Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
fice zuwa makwabtansu don yin ta'aziyyar mutuwa. Sarkin makera yaci gaba dakai gwauro yana kai mari sannu ahankali har saida yayi sawu goma sha biyar daga kofar gida zuwa tsakar gida sa'ar daya dawo tsakar gidan ne to ya samu ya zauna akan tabarkar karaunin dake shimfide a tsakar gidan kusa da wani murhu mai dauke da wasu guma guman duwatsu kan kuka har guda uku. Mai masaba ya dubi katon kokon wanda ke dauke da damammiyar furar sannan ya dauke kai gefe guda ya kurawa katon rumbun dake tsakar gidan idanu bayako kiftawa. Shekaru ashirin da suka wuce sarkin makera bashida wata sana'a da aka sanshi da ita sai Qira to amma a boye abayan kasa bashida wata sana'a data wuce SATA. Mai masaba garsakeken kato ne baki mai tarin gashin baki kamar ciyawa haka nan yana da tarin gemu duguzumzum babu kyaun gani sau da yawa idan ya dauki yan kananan yara da niyyar zaiyi musu wasa sai su fashe da kuka idan suka dubi gemun don yafi kama da abin tsoro fiyeda gaemu to amma duk da haka sa'ar da yana saurayi matarsa Habi tana mutuwar kaunarsa a cewarta wai gemunsa shi yafi burgeta fiyeda komai ajikinsa meyiwuwa matar tanada gaskiya domin tun daga samansa har zuwa sahunsa babu wani abin burgewa domin komai ajikinsa babba ne. Babban kai Faffaadan kirji mai kama da kofar gari manya manyan tafukan hannu wadanda ake jita jitar cewa wai ko doki ya mara dasu sai ya MUTU. Sarkin makera mai masaba ya fara ne da turun barayi domin tun yana saurayi yake karbar kayan sata ya sayar dasu sannu ahankali harya fara gawurta. Rannan sai wani mutum mai shigen irin kirarsa ya same shi yace dashi Kaga mai masaba ka dainawa batawa kanka lokaci abanza domin wannan sana'ar kirar daka sa agaba ba wani attajiri zaka zama da ita ba haka nan zakayi ta zama kullum kana babbaka kirjinka agaban wuta kamar fatar ganda kuma kaga turun barayin ma da kakeyi ba wata riba mai yawa ke gareshi ba ni ina ganin ka shigo cikinmu kawai saimu fara koya maka sana'ar mu ta DARE.... Tun daga wannan lokacin mai masaba ya shiga cikinsu wannan kusan shekaru ashirin kenan da wani abu. Kuma har yanzun nan dayake zauna yanata sakar zuci kamar gizo gizo bashida wata sana'a data wuce Sata. Don haka yanzu da mai masaba ya zauna yasa kokon futa agaba sai yafara tunanin shakka babu bazai iya samun saukin tunanin zuci har sai ya kaiwa babban abokinsa labarin katuwar akwatin da sarki yasa a kera domin aikawa da lu'u lu'u da zinare acikinta har kullum babu abinda ke damun mai masaba sai ganin yau kusan shekarunsa ashirin da doriya yana sace sace da fashe fashe kamar bera amma har yanzu bai wuce a kira matsiyaci ba tunda haryanzu jakinsa daya jal aduniya bayan kuma ga makwabtansa nan attajiran ma'abota tarin dawakai dabbobi da tumakai gami da tsuntsayen gida burjik kullum miyarsu da mai da nama amma shi kullum saidai yasha fura da tsatstsaman NONO. Wannan bazata yiwuwa ba. Ya jaddadawa kansa adaidai lokacin ne to ya tuna kokon furar dake gabansa cikin lalaci mai masaba ya dan dauki ludayi ya kwarfo furar nan yakai bakinsa ya dan kurba ga mamakinsa sai yaji furar wani daci daci takeyi cikin sauri ya fesar da abinda ya guntsa sannan ya mike tsaye a fusace. Gafara dai matarsa habi ta shigo gidan sannan tayi turus tana kallon mijin lokaci guda kuma ta kalli kokon furar agabansa kada dai kace furar baka sha ba? Na fara sha sainaji daci kamar kinsa shuwaka aciki. Habi ta harare shi daci fa kace ko kuwa dai bakinka ne yake dacin? Sarkin makera mai masaba ya juya ya nufi kofa batareda ya sake kallonta ba. Ina kuma zaka ta tambaye shi gidan babban aminina zani habi taji gabanta yafadi ras domin ta rigaya ta san duk duniya mijin nata bashida wani Amini daya wuce tsohon barawon nan shekaru ashirin da suka wuce kullum acikin fargabar rana zata iya kwace wa mijinta take amma cikin sa'a gashi dai haryanzu ko kai ba'a taba fasa masa ba amma duk da haka habi tasan ko ba dade ko bajima watarana bazata ga daidai ba don haka ayanzu da yace zashi gurin aminin nasa sai taji fargaba data dade tanayi ta sake mamayar zuciyarta don tasan aminan biyu basu taba kulla abin arziki ba a tsakaninsu Amininka wa kenan kake nufi habi ta tanbaya duk kuwa da cewa tasan wanda yake nufi Sarkin makera ya dubeta cikin murmushi yace Kinfi kowa saninsa ai ke kinsan duk duniya banida abokin daya wuce ZUNGERU. Yana gama fadin haka sai ya fice daga gidan cikin sauri matarsa habi tabishi da kallo cikin kaduwa adaidai lokacin ne jakin sarkin makera ya fara wani mummunan kuka Uhu.. U..Wuu. U habi ta dubi jakin a fusace tace Allah yayi min tsari dakai La'ananne tasha ji ana cewa duk sa'in dakaji jaki yana kuka wai shaidani yagani habi batayi mamakin jakin shaidani yagani yana bin mijinta abaya. ** ** ****** ****** ******** ******* ******* Zangeru na gaba dauke da fatanya matarsa tagogori nabinsa abaya dauke da balbela zugun zugum babu mai cewa kala kowa cikinsa ya duri ruwa kamar masu zuwa gidan makoki tagogori dakyar take tafiya ha nan balbelar dake dauke ahannunta ji takeyi kamar dauke take da maciji domin ita duk gani take kamar balbelar zata iya yin tsalle ta cakar mata idanu koma ta makureta. Idan har akwai abinda tagogori take tsoro baiwuce aljani ba. Saigashi yau da kanta ta dauko aljanar ahannunta zata kaita har gida. Zangeru kuwa wanda ke gaba yana jan kafa dakyar ji yake kamar ansa masa sasari a kafa a iya tsayin zamanin dayayi yana harkar sana'ar bera yayi gamo da hadararruka iri daban daban amma har zuwa wannan lokaci bai taba gamo da aljanu ba domin shi atunaninsa main banda yaji anata fada kuma wani malaminsa dake biyasa masa karatun kur'ani tun yana karami yataba masa bayanin wata aya da take magana akan aljanu dasai zangeru yace babu Aljanu ma sam sam aduniya tunda dai bai taba gamo dasu ba to sai gashi kuma yau da kansa ya dauko wa kansa jaraba. Sannu ahankali har su zangeru suka karaso cikin gari sa'ar da suka shigo ta cikin babban dandalin garin sai mutane sukayita binsu da kallo cikin mamaki domin abin mamakine ace mutum yarasa abinda zai zo dashi gida daga gona sai BALBELA. Adaidai lokacin da suka karaso kofar gidan sarkin aska ne sai matarsa wacce ta kasance kawa ce ga Tagogori ta leko tace Oh Tagogori ya kuma da balbela kuka zo mana daga gonar? Hala wannan balbelar yar Misra ce. Tagogori ta dubi mijinta zangeru sannan ta dubi matar sarkin aska da murmushin yake tace Meyasa kikace haka? Ko kina gani kikayi kyawunta yayi yawa? Matar sarkin aska ta girgiza kai tace A'a gani dai nayi duk balbelun dake cikin garin nan basu ishe ku ba har sai kunzo da wata daga daji. Akaro na farko sai zangeru ya dubi matan biyu dake jayayya yace kufa idan kuka fara jayayya kunyi tayi kenan Dan Allah tagogori taho mu karasa gida kada almuru ta riske mu akofar gidan wanzamai matar sarkin aska najin haka saita fashe da dariya tace A'aha zangeru indai yar sarautar nan tamu ce kakewa bakin ciki bari kaima abaka sabuwar sarauta daga yau na nadaka SARKIN BALBELU. suka fashe da dariya sannan zangeru suka wuce Lokacin da suka karasa gida almuru ta riga tayi haka nan har yanzu cikinsu dure yake da ruwa domin basusan yadda zasuyi da balbelar ba. Ahaka cikin tsananin fargaba suka shigo katuwar farfajiyar gidan ma'abociyar shuke shuken bishiyar zogale da kabewa daga bangaren kudu kuwa baka hango komai sai tarin ciyayi ko ina marasa amfani haka nan daga bangaren gaba wata tsohuwar rumfa ce shekararriya wacce wasu awaki guda biyu ke karkashinta a daure su kansu awakin asalinsu zangerune ya sato su awani kauye dake makwabtaka dasu. . In ka dauke rumfar dabbobin fankadediya farfajiyar gidan bata mallaki komai ba sai wasu bukkoki guda uku da kuma wani tsohon rumbu wanda rabonsa da ya dauki sama da damin gero biyar tun zangeru yana saurayi. Wadannan bukkoki guda uku da tsohon rumbun gamida awakin nan guda biyu na sata su kadaine arzikin dayayi yana sata sau dayawa tagogori tasha nuna masa cewa shifa zalinci ba abinyi bane kuma baisa mutum yayi arziki kuma koda yayi arzikin ma bazai tabajin dadin sa ba. To amma sai zangeru ya dubeta ya fashe da dariya yace tagogori kenan ai idan kikaji ana cewa ba'a arziki da kayan sata to daman satar batakai sata ba. Wannan shi yasa sa'ar da zangeru ya sato awakin nan guda biyu sai yace da Tagogori ga wadannan awakin kici gaba da kiwata minsu da sannu zan samo musu yan uwa domin lokaci yayi daya kamata na nuna miki cewa ana arziki da kayan sata kuma akalla dai ayanzu ko da mutuwa nayi nasan nabarwa dan Dana AMADI gadon awaki guda biyu. Wannan amadi da zangeru yake amagana akai shine babban dansa kwaya daya jal aduniya sabanin iyayensa amadi kyakkyawane dogo fari mai dan siririn fashin goshi zai kai kimanin shekaru goma sha tara aduniya tun daga kansa mahaifiyarsa tagogori bata sakeyin ko batan wata ba sai awannan karon data sami ciki akalla wata bakwai. Sabanin mahaifinsa Amadi bashida wani aiki daya wuce farauta wata sa'ar idan yafita farauta sai yayi wata guda baidawo ba. Don haka sa'ar da mahaifansa suka karaso farfajiyar gidan dauke da balbelar sababin sai sukayi mamakin ganin kayan farautar Amadi wasu zomaye guda shida yankakku da beguwa biyu da damo biyar duk zube atsakar gidan Amma shi Amadi baya nan. Zangeru ya dubi kayan farautar sannan saiya jefar da fatanyar ya zauna jagwab agabanZangeru ya dubi kayan farautar sannan sai ya jefar da fatanyar ya zauna jagwab agaban kayan farautar tagogori tayi sauri ta zauna akusa dashi sannan bakinta na rawa ta mika masa balbelar tace Ungo balbelarka. Zangeru yadubi tagogori a tsorace jikinsa na rawa kamar mazari ya mika hannu ya karbi balbelar yana mai addu'ar Allah yakawo dansu Amadi ko sa sami mafita domin yasan duk inda Amadi yake baiyi nisa ba tunda dai ga kayansa nan yadawo sa'ar da zangeru ya karbi balbelar sai yaci gaba da juyata ahannu zungum babu magana kamar kurma. Adaidai lokacin balbelar tayi mika gamida girgiza fukafukanta sannan tace cikin irin siririyar murya mai kada hantar ciki. Yanaga duk kunyi shiru kamar wadanda suka hadu da wani mugun abu? Inason ku saki jikinku dani tunda dai har dayanku ya ambata cewa yana kaunata ni kuwa nayi alkawarin har abada bazan taba cutarku ba. Balbelar tayi tsalle daga kan cinyar zangeru ta dawo kasa ta tsaya tsakanin ma'auratan guda biyu sannan ta bude dogon bakinta kamar mai kokarin yin hamma taci gaba da cewa kufa nake sauraro bayin Allah kun saki jikin naku dani kokuwa haryanzu tsoron nawa kukeyi? Balbelar ta sake yin shiru akaro na biyu zangeru yayi ta yan maza duk kuwa da cewa yawun bakinsa ya kafe karaf yace inason kiyimin alkawari daya indai da gaske ne kika kaunata. Alkawarin me kake son nayi maka? Ta tambaye shi zangeru ya dubu balbelar bakinsa na rawa yace so nake kiyimin alkawarin har abada bazaki taba rikida zuwa kamanninki na aljanu ba domin zanfi son ganinki akamanninki na balbela. Balbela ta saki wata kakkausar dariya mai kama da busar kakai tace indai abinda kake so kenan nayi maka alkawarin har abada bazan taba zuwa ma awata siffa ba saita balbela zan kuma kasance inatare dakai har iya karshen rayuwarka tana gama fadin haka sai balbelar ta juya ta dubi tagogoti wacce ke zaune ko kwakkwaran motsi batayi tace da ita Kefa baiwar Allah kina kaunata? Tagogori taji tsigar jikinta tayi wani yarrr cikin sauri ta gyada kai kamar kadangaruwa ki saki jikinki dani baiwar Allah ni mai kaunar kuce sannu ahankali zaku saba dani kamar yadda kuka saba da dan kyakkyawan yaron nan naku Amadi mafarauci. Ma'auratan biyu suka dubi juna cikin tsananin mamaki da kaduwa zangeru ya dubi balbelar cikin kaduwa yace a ina kikasan Amadi? Balbelar ta karkade fukafukanta biyu tace Munsha haduwa dashi acikin daji inda yake farauta tun yana karami nake ganinsa shine dai baisan ni ba. balbelar ta danyi shiru sannan ta dubi namun dajin dake zube a tsakar gidan tace ko jiya ma agabana ya kashe wadannan zomayen guda biyu balbelar nagama fafin haka sai tayi tsalle sama ta sake direwa sannan saitayi girgiza da karfi nan da nan wata bakar guguwa ta turnike wurin Tagogori ta tashi a tsorace ta nufi inda maigidanta zangeru yake tafada kan cinyarsa ta kankame shi cikin Razana kada ku tsorata ba wani abu zanyi muku ba aini da ku alkawarine babu cuta ko cin amana wata siririyar murya ce ke fadin hakan ba'a dade ba sai guguwar ta tsaya cak. Ma'auratan biyu sukayi ajiyar zuciya kana suka dubi inda balbelar take haryanzu tana nan tsaye saidai kuma wannan karon balbelar dauke take da wani madaidaicin dutsen kankara fari sol a bakinta tayi tsalle ta sauka akafadar zangeru sannan ta saki farin dutsen ya fado tsakanin cinyoyinsa. . Tagogori ta dada kankame zangeru atsorace ji takeyi kamar zata sume. Balbelar ta dubi farin dutsen tace dan zangeru dauki farin dutsen nan ka adana shi duk sa'ar da kake buatar wani taimako daga gareni jefa dutsen kawai zakayi a bakinka kokuma ka murza shi tsakanin hannayenka zan bayyana. Tayi tsalle ta baro kan kafadar zangeru ta sake direwa akasa sannan tace ni zan tafi sai kun bukaci ganina kuma. Tana gama fadin haka ta tashi firr ta tafi abinta. Zangeru da Tagogori suka bi balbelar da kallo cikin kaduwa har saida ta bace a sararin samaniya sannan sukayi ajiyar zuciya baki daya. Tagogori tayi sauri tabar jikin mijinta ta zauna akusa dashi sannan ta dube shi jikinta na rawa tace ga irinta nan ai lalacinka da shishshiginka ya janyo mana bakar jaraba har gida. Zangeru ya dauki dan farin dutsen da balbelar ta bashi ya juya shi ahannunsa sannan ya dubi tagogori cikin murmushi idan kika kara zaginta saina murza dutsen nan ta dawo miki yanzu yanzun nan Tagogori taja da baya a tsorace ka rufamin asiri don Allah zangeru wai me ke damunka ne? Kai yanzu harma fatan ka sake ganinta kakeyi? Ni wallahi da zaka biyata tawa ma da saika jeda dutsen nan acikin rijiya kaga mun rabu da ita kenan har abada zangeru ya saki wani busashshen murmushi kana ya dada duban dutsen dake hannunsa yace kin cika yanke hukunci da wurwuri tagogori kika sani ko watarana zamu bukaci taimakon nata? Adaidai lokacin da duk wannan ke faruwa ne to Amadi ya shigo gidan dauke da kwari da baka. Mahaifan nasa sukayi shiru lokaci guda sannan suka zuba masa idanu Lafiya naga duk kunyi jigun jigun? Zangeru yayi sauri ya saki murmushin yake yace lafiya amadi dawowarmu kenan daga gona ina fatan kadawo lafiya. Amadi ya ajiye kwari da bakansa agefe guda sannan ya dubi mahaifiyarsa yace lafiya lau amma inajin gobe ma zan koma daman zuwa nayi na kawo muku wannan ya nuna zomaye da sauran naman farautar dake zube a tsakar gidan. An gode amadi allah ya saka maka bari ma na tashi in gyara su Tagogori ke fadin haka lokaci guda kuma ta mike tsaye ta nufi inda yankakkun zomayen nan suke tana durkusawa akan zomayen kenan sai sukaji kamar daga wata garjejiyar murya tace Gafaranku dai masu gidan nan. Tagogori ta juyo cikin sauri ta dubi kofar gidan nan da nan taji yawun bakinta ya kafe bugun zuciyarta ya dadu ko daman kafin ma ta juyo tasan duk duniya babu mai wannan wargajejiyar murya mai kamar gogen tsumma sai mutum daya mutumin daya kasance babban amini ga maigidanta amma har yau bata taba farin ciki da ganinsa ba domin ta rigaya tasan mutumin tauraruwa mai wutsiyane ganinsa ba alheri ba. Mutumin dogo baki mai katon kai da tarin gashin baki da buzu buzun gemu da faffadan kirji kamar kofar gari ya matso kusa dasu ya dubi zangeru da faffadan murmushi yace tun ahanya naketa addu'ar Allah yasa na same ka ya danyi shiru tashi mu fita daga kofar gida wani labari ne ke cina. Shine nazo maka dashi tunda dumi duminsa. Zangeru ya mike cikin sauri fuskarsa a washe yace sarkin makeran duniya MAI MASABA ni daman nasan ai ungulu bata jewar banza dame kazo mana? Mai masaba ya dubi Amadi da tagogori sannan ya kiftawa zangeru idanu yace zo mu fita daga waje zangeru yabishi cikin sauri suka zagaya bayan danga Tagogori ta dubi Amadi cikin kunan rai shiko Amadi ya dubeta cikin mamaki yace da ita cikin rada wai daman haryanzu baba bai daina muguwar sana'ar nan ba? Tagogori taji kamar hawaye zai zubo mata don haka ta dauke kai gefe guda tace Mai hali ai baya barin halinsa Amadi . UKU 3 Inajin fa ga dukkan alamu zangeru tsuntsu daga sama gasashshe na kokarin fadowa cikin akushinmu Mai masaba yace da zangeru sa'ar da suka zauna akan ciyawar da ta mamaye jikin dangar gidan suka mimmike kafafunsu kamar masu daukar darasu. Daga inda jibga jibgan mutanen biyu suke suna iya hango wata katuwar duhuwa ma'abociyar yawan bishiyoyi da ciyayi haka nan adaf da duhuwar wasu jakaine guda biyu da shanu uku suna kiwo abinsu suna harbin iska babu abinda ya dame su aduniya. . Zangeru ya muskuta ya lalubi katon goro ya barashi gida biyu ya jefa rabi abakinsa sannan ya mikawa mai masaba rabin kana ya dada cewa bani labari nasha abokina me ka gano mana? Mai masaba ya jefa bangwalelen goron mai kamar taura gaba daya cikin bakinsa ya fara taunawa rumus rumus kamar jaki nacin danyar ciyawa. Dazu dazun nan na dawo daga gidan sarki an umarceni dana kera wata katuwar akwatin karfe yayi shiru yana duban fuskar zangeru. Zangeru ya daga hannu cikin kosawa yace to ci gaba mana ina sauraron ka An kiraka gidan sarki ance ka kero katuwar akwati Uhum Uhuim mai masaba ya zura hannunsa abaya ya karyo wani dan siririn kara daga jikin dangar ya fara sosa doron wuyansa da karan duk abinda yakeyi zangeru na kallonsa ya lura alamun damuwa karara a fuskar mai masaba abin ne yanada matukar hadari domin idan mukayi kuskure koda kankani ne zamuyi hasarar rayuwarmu idan kuwa mukayi nasara mun gama shiga sahun Attajirai kenan domin bamu ba hatta tattaban kunenmu sun rabu da talauci me yiwuwa ma dole ne mu bari garin. Zangeru ya shura kafafunsa biyu cikin rairayi sa'annan ya dubi mai masaba cikin kaguwa da damuwa ni har yanzu nakasa fahimtar inda soki burutsun nan naka yasa gaba yakamata ka warware min zare da abawa. Mai masaba yayi ajiyar zuciya yace wato wannan katuwar akwatin karfen danake baka labarin ansakani na kera sarki sabitu ne ke son kwashe duk wasu ma'adanai masu daraja daya mallaka zai aike dasu zuwa gurin babban amininsa sarku Lurwanu. Zangeru ya saki wani kwakkwaran huci rairayin dake gabansa yayi sama fuuu kamar yar karamar guguwa Ma'adanan da kake magana akai suturu ko makamai ko kuwa me? Mai masaba ya saki wata kekasashshiyar dariya wata sa'ar zangeru nakan dade banga shashasha kamar kaba. In banda abinka akan wasu suturu ko makamai karafan banza zan dauko kafa na biyo ka har gida don kawai jin dadin hira? To bari kaji inason ka bude kunnuwanka da kyau wannan akwatin da nake baka labari cika shi za'ayi da gwala gwalai zinare da Lu'u'lu'u. . Zangeru ya zabura cikin kaduwa numfashinsa ya dauke bakada hankali mai masaba lu'u'lu'u fa kace cikin akwati mai masaba yayiwa zangeru murmushin yake yace kada kayi shakkar abinda nake fada maka. To kai duk agurin wa ka sami wannan labarin? Kada fa wani makaryaci ya sayar maka da da'ifin labari kasamu wahalar banza nasan dai nufinka shine mu tare wanda sarkin zai aika muyi fashin akwatin ko ba haka kake nufi ba? Mai masaba ya fashe da dariya yace dadina dakai saurin fahimtar zance da inda zancen ya nufa ya danyi shiru sannan sai ya dubi zangeru yaci gaba kasan.Ya danyi shiru sannan sai ya dubi zangeru yaci gaba kasan sarkin dogarai tsohon abokina ne agurinsa duk na sami labarin don shine shugaban ma wadanda za'a aika da kayan acewarsa su shida zasu raka akwatin Kayan. Su shida zangere ya tambaya mai masaba ya gyada kai Kaga kenan ina har muna so muji dadin yi musu kofar rago muna bukatar karin mutum daya kenan kaga kowanne daya daga cikinmu sai yayi maganin mutum daga cikinsu fadawan kenan. Mai masaba ya gyada kai cikin gamsuwa kwarai kuwa muna bukatar karin mutum daya amma inajin ai MAKWARO naka yana gari ko? Zangeru ya danyi kasake yana tunani can sai ya gyada kai yace kwarai kuwa muna iya tafiya da Makwaro kasan kuwa gwani ne wajen iya harbi dan banza da katon kai kamar Murhu. Mutanen biyu suka fashe da dariya sannan suka mike tsaye lokaci guda zangeru ya dubi mai masaba yaushe ne ranar da zasuyi tafiyar? Mai masaba ya shafi keya wannan shine bansani ba yanzu dai kwana uku aka bani na gama kirar akwatin nasan kuma sarkin dogarai ne zaizo daukar akwatin zanyi kokarin na bugi cikinsa naji ranar da zasu fita da kuma ta hanyar da zasubi domin yanzun zuwa dai nayi na tsurkunta maka don ka zama cikin shiri kada kaji komai zangeru yace cikin gaggawa ni daman kullum ashirye nake wanda yake neman kuka ballantana aka jefe ni shi da kashin awaki ni dama fa wallahi mai masaba na gaji da kanana kananan sace sacen nan kullum fatana shine nayi katuwar satar da zan zama attajiri kada daga nan saina tuba nabar sata. Mai masaba ya fashe da dariya nace lallai abokina ko yaushe tunanina iri dayane da naka mutanen biyu suka fara tafiya ahankali suka bi yar siririyar hanyar da zata kaisu har can cikin gari koda suka fara tafiya sai zangeru ya dubi mai masaba yace Idan munyi nasara yaya zamuyi da wannan tarin dukiya? Mai masaba ya danyi shiru yana girgiza kai sannan sai yace Lallai kazo da babbar tambaya amma yanzu dai bri mu fara samun dukiyar tukunna samunta yafi yadda za'ayi da ita wuya idan mukayi nasara ba sai mu bar garin ba me kuma zai kara zaunar damu awannan garin gara mu tafi can nesa inda zamu sha gararin gabanmu cikin nutsuwa AI KUDI DA MACIJI MAGANINSU KASHEWA zangeru. Sa'ar da mutanen biyu sukazo rabuwa sai sukayi musabiha da juna kai ka dauka wasu shehunnan malamai ne alokacin ne to zangeru ya dubi mai masaba yace yanzu sai yaushe kenan zakazo muyi shirin karshe ? Da zarar nakai akwatin nakuma bugi cikin sarkin dogarai zan dawo kaidai sai kayi kokari ka sanar da Makwaro yazama cikin shiri mai masaba na gama fadin haka sai ya juya cikin sauri yabar zangeru tsaye. Zangeru na nan tsaye yana kallon bayan amininsa mai masaba har saida ya bace acikin duhun almuru zangeru ya juya ya nufi gida zuciyarsa fal da sake sake koda yafara tafiya sai ya tuna da farin dutsen dake daure agefen banten sa balbelar ta fado masa arai ga mamakin zangeru saiyaji hannunsa yakai ga dutsen zangeru ya mulmula dutsen da yan yatsunsa sai yayiwa kansa murmushi. Anya kuwa lokacin da zan bukaci taimakon balbelar baizo ba? Zangeru ya tambayi kansa sa'ar da ya sake mulmula dutsen. ** ** ******* ******* ********* ******* Washegari da la'asa sakaliya Gimbiya Hussaina yar sarki sabiu tayi hawa ita da wasu amintattun kuyangin sarki sabitu su shida suka nufi wani makeken gandun sarkin wanda ke dab da katuwar koramar nan ta DANMASU. Wannan shine karo na farko da Hussaina ta fita irin wannan kilisa ta shakatawa tun bayan da mahaifinta sarki sabitu ya kwanta rashin lafiya. Kada ku takurawa kanku akan rashin lafiyata ku tafi ganduna ku shakata ko kwa sami saukin damuwa sarki sabitu ne ke cewa ya'yan nasa biyu a safiyar ranar domin ya fuskanci tun bayan daya kwanta rashin lafiya bai kara ganinsu a cikin walwala ba. Wannan shi yasa Hussaina hawa ita da kuyanginta suka karaso cikin Ni'imtaccen gandun sai suka tarar tuni har bayin sarki sun kafa musu wata katuwar rumfa ta alfarma an shimfide cikinta da Tattausan kilisai da matasan kai da fitilu masu hasken gaske domin ga al'ada sukan kai har dare wata sa'ar basu koma gida ba. Wasu kuyangin guda biyu masu dan siririn wuya kamar na barewa suka kama wa gimbiya hussaina ta sauko daga kan dokinta tana sauka sai duk farfajiyar ta game da kamshin dake tashi daga jikinta cikin takama fuskarta na annuri ta nufi cikin rumfar ta cire katuwar alkyabbar dake jikina sannan saita dubi kuyangin tace bari in gangara cikin fadamar can nayi wanka ku shirya mana kayan sha na dangin zagi kafin na dawo Kuyangin suka amsa cikin girmamawa Gimbiya Hussaina ta nufi katuwar fadamar ma'abociyar sassanyar iska da tarin tsuntsaye tun daga nesa taji sanyi ya fara bugun fuskarta ga mamakinta saitaji duk da muguwar rashin lafiyar mahaifinata ranta yayi fari tas musamman da tajiyo tsuntsaye sai rera wakoki sukeyi cikinn muryoyi iri daban daban. Wannan katuwar fadamar ni'ima da Hussaina ta nufa tana da girman gaske kuma wani dan karamin bangare nata ya shigo ta cikin gandun sarki sabitu sau da yawa ma da ruwan koramar ne fadawa suke ban ruwan shuke shuken kayan zakin dake gandun na sarki don haka AYANZU da Hussaina tayiwa koramar tsinke saita dinga bin gefen koramar daya fara tun daga cikin gandun sarkin har zuwa waje. Sannu ahankali hussaina na tafiya agefen fadamar kyawawan kafafunta na fantsama da ruwa acikin ciyayin dake gefen koramar har dai ta kawo daidai wata yar duhuwar dogayen ciyayi wanda daga su ne hussaina zata riski inda take so tayi wankan domin duk sa'ar datazo gandun anan take wanka badon komai ba kuwa sai don dalilai guda uku. Na farko dai ruwan dake dab da wannan dogayen ciyayi tsabtacce ne na biyu kuwa ruwan bashida zurfi awannan bangaren babban

Chapter 2 of 8