Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
dalilinta na uku kuwa shine gurin yanata matukar sirri domin dogayen ciyayin sun zagaye bakin ruwan sunyi masa dan karamin kuri wanda in tana wanka a gurin babu wani mahaluki dake wucewa ta kusa da koramar daya isa ya hango ta saidai in ya kusanci gurin sosai. Wannan kuwa bai cika damun Hussaina ba domin har kullum idan tazo wanka takan ajiye kayanta ne agabar koramar kusa da inda zata iya daukarsu cikin sauri ya Allah koda zata jiyo motsin zuwan wani. Lokacin da Hussaina ta kawo dab da wannan ciyayi ne to taji wani kwakkwaran motsi acikin ciyayin hussaina ta tsaya turus taji kirjinta ya harba to amma bata tsorata sosai ba domin ta riga tasan babu wani abu mai hadari tattare da koramar amma da yake tun da take zuwa koramar bata tabajin motsin komai ba shiyasa ta faduwar gaba. Da farko ta ayyana cewa motsin yafi kama dana wani abu mai girma me yiwuwa wani dan karamin naman daji ne hussaina tace cikin zuciyarta tsawon lokaci hussaina na tsaye cak. A boye bayan ciyayin ita batayi gaba ba ita ko batayi baya ba shiru shiru ba'a sake motsin ba jin haka hussaina ta saki wani tattausan murmushi. Hussaina yar budurwa kin cika tsoro kamar ba yar sarki ba tace da kanta sannan cikin takama da tabbacin babu kowa awurin saita ta tarar da dogayen ciyayin ta nufi bakin koramar tana shiga tsakanin ciyayin ne to ta hango shi zaune akan wani dutse da ta saba zama ta tsane ruwan dake jikinta aduk lokacin da zata zo wanka bakin koramar. Hussaina tayi turus tsakanin ciyayin zuciyarta na harbawa tsakanin hakarkarinta domin azuciyarta ta dauka aljani ne saurayin dake zaune akan dutsen dogone fari kyakkyawan gaske na gani afadawa sarki saurayin yana dauke da siririn fashin goshi haka nan dauke yake da wani kyakkyawan kanari a hannunsa. Matasan biyu suka kurawa juna idanu na dan lokaci hussaina taji zuciyarta ta dulmiya cikin sauri ta sunkuyar da kanta a tsorace bata iya ci gaba da kallonsa ba. Kai amma fa wannan saurayi ko aljani ne da kyawu yake zita. Hussaina tace cikin ranta ga mamakinta saitaji nan da nan tsoron dake zuciyarta ya gushe sannan shaukin ta sake ganin kyakkyawar fuskar ya mamaye gurbin wajen. Ahankali sai hussaina ta sake dago kai sai sauratin yayi mata murmushi sannan ga mamakinta saitaji saurayin yace cikin wata tattausar murya. Kiyi hakuri ranki ya dade ga dukkan alamu na tsorataki ko? Hussaina ta dada kallon kyakkyawan saurayin batareda ta shirya ba sai taji murmushi ya subuce mata lokaci guda kuma ta girgaza kai tace masa Uhm.. Uhm ai ba wani tsorata sosai nayi ba... Kawai dai bantaba tsammanin ganinka anan bane. Dogon saurayin ya mike tsaye akan dutsen kana ya gyara wa kanarin dake hannunsa riko yace Nima tsautsayi ne yakawo ni ranki ya dade wannan tsuntsun dake hannuna shina biyo da kyar na kama shi. Gimbiya Ussaina tayi shiru tana sauraron saurayin akwai wani kallo da muryarsa keyi wanda yake burgeta. Idan kinyi min izini ranki yadade ni zan tafi daman abinda yakawo ni kenan kuma na kama shi kada ka damu ni bakayi min laifin komai ba ta danyi shiru tana dubansa na Gode ranki ya dade Allah yakarawa sarki Lafiya hussaina ta dubeshi cikin mamaki tace Anan garin kake ne? Saurayin ya gyada kai Ni Talakanki ne ranki yadade gidanmu na nan a karshen gari...mahaifina..manomi ne yace da ita bakinsa na rawa. Amma kuma bantaba ganin kaba? Ta tambaye shi cikin mamaki ai ban cika zama agida ba wani lokaci ma sai nayi wata guda ko fiye da haka bana gari ni mafaraucine kusan duk rayuwata acikin daji take. Jin haka sai ya burge gimbiya hussaina don haka cikin sauri ta dago kanta tayi mata kallon girmamawa tace Lallai ka isa jarumi.. Nikuwa babu abinda nafi so aduniya kamar Jarumi ta danyi shiru sannan saita matsa dab da dutsen da yake tsaye ta dube shi da tattausan murmushi dan saurayi yayi saurin sunkiyar da kansa kasa sa'ar data matso dab dashi haka nan kwarjinta duk ya daddaure masa jijiyoyin jiki to amma duk da haka yayi matukar jin dadin yabon da tayi masa na Jarumta. Yaya kayi shiru ai gara ka sauko daga kan dutsen ko kuwa kafison kayita tsayawa akai? Jikinsa na rawa saurayin ya sauko daga dutsen ya tsaya agabanta gimbiya hussaina kanarin rungume a kirjinsa wata..........Jikinsa na rawa saurayin ya sauko daga kan dutsen ya tsaya agaban gimbiya hussaina kanarin rungume a kirjinsa wata sassanyar iska ta huro daga cikin fadamar ta fara fifita matasan biyun. Saurayin yaji wani irin ni'imtaccen kamshi ya bugi hancinsa. Matasan biyu suka kurawa juna idanu na tsawon lokaci suna kallon banbancin ajin dake tsakaninsu na yar sarki da dan talaka haka nan zuciyoyinsu na masu fargabar rikicin da suke kokarin jefa kansu hussaina ce tafara ajiyar zuciya ta dube shi tace amma Kanarin nan naka nada kyau ban taba ganin irinsa ba. Saurayin yayi mata murmushin yake ko kina sonsa ne? Hussaina ta gyada kai da murmushi na dade inason nayi kiwonsa agida da zaka bani dana fanshe shi da zinariya. Cikin sauri sai saurayin ya mika mata tsuntsun gashi ranki ya dade nabaki shi kyauta...tsakanina dake babu ciniki gimbiya hussaina ta karbi kanarin cikin mamaki wai shin da gaske kakeyi? Tsakanina dake babu tsokana ko wasa ranki ya dade saurayin yabata amsa. Nagode madalla da wannan kyauta da kayimin da bazan mantawa dakai ba farin cikinki farin cikina ne ranki ya dade hussaina taji dadin abinda yace acikin zuciyarta kace kai mafarauci ne ko? Saurayin ya gyada kai yanzu yaushe zaka koma? Ya sunkuyar dakai yace ni da ason samuna ne ma yanzu zan koma daji da daddare ga mamakin saurayin sai yaga yar sarkin ta sunkuyar dakai cikin damuwa tana jujjuya kyakkyawan kanarin dake hannunta azuciyarsa kanarin ma har yafi dacewa da ita fiyeda ni dubi yadda ta rike shi sai sukayi kyau atare tamkar taurari biyu karama da babba. Dole ne saika koma yau din? Gimbiya hussaina ta tambaye shi. Saurayin ya girgiza kai yace ba dole bane ranki ya dade amman da zan sami yadda nake so danafi son nayi tafiyata yau domin zaman gida shi ke mayar da mutum Rago nikuwa da son samuna ne zanso mu sake haduwa anan bayan kwana biyu saurayin yaji gabansa ya fadi ras tun tuni ya rigaya yasani cewa rayuwarshi tana cikin hadari domin yana tattare da masaniyar cewa kyakkyawar budurwar dake tsaye gabansa yar sarki ce. Kokuwa baka son ka kara gani na ne? Tace dashi cikin rarraunar murya sa'ar dataga ya kasa magana. Cikin sauri sai ya girgiza kai yace babu wanda ya isa yace baya kaunar ya sake ganinki ranki yadade. Hussaina taji wani dadi ya lullube mata zuciya don haka saita dada motsowa kusa dashi tace cikin murmushi zanfi jin dadi azuciyata idan ka kirani da sunana HUSSAINA maimakon ranki ya dade ta danyi shiru tana kallonsa da dara daran idanunta farare masu jirkita hankalin mazajen duniya gashi kuma har zamu rabu bansan sunan wanda yayi min kyauta ba. Saurayin ya dago kai a kunyace bakinsa na rawa ya dubi kyakkyawar fuskar yar sarki yace sunana AMADI DAN ZANGERU. ** ** ****** ****** ******* ******* Zangeru ya dubi MAKWARO acikin hasken farin wata kana yayi kaki ya tofar acikin tarin ciyayin dake dab dasu cikin damuwa na rasa abinda ya hana mai masaba zuwa yace da makwaro lokaci guda kuma ya sake duban yar siririyar hanyar da ta bi ta bayan gidansa har zuwa cikin gari. Meyiyuwa ko sarkin dogarai ne ya hanashi tahowa kafa san shi da shegen surutu Makwaro yace mutanen biyu dake zaune cikin daren suna jiran mai masaba tun kafin shigowar almuru suke gurin domin kowannensu tattare yake da masaniyar cewa yauce ranar da mai masaba zaizo musu da karin bayani na karshe game da gagarumar satar da suke shirin yi. Wannan mutum dake zaune kusa da zangeru sunansa makwaro dan gajere ne mai adi adunqule yana da katon kai kamar murhu haka nan idanunsa yan mici mici ne kamar maciji bakinsa tsukakke ne kamar gidan tsutsa yanada faffadan hanci tababbe wanda ya maye kusan rabin fuskarsa haka nan yasa duk kusan yan matan garin suka tsane shi. Tun makwaro yana saurayi bai tabayin budurwa ba kuma haryanzu nan da yake dan shekara arba'in da daya bashida aure sai tarin muguwar bakar zuciya wacce tasa kusan kullum acikin kunci yake da bacin rai akwai sa'ar ma da shi kansa yake jin haushin kansa da kansa. Tun sa'ar da uwar makwaro ta haife shi tabar duniya mahaifinsa shine sarkin maharban garin harya mutu bai taba kuskuren harbin duk naman dajin daya sa agaba ba sai sau daya jal. Shi ma wannan hannunsa ne yake ciwo duk wani salon harbin kwari da baka na mahaifinsa saida makwaro ya haddace shi harma yafi mahaifin nasa kwarewa ance wai saboda tsabar iya harbinsa ko dan yatsa ka daga masa zai iya harbar iya harbinsa babu kuskure wasu sukace wai ko kurciya ce tazo wucewa ta sama idan yaga dama yana iya harbin tsinin bakinta batareda ya kuskure ba ance kuma wai wani shakiyin kauye yataba cewa da makwaro in har ya isa mai iya harbi to ya bari sai kakansa ya hau saman bishiya saran itace makwaron yasa kibiya ya harbi saman hancin tsohon amma kada jini ya zuba sosai haka kuwa akayi makwaro ya harbi tsinin hancin to saidai kuma abin yazo da ajali domin tsohon ko kwana baiyi ba yace ga garinku nan. Wannan da kuma wasu dalilai na kwarewar makwaro a fagen iya harbi su suka sa zangeru da mai masaba suka zabe shi amatsayin cikonsu na uku a shirin wannan gagarumar sata da suke shirin YiZangeru ya riga ya dade da sanin cewa makwaro ma kwararren barawo ne to saidai kuma shi ma kamar su har yau satar bata tsinana masa komai ba. Don haka sa'ar da zangeru ya tunkare shi da batun satar sai makwaro ya kada baki yace Daman kullum fatana kenan nayi gagarumar satar da duk labarinta zai watsu aduniya wannan shine halin makwaro har kullum yafison neman suna fiye da neman Abin duniya. Mutanen biyu sukaci gaba da zama cikin duhun dare fuskarsu sai naso take da gumi kamar waina kowannensu na sakar zuci. Ko jirana zakayi anan nabi bayansa? Zangeru yace da makwaro. Makwaro ya mirgina uban kansa mai kamar masaba yace kaji kamar motsin tafiya ma nake ji ko...? Mutanen biyu sukayi fakare suna saurare kamar zakaru tabbas sautin tafiyane ba'a dade ba kuwa sai suka hango zabgegiyar surar mai masaba acikin dan hasken farin watan yana tafe cikin sauri. Inda su zangeru suke zaune kusa da wata tsohuwar rumfa ce data gaji da tsayuwa ta fadi shekara da shekaru an rasa mai dogara mata ta tashi adacan zamanin wani tsohon sarki fatake ne ke hutawa acikin rumfar kafin su shiga gari. Lokacin da mai masaba yazo wucewa ta kusa dasu baigansu ba domin shi duk tunaninsa agida su zangeru zasuyi jiransa yana zuwa dab dasu sai yaji muryar zangeru tace Gamu nan tun dazu kai muke jira. Mai masaba yayi turus sannan ya juua gamida kashe idanu acikin dan hasken farin watan sannan ne to ya hangi mutanen biyu kamar aljanu rakube abayan tsohuwar rumfar ya matsa kusa dasu kana ya saki wani tattausan murmushi sa'ar da ya hangi katon KAN MAKWARO. Ashe kune anan mai masaba yace sannan ya zauna kusa dasu. Ya ya ake ciki bamu labari tun almuru muke nan makare muna jiranka har na fara shawarar binka ma mai masaba ya wangame baki kamar kada yayi wata doguwar hamma sannan ya dubesu yace Samun labarin babu wuya domin tun dazu mutumin namu sarkin dogarai yazo da fadawa daukar akwatin dama tun kafin yazo nasa an dama fura na ajiye masa yana zuwa na mika masa yana shan furar nan sai ya fara zuba kamar ruwan sama ni ko daman bugun cikin nasa ma banyi ba har saida ya amayar min da komai. Ma masaba ya danyi shiru yana susar kugu dan tsawon lokaci sannan saiyaci gaba da cewa Acewar sarkin dogarai su shida ne zasu raka akwatin kuma jibi da daddare bayan isha'i zasu tashi to saidai kuma akwai wani abu dake tattare da tafiyar wanda mu bamuyi tsammaninsa ba. Mutanen biyu suka dubi ma masaba sa'ar dayayi shiru kamar me kenan kake nufi zangeru ya tambaye shi. Mai masaba yayi atishawa yace akwai Yara guda biyu matasa ya'yan sarkin da su za'ayi tafiyar. Mai masaba ya dubi zangeru sa'ar daya fafi batun. Akaro na farko sai makwaro ya girgiza katon kansa yace menene abin damuwa don zasu tafi da wasu matasa basai nayi maganinsu ba ni abunda kawai yafi damuna shine idan mun kwace akwatin a ina zamu boye kafin kura ta lafa kunsan fa da zarar munyi nasara duk hankalun sarakunan yankin nan zasu tashi musamman ma aminan sarki sabitu bincike na farautar mu zai tsananta kafin kura ta lafa. Jin haka sai zangeru ya dubi mai masaba yace makwaro fa yazo da babbar magana me kake gani za'ayi mai masaba ya dube su yace ai wannan mai sauki ne ni daman tuntuni na gama tunanin wannan matsalar harma na gama maganinta azuciyata menene to maganin matsalar suka tambaye shi baki daya cikin doki. Mai masaba yakaiwa kakkauran wuyansa duka da tafkeken tafin hannunsa sa'ar da wani kwaro ya fara safa da marwa akan dogon wuyansa. Ni abinda nake gani shine me zai hana idan mun kwace akwatin mu koma da ita cikin katon kwarin nan dake kusa da fadamar damasu wacce ke makwabtaka da gandun sarki sai mu haka rami mu binneta agurin gindin wata bishiyar giginya. Yana fama din haka sai zangeru ya fashe da dariya bakada hankali mai masaba in ba hauka ba me zaisa mu saci kayan sarki mu rasa inda zamu boye shi sai akusa da gandunsa Mai masaba ya dubi zangeru shekeke yace abinda yasa nace mu binne akwatin anan shine idan bincike ya tsananta babu wani mutum daga cikin baradan sarki da zai tsammanin za'a boye akwatin a gurin nasan da zarar mun kwace akwatin duk hankula zasu koma ne kan garuruwan dake makwabtaka damu wannan shine dabarata. Zangeru ya dubi makwaro Makwaro ya dubi zangeru sannan sai suka gyada wa juna kai mai masaba ya dubi mutanen biyu yayi murmushi ina fatan kun fahimce ni mutanen biyu suka gyada kai sannan ne to zangeru yace ka tambayi sarkin dogaran hanyar da zasu bi tajikin duwatsun zangura zasu bi daga nan sai su yanke ta mararrabar kudu domin wai haryanzu zatafi musu sauri zangeru ya gyada kai sannan sai yadubi makwaro yace makwaro sarkin harbi wacce irin shiga kake ganin zamuyi musu makwaro ya mirgina uban kansa yace abinda zamuyi sai mu zagaye su ku sai ku tare su ta gaba nikuma na boye abayan duwatsun daga sun bullo sai ku farayi musu ruwan kibiya idan sun fara mayar.....Makwaro ya mirgina uban kansa yace abinda zamuyi sai mu zagaye su ku sai ku tare su ta gaba ni kuma na boye abayan duwatsun daga sun bullo saiku fara yi musu ruwan kibiya idan sun fara mayar da martani saina fito ta bayansu na fara harbo su daya bayan daya har sai na kare su. Zangeru ya dubi katon kan makwaro yace yaya kuma zamuyi da yan kyawawan yaran nan ya'yan sarki? Mai masaba ya bude baki zaiyi magana kenan sai makwaro yayi farat yace banace daku zanyi maganinsu ba? Zangeru yaji zuciyarsa ta harba idan har akwai abinda yaki jini shine kisan kyawawa yawun bakinsa ya kafe sa'ar daya tuna da irin tsabagen kyawun yar sarki gimbiya hussaina. Me zakayi musu? Makwaro ya dubi zangeru da fuskar katako yace KASHE SU ZANYI don babu ruwana da kyawunsu HUDU 4 Yau kwana biyu kenan daidai tun bayan haduwar Amadi da gimbiya Hussaina haka nan itace ranar datayi daidai da alkawarin sake haduwarsu abakin fadamar kamar yadda hussaina ta bukata. Lokacin da hussaina ta isa bakin fadamar sai tayi mamaki sannan ta tsunduma cikin damuwa domin ta dauka zata zo ta tarar da Amadi awurin zaune yana jiranta maimakon haka saita iska tsuntsaye burjik abakin fadamar sunata kai kawo abinsu suna wakoki cikin muryoyi iri daban daban da masu dadi da masu ban haushi kaikace bikin yar sarkin tsuntsaye akeyi. Gimbiya hussaina tayi tsaye bakin koramar tana yan waige waige amma babu ko motsin Amadi cikin damuwa da tunanin fargabar mai yiwuwa ma bazata sake ganinsa ba saita nufi dutsen nan data same shi wancan lokacin zaune akai ta zauna sannan ta zubawa tsuntsayen dake bakin koramar idanu bata ko kiftawa gashi dai a zahiri idan ka dubeta kamar tsuntsayen take kallo amma a badini basu take kallo ba babu abinda zuciyarta ke ayyana mata sai kyakkyawar surar dan saurayi AMADI Gimbiya hussaina ta tuno da daren jiya ta tuna da cewa koda daidai da barcin sa'a guda baizo idanunta ba tun sa'ar da suka rabu da kyakkyawan saurayin ta koma gida saita kasa zaune ta kasa tsaye. Meke damunki ne ? Hassan dinta ne ya tambayeta sa'ar da suke zaune tare dashi bayan almuru Gimbiya hussaina ta duni dan uwanta hassan saita rasa me zatace dashi. Domin ita dai tasan har suka rabu da saurayin babu wata bayyananniyar magana agame da soyayya data shiga tsakaninta dashi to amma kuma zuciyarta tarigaya tasan ta kamu da ciwon son wannan kyakkyawan saurayi. Ada can wani lokaci idan hussaina tana karanta labaran soyayya acikin littattafan larabawa takan ga wautar mata da suke nacewa akan son da' namiji domin aganinta wautace kawai. Yaushe ne ma za'ace kamar ita yar sarki ta kamu da ciwon son wani mutum talaka wanda shi bai ma damu da ita ba. Amma ayanzu da yake hussaina ta tsinci kanta acikin irin wannan yanayin saita fahimci ashe dai matan nan data sha karanta larabansu acikin littattafan larabawa basuda laifi ashe daman haka SO yake kamar Sartse. Kwanaki biyun da hussaina ke jira su zo sune mafiya tsayi data taba gani arayuwarta domin washe garin ranar da suka hadu da amadi sau daya tak ta sami damar cin abinci koda tasa abincin ma abakinta saitaji babu dadi kamar tana cin danqo haka nan duk sa'ar data tuno da Amadi saitaji zuciyarta na harbawa Gimbiya hussaina taci gaba da Allah Allah gari ya sake wayewa kota sake dora idanunta akan Amadi rana ta fara haske amma hussaina gani takeyi kamar ma yamma bazatayi ba aranar ballantana kuma har gari ya waye ta sami ganin Amadi da aka jima ta fahimci kamar ranar batayi mata sauri sai kawai ta koma daki ta kwanta da zummar wai bazata farka ba sai Magariba. Lokacin data farka saitaji lokacin ne ake kiran sallar azahar. Abubuwan suka taru suka dagule mata. Zuciyarta tafara bata shawarar me zai hana idan bazata iya daurewa ba ta dauki kuyanginta su rakata har gidansu Amadi mana ai kuma abin kunya ne ace yar sarki tabi talaka har gida wata zuciyar tace da ita. Don haka ayanzu da hussaina ke zaune akan dutsen tana jiran isowar amadi cikin rashin tabbaci saita yanke hukuncin cewa inhar aka jima baizo ba ko shakka babu gida zata bishi ta dan zame kadan daga kan dutsen da take zaune sannan ta zura kyawawan kafafunta cikin fadamar ta fara wasa da ruwa adaidai wannan lokacin ne taji motsi abayanta. Kiyi hakuti ranki yadade Allah huci zuciyarki na ajiyeki zaman jira wata sassanyar murya tace daga bayanta. Hussaina taji wani irin dadi ya mamayi zuciyarta cikin farin ciki ta juyo gareshi da tattausan murmushi akan jajayen lebbanta sannu da zuwa Amadi ina fatan dai lafiya? Amadi ya dube ta da murmushi ya gyada kai lafiya lau ranki ya dade wallahi mahaifina ne ya tsayar dani. Hussaina ta lumshe idanu cikin farin ciki ni da na dauka ma bazaka zo ba. Amadi ya girgiza kai cikin gaggawa haba ranki yadade ni na isa kiyi kirana naki zuwa...saboda tunanin alkawarin nan naki ko cikakken barci banayi Saboda me? Ta tambaye shi Amadi ya sunkuyar da kai kasa na tsawon lokaci bai amsa ba sannan daga karshe sai ya dago kai yace Saboda da zarar na rufe idanuna sainayi ta ganin surarki ranki ya dade... Gashi kuma tunanin kirkin ki da karamcinki ya kasa barin zuciyata. Hussaina taji dadi ya sake mamayar zuciyarta akaro na biyu ta dago kai ta dube shi ido da ido tace Amadi wannan shine kawai abinda ya hanaka bacci ko kuwa akwai wani abin daban? Amadi ya dube ta cikin rashin fahimta yace ban fahimce ki ba ranki yadade hussaina ta sunkuyar da kai awannan karon kana saitace cikin wata rarraunar murya Ni kuwa Tunaninka da Kaunar ne suka hanani barci. Zuciyar amadi ta harba tsakanin hakarkarinsa kamar zata huda ta fito bai taba tsammanin zata fito fili ta bayyana masa kaunar tata agare shi ba. Ranki ya... Amadi yayi shiru bai karasa ba sa'ar da yaga hussaina ta daga masa hannu. Hussaina sunana ina fatan ranki ya dade din nan zata fita daga bakin ka tayi murmushi sannan saita matso kusa dashi tace Fadamin da bakinka Amadi kana SO NA. Amadi yaji zuciyarsa ta yankwane aguri guda ko shakka bayayi yasan yana kaunarta domin shima abinda ya hanashi barci kenan adarare biyun da suka wuce to amma shi yasan wannan soyayya dake kokarin faruwa tsakaninsu tamkar siyayyar mafarki ce domin inashi ina yar sarki? Ranki ya... Hussaina.... Tun sa'ar dana fara dora idanuna akanki naji ina kaunar ki yo amma ni na rigaya nasan ni ba zan taba samun ki ba domin babu hadin dan talaka da dan sarki kada kace haka amadi domin kai bakasan gaibu ba...in Allah yaso kaine mijina Amadi. Ta sunkuyar da kai azuciyarsa yace Kai lamarin duniya da ban mamaki kaji kai yarinya saboda shaukin soyayya tana sambatun almara. Daman abinda yasa nace dakai inason mu sake haduwa anan domin muyi sallama ne kasan jibi zamu bar garin nan nida dan uwana hassan. Amadi ya dubeta cikin mamaki wane gari zaku koma? Wajen babban aminin mahaifinmu za'a mayar damu sarki Lurwanu nasan me yiwuwa kasan garin tunda kai mafarauci ne Amadi ya gyada kai kwarai kuwa nasan garin domin wazirin Lurwanu yasa fansar fatun damiwa agurina. Gimbiya hussaina tayi ajiyar zuciya jin cewa yasan garin idan kana ganin ba takura zanzo kabini garin amma kabari har sai mun sauka agarin da kwana biyu idan kaje zan tare ka abayan gari ko yaya ka gani? Amadi ya gyada kai a tsorace yace duk abinda kikace haka za'ayi HUSSAINA TA. Hussaina ta dube shi cikin tsananin farin ciki tace Nagode AMADINA duk duniya banida na biyunka cikin ruhina. Amadi yayi ajiyar zuciya gamida duban tsuntsayen dake jejjere abakin koramar yanzu yaushe zaku tafi? Jibi warhaka muna shirin tafiya domin da almuru zamu tafi In Allah yaso zan same ki abayan garin kamar yadda mukayi alkawari. Gimbiya hussaina ta cire wani kyakkyawan zoben azurfa dake dan yatsanta ta mikawa Amadi. Ga wannan ka ke tunawa dani kafin mu sake haduwa ni kuma zan tafi da kanarin daka bani cikin keji ya isheni debe kewa tunda dai kyautarka ce. Matasan biyun suka kurawa juna idanu suna murmushi domin basu son rabuwa da sun lura da kyau zasu hangi wata farar balbela daga can cikin tsuntsayen bakin fadamar tana kallon su cikin Tsananin mamaki da Kaduwa. ** ** ** ** ** ** ** Lah. Kaga dogayen duwatsun nan da baba yasha bamu labari hussaina tace da dan uwanta hassan cikin doki lokaci guda kuma ta mike hannunta daga kan dokin ta taba dutsen da kyawawan yatsunta. Hasssan ya dubi dutsen a yatsine sannan ya dubi yar uwar tasa hussaina yace kinga nikuwa babu abinda na tsana a rayuwata irin dogayen duwatse. Meyasa? Hussaina ta tambaye shi gamida murmushi domin ta riga tasan tafi dan uwan tagwaitakar tata jarumta. Kawai dai ni banason ganin dogayen duwatsu ne banayi wata sa'ar dai inga kamar mutuwa ce ke kokarin zuwa ta zare ni musamman ma a irin wannan lokaci na Duhu. Hussaina ta bushe da dariya kaidai wallahi matsoraci ne in ba haka ba kataba ganin an gujewa mutuwa? Ai duk inda kwananka ya kare ko a kan duwatsu ko acikin fadar babanmu sarki ko acikin duhu ko hasken rana sai mutuwa ta riske ka domin idan tazo babu tsimi babu dabara. Hassan ya dubi yar uwarsa da murmushi cikin duhun daren wannan gaskiyane yar uwata Hussaina. Sarkin dogarai dake daf dasu yayi murmushi acikin duhun daren sa'ar dayaji hirar dake gudana atsakaninsu sannan kamar yadda ya saba fadi akullum cikin zuciyarsa yanzu ma sai yace INAMA ACE 'YA'YANSA NE. Sarkin dogarai ya juya baya ya dubi yan rakiyar tasu mutum shida kowannensu cikin shigar yaki dauke da kibai masu dafi suna tafe suna sa kakkafar dokin da aka dorawa akwatin dukiyar atsakiya wata sa'ar ko motsin ganye sukaji sai sun juya da shirin kai sara kamar MACIZAI. Duk da wannan shiri da barazana da sukeyi basu taba tsammanin wani abu makamancin fashi zai faru akansu ba domin sunyi imani da cewa duk wani barawo dake hanyar yasan da irin jarumtar ta baraden sarki a tunaninsu babu mai iya tunkararsu da wata barazana. Mutanen duniya basuda tabbas suna iya baku mamaki sarkin dogarai Hambara yace dasu sa'ar da zasu baro gida. Wannan shi yasa baraden yan rakiya daukar takubba sabanin kwari da bakan da suka dauka tun farko acan gefe guda kuma bayan....Wannan shiyasa baraden yan rakiya daukar takubba sabanin kwari da bakan da suka dauka tun farko. Acan gefe guda kuma bayan duwatsun cikin duhu makwaro ne zaune yana dana kibiyarsa ta farko wacce da itace yake fatan mika sarkin dogarai lahira tare da sauran jama'arsa. Acan kuma karshen duwatsun sarkin barayi zangeru ne shida abokinsa sarkin makera da barayi mai masaba sunyi kwanto suna jiran karasowar tawagar ayarin tun farkon shigowar almuru suke nan makale har sun fara kosawa saboda tsabar rikon kibiyar a dane har hannun zangeru ya fara gumi suna nan makale lokaci kuma suna makyarkyatar sanyin asuba da yafara hurowa wata sa'ar jikinsu har buguwa yake dana juna kamar zakarun da ruwa ya jika. Adaidai wannan lokacin ne suka jiyo motsin

Chapter 3 of 8