Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
akam gado yana juyi babu irin tunanin dabaiyiba aransa, yagagara bacci yakuma gagara tashi yagagara motsi duk tashin hankali na bidansa, sallarhn magrib ce tasashi tashi ko dayaje masallacinma a gefe ya kudundunu, for the first time tunda mahaifiyarsa ta auresa daya mike yayi nafila rakaa biyu yana rokon Allah yabude masa haske a lamarin daya danno masa, Allah yasa abunda yake zargi bahakaba, yayi kuka sosai wanda kowa a masallacin yaji mamaki, abdullahi ne yadafa kafadarsa tareda cewa “zanyi mamakin abunda zai kawoka masallaci harkayi nafila, nasan bakaramin abune, Allah yashige mana gaba, sannan wannan yarinyar aliya!,” dasauri yusuf yakalleshi jin ya ambaci aliya , yace ” bata taba maka kama ba? Kaman kasanta abaya?, tanamin kama da nasanta anma na manta,” dasauri yusuf yace ba itabace wannan daga wata duniya tazo” abdullahi ganin yusuf ya amsa da zafin nama yatabbatar da maganansa don tuni yana zargin yayan nasa da son aliya, shidai babu keta balle hassada adduanshi tazama sanadin shiryuwan yusuf, Yusuf nakomawa fada yashiga daki baifi minti goma ba saiga bilki da aliya sunshigo rike da tire dinsu suka ajiye akan dinning sannan suka koma gefe, yatashi yazo yazauna abincin yake kalla anma baya shaawan ci, asalima baiyi niyyan saukowa daga kan gadonba saidon yakalli aliya dakyau hakan yasa yazo yazauna, kare mata kallo yayi wacce itakuma kanta a sunkuye ne batasan yanayiba, tabbas duk wanda ya tsura mata ido yasan batayi kama da baiwa ba, kuma duk mai ilmi da wayewa yasan cewa aliya wayayyiyar macece, ba daga kayaba kome tasaka wayayyen mutum baya buya , zuciyarsa tayi nauyi jiyake kaman yayi hauka, zaitona mata asirine don yaceci mahafinsa? Kokuma zai rufa mata asiri don yana sonta,duniya tamasa zafi, kansa ya sunkuyar akan table din tareda cewa “kufita” sunfice saidai aliya jikinta yabata ba lfy ba, tadai share suka dawo daki, * bilki tana jaje tareda cewa shekarana goma agydannan bantaba ganinshi haka ba, toh ko kinmasa wani abune?? Aliya bata kulataba alokacin shikuwa yarike kansa wacce take matsanancin ciwo, tunaninsa yarude, bude fridge yayi sannan yaciro giyansa kwalba guda saidaya shanye a lokaci guda, yakara ciro wani yakafa kai saidaya shanye, fadi yayi agun sai bacci, can karfe takwas bayan aliya tagama sallolinta tafito tayi magana shiru jin baimata isoba tasan meyake ayyanawa, donhaka tashiga tareda dubawa ga mamakinta taganshi a kasa kaman matacce, kanshi tanufa tana girgizashi sai dai yana numfashi hakan yasa ta tabbatar bacci yake, pillow tadauko masa sannan tasaka masa, tarufa masa bargon domin a.c na dakin akunnene, tana zaune ta zura masa ido tana tunani “yarima! Meyake damunka? Meya sameka kashiga damuwa? Bantaba ganinka hakaba!” Fuskarshi ta dishe ,zuciyanta na mata radadi jitayi kaman andaura mata dutse akirji, batasan hawaye nazuba a idontaba, dawuri tasa hannu tana gogewa, abun yabata mamaki daga ganinshi haka shine tafara kuka? “Yooo ni aliya wani irin so nake maka? Innalilahi, karnazo nagagara cimma burina, zuciya batada kashi” wasa wasa hawaye nazuba saigashi tanata kuka, oh ni benaxir abun mamaki dama haka first love din take?, Tun karfe takwas aliya take zaune akan yusuf bata runtsaba har karfe uku nadare tana gadinsa, lokaci lokaci dogaran suna lekowa don tabbatar da babu abinda yasami yariman, karfe uku tamike tayo alwala tahau sallah, a sujjadda ta tsinci kanta da rokon Allah ya shiryi yusuf, Allah yabashi lafiya ya yaye masa damuwansa sannan yanema masa mafita, sai asuba tahakura bayan sallahn asuba tacigaba da gadinsa, yusuf bai farkaba sai karfe goma nasafe tana ganin yabude ido tafara tambayanshi ko lafiyansa lao, yayi matukar jin kunya bayajin kunyan [9/28, 8:25 PM] Adda Bena: Mahaifiyarsa bayajin kunyan mahaifinsa anma ya tsinci kansa da jin kunyan aliya, ta taimaka mishi yaje bandaki sannan tafito. Wanka taje tayi sannan tacanja uniform dinta tamike kan gado, bacci mai nauyine ya kwasheta, Yusuf kuwa fitowarsa yaga babu ita dasauri yakira dogarinsa daya tareda cewa “ina aliya? Kiramun ita ai batagama aikin ba” ya amsa da toh, bilkisu ce ta tasheta anma haka tamike sukaje fannin, tea yasa tahada mishi yana kare mata kallo, tayi iya kokarints ganin ta danne baccin datakeji, tahadamai yaci da cake sannan yakoma kan gado, zata dita yace “dawo ki tsaya harsainayi bacci” tana tsaye haryafara bacci sannan tafito bacci takomayi, har azahar alokacin yatashi yaga bilki ransa ba karamin baci yayiba tareda cewa ina aliya? Kikiramin ita, ta sunkuyar dakai gami dacewa “bataji dadibane yarima tana bacci yanzu haka” yazaro ido mai yasameta?” “Babu baccin dabatayibane yajawo mata, tun shekaranjiya rabonta da bacci, ” shiru yayi yana tunawa tabbass yatashi yaganta kenan azaune ta kwana, tsanar kansa yayi yanajin haushin kansa oh aliya, kiyimini hakuri, shikadanshi kaman yakashe kanshi, mikewa [truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 9  benaxir  September 30, 2015  Hausa Novels  115 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Budewa yayi yashiga wanda yabawa bayin mamaki domin yaran sarakunan har matan basu zuwa gun, umma uwar soro ce kadai me shiga da fice agun, gaba dayansu kowa ya sunkuyar dakai domin sun gama tsorata, ayadda suka sanshi sunsan sarai cewa ba lafiya ba, bayada mutunci ko kadan , yakare musu kallo yaga wani gado ne akwai mutum kan gadon yanufa, aliya ce tana bacci , yazura mata ido sosai. Yasa hannu yasa ajikinta yaji yayi zafi sosai, bayin sunyi mamaki nan da nan kowacce tafara tsegumi, yafice fanninsa yanufa yadau wayarsa yakira likitan gydan, bashiri yazo anan yasa bilkisu suka kamo aliya suka kawota fanninsa aka dubata, likitan yace rashin hutu ne da wahala, da rashin sabo da wahalan, yabata pain reliever, da maganin bacci, haka dai yatafi hankakin yusuf atashe baiyi motsi agefenta ba, yanata kallonta yarasa wani yanayi zai fassara kansa, Maganan yusuf yashiga fannin bayi tuni tabaza cikin fada, falmata ranta yabaci sosai, data bukaci bayani agun jakadiya nan jakadiya ta ce mata “bayin sunce kwana biyu yana nuna alamun damuwa wa aliya” falmata tazaro idanu domin ta mugun tsorata, yanzu yarasa wacce zaice zai kula sai baiwa? Duk neman matanshi bai kare awaje ba harsai yazo gun bayi?” Jakadiya tadanyi gyran murya sannan tace ” gimbiya wannan fa inaga nufinsa daban, don sundade tare, inhar biyan bukata ne kinsan yarima yanayi sau daya zai shareta” falmata takara tsumuwa, batasan lokacin data mike tanufi fanninsa ba, dogarai suna kokarin yimata iso anma ko jiransu batayiba tafice tashigo, gabanta ne yayi mummunan fadi ganin yusuf yana zaune agefen aliya, da alamu yayi nisan tunani tunda baisan tashigo dakin ba, wani tsawa ta daka masa wanda saidaya firgita ganinta yasa yadan rusuna, bai idda ba tace “wani rashin hankali ne wannan? Jakadiya fita da ita!” Jakadiya taje ta tashi aliya wacce jikinta yayi zafi sosai tarasa yadda zatayi, donhaka taruketa zasu fice falmata tace “saketa!” Aikuwa aliya tajita akasa dasauri yusuf yanufeta yadagota zaifice da ita budan bakin falmata tace “zandaga maka nono yusuf, wlh inka kuskura kabita zandaga maka nono” cak ya tsaya ji yake kaman yayi hauka. Alokacin aliya tajanye jikinta tareda cewa “zan iya tafiya badamuwa karka damu” fitanta sashimsu tanufa inda kowa kallonta yake alamun tausayi bata kulasu ba takwanta, alokacin jakadiyar yakolo tazo ta dubata, acewarta yakolo na gaysheta da jiki, fitanta kenan alokacin yusuf yabar gydan don baiga amfanin zamansa ba, gydan aliya yanufa anan yakwanta yasha giyansa, barci ta kwasheshi, falmata kuwa tarasa yazatayi gwara tun wuri takauda aliya donhaka ta umurci azo da aliya, dakarfi aka kamo aliya tana kallonta aliya duk tacanja kamanni, falmata ta umurci da adauko bulali nan aka baza aliya ta kwashi dari masu karfi da zafi, tunda mahaifiyarta tahaifeta bata taba shan wannan azaban ba, aka kwara mata ruwan sanyi, falmata tace “sakamakon da ake samu kenan idan mutum yashiga hurumina,” suma aliya tayi anma haka falmata ta umurci a watsa mata ruwan sanyi tana farkawa aka daure hannayenta tabaya da kafafunta aka kwantar da ita akasa,tasa aka dauko kankara aka jera mata a cinyoyinta,kakkarwa take, duk tafita hayyacinta burinta baisamu yacika ba zata mutu, dukka wanda yakegun dole yatausaya mata. Bilki ce taruga da gudu fannin yakolo tasanar da ita abunda ke faruwa, bashiri yakolo tafito isowanta gun tace akunceta falmata takalleta sama da kasa tareda cewa “a matsayinki na wacece?” Yakolo tace “a matsayinta na baiwa ta!, inbaki manta ba ai kinkoreta nadauketa!” Faalmata taji kaman ta makuro wuyan yakolo tsaki taja tare dacewa “zanga wanda zai daina abunda nasashi,inku jahilai ne takoma tazauna a kujera; yakolo tayi murmushi dakanta tanufi kan aliya ta kunceta. Tarungumota sannan tanufi fanninta da ita, falmata tsaki taja tabar gun tareda zagin bayin, A fannin yakolo ta aika aka kira likita yaxo yamata dressing jikin yabata magunguna, abdullahi ne yashigo ya tsorata ganin yanayin datake ciki, tana bacci anan sukayi shawara da mahaifiyarsa a[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 10  benaxir  September 30, 2015  Hausa Novels  122 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Tana farkawa tayi mamakin ganinta afannin yakolo anma yakolo ta gwada mata bakomi, sallolinta tayi a zaune don bata iya tashiba, abdullahi duk tausayinta yacika sa gashi haryafara tsanar kansa yasan tabbas yasan aliya anma yamanta aina ne? Wannan wacce irin mantuwa ne, Yusuf bayan farkawanshi wanka yayi yacanja kaya sannan yarufo gydan yadawo fada, atake yafara neman bilki cikin kuka tasanar mishi da abunda yafaru, ranshi abace yanufi fannin mahaifiyarsa donjin baasi kamar kullum cemasa tayi “inzaka shekarana kana neman yanmatan da basu daceba baxan gaji da koransu ba, kanemo mai tushe mai asali, ” baice komi ba yafice , fannin yakolo yanufa wanda kowa saidayayi mamaki yagaysheta sannan yace “nazo daukan baiwa tace ” tagane meyake nufi anma tace “wacce baiwar fa?, ” yayi shiru sannan yace “marar lafiyannan aliya” tace “au! Aibansaniba kamanta mahaifiyarka ta koreta ne? Ni na karbeta, kuma daga yau na yantata donhaka daga kai har mahaifiyarka bakuda dama akanta!”. Zaro ido yayi yayin daya tuna kalmomin aliya na “karka yantani, karabu dani kuma ka manta dani” subhannalahi ai ta tona mishi asiri aliya batason a yantata, anma shiyasan yantata shine kadai hanyan dazai iya soyayya da ita, baice komi ba yabar gun A haka aliya taringa jinya kullum yusuf na hanyan gaysheta wani lokacin suhadu da abdullahi wani lokacin kuma da shehu, wanda baya zama agydan saboda makaranta wasa wasa saida aliya tayi sati sannan tawarke, aranan yakolo tabukaci tagayamata gaskiya, Tagayamata cewa ta yantata , aliya batasoba anma yanzu kam shine kadai hanyan dazatabi donta rama abunda falmata tamata, dole tarama saitaji zafi ninkin abunda taji, zataga itako falmatan wazai juya yusuf, uwace ita tafita daraja anma namiji kam inkika tsuguna kika haifeshi aikinsan wa ya mace kika haifawa, domin kuwa komi mace zaifara yiwa, dadday ne masu fara tuna uwayensu. Shiyasa bahaushe yace da ki haifi gwamna gwara kinhaifi matar gwamna domin gwamna matansa zaituna kafin ke, itakuwa komi uwarta da danginta, sungama magana da yakolo inda yakolo tabata kayyaki da kudade tace tatafi garinsu don hakan kadai ne zai tsirar da ita daga gun falmata, abdullahi ne yazo alokacin yazaunar da ita yace “dani da mahaifiyata muna tunanin akwai wani igiyan dangantaka a tsakaninmu dake inbahaka ba kuwa babu yadda zaayi ni kullum ina tunanin nasanki awani guri yayin da itakuma take tunanin cewa tana kaunarki haka kawai, toh ko dai babu mudai iyakacin gatan dazamu iyamiki kenan!” Aliya tayi godiya sosai tabbas baxata manta da hallacinsu ba, ko agun bayin kuwa su bilki nata kuka kowa yasaba musamman bilki tafijin jiki, da kuka suka rabu tafice tanufi gydanta ga mamakinta taga makullimta baya shiga kuma ba kofanta bane, tuni tasan aikin yusuf ne don if barawone bazai gyra kofan ba, tazauna agefen kofan tana tunanin yadda zatayi saitaji alamun key a gefenta tuni tadauka tabude taga yabude, dakin warin giya da kwalaben giya hakan yatabbar mata da cewa yusuf ne yake zuwa dakin, abubuwanta ta tattars sannan tarufo kofan, tarar machine tayi taje takama hotel kafin tasamu gida dondai tasan batagama aikintaba babu abinda zaisa tabar garin, wanka taje tayi tanayi tana kallon tabon cinyoyinta na dukan da falmata tayi tasake shower yana zubo mata, tuni tafara tunanin iyayenta kuka tayu sosai wanda saida yasamata ciwon kai tafito tayi sallah sannan takwanta wayanta takunna, msgs tagani dayawa na auntynta kusan kullum saita kirata taji yatake, tajero mata txt tareda mata adduan samun nasara, saikuma malaminta yana tambayanta yaya aikin datasa agaba? Sai daidaikum yan makarantansu dakuma invitation na bikukunan frnds dinta, bacci ne yakwasheta, bata tashiba sai bayan magrib donhaka tayi magrib tasanyo dogon abayanta tafita reception don cin abinci, tayi ordern fried rice da grilled fish, game take awayanta saikawai taga mutum yazo yazauna, bata kulashi ba shikuwa sai kallonta can data gaji da kallon tadauki wayanta tacanja sit yakara binta tuni taji abincin yafita mata akai hanyar dakinta tanufa yakuwa bita saidata fakaici mutane tarikoshi dakarfi hannayensa tawullosu tabaya tarike kara yasaka. Cikin zafin nama tace “meye kake bina?” Karan yakeyi babu daman magana anma yadaure tareda cewa “inason zama abokinki” danna hannun tayi dakarfi tare dacewa “ni ba saarka bace! Not interested!” Sakeshi tayi tareda nufa dakinta nan yafara tunani oh mace dakarfi kaman doki,dahaka yakoma shima Yusuf kuwa shigowanshi gyda yadan siyo kayan kwalamansa yashigo fannin yakolo don gayda aliya, ga mamakinsa tace ” na yantata tunda kasan hakan aikasan cewa zata tafi duk lokacin dataga dama, toh itama tatafi,” zaro ido yayi yasake kayan dagudu yafice mukullin mota yadauko yatuka wani wawan tuki dayakeyi saida ya tsorata mutane gydan aliya yanufa ya bude yaga bata ciki, yaleka kasan gado yaga ta tattare kayanta, wani tsaki yaja bakin ciki nacinsa hannunsa yabude da bango yana magana shikadai “aliya wlh inasonki, meyasa kikatafi? I[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 11  benaxir  October 1, 2015  Hausa Novels  144 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR zama yayi dirsham babu irin tunanin dabaiyiba aransa, yasan dai kome yasameta. Bazata taba barin garin batare data cimma burinta ba a dan sanin daya mata, macece mai tsayuwa akan raayinta, nan kuma takara bashi tsoro domin kuwa yasan tabbas bazata bar mahaifiyarsa ba, gida yakoma yatara dogarai yabasu cikiyanta, har cikiya da hotonta idan amsamu wanda yaganta zai samu kaso na dukiya mai soka Aliya kuwa tuni tasamu tanemi hayan gida ciki da falo, taje tasiya sabbin furnitures, da kayan kallo da duk wani abu datasan yana wancan gydan tabari, saidata koma gaba daya sannan hankalinta yakoma kan yadda zatasamu daman juya fada batareda sungantaba, tayi iya tunaninta anan ta tuna da bilki, toh tayaya zatayi magana da bilki babu yusuf? Dole shikadai zai iya dauko mata ita, inbahaka bilki bazatabar fada ba, ko acikin matan sarkin bawacce tafi kusanta balle tanemi alfarma, tsaki taja tasako dan riganta iya gwiwa da jeans, tadaura dankwalin akanta batayi kama da yaran hausawa ba ko kadan wanda tayi hakanne donta batar da kammani, yanayin garin yamata dadi sosai yadda take tafiya duk wanda zai ganta zai tabbatar da macece marar son damuwa da tashin hankali, masara tagani ta ciro gudan dubu daya a aljihunta tamikawa matan, matan tamika mata guda daya da canji aliya taki karba haka tabar mata canjin, matan tabita da godiya, hankalinta a kwance tanaci tana tafiya can taga taro andan cika dasauri tanufi gun, wasu ne suke fada ana kokarin rabasu ganin mazane ba yadda ta iya tajuya tatafi, har gyda taje sannan ta kwanta akan kujera taji dadin dan zaga garin datayi koba komi tayi exercise din kafa, buga kofa taji anyi batareda tunanin komi ba tamike tabude ga mamakinta saitaga ysuf, mayar da kofan tayi zata rufe atake yasako hannunsa bahali dole tabari, tana juyawa takama kanta tareda cewa “mekazoyi?” Cikin murna da farinciki ji yakeyi kaman ya rungumota yace “yazaayi bazanzo ba. Naxo gaysheki ne” tana zama tadauko wani takarda tana dubawa tareda cewa “mutanen garinnan munafukai ne, har anje anfadamaka inda nake, fitan danayi ko awa biyar banyiba” bai amsa ta ba illa zama dayayi yana kallonta, ta ajiye littafin tareda cewa “taimakona zakayi, inaso kadaukomin bilkisu akwai maganan dazamuyi” ganin tadage yace “maganan yadda zaki kashe babana da mamana?” Ta mugun tsorata anma tadanne tareda yin murmushi tanacewa “mesukamin? Babu , donhaka ni tambayan bilki kawai zanyi!” Yamike tareda cewa bazaki ganta ba nasan menakeyi, so kike kiyi amfani dani wurin ramakon ki ko?” Ganin datayi tamkar yasan komi ta tabbatar dacewa lallai yakaranta littafinnan donhaka tabata rai tareda cewa “ae!” Baiyi mamaki ba, dama yasan dole zaa rina, abunda zatace kenan, yamike tareda cewa “kinemi wani hanyan ramakonki badaniba, sannan kiyi adduan Allah yarufe bakina akanki” yana fada yabar gydan, ko ajikinta don tasan bazai fadaba, dazai fada tun tana baiwarta zaifada, tayi zama tana tunanin hanyan dazatabi duk iya tunaninta dole yusuf ne hanyan, inbai taimaka mataba babu yadda zatayi, gashi yariga dayasani tasan zaibi duk wani hanya domin yaga ya tsayar da ita, wanda aganinta bazai taba faruwa ba, donhaka dole tabi hanya daya, wato ta ajiye komi tajanyo yusuf ajikinta har yasota wanda bazai iya mata musu ba, wani zuciyan tace toh yanzumman ya aka kare? Donhaka bari tagwada tagani Kwanansa uku bai lekota ba, tana hankalce anma tana adduan Allah yasa yazo din, domin zuwanshi ne kadai mafita agareta, cikin ikon Allah dayamma kamar yadda takeyi, yau kuma dogon rigane ajikinta tadaura dankwalin taje cin masara, harta karbi masaran taji murya abayanta yanacewa shima abashi, juyawan dazayi taganshi, bata kulashi ba takarba tafara tafiya wanda yana binta abaya sanye yake da kannanun kaya sunyi asalim yimasa kyau, kowa kallonsu yake domin ba karamin kyau sukayiba, tayi kaman batasan akwai mutum agunba har sukaje kofan gydan tabude tashiga yabiyota, bata kulashiba tacire dankwalin gashin yazubo tazauna tamike kafafunta alamun tagaji, tanaji yana kiran sunanta tashareshi tamkar bada ita yake ba, ganin ta mayar dashi mahaukaci yanufi kanta kwalban coke dake hannta yakarba yawurga akasa tas tafashe, aliya bata dago ta kalleshiba balle ta tambayeshi, ganin zata haukatar dashi yasa yanufi kanta ganin zai mata hauka tasa kafa ta tokareshi hawaye ne a idonsa ” don Allah kiyi hakuri duk zuciyan dakikayi dani kiyi hkr, baxan iya rayuwa ba keba, wlh inasonki aliya kefe madafar zuciyata, na yadda ko meye zakiyi dani kiyi, kiyi amfani dani zanyi biyayya inhar zaki gwadamin so, komi kikeso zanmiki in bilkisu ce barin aika akirata” yamike zai fita tace “yarima!” Yajuyo yakaleta sannan tace ” kainake son kaje kadaukota dakanka” ba musu yace “toh (Kuyi hkr nayau bayawa, nayu latti ne,[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 12  benaxir  October 2, 2015  Hausa Novels  122 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Fitanshi baikai awa daya ba saigashi da bilkisu, tana shigowa aliya tajata suka shiga daki tabarshi a falo, shigansu bilkisu tayi mamaki kwarai, kallon gidan takeyi dakuma aliya wacce taga wautanta na rashin gane aliya tunfarko, tabbas aliya batayu kama da baiwa ba idan tayi laakari da yanayinta, aliya ta numfasa sannan tace ” kiyi hakuri bilkisu ke kadai na yarda inaso kitaimakeni, anma saikinmin alkwari cewa har mutuwarki babu wanda zaki fadawa” bilki tayi shiru,azaman duniya idan ana kirga masu sonta tasan dole aliya tazo aciki, domin ta taimaketa sosai donhaka batareda wani tunani ba tanuna amincewarta anan aliya ta fara kissa mata labarinta daga farko har karshe akan waccece ita, dakuma dalilinta nazuwa fada!, bilkisu ta tsorata sosai don bata taba kawo haka arantaba, anan taroki bilki datazama idonta acikin fada, bilki babu gardama ta amince aikuwa aliya ta mata alfarman komeye takeso zata mata, dawannan suka fito yusuf na falo har bacci yafara kwasansa domin sun dade adakin, bilki tafito haka yamayar da ita kamar yadda ya fito da ita, dawowansa yasami aliya na kallo shi abun na damunsa toh batada yanuwane suka barta take wannan garajen? Kayan kasada? Hakadai yazauna akujera yadurkusa dakanshi takaleshi ganin yadda yayi tace “meye ka sunkuyar dakanka kaman shege a rabon gado” abun yabashi dariya anma yadaure fuska bai tanka ba, ganin haka yasa itama ta tsuke tareda cewa “alakarmu bazata yiwuba inhar bakadena shaye shaye ba, daga yau kadena!” Yayi shiru yana kallonta ko falmata datace yabar shaye shaye tana masa fada baitabajin yadena ba sai ranan, yasa aranshi bazaikara shan wani abuba, “insha Allah nadena” jinhaka yasa tasake masa sukadanyi tadi duk maitarsa nason sanin meye plans dinta taki fadamishi, anan yake cemata auren abdullahi bayan sallah, ta ce “ni yakamata nashiga kasuwa ma saboda banda kayan azumi ko kadan, muje karakani” aikuwa suka fice tsum dogon riga iya gwiwa dakuma wando takara sawa sannan sukafito yakalleta dakyau azucinyanshi yace “wannan yarinyar yar bariki ne wlh” kaman tashiga zuciyansa tace “karkayi tunanin ni yar bariki ce, nayi rayuwar kudu” yayi murmushi tareda cewa “kinyi kyau” dakafa suka taka har kasuwa shikam har kafofinsa sunfara ciwo yasan yau sai yayi jinyansu amma itakuwa ko ajikinta tasaba , suka siya komi don inhar zata mika kudi shiyake mikawa, ganin zai rainata tace “nifa ba irin yanmatanku bane na zamani dazakuna kashewa kudi donku siya zuciyarsu” yayi murmushi sannan yace “oh mata dai, yanzu da bansayaba zakije kice yarima guda dan sarki anma haka yabarni nasa kudi nasiya tsabar rowa” abun yabata dariya tace ” toh aiku mazanne hannunku kaman kuna ajiyeshi agyda kafin inbanda haka ai kasan shi kyauta yana kara dankon zumunci, zuciya tanason mai taimaka mata, ko mata da mijine wlh inkana kyautata mata darajanka dabanne, aanma wasunku sai balain rowan tsiya, wani lokacin kunsan mace tafi karfin abu duk dahaka kumata mana, ko bazata karba ba. Anma wai saikuce kuna gwadata ne, waxaku rainawa hankali, gwara kanayi kana ihsani,” tabashi dariya nan yakara tabbatarwa macece mai experience na rayuwa, anma yadanne ransa yace ” samarin g.s.u marowata ne kenan?” Kut wlh a a, mukam yan gombe akwai kyauta” “Ta ina kika zama yar gombe????” “Oho dai gwaramu kaida kagama a.t.b.u samarin atbu ne da rowa” “Allah kije kiga mu har mota muna saya” “Ae naji wannan zubairun” Ganin me masara sukayi ta tsaya tana dubawa tadauko daya tabashi tareda cewa “Ci” yakarba ya gutsura ” hmmm dadi” Suna tafiya sunaci baisaba ba duk saiyajishi a tsarge anma yahadu da yar tasha yazaiyi da rayuwansa?” Gyda suka nufa kicin suka ajiye na ajiyewa sannan suka fito, yamata sallama yanufi gyda Tun ranan suka soma shakuwarsu har azumi ta shigo shine yarage zuwa don yana wuni bacci ne, aliya kuwa alokacin takafa ibadunta, tanajin labari lokaci lokaci agun bilki idan tasa yusuf yadaukota, falmata bata canjaba, donhaka aliya ma bata ajiye kudirinta ba, aliya tayiwa bilki kayan sallah, yayinda shima yusuf haka yasiyo akwati guda yaciko da kaya yakawo mata, taki karba anma ya ajiye yafice yabarta, taji dadi koba komi her first love worth it, ayanzu son datakewa yusuf yawuce duk wani tunaninta, akullum addua take Allah yabarsu tare, Yusuf kuwa satin farko shiru baisha giyaba , ana shiga nabiyu yafara canjawa, kana ganinsa kaga marar lafiya watarana ansha ruwa yashigo gun aliya anan yazauna kaman zaimutu tayi tambayan duniya anma yace mata bakomi, bata rabu dashiba harsai da ya rike cikinsa yana cewa “aliya ki gafarceni, kishi nakeji ” dasauri tadauko masa ruwa yasha anma ya girgiza kai alamun bashibane alokacin tagane meyake nufi, babu giya agidan duk tarude “karka mutu bazaka mutuba, Allah yaga zuciyarka kaci gaba da danneea” idonsa yayi jajur, duk yafita hayyacinsa batasan lokacin data fitaba, giyan taje tasiyo takawo mai tareda cewa gashi kasha kadan, ahaka harka bari” yakalleta idon jajur yace “nariga nayi alkawari bazan kara shaba, kibari kawai” hakan yasa ta je toilet tajuye gaba daya tafito sai karfe goman dare sannan yasamu kanshi yakoma gyda nanma yaje yakara tarar dawani tashin hankalin don falmata cewa tayi yaje shan giya baikulata ba hartagama hargowanta tafice anan kuma labari ya iso mata cewa kullum ana ganinsa tareda wata, nan ta bukaci a dubo mata wayene! Dukkan sarakunan gari ancika makil a fada, donyin council meeting wanda akeyi kowani laraba, masu sarautan duk kowa yazauna don a tattauna matsalolin al umma dake faruwa, inda anan aka shigo musu da kayan sha da ciye ciye, sungama lafiya inda waziri yasanar da auren abdullahi dazaayi a sati mai xuw, sannan yamusu barka da sallah, zaikoma yazauna sai yafara rike wuya yana muzurai, duk hankalin kowa yayi kanshi anan yakwanta yana muzurai, farin yawu yafara fitarwa, tuni aka nemo likita anma kafin ya iso, waziri yace ga garinku Labari tuni yazaga gari aliya wacce ta idar da karatun quraninta taga yusuf yashigo a birkice idonss jajur yana cewa “aliya nasan kinzo daukan fansa ne anma kina mace meya hadaki da kisa?” Takalleshi tareda cewa “wana kashe? Sannan meyasa zanyi kisan?” “Karki rainamin hankali waya kashe waziri?” Mikewa tayi zummur tareda dafa kirji “yarasu? Alhndlh? Amma waye haka yataimaken? Kenan bani kadai bace me harinsa” “Abunda zakice kenan? Ke wato kin kwashe kayanki agaban manzo” “Bawani kwashe kaya. Wlh bani bane, anma inaso nasan waye, burinmu daya, ni nayi niyan kashe waziri anma bada hannuna ba, naso nabi hanyar da hukuma zata hukuntashi, nawa tona masa asiri ne kawai” Ficewa yayi yabarta “Aliya tuni tafara tunani, azumi na garata anma haka tamike taji wayam batajin yunwa, duk ta kagu tasan waye mai tayata aikinnan, Wayarta ce tayi kara daukan dazatayi taga antynta ne “Aliya ki saurareni kiji yayanki yazo yadamu ingayamasa inda kike naki fada jin kince kar infada kowa, anma kuma yanemoki donhaka kizama ashiri zai iya samunki kibi ahankali don yadau alwashin kashe su ne acewarsa kina bata lokaci” Aliya tayi kufum kafin tace “wani yaya? Dama imada yayane? Yaushe aka haifes[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 13 & 14  benaxir  October 4, 2015  Hausa Novels  119 Views [10/4, 5:37 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Bata amsa ta ba saidai cewa datayi “ina kasuwa zankiraki idan nakoma gida saimuyi magana kedai kiduba dakyau zai iyayin wani abu daban, nibansan gurinki yazo ba sai yanzu dayake kirana” kashe wayan tayi aliya ta tsaya kallon wayan, bataci ta zamaba gwara tamike dakyau tanemi mafita duk da tasan cewa yusuf baxai taba fadawa kowaba, dole tafita neman danuwanta!, dole tabi diddigin kisan kafin sarki yarigata yasa akamoshi. Murna zatayu ko bakin ciki? Anma dai koba komi its a relief tanada danuwa ba ita kadai aka bari ba, tuni tafara tunanun yadda zataga bilkisu din abakin bilki ne kadai zata sami lbr, kayanta tacanja tadauko wani katon roba tafita shago takarbi pure water tajuye aciki ta tusa wayanta acikin zanin sannan tanufi hanyar fada, ahanya mutane su tsareta don siyan pure water abun yafara batamata rai ita tasaka ne don bukatunta daban akan meyasa zaana tareta don asiya? Dahaka dai tanufi fadan inda ta fara survey din gurin duk rashin hankalinta da kuma basiranta babu hanyan bi, katangan ma dogo ne irin dogon da babu dan adam dazai gwada shiga haka, agun aka siya pure watern dukka don yanada sanyi sosai roban da kudin tamikawa wani almajiri tadawo gyda, kwanciya tayi akan gado itakam zatayi hauka gashi ankusan shan ruwa haryanzu batasami hanyan shiga fadaba. Tasan dole tabi hanyan daya kamata tabi wato yusuf,bayan asha ruwa saigashi yazo ganinta yayi akan sallaya yaga batamasan yazoba hakan yatabbatar masa dacewa tunani take, shi gani yake kaman ita takashe waxiri anma yadda tayi dazu tasashi kokonto, kuma dayaje fada yasami lbrn duk abunda aka kawo aci daga kicin bilki tana fanninsa a lokacin toh kodai aliya tanada wani

Chapter 3 of 7