Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
ta fara nishi sai kace mai jin kashi. Sai da ya dau lokaci yana shafa jikinta daga nan kuma sai ya bankare kafafuwanta da nufin warwasawa. Caraf sai ga anisa ta mike zumbur. A wannan lokaci duk abunda takeji ya kau. Da karfi ta ture wannan katon dake shirin afka mata daga nan ta mayar da dankwalin ta. " Dama kin kawoni ne domin a cimin mutunci?" Anan anisa ta kama hanyar fita tana zub da hawaye. Da gudu zee ta biyota tana lallashinta. " Haba baby ya kina fadar haka sai kace ba wayayya ba. Nifa taimakonki xanyi domin ki zama daya daga cikinmu. Kuma ina tabbatar miki da cewa da ace kin tsaya to da yanzu an gama kome." Anan anisa ta finciko hannunta da karfi tana kallon zanen maciji. " Wannan macijin da aka zana a hannunki me yake nufi, kuma me yasa duk daukakin mutanen dake wannan gidan sunada shi?" Anisa ta tambaya PAGE 12 " Wannan zane na maciji dake hannuna an yi shine da wuta yadda bazai taba gogewa ba har abada. Kuma wannan macijin da kike gani shine uban gidanmu. Kuma kema kafin ki shiga kungiyarmu dole sai an miki shi." Zee ta bata amsa. " Maciji shine uban gidanku, to meye ya hadaku da maciji inba maita ba. Kuma menene nasha a cikin kwarya? Kada fa kicemin jini ne. Ashe ku mayyu ne. Mayyun jini. To idan ba jini bane menene nasha?" Anisa ta fada tana xub da hawaye. " Ni yanzu kinga tafiyata." Anan ta juya ta nufi kofar gida. Caraf sai zee ta rike hannunta. " Haba kawata ya zakiyimin haka. Wai kuwa kin san irin kunyar da kika jefani a yau din nan. To bari na fada miki wani abu. Bazaki zo kiga sirrinmu ba sannan ki fallasa mu a gari kowa yaji. Ga kaida duk wanda yazo nan to dolene yayi mana biyayya. Saboda haka dolene ki shiga kungiyarmu ko kinaso ko bakyaso. Yanzu kije duk inda zaki. Nasan ke da kanki zaki kawo kanki har wurinmu. " Anan zee ta koma cikin gidan ta kyaleta. Daga nan ne anisa ta nufi motarta. Dakyar take tukin har ta samu damar fita daga unguwar wadda ba gida gaba balle baya in banda wannan na su zee. To bayan takai gida ne ta tarar su mumy har sunyi bacci. A haka ta kishigida saman gadonta tunanin duniya ya dabaibayeta. Cikin hakane bacci ya dauketa. " Anisa, anisa, anisa." Anan ta sheko a guje wurin daddy. "Ban taba aika ki wani wuri ba tunda nake. Yau ma lalura ce shi yaza zan aikeki domin yan aikin duk basu zoba. Anan ya bata kudi tare da fada mata abunda yakeso ta siya masa. A cikin motarta ta shiga bata tsaya koina ba sai wani katon shago da ake siyar da shaddodi. To bayan ta siya ne kafin ta fito sai tayi kicibis da wani saurayi. Suna hada ido gabanta ya fadi. Anan ya mata kallon tsaf. Done kanta tayi ta fita shi kuwa sai ya biyo bayanta. " Don Allah yan mata idan bazaki damu ba ko zan iya sanin sunanki." Anan anisat ta kalleshi cikin mamaki. " Kai kuwa daga ina haka? Daganin mace sai ka noce." " Haba don Allah fa nace, yanzu kiyi hakuri ki fadamin sunan kawai." PAGE 13 " Kai ni kaga tafiyata banada lokaci." Inji anisat. Anan ta juya ta cigaba da tafiyarta. Shi kuwa bai damu ba sai ya fara binta yana lallashinta. Kajifa mata da yanga. Tun da ganinsa fa taji ya kwanta mata amma saboda jan aji irin na mata haka ta cigaba da juyashi sai kace waina a cikin tandu. To sai akayi sa a yaron mai baki ne, saboda haka cikin kankanin lokaci ya shawo kanta. Kafin kaceme ya samu abunda yake nema. A cikin sati daya kacal soyayya mai karfi ta shiga tsakanin wannan yaro da anisat. Yakan kawo mata ziyara akai akai har gida tare da fita da ita yawo har dai a cikin dare. Ba yadda su daddy basuyi ba domin ganin sun hanata fitar dare amma taki. Wata rana suna chat a whatsapp: Hamir: Slm Anisa: wslm Hamir: ya kk ne. Anisa: lfy lau kaifa. Hamir: Akwai inda nakeso muje yau da dare ina fatan ba matsala. Anisa: Nifa na fara gajiya da night club din nan kaji kuwa yadda su daddy ke fada. Hamir: Haba sweety,yanzu ke matsayinki na big girl ace gida ana miki haka. To ai munada yawa domin da kawayenki za a. Anisa: Da gaske? To yanzu ya kenan. Hamir: Kada ki damu zan zo har gidanku da dare. Anisa: Ok ba matsala. Hamir: Bye dear ki kulamin da kanki. Anisa na ajiye wayar sai ga mumy ta shigo cikin dakin. Anan ta zauna kusa da ita. " Anisa wai kece kuwa? Nifa sanina yata mai ladabi da biyayya ce kuma bata saba umarnina. Amma sai aka wayi gari kin canza. Kece yawon dare, shaye shaye, fadace fadace. To wai ina tambayarki yaushe zakiyi hankali ne?" " Haba mumy shaye shaye fa kikace." " E na fada kinayi, sau nawa kike shigowa a cikin maye bakisan inda kanki yakeba." Anan mumy ta dauko wata yar karamar jaka ta anisa dake rataye a bango. Ai kuwa tana budawa sai tayi salati. " Wato nan kike boye magungunan ki ko?" PAGE 14 Anan anisa tayi shiru domin tasan batada gaskiya. " To Allah ya shirye ki." Anan mumy ta dauki jakar ta fita. Bayan minti biyu da faruwar hakan sai ga abba ya shigo gigice. " Ke, ashe bakida hankali ban sani ba. Yaushe kika lalace haka?"A haka daddy ya sameta da fada inda yake shiga banan yake fita ba. A hakan anisa tayi shiru domin tasan halin abba idan yayi zuciya. Inda sabone ai ta saba da fadansa. Can kuma sai ga mumy ta shigo aguje tana bashi hakuri domin shi nufinsa ya doketa. Anan dai ta lababa shi ya hakura ya fita. Ita kuwa anisa abun ko a jikinta bata damu ba jira kawai take dare yayi hamir yazo. Da misalin karfe 8: 30 PM hamir yazo. To anisa ta riga tasan yau fa idan akaga fitarta to karyarta ta kare saboda haka saita diro ta taga. A hankali take tafiya sai kace hanwawa. To bayan ta fita gidan ne saita tarar da wata jeep a fake. Ai kuwa kai tsaye ta shiga domin tasan ko su waye a ciki. Da shigarta ta tarar da kawayenta wadanda take haduwa dasu a night club. Matan su biyu ne sai ita cikon ta uku. Sai hamir da abokansa biyu.. Gaba daya dai su shidda ne a motar. Wato mata uku maza uku: hamir, safyan, da najib. Sai anisa, mamee, da kuma ruky. Hamir ne ke tuka motor domin shi ne yasan inda zai kaisu. A wannan lokaci kowanensu cikin jin dadi yake sanadiyar tafiyar dare ce zasuyi. To anan suka yanki titi sai tafiya ake ba kakkautawa. " Hahhhha. Sheri mamee har kin ban dariya." Haka ruky tace sanadiyar wani labari da mamee ke bata. " To idan kece ya zakiyi?" Mamee ta tambaya. " Me zan yi kuma. Guduwa mana." Ruky ta bata amsa. " Ai ko kin gudu zasu iya binki fa. Bakisan matsafa neba." Inji mamee. " Wai menene kuke tattaunawa haka sai dariya kukeyi?" Anisa ta tambaya. " Ai ina gaya miki kawata wannan yarinya ce mamee da shegiyar karya. Wai labarin wasu ne takeban masu amfani da jinin mutum." Inji ruky. " Ke waya fada miki karyane. Duk abunda na fadi da gaskene." Cewar mamee. PAGE 15 " To nidai a dawo farko inaso naji farkon labari." Inji anisa. " To yanxu idan abunda mamee ta fada ya zama gaskiya ya kenan?" Hamir ya fada. Anan suka kyalkyace da dariya su a ganin su ya za ayi wnan abu ya faru. A haka suka cigaba da tafiya suna ratsa dazuzzuka a guje. To suna cikin tafiyar ne sai hamir ya faka motar. " Wai menene ya faru?" Najib ya tambaya dama shine a gaba kusa dashi. " Zan dan yi larurane, fitsarin ne ya matseni." Anan hamir ya fita ya bar su a cikin motar. Su kuwa sai suka cigaba da firarsu kafin ya dawo. " Wai hala wane wurine zai kaimu?" Anisa ta tambaya. " Tab, wai kema bai fada maki ba kike nufi?" Najib ya fada. " E mana. Tsamanina ya fada muku ai." Anisa ta bashi amsa. " Kada ku damu inaga baxai wuce club ba." Cewar safyan. " Amma fa yakamata ace ya dawo yanzu. Bari na fita na duba." Anan safyan ya fito cikin motar yana kiransa amma ko alamarsa babu. Saboda tsananin duhu dakyar ya dawo cikin motar ya dauki yar karamar torch-light. Anan ya fara tafiya yana haskawa amma ba hamir ba alamarsa. " Inaga fa akwai matsala kada fa ace hamir ya bata." Cewar ruky. " Hahahha. Kufa mata tsoro fa ya muku yawa. Wai bata. Hala an fada muku shi mace ne da za a saceshi." Najib ya bata amsa. " To kufa kada muyi zaune a nan wani abu ya samemu. Ni har na fara jin tsoro." Inji mamee cikin wasa. Anan suka kyalkyace da dariya suna kallonta. " Ashe dama kina tsoron tafiyar dare?" Najib ya tambaya. " E mana. Idan muka haddu da mayyun jini fa." Mamee ta fada cikin kashe idanu. " Wannan labari fa ba da gaske bane. Wai kun taba ganin inda mutum yaci mutum?" Najib ya kara tambaya. " Au dama baka sani ba. To sau nawa akayi. Na taba jin labarin wani gida dake cikin......" To kafin mamee ta iyar da maganar sai sukaga safyan ya shigo gigice. Anan suka fara kallonsa a tsorace. " Lafiya kuwa. To ina hamir din." Anisa ta tambaya. PAGE 16 " Kai. Ku bani makullin mota. Ni bazan xauna a nan ba. Yanzu gida zan wuce. Ku bani makullin motar na tuka." Anan ya mike da nufin komawa gaba. Su kuwa su anisa sai suka rikeshi suna tsammanin ko ya zautu ne. Kubce kubce yayi tayi domin su barshi ya tafiyarsa amma sukaki. " Ku sakeni in tafiyata. Ni bazan mutu a nan ba. Bazan mutu a cikin wannan tafiya ba." haka safyan ke fada yana fisge fisge su kuwa suka rikeshi gam. To bayan yaga bazasu sakeshi ba sai ya fara zub da hawaye. " Haba safyan, wai wannan kuka fa. Yanxu dai ka fada mana wai meke faruwane?" Anisa ta tambaya. " Nasan zakuga kamar na haukace ko? To da hankalina. Kuma duk abunda nake ina sane. Idan har kunaso mu rayu to dole mu bar wannan wuri yanxu idan ba haka ba to nan bada jimawa ba zamu zama gawawwaki." Cewar safyan. To anan hankalinsau ya tashi gaba daya. Kowanensu ido ya fito sai kace mazuru. " To yanzu sai ka fada muna menene ka gani kuma ina hamir yake?" Anisa ta tambaya. " Hamir ya yaudaremu. Ya cucemu. Ni dana sani da ban bijirewa iyayena ba. Dana sani da banyi tafiyar dare irin wannan ba. Yanxu shi kenan haka zamu mutu." Anan safyan ya cigaba da kukansa. Ba yadda basuyi dashi ba ya fada musu kome ya gani amma ya kasa. " Tunda bazaka fadaba ni bari na fita na gani." Inji anisat. Anan taja ganbun motar da nufin budewa. Ai kuwa kafin ta bude kawai sai taji saukar gatari akan ganbun. Anan tayi wani ihu ta kulle ganbun. " Wayyo Allah. Gasunan fa." Inji safyan a tsorace. Anan suka farajin sara ta koina. Cikin karfin hali najib ya kunna motar da karfi ya wani juyawa kafin kaceme ya fizgi daji. Ai kuwa sai motar ta kubce, shi kuwa ya kasa controlling dinta. Daga nan sai suka fara ihu ganin mutuwa a fili. Sai da motar tayi tafiya mai nisa kafin ta bugi wani icce. Daganan saita tsaya hayaki sai fita yake. Cikin sauri su anisa suka fito sai tari suke da sheshsheka. A wannan lokaci kowanensu ya tsorata sosai domin basuyi tsammanin cewa zasu rayu ba. PAGE 17 " To yanxu meye abunyi kenan?" Mamee ta tambaya. " Bako shakka dole mu bar wannan daji yanzu idan har munaso mu rayu." Cewar ruky. " To amma su waye wadannan dake son kashemu?" Najib ya fada. " Wannan itace amsar daya kamata mu gano." Inji anisa. Haka suka cigaba da tattaunawa ta yadda zasubar wurin amma ba wani nagartaccen tsari da suka hango. Ba yadda basuyi ba motar ta tashi amma taki. A haka suka hankura domin sun san cewa sun kawo kansu ga mahalaka. Suna cikin hakane sai suka farajin gudun wasu mutane kamar sun nufosu. Ai kuwa su anisa najin haka sai suka rantama a guje. Kowanensu sai gudu yake kamar ransa zai fita. Sai da sukayi gudu mai nisa kafin su tsaya sanadiyar sunji kamar an daina binsu. To anan suka fara tafiya suna waige waige. Kai daganin tafiyarsu kasan sun gaji mutuka. Amma saboda tsoro haka suka daure kamar basa gajiya sai shiga suke a cikin dajin. " Nifa na gaji. Gaskiya bazan iya tafiya ba." Anan ruky ya zukunna tana sheshsheka. Ganin haka yasa kowanensu ya dan gincira kusa ga itace domin su samu sarari. Can sai anisat ta mike da sauri. Cikin fushi ta ci kwalar safyan. " Ka fada mana menene ke faruwa damune. Su waye ke kokarin kashemu. Kuma dazu daka fita me ka gani?" Anan safyan ya fara nishi guda guda saboda matsar daya sha. " Duk abunda mamee ta fadi gaskiya ne. Bako shakka hakane batayi karya ba." Anan anisa ta sakeshi domin ya cigaba da bayaninsa. " Bako shakka hamir yana daya daga cikin wadanda muke zargi domin fitar danayi saina ganshi yana........" To kafin ya iyar sai suka farajin halbin kibau. Ai kuwa cikin sauri suka mike. Shi kuwa safyan kafin ya gyara sai yaji saukar kibiya a bayansa. Anan yayi ihu ya fadi yana fizge fizge saboda zafin da yakeji. Najib ne ya dauko shi daga nan sai suka cigaba da gudun. Sai dai najib shine baya saboda daukar dayawa safyan. A wannan lokaci sun san cewa da an kamasu to sunansu gawa. Saboda haka suka takarkare wurin kariyar kansu. PAGE 18 Sai da sukayi gudu iya ransu kafin su kawo wani wuri mai ramuka da kwazazzabai. To anan suka boye a cikin wani kungurmin rame. Sun dade a wurin ko matsi basayi kafin su fara ganin wasu halittu suna isowa a wurin. Kai da gani kasan su ake nema. Tufafin jikinsu bakake ne sai wasu muggan makamai da suke rike dasu. Ba a ganin fuskarsu domin sun rufeta da bakin kyalle. Abun mamaki kuma shine tafiyarsu daban ce. Domin sunada mutukar sauri sai kace iska. Kai da ganinsu dole ka girgiza saboda kasan a buge basa buguwa. Anan su anisa suka sandare cikin rame ko shaida basa son yi saboda tsoro. Sai da wadannan mutane suka zagaye wurin tsaf basu gansu ba daga nan sai suka nufi wata hanya suka wuce. To anan ne suka fito suna haki kamar ransu zai fita. Shi kuwa najib a lokacin ya ajiye safyan a gefe sai zubar da hawaye yake. Su anisa ne suka zo suna girgiza shi amma ko motsi bayayi. A nan mamee taxo tana girgixa shi. " Haba safyan ka tashi mana. Nasan ba zaka tafi ka barni ba. " A haka ta cigaba da girgiza shi amma ina. Daga nan sai ruky ta tayar da ita domin sun san cewa rai yayi halinsa. Mamee ta durkusa sai zubar da hawaye take saboda rashin safyan. " To yanzu haka zamu mutu kenan? Su waye wadanna mutane? Kuma me yasa suke son kashemu. Gaskiya bazai yiwu ba, ni yanzu sai na gano ko su waye tare da daukar fansa." Anan mamee ta nufi hanyar da suka fito. Ai kuwa mikawarta keda wuya sai ga wadannan mutanen sun fito. Su anisa na kiranta amma ina ko jinsu batayi. A haka wadannan mutane suka kamata suka wuce da ita. Su anisa kuwa na ganin haka suka runtuma basa ko juyawa. A haka suka ci gaba da gudu cikin bakin ciki domin sun san cewa mamee sai dai Allah yaji kanta. Yanzu sun koma su uku kenan: Anisa, ruky da najib. Shi kuwa hamir ba duriyarsa tunda ya fita. Abunda basu sani ba shine wai yasan halin da suke ciki kuwa. To idan ya sani ina yake kuma me ya fitayi. Gashi dama safyan ne yaga wani abu a tattare dashi kuma gashi ya kare balantana ya fada musu abunda ya gani. PAGE 19 A haka suka cigaba da gudu har saida suka iso wani katafaren gida. To anan suka fara jin dadin domin a ganinsu zasu samu taimako. Da karfi suka shigo gidan suna dube dube. Basuga kowa ba inbanda wata mace kan kujera sai dubansu take. Anan ta musu sannu da zuwa tare da zaunar dasu kan kujeru. " Ki taimaka mana. Wasu ne keson kashemu gashi bamusan ko su waye bane. Idan kinada waya ki bamu akwai wadanda zamu kira." Najib ne ya fadi cikin sheshsheka. Anan matar ta kalleshi cikin murmushi. " Da ace zan iya taimaka muku..." Daga nan sai matar ta tashi tsaye. Taku uku tayi daga nan saita juyo. Ai kuwa juyawarta keda wuya sai sukaga ta rikida. Anan gaban anisa ya fadi domin ba kowa ceba in banda kawarta zee. " Ke a ganinki zaki iya tsere mana ko? To duk inda kikaje muna ganinki." Xee ta fada tana kallon anisa. " Dama na fada miki cewa keda kanki zaki kawo kanki har wurinmu. Ai kuwa gashi kinzo da kanki." Anan tayi shiru saboda shigowar wani a gidan. Su anisa na juyawa sai sukayi arba da hamir. Ba yadda basuyi ba domin su tashi daga saman kujerar da suka zauna amma sun kasa. Zee na ganin haka sai ta fashe da dariya." Ai kubar wahalar da kanku domin idan zaku shekara a nan bazaku iya tserewa ba sai yanda naso nayi daku." Daga nan saita kalli hamir. " Da kyau hamir aikinka na kyau. Zo matso kusa gareni." Anan suka fara sumbatar juna suna kyakkyata dariyar mugunta. Daga nan sai hamir yazo kusa ga ruky. Wata yar karamar yuka ya dauko daga nan sai ya fara dasasawa a makwogoronta. Ai kuwa nan take jini ya baltsu. Shi da zee suka tara bakinsu sai sha suke. Su kuwa anisa da najib sai zub da hawaye suke saboda tausyawa ga yar uwarsu. Hardai najib yayi mutukar bakin ciki domin shine ke sonta. " Nan bada jimawa ba za a gabatar daku ga uban gidanmu." Inji zee. Daga nan sai aka kaisu wani daki mai duhu aka kulle. Anisa ce ta shiga cikin tunani, ko wane uban gida zee take magana akai. Kada dai ace wannan macijin data gani an zana a hannunta. PAGE 20 Ba a wani dadewa ba saiga xee ta shigo dakin tare da wasu samudawa. Da ganinsu anisa ta ganesu. Wato sune wadanda suke binsu a lokacin da suke gudu cikin daji. To anan aka fito dasu cikin gidan. Wadannan mutanen dake binsu sun tsayu sai buga ganguna sukeyi. Anan aka ja su anisa sai tafiya akeyi dasu kamar an koro shanu. Sai da akayi tafiya mai nisa sannan aka kawo wani wuri cikin dokar daji. Anan aka kunna wuta. Su kuma wadannan masu bakaken kayan sai suka fara zagayen wutar suna fadin wasu kalamai da su anisa basajin abunda suke fadi. Wasu kuma sai kada ganguna sukeyi. Ana cikin hakane sai ga wani irin zabgegen maciji ya ratso ta cikin jama a. Shi dai wannan maciji abun kallo ne domin girmansa jikinsa yafi daki. Ai kuwa suna ganinsa sai suka durkusa saboda girmamawa. Shi kuwa macijin sai wangame baki yake tamkar an bude kofa. Anisa na ganin wannan maciji sai ta tuno da zanen data gani a hannun zee. Bako shakka wannan macijin ne suka zana. Wasu samudawan ne suka janyo anisa da karfin tsiya. Anan najib ya kura musu idanu yaga me zasuyi. Ai kuwa sai yaga sun dukar da ita gaban macijin. Daga nan sai hamir ya dauko wani takobi da nufin datse mata kai. To kafin ya iyar da nufinsa ne najib yayi kukan kura ya zubar da mutanen dake rike dashi. Wani naushi ne yama hamir sai da ya fadi rikicaa. Daga nan sai ya tallabota da nufin su gudu. Kawai sai anisa taga jini na fita a bakinsa. Anan ya saketa. Dubawar da anisa zatayi haka sai taga ashe zee ce ta sokama najib takobi har sai da ta bullo ta cikinsa. " Kada ki damu dani ki gudu. Ki gudu nace." Inji najib. Anan najib ya fadi yana nishi dakyar. Ita kuwa anisa sai taci na kare ai kuwa sauran jama ar sai suka rufa mata baya da nufin su kasheta. Daganan sai aka fara tsere. A wannan lokaci anisa da karfin tsiya take gudu domin tasan da sun kamata to sunanta gawa. Ba yadda basu yiba domin ganin sun cimmata amma taki. A duk lokacin data waiga ta gansu sai ta kara kaimin gudu. Haka ta cigaba da gudun har tabar dajin ta kawo bakin titi. Anan ta hau titi ita kadai a cikin wannan dare sai gudu take. Gashi ba mota ba kowa balantana ta koma gida. A haka ta cigaba da gudu saman titi har saida wasu yan sanda masu patrol suka risketa. Anan ta fada musu abunda ya faru. To bayan yan sandan sunje wurin sai sukaga gidan ya bace bat ba a ganinsa. Saboda haka dole suka dawo. Daga nan kuma sai suka taimaki anisa tare da mayar da ita har gida........ PAGE 21 Dare mahutar bawa, idan lokacin ka yayi dole a tareka, dare mahutar bawa, idan kazo dolene komi ya samu akasi. Dare mahutar bawa, duk wanda bai zauna wuri daya ba to bayada banbanci da matacce. Wannan magana haka take ba tantama, nasan yanzu ka samu nagartacciyar fahimta akan abunda nake nufi. Bako shakka nayi dana sanin kin bin umarnin iyayena. Domin da ace nayi abunda sukeso da irin hakan bata faruba. Ni kadaice na dawo cikin mu shidda, sauran kuwa duk sun kare. Zee da hamir suna raye. Saboda haka nasan wannan gwagwarmaya bata kareba. Maita gaskiya ce. Kuma koina akan samu mayyu. Sai dai har yanxu ba a san mafarinta ba, da kuma yadda ake gane masu fama da ita ba Ba kowane abokine na kwarai ba. Wani kanyi abota dakai domin wani abu da yake bukata a wurinka. Wani kuma kanyi abota dakai domin ya juya maka ra ayi. A duk lokacin dana tuno rayuwar danayi a baya nakan yi nadama sosai domin nasan tabargazar dana afka a baya. Bako shakka zama da madaukin kanwa shi kasa gira tayi toho. Wannan magana haka take. Domin mutum abun tsoro ne. Indai kana tare da mai mugun hali to fa dakyar bai shafa ma ba. Ni na tabbatar da wannan domin naga an shafa min. Ban taba tsammanin cewa halina zai sauya ba. Amma sai gashi ina cikin wadanda ake kwatance dasu akan aikata barna. Nayi kuka sosai kuma nayi bakin ciki sosai amma ba yadda na iya dole na hakura. Na rasa abokaina wadanda bazan taba mantawa dasu ba. A hakan nayi nadama tare da yin abunda ya kamata. Iyayena basu gujeni ba. Haka sauran kannena. Sun rungume ni tare da share min hawaye. Babban abunda ke damuna shine makiyana suna raye. Wato hamir da zee. Kuma nasan kul a jima kul a dade sai sunyi kokarin yin wani abu a gareni. Saboda haka saina zurfafa domin in gano hanyar da zan kare kaina daga sharrin su. A yanxu na gama bincikena kuma nasan abunda zanyi. Wannan farawa ce ba karshe ba to amma me zai faru a karshen?TAFIYAR DARE 2 MAYYUN JINI AUTHOR: ABDUL KING ARTICLE EPISODE 2 PAGE 22 A cikin duhun daren wata rana, wata mota kirar sienna ta samu kanta a saman titi sai tafka wani namijin gudu take. Mutum biyar na a cikin motar sai ihu suke saboda music dake tashi duk ya cika musu kunne. Basu damu da hakan ba sai faman nishadi suke suna fira. Aswad da namil sune gaba. Sai nabilat,humairat, saudat a baya. Kai da gani kasan sun yi tafiya mai nisa. Kuma yanzu hakan suna kan hanyarsu ta zuwa wani gari domin yin al amurran yau da kullum. " Hahhh.Wai yaushe zamu isa ne?" Saudat ta fada cikin dariya. " Hmmn, yan mata kenan. Ai inaga ko yanzu akwai awa goma a gabanmu." Aswad ya bata amsa. Anan sauran suka kyalkyace da dariya. " Haba aswad ai wannan ba girmanka bane. Kana abu sai kace faisal." Nabilat ta fada cikin wasa. " Wai dama ke bakisan halinsa ba. Ai wannan kurun da kike gani ba makaryaci kamarsa." Namil ya fada bayan ya dan doki aswad a ciki. " Yanzu ke dear har kin yarda da abunda yace. Ki rabu dashi kawai ni zanyi maganinsa." Cewar aswad bayan ya rike sitari gam saboda shigowar wasu ramukka. Hanyar ba kyau motar sai gwaram gwaram takeyi. To bayan sun wuce gadar ne sai fira ta koma sabuwa. Domin a wannan lokaci saida kowa ya fadi albarkacin bakinsa harda humairat wadda ke latse latsen waya. Suna cikin firar ne sai mota ta fara rage gudu. " Ya naga haka wai lafiya kuwa?" Namil ya tambaya. " Bazance mai neba domin munyi full tank tun a gida. " Aswad ya fada yana dube dube. Can sai motar ta tsaya cak wuri daya. Sa ar da suka samu shine sunyi parking me kyau a gefen titi. To anan suka fito cikin mamaki abunda yasa motarsu ta tsaya. " To yanzu meye abunyi kenan?" Saudat ta tambaya. " Kada ku damu bari na kara gwadawa ko zamu dace." Inji Aswad. Anan ya shiga motar ba yadda bai yiba amma taki tashi. Anan namil ya taimaka masa suka bincike motar tsaf komi dai dai amma kuma taki tashi. PAGE 23 " Amma fa wannan abu daban mamaki to wai meke faruwa da motar nan ne. Gashi kuma harda full tank akayi." Nabilat ta fada cikin rashin jin dadi " Ai kedai bari. Ni yanzu haka wani abu nakeji. Mu kadai cikin dokar daji sai kace mayyu." Humairat ta fada tana kalle kalle. Ita kuwa saudat bata damu ba. Wayarta ma ta dauko wai hotuna zatayi. " Kuzo muyi pic mana." Ta fada cikin yanga. " Pic kuma? Lalle saudat kin haukace, ke yanzu bakya ganin halin da muke ciki har kina maganar hoto." Namil ya fada cikin takaici. " Kai kuwa miye ruwanka a ciki. Ai ba da kai nake magana ba, zaka iya bari sai idan na ambace ka." Saudat ta rama. " E to zagarni tunda na fada miki gaskiya." Cewar namil. " Aiko ban zageka ba kasan abunda kayi bai daceba. Shi yasa akeson mutum yayi tunani kafin yayi magana. Mtssss. Aikin banza kawai." Saudat ta fada cikin takaici. Shi kuwa namil sai ya kyaleta bai tanka ba. Anan suka cigaba da gyaran mota shida aswad ko zasu dace amma ina ba abunda ya faru. " Ni inaga me zai hana mu shiga cikin

Chapter 2 of 6