Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ๏ปฟDAIMAN Na Mamuh geeh Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo BISMILLAHIR- RAHMANR-RAHEEM. Ina mika dukkanin godiata ga masoyana masu son novels dina, Kuma akoyaushe ina samun sakon fatar alkhairanku...ngd allah yabar kauna. 1โ†’5 Sallama take kwadowa tun akofar gidan harta shigo dan karamin tsakar gidan. Sanye takeda atampha `yar leda kalar kore shar wato kalar asalin `dan `kauye..sai wani gyale fari data yafo mai bakin lesi da `yar jakar hannunta `baka data farfashe alamar tsufa duk da itace tafi kowa wayewa akauyen tunda itake zuwa birni. Shekarunta xasu kai talatin da takwas zuwa da arba'in zuwa da sama. Wata sallamar takuma kwadawa tana fadin, Wai duka gidan bakowane nake sallama ba'a amsawa? Daga bayanta taji an amsa mata cikin wata yar siririyar murya. Juyowa tayi adan tsorace tana ganinta ta hade fuska tareda watsa mata harara tace, Lallai na yarda da kinsamu sake a wurin ladingo. Munafuka mai kamada mayyar uwarta ace kina cikin gidan nan naketa rangada sallama amma kikayi lukus a daki. Toma wai uwar me kike adakin ne. Sunkuyar da kanta tayi muryarta na `dan rawa tace, Kiyi hkr iya jummai wlh kainane yake ciwo banjiba. To dama ina zakiji ladingo ta daure miki gindin iya shege. Ladingon ce tafito daki cikin sauri tana daurawa guiguyayen kanta dankwali murya cikeda masifa tace, Wai hayaniyar me nakejine a gidan? Washe jajayen hakoranta tayi dasuka dafe tana fadin, Aa jummai lfy daga zuwanki kike fada,badai wannan mai kamada muciyarce ta tabakiba yanxu nasa buba ya yayi mata dukan shanu ba. Aa kyaleta ai dagayau kuma andaina dukanta dan nazo mana da mafita akanta kuma wllh ba karamin samu zamuyiba ke wlh har makka sai munje. Washe baki ladingo tayi cikeda farin ciki tace, Haba jummai yanxu naji zanje, Nidai idan xamu samu kudin aiko gidan cire kaine xan bada ita na huta da ganin wannan shegiyar fuskar tata mai kama da jariran aljanu. `Dakin ladingo suka shige. Tadan leko tace, Kuma wlh kafin nafito ki tabbatarda kinyi wanke wanke kin dora mun abincin saidawata na rana.munafuka dangin ifiritu. Sum sum tawuce tafara hada kayan wanke wanke dan ita tarigada tasaba da xagi,cin zarafi,duka da wahalar babah ladingo da `yayanta buba da idi dakuma babbar aminiyarta wato iya jummai. โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹ Gyara zama tayi takalli aminiyar tata tace, Ladingo wani alherine nagani nace to lallai kece kika cancanta dashi. Wato can gidan hajiyar danake zuwa birni kai mata yan aiki. Da sauri ladingo ta kada kai tace inajinki jummai. Wato wani alhajine mai shegen kudi a acan habuja, `dansa dayafiso fiyeda komai aduniyarnan yasamu matsala ta tabin kwakwalwa ta sanadin shan ko menene ma sunan?ni namanta sunan abun. Mahaifiyar yaron ta rasu tun yana yaro ta a kasar turawa yatashi acan yakoyi shan abun har yasamu matsala. Matar alhajin ita tace bazata iyaba shinefa akayi takai masu aiki duk wadda aka kai giduwa suke basu iyawa sbd. Mahaifin yaron kuma bai cika zamaba. Anyi na asibin tarsun gaji shine aka kira malami yace sammu ne akayiwa yaron. Atakaice dai baasamu me iya zama dashiba shine malamin yace ayi masa aure sbd matarsa bazata gujesaba. Anyi neman matar dazaa aura masa babu sbd kowa tsoro yake. To matar alhajin saita bugowa hajiyar danake zuwa gurinta tace asamo masa koda yar kauyece idan yaso inya warke sai ya saketa.kuma ta bada kyautar miliyan daya ga duk wanda yabada 'yarsa aka daurawa yaron. Shine naga wannan mai kamada masillar kitson batada wani amfani agareki ba gwara ki badata ki hutada dangin mayuba. Wani irin fitsarine yakusa kufcewa ladingo ta waro ido jikinta na rawa tace, Jummai miliyan daya? Yazamuyi dasu? Kwantar da hankalinki Miliyan daya dinnan rabawa zamuyi muda 'yayanmu tunda duk babu mai abinyi acikinsu sai sace sace kinga kuwa mun huta. Wata irin guda ladingo tasaki tana shewa tace, Wllh jummai idan kinje yau kice nabasu ita ko gobe sukeso suxo adaura nabasu........ ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husna bbchoudiallo 6โ†’10 Cikeda farin ciki tareda kwarin gwiwa ta isa kano gidan haj salamatu ta zayyane mata ansamu yarinyar daza'a daura auren da ita. Cikin farin ciki itama haj salamatu takira matar alhajin haj zeenat tafada mata ansamu. Murna tayi sosai tareda cewa, To shikenan yanxu zan aiko da kudi dubu dari biyar asiyawa yarinyar kaya, Kuma akoya mata abubuwan daya kamata dan nan dataxo babu me lokacin koya mata yanda zatayi aiki da abu kuma inson tadanyi clean kafin nanda sati sbd daddynsa dayazo za'azo adaura auren aranar juma'a. So banason yazo yaganta kaca kaca yace anfasa dan gskia baxan iya cigaba da wahalar nema masa masu kula dashi. Kuma inason tazo nan kano gidanki ace kece uwarta dan banasan yasan 'yar kauyece. Kin gane zance kuwa. Cikin rawar jiki tace, Ai duk abunda kika fada kamar angamane haj. Yauwa to sai anjimanku. Tana datse kiran haj salamatu takalli jummai tace, To jummai kindai ji abunda tace dan haka ya kike ganin xaayi da iyayen yarinyar? Cikin washe baki jummai tace, Ai haj ita yarinyar batada kowa sai matar mahaifinta data bada ita wato aminiyata sbd uwar yarinyar tarasu kuma batada dangi sbd buxuwace daga nijar ta tsallako wai iyayenta gobara ta cinyesu shinefa mijin aminiya ta ladingo ya aureta suka haifi yarinyar. Bayan haihuwar yarinyar awuein haihuwa ta biyu ta rasu batareda ta haihun ba. Bayan rasuwarta da shekara bakwai shima malam din yarasu sai yarinyar ta taso hannun aminiyata ladingo. Kuma haj yarinyar shegen kyau ne da ita kamar jikar aljanu ga gashi kamar ka ara kayi kitso dashi,sannan duk kauyen nan ita kadai tayi karatu dan malam kafin yarasu dakansa yake kaita yadaukota. Wata irin dariyar farin ciki haj salamt tayi tace, Gaskia shiyasa nake yaba miki jummai dan kin iya xaben kwarai Ta shekarar yarinyar nawa?kuma yaya sunanta? Shekararta goma sha shida kuma sunanta NAZLI. ******** Karfe uku a kauyen takai tayi musu cikin gidan babah ladingo. Kudi masu yawa kimanin dubu hamsin haj salamatu ta zubewa ladingo agabanta tace, Wannan somin tabine na abani yarinyar naje da ita nafara shiryata kafin sati saiku samemu acan kano sai a daura auren acan suwuce da ita. Idi ne yayi saurin waftar kudin yace, Ai dama ko bakizo yau daukartaba mun shirya kaita gobe dan kawai ayi auren mu musamu kudin shanawa. Buba yace, Nidai kubani kasona na wannan daaka kawo natafi dan inada gurin xuwa kafin akawo masu yawar. Ladingo kuwa kwalawa nazli dake tsakar gidan tana jibgar wankin ladingo hardana buba da idi kira tayi tana xuwa ta durkusa kofar dakin cikin nutsuwa da sanyin murya tace, Gani. Maza je kihada tsummanki birni xamu yanxu. Rass gabanta ya buga dan tasan abunda suke niyar yi mata na aura mata mai tabin hankali dantayi jinyarsa akan kudi sbd taji firarsu lkcin datake fadawa su buba jia. Kwana tayi tana kuka dan ta kara tabbatarda rashin gatanta amma bazata bijire mataba dan kota bijire din to ta tabbatarda korarta zasuyi a gidan data rasa gurin zuwa gwara tabi umarninsu ko kashe tane marar lfyar yayi ta huta da bakin ciki da azabar datake ciki. Amotar haj salamatu sukazo har ladingo din dan tace itace uwar amarya sai andaura aure zata koma. โšœโšœโšœโšœโšœโšœ Satinsu daya a kano kuma ayaune ake daura auren bayan anyi komai na neman aure a gun mijin haj salamatu dan shima lashe money ne bare dayaji 'dan hamshakin mai kudin nanne ALH ZAID OMAR. Duk wani abunda akeso takoya haj salamatu ta tsaya takoya mata irinsu, Amfani da abubuwan dake cikin toilet din gidan masu kudi, Da hada shayi, Da gyaran guri da sauransu. Sannan sun siya mata kaya dai dai misali shidinma dan dai kada haj zeenah taganta da tsumman kayanta. NAZLI kyakkyawar yarinyace fara tas me dogon gashi da dogon hanci gatada manyan idanu da dan lips dinta jajaye. Duk da tana cikin tsananin wahala hakan bai hana tsananin kyawunta da nutsuwarta fitowaba. TAFARU TAKARE Karfe goma sha daya alh zaid umar ya iso kano da tawagarsa kai tsaye suka wuce babban masallacin jumaa dake kano dan acan xaa daura auren na dansa tilo dayake masifarso duk da dai angon bazai yiyu afito mutane dashiba yana can abj yabarosa. Mijin haj salamatu alh yaro shi ne uban amarya wakilinta. Guri yacika ya batse da manyan mutanen nigeria harma da jajayen fata jiniyoyine kawai ke tashi. Karfe 'daya daidai dubban jamaa suka shaida daurin auren na TAMEER ZAID OMAR DA NAZLI ADO TAKAI. Tanajin alh yaro yashigo gidan yace andaura aure kuma ga jeep jeep nan guda goma alh ya aiko akai masu kai amarya airport suwuce abj. Ido ladingo ta zaro tace ita wllh ba inda zata asallameta kudinta takomawarta gida taredasu buba dasuka dauri auren. Dubu dari hj slmt tabata suka wuce bayan nazli ta riketa tana sakin wani irin kuka maiban tausayi wanda har akaro nafarko da ladingo taji tausayinta amma tana duba gudin hannunta saita fincike tafice tana fadin, ALLAH YASA YA 'DIRKO MIKI CIKI ACIKIN HAUKARSA. Kuka take sosai mara sauti har suka isa aiport din itada hj slmt da jummai da wasu aminan hj salamatun. Sam tashin hankalun datake ciki baibarta taji tsoron jirginba har suka isa abj wasu jibga jibgan motocin suka kuma daukarsu. Wani hamshakin katon gida suka suka shiga mai hawa uku. Haduwar gidan hartayi yawan fada ga masu tsaro zagaye da gidan. A boys quaters aka saukesu yan aikin gidan suka dingi kawo musu abinci danasha. Ruwa kawai tasha ta tsaya kallonsu iya jummai sunata kwasar gara. Suna gamawa aka aiko haj nason ganinsu suka mike dukkaninsu suka bi bayan yar aikin. Ya salam. Falon dasuka shiga haduwarsa sam ta baci abd uwar dukiyar da aka narka acikinsa. Zaune take akan daya daga cijin sofa din falon ta xuba ado tana baza kamshi. Kallonsu tayi tace, Tunda kun gama abunda yakawoku ga motanan yau komai dare xata kaiku kano. Mint dun dubu daya ta mika musu tareda cewa su wuce idanda wani abu xata kira hj slmt a waya. Mikewa sukayi jiki asanyaye suna mamakin wulakanci irin na hj zeenat din Sun kawo mata 'ya amma ba godi bare nagode saima maidasu gida dazatayi adaren ko hutawa bazata bari suyiba. Hj slmt ta kalli nazli tace, Kiyi hkr nazli allah yabaki dauriya da hkr. Suna ficewa ta fashe dasabon kuka dan ita gidan tsoro yake bata. Kallonta dakyau hj zeenat tayi taga tayi yarinta amma aitunda andaura aure ai xata iyane tayi gyaran murya tareda cewa, Kidaina wannan kukan dan bautar aure xakiyi idan kuma ya warke yasan yanda zaiyi da auren.amma dai yanxu kitashi akaiki part dinsa.ma'ana hawan karshe can ne part dinsa Hawa na biyu kuma namu nida dad dinsa saina kasa gaba daya shine na baki da masu aiki. Tameer baya iya mgn, Baisan kowaba sbd kwakwalwarsa ta juye dan hk yanxu aikinki kulada cins,shansa,tsaftarsa da komaima nasa. Nafeesa dauki akwatinta kikaita sama part din tameer kafin gobe taxo tagaida dad dinsa dan a goben xaikoma paris. Stairs suka haye har hawa na karshe ta bude kofar falon dayafi na kasan tsaruwa da haduwa tashiga har kofar dakin dayake cike takalli nazli tace, Ni daganan xankoma kixo ki rufe muku falon dan yana fitowa idan akabar kofar abude. Jikinta babu inda baya rawa amma haka ta rufe kofar falon hwy nabin fuskarta na tsoro da fargaba. Hakanan taji tanason ta leka dakin taganshi taga ya yake. Ahankali gabanta na faduwa ta tura kofar dakin ta leka. Wani dan saurayin farin balarabe ta hango kwance a makeken gadon dakin yana bacci hnkl kwance kamar me cikakkiyar lafiya... ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰ mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• NA MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husna bbchoudiallo 10โ†’15 Saurin komawa tayi da baya tayi tareda jan kofar jikinta na makyarkyata fitsari na neman kufce mata tsabar tsoro Sannan hawaye suka balle mata tayi saurin kuwa bakin kofar fita ta durkusa tana kuka tareda toshe baki dan kada kukan yafito. 'Kiyayyar dasu babah ladingo kemun harta kai su aurawa ajani ni dan wllh wannan ba mutum bane dan bantaba ganin mutum mekyau irin hakaba sannan gashi fari sosai yamafi 'dan megari dake birni karatu fari. Kuka takara fashewa dashi rawar jikinta na tsananta. Jin karar bude kofar datake tsugune ne yasa ta mike da sauri kamar fitsari zai zubo mata fuska cike tab da hawaye. Wadda takowota dakince tadawo daukeda tray din abinci da magunguna takalleta taga yanda tayi shabe shabe da kuka da zufa duk da splite air con dake palon kusan guda uku batasan sanda tabushe da daria ba. Ganin dariyar datakene yasa hankalin nazli yakara tashi takara barkewa da kuka. Ganin dai da gaske take kukan ne yasa ta daina dariyar ta aje tray din akan center table din palon takalli nazli duk saitaji tabata tausayi sbd kasancewarta yarinya amma sbd kwadayi iyayenta sun aurawa mai tabin hankali ita. Yi shiru kidaina kuka ki fadi maiyasa kike kuka. Jan numfashi tayi cikeda tsoro tace, Tsoronsa nakeyi wlh bantaba ganin mutum mai kamarsaba. Wata muguwar dariyace tazowa nafeesa amma saita gimtse sbd kada ta kara tsoratata akan wanda take ciki. Kinga xo xauna nafada miki komai akansa. Kasa xama tayi akan royal kushins dake palon sata sulale ta zauna akasa tana cigaba da shararar hawaye. Itama nafisar akasa tazauna dan dama basa hawa kujerun gidan sbd zamansu yan aiki kuma hakan umarnin hajiyar gidanne wato haj zeenat. Yaya sunanki? Cikin muryar tausayi tace nazli. To nazli zan fada miki komai gameda tameer dan yanda zakiji saukin fara dawainiyarsa. Na farko abunda zan fada miki shine Baya tashi bacci kullum sai karfe goma sbd allurar da dr yake zuwa kullum dare yana masa sbd yasamu yayi bacci dan idan bada alluraba baya bacci. Abu nabiyu kuwa shine daya tashi zaki kama hannunsa kikai toilet kiyi masa brush kafin nan nikuma nakowo masa abincinsa saiki bashi kibashi magani daga nan sai masu yi masa wanka zasuzo suyi masa sai sauran aikin sa masa kaya nakine. Atakaice dai sallarsa da cinsa da duk wani abun bukatarsa yana kanki. Sannan babban abun shine ba'a barinsa shikadai adaki ko afalo ko a inama sbd tabin hankalin nasa mugun tsoro yasakar masa. Kidainajin tsoronsa dan mutumne kamarki. Abunda yasa kika ganshi haka mahaifiyarsace yar kasar larabawa Dan haka ki kiyaye duk abinda kikaga baki saniba idan nashigi kawo abincinku kya sanar dani dan haj bataso yan aiki na hawowa sama saini kadai nima idan ba abinci xan kawoba bana hawowa. Mikewa tayi da sauri ta fice sbd kada haj tafara kiranta bata kusa. Wani irin wawan tagumi ta rabka tana juya bayanin nafisa a xuciyarta kafin tamike ta nufi dakin dan kara lekawa taga balaraben. โšœโšœโšœโšœโšœโšœ Ahankali yabude dara daran idanuwansa jin babu motsin akwai mutum adakin yasa yayi saurin xabura ya mike tsaye a tsakiyar gadon yana raba idanu. Motsin shigowa dakin yaji aiko tsoronsa ya tsananta ya diro daga gadon da sauri yayi bayan kofar ya labe tareda saurin ciro durowar madubi ya lafe bayan kofar. Ahankali kamar barauniya ta turo kofar tareda turo kanta aiko batayi auneba taji saukar abu kamar an kwada mata guduma ta dago idanuwanta dasuka fara ruwa ta dorasu akansa kafin ta sulale ta zube asume... ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰ mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†in dedication toโ˜† Husna bbchoudiallo 16โ†’20 Ahankali suke saukowa daga stairs din hannuwansa makale da nata. Gabantane ya fadi da karfi nan jikinta yafara rawa badan komaiba sai dan haj xeenat data gani hakimce a falon tana aiko musu da kallon, Tsana,haushi dakuma mamaki dan idanda abundata tsana arayuwarta to tameer ne sbd son da mahaifinsa ke masa yasa takasa samun yanda takeso da tarin dukiyar ta alhajin. Shima tameer na ganinta yayi saurin lafewa abayan nazli yana kara kankameta. Cikeda izza tana yamutsa fuska tace, Kifadamun ubanda yasaki sauko da wannan dan iskan mahaukacin nan inda nake baki. Aminanta dasuke tare azaune palon ne suka bushe da daria 'dayar nacewa, Wlh komai yafaru laifin kine zeenat dan babu yanda bamuyi dakeba akan kisan yanda kikayi aka turashi gidan mahaukata ki huta gaba daya amma kinki. Cikin haushi tace, Aike badan matsiyatan kudin danake tatsa a gurin ubansaba idan yana nan din da tuni na gargadasa gaba sa gidan mahaukata. Maida kallonta tayi kan nazli datayi wuki wuki tana sauraran makircinsu. Tace, Wuce munafuka matsiyaciya kuma wllh kinkusa barin gidannan dan naga alamar mahaukacinnan yafara sakewa dake nikuma ko acijin hauka banason nagansa cikin farin ciki. Sum sum tajuya idanuwanta nakawo wasu irin hawayen tausayinsa. Suna komawa a palo tazauna tana fidda hawaye masu ciwo sbd ganin allah sarki ita batada iyaye tanashan azabar babah ladingo sbd rashin gata. Shikuma gashi da gata dajin dadin dunia amma anjuyarmai da kwakwalwa. Saukar hannunsa taji afuskarta yana share mata hawaye wani sabon tausayinsa yataso mata takallesa cikin hawaye tace, Nayima alkawarin jure duk wata wahala da barazana dazan fuskanta daga matarnan na tsaya na lura dakai har tsawon lokacin dazaka dauka kafin ka warke. Kamar yasan abunda tafada sai kawai sakar mata murmushi tareda riko hannunta ya dora abakinsa tagane yunwa yakeji ta mike tareda bude fridge tadauko musu drink da biscuite Da farko kin ci yayi amma ganin taci shima ya bude baki tafara bashi. Suna gamawa suka zauna palon suna kallon tv wanda dagashi har ita babu mai fuskantar komai sbd shi dakeda ilimin yanxu beda amfani tunda kansa ya juye. Itakuma bayan primary datayi lkcin abbanta nada rai bata iya komaiba bare uban turancin da ake rerowa a tv. Da tsakar dare tana kwance akasa kamar kullum saitaji kamar gadon da tameer din ke kwsnce na jijjiga Tayi saurin tashi jikinta na bari saiko tagansa a kwance sai rawar sanyi yake har hakoransa na kukan haduwa da junansu. Akidime ta dira gadon tana kiran sunansa yanajinta amma ko motsi baya iyayi takamoshi jikinta dukda yayi mata girma amma haka takamasa ta rungume tana sakin kuka ahankali dan gani take kamar mutuwa zai ita kuma ayanxu jinsa take kamar shikadaine dan uwanta. Tun tana kuka har bacci yadaukesu ahaka basu saniba Washe garima sai goma suka tashi. Tun daga ranar takoma kwana akan gadon sbd kota kwanta akasa shima saukowa kasan yake ya kwanta kusa da ita kota lallashesa baya yadda yakoma. Hakan yasa takoma gadon suna kwana atare. โšœโšœโšœโšœโšœ Duk yanda haj xeenat ke tunanin shakuwarsu abun yawuce nan dan sunyi wata irin shakuwa. Da gayya haj zeenat tadakatar da dr xuwa yana masa allurar dakesa sa bacci da dare wanda aranar dabaayiba sam basuyi bacciba yanata zabure xabure tana ganin hakan ta fashe da kuka tareda rungumesa tana cigaba da kuka. Kamar wasa sai taga bacci yadaukesa Tun daga ranar saita rungumosa jikinta suyi baccinsu hnkali kwance. Kwanciyar hnkalin data samune da cima mai kyau yasa ta ciko kirar budurcinta ta bayyana ga wani kyawu da fatarta tayi. Haka shima samun kulawa dayakeyi daga garetane yasa ya 'kara wani irin ja da kyau. Yanxu ita ke masa wanka sbd duk masu hidimarsa haj zeenat ta dakatar dasu sbs acewarta nayi wahalar nikadai. Sanin bashida hnkli baisan komai bane yasa nake sakewa muyo wanka atare ina saka ko wane irin kaya agabansa dan ganin baisan komaiba. Much luv๐Ÿ˜˜ AMINA JAJI Daiman fan. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• NA MAMUH GEEE โ˜†in dedication toโ˜† Husna bbchoudiallo 21โ†’25 Tadau fiyeda shekara agidan kuma acikin wannan shekarar abubuwa dasuka faru sune shakuwar dake tsakaninta dashi ta wuce tsammani wand hartakejin yazama wani 'bangare na rayuwarta datakejin bazata iya rayuwa babushi. Jin tsananin sonsa take akowane second na rayuwarta. Hutu da kwanciyar hankali yasa gaba daya ta canxa ta cika ta ko'ina dan yanxu taxama cikakkiyar budurwa. Kiyayyar da haj xeenat keyiwa tameer gaba daya tadawo kanta soboda wata irin kaunsa da daddyn ya dora mata ga uwar dukiyar dayake kashe mata itada mahaukacin dansa shiyasa tadau mummunan kudiri akansu. Xama suke kamar wasu makiya dan yanzu ko ruwa idan ba ita ta daukoba bata bari abawa tameer dan hakama itake musu girkinsu akicin din palonsu. Sannu ahankali har dad yasa aka kawo mai koya mata karatu agida tun bata ganewa hartafara ganewa hakama handbag dinta wato tameer duk inda tasa kafa ta dauke yana biye da ita. Lokcin da dad yasiya mata mota yasa aka koya mata bata wani jimaba ta iya shiyasa yanxu har saukarsa take suje yawo sudawo abunsu. Abu daya ta fara fuskanta yanxu akansa shine duk yaga anyi abu idan ya burgesa to sai ya gwada shima. Duk yanda taso gason jin muryarsa bata samuba sbd haryanzu baitaba maganaba saidai taji sautin muryarsa lkc dayake daria idan suna wasa. โšœโšœโšœโšœโšœ Sanye takeda doguwar riga wani shaking material dayayi masifar yi mata kyau tasanya dan karamin hijab tanata sauri ta gama ta sauka sbd malaminta yazo tun dazu. Xaune ta taddasa a palon yakurawa tv ido yana kallo kamar idanuwansa zasu fado Tasaki murmushi tarafa tafiya cikin san`da sbd tasamu taje ita kadai tunda hnklinsa yatafi a kallo kuma dama kotaje dashi makalkaleta yake ya hanasu karatun yanda yakamata. Caraf taji anriko hannunta gabanta tayi mummunan faduwa sbd rikon baiyi kamadana tameer ba sbd shi makyalkyaleta yake. Araxane tajuyo amma ga tarin mamakinta saitaga shine tsaye yarike hannunta din kuma riko mekyau sbd yanda takasa kwace hannnun. Hankalinta bai tashiba saidataji yakai mata wata kyakkyawar runguma datasa numfashinta kusan daukewa sbd a iya saninta ta tameer baya rumgumarta saidai ya cukwuikuyeta. Numfashinta taji yana fita da sauri ta zame da sauri tana dafa bango sai alokacin idonta yasauka akan tv taga wani romance film ne ake a tashar tayi sarin xuwa takashe tadan kallesa saitaga gabaki daya jikinsa amace yake. Sum sum tawuce shikuwa akaro na farko yau baibita wani guriba. Sam yau bata gane komai akaratunba hakadai aka tashi karatun takoma. Kwance ta taddasa a palon yana ganinta yataso suka shiga bedroom tare ta aje littafanta suka koma palon nan da nan ta sake suka cigaba da wasarsu ta guje guje apalon kamar koyaushe. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah 31โ†’35 Kashe gas din tayi ta fito kamar me satar hanya takoma daki ta zauna. Har dare 'kin bari tayi su xauna guri daya. Da daddarema haryayi bacci idonta biyu tana kallonsa dan ganin take idan tayi bacci wani abun kuma xaiti mata. Da safe ma tun tana gudunsa harta daina sbd shi baimasan metakeyiba tunda ba wani hnkline dashiba. Da maraice bayan sungama komai sun sauka gurin karatu ta lurada duk karatun datake idanuwansa nakan lips 'dinta datake motsawa Duk saita fara rudewa sbd tsoron kada yayi mata kiss agaban malami Aiko bata gama tunaniba taga fuskarsa ta nufo tata fuskar Tayi zambur ta mike jikinta na rawa tana raba idanu. Malamin yakalleta yanason tambayarta amma sai duk yaga a rude take. Kafin yayi wata magana cikin sauri tace, Mlm ina...ina..inajin ciwon kai abari sai gobe. Da sauri ta wuce har 'kafafunta na hardewa. Bin bayanta yayi shima da sauri suka shiga palo takama stairs ta haye. Yanda take haye stairs 'din arude da saurine yasa ta taka ba daidaiba ta zame Tameer dake biye da ita abaya ya ca'beta atsorace shima yana ware ido da le'ka saman yana duba wanda ya turota ta fado "danshi atunaninsa turota akayi. Amma harya haye saman da ita baisaniba yanata ware idanu atsorace. Kasa 'dauke idanunta tayi akansa tun lokacin daya tarbota harya 'dauketa ya hayo saman da ita. Wani irin masifaffen sonsa takeji yana bin jinin jikinta tana kallon kyakkyawar fuskarsa har suka iso palon batasaniba saidataji yasaketa tim tafadi tsakiyar palon amma sam bataji zafiba saima binsa tayi da kallo tana murmushin dashi baimasan tanayiba. Saidaya gama le'ke le'kensa kafin yazo gabanta data shagala da kallonsa duk inda ya wulga shima saiya saki murmushi ahankali yana kallon tsakiyar idanunta. Ahankali ya taka ya isa gabanta har numfashinsu na haduwa sosai Tayi saurin juya masa baya tana murmushi Ya tsurawa bayanta ido yana kallon

Chapter 1 of 9