Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
daki ke kadai sannan ki cire layar dake makale a wuyanki ki warware ta domin akwai wani tsohon sako na kakanki ne na can baya ya barwa wani daga cikin 'ya'yansa amma basu sami damar budewa ba domin sun dauka layar maganin tsautsayi ce abinda basu sani ba shine layar ba maganin komai bace sako ne aka rubuta aciki tun tsawon shekaru dari da ashirin din da suka wuce sakon yana rufe har yau inason ki warware layar ki karanta sakon da yake ciki domin arzikin ki yana cikin layar a nannade. . Farar balbelar tayi shiru tana duban aisha wacce hannayenta biyu ke dake da layar dake makale a wuyanta aisha naga kamar kina shakkar abinda nake cewa inason yanzun nan ki warware layar agabana ki karanta koda sidira biyu ce domin ki tabbatar da abinda nake fada miki. Cikin rawar jiki sai aisha ta ciro layar dake wuyanta ba wai don tayi imani da abinda balbelar ta fada ba sai don a tunanin ta idan taki bin umarnin aljanar mai siffar balbelar zata iya hallakata cikin abinda baifi mintuna biyu ba aisha ta warware layar da kyar tana gumi sannan ahankali kamar mai yin tiyata saita fara warware rubabbiyar takardar ba'a dade ba ta warware layar baki daya sannan ne to ta dubi wasikar cikin kaduwa da kuma mamaki rubutun wasikar da Ajami na larabci akayi shi bada rubutun hausa ba aisha ta dago kai gumi sai zuba yakeyi kamar ruwa aisha ta dubi balbelar a rude rubabbiyar takardar rike a hannunta. Balbelar ta karkada fiffike cikin lalaci karanta farkon wasikar aisha kafin kije gida ko kya dada gaskatani Aisha kafin ta dawo da idanuwanta kan rubabbiyar takardar dake kokarin rabewa gida biyu sannan ta kurawa kananan rubutun idanu ta fara karantawa kamar Haka. . DAGA SARKIN BARAYI ZANGERU. Zuwa ga Dana AMADI kafin in sanar dakai komai inason kasani cewa tunda nake a rayuwata ban taba tsinana wani abin kirki arayuwata ba sai SATA. Ya isa haka nan Balbelar ta katseta sannan tayi girgiza har sau uku wani dan kankanin dutse fari mulmulalle ya fado daga bakinta. Dauki wannan dutsen aisha na san nan bada dadewa ba zaki bukaci ganina idan bukatar ganin nawa ta taso saiki murza dutsen har sau uku atafin hannunki zaki ganni na bayyana. . Aisha ta durkusa ta dauki dutsen jikinta na rawa ta jefa shi cikin jaka sannan saita dago kai zata dubi balbelar. Gaban Aisha ya fadi domin bataga komai ba ko sama ko kasa balbelar ta bace sai famfon nan mai tsiyayar ruwa. Mafarki nakeyi? Aisha tace muryarta na rawa sannan saita leka cikin jakarta haryanzu farin dutsen nan na nan. . ** ** * ** . SHIDA SHAFI'U ya kurkuda ta tsakanin tarin motocin cikin sauri ya nufi inda motarsa take ya bude kofar motar kafafunsa a kasa ya zauna akan kujerar gaban motar sannan ya dubi agogo cikin damuwa. Me ya tsayar da aisha ne? Ya tambayi kansa ko shakka bayayi lokacin tashinta yayi kuma ya tabbata tanan aisha zata zo wucewa shafiu ya lalubi aljihun wandon cikin damuwa ya dauko naira darin karshe data rage masa ya fara jujjuta ahannunsa sannan sai ya shigar da kafarsa daya cikin motar ya jingina kansa da majinginin motar kana ya lumshe idanu yana kulle kullen zuci kulle kullen da yake fatan zasu kaishi ga dora hannunsa akan makudan kudin da yake fatan ya taimaki aisha dasu. . Wannan saurayi shafiu dogo ne kyakkyawan gaske wankan tarwada mai kyawun fatar jiki yana da tarin gashin gira haka nan kuma yanada tarin gashin kai duguzunzum kamar kayar bushiya . (NAZIR ADAM SALIH WANNAN SIFFA TA SHAFI'U DAKA ZAYYANO SAIKACE PHOTO COPY DINA ? NIMA HAKA NAKE SAK SAIDAI DAN BAMBANCI DAYA KATON KAI DA KARKATACCEN HANCI HAHAHAHAHAH) . Wata sa'ar idan ta rayawa shafiu sai ya runa gashin ya mayar dashi fari fat kamar gashin tunkiya wannan shi yasa dayawa daga cikin abokansa na gida dana jami'a suke kiransa da suna sisko duk wannan bata dami shafiu ba domin tunda aka haife shi aduniya ya fara wayo akidar samarin Amurka ta shiga zuciyarsa yasha cewa wai shifa da akai shi Makka yayi sati guda wai gara akaishi Amerika yayi sa'a guda shafiu sisko yasha bakin cikin jin cewa an taba zuwa dashi amurka amma alokacin yana goye abayan mahaifiyarsa duka duka baifi shekara guda ba aduniya. Wannan Al'amari yana matukar bakantawa shafiu sisko domin yasan a yanzu ko mahaifinsa bai isa ya kai kansa amurka ba ballantana ma har atafi da shi banda irin wannan akida rayuwar turawa kuma shafiu yana da hali irin na kuruciyar bera tun yana karami dan shekara biyar yake dan dauke dauken kananan kudi har dai takai yafara yin manya manya to saidai kuma wani abin mamaki tun da shafiu ya fara yan sace sacensa bai tabayi awaje ba saidai agidansu. . Watarana mahaifiyar shafiu HAJIYA KARAMA ta taba cewa da mahaifinsa....Watarana Mahaifiyar shafiu HAJIYA KARAMA Ta taba cewa da mahaifinsa yanzu ashe Alhaji haka za'a zubawa yaron nan idanu yanata yin wannan mugun abun? Ki godewa Allah da ba wasu yake daukarwa ba kudina ai nasa ne kibar shi yayi abinda yaso watarana bazaiyi ba mahaifin shafiu ne yake cewa da ita haka tun daga ranar nan bata kara maganar ba domin tasan mahaifin shafiu na matukar kaunarsa ko kadan baya bukatar wani abu ya taba shafiu kamar wata kwayar idanu. . Sannu ahankali sace sacen shafiu suka fara bunkasa domin idan ya rasa kudi sai ya dauki kananan kadarori yana sayarwa duk kuwa da cewa akullum kwanan duniya sai mahaifinsa yabashi kudin kashewa kudi basu taba isar shafiu ba domin almubazzarine na gaske jama'a dayawa basuyi mamaki ba domin shafiu bashida wata harka sai ta mata shafiu kwararrene wajen yaudarar yan matan zamani ance a tarihinsa ba'a taba ganin macen dayasa agaba ta gagare shi ba domin yanada baki da iya lafazi mai dadi da jan hankali gashi kyakkyawa hakanan mace ko da jimina ce sai shafiu ya taba duk irin kudin da take bukata. Ana cikin wannan hali ne kwatsam rannan sai shafiu ya dora idanunsa akan aisha tun ranar dayaga aisha zuciyarsa ta kasa samu hutun tunaninta shafiu yayi imani da cewa duk sa'a guda sai yayi tunanin Aisha sau ashirin da biyar gamida manya manyan faduwar gaba guda UKU. Aisha itace mace ta farko da shafiu yaji yana kauna harga Allah cikin zuciyarsa badon komai ba sai don wasu abubuwa guda uku na farko dai shine duk sa'ar daya dubi Aisha saiyaji duk tausayinta ya kamashi kuma ko kusa ko alama baya son yayi mata wani zance irin na yaudara da sakarci kamar yadda ya saba yi da sauran matan dayake mu'amala dasu. Na biyu shine tunda yake bai taba ganin mace mai kyawun dake sa gabansa faduwa ba sai Aisha domin aduk lokacin daya dubeta sai yaji zuciyarsa na harbawa jikinsa ya dauki rawa yawun bakinsa ya kafe wata sa'ar ma har gumi ne ke karyo masa. Abu na karshe kuma dayasa shafiu yake mutuwar kaunar aisha shine fatali da halin ko in kula datakeyiwa al'amuransa. Shafiu ya lura da cewa aduk lokacin da aisha tazo wucewa takusa dashi bta ko daga kai ballanta ma ta dube shi sabanin sauran mata wadanda ko basu dube shi don kyawunsa ba sa dubeshi don sunansa da kuma tsabar farin jininsa agurin yan mata mawu ra'ayin rayuwar turai wata jita jitar ma nacewa aduk inda ka zagaya aciki idan ka sami goma ka tambaye su wanene shafiu sisko takwas daga cikinsu zasu sun sanshi domin ko da bai taba kawance dake ba tabbas yayi kawance da kawarki ko kuma da kawar kawarki to amma duk da wannan suna nasa Aisha bata dauke shi abakin komai ba hakanan ko da ya gaisar da ita ma yayi da kyar take amsawa. Wadannan abubuwa su suka taru suka tsunduma shafiu acikin tekun begen aisha wanda ayanzu da yake zaune cikin motar yana jiran aisha sai ya fahimci tekun begen yayi masa muguwar jikawar da duk wata mace ma ayanzu baya kaunar magana da ita sai Aisha. Ayanzu da shafiu yake zaune cikin motar yana jiran isowar aisha zuciyarsa tana cikin tsananin damuwa domin yan kananan kadarorin dayake dauka yana sayarwa duk sun kare haka nan kudin da mahaifinsa yake bashi aduk kwanan duniya sun yanke domin shi kansa mahaifin nasa yana bukatar addu'a sakamakon karayar arziki taban mamaki data same shi ayanzu haka idan ka dauke motoci biyu da gidan da suke zaune aciki gami da wani dan mitsitsin kango da samari yan duniya ke shaye shaye aciki mahaifin nasa bashida komai sai tarin furfura aka samakaon yawan tunani da bakin cikin karayar arziki. Shafiu ya riga yayi rantsuwa cewa duk hanyar da zaibi yayi kudin da zai baiwa Aisha don bazai iya ci gaba da ganin macen dayafi kauna fiye da komai aduniya cikin tsumma ba bayan kuma adacan yan iska ma ya kashe musu kudi a banza. Shafiu na kwance agaban motar idanunsa a lumshe can sai yaji kamar ance bude idanunka ka waiga baya shafiu ya tashi zaune sosai ya waiga baya sannan ne to ya hango ta ita da wasu yan mata guda uku sun fito daga dakin karatu sun kama hanyar da zata kaisu gurin shiga motar haya cikin sauri shafiu ya fito daga motar bai ko damu da ya rufe motar ba sai ya nufi inda su aisha suke cikin sauri aisha taji ajikinta dan haka saita dan waiga bayanta kadan Na shiga uku tace cikin zuciyarta sa'ar data ga gadan gadan gurinsu shafiu ya nufo. . Sannu Aisha...har kun tashi shafiu yace da ita sa'ar daya karaso inda suke idanunsa akanta ita kadai suke bai damu daya gaishe da sauran kawayenta guda uku ba hakan shiyasa yan matan ukun dake tare suka wuce gaba kadan suka barshi da aisha a tsaye Aisha ta gyada kai gamida murtuke fuska tace Eh mun tashi kuma sauri nake zan koma gida shafiu ya dubi aisha sai mamaki ya kamashi domin baiga layar nan dake makale a wuyanta ba har yafara tunanin ya tambayeta labarin layar sai kuma ya fasa domin a tunanin maganar dayayi mata dazu ce tasa ta boye layar. Ni zan tafi sai gobe ko aisha tace dashi lokaci guda kuma ta fara ja da baya, in bazaki damu ba bari na dauko motata nakaiku gida naga kamar wahalar mota akeyi Aisha ta girgiza kai cikin gaggawa sannan ta dubi kawayen ta dake can gefe guda tace A'a na gode tare muke da wadancan ba sai in dauke ku gaba daya ba.? Aisha ta dada girgiza kai kayi hakuri wallahi mun gode sannan saita dan juya tace Sai gobe ko shafiu ya goge gumi ya dubeta zuciyarsa a karye yace a sanyaye to shi kenan Aisha Allah ya kiyaye daman so na ke kawai na ganki muyi sallama shiyasa nake ta jiran fitowar ki tun dazu. Koda ya fadi haka sai aisha taji tausayinsa ya kamata akaro na farko a dan takin lokacin sai zuciya tace da ita tsaya koda mintiuna biyar ne ki saurare shi can kuma sai wata zuciyar tace da ita ke rabu dashi sha sha sha yi tafiyarki kawai kada ki saurare shi Iblis ne so yake ya hure kunnuwanki me wannan dan karyar yagani ajikinki da har zaice wai yana kaunarki wannan ita tasa aisha juyawa bayanta tanufi inda kawayenta suke. Koda su aisha suka juya suka nufi gurin shiga motar sai aisha taji ajikinta cewar shafiu na nan inda ta barshi tsaye haryanzu yana kallonta duk da haka bata juyo ta kalle shi ba domin abin dayafi damun zuciyarta alokacin shine maganganun da Aljanar balbelar nan tayi mata da kuma mulmulallan dutsen nan data bata A tunanin Aisha gani takeyi kamar kowane lokaci daga yanzu mulmullen dutsen rikewa zaiyi ya zama wani Katon ALJANIN. ** ** ** ** Sa'ar da aisha ta isa gida saita wuce kai tsaye zuwa cikin dakinta sannan taja kofa ta rufe lokaci guda kuma tasa jakarta agaba ta kuma mata idanu bata ko kiftawa zuciyar ta na wasi wasi shin yanzu zan karasa karanta bayanin wasikar nan ne ko kuwa na bari saida tsakar dare aisha ta tambayi kanta duk kuwa da cewa tayi imani da bazata taba iya karanta wasikar layar da tsakar dare ba tunda dai ta shafi aljanu aisha ta godewa Allah domin lokacin data dawo daga makarantar uwar rikonta bata nan tafi unguwa dan haka babu kowa agidan daga ita sai tattabaru da kaji da kuma wata shegiyar akuya mai kukan tsiya wannan shi ya baiwa Aishat damar shiga daki ta kulle kanta aciki. Tsahon lokaci tana nan zaune tayi tagumi wacce akayiwa mutuwa daga karshe dai sai ta yanke shawarar bari ta karasa karanta wasikar kada taki karantawa tayiwa Aljanar laifi cikin lalaci jikinta na rawa aisha ta lalubo takardar daga cikin jakarta amma bata yarda dutsen nan da aljanar ta bata yataba taba aisha ta warware wasikar sannan taci gaba da karantawa kamar haka. . ......Aduk iya tsayin zamanin danayi ina sata ban tara komai ba da zan iya bar maka gado gashi kuma mutuwa ta rutsani adaidai lokacin danake dab da cimma nasarar sata ta karshe aduniya wacce daga ita ne nake sa ran yin bankwana da sata Amadi inason idan ka gama karanta wasikar nan ka bari sai bayan shekara biyu ka nufi katuwar fadamar nan ta DANMASU dake daf da gandun sarki kabi bangaren arewa zaka ga wata doguwar bishiyar giginya a daf da fadamar idan ka duba kadan daga arewa da bishiyar zakaga wani dan kwari mai kama da lalatacciyar kushewa ina umartakar daka tono cikin ramin zaka sami duk irin dukiyar da kake bukata a zaman ka na duniya ina kuma gargadin ka da cewa da zarar ka dauki dukiyar kayi hanzari ka dauke mahaifiyarka TAGOGORI kubar garin domin zamanku na da hadari matuka. Nine mahaifinka ZANGERU. . Aisha tayi ajiyar zuciya sa'ar data kai karshen wasikar sannan saita sake dawowa da baya ta fara karantawa tun daga farko sannu ahankali har saida ta karanta wasikar sau goma sha uku amma bata fahimci komai aciki ba aisha ta share zazzafan gumin dataji ya fara sartu akan goshinta. . Ina umartar ka daka tona cikin ramin zaka samu duk irin dukiyar da kake bukata a zamanka na duniya. . Kalaman wasikar suka fado azuciyar Aisha shin wacce irin dukiya ce acikin ramin a binne kuma a ina ramin yake? Shin haryanzu dukiyar tana cikin Ramin. Wannan dama wasu sune irin tambayoyin da suka fara kai kawo acikin zuciyar Aisha haka nan kuma tasan duk duniya babu mai bata amsar tambayarta sai Aljanar Balbelar nan mai dogon wuya idan har akwai abinda aisha take tsoro shine tayi kiran balbelar tunanin mulmullen dutsen nan dake cikin jakarta ya fado mata. . Inason ki warware layar ki karanta sakon dake ciki domin arzikinki yana ciki. . Kalaman balbelar suka fara kai kawo acikin kwakwalwar Aisha shin da gaske arzikin nawa ne aciki ko dai Aljanar ce ke son wasa dani Aisha ta tambayi kanta acikin zuciyar ta ai kuwa balbelar tace daya daga cikin kakanninta ne ya rubuta sakon. Aisha taci gaba da cewa cikin zuciyarta . Tunda nake ban taba tsinana wani abin kirki arayuwata ba sai SATA. . Aisha taji gabanta ya fadi sa'ar data tuno daya bangaren kalaman wasikar shin dukiyar da aka binne din ta sata ce? Ta sake tambayar kanta. Aisha na nan zaune cikin rudani zuciyarta kunshe da tambayoyi sama da tasbaha guda duk babu amsoshinsu har zuwa sa'ar dataji an kwankwasa kofar dakinta da karfi Ance. Ke dan ubanki me kikeyi ke kadai acikin daki kamar Boka. Marakiyarta ce keta banbanmin fadan wajen cikin sauri aisha ta dauke takardar wasikar ta cusa cikin jakarta sannan ta nufi kofar dakin ta bude a tsorace ta dubi..Marikiyarta ce ke ta banbamin fada a waje cikin sauri aisha ta dauke takardar wasikar ta cusa acikin jakarta sannan ta nufi kofar dakin ta bude a tsorace ta dubi masifaffiyar uwar rikon nata. . Mama.....sannu da zuwa har kin dawo? Eh na dawo me kikeyi ke kadai acikin dakin? Zauna kenan daga makaranta shine na... Rufamin baki shegiya uwar gulma malalaciyar banza malalaciyar wofi shine wato tun da safe nace kizo ki wanke tsummokaran ki da kayan kikace saikin dawo daga makaranta shine kuma kika dawo kika shige daki abinki ko? To fitowa zakiyi yanzun nan sai kin wanke kayan gaba dayansu in ma bazaki wanke naki ba sai kin wanke nawa. Ba'a fi mintuna biyar ba da faruwar hakan sai aisha ta fito zuwa tsakar gidan tafara wankin tsummokaran kayanta hawaye yana kwarara akan kumatunta sa'ar data dubi kayanta taga duk sun rube sun kokkode gashi kuma kala hudu ma kawai suka rage haka nan kuma babu ranar samun wasu tunanin mahaifanta ya fado mata azuciya duk da cewar sa'ar da suka mutu batafi yar shekara bakwai aduniya ba amma haryanzu tana iya tuno zaman farin ciki tayi dasu a kuma mummunan hadarin daya kawo karshen rayuwarsu ya kuma kawo karshen duk wani farin ciki nata aduniya. . Shekara goma sha bakwai da suka wuce baya yarinya aisha tana gaban mahaifan cikin jin dadi da gata mara misaltuwa. . Mahaifanta Ahmed da saudatu bawasu masu hannu da shuni bane to amma suna da rufin asiri na zaman duniya mahaifin aisha malamin makaranta ne wanda bai dauki duniya da zafi ba haka nan bawan Allah ne nagari ma'abacon tasbihi ga ubangiji akusan kowane lokaci sa'ar dayake raye abokansa na kuruciya sunfi kiransa da A.A domin sunansa daya da mahaifinsa wanda shima sunansa Ahmad ayadda abokansa ke fadi ance wai kakansa ma sunansa Ahmadu acewar su wai sunan ya zamewa iyalin gidansu kamar gado kusan kowa sai ya sanyawa sunan dansa irin sunan mahaifinsa koda kuwa daga bangaren mace dan yafito. Irin wannan al'ada ita tasa mahaifin Aisha addu'ar allah yabashi da namiji domin ya sanya masa sunan mahaifinsa kamar yadda shima akayi masa Allah mai yadda yaso sai yabashi diya mace wacce aka sanya mata sunan AISHA. Wata safiyar talata da safe mahaifin aisha tare da ita sukayi shirin tafiya wani guri domin sadar da zumunci lokacin da suka fito zasu tafine to mahaifin aisha ya lalubi aljihunsa ya dauko wata laya ya mikawa Aisha ungo wannan layar rataya ta a wuyanki maganin tsautsayi ce in dai kina tare da wannan layar in Allah ya yarda babu abinda zai taba samunki na daga tsautsayi aisha ta karbi layar tana dariya ta rataya a wuya alokacin tana karama dan haka saita dinga murna don daman sa'ar da take ganin layar a wuyan mahaifinta tasha kokarin ta rabashi da iya yana Ki. Baba wannan layar a kasuwa ka sayo min? Mahaifin aisha ya fashe da dariya yadubi mahaifiyarta saudatu kinajinmu da Aisha? Wai a kasuwa na sayo mata wannan layar saudatu ta dube shi da murmushi tace Ina ruwan yar baba mahaifin aisha ya dubeta da murmushi sannan ya dafa kanta yace wannan layar gado ce aisha nima mahaifiyata ce ta bani ita tun ina karami kamarki ki riketa da kyau kada ki jefar da ita kinji Aisha? Idan wataran kin sami 'ya kema saiki bata. Hakanan dayace da Aisha saiyasa lokacin da suka shigo mota suka fara tafiya sai sukaga maimakon aisha ta rataya layar a wuyanta saita makalata a wuyan YAR TSANARTA mahaifan aisha suka fashe da dariya sha sha sha ba yar roba nake nufi ba mahaifinta yace da ita cikin murmushi wannan shine ya zamo murmushi na karshe da zaiyi agareta domin awannan tafiyar ne kafin su kai garin da zasu suka yi hadari babu wanda ya shura acikin motar sai AISHA An sami aisha agefen motar zaune da layarta a wuya da yar tsanarta ahannu tana kuka Aisha bata gaji wani abin kuzo ku gani agurin mahaifanta ba inka dauke tsohon gidan mai kamar makabarta da suke ciki sai tarin litattafai da layar dake wuyan aisha gamida kudin mahaifinta naira dubu uku da dari biyar aisha bata gaji komai ba agurin mahaifan nata sai hakuri da hankalinsu. . Bayan anyi sadakar bakwai sai HAJIYA KANDE wacce kanwace agurin mahaifin aisha ta bangaren uba haka nan kuma mace daya jal data rage acikin yan uwansu na kurkusa ta dauki Aisha. Wannan mata Kande masifaffiya ce haka nan aka haifeta da masifa kuma tanajin dadin masifa dan ance wai sa'ar da tana budurwa a kullum sai anyi fada sau goma da ita arana lokacin data dauki aisha ta daukane akan dole ba don taso ba sai dan tana gudun maganganun jama'a domin ita kadaice mafi kusanci da aisha acikin danginsu da suka rage a doron kasa don haka tun ranar da aisha ta shiga hannunta tafara gallaza mata kullum saita jibgeta kamar ganga wata sa'ar ma har kan ruwan cikin aisha take hayewa tayita duka gata da nauyin tsiya kamar Alhaki ance sau biyu tana sumar da Aisha kafin ta zama budurwa. Aisha tana yar shekara goma sha biyar Kande ta sayar da tsohon gidan data gada. Bazan iya wannan jaraba ba kullum sai na saya miki abinci gaki da cin tsiya kamar gara to ga gidanki nan na sayar kudin nake saya miki abinci da sutura da kuma daukar nauyin karatunki in ma kin cinye kudin ki ne. Kande ce ke ta wannan masifar sa'ar data sayar da gidan sannu ahankali Kande ta cinye kudin Aisha kakaf. . Don haka ayanzu da aisha take durkushe tana wanki tana kuka tana tuna rayuwar da sukayi da mahaifanta bata da komai aduniya sai wannan layar dake wuyanta da kuma tsummokaran kayan ta kala biyar da Dankwali biyu duk ya kode yan tauye ya zama dan zarere kamar rawanin Maroki. Aisha ta mike tsaye daga kan kayan wankin ta goge hawayen dake sartu akan fuskarta koda aisha ta koma kan wankin saitaji ga mamakinta shafiu ya fado mata arai abin yabata mamaki me yiwuwa ko don ta fahimci ayanzu bata da wani mutum dake kaunar ta adoron kasa idan ba shi ba babu mamaki kuma kodon zuciyarta tana neman wanda zata fadawa sirrin dake cikinta sirrin da duk duniya babu wanda yasani daga Allah masanin komai sai Aisha saikuma Balbelar data bata labarin sirrin. ** ** ** ** Washegari da safe misalin karfe bakwai aisha tafito sanye da kodadden kayanta masu kamar algarara dauke da jakarta a kafada zata tafi makaranta. Lokacin data fito daga dakinta zuwa tsakar gida saita sami Kande zaune tana wanke wanke tana ganin aisha saita mike tsaye a fusace sannan idanunta suka kai ga wuyan Aisha Dan Ubanki ina kika kai layar gadon taki? Aisha ta sunkuyar da kai tace a sanyaye jiya ta fadi a makaranta.... Kafin aisha ta rufe baki ta kifeta da mari Tas Tas har sau biyu aisha ta rufe fuska hawaye ya fara sartu azuciyarta kuma tana cewa Wallahi ko kasheni zakiyi bazan baki labarin layar ba. Shegiya tsinanniya wato saboda kin gama raina ni saida kika jefar da layar nan ko? Adaidai lokacin da wannan ke faruwa ne to wani dan siririn yaro mai kananan idanu ya shigo gidan wai ana kiran aisha a waje Kande ta dubi yaron cikin tsananin mamaki sannan ta dubi aisha domin tunda Aisha take wani saurayi bai taba kiranta ba musamman ma kuma yanzu da sassafe. . Jeka kace tana zuwa kande tace da yaron azuciyarta kuma ta kudiri mugunta domin ta tabbata duk saurayin da zaiga aisha cikin wannan tsummokarar bazai kara sha'awar zuwa gurinta ba Kande ta juya ga aisha tace Sai ki fata kiga wanda ke kiran wani asararrane shima da taya bera bari in banda sakarcin samarin zamani ma menene abin sha'aqa agurinki da har zaizo miki haka da sassafe aisha ta share hawaye batace komai ba saita juya ta nif kofar gidan itama zuciyarta cike da mamakin wanda yazo nemanta da sassafe haka kamar wadda tayi laifi da farko aisha tayi tsammanin ko wata kawarta ce dake nan makwabta wai ita SAFIYA to amma kuma idan Safiya ce ai shigowa zatayi ba turowa zatayi ba. Aisha ta fita kofar gidan zuciyarta nata sake sake tana fita kofar gidan saitayi turus a zaune agaban bakar mota marsandi kofarta a bude sanye da shudin wando jeans da bakar riga damammiya a kirjinta an rubuta 50 CENT kafafunsa sanye cikin wani katon takalmi fari a mulmule kamar tamaula gashin kansa bucu bucu ya rune shi fari fat kamar gashin tunkiya idanunsa boye cikin bakin tabarau SHAFI'U ne yake cin Cingam hannunsa na hagu dauke da karan sigari tanacin wuta. Kirjinsa na harbawa Das Das aisha ta matsa kusa da kofar motar lokaci guda kuma tasa dan yalolon gyalenta ta rufe hanci domin tuni warin hayakin tabar ya fara shake mata makwogoro shafiu ya lura da hakan cikin gaggawa ya jefar da tabar waje yasa kasan takalminsa ya take. Tunda bakya son warinta daga yau har abada na daina shan taba Aisha daka kyauta wa kanka aisha tace dashi cikin damuwa tana dubansa shafiu waya nuna maka gidanmu me kuma ya kawo ka gidanmu? Shafiu ya dubi aisha cikin damuwa yace So da kauna ne yakawoni aisha zuwa gidanku kuma tambaya nayi aka kawoni kinsan ance me san tsuntsu shike binsa da jifa har cikin shekarsa aisha tayi ajiyar zuciya ta sunkuyar dakai akwai alamun damuwa karara a fuskarta Shafiu ya dubi aisha sannan ya tausasa murya bakiji dadin zuwana ba ko? Bakya kaunata ko Aisha? Akwai alamun karaya karara a muryarsa akaro na farko sai aisha ta dago kai ta dube shi ta girgiza kai tace. Ba kai bane bana so Shafiu ni irin dabi'unka ne ke damuna shafiu ya dubeta sannan ya dubi jikinsa cikin tsarguwa. Dabi'una kamar wanne kenan? Fadamin su aisha duk abinda bakya so wallahi nayi miki alkawarin bazan sake yinsu ba har abada dama tuni na riga nayi miki alkawarin daina shan taba ko? Aisha ta dube shi cikin tausayi ko shakka batayi ayanzu tasan da gaske shafiu yakeyi kaunarta yake akwai wani abu a fuskarsa daya tabbatar mata da hakan. . Dubi gashin kanka guduzumzum kalli faratan hannunka zako zako kamar aljani fatar bakinka har dani jan baki dubi irin wannan kwandalelen zobe dake hannunka shafiu Aisha tayi shiru

Chapter 5 of 8