Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
shafiu ya shafa duguzumzum din gashin kansa yace Idan duk na rabu da wadannan abubuwa zaki iya kaunata Aisha ? . BAKWAI. 7 Tsahon lokaci matasan biyun suna nan agurin daya a zaune daya a tsaye kawunansu a sunkuye...Tsahon lokaci matasan biyu suna nan agurin daya a zaune daya atsaye kawunansu a sunkuye wannan shine karo na farko da shafiu ya farajin kunyar wata diya mace aduniya. . Bakice komai ba, aisha tayi ajiyar azuciya ta dago kai ta dube shi akaikaice tace Yanzu saboda ni duk saika daina wadannan abubuwan shafiu? Shafiu ya buga katon takalminsa daya akasa yace duk abinda kike so na bari fadamin shi Aisha wallahi nayi miki alkawarin zan bari saboda ke indai zaki kaunace ni Aisha ta sunkuyar dakai kasa na dan lokaci sannan tace a sanyaye kana Kaunata shafiu? Shafiu ya dubeta cikin tsananin mamaki yace saidai inso kike na maimaita miki amma ina tsammanin aina fadi kalmar ina kaunarki tafi sau dari tun farkon haduwarmu dake Aisha ta dada yin ajiyar zuciya akaro na biyu indai da gaske ne kana sona shafiu ina son ka kudure aranka da kyakkyawar niyya cewa daga yau ka daina duk wata muguwar dabi'a dabata cikin addini amma saboda Allah badan ni ba shafiu ya dubeta a rude Ban fahimceki ba aisha Abin da nake nufi shine ka nutsu kabar mugayen dabi'a na sabon Allah ka kuma bari don Allah ba don ni ba kaga sai Allah yabani ladan sanadin shiriyarka da nayi shafiu ya kurawa aisha idanu na tsawon lokaci sannan yace Na fahimceki aisha in Allah ya yarda daga yau zaki fara ganin canji acikin al'amaruna daga yau din nan aisha ta dube shi da wani irin yanayi a fuskar ta mai kamar murmushi tace Amma danaji dadi shafiu na fiki jin dadi aisha. Tunda har nayi abinda ya faranta zuciyarki a karo na farko ya danyi shiru sannan ai ya dubeta yace Aisha ina son kiyimin wata alfarma. Aisha ta dubeshi tace Alfarmar me kuma ni zan iyayi maka? Shafiu yace so nake kiyimin abinda ban taba ganinsa a fuskarki ba Aisha ta dube shi a rude Menene kuwa wannan abu? Murmushi nake nufi Aisha tayi sauri ta rufe idanunta sannan sai wani tattausan murmushi ya subuce mata shafiu yaji wani dadi ya lullube masa zuciya. Daman zanfito kenan ka aiko yaro. Shafiu ya janyo wata katuwar jaka dake kusa dashi agaban motar ya ajiyeta akusa da kafar aisha mika wannan jakar cikin gida saikizo mu tafi kinga mun kusan makara aisha ta dubi shafiu cikin kaduwa sannan ta dubi jakar. Shafiu wannan kuma jakar ta mecece? Shafiu yayi murmushi Atamfofi ne guda uku kawai da leshi guda biyu da takalma kafa biyar kiyi hakuri aisha banida kudine shiyasa ban sayo miki dan kwali da turare ba aisha nta dubeshi cikin kaduwa ta girgiza kai. . Ina haba shafiu wannan kayan ai sunyi yawa ka gan..... Shafiu ya daga mata hannu yace haba Aisha kefa USTAZIYYA CE kinsan babu me mayar da hannun kyauta baya sai shaidan Aisha ta sunkuyar da kai shafiu ya fashe da dariya yace Na daureki ko Ustaziyya Aisha? ** ** ** ** ** Tun karfe uku shafiu ya gama daukar darasinsa yana fitowa daga dakin karatun bai tsaya kama tasha ba kamar yadda ya saba sai ya wuce kai tsaye zuwa cikin motarsa ya zurawa hanya idanu yana jiran fitowar Aisha. Karfe hudu da yan mintuna aisha ta fito tun daga nesa shafiu ya hangota hakanan ma aisha ma ta hango shi. Shafiu ya daga mata hannu aisha ta nufi motar shafiu sannu da zuwa aisha yaya lacka din? Aisha tayi murmushi mun gode Allah shigo daga ciki mana ko kunya kikeji nasan halinku ustazan nan Aisha tayi dariya lokaci guda kuma ta bude kofar motar kusan duk a tsorace ta zauna kusa dashi amma kafafunta na waje kaima ai yanzu ka zama ustazun aisha tace tana dariya shafiu ya fashe da dariya Aisha ta dubi shafiu da murmushi tace Kayi sallar la'asar kuwa? Shafiu ya girgiza kai wallahi banyi ba yadanyi shiru Yakamata ka daina barin lokacin sallah yana wucewa gara ka dauke kanayinta akan lokaci shafiu ya sunkuyar da kai ga mamakinsa sai ya sami kansa yana mai kunyar hada idanu da ita. . In Allah ya yarda daga yau na daina bari sallah na wuceni Aisha ta dubeshi da murmushi tace wallahi kuwa daka burgeni shafiu ya dubeta cikin murna Jin dadinki aisha shine farin cikina aisha ta lumshe idanu ina fatan dai Sallar la'asar din ce kawai bakayi ba ko harda azahar ma? Shafiu ya danyi jim sannan sai yace Gaskiya bazanyi miki karya ba aisha rabona da salla tun asuba amma in Allah ya yarda aga yanzu.... Aisha ta katseshi gami dayi masa murmushi cikin wasa Ah gaskiya tashi kaje kayi salla ka dawo kafin ta rufe bakinta shafiu yafito daga motar ya rufe kofar sannan saiya leka ta cikin tagar motar yace Bari naje nayi sallar amma zakiyi kirana acikin motar ko? Aisha ta gyada kai gamida juya masa fararen idanunta ta gyara zama Je Ka dawo (My One) Ina nan ina jiranka . My One shafiu ya nanata kalmar cikin zuciyarsa ransa yayi dadi tunda yake wata mace bata taba cewa dashi haka ba saidai ko shi yayi kokarin fada musu hakan idan yana kokarin yaudarar su. Shafiu ya ruga cikin sauri ya nufi Masallaci . Harkayi me? Har nayi sallolin aisha ta rike baki Kai shafiu wannan sallar taka da sauri take CONCORD yanzu harka gama sallolin biyu? Shafiu ya dubeta yace Sauri....sauri nayi nagama aisha bana son na barki kina ta jirana Aisha ta girgiza kai Idan ana sallah.. Idan ana sallah shafiu ba a tunanin kowa sai Allah kuma nutsuwa ake bukata ta danyi shiru sannan saitaci gaba da cewa kamata yayi ka sayi yan litattafai na karatun addini ka koma makaranta koka san Allah da kuma yadda ake bauta masa shafiu ya gyada kai idan na mayar dake gida saiki rubuto min sunayen litattafan da yakama na saya dama akwai wani malami anan bayan gidanmu saina fara zuwa gurinsa da daddare Yawwa shafiu ko kaifa aisha tace dashi sannan sai idanunta suka kai ga rukuni balbelu dake wucewa su takwas a sararin samaniya nan da nan taji gabanta ya fadi Ras (ARZIKIN KI YANA CIKIN WANNAN LAYAR) Kalmar aljanar balbelar ya fadowa aisha lafiya naga duk kamanninki sun sauya? Shafiu ya tambayeta yana kallon canjin yanayin fuskar ta cikin mamaki. Babu komai Aisha tace dashi gamida murmushin yake tuni har gumi ya fara sartu kyakkyawar fuskarta me sheki kamar madubi arana shafiu ya dada dubanta ya girgiza kai yace. Kada kiyimin haka kefa ustaziyya ce bai kamata kiyimin karya ba abinda baki sani ba shine duk da gurbacewar tarbiyar nan tawa da kike gani Allah ya hore min wata baiwa in dai har mutum yafada min karya dana duba fuskarsa nake ganewa musamman MATA sanin kanki ne aisha ni kwararre ne a fagen mata duk da cewa dai ke kin zama daban kin sami nasara akaina amma hakan ba zai hanani na gane karya daga bakin abar da nake kauna fiyeda komai a duniya ba Shafiu yayi shiru aisha ma ta yi shiru ta sunkuyar da kai Minti guda da yan dakiku suka shafe babu wanda yace da wani Kala Kada ki damu Aisha idan bakya son kifada min abinda ke damunki shikenan bana son wannan ta zamo sanadiyyar bacin farin cikin rayuwata Aisha ta dago kai cikin cikin sauri tace. . Kayi hakuri shafiu kada kayi fushi dani....shafiu ya saki murmushi yake duk kuwa da cewa ransa ya sosu ban taba yin fushi dake ba aisha kece me sa fushina ma ya dawo farin ciki aisha tayi ajiyar zuciya. Fada masa kawai. Wata zuciya ta fara yi mata kururwa shi kadaine me kaunarki aduniya kinsan kuwa babu wanda ake sirri dashi sai masoyi aisha ta dubi shafiu tace Shafiu jiya kace kana son na baka labarin layar nan daka gani awuyana shin haryanzu kana son jin labarin layar tawa.? ** ** ** ** Wata jibgegiyar budurwa fara jau ta sheke da dariya sautin muryarta kamar bindiga tace Allah ya kiyaye na auri Tsololo kamar ka cab. Dube ka fa saikace Lawurje jiki duk ba nama. Dan tsololon saurayin dake tsaye gabanta sanye da wani kwabdeden tabarau fari ya dubi budurwar da murmushin yake duk kuwa da cewa muzantashi din datayi yayi matukar kona masa zuciya To ke in banda lalacewar zamani ma ina ni ina zabiya abinda baki sani ba shine nifa jibgegiyar mace irin ki ba kalata bace gaku da cin tsiya kume ke yanzu in banda anayi miki alkunya ma kullum fa sai kinyi tusa sau saba'in acikin aji sai Kace BODARA Wasu samari acan gefe guda suka tuntsire da dariya har da shewa. Shafiu yaso yabi sahunsu wajen kyakyatawa to amma labarin layar da aisha ta gama bashi ya cire duk wani nishadi dake cikin zuciyarsa domin tun kafin ta gama bashi labarin yafara gumi musamman ma sa'ar daya fahimci cewa maganar dukiya ce a binne a cikin kasa duk da cewa dai labarin Da aisha ta bashi yafi kama da almara amma shafiu bai daina keta gumi ba. Cabdin dukiya abinne? Shin da gaskene gwala gwalai ne? Ko kuwa zinariya ce me yiwuwa ma. . Tunanin me kake naga kayi shiru? Aisha ta tambaye shi sa'ar dataga tun data gama bashi labarin baice Uffan ba Shafiu yayi ajiyar zuciya sannan ya dago kai ya dubeta akaro na farko tun bayan da tagama bashi labarin. Kina nufin kice min layar dake wuyanki shekararta dari da shirin 120yrs ? Aisha ta dubeshi cikin damuwa Nima fa balbelar ce ta fadamin ta danyi shiru daman nasan da wahala ma ka yarda domin abin yafi kama da tatsuniya in ban da naga kamar ranka ya baci ma da bazan baka labarin ba ina ganin mu bar zancen kawai musa soyayyarmu agaba kaji shafiu? Shafiu ya girgiza kai yana kallon sararin samaniya ta cikin gilashin gaban motar amma a zahiri ba gilashin yake kallo ba kwakwalwarsa ce ke kai kawo. Bazamu bar zancen nan ba aisha kinajin abinda tace dake fa ARZIKIN KI NA BINNE ACIKI waya sani ma ko lu'u lu'u ne aciki kin ko riga kinsan yadda suke da matukar daraja awannan zamanin idan har kika same su mun gama warkewa aisha. Aisha ta dubi shafiu cikin mamaki kana nufin kace dani ka gaskatani labarin dana baka? Shafiu ya dubi aisha fuskarsa a murtuke yace shigo da kafafunki cikin motar ki rufe kofar aisha taso tayi gardamar yin hakan to saidai abinda ta gani a fuskarsa shi ya gargadeta cikin sauri ta janyo kofar motar ta rufe Takardar da kika baro daga cikin layar tana ina? Aisha ta dubeshi a rude tace Gata nan acikin jakata Daukota mu gani Aisha ta bude jakar hannunta na rawa ta mika rubabbiyar takardar sannan ta dauko sauran kwanson fatar layar data barke ta dora masa a cinya shafiu ya warware takardar ahankali ya kurawa rubutun ajamin idanu na tsayin lokaci shafiu ya tsinewa jahilci a karo na farko arayuwarsa domin bai iya karatun ajami ba cikin takaici.Shafiu ya tsinewa jahilci akaro na farko arayuwarsa domin bai iya karatun ajami ba cikin takaici ya mikawa aisha yace a tausashe. . Sake karanta mana abinda ke ciki meyiwuwa mu dan fahimci wani abu daga ciki Aisha ta dubeshi da murmushi tace Anya kuwa akwai abinda zamu iya fahimta aciki? Shekara dari da shirin fa ni dai sau goma sha biyu ina karantawa ban fahimci komai aciki ba yanzu haka ma ba anan garin aka binne akwatin ba ni dai aganina wannan duk shirme ne irin na Aljanu ba gaskiya bane shafiu ya girgiza kai gamida dada mika mata takardar. Gaskiya ne aisha jikina ya bani hakan domin bai kamata da kika buda kiga sakon rubutun aciki ba inda karyane duk da yake dai nasan.... Ya danyi shiru. Ke dai sake karanta mana bi ahankali kadan kadan me yiwuwa ma tashi ma tsinci dami a kala aisha ta dube shi na dan lokaci sannan saita zunkuda kafada ta saduda ta fara karanta wasikar mai rubutun ajami. Shafiu yayi fakare baya ko kwakkwaran numfashi yana sauraron Aisha. (KABI FADAMAR NAN TA DAN MASU DAKE DAF DA GANDUN SARKI KABI BANGAREN AREWA) Dan tsaya haka aisha. Shafiu ya tsayar da ita cikin gaggawa aisha ta dago kai daga kan takardar ta dube shi Me yafaru? Shafiu ya nuna takardar da hannu yace Fadamar wa ma kikace? Sake karanto gurin Aisha ta sake kurawa takardar idanu sannan saita daga kai tace. FADAMAR DAN MASU. Shafiu ya dubi aisha cikin doki yace. Haryanzu baki fahimci komai ba? Aisha ta gyada kai cikin damuwa haba aisha Dan Masu fa duk garin nan wanene bai san DAN MASU HOTEL ba? Aisha taji zuciyarta ta harba cikin sauri tace. Fadamar dan masu fa akace ba Otal ba shafiu ya matso dab da aisha cikin doki yace da ita a tausashe Abinda baki sani ba shine otal din abakin katon dam din nan na dan masu aka ginata shin ke baki taba zuwa bane? Aisha ta girgiza kai sau daya aka taba gayyatata liyafar bikin wata kawata danaji an ambaci otal nace bazani ba shafiu ya shafi dugunzunzum din gashin kansa da hannu yace saurara da kyau kiji Aisha wannan Otal din danake baki labari gurin zuwana ne tafiyar kilomita goma sha biyar ce daga nan mun sha zuwa PARTY da yan mata akwai wani abokina dake aiki a otal din sunansa USMAN TASKA ya taba cewa dani asalin wannan dam din na Danmasu wata katuwar fadamace aka mayar da ita dam shafiu ya danyi shiru sannan sai ya daki kan sitiyarin motar da karfi cikin doki. Meye haka? Aisha ta tambaya atsorace aisha inajin Allah fa yakawo arzikinmu shin kin taba sanin Inda gandun sarki yake kuwa? Aisha ta girgiza kai Nifa kifin rijiya ce babu inda nake zuwa. To bari in fada miki tsakanin gandun sarki da danmasu dam baifi daga nan din nan da muke ba zuwa dakunan kwanan mata aisha ta dube shi cikin kaduwa. Kana nufin kace dani anan aka binne akwatin shafiu ya gyada kai yace Ko shakka ko shakka banayi Aisha amma dai ki bari yau din nan in dare yayi zan tafi otal din na sami abokina usman taska zan so na karewa bakin dam din kallo me yiwuwa ma har zuwa Gandun sarkin. Aisha ta dubi shafiu da murmushi kai shafiu da son duniya kake dubi duk yadda kabi ka tsatstsara abin nan kamar da gaske Shafiu ya bata rai ya dubi aisha Aisha wallahi abinda nake fada miki ya wuce wasa kada kiyi mamaki nan da sati guda mun gama shigowar gari aisha ta fashe da dariya. Allah yasa shafiu ya dubeta cikin murmushi yace Zaki iya bar min takardar nan agurina zuwa gobe? Aisha ta gyada kai riketa ma nan da wata daya ka dawo da ita bana fatan sati guda ma ya wuce ban gano inda dukiyar nan take boye ba y danyi shiru sannan sai ya dubi aisha da murmushi idan dukiyar nan tazo hannunmu dame dame zaki saya ma'ana me zakiyi da kudaden? Aisha ta sake fashewa da dariya tace Oh na shiga uku wannan fa shine zakin mazallako wai 'Da daga ciki yana rokon uba kwabo tun kafin dukiyar tazo tun kafin ma kayi tunanin inda zaka sayar harka fata kasafi shafiu ya dubeta cikin dariya. Haba aisha ai dillalin wada shiyasan kudin jariri ke dai a sami kudiyar ai sayarwa ba aikibane agurina ya danyi shiru Duk da haka dai ya kamata ki fara kasafin abinda zakiyi da kudin kinga da sunzo hannu shikenan sai Yi aisha ta sake fashewa da dariya domin ita harga Allah bata taba kawowa aranar za'a sami wata dukiya binne a kasa ba to amma gudun kada yaga kamar bata goyon bayansa saita dubeshi tace cikin dariya. To ni yanzu shafiu idan na sami wadannan kudade masu dimbin yawa me zanyi dasu ne? Shafiu ya wangame baki cikin kaduwa da mamaki yace Me zakiyi dasu fa kikace? Haba aisha ai KUDI DA MACIJI MAGANINSU KASHEWA. Aisha ta fashe da dariya Allah nuna mana ranar kashe su. Shafiu ya lumshe idanu cikin farin ciki Yace Ameen Ameen Aishata. ** ** ** ** Karfe tara saura kwata daidai ya karaso Danmasu hotel zuciyar nata sake sake da zane zane idan banda nufin Allah ma da tun a hanya zaiyi hadari domin sau uku manyan motoci suna auna shi dan ko kusa ko alama tukin kawai shafiu yakeyi amma hankalinsa baya kan motar haka nan duk kusan minti biyu sai ya shafi aljihunsa ya tabbatar tana nan domin ga shafiu takardar tamkar Cek din milliyar dubu take. Shafiu...Domin ga shafiu takardar tamkar cek din milliyar dubu take. . Shafii yayi mamaki sa'ar da yayi fakin da motarsa ya nufi farfajiyar otal din ba wani abune sashi mamaki ba sai ganin babu kowa a farfajiyar otal din ko ina ka duba a bushe kamar makabarta sai jifa jifan ma'aikatan otal din nan da sunan sunturi Shafiu ya nufi dakin tarbar baki na otal din kenan sai ya hangi usman taska shi kadai yana zaune akan kujerar roba ya jingina da bishiyar dabino tsinken tsire a hannunsa na dama ha nan hannunsa na hagu na rike da sigari yana ta karawa sararin samaniya hazo abinda idan ka dube shi da kyau alokacin saika rantse da Allah babu abinda ke damunsa aduniya nan kuwa idan da za'a rutsa shi ko naman jikinsa za'a saya ba zai biya kudin bashin da ake binsa ba. Shegen sama me ya kawoka haka yau tunda wurwuri naga kuma kamar ma kai kadai ne ba joni ko? Usman taska ne ke magana shafiu ya matsa kusa dashi suka tafa sannan ya zauna akan wani katon dutse fari dake kusa da bishiyar dabinon ya dubi Usman taska yace. . Me yafaru ne naga Otal din naku haka So Dry kamar an share naga kuma banji hayaniyar yan duniya agurin wanka ba Usman taska yayi murmushi yace. Yaushe rabon ka da otal din nan ne? Shafiu ya dan karkata kai gefe kamar zakara yana tunani nafi sati guda rabona da nan kasan ni yanzu nafara girma aure ma nake son yi na huta kune dai kullum jiya ya yau ba kwa girma usman ya fashe da dariya yace. Haba shafiu girma dai ai mun riga munyi shi tun da dai ba haka aka haife mu ba saidai ko HANKALI ya danyi shiru yana kyakyata dariya wacce lalatacciyar ce zata yarda ta aureka shafiu ya dubi usman da murmushi. . Yanzu dai ni ba wannan bace ta kawo ni tashi zakayi mu dan zagaya zuwa can bakin dam gurin yan wanka saika bani labarin abinda ke faruwa din cikin sauri usman taska ya mike tsaye daman wallahi nagaji da zama gashi kuma yau Otal din babu kowa duk sai gundura. Suka fara tafiya ahankali zuwa bakin katon dam din dake fuskantar otal din daga inda suke suna iya hango ruwan dam din yana tambal tambal abin gwanin ban sha'awa gashi kuma bishiyoyi da sukayi sahu sahu abakin dam din duk anbisu da kananan kwaya kwayen lantarki saisi sukeyi kamar rana hakan shi ya baiwa ruwan dam din launin tsanwa tsanwa shudi shudi idan ka hangeshi daga nesa. Wai me yake faruwa ne usman? Shafiu ya tambayi usman ya busa hayakin sigarinsa sama sannan ya yagi dunkulen nama daga jikin tsinken tsiren ya fara tauna cakam cakam kamar me cin cingam. Wasu yan iska ne wallahi sukazo daga cikin gari zasuyi fati kawai sai suka kaure da fada har an kashe mutum uku kuma abin haushi wai duk akan wata Bebi. An kashe mutum ? Shafiu ya tambaya cikin kaduwa an kuma raunata mutum ashirin bashiyasa ai kaga bakin ruwan ba kowa tun jiya yan sanda suke kame har mutum abin ya tabamu har an kama mutuniyata ma MONIKA shafiu ya fashe da dariya. Saika tafi beli usman ya girgiza kai yace Allah sawwaka kai nifa yanzu wallahi so ma nake na tuba na koma ga Allah wadannan al'amuran duk sun fara isata domin na fahimci kamar duk babu riba Da ka kyautawa kanka wallahi shafiu yace. Koni nan ma da kake ganina na tuba wata yarinya na samu ustaziyya mai yawan wa'azi duk ta karyamin gwiwa wallahi. Usman ya fashe da dariya yace Uhm.. Uhm fa shafiu kada kayi tuban muzuru. Allah ya sauwake shafiu yace gamida murtuke fuska ganin hakan sai usman yayi shiru sukaci gaba da tafiya zugum zugum abakin dam din. . Wai ina zamu ne? Usman ya tambaya sa'ar da yaga tafiyar tayi nisa har sun fara tunkarar Gandun sarki Akwai abinda nake son nagani kasan kwana biyu ban zagaya bakin dam din nan ba sukaci gaba da tafiya sannu ahankali har suka kawo daf da wasu manya manyan bututu na ruwa an tara su jibgi guda abakin dam din. Wadannan kuma bututun na menene? Shafiu ya tambaya lokaci guda kuma yana kallon katon ramin mai mai tsayin gaske dake gabansu tuni har an fara binne wasu daga cikin bututun ruwan acikin dogon ramin. Kamfanin ruwa ne ke kokarin kafa wasu manya manyan injinansu wadanda zasu ringa tura isashshen ruwa cikin gari da tuni ma aikin yayi nisa in badan ma'aikatan dake haka sun tarar da dutse ba shafiu ya dubi usman cikin mamaki dutse fa kace ainaga duk fadin dam din nan babu wani babban dutse ballantana ma har a sami wani dutse a karkashin kasa. Usman ya zuki guntuwar tabar dake hannunsa ya jefa sauran cikin ruwa. Abinda yayi ta baiwa mutane mamaki kenan yanzu kokarin da akeyi shine a kokarta fasa dutsen idan kuma ba zai fasu ba sai a karkata ramin yabi ta wata hanyar daban shafiu yayi shiru yana sauraron usman da ace rana ne babu abinda zai hana usman ganin fuskar shafiu jike shakaf da gumi hakanan bugun zuciyarsa ya karu akan na da. . Adaidai inane aka sami dutsen usman ya dubi usman shafiu yace Ga ramin nan abayanka kusa da BISHIYAR GIGINYAR CAN shafiu yaji yawun bakinsa ya kafe cikin sauri ya dubi usman taska yace Ko zan sami cocila a otal dinnan naku? Usman ya dubi shafiu ya girgiza kai Kaifa Baka Rabuwa da rigima me kuma zakayi da cocilar? Shafiu yayi masa murmushi yace 'Ka dauka kai kaine taska makunshin labarai? So nake nima naga dutsen da idanuna yana rufe baki sai ya nufi ramin cikin sauri ya gangara ciki idan ka gama tsurkun ka sameni anan usman yace sannan sai ya kunnawa sabuwar sigari wuta ya zauna akan yashi ya zurawa ruwan dam din idanu yana tambal tambal Shafiu na shiga cikin ramin sai yaji ya taka wani abu mai taurin tsiya kamar dutse jikinsa na rawa ya lalubi aljihunsa ya zaro wayar salularsa sannan ya danna wani madanni nan da nan haske yazo a fuskar wuyar salular tsahon lokaci shafiu yana nazarin abin ko shakka babu abin yaso yayi kama da dutse amma shafiu ya tabbata ba dutse bane domin tun sa'ar da kafafunsa suka dirga akan abin yaji sautin baiyi kama da na dutse ba. To amma saboda ya matsu daya tabbatar da abinda yake zargi sai wata dabara ta fado masa jikinsa na rawa ya fito daga cikin ramin yafara dube dube ba a dade ba ya hangi wani dan madaidaicin dutse ya buga akan abin da karfin gaske maimakon yaji sautin yabayar da KWAS. Sai yaji yabada wani DUM.. Nan da nan shafiu ya mike tsaye ko shakka bayayi abinda yake zargine dukiyar masoyiyarsa sa ce Aisha Allah ya nuna masa ita a saukake. . Usman ya mike tsaye gamida hamma sa'ar da shafiu ya nufo inda yake cikin sauri harka gama tsurkun? Shafiu bai bashi amsa ba sai yace yaushe ne masu hakar ramin nan suke tunanin fasa dutsen? Usman ya fesa hayaki sama. Me yiwuwa sai nan da sati guda kasan rigimar da akayi anan shekaranjiya tasa jami'an tsaro sun sa dokar tabaci anan harna tsawon sati guda kafin su gama bincike binciken su na Al'ada. Kana nufin kace daga yanzu har zuwa sati guda ba'a son aga kowa agurin ? Usman ya gyada kai yace Koda da rana ne kuwa ballantana da daddare shafiu yaji yawun ya dada yin sallama daga bakinsa tuni har yafara tsammanin yazama milloniya wai gashi nan ma har yan maula sun zagaye shi yana ta bari da naira. Samarin biyu sukayi cirko cirko na tsawon lokaci suna kallon juna can sai shafiu ya dubi doguwar bishiyar giginyar nan yace wai usman irin wannan bishiyar giginyar takanyi kamar shekara nawa aduniya kafin ta mutu? Usman ya busa hayaki sama acikin tsananin mamaki domin ya lura akwai wani abu a tattare da al'amarin shafiu. Wani kakana ya taba cewa dani bishiyar giginya na iya kaiwa shekaru casa'in aduniya koma fiye da haka in har ba sareta akayi ba nan da nan shafiu yaji gumi ya fara sartu abayan rigarsa. Shafiu me yafaru ne kaketayimin irin wadannan tambayoyi kamar wani dan sandan ciki? Shafiu yayi shiru bai amsa ba wai tunanin me kaketayi? Shafiu ya juyo firgigit sannan sai ya dubi usman da murmushi yake yace. Tunani nake ina ma ace bishiyar giginya tanada yawan inuwa dana shukata a tsakar gidanmu. . TAKWAS 8 Haba Aisha kinsan dai ai ba zanyi miki karya ba wallahi saida na taba saman akwatin da hannuna na tabbata itace ke har bishiyar giginyar da aka fada aciki wasikar na gani Aisha tayi shiru tana sauraronsa cikin tsananin kaduwa ta fara fahimtar abinda take dauka amatsayin tatsuniya ne ke naman ya zama gaske. Yanzu abu daya nake son kiyimin Aisha indai kikayi hakan na tabbata gobe iyanzu dukiyar tana hannunki Don ba'a jira lamarin kudi ba kuma a bata lokaci ko kankani Me kake son nayi maka? Shafiu ya danyi shiru sannan yace Ina dutsen da kikace Aljanar nan ta baki? Aisha ta bude baki cikin kaduwa me zakayi dashi? So nakeyi kiyi kiran ta mu tambayeta inda hakikanin akwatin nan take koma kara tabbatarwa domin in dai abindata fada gaskiyane yakamata tasan inda aka binne dukiyar taki. Ko bahaka ba? Aisha tayi shiru na tsawon lokaci tana kallon kofar gidansu

Chapter 6 of 8