Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
bayyana mata ko ita wacece. " Sunana anisat, ni yar sanda ce mai binciken manyan laifukka kuma yanzu haka akwai abunda nake bincike a wannan kauye naku saboda haka inaso ki bani hadin kai dari bisa dari." Anan ta nuna mata ID card dinta. Ita kuwa mairo batasan ko meye ID card ba iyaka dai ta karba tana kallon foton anisa dake ciki. PAGE 48 " Wai ko kun taba yin bako a wannan gari naku?" Anisa ta tambaya. Anan mairo tayi dan tunani mai zurfi, cikin kankanin lokaci sai ta tuno da mutumin da suka gani jiya a wurin rafi. Daga nan sai ta amsa da cewa. "E kwarai kuwa." " Ina fatan dai zaki iya bayyana min ko shi waye!" Anisa ta fada. Anan mairo ta fada mata wannan mutumin da suka gani jiya wurin rafi tare da zanen dake hannunsa na maciji. Haka anisa ta cigaba da yiwa mairo tambayoyi ita kuwa sai bata amsa take. Daga karshe sukayi sallama anisa kuwa sai ta dauko cake ta bata. Mairo ta karba cikin mamaki domin tunda take bata taba ganinsa ba. Da anisa ta fahimci hakan sai ta fada mata cewa abinci ne. Haka anisa ta shiga motarta ta manta ta karbi ID card dinta. Ita kuwa mairo a tsammaninta an batane kyauta. Anan ta kama hanyar gida tana tafe tana tsalle tsalle. Bayan magrib ne mairo ta kaiwa dije ziyara. Anan ta bayyana mata yadda ta gamu da wannan yar sanda anisa. Da kuma kyautar data bata na hotonta. Sai kuma dan cake din data bata. Da karfi dije ta karbe cake din ta bantali dan kadan. Ai kuwa tanajin dadi sai ta finciko shi iyakar hannunta. Daga nan kuma saita amshe ID card din ta rataya a wuyanta kamar sarka. Ita kuma mairo bata damu ba anan ta barta shi. Haka sukayi sallama mairo ta koma gida. Bayan sati daya da faruwar hakan, yar dawar da akaba su dije sai ta kare. Sabida haka sai rayuwar da ta dawo. A kowane lokaci dije kanyi bakin ciki sosai idan taga yadda rayuwarsu take. Ba jin dadi balantana walwala. Saboda wannan dalili sai ta yanke shawarar cewa bari ta gwada zuwa rafin nan wata kila ko zata gamu da yar sandan nan. Idan ta gamu da ita ta mata tambayoyi kila ta bata irin abunda taba mairo wato cake. Da daddare ne amma ba sosai ba. Sai dije ta fita ita kadai da nufin zuwa rafin nan. Haka ta kama hanya tafiya take da sauri kai kace wadda aka yiwa busharar wani abu. A wannan lokaci yunwa ke damunta sosai domin rabonta da abinci har ta manta. Babban abunda yasa ta yanke wannan shawarar na tafiya rafi shine ko wata kila ta dace ta gamu da wannan yar sandan wato anisa. PAGE 49 Idan ta gamu da ita wata kila ko tamata tambayoyi yadda tama mairo. To idan aka yimata tambayoyin kila ta samu cake ko ta rage yunwar dake damunta. A haka ta cigaba da tafiya ba sassauci. Sabida tsabar yunwar dake damunta ko takalma bata dauko ba. A kasa take tafiya bata damu ba. Bayan ta isa rafin ne sai ta tsaya tana duban ruwa amma kowa babu. Wurin yayi tsit sai kace makabarta. Anan dije ta duka cikin bakin ciki. Cikinta ne ke wani murdawa saboda yunwa. Cikin rashin tsammani sai taga an hasko mata haske. Tana dubawa sai taga mota tafe wurinta. Anan dije ta mike cikin jin dadi domin a zatonta yar sandan ce. Kaji wani abu, da takardar cake din tazo. Anan ta falfala da gudu saida sukayi gab da gab sannan ta tsaya. Kawai sai taga namiji ya fito a ciki. Dubawarta keda wuya sai taga ba kowa bane in banda wannan namijin da suka fara gani a ranar da santsi ya kwasheta ta fada rafi. Anan ta mika masa takardar dake hannunta na cake. Shi kuwa mutumin yana karba sai yayi murmushi. A nan ya jawota inda motarsa. Yana bude motar sai dije ta leka ciki. Ai kuwa a guje ta shige ciki domin ba kome in banda abinci kala kala tare da irin cake din da takeso. Kwance tayi ruf da ciki sai diba take tana kaiwa baki. Abinka da sakarya batasan ko waye shi ba iyaka dai daga ganisa ta shige motarsa. Koda yake ba laifinta bane, tsananin yunwa ce ta jawo hakan. Shi kuwa mutumin da ganin hakan sai ya tsaya cak yana kallonta. Haka dije tayi cin hauka har saida tayi tatil. Daga nan sai ta fito daga motar tana gyatsa. Fitowarta keda wuya sai kunya ta kamata ganin mutumin na kallonta. " Amma fa na gode sosai." Ta fada tana dubansa. Shi kuwa murmushi yayi ba tare daya tanka ba. " Wai a wannan gari kake?" Dije ta tambaya amma shiru bai tanka ba. " Ni sunana dije kaifa?" Anan ya kara yin murmushi baice kome ba. Anan dije ta fara tunani wai ko baya magana ne. Can sai taga ya shiga motarsa. Anan ya juya ya nufi inda ya fito. Haka dije tabi wannan mutumi da kallo har ya bace mata da gani. Ita kuwa sai ta dawo gida cikin mamaki. Haka kuma taja bakinta ta tsuke ba tare da fadawa kowa ba harda mairo da take kawarta. PAGE 50 A yau dije tayi bacci mai dadi domin tunbinta a cike yake. Taji mutukar dadi na ganin wannan mutumi domin ya bata abunda takeso.Iyaka dai abunda ke damunta shine wai kuwa yana magana? To idan yana magana me yasa ya kyaleta a ranar. A haka dai ta cigaba da tunanin cewa kila baya magana. Saboda wannan abu daya faru sai dije ta maida rafi wurin zuwanta a duk lokacin da takejin yunwa. Sai dai bata zuwa sai a cikin dare domin mutumin a lokacin ake ganinsa. Bata fadawa kowa halin da take ciki ba domin ganin take idan ta fadawa su umma sukan iya hanata zuwa. A kan hakan ne ta tsuke bakinta ko babbar kawarta mairo bata fadawa ba. A duk lokacin da taje yakan bude mota ta shiga har sai tayi tatil da abinci. Kuma a duk lokacin da tayi masa magana baya amsawa sai dai murmushi. A kwana a tashi har suka fara sabawa da juna. Wataran idan tazo yakan rungumeta yana mata wasa amma kuma baya magana. Dije bata damu da duk abunda zai mata ba in har zata cika cikinta. A wannan dalili takan bashi hadin kai suyi wasansu daga nan kowa ya kama gabansa. Wata rana a cikin dare bayan dije ta iso wurin. A mamakinta bata ganshi ba. Sai da tayi tsayin kusan minti talatin sai gashi ya zo. Ai kuwa kai tsaye ta shiga motar. Shigarta keda wuya sai ya kunna ya tayar. Dije tayi mamaki ko ina zai je da ita. Taso ta tambayeshi amma data tuno baya magana sai ta tsuke bakinta. Iyaka dai ta jawo kayan abinci sai kalaci take cikin jin dadi. A duk lokacin da suka hado ido sai yayi mata murmushi saboda hakan dije bata damu ba iyaka dai a tunaninta yana yawon shakatawa ne da ita. Abu kamar wasa sai ga tafiya tayi nisa har suka fita cikin garin dije bata ankara ba sai faman shagali take da su cakes. Anan suka hau titi sai gudu yake a tamanin. Sai da sukayi tafiya mai nisa sannan dije ta dawo cikin hayyacinta. Anan ta gane cewa ba cikin garinsu ne ba. Saman titi ne suke tafiya sai dazuzzuka masu ban tsoro dake a gefen titin. PAGE 51 Anan dije ta fara damunsa daya tsaya amma ina ko kallonta bayayi. Tuki yake iya karfinsa. Ita kuwa sai ta fara ihu tana bugunsa amma yakiji. Da dai taga bazata fita ba kawai sai ta rike sitarin. Anan motar ta fara kalan keluwa sai da kyar ta tsaya. Ai kuwa motar na tsayawa dije ta fito a guje. Anan tayi arba da wasu mutane masu kirar samudawa. Kowanensu sanye da bakaken kaya sun lullube fuskarsu da bakin kyalle. Can sai ga mutumin shima ya fito. Dije na ganinsa sai ta sheko ta rungumeshi a tsorace. Shi kuwa hannunsa yasa ya bugeta can gefe. Anan taga an miko mishi takobi. Shi kuwa cikin sauri ya nufota. Dije na ganin haka sai ta rantama a guje cikin dajin. Su kuwa masu bakaken kayan sai suka dafa mata. Anan aka fara tsere tsakanin dije da wadannan mutane. Sai halbota mata kibiyoyi suke amma duk a banza domin bata samunta. Suna cikin gudun ne sai suka tsaya wuri daya suna dube dube. Wato dije ce ta bace musu da gani basusan inda ta shiga ba. Sai da suka dade suna binciken wajen amma ko duriyarta babu. Daga nan sai suka nufi wata hanya suka tafiyarsu. Can sai ga dije ta fito. Ashe dama cikin wani rame ne ta shiga sai ta sanya ganyayyaki a sama yadda ba kowa zai gane akwai mutum a wurin ba. Cikin dajin ta kara shiga sai faman gudu take tana mamakin irin wadannan mutane da kuma abunda yasa sukeso su kasheta. Bako shakka akwai ban mamaki a tattare dasu domin gudunsu daban yake da sauran mutane. Idan suna gudu kai kace akan iska ne suke gudu. Haka dije ta cigaba da gudun a cikin daji sai da tayi nisa sannan ta tsaya tana haki. To anan ne ta kara duban dajin taga irin bishiyoyin dake ciki. Wato dajin ya kasance wangameme mai ban tsoro. Ko ina itace ne dogaye masu furanni. Haka dije ta cigaba da tafiya tana sauri ko zata samu taimako. Sai da tayi tafiya mai nisa amma ko kadangare bata hadu dashi ba. To anan tsoro ya fara dabai bayeta domin duhun ya tsananta. Dakyar take ganin inda take takawa. PAGE 52 Dije tayi mutukar dana sanin kin yin hakuri halin gidansu na talauci wanda ta tsinci kanta a ciki. Gashi yanxu ta jefa kanta ga mahalaka. Babban abunda ke damunta shine can a gida ba wanda yasan inda take balantana a kawo mata dauki. Tana cikin tafiyar ne saita hango an kunna wuta a wani wuri. Da sauri ta nufi wurin inda ta isko mace da namiji a zaune sai firarsu suke. Tana isowa sai ta fara yi musu bayyani cewa su taimaketa za a kasheta. To abunda ya bata mamaki shine suma wadannan mutane basajin hausa kamar wancan mutumin daya daukota. Wani yarene suke wanda batasan kome suke fadi ba. Koda sukaga dije a galabaice ta zube kasa sai nishi take dai dai. Sai macen ta tallabota tana mata fifita. Dije najin suna magana amma batasan abunda suke fadi ba. Anan suka kashe wutar dakeci. Ita kuwa macen na rike da dije har saida suka kai wata yar bukka. A cikin bukkar an gyarata sosai da kayan alatu. Anan ta kishingida dije saman gado sai fita take mata. Ana cikin hakane sai ga wata mace ta shigo bukkar. Anan ta kurawa dije idanu bata ko kyaftawa. Daga nan kuma sai suka fara wata magana da wannna matar dakema dije fita cikin wani yare. To bayan sun kare sai matar ta juya ta fita. Haka shima namijin sai ya bita. Anan aka bar dije da mai mata fita. Bayan wani dan lokaci sai dije ta farfado. Hankalinta ya fara dawowa. Anan ta kalli matar amma batace kome ba. Ita kuwa matar sai murmushi take mata. To anan ne ta lura da zanen macijin dake hannunta irin na wancan mutumin data hadu dashi a rafi. Anan dije taja da baya a tsorace. Ita kuwa matar na ganin haka saita rungumeta tana sumbatar ta. Tun dije na kokarin ta kubce har takai ta tsaya wuri daya saboda abunda takeji yana shiga. Anan ta mimmike kafafuwanta saman gado sai wani nishi take. Ita kuwa matar sai matsar jikinta take duk inda taga dama. Daga nan dije bata kara sanin abunda ya faru ba. PAGE 53 Firgigit ta farka. Anan ta ganta cikin wani daki mai duhu an daure kafafuwanta da hannayenta. A mamakinta ba a cikin bukka bane. Hasalima shi wannan daki kamar a cikin gida yake, sai dai shi wannan wane gida ne kuma ya akayi tazo nan? Anan dije ta rasa abunda ke mata dadi domin a halin yanzu tana tsaka mai wuyar sani. Batasan inda takeba kuma batasan abunda ke iya faruwa da ita ba. Bako shakka hakuri shine maganin zaman duniya, duk wanda bai yi hakuri ba to bazaiga hakuri ba. Wato da ace dije tayi hakurin talaucin da suke ciki da irin hakan bai faru ba. Amma sai gashi kwadayinta na son abun duniya ya kaita ya baro. Bude dakin akayi a hankali. Can sai aka hasko mata fitila. Tanaji sai taga an tallabota an azata saman kujera mai tayu. Ita wannan kujera da an turata sai ta fara tafiya. Ai kuwa anan aka fara tura dije saman kujerar sai ihu take tana neman taimako. " Waye kai? Me kakeso a gareni?" Haka ta cigaba da fadi amma ko jinta bayayi. Da sauri ya nufi wani lungu da ita. Sai da yayi tafiya mai nisa sannan ya tsaya a kofar wani daki. Anan dije ta tabbatar da cewa lallai yanzu a cikin wani gida ne ba bukka ba. To amma ya akayi taxo gidan? Bayan sun shiga dakin ne sai ta ga cewa ashe mutumin nan ne wanda yayi sanadiyar shigowarta dajin. Anan ta kura masa ido sai harararsa take. " Macuci azzalumi me kake shirin yi dani, kuma nan inane ka kawoni." Haka dije ke fadi cikin bakin ciki amma shi ko damuwa bai yiba iyaka kallonta jikinta yake yana murmushi. Anan yazo yana shafa fuskarta a hankali. Yana cikin hakane dije ta gatsa masa cizo. Sai da yayi kara sosai sannan ya fadi. Ai kuwa tashinsa keda wuya ya gabza mata mari sai da ta kife saman kujerar. Daga nan ya jawota ya aza saman kujerar. Cikin fushi ya kara gabza mata wani marin. Daga nan kuma sai ya dunkule hannu yana dukanta kamar bazai barta ba. Fuskarta ya nunnuga sai da ya mata jina jina kafin ya fita dakin cikin fushi. Anan yabar dije cikin rauni mai yawa jini sai tsiyaya yakeyi. Kai da gani kasan taci wuya domin gaba daya fuskarta ta canza ko ina sai jini ke fita. PAGE 54 Haka dije taci gaba da zama a wannan daki sai nishi take dai dai. Saida aka dau lokaci kawai sai ga matar nan data gamu da ita cikin bukka ta shigo. Anan matar tazo kusa da ita. Hannuta rike yake da wani karamin akwati. Cikin murmushi matar taxo kusa ga dije. Daga nan saita bude akwatin ta dauko wani kyalle. A hankali tabi fuskar dije tana shafe jinin dake tsiyaya a fuskarta har saida ta tsanar da ita tsab. Tana kammalawa sai ta fita. Fitarta keda wuya sai ga wannan mutumin na farko ya shigo. Cike da murmushi ya shigo yana duban ta. Anan dije ta done kai ko kallonsa batason yi. Shi kuwa sai ya tallabo fuskarta ya kura mata ido. Can kuma sai ya kyaleta. Wata yar karamar yukace ya fito daga jikinsa. A kirji ya soka mata sai da tayi kara sannan ya fito da yukar. Anan ya jawo yukar a gefen jikinta har saida ya keta mata riga yadda ana ganin kome a fili. Jifa yayi da yukar sai kallonta yake kai kace mussa taga nama. Hannunsa ya dora saman jikinta sai shafawa yake ko ina. Kafin kaceme sai ya jawota jikinsa. Ita kuwa dije ba yadda ta iya domin a daure take. Da mutumin yaga kamar idan tana daure bazai iya yin abunda yakeso ba sai ya dauko yukar ya kwanceta. Anan dije ta kyaleshi sai da ya shagala yana warwasawa kafin ta manna masa cizo a kunne. Ihu ya kurma yana dukanta ita kuwa taki sakinsa. A haka suka fara mulmule mulmule cikin dakin amma dije taki sakin kunnen saida ta guntule shi. Daga nan saita tashi ta dauko kujerar nan mai tayu. A kai tayita rafka masa har saida ya suma. Anan ta fita dakin a guje ta barshi cikin jini. Gudu take iyakar gudu amma ta kasa ganin karshen gidan domin ko ina lungu ne. Tana cikin gudun ne saita jiyo ihun wasu a cikin wani daki. Sai dai ba damar shiga domin wasu samudawa ne rike da makamai a kofar dakin sai kai da komo suke. Anan dije ta labe tana tunanin yadda za a yi ta shiga dakin domin ganin ko su waye ke ihu. Can sai taji kamar an yi magana a cikin dakin. Kawai sai samudawan suka shiga ciki dama su biyune. Ita kuwa dije sai ta bisu jikinta na karkarwa. PAGE 55 Labewa tayi bayan wata kujera tana duban abunda ke faruwa. Wasu mata ne biyu aka sarkafe a gina jikinsu duk jini ne. Sai wani mutumi mai siffar ban tsoro rike da gatari yana magana da wadannan samudawan da suka shigo ciki. Wadannan mata duka yan garinsu su dije ne. Dayar itace nana wadda suka hadu da ita a gulbi tana wanka. Dayar kuwa abokiyar nana ce, akan kirata da ladiyo. Anan mamaki ya kashe dije koya akayi sukazo wannan gida? Tana kallo sai taga mutumin ya ajiye gatarin yabi wadannan samudawa biyu suka fita tare. Fitarsu keda wuya sai dije ta fito bayan kujerar ta nufi wurin su nana. Ai kuwa nana na ganinta sai ta fara ihu a tsammaninta mutumin ne ya dawo. " Kiyi shiru mana kada suji. Bari na kwanceku." Inji dije. Anan nana ta jiyo tana kallonta. " Dije, me ya kawoki nan?" Nana ta tambaya." Yanzu ba lokaci bayani bari sai mun fita." Dije ta bata amsa. Anan ta dauko gatari ta sare kacar da aka dauresu da ita. Sai gasu sun fado kasa timmm. Saida yar karamar kura ta tashi saboda nana mai jikice sosai. Ita kuwa ladiyo ko motsi batayi saboda ta dade da suma. Anan nana ta goyata. Ita kuwa dije sai ta dauki gatari ta jagoranci tafiyar. Gudu sukeyi dakyar suna lalube a cikin duhu. Gidan ya kasance katon gaske sai kace gari. Ga lunguna birjik. Dakuna kuwa ba a magana domin ko ina sune hagu da dama. Suna cikin gudun ne sai suka iso wani wuri da mutane sunyi sahu sai tafiya suke suna waka. Dukkaninsu sun sanya kaya jajjaye. Ba a jin abunda suke fadi cikin wakar domin wani yarene suke fadi. Kayan da sukasa sun lullube dukkan jikinsu yadda ba a ganin kome in banda fuskarsu. Anan su dije suka labe suna kallon ikon ALLAH. Mutanen hade suke maza da mata sai tafiya suke a cikin sahu. Shi kuwa shugaban tafiyar shine a gaba yana jagorantarsu. Mutanen bari biyu ne. Rabi a gefen dama rabi kuwa a hagu. Sai shugaba a can gaba. To a tsakiyar wani irin makeken maciji ne wanda tsawonsa yafi a kirga. Haka kuma fadinsa sai kace daki. Macijin na tafiya cikin kasaita yana wangame baki. PAGE 56 Anan dije ta gane cewa wannan macijin shine aka zanawa wannan mutumin da ya kawota dajin. Kuma irinsa ne ta gani a hannun wannan matar ta cikin bukka. To indai hakane kenan wannan maciji alama ne na cewa kungiyarsu daya. Bayan wadannan mutane sun wuce sai su dije suka bi wata hanya sai faman gudu suke ba kakkautawa. Basuyi wani nisa ba sai nana ta gaji. Anan ta ajiye ladiyo domin ta huta. Ita kuwa dije sai ta kasa zama ta kasa tsayi. Iyaka taje ta dawo gabanta sai faduwa yake. Kai da gani kasan a cikin tashin hankali take. " Wai meye wannan abu? Ke bazaki zauna ba?" Nana ta tambaya. " Ai bazan iya kome ba a yanzu har sai mun fita daga wannan gida." Dije ta bata amsa. " To wai ke yama akayi kika shigo wannan bala i alhali bakya yawo?" Nana ta tambayeta. " Hmm. Da kenan. Yawo yanzu kam......" Anan dije tayi shiru domin jin wata mata ta fito daga wani daki sai tafiya take kwas kwas kwas. A haka matar tabi ta wurinsu ta wuce amma bata gansu ba domin sun manne jikinsu a bango. Gashi kuwa wurin tsananin duhu ne dashi. To bayan matar ta wucene sai suka tashi suka nufi wata hanya. A wannan lokaci ba gudu sukeyi ba. Sassarfa ce sukeyi domin sun fara gajiya da gudun. Har dai nana da take da jiki baya bari ta motsa sosai. " Gaskiya na gaji da goyon nan fa." Nana ta fada. " Ki daure mana tun da bazamu yar da ita ba. Mucigaba da zaga yawa watakila mu samu hanyar fita." Inji dije. Suna cikin maganar sai ladiyo ta fara tari. Anan suka ajeta gefe suna girgizata ko zata mike. Ai kuwa cikin sa a sai ta bude idanu. " Kai, meke faruwa ne?" Ladiyo ta tambaya. " Yanzu dai ba wannan ba. Tashi mu cigaba da tafiya." Inji nana. "Hala ina su lami?" Ladiyo ta tambaya. " Bamu sani ba. Amma mu bincika ko ma gansu." Nana ta kara fada. " Au, ashe baku kadai bane. Kunada yawa kenan?" Cewar dije. " Ai su biyu kawaine bamu gani ba. Wato lami da rabi." Inji nana. " To me zai hana mu bincika ko zamu gansu?" Inji dije. " Nima abunda nake shirin cewa kenan." Cewar nana. PAGE 57 Anan suka tashi su uku sai faman sauri suke ba mai yarda a barshi baya. Suna cikin tafiyar ne sai sukaji motsin wasu a gabansu. Anan suka manne a gina suna jira suga ko su waye. Can sai ga wasu samudawa sun tallabo wasu mata biyu akan kafada. Matan ko motsi basayi kamar matattu. Bayan sun wucene sai su dije sukabi bayansu domin suga ko su waye. Haka suka cigaba da tafiya cikin sanda idan sukaga kamar zasu juyo sai su labe. Cikin wani daki suka ajiye matan daga nan suka fito suka tafiyarsu. Su kuwa su dije da karfi suka fada cikin dakin. Cikin sa a suka tarar da wadanda suke nema wato lami da rabi. Sai dai ita lami rai yayi halinsa domin har sun yanke wasu sassa na jikinta. Anan nana ta fara kuka na tausayawa zuwa ga abokiyarta. Su kuwa su dije sai faman lallashinta suke. Sai da kyar suka ciyo kanta. " Hamir ya cucemu, ya cucemu daya kawomu wannan gida." Nana ta fadi cikin dana sani. " Hamir kuma? Wai har yanzu baku daina wannan sana a taku tabin maza ba? Kenan a can kuka hadu dashi." Dije tace tana dubanta. Anan nana tayi shiru batace uffan ba. Ita dai tasan abunda ta aikata ita da kawayenta wanda shine yayi sanadiyar kawosu wannan gida. Anan suka tallabo rabi sai fifita suke mata. Sai da suka dau lokaci sunayi sannan hankalinta ya dawo jikinta. Suna ganin ta mike sai suka nufi hanyar fita daga dakin. To kafin su fita ne sai sukaji takun wani kamar yanason shigowa ciki. Cikin sauri suka lallabe suna jiransa. Ai kuwa yana shigowa suka yi masa taron dangi. Mai bugu nayi mai cizo nayi har suka kaishi kasa. Anan suka fita dakin suka barshi kwance cikin jini. A wannan lokaci tafiya suke kamar wadanda aka yiwa charge domin duk wanda suka hadu dashi to sai sun masa jina jina. Sai dai idan sukaga mutanen nada yawa to sai su labe har sai sun wuce. Amma daga mutum uku zuwa kasa duk wanda suka hadu dashi to sai sun ji masa rauni. Haka suka cigaba da gudu a cikin gidan amma ko alamar karshe basu gani ba. Duk inda suka duba lungu ne. Haka kuma dakunan gidan sun kasance daki cikin daki har ba adadi. Wannan abu kan mutukar rudasu sai su rasa shin wai gaba sukeyi ko baya. PAGE 58 Wani lungu ne suka shigo. Tafiya sukeyi amma kamar a cikin ruwa suke tafiyar. Sai daga baya suka gane cewa jini ne ya cika lungun gaba daya kamar anyi anbaliyar ruwa. Suna cikin tafiyar ne sai suka fara jiyo karagin wani abu. Kai dagaji kasan wannan abu zaiyi ban tsoro domin wani gurnani ne yake marar dadi. Suna cikin tafiyar ne sai sukaji ladiyo na ihu. Anan ta fadi kwance. Wani abune ya laulaye kafarta sai janta yake iyakar karfinsa. Anan su dije suka kai mata dauki suna jawota amma abun yaki sakinta. Saboda tsabar karfinsa ya janyeta. Anan sukayi tsaye a tsorace kowane sai kalle kalle yake. Can sai sukaji an jefo musu wani abu. Ai kuwa suna dubawa sai sukaga sassan jikin ladiyo an yankata guntu guntu. Kai daban, kafa daban. Kome daban. Ganin wannan abu ya mutukar tsorata su. Ita kuwa dije batasan lokacin data yar da gatarin data dauko ba. Anan suka juya baya da nufin gudu. Kafin suyi nisa sai sukaji suma an laulaye kafafuwansu. Anan aka fara jansu suna ihu sai faman rike gina suke. Ba yadda basu yiba domin su tsira amma ina sai da abun ya janyosu. Ai kuwa suna kawowa gab da abun sai dije ta gane cewa wannan macijin ne da suka gani dazu shine ke jawosu da halshensa. Anan ya wangame baki da nufin suna fadawa yayi musu cin gyada. To kafin su kai ga bakin nasa ne dije ta wankala ta dauko gatarin data yar, saida ta saita da bakin shege ji kake kimissss. Anan macijin yayi kururuwa ya balla a guje. Daga nan sai suka tashi suna nishin wuya. Wata hanya ce suka nausa suna tafiya dakyar. Bayan sun dan yi nisa sai suka kai ga wata katanyar kofa. Anan suka daga kai sama amma basuga karshen tsawonta ba. Kofar ta kasance mai karfin gaske domin karfe ne aka narka kafin ayita. Ba yadda basu yiba domin ganin sun bude kofar amma gam taki budewa. Saboda haka sai suka yanke shawarar su hau samanta. Ai kuwa nan take suka dane dama tanada matattakala. Sai da sukayi nisa saman kofar. Kadan ne babu su kai ga karshe sai ga masu bakaken kaya sun iso wurin. Ko wane rike yake da kwari da baka. Sun lullube fuskarsu da bakin kyalle ba a ganin kome. Anan suka fara sakar musu ruwan kibau su kuwa su dije sai suka kara kaimin saurinsu. PAGE 59 Duk da kasancewar nana mai jikice amma haka ta takarkare bata yarda an barta bayaba. Ita kuwa rabi a wannan lokaci ta fara gajiya sai nishi take dakyar. Wasu daga cikin masu bakaken kayan sai suka dane kofar suna bin sawun su dije. To a wannan lokaci ne aka sako wata kibiya. Cikin rashin sa a ta shige hannun rabi. Anan tayi kara ta saki kofar amma kafin ta fado sai nana ta rike ta da hannu daya. Anan nana ta nuna mata data daure su ci gaba. Can kuma sai aka kara sako mata wata kibiya. A wannan lokaci fadowa kawai tayi domin kibiyar ta huda wuyanta. Su dije na kallo amma ba yadda suka iya. Haka suka tsallake suna jimamin rasa abokiyarsu. Anan suka yo kasa sai taka matattakalar sukeyi har suka kawo kasa. Daga nan suka diro. To

Chapter 5 of 6