dan xuciyarsa takasa nutsuwa aiko yana riqe handle 'din qofar xai shiga yayi dai dai data fara magana ya tsaya cak yana sauraronta. ZAN BAWA FANNAH GUBA TASHA TA MUTU NIMA NA HUTA DAN NAGAJI DA WANNAN WAHALALLIYAR RAYUWAR. Cikeda farin ciki suka miqe suka shige uwar 'daka batareda tunaninsu yabasu plan ne tayiba sbd sun san zatayi komai kan tameer. Wani wawan jirine ya 'dibesa yayi saurin dafa bango idanunsa suka ka'da sukayi jajir Wata mummunar tsanarta ta rufesa, Qanwarsa dayafi so dakomai ita zata kashe masa da guba. A fusace ya banka qofar ya shiga. Tsaye take riqeda qullin gubar dasuka bata sai wayarta dake hannunta tana shiein fitowa. Duba palon yayi babu kowa sai ita ka'dai tana waya tana fa'dar kashe fannah xatayi. Jikinsa har mazari yake ya shaqota xatayi magana ya 'daga hannu ya sharara mata kyakkyawan marin dayasa hancinta 6arewa da jini... TO FAH..... ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰ mamuh geee [7:39pm, 15/01/2017] โ“‚amuh geee: ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 176โ†’180 Damqo hannunta yayi yafara janta zuciyarsa na tafarfasa. Ji yake inama baije kunnuwansa suka jiyo masa itaba. Jan qarfi yake mata ido jajir saidaya kaita tsakiyar palonsa ya wurgar da ita ta xube a qasa idanuwanta jajir sbd tashin hankali Kukama sam baiga gurin xuwaba dan abun yafi qarfinsa. Cikin karaji yace, Ke wacece? Me kikeyi anan cikinmu? Meye dalilinki nason kashemun fannah? Waya saki? Wa kikewa aiki? Wa....... Jikinta rawa ya 'dauka tashin hnkalin da bata ta'ba jiba ya dirar mata ta matso ta xube a qasan kwance ta kama qafarsa a ru'de tafara fadin, Wlh bazan ta6a cutatarda kai ba bare abunda nasan kana tsananin so, Koba dan kai ba vazan iya cutar fannah ba sbd halaccinta gareni, Dan allah kada kayi xargina walh bazan iya cutar...... Cakumota yayi jikinsa har rawa yake tsabar 6acin rai Fuskarnan tayi jajir Ya maqureta abango da qarfi yace, Jst tell me d damn truth who the hell are u before i do sumtin crazy. Duk tashin hankalin data shiga abaya baikai mata wannan ba dan yau tameer ne dakansa ke... Jijjigata yayi da qarfi kamar qato dan uwansa Sai alokacin wasu hawayen baqin ciki da takaici suka gangaro mata ba abunda takeso sama da mutuwa alokacin. Sakinta yayi ta xube qasa a zafafe ya bu'de fridge 'din palon ya 'dauko robar swan 'daya ya bu'de ya finciki qullin gubar ya fazge ledar ya juye acikin ruwan jikinsa sai cira yake Ya 'dago hannunta yasa mata tana durqushe jagwaf sai hawaye take cikin baqin cikin kasancewarta araye hartaga wannan baqar rana. Cikin wata irin tsawa da karaji yace, Kince ba kasheta xakiyiba then prof yourself and drink it. Qura masa ido tayi hawayenta na qara gudu ga idanun sun ka'da jajir sbd tashin hankali. Cikin tsakiyar idanunsa take kallo gaba 'daya ya juye kamar wani xaki. Prof me wrong and drink it idan kuwa ba haka walh i wont spare you Hannun police xan miqaki harsai kin fadi abunda yasa kikeson kashe qanwata. Tabbas rayuwarta batada wani sauran amfani gwara tasha ta mutu kowama ya huta

Chapter 5 of 9