Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
alokacin karfe goma da rabi na dare domin shafiu na barin otal din gidansu Aisha ya wuce kai tsaye da yake uwar rikonta kande ta dauke daya daga cikin atamfofin da shafiu yabata ba'a sami wata matsala ba wajen fitowar aisha. Abin mamaki kande ce ma turo ta da kanta. Yi sauri ki fita mana sai wani nuku nuku kikeyi wannan yaro ai ya isa dan arziki wallahi ga shi daga zuwansa har ya fitar damu daga cikin tsummokara. To aisha kefa nake jira kinyi shiru. Aisha ta dubeshi a tsorace tace wallahi shafiu tsoron kiran Aljanar nan nakeyi kaga.... Shafiu ya ya daga mata hannu menene abin tsoron bayan tace bazata cutar da ke ba? Aisha tayi batace komai ba. In kuma kina ganin dai tsoron bazai barki kiyi kiranta ba to kirawo ta mana yanzu tunda ina tare dake. . Aisha tayi ajiyar zuciya in dai kana tare dani bana tsoron komai shafiu bari na kirawota ta bude jakarta ta fara laluben farin dutsen abinda bata sani ba shine tuni cikin shafiu ya fara kugi domin shima a bala'in tsorace yake to amma da yake ransa yana kan dukiyar dake binne saiya dake zuciyarsa amma gumi tun daga goshinsa har zuwa kan babban dan yatsan kafarsa zuba yake. Aisha ta dauko dutsen daga cikin jakar ta dorashi akan tafin hannunta ta lumshe idanu sannan ahankali saita fara murza dutsen a tafin hannunta. Shafiu yayi mutuwar tsohuwa ko kwakkwaran numfashi bayayiShafiu yayi mutuwar tsohuwa ko kwakkwaran numfashi bayayi. . Wata guguwa mai karfin gaske ta turnuke zagayen motar sannan sai sukaji motar ta fara girgiza kamar za'a dauke su sama tsawon lokaci ana girgiza motar sannan kwatsam sai balbelar ta bayyana a gaban motar. Matasan biyu suka zura mata idanu cikin kaduwa Kada kuji tsorona ku tambayi duk abinda kuke so daman nasan zaki neme ni ta dubi Aisha. San..nu da...zuwa aisha tace bakinta na rawa Yawwa aisha yi sauri ki fadi abinda kike son fada ina BIRNIN SIN fa kuka kirawoni sauri nakeyi zan koma na baro yarana acan. Aisha ta dubi shaiu sannan ta dubi balbelar cikin hali So...muke mu san inda aka binne akwatin. Balbelar ta girgiza kafadunta sannan ta dubi shafiu tace Ramin daka shiga dazun nan anan akwatin take kasan akwai wani bawana dana ajiye shi yayi gadin akwatin yau shekara dari da shirin yana zaune agurin yana gadinta. Ko dazu ma saida ka taka shi baka ganshi ba. Shafiu ya dubi aisha duk da yake a bala'in tsorace yake saida ya daga mata gira to in bakuda wani abu kuma da kuke son tamaba ni zan tafi Mun...gode Madalla sai kuma wani jikon Aisha tace bakinta na rawa. Balbelar ta dubi shafiu tace idan Allah ya kaddara auranka da ita ka riketa da kyau yarinyar kirki ce sannan ta bace. Matasan biyu sukayi ajiyar zuciya lokaci guda shafiu ne yafara magana to sai yaya kuma? Saiki shirya gobe warhaka muna can in Allah ya yarda ko sha biyun dare bazatayi mana acan ba zamu dawo da dukiyar kana nufin har dani zamu tafi? Aisha ta tambaye shi a tsorace. Shafiu ya fashe da dariya cikin farin ciki yace Haba Aisha kiyi amfani da hankalin ki mana ai idan bakya agurin akwatin bazata dauku ba don bana tsammanin karama ce maiyiwuwa mai nauyin tsiya ce. Kuma ni me zan iyayi ina mace? Shafiu ya dubeta kana ya matsa dab da ita har tanajin numfashinsa afuskar ta yace Bakiji abinda tace ba? Akwai wani bawanta dake gurin yana gadin akwatin shi zamu sa ya janyo mana akwatin daga karkashin kasa. Aisha ta bude baki cikin kaduwa. Shafiu kada fa son abin duniya yasa ka zarewa in banda abinka a ina zamu ganshi Aljani ne fa shafiu ya sake fashewa da dariya wannan shine dalilin daya nace dake zamu tafi idan munje bakin ramin saiki murza dan dutsenki idan balbelar ta bayyana saiki roketa alfarma tasa wannan bawan nata dake gadi agurin ya zaro mana akwatin ko kuwa ya kika gani? Aisha ta dube shi da murmushin farin ciki adaidai lokacin ne to Aisha ta kula da kansa Kai shafiu yaushe ka aske wannan gashin naka? Shafiu ya fashe da dariya sai yanzu ma kika lura? Aisha bata iya bashi amsa ba saitaci gaba da kallonsa sama da kasa Alokacin ne ma ta lura ashe har zako zakon faratan dake hannunsa duk ya yanke. Wallahi daka aske gashin saika zama kamar ba kai ba. Shafiu yayi murmushi sai nayi muni ko? Aisha ta girgiza kai tace haba dai ai haka ma wallahi kafi kyau inama ace ina iya kallon ka sosai batareda jin kunya ba SUKA FASHE DA DARIYA. ** ** ** ** Washegari tun da asuba shafiu ya tashi yayi sallah. Wannan shine karo na farko acikin shekaru goma sha takwas da shafiu ya tashi sallah da suba rabonsa da sallah tun yana dan shekara goma aduniya alokacin bai gagari mahaifansa ba. Mahaifin shafiu zaune a dakin shakatawa suna karin kumallo sai suka ga shafiu ya shigo falon ahankali kamar maiyin sanda mahaifan suka kura masa idanu cikin kaduwa domin sun san shafiu in har ba makaranta zashi ba babu abinda zai tashe shi da karfe takwas na safe. Mahaifinsa ALHAJI SADIQ ya kalle shi sama da kasa cikin kaduwa domin ya lura da cewa dugunzunzum din gashin nan da yayi matukar tsana shafiu ya aske shi. Ina kwananku shafiu ya gaishe su a durkushe Lafiya lau shafiu... Suka amsa baki daya cikin mamaki tsawon lokaci babu wanda yace kala can sai Alhaji sadik ya dubi dansa yace a sanyaye shafiu yau kuma shiriya ce Allah ya kawo ma? Shafiu kansa a durkushe yace Eh baba. Zuwa ma nayi na roke ku gafarar abinda nayi muku abaya. Nayi muku alkawarin daga yau nabar shirme da sakarci mahaifiyar shafiu ta fashe da kukan farin ciki Mun yafe maka shafiu. Allah sadik ya tashi tsaye sannan ya dubi dansa cikin farin ciki Na godewa Allah daya shirya min kai kuma tunda Allah yasa shiriya tazo maka saika nemo wacce kake so ayi maka aure. Shafiu ya dago kai cikin farin ciki yace Gobe in Allah ya kaimu zan zo muku da ita baba mahaifansa suka dubi juna sukayi murmushi toh ai shikenan shafiu kuma indai naga ka zarce ahaka zan mika ma ragamar harkokina ahannunka duk da yake dai ba wani abu nake dashi kamar da ba amma In Allah yakaimu jibi za'ayimin wani tsohon biyan bashi na kusan naira Milliyan hudu da zarar an kawo min su kai zan Dankawa. Wannan wani abu ne daga Allah lallai babu abinda yafi komai dadi aduniya irin bin hanya madaidaiciya shafiu yace cikin zuciyarsa duk da wannan alkawarin da akayi masa na wannan makudan kudi zuciyar shafiu bata daina tunanin dukiyar dake binne a karkashin kasa ba. ** ** ** **** **** ****** ******* ***** . Wani katon gyare yayi tsalle yafada faskeken kunnen daya daga cikin yansandan dake bobboye abayan bishiyoyin suna nazarin bakin ruwan. . Dansandan ya kaiwa kunnen mari katon gyaren ya tashi dansandan ya mari kunnensa a banza. Kai wannan masifa dayawa take dansandan yace cikin zuciyarsa sau dayawa yakan zargi kansa da kansa amatsayin mahaukaci domin wai in ba mahaukaci ba wane ne zai shiga aikin dansanda aikin da akullum bashida wata riba sai ta bakin jini kullum kana gadin jama'a da dukiyoyinsu sukuwa nabinku da tsinuwa. Shekarunsa ashirin da biyu yana aikin dansanda amma haryanzu bai wuce sajan ba idan karshen shekarar yazo yake sa ran yin ritaya. Wannan dansandan sunansa AUDU ada can baya yasha niyyar barin aikin dansandan amma sai wani abokinsa yace dashi Haba audu kada ka jahilci aikinka mana wannan aikin da kake rainawa fa babu abinda yafishi muhimmanci domin daku yansanda da malaman makaranta idan babu ku babu gari kaidai abinda zakayi kawai shine ka tsarkake zuciyarka ka nemi Halali acikin aikina sai Allah yabaka lada yakuma albarkaci aikin Amma zancen wai kabar aiki wannan duk bata taso ba. Wannan kalami na abokinsa shi yasa audu kaiwa har tsayin wannan lokaci yana aikin Dansanda daga inda Audu yake fake yana iya hango duhuwar sauran abokan aikinsa su bakwai duk a rabe dauke da bindigogi suna nazarin bakin ruwan Audu na nan a makale zuciyarsa tana yi masa sake sake domin matarsa nada tsohon ciki kuma awatan zata haihu haka nan har izuwa wannan lokacin bai sayi koda buzu ba. Audu ya lalubi aljihunsa ya zaro kwalin taba cikin damuwa. Dan cin hancin ma da muke karba anyi mana bakin ciki gashi dai ba wani kyautata mana akeyi ba amma saboda bala'i kuma ance wai duk hancin wanda mukaci yakaimu Kara... Tunanin audu ya katse adaidai lokacin daya hangi hasken fitilar mota ta nufi bakin dam din abinda yabashi mamaki domin tunda aka kawo su adaren jiya kimanin karfe goma sha biyun dare har zuwa yanzun nan basuga motsin wani mahaluki abakin ruwan ba. To me yakawo mota kuma? Cikin sauri jikinsa na rawa audu ya fito daga inda yake labe bindigar dake hannunsa ta dada nauyi in har akwai abinda audu yaki jiki shine akaishi aikin da za'a iya yin bata kashi kullum addu'arsa itace Allah yasa yagama aikin dansanda ido biyu kafa biyu hannu biyu. Kamar audu sauran yansandan ma sun ga zuwan motar don haka sai suka firfito daga inda suke make kamar yadda aka umarce su sukabi cikin duhun kamar aljanu suka nufi inda sukaga motar tayi. . Shafiu yafito daga cikin motar ya rufe sannan ya zagaya ya budewa aisha itama ta fito amma jikinta na rawa kamar mazari da za'a tsaga jikinta alokacin zaiyi wuya a sami wani digo na jini. Shafiu ya zaro wata katuwar cocila sabuwa daga aljihunsa sannan ya haske cikin ramin lokaci guda kuma ya jiyo ya dubi aisha yace toh Aisha aiki ya rage naki ga ramin nan munzo Ya dada haska mata cikin ramin da cocilan. Aisha ta kurawa ramin idanu na tsawon lokaci har yanzun nan takasa imani da cewa wai shekaru dari da shirin da suka wani daga cikin kakanninta ya binne dukiya acikin wannan ramin. Kinga ma bishiyar giginyar da nake fada miki keda ganinta ai kinsan ta dade dubi fa saboda tsayi harta lankwashe kamar macijiya. Aisha ta zubawa bishiyar idanu na yan dakiku sannan saita dawo da idanunta cikin Ramin. Toh aisha yi maza kiyi kiranta koma koma gida da wuri naga sha dayan har ta gota Aisha ta sauke jakarta daga kafada sannan ta bude jakar shafiu ya matso kusa da ita cikin sauri ya haske cikin jakar da cocilan hannunta na rawa ta dauko dutsen sannan ta murza shi atafin hannunta Sabanin yadda sukayi tsammani guguwa zata tashi awurin awannan karon lokaci guda balbelar ta bayyana abakin ramin ta kada fiffike tace Ai ina nan kusa daku bama sai kinyi bayanin komai ba duk shawarar da kuka yanke jiya ina nan tare daku inajinku In banda abinku ai ni ma ina iya dauko muku akwatin don baku san irin kaunar da mahaifinku ya nuna min bane shiyasa kuma nayi masa alkawarin isar da duk wani sakon nasa. . Tana gama fadin maganar sai tayi girgiza nan da nan kamar budar ido sai kasar wurin ta fara tsagewa sannu ahankali sai sukaga akwatin ta babbako daga cikin kasa ita kadai kaikace raine da ita sannu ahankali ta sauka akusa da inda motarsu take. Balbelar ta kada fuffukanta sannan ta dube su tace Shikenan kwadayinku ya kwanta? Aisha da shafiu suka gyada kai lokaci a tsorace domin abinda suka gano yayi matukar girgiza su. To ni zan tafi sai kuma mun sake haduwa. Kafin kiftawa da bismilla ta bace. Shafiu ya dubi aisha. Aisha ta dubi shafiu jikinsu na rawa cikin sanda shafiu ya matsa kusa da akwatin ya dallara hasken cocilarsa kamar yadda yayi tsammani haka ya ganta to saidai bata kai girman dayayi tunani ba duk jikin akwatin jajur yake da tsatsa tun da yake bai taba ganin irin akwatin ba ko da kuwa a hoto ne domin wannan akwatin a dunkule take sunduki sunduki. Haka nan akwai wasu abubuwa masu kama da madauki ajikin akwatin har guri shida awannan lokacin ne to aisha tayi abinda ta baiwa shafiu mamaki......Hakanan akwai wasu abubuwa masu kama da madauki ajikin akwatin har guda shida awannan lokacin ne to Aisha tayi abinda ta baiwa shafiu mamaki domin yana tsaye akan akwatin sai yaga Aisha ta matsa kusa da akwatin ta durkusa sannan saita sa hannu ta dafa akwatin tsawon lokaci tana nan a durkushe duk da yake baya iya ganin idanunta amma jikinsa yabashi cewa kuka take yi. Kukan me kikeyi Aisha? Babu komai. Tace dashi bakinta na rawa sannan saita mike tsaye ta dube shi tace Tayaya zamu iya sa ta acikin mota? Shafiu ya bude baki kenan zai amsa sai wata bushashshiyar murya daga cikin duhun tace da can lokacin da kukayi satar bakuyi tunanin hakan ba? . Aisha da shafiu suka juya a firgice sannan ne to sukayi ido biyu da yansandan kowannensu rike da bindiga suna zazazare idanu. AISHA TA KWALLA IHU A RAZANE. ** ** ** ** Yansandan suka dubi juna a rude cikin tsananin mamaki sa'ar da Aisha ta gama basu labarinta. Lokacin da yansandan suka ritsa su sun yi niyyar tafiya dasu ofishin yansandan gaba dayansu har da akwatin to amma kukan da aisha tayi ta rafsawa a tsorace tana magiyar cewa abarta zatayi bayani shiyasa INSFETA ZAKARI ya amince sannan yasa yansandan suka kawo motarsu bakin ruwan aka jefa aisha da shafiu aciki sannan aka nemi dasuyi bayanin abinda sukeyi abakin ruwan da wannan uban daren kuma dasu fadi inda suka samo akwatin in dai ba sato ta sukayi ba. Don haka sa'ar da aisha tagama basu labarin sai sukaji abin kamar almara Insfekta Zakari ya harari aisha gamida buga mata tsawa yace Ke kada ki raina mana hankali yanzu ke kina nufin mu yarda da wannan tatsuniyar da kika fara mana? Aisha ta fashe da kuka wallahi ba karya nakeyi ba ai ga akwatin nan gakuma takardar wasikar nan ma agurinsa ta nuna shafiu wanda ke zaune bayako motsi saboda tsabar tsoro duk da wayewarsa babu abinda yake matukar tsoro irin DANSANDA. Yanzu idan nace inason naga ita takartdar da kakan naki yabaiwa aljanar tabaki zaki iya nuna mana? Insfekta zakari ya tambayeta cikin sauri. Aisha ta dubi shafiu tace Basu takardar nan shafiu. Jikinsa na rawa ya lalubo takardar daga aljihun wandonsa ya mikawa Insfekta zaka. Insfekta Zakari ya zurawa rubutun ajamin idanu. Dayake wani zamani daya wuce yataba karatun Allo rubutun ajamin bai wani bashi wahalar karatu sosai ba amma duk da haka da kyar a daddafe ya hada bakaken sannan ya karanta wa sauran yansandan A Fili. Jami'an tsaron sukayi shiru na tsawon lokaci sa'ar da suka fahimce ashe akwatin dake nan dab dasu acike take da dukiyar Milyoyin Kudi. Insfekta zakari yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi Aisha da shafiu yace na yarda da abinda kuka fada amma fa hakan baya nufin bazamu iya cazar ku da laifi kwata kwata bane kunga dai kayan nan da kuka dauko suna da hadarin gaske tunda ko shima kakan naki dukiyar ba tasa bace sata yayi. Saboda haka kinga dolene hukuma tayi bincike akai mai tsayin gaske kafin a gano wanda ya mallaki dukiyar nan tun tsawon shekaru dari da ashirin. Ya danyi shiru. Aisha taci gaba da shishshikar kuka hakan ya daya gani yayi matukar faranta masa rai don haka sai yaci gaba da cewa amma duk da wannan hadarin da kuke ciki idan kuna so zan iya taimakon ku. Aisha da shafiu suka dubi juna a tsorace Muna....so suka amsa baki daya Insfekta yayi gyaran murya yace to abinda nake so daku shine kuyi gum da bakinku kada ku sake wani yaji labarin akwatin nan sannan kuma zan rike wannan wasikar agurina zamuci gaba da bincike har zuwa lokacin da zamu gano mai dukiyar ku kuma kuyimin alkawarin zakuyi shiru da bakinku idan kukayi haka zan sallame ku yanzun nan ku tafi gida idan kuka sake labari ya riskemu cewa kun bada labarin acikin gari to zamuyi muku kamun Yan Fashi kun yarda? . Cikin sauri su aisha suka gyada kai insfekta zakari ya kunnewa sigari wuta cikin farin ciki sannan ya lalubi aljihunsa ya dauko Albashinsa cancakat da aka biya shi awannan ranar ya mikawa Aisha yace ga wannan yan mata kya rage bacin ran da zaki shiga nasan tuni kin gama kasafin abinda zakiyi da dukiyar kakanki ko? To hukuma bazamu amince da haka ba domin shima ba nasa bane sata yayi da'ace wasikar ta nuna cewa dukiyarsa ce to da babu abinda zai hanamu baki kayanki. Aisha ta karbi kudin a tsorace shafiu kuwa ji yake kamar zuciyarsa zata fashe domin yanaji yana gani an raba su da milyoyin kudi an basu dubun naira . Ku tashi ku tafi ku kuma iya bakinku kunji? Insfekta zakari ya umarce su Jikinsu na rawa suka nufi marsandin shafiu har suka shiga motar suka tafi babu wanda yace da wani QALA tafiyarsu keda sai Insfekta Zakari ya dubi sauran yansandan ya fashe da dariya sannan yace to ku saurara da kyau kuji yau Allah yakawo karshen wahalar da muka dade muna sha shekara da shekaru ina fatan kowa daga cikinku zai iya bakinsa domin wannan wata kyautace daga Allah ina ganin abinda ya dace kawai shine mu sa bakin bindiga mu bude akwatin nan mu kasafta dukiyar dake ciki kowa tasa ta fisshe shi ko kuwa ya kuka gani? Kunsan dai ba aikin kama barayi aka turo mu baki ruwan nan ba kwantar da tarzoma muka zoAudu ne yafara cewa haka za'ayi yallabai sannan sai sauran ma suka amsa baki daya mintuna biyar da faruwar hakan yan sanda suka sa bakin bindiga suka balle daddiyar akwatin yar shekara dari da ashirin a karkashin kasa. . Insfekta zakari yakoma cikin mota ya dauko cocila sa'ar da aka bude tsohuwar akwatin yansandan guda takwas suka zagaye ta kowa na hadiyar yawu zasu kwashi banza daga inda suke tsaye suna iya hangen wasu abubuwa manya manya acikin akwatin. Koda Insfekta zakari yataho dauke da cocilan sai yansandan suka dada marmatsawa domin su ga zinare da lu'u lu'un dake ciki Insfekta zakari ya haske cikin akwatin nan da nan yansandan suka dauke Numfashi lokaci guda cikin kaduwa da abinda suka gani. Insfekta zakari yaji kamar hanjinsa ya tsinke. A ajiye acikin akwarin GUMA-GUMA dasu har guda biyar wasu manya manyan duwatse ne kan kura. . Cocilar dake hannun insfekta zakari ta kwace ta fada cikin akwatin fus ta fashe ya juyo bakinsa a kafe ya dubi Audu yace Mun dauki adireshin yaran nan kuwa ? Audu ya girgiza kai cikin kaduwa gami da GODEWA ALLAH DA BA KUDINSA AKA BAWA 'YAR KYAKKYAWAR NAN BA yace. Bakace mu dauki adireshinsu ba yallabai. ** ** ** ** Washegari misalin karfe hudu da rabi na yamma shafiu yayi fakin da bakar marsandinsa a kofar gidansu aisha zuciyarsa cike da bakin cikin ta leko ta koman da suka gani adaren jiya. Ga mamakinsa lokacin data fito saiyaga ita ko ajikinta wai an mintsini kakkausa (ASMA'U MATORI) domin cikin farin ciki ta tare shi tana murmushi SANNU DA ZUWA MY ONE. Shafiu ya dubeta fuskarsa a murtuke yace na fahimce ke Aisha ko jimamin asarar da kikayi bakyayi Aisha ta dube shi gamida girgiza kai daman ba rabona bane shafiu haka allah ya kaddara domin idan abu ya kasance rabonka ne Allah yabaka duk duniya babu wanda ya isa ya hanaka shi haka nan ma idan ba rabonka bane to fa babu wanda ya isa ya baka. Ina fatan zaka manta da komai musa abinda yake gabanmu acikin zuciyarmu Ta danyi shiru sannan tace babu abinda nake kauna aduniya fiye da kai Shafiu wallahi dukiya dana rasa ajiya bata kai ko rabinka ba agurina Nagodewa Allah da bakaine ka kubuce min ba. . Hakan datace shi ya tausasa zuciyar shafiu tayi fari tas don haka ya saki wani fatalwan murmushi yace Haba ai abin ne da ciwo...to amma dai ta bakin naki domin duk dukiyar da zan samu aduniya banza ce idan babu ke Aisha. Aisha ta lumshe idanu naji dadin abinda ka fada wallahi harkasa zuciyata tayi sanyi. Yanzu ma ai shiryawa zakiyi mu tafi Aisha ta bude baki cikin mamaki ina zamu? Mahaifana ne suke son su ganki jiya nabasu labarin ki. Aisha ta rufe idanu a kunyace tace 'kai haka da wurwuri? Shafiu ya harareta yace haba aisha shekarata nawa ina kaunar ki? Don Allah je ki shirya kifito mu tafi suna can suna jiran isowarmu. . Gani nan zuwa my one ta ruga gida aguje shafiu yabita da kallo sannan ya girgiza kai cikin murmushi 'Karfe biyar na yamma suka isa gidansu Shafiu aisha ta caba ado da daya daga cikin leshin da shafiu ya saya mata ya kuma sa akayi mata dinkin gaggawa duk da yake duniya ta juyawa mahaifin shafiu baya saida aisha ta rude da ganin yadda aka tsara farfajiyar gidansu shafiu. Shafiu ya bude mata kofa ta fito sannan sai ya dubeta da murmushi yace zo muje bayan mota nabaki abinda na sayo miki domin ki basu amatsayin kyautarki ta musamman ga iyayena. Aisha ta rike baki duk duniya banida mai kula dani kamar ka. Shafiu yayi murmushi sannan cikin farin ciki sai ya zura dan makulli abayan motar domin bude but din motar don ya dauko kyautar. Yana bude bayan motar sai yayi tsalle gefe guda a tsorace aisha ta rike kafadarsa a firgice tana duban bayan motar sannan ta karkada fuffuke tace KUYI HAKURI NA TSORATA KU KO? Ina son ku sano ba nufina na cuce ku ko na tsorata ku ba nazo ne domin na baku dukiyarku da akaso a zalunce ku adaren jiya yau Allah ya nuna min ranar da zan cika alkawarina dana dauka tun tsawon shekara dari da shirin da suka wuce. Ku leka ku gani dukiyar ku tana bayan motar nasan jiya kwana kukayi bakuyi barci ba kun hadu da azzalumai bata gari ai nayi maganinsu danasa musu GUMA GUMAN DUWATSU ACIKI. . Balbela tayi shiru sannan sai ta dubi aisha tace To Aisha sai watarana daga yau bazaki sake ganina ba tana gama fadin haka saita bace. Shafiu ya dubi aisha murmushi ya subuce masa tun kafin ma ya leka bayan but din motar ya hangi haske da walkiya na tashi aciki. Jikinsu na rawa suka leka numfashinsu ya dauke cak sa'ar da suka ga but din motar cike da wasu irin kananan duwatse masu kyawun gaske suna haske da walkiya. . Dukiyarmu ta dawo aisha shafiu yace sannan yayi tsalle sama ya dire yayi ihu cikin murna ga mamakinsa saiyaga Aisha ba murna takeyi ba maimakon hakan ma sai hawayene ke zuba daga idanunta Kukan me kuma kikeyi? Aisha ta goge idanu tace shafiu kada fa ka manta da cewa wannan dukiyar ba hakkinmu bace domin shima kakan nawa.KARSHE. THE END . Kukan me kuma kikeyi? Aisha ta goge idanu tace Shafiu kada fa ka manta da cewa wannan dukiyar ba hakkinmu bace domin shima kakan nawa SATO TA YAYI. . Shafiu yaji kamar Aisha ta kwada masa guduma a kirji To yanzu me kike nufi? So kike mu dauki dukiyar aka mu shiga gari neman wanda akayiwa sata shekaru dari da shirin da suka wuce ko me? . Ganin ransa ya baci sai Aisha ta matsa kusa dashi ta dafa kafadarsa akaro na farko tace a tausashe Shafiu abinda nake son ka fahimta shine wannan dukiyar ba tamu bace bamuda hakkin taba ta kanaji fa abinda yace shima sato ta yayi. Shafiu ya dubi asiaha a fusace yace To Idan dukiyar ba tamu bace ta wacece? Fada min mana aisha dukiyar wacece aduk fadin garin nan? . Aisha ta fashe da kuka sannan ta girgiza kai tace WALLAHI NIMA BAN SANI BA. Shafiu ya matsa kusa da ita yace kada ki sani ciwon zuciya Aishata Yaya Arziki yana binki kina gudunsa ? . KARSHE. . NAZIR ADAM SALIHI (Nas) An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels

Chapter 7 of 8