Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
hidima a gidan hidima sannan kuma matar mai hidima, farin cikin mai hidima, zuciya hasken annurin mai hidima, zakanya saidai aganki anesa badai a matso kusa ba,” Wani irin murmushi da dariya falmata tayi cikin jin dadi, ta daga giranta sama sannan tace “kinga na kashe da’ saura uwarsa sannan uban gayyan uban gidan, yusuf[truncated by WhatsApp] HALACCON SARAUTA 32  benaxir  October 26, 2015  Hausa Novels  145 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR jakadiya tana rusune harta mike ta fice. Bawanda yakai falmata farin ciki aranan saboda tana ganin wanda zai tare mata sarautar danta yafadi kasa yamutu, shehu kuwa baiyi hankalin dazata sashi a sahun masu karban sarautan ba. Donhaka tuni tafara tunanin hanyan dashi kanshi sarkin zai mutu, babu tsoron Allah babu tunanin lahira, tunaninta shine takashe duk wanda tasan zaishiga tsakaninta da mulkin garin, Sai dare sannan aliya tafarka atake sufyan ya tallabota yadawo da ita gida yana ganin inna baikulataba yashige da aliya ciki, saida yatabbatar takwanta ya rufo kofan sannan yafito inna tana tsaye tana jira yafito, baikulata ba tana kiransa, inba don babu gun da zaikai aliya ba da gidan nata saisu tattara subar mata shi, Cikin dare aliya tayita firgit tana wasu mafarkai, dolenta tamike,alwala tadauro tafara sallah har asuba tana yiwa abdullahi addua, tausayin matanshi da abunda zasu haifa yacikata, Dasafe sufyan nazaune wayansa tayi kara alh.hamidu ne yake cemasa yazo suna jiransa, baiyi bacciba tsabar yana tunanin hanyan dazsi bullowa maganan, motansa yaja yafice gydan alh.hamidu yanufa suna zaune a tsakar gydan suna jiranshi, sun gaysa yabasu girmansu sannan yazauna, inda hussieni yake tambayansa alkawarinsa, sufyan yayi murmushi sannan yace “komi zaizama naka idan kabani tarihin yadda akayi ka kashe mahaifina!” Ba hussieni ba har alh.hamidu saida yabude baki don mamaki,hussieni yagagara cewa komi,hakan yakara tunzura sufyan, hawaye ne suka fara zubo mishi yafara magana cikin sanyin jiki “Ashe karshen duniya zatazo dahar danuwa zaisa hannu yakashe danuwansa saboda dukiya?saboda mulki?” Bawanda ya amsa mishi kaman tsoffin barayi da aka kamasu hussieni kanshi akasa yafara magana “kai mahaifinka ne. Nikuma danuwana , wlh tlh ba abunda nashirya yafaru ba kenan, Allah dai yayi zanzama sanadi, tabbas munyi musu da shi batun mulki anma ban kwallafa raina ba. Nasan na umurta da amai dukka anma bance sukasheshi ba, bankuma ce suhada da mahaifiyarka ba. Allah yayine lokaci yayi don Allah kayi hakuri, karkuma kabari kanwarka taji alokacin sufyan yayi kukan zuci daya tuna da iyayensa anma tuni ya watsake saboda ayanzu zucuyarsa tabushe yana tunanun daukar fansa, recordern dayake recordn yasawa stop sannan yamike yafice batare da ya ce musu komi ba dama yakira lawyernsa awaya tuni yadamka masa shaidansa tareda basa go ahead nashigar da kara kotu, koba komi yanzu yaji sanyi aransa Aliya kuwa tacanja gabadaya ba abinci sai ruwan lipton, sufyan yayi lallamin harya gaji yusuf ma yayi nass Bayan sati biyu alokacin anwatse a gun rasuwa. Sannan alh.hamidu da alh.hussieni sun shiga kotu inda zaa fara sauraren karansu Aliya tadan sake, yanzu hankalinta ya kwanta maganan rama mutuwan iyayenta anmma abunda yafi bata ciwo shine danuwan mahaifinta shi yakashe mahaifinta. Abunda ciwo,saidai yanzu tabar komi agun Allah har lokacin sufyan baya magana da inna , aliya tayi iya kokarinta anma yafaskara yusuf na iya kokarinsa ganin ya farantawa aliya yayinda soyayya mai karfi tashiga tsakaninsu, tuni yafara maganan aurenta yasamu falmata da zance atake tace batasan zance ba, nan yakoma kan yakolo ta yadda takuma sa albarka inda anan yasako waziri da sarki, dafarko waziri yaki amincewa acewarsa dole yusuf yadauko yarinya mai asali, nan fa yusuf yazayyana masa rayuwar aliya tundaga farko dakuma wahalhalun datasha waziri yayi mamaki sarai anma yace zai gwada tunkarar sarki, sarki yanajin magana yatambayi wacece atake waxiri yace yar marigayi galadima,sarki yaji dadi sosai tuni yafara murna, wannan yarinyan ai ita keda asali, nan waziri yace “anma akwai matsala mai martaba, yarinyan tashin hannun mace tayi dakuma tashin gari” Sarkin yayi shiru don tantance me wazirin ke nufi donhaka yace “yi bincike mai tsanani muji”dahaka waziri yabar maganan, falmata taji labarin abunda ke faruwa donhaka ta nufi sarki da maganan anma yanuna mata shi ba ruwansa,don shikanshi yanaso yusuf yayi aure, baitaba tsammani kuma yusuf zaikawo yarinya yace yanaso ba donhaka tuni tarikice duk tana tunanin hanyoyin dazata hanashi wanda shi yusuf har daina zuwa gaysheta yayi tsabar yasan kalan mitanta, Aliya kuwa tasan bakaramin rikici bane zai afku donhaka tuni tafara lura da takunta, ga masu nufinta da sharri, ita anata taso ta tattara tabar garin bata da dsmuwa da gun anma dole tajira a idar da case din iyayenta a kotu, Waziri yayi iya bincikenansa akan aliya tuni yakira yusuf “Kana sane da tayi bauta agydannan?” “Tayine alokacin batasan kowa ba” “Kasan dai yanayin rayuwarta bai shiga danaka ba” “Nasani shiyasa nake rokonka daka sa baki, kaikadai ne inka yabeta sarki zsi yadda, don Allah kataimaka” “Zan yi iya kokarina, anma kai kasan halin mahaifiyarka” Dawannan suka rabu inda yaje yagabatar da zancen da duk wani tarihin aliya agaban sarki, sarki yadannan approve makake, nima dai benaxir na dannan approve duk da munsan amincewan mezai jawo, ansa rayuwar aliya cikin hatsari da damuwa, anma munsan cewa aliya ce kadai zata iya gyrawa falmata duwawun zama, muje zuwa gobe[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 33  benaxir  October 27, 2015  Hausa Novels  106 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR falmata kashe kanta ne batayiba domin amincewar da sarki yayi, ta tura duk wanda take ganin zai iya magana wa sarki anma taci tura, waliyyim aliya shine alh.hussieni anma sufyan yayi kif da ido akan bai san zance ba, dole akarshe aka bukaci alh.hamidu yazama waliyyi, duk soyayyan dayakewa hassana yayine domin yasamu hankakinta anma daga karshe yaga sone na gaskiya , hussiena ma tasha alwashin zaman lafiya kam aliya da yusuf bazasu sameshiba agydan Anyi zama a kotu inda lawyernsu sufyan yaci karan, kotu tabawa alh.hussieni zaman prison na shekara ashirin da daya sannan ta bukaci daya fidda gadonsu ko kuma kotu taci tararsa, a ranan aliya tayi kukan farim ciki tunda take bata tabajin kwanciyan hankali irinna ranan ba, jitayi kaman ansauke mata dutsen badr akirjinta, tuni ta maida hankalinta kan batun aurenta duk da tasan tashin hankalin dazata shiga, antyn abuja ne ta bukaci taje don su samu ayi siyayyanta, ta tattara dan komatsanta duk da yusuf bai so ba, shi yanzu babban damuwansa yaga ya aureta, Sunyi sallama tatafi yayinda yakoma fada, shigansa yatarar da bilkisu da abincinsa, zama yayi yarike kai yana tunani kansa yamasa nauyi har yanzu falmata taki yarda da auren, yasan son zuciyanta ne anata tunanin wai saidai ya auri hussiena, shi haryau hussiena bata kwanta masa arai ba , bilkisu ce tayi tari hakan yadawo dashi daga tunaninsa yakalleta sannan yace “meke faruwa acikin gyda gameda aurena” kanta a kasa tace “Gimbiya yakolo tafara shiri, yayinda gimbiya falmata bata fara ba, ita shirinta da hussiena takeyi” Baice komi ba yatashi yafice sannan yanufi fannin falmata anma sa iso sannan yashiga daga ciki tana zaune akan kujera yazauna akasa abinda bayayi, hakan yatabbatar mata da bukata yazo dashi, bata kulashiba yasa kanshi akasa sannan yace “Ina neman amincewarki na auren aliya” “Ban bayarba, kuma ko bayan raina ban sa baki ba” “Inaso kibani hujjanki wanda addini ta haramta min auren aliya” “Yar kan titi!! Yarinya tagama gantalinta agari! Kowani dan iska ya kwasa! Kainan tayi fitsari tabaka kasha ba dole kabiya kaman agwagwa ba!” Ga mamakinta taga yamike yafice , baikuma cewa komiba, tunda shi mahaifinsa yasa albarka hujjanta ba kwakkwara bane dazatace masa kar ya auri aliya, fannin yakolo yaje, yasami hauwa tana ganinsa tafice don haryanzu tsoronsa takeji, yakolo tayi murmushi tareda masa iso, bayan karasowarsa yazauna dum a kasa, nan da nan tagano alfarma yazo nema, yagaysheta ta amsa masa sannan yace “Naje gun gimbiya na nemi ta amince min auren aliya taki yarda, kuma hujjojinta ba ingantattu bane, kitaimaka ko zakisa baki” “Bakomi yusuf, kasan mahaifinka inta sa rai akan abu, kai yakamata ka lallabata anma zan gwada kokarina kaji” “Nagodr Allah yasaka da alheri” Ficewa tayi, tuni abdullahinta ya fado mata arai, tasan yarinyar dayakeso aketa rikici akai, gashi cikin mata yafara fitowa duk da sunriketa tana fadan akan saita haihu tukun zasu barta tafita, Yakolo tayi iya kokarinta don fahimtar da falmata anma falmata kaman ana zuba mata man fetur, dahaka biki ya matso kusa aliya tadawo gari saidai tagagara zama, rokon yusuf tayi akan ko zai taimaka yabata aron bilkisu, haka kuwa akayi , tuni bilki tafara taimaka mata, jin aliya zata auri dan sarki tuni dangin nesa da wanda aka manta dasu suka fara bayyana kowa saiyace yazo auren marainiyan Allah, Ran jumaa aka daura auren aliya da yusuf, inda akayi dinner daredare nagani nafada, munsha gwaggori munsha rawa,yusuf na makale da matarsa, hannunsa gam anata shi yanzu gani yake duk duniya bawanda yakaishi hakuri da juriyan dayayi, angama dinner inda aka kai amarya fanninta side guda aka ware mata a fada, dakuna uku da falo biyu,tabbas tasamu kaya tasha gata, sufyan yashare mata hawaye tayi kukan rashin iyaye anma batayi maraici ba, kowa yayi mamakin ganin yadda falmata tasake ranta da maganan biki, harwani jan aliya take ajiki, acewarta komi yawuce,anma aliya tagagara sakewa da ita, randa aka kaita an watse aliya tana kunshe jikin gyalen kyabban da aka rufata dashi duk ta kagu tana jiran angon nata,don tsoro takeji dakin ya mata girma sosai, kukan kare tafaraji, dafarko bai dametaba anma datayi tunanin gydan babu inda aka ajiye kare, tuni tafara tsorata kodai yusuf yasiya ya ajiye a fanninta ne? Toh anma matsalanta shine jin kukan take kaman agabanta yakeyi, hannunta ne yafara bari tafara salati da dan karfi sannan taji shiru, can kuma takarajin kukan karen daga nesa saikuma karan kofa, saura kadan tasake fitsari awandonta taji anbude kofan, yusuf ne batasan lokacin data rungumoshiba, jikinta na bari jinhaka yasa shima ya kamata, sunfi mintoti ahaka kafin yajawota yazaunar da ita akan lallausan gadon, “leeya meya sameki?” Bata bashi amsaba, tafarajin wani kukan karen wannan karon harda kulya, salati takeyi jikinta na bari, tuni jikinsa yayi sanyi domin bata cikin hayyacinta, alwala yadauro yace itama tayi anma dole saida yarakata toilet din don tsoron datakeji. Tafito yajasu sallah yakamo kanta yatofa mata addua, sannan yafara tambayanta akan littafai daga kan fiqhu, hadiths da dan tauhid, yayi mamaki sosai dayaga tanada sani, baitaba zaton tasani sosaiba, daganan ne yace “mezakici?” “Babu kabarshi” Cire mata kallabin yayi, sannan yarikota naman ya yaga kadan yafara bata tana tauna ahankali yabata da soya milk haka taci takoshi sannan yace tadan kwanta, tana kwanciya taji kukan karen zumbur tamike kaman an tsira mata allura, rikota yayi yana tofa mata addua, atakaice haka suka kwana a zaune har asuba, dazaran zata kwanta sai kukan kare ko qulya, asuba nayi sukaji shiru, hakan yabashi daman fita masallaci, tana sallah bata fitoba saboda baccin daya kwasheta, karfe shida daidai saiga umma uwar tsoro falmata ta turota buga mata kofan tayi can dai tabude, bata tasheta ba ta nufi kan gadon taja bedshit din tafice, kaiwa falmata tayi wanda tana zaune tana jira ganin babu komi akan bedshit din yasa ta salati, tana cewa “saida na gayawa yusuf wannan yarinyan tagama gantalinta, yaki yarda, kue kudauko min ita,” Dauko aliya cak akayi aka wurgata akasa. Jiri ne yake dibanta anma tuni ta warsake don ruwan sanyi tas falmata tasa aka watsa mata, alokacin yakolo tazo ranta yayi mummunan baci, inba raina darajan dan adam ba yazaayi matar danki dan cikinki zakina wulakantawa? Tuni fa gyda ya hargitse, nima benaxiratu idona na rufewa anma dole nabude[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 34,35  benaxir  October 29, 2015  Hausa Novels  110 Views [10/29, 7:11 PM] Adda Bena: [10/29, 6:45 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya bata iya daga kai ba, tarasa meyake mata dadi, ayayinda falmata da yakolo ke magana, anma falmata tayi kif da ido tareda “cewa tunda ba danki bane saikiyi hakuri” yakolo taji zafin kalman dakinta takoma don abun yafi karfinta, Yusuf nafitowa daga masallaci yaga shehu wanda yayi latti, donsai alokacin zaishiga masalaccin [10/29, 7:10 PM] Adda Bena: Ganin yusuf yasa ya tarbesa tareda cewa “kayi sauri kashiga ciki kaga ikon Allah hakan yasa yadada sauri jikinshi nabashi wani abu yafaru ne,aikuwa idonsa kan aliya yayi tana zaune a kasa , Allah sarki marainiyar Allah dasauri yaje yadauketa falmata nakiranshi bai kulataba fanninsu yanufa da aliya daki yakaita yaga babu bedshit nan da nan yagane me akayi mata ajiyeta yayi yaje yadauko kettle yahada mata ruwan zafi sannan yace “tashi kishiga,” da taimakonsa tashiga bandakin tarufo, jin ta dade baikuma ji motsin ruwa ba yasa yabude bandakin tana zaune acikin bathtub din tana kuka, tausayinsa yakamata bata rai yayi sannan yace “zanmiki wankan” kallonshi tayi adan tsorace anma bai kulata ba, yarufo bayan gidan yakamota, tagara yimasa gaddama, haka yacire kayan yakunna showern kunya duk yarufeta, tagagara motsi haka yacudeta kaman jaririya sannan yadaukota ya ajiye, ya shafa mata mai yaciro mata kaya marar nauyi wani dogon riga ne haka, daya ciro yasamata, yahada mata tea a falo yazo yazauna ya lallabata tasha, itakam sai ganin ikon Allah take, mutumin datake masa kallon soko yau gashi soko na aikinsa,saida ya tabbatar batada matsala sannan yashiga yadau wanka, yafito fannin bayi yanufa, yasa akira masa wanda suka dauki aliya , sannan yafara fada akan me zasu taba mishi matarsa nemo dogarai yayi yasa aka basu jikinsu, saidaya tabbatar kowacce taji jiki sannan yanufi fannin yakolo yagaysheta anan tadada basa hakuri yanuna bakomi , yanufi gun falmata wacce tacika fam tana jiransa, zuwansa tafara masa fada akan me zai hukunta bayi sannan yafara gayda kishiyanta kafin ita, tunda tafara magana baice mata uffan ba harta gama,hakan yakara tunzurata tuni ta kullace aliya aranta, gani takeyi ta mallaka mata da, fitowarsa yanufi gun mahaifinsa suka fara gaysawa, kafin yakoma fanninsa, tare suka wuni har dare alokacin aliya tafarajin wannan kukan kuma, tuni tafara tsorata [10/29, 7:39 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR haka suka kara zama adaren basu runtsa ba, tuni aliya tafede rashin bacci yafara takurata. Ga ciwon kai ita saitana jinta asama itabaa kasa ba, baa sama ba, kaman jira kaman ana yawo da ita, Ga rashin kwanciyan hankali haka suka jera sati ahaka bata bacci daredare dasafe kuma inta kwanta saitahau mafarki,ganin abun banayi bane yasa yusuf yakira sufyan suka gayamasa abunda yafaru tunda yake baitaba shiga tashin hankalin ba, nan yafara dana sanin amince mata ta auri yusuf, bai kawo kowa aransa ba anma yasan akwai wanda basuson aliya da yusuf, akwai wani malamin da sufyan yasani donhaka ya umurci yusuf da aliya suje gunshi, Babban malami ne yanada almajirai nan yusuf yabukaci ganinsa, aka musu iso a zaure, malamin yashigo , aliya sanye takeda babban gyale yarufe fuskanta hannunta ne kawai awaje, malamin nazama, yace “subhanallah, ciro abun hannunki” dasauri tafara ciro zobunan, yace “a a. Na azurfan” cirowa tayi tamika masa, yakarba dasauri ya kira almajiri daya yamika masa sannan yace yaje ya sa awuta, sannan yajuyo yakalli aliya tareda cewa “baiwar Allah kinata yawo da tsafi ajikinki, ai kurwanki ake yawo dashi asama, ” tuni jikinta yafara bari, yusuf yakalleta tareda cewa “waya baki zoben?” “Acikin kayan aurena nagani” baice komi ba inda malamin yace sutafi meke tafe dasu, tamishi bayani zalla zallah Yace “dafarko jirin dakikeji wannan zoben ne, shiyake jawo haka yawo ake da kurwanki asama,, nabiyu kuma asiri ne akamaki mai suna janduks, shi wannan sihiri anayine wa mutum inda mutum zaisa ranshi a tsaka,” daga yusuf har aliya gyra zama sukayi don kowannensu yagama tsorata jikinsu na bari, musamman aliya, duk dabarun sihiri data karanta bata karanto dawannan ba, “Sihiri ne akewa mutum na kwana ashirin, dafarko akan dauki hoton mutum kowani abu dakika mallaka a yi amfani dashi, sannan wannan sihiri shine zakina jin kukan dabobbin dakikafi tsoro, inkin kwanta kuma zakina mafarkin kura, shiwannan kura zaina binki ne,har kwana ashirin idan kuran ta yakeki zaki mutu acikin kwana ashirin, idan kuma ke kika yaketa zata koma kan wnda yayi sihirin, kinada wani tabo ajikinki dakika samu a mafarkin?” Ta gyada kai tareda cewa “kuran danake mafarkinsa kullum inna tashi sainaga cizon ajikina yayi baki”. Yace “haka sihirin take, yanzu zanbaki dabarun karyawa, inbaki karyaba zaki iya rasa ranki Allah ya sauwaka” aliya da yusuf jikinsu na bari sukace to inda yaci gaba da bayani yana cewa “Akofar dakinki ko kuma tsakar gydanki kinemi rami akwai inda aka birne laya kiduba, dole sai an birne laya medauke dasunan wanda akeso ya mutu din, kinemo acire, sannan inzakiyi bacci kikaranta yasin, fatiha, falaq, nas, da suratul jinni, kikaranta kikwanta zakiyi mafarki anma zakisamu karfin yakanta, donhaka kisamu ki kashe wannan kuran hakan kadai zaisa kizauna lafiya, sannan dalilin ganin wannan kuran wanda yayi asirin kowani dare yana kona laya da takarda me dauke da sunanki donhaka saiki dage da addua wani lokacin mune bama nemawa kanmu tsari, munsan sihiri nakama mutum anma zamu iya karyawa,ki kasance kina bacci da alwala, ki kasance kin rike hisnul muslim,ki guji zama cikin najasa, Allah yana taimakawa wanda ya taimakawa kansa ne” Sunmasa godiya sosai sannan suka mike sukafito dakyar aliya take tafiya jin ance kwana ashirin, acikin kwana ashirin taci bakwai, ashe dama haka abdullahi yaji daya bata kodanta yasan zai iya mutuwa kowani lokaci, ashe haka yaji? Innalilah kuka tafarayi yusuf harya tukata gyda. Sannan yafara lallabinta, dakyar tashanye kukan tafito bilkisu takira tareda cewa tanemo dogarai, suna isowa tafito itama tace sufara tone gun duk inda sukaga laya kowani abu na alajabi su kawo, tana tsaye akansu tana jira nima benaxiratu nadau gatari daya nafara dube du[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA (THE END)  benaxir  November 1, 2015  Hausa Novels  126 Views [11/1, 7:04 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR (First of all, m sooo sorry kunjini shiru kwana biyu nd i couldnt explain myself, y’all should find a place in ur hrts to forgive me,bikin one of my closest frnds nayi. Sunyi kokarinsu don ganin sunsamu laya kowani abu makamancin haka don samun babban kyauta kamar yadda aliya tamusu alkawari, basu sami komi ba haka suka hakura har dare ana abu daya, aliya duk tashiga damuwa da tashin hankali, anki abarta tahuta da mijinta ankuma ki abarta tazauna lafiya, Daredare takaranta surorin kamar yadda akace tayi takwanta zuciyanta cike da son kama kowacece, acan tafarajin kukan kulya da kare nan da nan tafara Allahumma ajirni fi musibati waakrijhi khailriha, tanayi tana hadawa da auxubillah, ahaka tazauna yusuf na gefenta yana tayata addua yagagara bacci duk da taso yayi anma yaki, hakan yasa suka zauna suna ta addua ahaka har asuba, asuba nayi yafice masallaci itama tayi sallolinta sannan tawuce kan gado , tana addua harta jira bacci ya kwasheta Tayi dan mafarkan Allah kuma yabata nasara ta jiwa kuran ciwo, itama ta ji ciwo bata tashiba sai karfe daya. Inda tayiwa yusuf bayani yace tacigaba dahaka har na sati kamar yadda malamin yace zata kashe kuran inhar tana kokarin fada dashi, [11/1, 7:35 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR kullum tana fada dashi kuran yadawo baida ishashen karfi, aranan tafito tana son zuwa fannin yakolo ko zasu gaysa, wani bakin abu tagani rana ya hasko mata, harta wuce takoma tadauka ga mamakinta laya ne, hannunta na bari tadauka tana addua, harta isa dakinta tana isa tanemi babban container tazuba sannan tarufe, wayanta tadauka takira yusuf yana dauka muryanta na rawa tace “kayi sauri kazo gyda, don Allah kayi sauri” yadda yaji magananta tuni ya tsure dama yashiga kasuwa ne babu shiri yadawo fada, tana zaune a falo yashigo anan tanuna masa shima ya mugun tsorata anma dole yadanne nasa don karta rude, wurin malamin suka nufa dashi, yadauki layan sannan yace tayi addua ta tofa ajikinta ta kona layan agun, aikuwa tana haka yace toh yanzu saura takarasa nakasa kuran inhar tayi haka toh ba tabbas wacce tamata wannan sihirin, asiranta zai tonu dahaka sukayi sallama dashi. Sunkoma gida sukaga fannin falmata a cike arude yusuf yashige aliya na biye dashi abayanta, falmata ce adaki tana kwance sai kuyangu akanta, dakuma yakolo su umma uwar soro, mutane dayawa dai haka, hankalinshi tuni yafara tashi, yaleka ta dakyau ga mamakinsa ganinta yayi kaman ba itaba, kamanninta duk yacanja, tacanja wasu manyan kuraje ne suka fito mata, ga doyi kuma, kowa hannu na hanci tuni yakai nashi hannun , anan akace kowa ya watse aka barsu kadai adakin umma uwar soro tace takai awa daya ahaka, don tunda jakadiya tazo tamusu bayani akan falmata nakwance kawai saiga kurajen sunfara fitowa abun kuma bai tsayaba, shiru yayi zuciyarsa na masa zargi, anma duk dahaka yazauna, duk iya kokarin da akayi dawasu likitoti abu yaki tafiya wari yaki tsayawa, falmata acikin dakikai kadan tadawo abun tausayi, wanda hakan tuni yafara yawo a fada, falmata tayi sihiri yadawo kanta acewarsu kenan, kowa sai Allah kara yake, dama ta addabi kowa acikin fadan, kowa yanata farinciki, yayan cikinta ne kawai suke kukan abun, suma ni benaxir na tabbata don ita tahaifesu shiyasa, inbahaka ba babu yadda zaayi suji haushin abunda yake samunta, yusuf dai zama yayi agefenta yana kallonta yarasa ma yazaiyi sannan kuma mezaice mata, [11/1, 8:01 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR dahaka tana kallonshi tana zubda hawaye, aliya ma tana daga gefe tayi tagumi duk tsanar falmata datayi yaukuma tausayinta taji, tamike tadauko ruwa sannan tabata, tana jingine a kujera, tana kallon aliya yusuf ma nagefe, Wani abun mamaki shine tun ranan aliya tadena jin kukan kare da kulya, sannan tafara baccinta abun ya matukar bata mamaki hamdallah tarinkayi wa Allah tana godiya, tayi salollinta, Falmata ankaita asibiti anma sunbada shawaran ayi maganin gida nan da nan aka nemo mai maganin gargajiya, yusuf kuwa yahado da wannan malamin bayan dan magana dasukayi sai malamin yace mishi tabbas itace, yusuf jikinshi yayi sanyi donhaka dakyar yakira aliya malamin itama yamata bayani kuka tayi sosai jikinta yayi sanyi, tanata tunani duniyan shinawa yake? Da girmanka da mutuncinka zaka nemi gun boka , me boka zaimaka wanda Allah baimaka ba? Mezaka tanadar wa kanka agun boka? Daya wuci wulakanci da dizgi, duniyar kanta nawa take da mutum zai sa rayuwarshi ta kaskance, ta zama wulakantacce, Takoma gun falmata anma bata canja mata fuska ba, tacigaba da zama tana jinyarta da bayin dasukenan, Wannan hali na aliya yasaka falmata jin kunya, taji inama tunfarko bata kullaceta ba, bata mata asiriba, sannan bata musguna mata ba, tana kuka taroki gafaran aliya takuma nuna nadamarta a fili, aliya tanuna mata bakomi hakan yasa tacire komi aranta, mijinta kuwa tuni tasamu kanshi duk da dafarko yana fushi da halin mahaifiyarsa aliya tayi iya kokarinta ta gwada masa muhimmancin mahaifiyarsa dakuma hatsarin fushi da ita, tabbas yayi alfahari da aliya domin kuwa tazamto masa garkuwa, itace macen da annabi yace a aura wacce zata gyra maka yayinda kashiga hatsari wacce zata zamo maka garkuwa,yana alfahari da aliya yana kuma tausayinta a matsayin marainiya, Falmata ahankali tafara samun sauki da yusuf yahado malamai anata addua da saukan qurani, domin sarkin yayi tashi harya gaji, Allah cikin ikonsa tasamu sauki duniya takoya mata hankali ta nutsu tazama mutumiyar arziki domin kuwa hatta bayi darajasu take, kansu yazama ahade da yakolo Yayinda aliya tahade da mijinta, abun alfahirinta,garkuwan jikinta sannan sanyin idaniyanta Sufyan yazo ya auri hassana wacce ta tare a gydan da sufyan ya kare mata,zaman lafiya alhmdlh nima benaxir omar ina jinjina muku dakukayi hakuri dani duk da matsalan dana rinka samu bansamu na karasa muku da wuriba dakuma rashin cigaba akan lokaci, nagode sosai Allah yabar zumunci Ina gayda rukayya bayero for helping out, yu really made me do dix, Kausar nd ummi aisha na sadaukar da littafinnan agareku don nuna godiyata agareku, Tom ni benaxir omar nagode muku saikunjini asabon labarina dazanyi anan gaba An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7