Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
bayan sun diro ne sai suka tabbatar da cewa yanxu sun fito daga gidan. Anan suka fara gudu baji ba gani kai kace mahaukata. Haka suma masu bakaken kaya suna dirowa sai suka bisu a guje. Sai da gudu yayi gudu sannan suka fara hango dishi dishin titi tare da jin jiniyar motar yan sanda. Anan su dije suka kara kaimin gudu domin su cimma motar yan sandan ko xasu samu taimako. Gudu suke suna ihu ko yan sandan zasuji. Suna cikin gudun ne sai sukaga wasu mutane sun diro saman itace a gabansu. Mace da namiji ne idanuwansu sunyi wani baki bakyan gani. Kuma a wannna lokaci ne masu bakaken kaya suka cimmusu. Anan nana ta gane namijin. Shine saurayinta hamir wanda yayi sanadiyar kawota wannan gida itada abokanta. " Ke a tsammaninki kinsha ko? To yanxu zakibi yan uwaki dama suna can suna jiranki." Anan ya bude hakoransa marar kyan gani yayi cikin su dije. To kafin ya karasa ne sai sukaga ya fadi. Suna dubawa sai sukaga yan sanda biyu mace da namiji ashe sune suka halbeshi. Dije na kallon macen yar sandan saita ganeta. Itace anisa wadda mairo ta bata labarinta. Kuma har ta karbe ID card dinta daga hannun mairo. Anan anisa ta juya zuwa ga macen wato abokiyar hamir. " Sannunki zee, sai gashi yau mun kara hadewa. Kuma sai gashi na kamaki a lokacin da nakeso." Inji anisa. " To daga nan fa?" Zee ta tambaya. " Sai zuwa lafira." Anan anisa ta bindige zee kasa. PAGE 60 Su kuwa masu bakaken kaya na ganin haka sai suka rantama a guje. Anan anisa da abokin aikinta suka rufa musu baya a guje. Sai da su masu bakaken kayan gudunsu daban yake. Suna gudu sai kace iska. Kafin kaceme sun ba su anisa tazara mai yawa. Suna kaiwa ga gidan. Taba kofar kawai sukayi sai suka bace bat ba a ganinsu. Haka shima gidan sai ya bace bat wurin ya koma fili. Anan anisa ta fara cizon hannu domin wannan shine abunda ya faru a lokacin da yan sanda suka taimaketa bayan ta fito daga gidan. Yan sandan suna zuwa gidan sai sukaga ya bace ba a ganinsa. Haka anisa ta dawo tare da abokin aikinta wurin su dije. Anan dije ta bata ID card dinta tare da fada mata yadda akayi ta sameshi da kuma labarinta. " Kada ki damu dije. Xan taimakeku keda iyayenki. Daga yanzu bazaku kara zama cikin wannan hali na talauci ba. Zan mayar dake birni inda zaki samu ilimi na zamani wato boko keda kanenki. Shi kuwa abbanki zansa a nema masa aiki mai tsoka." Anan anisa tayi gyaran murya kafin ta cigaba. " Wannan namiji da kike gani sunansa aswad. Abokin aikina ne. Kuma shima ya taba shiga irin halin da kiki tsinci kanki. Ba shi kadai ba har ni nan na taba fadawa ciki." Haka suka cigaba da tafita suna hira har suka kawo bakin motar. To kafin su shiga ne dije da nana suka kalli juna cikin farin ciki. Daga nan sai suka shiga motar su anisa. A wannan lokaci hasken safiya ya fara fitowa amma ba sosai ba. Aswad ne ke tuka motar sai anisa kusa dashi. Dije da nana a baya. Anan aswad ya mika ya nufi hanyar fita dajin. Daga karshe dai anisa ta taimaki dije sosai itada iyayenta. Ta basu gida a cikin birni. Shi kuma abba an samar mashi aikin gwamnati. Dama yanada qualification na N C E aikine bai samu ba. Dije da kanenta sun zama yan birni gadan gadan domin a gidan anisa suka tare ita ke daukar dawainiyarsu. Iyaka dai idan ta samu dama takan kaiwa abokanta na kauye ziyara. Haka ta riki zumunci batayi watsi da su mairo ba. Da su nana. PAGE 61 Ni anisa, a kullum idan nayi tunani nakan yi mamakin wannan duniyar da muke ciki, yadda al amurra suka tabarbare ba mai tausayi balantana hakuri. Na gano hakan ne sanadiyar wannan lamari dana gani ya faru akan idona. Wato hakuri shine maganin zaman duniya. Saboda haka duk wanda bai yi hakuri ba, to bazai ga hakuri ba. Talauci masifa ce, fitina ce kuma bala i ne, wannan dalili shine yasa akace kowa ya tashi ya nemi nasa ba don komi ba sai don kariya daga wannan masifa ta talauci. Wato da ace dije tayi hakurin talaucin data tsinci kanta a ciki. To da bata shiga wannan masifa ba. Haka shima karuwanci fitina ne. Domin da ace nana batabin maxa to bazata hadu da hamir ba har ya kawota wannan gida na maita ba. Maita gaskiya ce. Kuma koina akan samu mayyu. Sai dai har yanxu ba a san mafarinta ba, da kuma yadda ake gane masu fama da ita ba. Da gaske akwai wannan gida. Kuma ba abunda akeyi a ciki in banda yankan mutane. Sai dai har yanxu ba wanda ke iya cewa ga inda gidan yake saboda an asirceshi. Zee da hamir sun mutu. Amma kuma shugabansu bai mutu ba. Haka ma macijin da suke bautama yana raye. Kai in takaice maka labari da yawa daga cikin mayyun suna raye. Kaga kenan labari bai kare ba. Domin zasu cigaba da gudanar da miyagun ayyukansu har abada. Wannan labari ba shirme bane gaskiya ce. Kuma yakan iya faruwa gareka, gareki, ko kuma garemu. Ka tsaya kayi tunani, ka hanga, kuma ka auna sai ka rubuta abunda ka gani a cikin wannan labari idan ba kamshin gaskiya a cikinsa. Sanina ne cewa duniya ta canza daga yadda muka santa zuwa akasin haka. Duk abunda baka tsammamin ya faru shi yake faruwa, kuma duk abunda kake ganin zai faru shine baya faruwa. Addu a itace takobin mumini kuma duk wanda ya riketa to bazai tabe ba har abada. ALLAH ka tsaremu, ka karemu daga sharrin duk wani mugu na boye dana zahiri. Ameen. THE END Based on the novel by abdul king article. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6