Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Jummai tace "Malam ai se a saka Dije ma tunda kaga tayi Girma". Malam yace "anya ba'a bari ta kai goma ba ,ko bakwai." Da gudu Gwamma ta fito "wallahi kar wanda yakaimun yarinya makaranta".Malam ya d'aga Mata hannu "waya saka dake ehe?,meye naki aciki? nayi maki tsakani damu don haka Ke 'yar kallo ce, idan kinga bazaki iya ba,ga k'ofa nan abud'e take". Jiki a sanyaye ta Koma.Haka dai rayuwar ta kasance a yanzu hankalin Jummai da Hansai ya kwanta, har k'iba sukayi.

Chapter 10 of 40