Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
ne bayan bilki? Kokuma gaskiya ne ba ita takashe shiba? Hakadai yazauna agabanta ganin tadamu batasan yazo gunba yabuga kanta kadan tuni takaleshi yayi murmushi tareda cewa “waya taba minke yanzu na ajiye tarbiya ta da rawani na Nazuba mai farillai da mustahabban rashin mutunci” kallonsa tayi tareda cewa “kaifa asalim dan tasha ne ko baa taba gayamaka ba?” Yayi dariya tareda cewa “gashi kinfadamin? Bazaki kira bilki kiji daga gareta ba?” Jin yafadi haka ta tabbatar gwadata yake donhaka Allah ma yataimaketa bata fara fadaba, donhaka tace “a a bani da abun fada mata”* tuni yaji sanyi aransa don yatabbatar da ita tasata zata bukaci taji wani abu tadin mutuwan suka farayi inda tabugi cikinsa taji abunda takesonji , tabbas wanda yasa maganin daga kicin yafito tadaisan yayanta bazai je as bawa ba don bawanda zaiyi tunanin haka , toh yazama kenan yana da mai taimaka masa bata idar da tunaninta ba yacigaba dacewa “yanzu inaga bikin abdullahi zaa daga saboda rasuwannan, ” “Wacece budurwarsan nan?” “Yar galadiman yanzu” “Ni naganshi ma dazu dawani da na tambaya akacemin dan galadima marigayi ne” “Toh bantambaya ba wani galadiman ba, tunda san ke kadaice agun wanda yarau da ko?” Gabanta yayi mummunan fadi anma tadaure takirkiro murmushi zuciyanta na bugawa dakarfi tace “ae! Nikadai suka haifa saidai dayan galadiman, wat a bad luck duk sauran masu sarautan basu mutuwa sai galadima!” Ya jinjina kadan sannan yace “yanzu gashi wazirin yarasu shima ai Allah dai ya dakatar ahaka” “Ameen” “Sarki yasa ayi bincike sosai you have to be careful sosai, don nasan wannan bazai dauka dasaukiba acikin fadansa akashe mutum” Duk ta kagu yabar mata dakin tayi tunani donhaka tafara baccin karya, ganin haka yasa yace “opps! Harkinyi bacci barin koma ” Yana fita yarufo mata kofan tawaje tuni tamike tazauna dakyau, yayanta yaje as mutumin arziki yana shuka tsiya daga kasa, lalle toh ai babu marabansu da ita, gashi batama san sunan yayan ba, yanzu yazatayi? Tunani yazo mata tunda yusuf yace suna yawan zama tare dole ta ziyarci fada, Taci wanka tasha kyau sosai abaya ne bski ajikinta tafice tsum tanufi fada ganin fadawan suka fara tsareta tanuna musu cewa tazo gaysheda gimbiya yakolo, dolenta tajira aka tambayo gimbiya sukace ai aliya ce. Nan tabada dama aka shiga da ita, Tagama survey dinta kafin tanufi fannin yakolo tana isa yakolo tagwada farincikinta sosai takuma ja ta ajiki, aliya tagwada mata yau tazo gari don tagaydata nan da nan yakolo tace “toh dole nabaki masauki, zaki zauna a fada harsai lokacin dakika ga daman tafiya” [10/4, 6:11 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya tanuna jin dadinta tareda cewa “barinjr hotel din dana ajiye kayanna nadebo tukuna” dahaka suka danyi tadi aliya ta musu taaziya inda yakolo ta amsa, fitowa tayi tanufi fannin da aka kaita taroki bayin da su kira mata bilki don Allah sunji dadin ganinta suma dahaka suka kira bilki itama magana ce acike a bakinta, nan ta zayyana ma aliya cewa bawanda yasan waye , aliya ta tambayeta waye abokin da abdullahi ke shigowa dashi tace ” awh dan gidan galadima marigayi ne , sunanshi sufyan, tun wancan satin yazo” “Kisa masa ido! Sosai fa” “Toh” Suna rabuwa tafito tanufi gydanta tadibi kayanta na sati biyu hade da kayan sallahnta sannan tadawo fadan, tuni ta makale wa fannin yakolo tunda taji labari cewa sufyan da abdullahi suna yawan shigowa” tuni shakuwa tashiga tsakaninsu domma duk yaranta mata sunkoma makaranta saura abdullahi ne shehu ma bayanan, aikuwa an idar da sallah sai gasu sunshigo tana zaune akan kujera suma suka shigo abdullahi na ganinta yafara murmushi “aliya ce yau agydannan?” “Yarima na gaydaka” nan tajuyya takalli sufyan saida gabanta yafadi shima kallonta yake, kammaninsa daya da babanta, tabbas yayanta ne babu tantama ta amince, Allah mai iko anma yadda yayi ta tabbata bai ganeta ba, taji dadin haka donhaka sai suka gaysa sunadan tadi, yakolo tashige daki tabarsu inda sukasha hiransu sosai anan tadansan wasu abubuwan akanshi, nacewa ashe kasar waje aka tafi dashi tun primary yaje gun kanin babansu a cyprus anan yafara makaranta harya gama, jitakeyi kaman taje ta rungumi yayanta anma babu dama,koba komi tanada danuwan dazata kishingida ajikinsa idan tashiga damuwa, basu tafi ba sai karfe 10 sun sake sosai abdullahi ma baida matsala har cewa yayi washegari zasuje gun matar dazai aura takuma amince, , donhaka washegari dasuka shirya tashiga mota abdullahi na gefe sufyan na tukawa, suka isa yarinyan tanada kyau ga kamala da mutunci da dattako, tana kallom aliya da sufyan tace “anma kai yayanta ne ko? Kuna kaman sosai” gabanta yayi mummunan fadi bashiri taji sufyan yayi dariya yana cewa “tsabar soyayya ne muka dawo kama, budurwa tace fa” tace “awhh gaskiya kam, Allah bar soyayya” Yabar aliya da tunani tuni shima abdullahi yafara tsokansu Yusuf yaje gidan aliya yaji shiru yabude da extra key dinsa anma duk dahaka baiganta ba, akwai kayanta donhaka saiyayi tsammani kotaje wani gurine ganin har karfe sha daya yatabbatar masa da bazata kwana a gida ba, aduk zamansa da ita baitaba jin takira sunan wani ko taje gun wani ba balle yayi tsammanin zataje, tuni yafara tunani lallema tayi sabon saurayi, tafita dashi kishi duk yabi ya turnukeshi dahaka yadawo, washegaru ma yakoma shiru bata dawi ba dayagaji yakoma shigowansa gida kenan yaganta tafito a mota tareda abdullahi dakuma sufyan, tunaninsa tadaure kayan jikinta yatabbatar masa da ba baiwa bace tadawo, toh metazo yi? Wannan yarinya da kwainane. Suna tafiya yakamota tabaya tajuyo tareda fuzge hannunta menene! “Mekikazo yi anan? “Meruwanka?” “Bazaki fadaba?” “Ziyara nazo na sati biyu, kuma karka kuskura kanuna muna tare don zan dizga ka” Yayi mugun tsorata lalle yarinyannan munafuncinta ko sallah bayayi, Aliya da sufyan da abdullahi sun shaku sosai don ran sallah saidata fita tagansu suna hawa, duk da ta kalli masoyin nata wanda bakin ciki yasa yanzu yake shareta yakoma ruwa tsundum ba shan giyansa, Satinta biyu cif tasamu tahada duk wani info din dazata hada, ayadda taga sufyan bai ganetaba ita aganinta tagama dashi duk wani hanyoyinsa zata toshe, sunmata goma na arziki kafin ta tafi gydanta takoma ta zauna tana tunani tabbas yakammata tamike tsaye jin datayi abdullahi da sufyan suna magana a mota ya tsaya mata arai tagagara ganewa kuma ” toh wanda bashida laifi ya mutu dalaifin wani” Sallah tayi takwanta acikin barci taji kaman ana shafa kafanta bude ido tayi mugun figita tayi don ganin wanda ke gabanta, sufyan ne sanye da kananun kaya, tajuya takalli dakin ta tabbatar dacewa ae gydanta nefa sannan ta kalleshi “sufyan mekazo yi anan?” “” hello little sister! Long [truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 15  benaxir  October 5, 2015  Hausa Novels  103 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR “So am d fool here” yadanyi murmushi sannan yace “Kinda” zama yayi agefen gadon yayinda itama tamike tazauna, “meyasa kika kasheshi? Kinsan hukuncin kisa?” Kallonshi tayi a harzuke sannan tace “meye zakawani ce nakasheshi? Sharri zakamin?” “If bake kika kasheshiba toh waye?, yayi daidai ma domin kuwa bashi yakashe baba ba!, bakuma sarki bane” zare ido tayi jin yace bashi yakasheshiba , sannan jin kuma bashi yakashe mahaifinsu ba toh waye? , “keda kike zaune anan fiye da watanni ni acikin sati naxo nasamu lbrn dakika garara samowa,” “Yoo toh ai kai namiji ne ka manta? Zaka iya shiga ka fita duk inda kakeso, nikuwa mace inada limits,” “ba abunda ke tafe dani ba kenan, gidannan zaki tattara kibarshi acikin satinnan, kikoma gydan inna nagayamata zaki koma,kina ya’mace kina zaune ke kadai, in wani abu yafaru fa, kinje kin koyo halin yahudawa,” “Nifa zaka takuramin wlh, kaida kaje can wani bariki ne baka koyo ba, angayamaka bana lura dakai da abdullahi ne? Kuma akanme zanje gun inna? Nasan da ita ai naki zuwa” “So kike kizauna saboda wannan katon yusuf din yana zuwa kuna rufe daki kubiyu ko? Mekuke ayyanawa?” “Awhhhsh yayah kanada zato, nifa ba abunda yataba hadani dashi!” “Ki rantse baitaba rike yatsanki ba” “Ae baitaba ba” tana fada tana murkuda baki, hannu yasa ya riko kunnenta tareda cewa “ko ki tattara ko namiki duka” “Wayyo yayah sakemin kunne zafi,” yasake tacigaba da murguda masa baki tana tattare wayoyinta “nikam ka fita wlh, duk kazo ka takurani” “Ba inda zanje, ki zauna ki sauraren, waziri baya gari lokacin da akayi kisan baba, wanda hakan yana nuna baisan da labari ba, alokacin yaje taaziyan mahaifin matarsa, dole mukara tsananta bincike,” “Toh naji katafi sai anjima”mikewa yayi yafice tareda murmushi rufo kofan tayi, tazauna tana tunani tasan yadda yafara maganan nan bazai barta ba saiyasamu biyan bukata, duk yana nema yatakurata tana zaman lafiyata, yusuf ne yashigo fuska a murtuke ganin yazauna bai kulataba tace “meye kashigomin kaman gunki” Bai kulataba sai haki dayakeyi ganin zai bata mata lokaci tadauko jakanta sannan tafito harzata wuceshi yamike yarufo kofar, ganin yatsaya kaman gunkin gasken, ta harzuka sosai tabugeshi da zummar tawuce hannu daya yasa ya bangeta, saigata a kan gado, yakoma yazauna akan kujera sannan yafara “Aliya kinsan inasonki, kuma bana danganta soyayyanki dakomi, aliya meyasa kike min haka? Meye tsakaninki da sufyan yanzu naga yafito daga gydannan? Dama dalilinki nazama a fada kenan don ku shaku dashi? Meyasa kike haka aliya? Kina wahalar min da zuciya” Dariya tayi tareda cewa “sufyan fa kace,” Mikewa yayi yabuga table din dake gabansa dakarfi sannan yafice binshi tayi da kallo don mamaki take harta mike tafito saigashi yadawo rike kanta yayi dakarfi, yaki sakewa, gashinta nazafi tanacewa “yarima ka saken, dazafi nace kasaken HALACCIN SARAUTA 16  benaxir  October 6, 2015  Hausa Novels  110 Views [10/6, 7:05 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Bai saketa ba baikuma kulataba, kan kujera yakaita tazauna zuciyanshi na kuna yaja tsaki yafice, duk da zafin datake ji bashi zaisa tagagara yin dariya ba, tadauko ribbon ta tace kan sannan tafara hada akwatinta,wayanta taji yana kara tadauko tareda dubawa antynta bashiri ta dauka tasa a kunnenta “Anty ina wuni inashirin kiranki” “Bakomi yakike? Kinhadu da yayankin?” ‘Ae yatakurani wlh” “Hehe amfaanin yayan kenan “Cewa fa yayi intattara inkoma gun anty kuma wlh banaso, don bazan sake nayi abunda ke gabana ba,” “Ai yafi kina ya mace ba daidai bane kizauna a gyda ke kadai, shiyasa tunda nake gayamiki banaso ai bayadda na iyane dake da taurin kanki “Kai anty ni yanzu mene ne lbr?” “Lbr shine ki lallaba danuwanki kimasa biyayya, shikadai gareki shine gatanki, maganan ramakon nan kibarshi haka, kifito da mijin aure” “Hahahahaha anty zakisa cikina yayi ciwo, cewafa kikayi aure, nida ko mashinshini bandashi” “Kedai kikaki sauraransu, bari zantura miki adduoin dazaki nayi kingane?” “Toh anty sai anjima” Kallon wayan ta tsayayi tana daria, ita sai yanzu tunanin aure yazo mata, bayan tadan kimtsa kayan ta tattara tafito don zuwa siyayyan dan abunda baa rasaba, tsintar tsohuwa tayi ahanya sukayi ta tadi ta shagala sosai, komawanta gyda tasamu dakinta fanko sufyan yasa an tattara dakin tsum, haushi taji kaman ta tashi sama anma babu yadda ta iya, wayanta tadauka da zumman kiranshi saita tuna batada numbanshi, tsaki taja rike da ledodin hannunta tanufi gydan inna tashiga da sallama inda innar taketa murna kaman ta hadiyeta, ga kayannan kwartaye sunfi goma suna shigarwa hakan yasa tadaina mamaki domin kuwa ita tasan cewa Dan zuwanta kasuwa da bata wuce awa uku ba baikai ace an tattara mata kayanta ba, wato ya nemo kwartaye don su samu suyi sauri kartahanasu kwashewa, tana tsaye tana gantsaran goruban data saya tana kallonsu harsuka kimtsa mata kayanta tsaf, harzasu tafi tace “ai baku gama ba” takarbi tsumma da tsintsiya agun inna tabasu suka share suka goge, taciro musu zanin gado suka gyra, sannan tayi murmushi tareda cewa nagode! Koba komi sunji jiki, tashiga dakin yaji komi tsaf kunna a.c tayi tasaka turaren wuta sannan tashiga wanka, fitowarta tasamu inna ta aiko mata da abinci ,tabude taga tuwon shinkafa ne da miyan agushi yasha kasusuwa, bude ciki tayi sosai don bata cika girki ba, inzatayima bata yin tuwo Bude ciki kawai tayi taci tayi nak tayi gyatsa sannan ta mike akan gado, Yusuf kuwa hanyan gydanta yanufa yaga babu kowa, hankalinsa tayi kololuwan tashi,domin kuwa duk a tsammaninshi abunda yamata ne yasa tacanja gydan yasan bakaramin wahala zaisha ba kafin yakara samota, haushin sufyan da takaicinsa yamasa yawa, gashi a ranar anfara bikin abdullahi wanda da har andaga saboda mutuwan waziri anma sarakunnan suka nuna badamuwa adaura kawai don matan makaranta zata wuce daganan, fada tacika makil yana tunanin ta ima zaiga sufyan don yatambayeshi, saanshi daya zaaje dinner duk da baiyi niyyan zuwa dinnern ba anma haka yashirya tsum yaja mota yanufi gun, duk iya kokarinsa na son ganin sufyan bai ganshiba, haka yahakura yazauna kanshi akasa, matan dake gun duk hankalinsu yayo kanshi dn yusuf bana zubarwa bane saidai shiyana ta tunanin masoyiyarsa ba, sufyan ne yafito manni wa amarya da ango [10/6, 8:35 PM] Adda Bena: Yusuf na ganinshi yamike yanufi kansa cikin bakin ciki da takaici har wani duhu duhu yake gani, yana isowa ya damko sufyan dakarfi sufyan yajiyo tareda matsowa yana dan taka rawan shakiti bobo, yusuf yace “Ina taje?” “Bangane ina tajeba?” “Bata gayamaka inda zatajeba?” “Tafadamim, baikamata kasaniba, inaso kafita harkanta, kafita hidimanta, ba saar yinka bane,” Yusuf daya kara damkoshi sai tunkudr shi yayi akasa dakarfi wanda saida hankalin mutane yadawo kansu HALACCIN SARAUTA 17  benaxir  October 7, 2015  Hausa Novels  100 Views [10/7, 9:02 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR sufyan yamike yana karkade kayan jikinsa tareda kallon yusuf, yusuf baiji kunyan wani abuba yakara nufa kanshi ya damko shi dakarfi abdullahi wanda ke filin yanufi kansu don rabasu, anma yayi latti domin sufyan yasha naushi, yusuf tsakaninsa da Allah ya mammaujeshi alokacin dakyar abdullahi yasamu ya kufce sufyan sannan yashiga tsakaninsu, wasu ne sukaja yusuf don yadena abun kunyan dayakeyi wanda magana tuni ta yadu, yarima yana fada ,sufyan mota aka nufa dashi don yawuce masaukinsa gogan naku kuwa fada aka wuce dashi alokacin zuciyarshi tafasa take duk ya rikici a gigice aka kaishi fanninshi falmata ce tanufo kanshi don labari ya isota cewa fada yake akan liya, cikin fushi wanda bai taba ganinta aciki ba ta umurci kowa ya watse yabarta da danta “yusuf mekakeso namaka? Kai ba karamin yaro ba yusuf, wani irin rayuwa ne haka yusuf? So kake ka kasheni?daga yau acemin kasha giya, jibi mata, yau kuma akan baiwa kake fada? “Kidena cemata baiwa saboda a yanta ta, rabon dakiji anganni da wata tun yaushe? Tun ran da nahadu da aliya!, giya fa? Tun yaushe???” “Da Allah min shiru da bakinka da rimi rimi abun arziki kadena sha, meyasa kadawo sha?” “Saboda narasa wacce tahanani sha” “Kana nufin kacemin ba don Allah kabari ba sai don ita?” “Dazan bari dana bari tuntuni, anma don ita nabari Allah nagani donhaka karkiga laifina. Kinaso in nutsu kema ya kamata kidena musgunawa yaran wasu, kidena neman batanci da yaran wasu” Hannu tasa ta gaura masa mari, wanda saidayaga walkiya a fuskansa.”ina magana kana magana?; yaushe nahaifeka? Kai wato mace dadi ko, kaje ta tusaka kasan pant dinta,” “Nifa ko tabata bantabayiba” “Yimin shiru munafiki, duk duniya bawanda karaina kaman ni, nagaji zangayawa sarkin saimugani ko shi zaka ji maganansa!” [10/7, 9:09 PM] Adda Bena: Bata saurari mezai ce ba tafice, fanninta tanufa, gaskiya yakamata tadauki babban mataki akan aliya, jakadiya takira tareda cewa ” kinemomin duk inda aliya tashiga ki kawomin ita nan” Aliya kuwa tana zaune akan gado tana game din candy crush bacci yaki daukanta, sufyan ne yakirata awaya tadauka “Kekuma kina tareda mahaukaci ne bansaniba?” “Waye mahaukacim?” “Mahaukacin saurayinki mana, zaimin hauka a bainar jamaa, total yarinta?” Tana kwance ne saidata mike, ita duk tunaninta hala yusuf yasha wani abune yaje da zafin kishinsa yayi wani yarintar, “Yaya meyasameshi? Yana ina? “Anma zanmiki rashin mutunci, bazaki tambayi jikina ba saina wani kato? Nidana sha duka?mtsw” “Kayi hakuri bazai karaba, anma don Allah yana ina?” “Gidan ubansa” “Shikenan don Allah kana hakuri dashi” Bai saurareta ba yakashe wayansa don yaga itama giyan soyayyan ke dibanta [10/7, 9:29 PM] Adda Bena: Ta kashe wayan takira wayan yusuf wanda ke kashe ahaka taketa tryn har bacci ya kwasheta, bata juyaba sai asuba, Har rana tana tryn numbansa baya shiga ta tattara sallayanta tanufi tsohon gidanta a kofar gydan taja kujera tana zaune tayi hakane dan yusuf ko zadu hadu, wasu yanmata ne guda biyu kana ganinsu kaga yan biyu don inka cire kayan jikinsu dasuka saka daban daban kominsu na siffar jikinsu iri daya ne, suka nufo kanta daya sanye da abaya daya kuma sanye da atamfa Mai abayar takarewa aliya kallo bisani tayi tsaki sannan tace “yanzu wannan jaka dabbar ce daman? Baka mummuna kaman kasam takashi na!? Shikuwa yarima meyagani anan? Mai atamfan itama takare mata kallo sannan tace “bar munafiki nema yake yajamin raini da kaskanci, ta ina zaahadani dawannan gidahumar? Banza talaka!” Aliya zuciyanta na tafasa musamman datagano maganansu cewa mai atamfar ce budurwar yusuf. Bata kulasu ba tadanne zuciyanta tanufi sgiga gidan, coke din hannunta tasaka ta watsawa aliya a jiki, wani juyowa da aliya tayi ta damko makokoronta “KE WLH TLH NI KARAMAR MAHAUKACIYA CE!!!ZAN ZUBAMIKI RASHIN MUTUNCI!!! Kuyi hkr daga yau har zuwa saturday zakuna samun kadan kadan due to am a little bit busy, HALACCIN SARAUTA 18  benaxir  October 8, 2015  Hausa Novels  109 Views [10/8, 8:34 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR mai hijabin wacce itace hussienan takalli aliya cikin rashin tsoro tasa hannu itama tariko wuyanta, tareda cewa “ke angayamiki tsoron ki akeji?banza karuwa jaka dabba!” Aliya tasa hannu ta make bakinta tareda cewa “ki iya bakinki don banda mutunci” “Dama ina kikeda mutunci banza” Aliya fuzgan jikinta tayi tareda tattare komatsanta tafice tabarsu agun, gyda tanufa ta zauna akan kujera cike da bakin ciki da takaici, yusuf tasan zainemeta, anma wasu irin dabbobine wannan? Lalle zasugani shikuma yusuf zaixo yabata labarin suwaye, Sufyan [10/8, 8:59 PM] Adda Bena: Ne yashigo kafanta yatare hanya ya mauje kafan yawuce hakan yasa ta tashi, tareda kallonsa “haba yaya dame zanji bakin cikin wancan yanmatan komeye?” “Wasu yanmata?” “Yanmatan yusuf bansansuba, kuma baitaba ban lbr ba” “Wannan saurayinkin baiyi kama da mutum ba, nima haka yamin hauka, bawannan bane takawoni, angama binciken wanda yayi kissan waziri ansamu cewa wata baiwa ce tashigo fadan itada mahaifinta waziri ya kwace gydansu da duk wani abu dasuka mallaka. Sannan yayi hanyan sanadin mutuwar matarsa, yanzu dai zaayi hukunci jibi, [10/8, 9:35 PM] Adda Bena: Kuma abincike na nasamo cewa akwai wani alh.hamidu shine kanin galadima na yanzu suna tare da baba randa zai rasu donhaka dole munemi hanyan dazamu sameshi donjin bayaninsa,” “anma yaya fisabillilah” Bai saurareta ba yafice don yunwa ne ta isheshi cikin gyda yanufa yatarar da inna yaci yakoshi sannan yafice, fitansa kenan saiga yusuf wanda CID dayasaka su suka masa kwatance ya iso gydan, sallama yayi yashigo suka gaysa da inna wacce take zaune yadda yamata ladabi taji tana kaunarshi yatambayi ko aliya tananan, tace akaishi fanninta, aliya tamike kafafu batasan da shigowanshi ba hannu yasaka ya mintsineta, “innalilalh ” tamike a razane wanda hakan yasa yayi murmushi, bata rai tayi kaman tunda aka halliceta batayi dariyaba tuni yasha jinin jikinsa, “meya faru don Allah?” Bata kulasa ba tamike tagyra jikinta tajawo gyale sannan ta yafa sannan tace “meye haka kashigowa mutane ba sallama, ko kamanta dakin mace ne?” Yayi mamakin magananta zaiyi magana tace “kafitamin kuma karka kara dawowa” baice komi ba kuma bai tashiba hakan yasa ta kwalawa idi kira, almajiri ne idi kato jibgege, hakan yasa yusuf naganinshi yamike jiki a sanyaye HALACCIN SARAUTA 19  benaxir  October 10, 2015  Hausa Novels  115 Views [10/10, 8:04 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Yana fita tarike kanta domin ciwo yake mata, itakanta tasan matsananinci so dakuma kishin datakeyiwa yusuf bana wasa bane,gashi yaje yadauko maganan yanmata yazatayi da rayuwarta inhar hakanne dagaske? Shikenan zaidaina sonta? Kawai tazauna tafashe da kuka, kuka takeyi nanma ta tuno da iyayenta tafara wani sabon babin kukan, inna ce tashigo ganin tana kuka tafara lallabinta dakyar tayi shiru. Itakanta tasan cewa aliya tayi rashin iyaye, saidai batason ta tada mata hankali ne anma ganin tadamu da ramako gakuma kukan datakeyi, don itadai tasan cewa dakyar rana yazo yafadi, aliya batayi kuka ba,a fuska akwai karfi anma zuciyanta mai rauni ne, saidata tabbatar cewa aliya tayi shiru sannan tace “inaso ki goge hawayenki ki saurareni, yau zanfadamiki tarihin iyayenki, tarihin rayuwarki, na boye da wanda ke kanki bakisaniba hatta yayanki baisaniba” jin haka yasa aliya ta gyaro zama tashare hawaye sannan tace “inajinki inna” “Mahaifinki hassan adamu shine galadima na 55 a garin yombi, kuma ya gada ne kaka da kakkani, sunyi auren soyayya da mahaifiyarki aisha, wacce tahaife ku rai biyu dake da sufyan, mahaifinki dan biyu ne haryau baki taba tunanin kitambaya ba?” Alokacin aliya ta tabbatar batayi wayo ba, tunaninta yayi nisa a yin ramako har bata hango kananun matsalan dake gabanta wanda matsalan da ake samu yanzu kenan, abu yasami mutum maimakon kazauna kabincika daya bayan daya zuciyanmu sai tayita ta mana raye raye muje har ga aikata zunubi,anan inna tacigaba “kekam ko ni kin gujewa kinki zama kinsanni, bayan ni ce gambon su mahaifinki su yan biyu ne hassan da hussieni, saini gambonsu, mu uku ne, hussienin mahaifinki yanzu haka yana raye anma baa garinnan ba, yana can senegal yana zaune da matarsa, kuma musabbabin tafiya shine mahaifinki dashi an bukaci abawa dayansu sarauta, sai shi hussien yagwada yanaso kuma mahaifinki bayaso, donhaka saiyake taimakawa don abashi bayan rasuwar galadima na 54 cikin ikon Allah sai mutanen fada sukaki yadda acewarsu hussieni na da aladun bature. Dawasu halaye wanda ni bansaniba anma sunfada anyi rikici sosai a kafin aka yanke bawa mahaifinki, randa akabawa mahaifinki aranan shi hussieni yabar garinnan bayan dogon magaanam dasukayi adaki dagashi sai hassan, haryau bawanda yasan mesuka fada, kuma tunranar hussieni ya tsani hassan dinsa, yakuma tsaneku, donhaka son yusuf shiga gydan sarauta inason gayamiki sai me shiryi, wacce kikeda kyakywan niyya, mace mai ilmi hazaka da karamci, don sarauta dakike gani yana raba uba da da, balle wa da kani Bayan tafiyan hussieni munyi jimami sosai, don mahaifinki har a asibiti ya kwanta don kewar danuwansa, munyi rashi sosai saidai ya gwadamana baya sonmu, yagwada mana abun duniya tafi masa mu, dakyar mahaifinki ya taso daga ciwo, sannan bayan haka yazo yanuna rashim amincewarsa na karban sarautan, nanma anyi daga kafin yakarba don inhar sarautar tabar hannunmu zata koma wani gida ne bazata dawoba, kaka da kakkani sarautar tamu ce, bayan mahaifinki yahau tundaga ranan yafara samun barazana, mafarkai kala kala, gashi ke kanki nasan zaki tuna lokacim da ummanki tayi barim yanbiyu sau uku, sufyan yazo yafara abu kaman tababbe bayason makaranta yafara bin almajirai babban dalilin dayasa hassan yadaukeshi yakai kasan waje kenan donhaka malamai suka bashi shawaram yadagashi a garin yombi, dalilin dayasa kenan kikaga anrabaki da danuwanki, kekuma ba abunda yasameki, wanda hakam yasa mutanen gari suka fara surutun cewa lallai lallai asiri akayi muku wanda bayaso babanki yasami magaji, ummanki tadamu sosai musamman da aka rabata dashi [10/10, 9:06 PM] Adda Bena: Ana haka shikanshi hassan yafara samun matsala da yan fada, kinsan ance baasamun mugun sarki sai mugun bafade, donhaka yalura duk munafukai ne agefen sarkim saiyazama shikadai mutum dayake kin yadda da maganganunsu, donhaka tuni tsana da keta, da hassada yakara shiga tsakani, donhaka rayuwarku gaba daya tadawo abin hatsari, hakam yasa ya kwasheki yakai makarantan kwana don kar wani mummunan abu yasameki, ran mutuwan mahaifinki kuwa ina asibiti mai gidana yana jinya, aka turomin labarin mutuwarsa, nayi jimami sosai nabukaci adauko ki daga makaranta akacemin a a abarki don kuna jarabawa, da sati daya surukata tarasu munje kaue taaziya kafin nadawo kika dawo kika tattara kika tafi abuja koda nadawo nayi bakin ciki anma dana gane gun wa kikaje saina bari kawai nasam zata rikeki amana, mukan yi waya da ita lokaci lokaci Tana gayamim awani hali kike ciki, saidai bantaba yarda tahadamu ba, aganina guduna kike zanbaki wuri, kinji takaiccecen tarihinki nasan bakisan da hakaba, iya abinda zan iya sanar dake ayanzu ne, saikuma ina gargadinki da duk wani magana dakikeyi nacewa zaki dau fansa, kidenashi na gargadeki daki daina, karkije ki janyo abunda zai dameki dakuma tashin hankali agareki, abinda yawuce yawuce, inkuma kinki yadda zaki girbe abunda kika shuka, domin bishiya kikeso ki tumbuke, dafatan kinjini? (Insha Allah daga gobe zaku fara ganin dayawa, nagode da sauraramim dakukayi so[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 20  benaxir  October 11, 2015  Hausa Novels  116 Views [10/11, 7:33 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya ta gyada kai wanda itakanta inna tasan cewa baikai har zuci ba, tana tantama dakyar ta amince anma tana tsoron abunda zaije yadawo idan aliya tayo bincike, bata cika son bincike ba itakam, tadai mike tabarta, tana fita aliya ta watsa ruwa tasako dogon riga tadaura dankwalin sannan tafito, inna ta kalleta “ina zuwa?” “Kasuwa” ta amsa, inna takare mata kallo , saidai batace komi ba saikin dawo, aliya tasan mezatace donhaka ne ma tagodewa Allah datayi shiru, Allah yagani batason takuri rayuwarta ba tsanani, tafice saidai itakanta tasan tafita ne don taji gydan ya isheta batada dalilin fita, ganin me awara tayi tanemi gu tazauna tasiya ta murmuzashi a cikin ledan yadawo kaman kwado sannan ta tusa a jakarta, gydanta nada taje haryanzu baa shiga gydan ba, tashiga tazauna taci awararta ta koshi dama tana yawo da coke dinta, takora da coke sannan tafito da zummar takara gaba, hanyan fada tanufa kai tsaye batareda wani tunani ba, harta yanki kwana taga sufyan agabanta bai saurari mezatace ba ya damko hannunta ya wuce da ita basu tsaya ba sai awani lungu, “Meye kuma yaya?” “Bakida hankali ko? Ina zakije?” “Fada zanje” “Kimusu meye” “Na ga yusuf” “Mahaukaciya,wuce mutafi” Fizgan hannunta yayi suka isa bakim titi ya tsari keke napep suka hau sannan yayi kwatancem gun, “Da kafana nazo, dakayi hakuri zankoma da kafana!” Bai amsata ba har suka isa yamikawa mai keken kudinsa sannan suka shige inna tana tsakar gyda taga yazo yawuce da aliya donhaka ta dauraye hannunta dama tana wanke kayan miya ne, tabisu don ganin meke faruwa, “Bakida hankali ne? Sau nawa zangayamiki aliya sau nawa zangayamiki ki fita hidimar fada!, kifita rayuwarsu, mutanennen baruwanki dasu, yusuf dinnan nagayamiki mahaukaci ne ki hakura dashi kinki yadda wato ga karamin dan iska” Inna tashiga dakin ganin yana matsifa yaki shiru tace “meyene yake faruwa? “Inna kiga shigan jikinta, yarinya gaba daya tadawo inyamura, aladan yarbawa, kinmanta akasan hausa kike? Kinje kin dauko dabian wasu kina mana anan!” “Yau nashiga uku zaku kasheni, meye zaka wani ce yarbawa, agarin yarbawa nazauna? Kaidai inzakayi matsifanka kayi ai gwara ni kai fa? Wayasan mekake aikawata, dogon riga ne ajikina meye aibunsa, ?” “Dakikasa dogon rigan shine zaki cire dankwalin?kin yafashi a gefe ,kokuma kisaka gajeren wando kina yawo a kasuwa, zanga ta inda zaki auru a garinnan, dawannan halin tashan kikeson auren dan sarki? Wazai baki? ” Haushi suka bata itadai tasan ba laifi tayiba sunbi sunsa mata ido, wacce tasa atamfa ta rataye gyale awuyanta tarufo

Chapter 4 of 7