Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KUDI DA MACIJI NAZIR ADAM SALIH 2005 Ebook creator Shuraih usman 2018 Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Nazir Adam Salih KUDI DA MACIJI l-01 NAZIR ADAM SALIH (Nas 2005) KASHI NA FARKO 1884 DAYA Abakin Wata katuwar fadama da misalin karfe hudu da rabin wata ranar Juma'a ta karshen karni na goma sha takwas wasu jinsin tsuntsaye sukayi sahu sahu abakin fadamar suna ta shakatawa abinsu domin kuwa babu abunda ya dame su don basa fargabar a fada musu da yaki ko kuma a kawo musu hari kamar yadda sauran jama'ar gari keta kwanan zullumin kasancewar wadannan abubuwa guda biyu akansu. Da yawa daga cikin tsuntsayen dake bakin fadamar neman abincinsu sukeyi yayinda wasunsu kuma keta wanka abinsu wasu ko sai shawagi sukeyi a gefen fadamar suna kaiwa yan kananan kifaye hari ko Allah zaisa su dace su sami Abinci. Acan gefe fadamar daga yamma wani manomi ya jefar da fatanyarsa gefe guda ya mike tsaye ya share gumi kana ya juya ya dubi matarsa wacce ke ta faman aiki babu ko sassautawa kaikace itace Mijin. Matar ta dago kai ta dube shi a yatsine tace To Uban malalata yanzu fa saikace harga gaji ko? Na dauka tun duku dukun nazo gonar nan bance nagaji ba saikai dakazo da tsakar Rana. Manomin ya dubi matar cikin murmushi haba Tagogori ke kinsan Ai nayi kokari ma da na kawo haryanzu ina noma nifa na rigaya na fada miki bazan iya noma ba gara ki kyale ni akan sana'ata Tagogori ta dubi mijinta a fusace domin tasan abinda yake nufi Oh Amma dai zangeru wallahi kaji kunya yanzu ace mutum ya fifita SATA akan sana'armu ta Gado Noma? Zangeru ya dubi tagogori ya fashe da dariya sautin dariyarsa ya watsu aduk fadin fadamar harda dama daga cikin tsuntsayen dake garin suka tashi a tsorace. Haba Tagogori kin manta da cewa abindana gada kenan tun kaka da kakanni? Ta gogori ta jefar da fatanyar dake hannunta ta mike tsaye sosai ta dube shi kai kasan da tun farko nasan kai BARAWO ne na rantse da Allah bazan fara ma aurenka ba. Zangeru ya sakato datti daga kogon kunnensa cikin murmushi yace kinga kuwa ni a ganina wallahi duk cikin sa'anninki babu wacce tayi dace da miji kamar ke domin ke kadaice kikayi dacen auren Jarumi. Tagogori ta turo baki gaba kamar suda wanene Jarumin? Zangeru ya bugi kirjinsa da karfi yabada wani sauti Fuss tsuntsaye suka sake watsewa ya dubi matarsa Tagogori tace Ni Kuwa aganina babu rago kamar malalacin daya zabi sata fiyeda noma dubi fa ciki ne dani wata biyu amma tun hudowar rana nake aiki haryanzu bangajiya ba. Zangeru ya kurawa matarsa tagogori idanu na tsawon lokaci sannan saiya danki fatanya ya rataya a kafada yace shiyasa nake son ki rabu da wahala amma har kullum inata kokarin nuna miki Annabi kina runtse idanu dubi cikinki ya fara girma amma kullum kina kara cusa kanki cikin wahala ya danyi shiru yana kallonta. Ganin tayi shiru batace komai ba sai yaci gaba. Toni yanzu tagogori in banda abinki ma dan abin nan da zamu samu awannan yar gonar nawa yake? Sanin kanki ne acikin dare guda ina iya tara miki abinda zamuyi shekara guda muna ci amma duk in kin bi kin dami kanki. Tagogori ta sunkuyar dakai tana murmushe kasar dake mammanne ajikin busassun yan yatsunta wadanda tsabar wahala da noma duk ya busar dasu kamar itace. Akwai alamun gajiyawa a fuskarta kuma dayake zangeru ya kura mata idanu ya fahimci hakan. Wannan shi ya kara masa kwarin gwiwar cewa dauki fatanyarki mu tafi gida kinga rana ta tasamma faduwa. Tagogori ta dago kai ta dube shi ranta a bace ta bude baki kamar zatayi magana saita fasa ta dauki fatanya ta saba fatanyarta a kafada. Zangeru ya dubeta da murmushi yace kwantar da hankalinki Tagogori nan da badi zan zama babban attajirin da ba'a tabayin kamarsa ba aduk garinmu yana gama fadin haka saiya juya ya fara tafiya. Tagogori batace dashi kala ba sai kawai ta bishi abaya suka nufi bakin fadamar nan wadda ga Al'ada aduk lokacin da sukazo noma anan suke dauraye jikinsu su sha ruwa kafin su koma gida. Sa'ar da suka kai bakin koramar sai suka tsugunna suka fara dauraye jikinsu sassanyar iskar yammacin dake hurowa daga cikin fadamar ba karamin jefa zangeru cikin nishadi takeyi ba sau da yawa ya gwammace ya wuni ya kwana gindin fadamar yana shan iska da lofe a hannunsa fiyeda ace ya noma daidai da kunya biyu. Adaidai lokacinne to tagogori ta dube shi tace naji dazun kanayin wani mafarki wai kwananan zaka zama babban Attajiri ko? Tayaya to zaka zama attajirin? Da lalaci ko da me? Tayi shiru tana kallon mijinta zangeru wanda ke zaune ya tura kafafunsa biyu cikin fadamar idanunsa lumshe yana sauraren kukan tsuntsaye. Zangeru ya bude idanunsa ya dubeta. Kina shakkar zamana Attajirine? Tagogori tayi dariya a karo na farko. Attajiri fa kace niko naga mutumin da ko kankani bashida son yasha wahala arayuwarsa tayaya zai zama Attajiri? Zangeru ya girgiza kai yace tagogori kenan wato wani lokaci kikan bani mamaki da kike daukata amatsayin rago ko malalaci kada fa ki manta cewa sana'ata tafi karfin rago ko malalaci yadanyi shiru ya girgiza kafafunsa akan ruwa akwai alamar murmushi abakinsa duk kuwa da cewa baifito fili ba to amma tagogori ta lura da hakan. Sau da yawa idan taga zangeru yana irin wannan boyayyen murmushi bata magana domin duk sa'ar da zai fita wata gawurtacciyar sata irin murmushin yake yi. Sannu ahankali zan tabbatar miki da zamana attajiri tagogori ta sunkuyar dakai tace to Allah ya sauwaka. Daga nan basu sake cewa da juna komai ba sai ma'auratan biyu suka cigaba da wanke jikinsu tsahon lokacin suna cikin wannan hali zangeru na cikin tsananin nishadi domin wani sa'ilin shi kadai sai ya daki tsakiyar ruwan da kafarsa ya fashe da dariya Tagogori bata tanka masa ba. Daga inda zangeru yake zaune yana iya hango jerin sahu sahun jinjin tsuntsayen dake kai kawo suna shawagi a saman fadamar kamar jirage a cikin ne to ya lura da cewa akwai wata BALBELA ita kada tana tsaye abakin fadamar. Duk cikin jinsin tsuntsayen ita kadaice batada yar uwa balbelar ta taso ahankali cikin lalaci ta sauka adaidai inda su zangeru suke zaune zangeru ya dubi balbelar cikin murmushi sannan ya dubi matarsa yace tagogori dubi wata balbela mai kyau ta ziyarce mu tagogori ta dubi balbelar shekeke tace na ganta sannan ta dauke kai gefe guda. Yaya naga kin bata rai? Tagogori ta hade fuska tace haka dai ka iya gashi nan yanzu ka rabo mu da aikinmu ka kawo mu bakin fadama muna zaman banza kagani in ba yanzu zaka tafi ba ni kabarni in tafi gida ko kuma in koma gina na karasa sauran aikin dake gabana. Zangeru ya dubi tagogori cikin murmushi kana iya duba balbelar yace bakisan irin yadda nake kaunar tsuntsaye ba ne musamman ma balbelar nan fara mai dogon wuya da jan baki kyakkyawa kai ina ma ace ina iya zama tsuntsaye dana zama Balbela tagogori ta fashe da dariya tace Oh zangeru al'amuranka sai kai. Zangeru ya dubi matarsa cikin nishadi yace Allah kuwa tagogori da gaske nakeyi domin bakiji yadda nake kaunar balbelar nan ba bari mugani yana fadin haka saiya mika hannunsa zai kama balbelar. Ga mamakinsa sai kawai yaga balbelar ta taso da kanta ahankali ta sauka akan cinyarsa nan da nan ya dubi tagogori cikin farin ciki kinga abinda nake fada da miki ko itama balbelar a hannunsa cikin tarairaya dubi tagogori ungo rike min ita zan tafi gida tagogori ta mike tsaye ta dube shi tace kaga idan bakada aikinyi ni inada shi agida sai kawai ta juya zata fara tafiya. Adaidai lokacinne to sukaji kamar daga sama ance "Haba baiwar Allah tunda yace dake ki rike masa ni yana kaunata ba saiki daukeni ba." Tagogori ta tsaya cak kamar an soketa da kibiya ta juyo a razane ko shakka batayi ba zangeru ne ke mata magana ba. Zangeru yaji sautin muryar shi kansa saida abin yasa shi mutuwar tsohuwa zaune abakin fadamar numfashinsa ya dauke ya dubi balbelar cikin tsananin kaduwa ko shakka bayayi balbelar ce ke magana tagogori ta dubi zangeru a tsorace tace bakinta na rawa Wa..ne ne keyi min..magana naji muryar kamar ba... Kai ba? Zangeru ya dubi balbelar dake kan cinyarsa cikin kaduwa sannan ya dubi tagogori 'Nice nake yi miki magana baiwar Allah gani nayi yadage akan cewa yana kaunata ke kuma sai kokarin rabamu kikeyi. Tagogori taja da baya cikin kaduwa tace kiyimin rai baiwar Allah ke kike ganinmu ba mumuke ganin ki ba..wallahi bansan...tagogori ta kasa karasawa saboda tsabar firgita. Kada kiji tsorona domin ba zan taba cutar ki ba tun da mijinki ya ambata yana kaunata abinda nake so dake shine ki daukeni kamar yadda ya umarceki kutafi dani gida domin daga yau har iya rayuwarku zaku kasance tare dani bazaku taba rabuwa dani ba tunda dai kuna kaunata zangeru yayi ta yan maza ya tashi tsaye sai balbelar tayi tsalle ta hau kafadarsa tace zo ki daukeni tagogori tagogori taji kamar an doke kafafunta da gora nan da nan taji juna biyun dake jikinta ya fara motsi kamar zatayi bari tun kafin lokacin haihuwarsa ya karaso. *** *** ******* ****** ****** ****** ******** Adaidai lokacin da duk wannan ke faruwane akayiwa wani tsohon malami gwanin iya bugun kasa iso agidan sarki SABITU wannan malamin tsohone kwarai da gaske kuma babu wanda yasan takamaiman shekarunsa aduniya domin duk garin babu koda wanda yakusan sa'a dashi to amma duk da haka jita jita ne cewa tsohon zaiyi kusan shekaru dari biyu zuwa dari da hamsin aduniya kai akwai ma wani makaryacin baduku agarin dayayita yada jita jitar cewa wai tsohon yakai shekaru dari biyar da tamanin wasu ko suna tunanin ma tsohon malamin ba Mutum bane Aljani ne. To kma dai menene wannan tsohon malami mai suna MALAM DAWAYE shine babban malamin sarki sabitu kuma shi kansa sarki sabitun ya gaji wannan malami ne agurin mahaifinsa sarki MAI KWARANGWAMA. Malam dawaye dogo ne fari siriri sosai ta tankware kamar baka tun daga kansa har zuwa gemunsa babu alamar bakin gashi sai fari tass kamar an shafa masa garin Alli to amma wani abin mamaki girar idonsa guda daya ta bangaren hagu bakace siliq har tana kyalli kodayake wasu shakiyar sunce wai bakin shuni yake sha mata. Lokacin da wannan lamai ya karaso gidan sarki la'asar sakaliya ce sarkin dogarai HAMBARA shine yayi masa iso ya kuma wuce kai tsaye dashi har zuwa inda sarki sabitu yake kwance wanda yau kusan wata guda kenan.. KUDI DA MACIJI - 02 Sarkin dogarai hambara shine yayi masa iso ya kuma wuce kai tsaye dashi har zuwa inda sarki sabitu yake kwance wanda yau kusan wata guda kenan yana fama da matsananciyar rashin lafiya. Malam Dawaye ya durkusa gaban shimfidar sarki yayi gaisuwa sarkin dogarai ya amsa masa sannan sai sarkin dogaran ya mike tsaye zai fice daga dakin domin yabasu guri su gana. Sai sarki sabitu ya dago kai daga kwance ya dubi sarkin dogarai sannan yace cikin shakakkiyar murya idan anyi sallar magariba inason kazo min da SARKIN MAKERA. An gama Allah ya dada ma lafiya da imani sarkin dogarai ya amsa sannan ya fice azuciyarsa yana cewa anya kuwa sarkin nan ba mutuwa zaiyi ba domin ya fahimci kusan kullum a yan kwanakin nan sai sarki sabitu ya gana da akalla aminansa guda uku zuwa hudu kuma duk acikin sirri ficewar sarkin dogarai keda wuya sai malam dawaye ya sake fadawa gaban sarki ya dada gaisuwa sannan yace Allah ya kara ma lafiya da nasara gani. Sarki sabitu ya dubi malam dawaye daga kwance na tsawon lokaci akwai alamun karaya da sallamawa duniya karara akan fuskarsa. Malam dawaye ya fuskanci hakan don haka sai ya sunkuyar da kansa kasa ba zai iya hada idanu da sarkin ba domin sai ya zubar da hawaye tsawon lokaci suna cikin wannan hali daga karshe dai sarki sabitu yace malam dawaye abinda yasa na kirawo ka shine na fahimci rashin lafiyar nan tawa bata tashi bace kuma ba tun yau ba ka rigaya kasan irin muguwar kiyayyar da wazirina DANDUNA Keyimin kasan kuma cewa babu makawa da zarar na mutu shine zai zama sarkinku ya danyi shiru yana mayar da numfashi. Dawaye a kullum na tuna da irin kiyayyar dake tsakanina da waziri dandunawa saina shiga cikin tsananin damuwa domin bansan irin halin da yan kananan ya'yana hassan da hussaina zasu shiga ba wannan shine dalilin dayasa na kiraka domin ka buga min kasa ka gano min irin yadda zasu kasance a hannun azzalumai waziri dandunawa bayan mutuwata. Sarki sabitu yayi shiru yayinda shi kuma malam dawaye ya shafi dogon gemunsa fari tas mai kamar gashin tunkiya sannan ya janyo allon bugun kasar dayazo dashi agabansa ya baza shida hannunsa sannan ya dubi sarki sabitu yace Allah ya baka nasara da lafiya an gama bari mu gani ai wuyar aiki ba'a fara ba. Fuskar sarki sabitu ta washe kadan domin yasan tsohon malamin bai taba bugun kasa an sami wani kwakkawaran sabani ba. Domin a tarihi a kuma iya tsawon lokacin da sarki sabitu yayi yana mulki wannan tsohon malami ya buga masa kasa sau goma sha uku inda duk ya tabbatar masa da samun nasarar yaki. Amma sau daya tak aka sami sabani inda sukayi kare jini biri jini su da Kudawa wannan shine yasa duk wani abu daya shafi kasar tun daga hangen al'amuran da suka shafi yanayin gari zuwa albarkatun noma tsohon malamin ne ke bugawa ya sanar da sarki. Malam dawaye ya dubi allon duban dake dauke da lallausan yashi sannan ya fara zana alkaluman lissafi na duba yana gogewa lokaci lokaci sai ya daga kansa ya girgiza sannan daga karshe sai ya dago kai ya dubi sarki yace. Allah yabaka lafiya da nasara dabarar da kake kokarin yi itace kawai mafita kana son aikawa wani babban amininka dukiya mai yawa domin ya boyewa ya'yanka ko? Sarki sabitu ya gyada kai a tausashe tabbas wannan shine nufina malam dawaye yaci gaba da cewa tabbas wannan dabara ce mai girma domin abayanka waziri dundunawa tabbas shi zai zama sarki kuma abin bakin ciki zai zamo daga cikin manyan azzaluman sakarunan da ba'a taba yinsu a kasar nan ba inason kuma ka sani cewa da zarar ka mutu sarauta zata bar hannun yan gidanku za kuma a cusgunawa yan gidanku da ya'yanka guda biyu hassan da hussaina wanda daga karshe zai zamanto duk sun fice daga gidan sarautar nan baki daya Allah ya kara ma nasara wannan shine abinda na gani. Malam dawaye yayi shiru lokaci guda kuma ya sunkuyar da kai domin ya fahimci cewa hawaye ne ke zuba kamar ruwa daga idanun sarki sabitu shi kenan malam dawaye allah ya hada fuskokinmu a Darussalam sarki sabitu yace dashi. Malam dawaye ya mike tsaye ga mamakinsa sai yaji hawaye ya kubuto daga cikin idanunsa sai ya fara kwaranya akan fuskarsa zuwa cikin farin gemunsa. Malam dawaye ya sake duban sarki sabitu dake kwance wanda tuni har ya rufe idanunasa ya kalle shi kallon da tuni jikinsa yabashi cewa mai yiwuwa shine na karshe sannan ya juya ya fice daga dakin. Ficewar malam dawaye keda wuya sai ga sarkin dogarai tare da sarkin makera sun shigo sarkin makera ya fadi agaban sarki yayi gaisuwa sarkin dogarai amsa masa. Sarki sabitu ya dubi sarkin makera mai masaba yace inason nan da kwana uku ka kera min katuwar akwati ta bakin karfe wacce zata iya daukar zinariya lu'u lu'u da tagulla masu yawan gaske ina kuma son kayi mata hannaye masu karfin gaske wadanda idan anzo dora akwatin abayan doki baza'a sha wahala ba. Sarki sabitu ya saurara kadan yana mayar da numfashi tuni har idanunsa sun fara zubar da ruwa gashi kuma bakinsa sai rawa yake bayan ya dan ya dan huta sai yaci gaba. Inason kuma kayiwa akwatin manya manyan kwaduna guda shida wadanda idan ba anyi da ya'yan makullayen kwadunan ba duk karfin mutum kada ya iya budeta ina fatan zaka iya? Sarkin makera mai masaba ya gyada kai jikinsa na rawa Allah ya dada ma nasara zan iya. Tun dayake arayuwarsa bai taba shiga dakin shakatawar sarki ba sai yau to amma fa ba wai wannan bace tasa jikinsa ke rawa zancen dayaji na zinariya da lu'ulu'u su suka tayar masa da hankali fiye da komai domin duk da yake ya tabbata sarkinsu sabitu mutum ne mai tarin dukiya amma bai taba tsammanin yana da zinare da lu'ulu'u da zasu cika katuwar akwatin bakin karfe ba. Sarkin dogarai yaji bayan rigarsa ya fara jikewa da gumi hakan nan zuciyarsa na ta raya masa cewa ya kamata idan sun fita waje ya tambayi dogarai cikin hikima me yiwuwa ya tsukunta masa dalilin dayasa sarki yake son ayi masa akwatin. Inason kayi mata hannaye wadanda idan anzo dora akwatin abayan doki baza'a sha wuya ba... Kalaman sarki sabitu ne ke kai kawo cikin kwakwalwar sarkin makera mai masaba to wannan na nufin kenan dukiyace sarkin ke nufin aikawa da ita wani guri. Wannan tunani shi ya dada sa jikin mai masaba ya dauki rawa kamar nazari. Nan da kwana uku nake son ka gama kirar akwatin zan tura sarkin dogarai ya dauko muryar sarki sabitu ta sake dukan kunnen sarkin Makera. Nan da nan ya zabura ya dawo cikin hankalinsa azuciyarsa yana cewa irin wannan kuskure shike janyowa mutum yanka agurin sarakai. Ranka ya dade angama insha Allahu nan da kwana uku zan gama sarkin makera ya sake faduwa yayi gaisuwa sannan ya fice daga dakin jikinsa na rawa ficewarsa keda wuya sai sarki sabitu ya dubi sarkin dogarai yace inason ka zabo min amintattu daga cikin mutanenka jarumai kamar mutum shida inason zan aike ku da wasu kaya zuwa gurin babban aminina sarki LURWANU. Sarkin dogarai ya rankwafar da kai cikin biyayya da girmamawa sannan kuma da tausayawa batun yau ba ya rigaya ya fahimci muguwar adawar dake tsakanin sarkin nan sabitu da wazirinsa dandunawa haka nan ya riga yasan da yawa daga cikin fadawan dake gidan sarautar duk dandunawa suke goyawa baya don haka ayanzu da sarki yaceshi ya samo amintattu daga cikin mutanensa baiyi mamaki ba domin ya rigaya ya san cewa tun sa'ar da tsohon sarkin yafadi rashin lafiya goyon bayansa ya raunana agidan sarauta. Allah ya dade da ran sarki angama sarkin dogarai yace wani zazzafan hawaye yayi sartu a kumatun sarki sabitu sa'ar daya dubi sarkin dogarai na gode da biyayyar da kake yi min nasan kai kadaine ka rage mai kaunata daga cikin mutane na shi yasa nake son tattara dukiyata da duk wani abu dana mallaka na daga gwala gwalai zinare tagulla da lu'ulu'u zan zubasu acikin akwatin nan danasa sarkin makera ya keramin ku kai min ita gurin sarki lurwanu zan hadaku da ya'yana hassan da hussaina ku tafi dasu can wurinsa domin ni nasan tawa ta kare... Ba zan dada wasu kwanaki masu tsayi ba aduniya... Zuciyarsa ta karye ya fara shishshikar kuka. Sarkin dogarai yayi sauri ya sunkuyar da kai idanunsa cike da kwalla tunda yake bai taba ganin sarkinsa na zubar da hawaye ba koda barkono ne ya shigar masa idanu. Allah ya dada ma lafiya kana iya dogara dani in Allah yaso zan isar ma da duk sakonninka agurin aminanka sarki lurwanu fuskar sarki sabitu ta dan saki wani dan kankanin farin ciki ya haskaka fuskar Nagode daman nasan kai kadaine zan iya dogara dashi... Sarki sabitu yayi shiru adaidai lokacin da sukaji wata zazzakar murya tayi sallama a kofar dakin ba'a dade ba wasu kyawawan yara yan kimanin shekaru goma sha hudu hudu suka shigo cikin dakin sarkin dogarai ya dubi hassan da hussaina cikin tsananin tausayi sai yaji idanunsa sun ciko da kwalla mahaifiyar yarance ta fado masa azuciya yau kusan shekarunta goma sha hudu kenan da mutuwa tana haifar yan biyun ta mutu. Azamanin da take raye ta taba bashi kyautar rigar saki. Sarkin dogarai ya sake kallon yaran sai yaji wani dadi ya lullube zuciyarsa aransa yafara fatan inama ace ya'yansa ne domin tun dayake bai taba haihuwa ba haka nan bai taba gajiya da kallon kyawawan yaran ba musamman hussaina tauraruwa mai kyawun duniya kamar yadda mawakin sarki yataba ce mata. Yaran biyu suka shigo dakin sukayi gaisuwa ga mahaifinsu sannan suka zauna akan kilishin daya mamaye dakin sarki sabitu ya yunkura daga kwance yatashi zaune da kyar ya dubi yaran biyu yace gasunan sarkin dogarai nabaka su amana ahannunka ka isar dasu gurin Aminina su da dukiyarsu kada ka bari wani abu ya same su duk abinda ya same su ahannunka. Sarkin dogarai yace Allah ya dada ma lafiya babu wanda ya isa yataba su matukar ina raye har sai na isar dasu sarki sabitu ya saki jikinsa gamida ajiyar zuciya sannan ya koma ya kwanta. Adaidai lokacin ne to yarsa hussaina ta dube shi tace baba ina zaka kai mu? Sarki sabitu ya dauke kai gefe guda domin bazai iya hada idanu da ita ba don kada taga halin dayake ciki zuciyarta ya sosu gurin aminina sarki lurwanu za a kai ku Hussaina ta dube shi cikin mamaki baba acan zamu zauna ko za'a dawo damu?Hussaina ta dube shi cikin mamaki Baba acan zamu zauna ko za'a dawo damu? Sarki sabitu yayi shiru na tsawon lokaci sannan saiyace me yiwuwa ku dawo...me zai hana watan watarana kuna iya dawowa ai nan garinku ne hawaye ya subuce masa. BIYU 2 Lokacin da sarkin makera mai masaba ya karasa gida sai ya kasa zaune ya kasa tsaye haka nan daga ya zauna ya dan sarara saiyaji kalmar zinare lu'u lu'u tagulla na yawo cikin kwakwalwarsa me ke damuna ne? Ya tambayi kansa da kansa. Kusan sa'o'i biyu kenan da suka wuce yana faman sintiri daga kofar gida zuwa cikin gida. Tun sa'ar daya dawo daga gidan sarki matarsa HABI ta dama masa fura kanata shimfida masa tabarma karauni kamar yadda ta sabayi ga al'ada sannan ta

Chapter 1 of 8