Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
ga kasa. Ita kuwa sai murmushin keta takeyi. Tana cikin yi masa wannan lahani sai wani ya shigo dakin. Tana ganinsa saita tsaya. Daga nan sai suka fara wata magana da wani yare. Aswad naji amma bai san abunda suke fada ba. Daga nan kuma sai tayi jifa da yukar tabi mutumin. Aswad na kallo suka fita dakin. To anan ne ya fara tunanin abunyi kafin ta dawo. Domin yasan idan ta dawo to lahanin da zata yi masa sai ya ninka na daxun. PAGE 36 Yukar data jefar a kusa gareshi take. Sai dai matsalar itace ko motsin kirki baya iya yi balantana ya tabuka wani abu. A haka dai ya daure yana mike hannayensa ko zai iya daukar yukar. Dama an ce mai nema na tare da samu ai kuwa cikin sa a ya dauko yukar. Dakyar ya lankwasa ya yanke kacar dake hannunsa na hagu. To kafin ya yanke na daman ne saiga zee ta dawo. Shi kuma yana ganinta cikin sauri ya boye yukar a jikinsa. Daga shigowarta ta kura masa idanu ko kyaftawa batayi. Ai kuwa batayi wata wata ba ta afka masa sai sumbatarsa take. Shi kuwa aswad dama yasan abunda ya tanadar mata saboda haka bai damu ba sai ya bata hadin kai. Saida suka dade suna sumbatar juna amma bata gano cewa ya yanke kacar da aka daureshi da ita ba. A haka abu yayi kamari zee sai nishi take, shi kuwa ya dada kankaneta a jikinsa kamar da gaske. Suna cikin yini ya fito da yukar ya soka mata a kirji. Anan ta fadi tana kururuwa shi kuwa jini ya fallatso. Da sauri ya yanke dayar kacar ta hannunsa na dama. Daga nan ya kara soka mata yukar a dayan kirjin. Sannan ya tallabota ya daura saman bencin da aka daureshi. Anan ya daureta tamau sannan yayi tafiyarsa ya barta tana ihu. A guje ya fita dakin don gudun kada wasu su shigo. Yana cikin gudun ne sai ya lura cewa inda yake takawa akwai digon jini. Saboda haka sai ya yanke shawarar bin sawun jinin domin yaga mai shi. Ai kuwa haka ya cigaba da tafiya guda guda har saida yakai wani daki. Shigarsa dakin keda wuya sai yayi arba da humairat tana nishi daya bayan daya. Cikin sauri yazo wurinta duk jikinta ya rine da jini. Sunkuyawa yayi kusa gareta yana zub da hawayen tausayawa. Tana ganinsa sai tayi murmushi duk da cewa cikin ciwo take. A nan ta jawo kansa har saida jikinsa ya hade da nata. " Ka kulamin da kanka. " Haka ta fadi cikin kunnensa daga nan bata kara cewa kome ba. Iyaka dai yaji kalmar shahada wadda itace kalmarta ta karshe. Aswad yayi kuka sosai domin a cikin ransa ba yarinyar da yakeda muradin aure irin humairat. Sai kuma gashi ta tafi ta barshi. A haka ya rungumeta a jikinsa yana kuka cike da tausayawa. Saida ya dau lokaci a hakan kafin ya saketa ya fita dakin. PAGE 37 A haka aswad ya fito dakin cikin jimamin rasa humairat. Tafiya yake dakyar kai da gani kasan ya gaji sosai. To anan ne ya fara bidar hanyar fita daga gidan domin a ganinsa namil da saudat sun mutu. Gidan ya kasance katon gaske sai kace gari. A haka aswad yayi ta kalwade amma ya kasa gane hanyar fita. Duk inda ka duba lungu ne cike da dakuna birjik. Sai dan neman duhun daya mamaye gidan gaba daya. Ga fitilllu amma basaci sosai saboda haka mutum ba ko ina yake gani ba. Kuma kasancewar lokacin a cikin darene. To sai duhun ya karama gidan ban tsoro. Shi kuwa aswad sai tafiyarsa yake yana tuntube da gawawwakin mutane. To yana cikin tafiyarne sai yaji gudun wani kamar an biyo shi. Anan ya labe domin yaga ko su waye. Ai kuwa suna wucewa ta wurinsa sai yaga wadannan samudawan ne masu bakaken kaya suka biyo wani da nufin kasheshi. A guje ya bisu da nufin yin taimako. Koda ya cimmusu sai ya tarar sun kama mutumin zasu sareshi. To kafin su aiwatar da nufinsu ne ya taresu da fada. Gawawwakin mutane ya rinka dauka yana dukansu dashi. Shi ma mutumin na ganin haka sai ya samu damar kubcewa. To anan aka fara bata kashi tsakanin wadannan miyagu dasu aswad. Saida suka dau lokaci suna fadan kafin su samu damar kai mutum biyu kasa cikin su goma. To da sukaga fadan ba mai karewa bane balantana gashi sun fara gajiya. Cikin wayo suka runtuma a guje su kuwa miyagun suka bisu. Ba inda wadannan miyagu basu duba ba lungu lungu sako sako amma basu gansu ba. Saboda haka suka juyo da nufin komawa. Su kuwa su aswad sai suka fito daga maboyarsu. To anan aswad ya gane cewa namil ne ashe dama bai mutu ba. Cikin jin dadi suka yiwa juna barka tare da cigaba da binciken gidan ko xasuga saudat. " Amma fa naji dadin ganinka abokina, ina fatan dai ka gano inda su nabilat suke?" Namil ya tambaya. Anan aswad yayi shiru bai tanka ba. " Lafiya kuwa ya naga kayi shiru?" Ya kara tambaya. " Yanzu dai muje mu nemi saudat, domin nabilat da humairat sai dai muyi musu addua." Cewar aswad. PAGE 38 Anan namil ya done kansa cikin jimamin wannan magana. Daga nan sai suka mike hanya suna tafiya suna juyawa don tsoron kada a kawo musu harin ba zata. Sai da sukayi tafiya mai dan nisa kafin su fara jiyo ihu a cikin wani daki. A hankali suka bude dakin. Ai kuwa shigarsu keda wuya suka tarar da saudat a daure saman kujera. Wani mutum ne fuskarsa a cabe sai kace dodo. Da wasu dogayen hakora da yake fama dasu marar kyan gani. Yankan sassan jikinta kawai yake da yuka tana ihu. Mutumin na juyowa sai yayi arba dasu. Cikin sauri sai ya dauko gatarinsa yayi cikinsu. Namil ne ya tare shi suka kaceme da azababben fada. Shi kuwa aswad sai ya nufi wurin saudat da nufin kwanceta. Bako shakka mutumin yafi namil karfi nesa ba kusa ba amma duk da hakan bai yarda an kaishi kasa ba. Wani takobi ne ya dauko dake rataye a bangon dakin. Dashi yake kare harin wannan mutumi mai siffar dodanni. Shi kuwa aswad yana kwance saudat sai ya turata waje domin ta jirasu. Yana dawowa sai yaga mutumin ya kai namil kasa yana neman hallaka shi. Da sauri da dauko wata kwalba ya makama mutumin da kai. Ai kuwa dole ya saki namil. Anan aswad ya tallabo namil suka fita dakin. Fitarsu keda wuya sukaci karo da miyagun sai nemansu suke. Shi kuwa namil baya iya gudu domin akwai rauni a kafarsa. Haka dai aswad ya rika shi suka cigaba da gudun su uku. Su kuwa miyagun sai halbo musu kibiya suke. Suna cikin gudun ne sai sukaji namil yayi wata kara. Anan suka duba sai sukaga ashe yuka ce ya taka har ta huda kafarsa ta fito. Ba yadda basu yiba su fitar da yukar amma suka kasa. Gashi kuma yukar a kasa take idan ba a fito da itaba to bazai iya tafiya ba. " Ku tafiyarku wata kila ku tsira da ranku. Ku barni nan domin nasan lokacina yazo." Haka namil ke fada yana zub da hawaye. A wannan lokaci kuma miyagun sun kusa cimmusu. Duk da hakan aswad bai saurari maganarsa ba. A haka yayita kokarin fitar da yukar amma abu ya faskara. To anan ne suka kyaleshi domin miyagun na gab da cimmusu. PAGE 39 A guje suka shiga kwana sai kace motar da ba burki. Bayan sunyi nisa kadan sai suka jiyo karar namil. Anan suka fara zubar da hawaye domin sun san cewa an kashe shi. A haka aswad da saudat suka cigaba da mugun gudu sai kace ransu zai fita. Cikin gudun ne suka samu kansu cikin wani daki. Sai wata katanyar makwarara lake a kasan dakin. Aswad yayi mamakin ganin wannan makwarara domin tayi kamada wadda ya shigo cikin gidan. Amma kuma yasan ba ita bace domin shi wannan dakin ko alamar jini babu. Kamar an dade ba a yi amfani dashi ba. Cikin makwararar aswad ya shige ita kuwa saudat ta bishi a baya. A haka suka cigaba da tafiya har suka samu damar fitowa daga gidan. To bayan sun diro ne sai suka kalli juna cikin jin dadi suna mamaki har yanxu cikin darene duk dadewar da sukayi a gidan. Tsayuwa sukayi na dan lokaci suna ma gidan kallon tsaf. Wato makeken gidan sama ne mai ban tsoro. Haka shima dajin cike yake da dogayen itace sai furanni ko ina. To suna cikin wannan dube duben ne sai sukaji motsi a bayansu. Dubawarsu keda wuya sukaci karo da wadannan miyagun suna fitowa ta makwararar da suka fito. Ai kuwa cikin karfi su aswad suka ranta a guje ba sassauci. Gudu suke suna tsallake ramukka sai kace doki. Saida suka dau lokaci suna gudun sannan suka fara hango dishi dishin titi. To anan suka kara kaimin gudunsu domin su cimma titi su gani ko xasu samu mota. Su kuwa wadannan miyagu sun rufa musu baya sai halbinsu suke da kibiya. Cikin gudun ne saudat ta fada wani kwazazzaben rame mai shegen zurfi. Anan aswad ya tsaya yana tunanin yadda xai daukota ta. Ita kuwa sai ihu take domin tasan da sun zo wurin to karyarta ta kare. Da sauri aswad ya katso bishiya mai dan kwari. Anan ya tura mata, cikin sa a kuwa ta rike. A hankali ya cigaba da jawota har saida ya fito da ita. To anan ya juya da gudu da nufin ta biyoshi. Sai da ya dan yi nisa sai yaji tsit kamar bata biyoshi ba. Ai kuwa yana juyowa sai yaga ashe miyagun ne suka halbo mata kibiya har ta nutse a cikinta. Yayi nufin ya taimaka mata amma dole ya fasa domin suna gab da karasowa. A haka ya kyaketa suka isar da ita shi kuwa yayi ta kansa. PAGE 40 A wannan lokaci hasken alfijir ya fara fitowa. Haka aswad ya cigaba da gudun har saida ya kawo bakin titi. Anan ya hango wata yar karamar mota ta yan sanda. Hannunsa ya fara dagawa yana nuni cewa su tsaya. To bayan motar ta tsaya ne sai yaga ashe mace ce yar sanda ita kadai a ciki. Anan ta kalleshi taganshi jina jina. " Malam lafiya kuwa?" Ta tambaya. " Ba lafiya ba. Don ALLAH ki tamikeni. Kasheni zasuyi." " Su waye?" Ta tambaya. Bai tsaya amsa mata ba iyaka ya bude motar ya shigo. " Muje kawai zan miki bayani." Ya fada. Anan ta tayar da motar tana dubansa cike da mamaki. " Hala meye sunanka?" " Aswad." " Ni yar sanda ce kuma zan taimakeka idan har mun isa cikin gari." Haka ta fada tana juya sitarin. " Kada ka damu sunana anisa." Ta fada bayan ta kama hanyar fita daga cikin dajin. A haka aswad ya samu damar tsira daga sharrin wadannan miyagun mutane bayan ya hadu da anisa. Maita gaskiya ce. Kuma koina akan samu mayyu. Sai dai har yanxu ba a san mafarinta ba, da kuma yadda ake gane masu fama da ita ba. Aswad ya tafi da zimmar cewa kul a jima kul a dade sai ya fanshi kisan gillar da aka yiwa abokansa. Haka itama a anisa, wannan dalili shine yasa ta yanke shawarar zama yar sanda domin ta fadada bincike domin ganin bayan wadannan mayyu. A duk lokacin daka tsinci kanka cikin daji, kada kayi tsammanin cewa irin hakan bazai iya faruwa ba. Ka dauka cewa fiye da hakan kan iya faruwa. Wannan ba labari kawai neba. Gaskiyace, da gaske akwai mayyu masu irin wannan dabi a can a wani gida. Gidan yana a cikin daji. Sai dai har yanzu ba a san inda dajin yake ba balantana a gano gidan. Aswad da anisa zasu hada kansu domin ganin sun cika burinsu na ganin cewa wadannan mayyu sun kare, to abun tambaya anan shine ta yaya zasu cika wannan buri tare da daukar fansar kisan da aka yiwa abokansu? The story continues on the third version of the last episode........TAFIYAR DARE 2 MAYYUN JINI AUTHOR : ABDUL KING ARTICLE EPISODE 3 PAGE 41 Ni anisa, a kullum idan nayi tunani nakan yi mamakin wannan duniyar da muke ciki, yadda al amurra suka tabarbare ba mai tausayi balantana hakuri. Na gano hakan ne sanadiyar wani lamari dana gani ya faru akan idona. Wato hakuri shine maganin zaman duniya. Saboda haka duk wanda bai yi hakuri ba, to bazai ga hakuri ba. Talauci masifa ce, fitina ce kuma bala i ne, wannan dalili shine yasa akace kowa ya tashi ya nemi nasa ba don komi ba sai don kariya daga wannan masifa ta talauci. Bari in fada maka wani labari na wata yarinya wadda wanna masifa ta rashi ta faru akanta. Sanadiyar hakan yasa al amurran rayuwarta suka lalace sabida kin yin hakurin da tayi. Sunanta khadija, akan lakanceta da dije, haka ta kasance cikin wannan sababi na talauci ita da iyayenta. Abbanta Dan shago ne dashi sai kuma noma da yakeyi duk shekara. Wataran sukan yini basusa hatsi a baka ba saboda masifar rashin da suka tsinci kansu a ciki. Wannan rayuwa da khadija samu kanta a ciki ya jefata halin kaka ni kayi. Wanda daga karshe ta kasa jurewa da jarabawar da aka yi mata. Anan kuma ta fara dana sanin abunda ta aikata. Kafin dai muje ga labarin bari mu waiwayi abunda ya faru a baya. Bako shakka na gama binciken da nake gudanarwa. Kuma a yanzu hakan ina kan bakana na daukar fansar kisan gillar da aka yiwa abokaina. Sai dai har yanxu akwai abunda nakeso na tabbatar kafin na fara aikin. Zee da hamir sune manyan makiyana. Amma da sannu zasu gane kuskurensu. Kuma da sannu zasuyi dana sanin abunda suka aikata. Yanzu bari muje ga labarin khadija da da kuma makasudin faruwarsa. Tare da jin yadda muka kare da wadannan miyagun makiya nawa masu farauntar mutane. A duk lokacin dana tuno abunda ya faru nakan yi bakin ciki sosai. Amma duk lokacin dana tuno abunda na shirya sai nayi dariya mai yawa. Nasan cewa kul a jima kul a dade assiri zai tonu. Kuma karshen alewa kasa. Haka kome nesan jifa kasa xata dawo. Wata rana a cikin wani kauye........... PAGE 42 " Wallahi ni umma yunwa nakeji." " Haba dije, yanzu kiyi hakuri kije rafi sai ki debo mana ruwa. Idan malam ya dawo maga abunda ya samo mana ko." " To ni kullum sai na yini ba abunda naci, kuma abincin ko dadi babu." " Yanzu dai kiyi hakuri diyata ta kaina. Sheka maxa ki debo mana ruwan." Haka dije ta karbi tulun badon tasoba. Tafiya take tana gunguni cikin takaici. " wani shegen tuwo kamar kanacin dussa. Da wata banzar miya ko gishiri babu. Mtsss." Haka ta fada cikin gunguni bayan ta kai kofar gida. " Laaaa dije, dama yanzu nake cewa in biya miki sai gashi kin fito, yanzu dai taka muje nasan rafin nan ya cika." Inji kawar dije wato mairo. A haka dai dije ta daure ta sakar mata dan guntun murmushi. Daga nan sai suka kama hanyar zuwa rafi. Ita kuwa mairo ta kasance mai surutu sosai. Tafiya suke sai zuba take ba sauki. Tun dije tana iya amsawa har takai sai dai tace to. Sai da suka kai bayan gari sannan suka iso rafin. Mutane maza da mata kowa sai sha anin gabansa yake. Masu dibar ruwa nayi masu wanki nayi. Wannan lokaci marecene sanya sanya domin magrib ta gabato. Dije ta kasance kyakkyawa abun kallo, saboda haka daga isowarsu duk samarin dake wurin suka tsura mata ido kowa sai fadin albarkacin bakinsa yake. Ita kuwa dije bata damu ba domin ta saba da irin wannan kallon da ake mata. Kai da ganin tafiyarta kasan ba lafiya. Domin yinin yau komi bata ciba tun da safe. A cikin shagon nasu kome babu domin duk sun cinye abunda ke ciki. Tun da safe abba ya fita nemo abunda zasuci amma gashi har marece bai dawo ba. Dije ta kasance mai tarbiya, ladabi ga kuma kunya. Sai kuma tarin ilimin addinin da take dauke dashi. Dakyar ta sunkuya tulunta a cikin ruwan. Ai kuwa tana janyowa sai santsi ya kwasheta cikin ruwan. Ita kuwa mairo dama a kusa gareta take. Cikin sauri ta ajiye tulunta ta shiga cikin ruwan domin ceto dije. Anan ta tallabota tare da tulunta. PAGE 43 " Sannu dije." Wasu yan mata da suka kewayeta suna mata jaje. Can kuma sai ga gungun samari sun iso wurin. " To ita ya jikin nata." Babba daga cikin samarin yayi magana. " E to da sauki." Mairo ta amsa. " To ALLAH tsare gaba." Ya kara fada. A haka aka yita zuwa ana ma dije jaje. Ita kuwa kwance take sai nishi take dai dai sabida ruwan da tasha. Bayan wani dan lokaci ne mutane suka fara watsewa aka bar mairo da dije. Ita kuwa mairo sai fita take mata dai dai domin ta farfado. Duhu ya farayi a wurin sai kuma iskan dake hurawa mai shiga jiki. Ita kuwa mairo sai karkarwa take tare da dube dube cikin tsoro. Suna cikin wannan hali ne sai taga an hasko musu wani haske. Anan mairo ta juya a mamakinta sai taga mota na xuwa wurinsu. Tayi mamaki sosai da ganin motar domin a kauyen nasu ko mai mashin babu. Ita kanta rabonta da taga mota an fi shekara. Anan ta kurawa motar idanu har ta iso wurinsu. Ita kuwa dije sai ta fara farfadowa. To bayan motar ta iso gab dasu sai sukaga wani mutumi ya fito daga ciki. Shigarsa ba irin ta mutane bace domin kayan nasa dai abun tsoro ne. Haka siffar jikinsa domin kirar samudawa ce dashi. Dije na ganinsa sai ta tashi da karfi. Hannunsa ta kalla daga nan sai ta ja da baya. Anan ta juya da nufin barin wurin. " Ke baki dauki tulunki ba." Mairo ta fada amma ina dije bata amsa ba sai tafiyarta kawai take. Anan ta dauko tulunan ta ba dije nata daga nan suka fara sauri domin su bar wurin. Shi kuwa mutumin sai ya bisu da kallo har suka bace masa da gani. " Dije yau naga abun mamaki." Mairo ta fada tana waige waige ta gani in bai biyosu ba. " Wai ko kinga hannunsa?" Ta tambaya. " Hmm, ni ban taba ganin wanda aka yiwa zanen maciji ba a hannu." Mairo ta fada cike da mamaki. " Maciji fa kikace?" Dije ta tambaya. " E mana, wai kina nufin bakiga hannunsa ba. Ai zanen maciji ne aka yi masa a hannu kuma irin wannan zanen da baxai goge ba har abada." Cewar mairo. PAGE 44 " To kuwa indai hakane abunda na gani ya zama gaskiya." Inji dije. " Hala me kika gani?" Mairo ta tambaya. Anan dije tayi shiru bata amsa ba. " Abunda nakeso dake shine idan munje gida kada ki fadawa kowa abunda ya faru." Inji dije. " Kada ki damu kawata an gama." Mairo ta fada. Haka suka cigaba da tafiya har suka iso cikin gari. Daga nan suka yi sallama kowa ya kama hanyar gida. Ai kuwa da shigar dije a gida sai ta tarar dasu umma sunyi zaune zugum sai kace wadanda aka yiwa mutuwa. Dan kanenta ne a kusa ga umma ya gincira sai cizon baki yake sabida yunwa. Shi kuwa abba ya debe hular sai zufa ke kwarara a jikinsa. " Umma kada dai kicemin yauma ba a samo ba." Dije ta fada bayan ta ajiye tulun. Anan suka jiyo suna kallonta amma ba wanda ya tanka mata. " Innalillahi wainna ilaihir raji un. Gaskiya ni na fara gajiya wannan abu dame yayi kama. " Anan dije ta shiga dakinta sai rusa kuka take. Tana cikin kukan ne abba ya shigo yana lallashinta. " Haba dije kiyi hakuri mana, shi rashi na Allah ne kuma samu na Allah ne, kuma nasan Allan nan daya jarrabemu da wannan rashi bai manta damu ba. Iyaka dai...." " Iyake me?" Dije ta katseshi. " Kana zama da mutum kullum babu. Ni nayi dana sanin kasancewa a cikin wannan gida. Da ace mutum yana zabar inda yakeso da bazan yarda na fito ta wannan zuri a ba." Haka dije ta fada cikin kuka. Shi kuwa abba sai ya matso kusa gareta yana shafa gashin kanta. " Haba diyata ya kina wannan magana. Sai kace wadda bataje arabiya ba. Ni a ganina kome nufin Allah ne. Kuma Allah yasan abunda yasa ya jarrabemu da wannan rashi. Tana iya yiwuwa ya gwada mu ne ya gani ko zamu iya hakuri da masifar da muke ciki. To kinga kuwa idan bamuyi hakuri ba bazai taba yaye mana wannan masifa da muke ciki ba. " Jarabawa? Ai wannan jarabawa tayi yawa kome hakurinka dole ka gaji." Cewar dije. " Haba dije kada kiyi sabo fa." " To idan nayi sabo sai me?" PAGE 45 Anan dije ta tashi da karfi. " Ni tafiyata zanyi bazan iya zama cikin wannan talauci ba." Shi kuwa abba sai yabita yana lallashinta. To anan ne umma ta shigo da taji hayaniyar tayi yawa. " Haba dije yanzu idan kika fita to ina zaki. Mu fane iyayenki kuma bakida wasu wadanda suka fimu." Umma tace bayan ta riko hannunta. " Ni bazan zauna bakin talaucin ku ya kasheni ba. Baci ba sha Kullum haka." " Kibar daga murya kada makwabta suji." Umma ta tsawatar. " To idan sunji sai me? Ai abunda na fadi gaskiya ne ba karya ba." Anan dan kanenta ya sheko ya rungumeta. " Yaya kada ki tafi ki barmu mu kadai a nan." Anan dije tayi shiru tana duban kanenta daga nan kuma sai ta koma dakinta tayi kwance ruf da ciki. A haka sukayi bacci basuci kome ba cikin rashin jin dadi. Tunda kulu kulun safiya umma ta farawa bugawa dije kofa domin ta tashi. Cikin magagin bacci ta bude kofar sai hamma takeyi. " Yaufa ki tashi akwai aiki a gidan nan. Yanzu nan koje ya kawowa abbanki sadakar dawa tiya uku. " " Laaa, dawa. Hehehehe." Anan dije ta fada jikin umma ta kankaneta cikin murna. Tun bata wanke baki ba ta nufi dakin umma a guje. Dawar ta dauko tiya uku ta fara durawa cikin bakinta sai da umma ta jinye bokitin. " Wai dije lafiyanki kuwa. Kinacin dawa danya idan ta halakaki fa. Yanxu yi maza ki shirya akwai inda zan aikeki. " Bayan dije ta kimtsa ne sai ta shiga dakin umma domin taji sakon da zata bata. Bayan an mata bayanin abunda akeso tayi sai ta fito daga gidan. Tafiya takeyi tana taku dai dai. Yau dai fuskarta cike take da annuri ba kamar jiya ba. Wani lungu ne ta shiga inda gidaje dai dai kune. Haka dije ta cigaba da shiga lunguna lunguna tana dan wakenta na yan mata. Bayan tayi tafiya mai nisa ne sai ta kawo gonar abba. Anan ta gyara daurin kallabinta kada ya fadi. PAGE 46 Ai kuwa tana kutsa kai ciki sai ta farajin nishi na fitowa a bayan wata bukka. A hankali ta fara tafiya domin taga ko waye. Tana kaiwa wurin sai ta tarar da mairo na fesa wani irin zawo. Da karfi mairo ta mike tsaye saboda tsoro. Batasan lokacin fa fitsari ya fara fita daga tsaye ba. " Shegiya dubi gabanki." Dije ta tsawatar. " Wai na manta." Cewar mairo bayan ta dauko zanenta. " Ashe dama kece ke mana xawo tun da safe ko?" Dije ta tambaya. " Haba kawata yau fa dai ne. Kuma yau din ma matsiyata yayi." Inji mairo cikin kunya. " To meye kika zoyi nan?" Dije ta tambaya. " Au, har kin manta cewa muna fitowa tsintar kara? Yanxu haka fa girki ne za ayi shine aka tadani naxo tsintar karan." Mairo ta fada. " Hmm, yar kawata kenan." Mairo ta fada bayan ta matso kusa ga dije da nufin rike hannunta. Ai kuwa da karfi dije taja da baya tana like hanci. " Gaskiya wari kikeyi sosai, yanxu dai muje ga gulbi can ki wanke wannan kazantar dake jikinki." Inji dije. " Ni din ke wari?" Mairo ta tambaya. " E mana, koda yake ance gwalo bayajin warin jikinsa." Dije ta fadi cikin yanga. " To yayi zan rama ai, yanxu dai muje gulbin ko bazaki rakani ba?" Mairo ta fada cikin murmushi. " Allah zance baxan jeba." Inji dije " To yanzu dai kiyi hakuri muje." Mairo ta fada cikin wasa. Haka suka cigaba da tafiya suna fira har suka kai bakin gulbin. Da zuwa mairo ta nufi wurin da nufin shiga. Kafin ta kai sai taji an katsa mata tsawa. " Kai, uban waye ke lekena?" Anan sukaga nana ta fito daga cikin gulbin wai ashe wanka takeyi a ciki. Nana ba karamar shakiyiya ce a garin ba domin har maza suna shayinta. Ta kasance katanya kakkarfa mai siffar karfi. Anan ta fito daga cikin gulbin zigidir tana duban su dije. " Wallahi ni zanci uban yaro. In banda iskanci me ya kawoku nan ne?" " Kiyi hakuri nana bamusan kina ciki ba." Mairo ta fada bayan ta done kanta. PAGE 47 Anan nana ta matso kusa dasu. Su kuwa kowane jikinsu sai dar dar yake kada suji mazga. Sun san da cewa nana bata buguwa a garesu. A wannan lokaci sun mata kallon tsaf. Bako shakka nana ba karamar katanya bace. Damatstsan nan cike suke kai kace yar dambe. Zanenta ta dauko ta yafa. " Wallahi kun kuru yau banajin fada da sai naci ubanku. Shegu masu kan goriba." Anan nana ta bangajesu ta wuce. " Hmm, shegiyar ji tafiyarta. Kato kenan." Mairo ta fada cikin karamar murya. " Ke me kikace?" Nana ta juyo. " Haba nana ai badake takeba. Wannna magana fa tsakaninmu ne." Dije ta bata amsa. " Au, kin kuru." Nana ta fada bayan ta cigaba da tafiyarta. Bayan nana ta wucene sai mairo ta shiga gulbin. Anan ta tsaftace kanta daga nan suka nufi wurin tsintar karan. Suna gamawa suka nufi hanyar gida. To akan hanyarsu ne suka gamu da ummar dije. " Wai me ya tsayar dakene tun daxu?" Umma ta fada. " Ba kome umma." Dije ta bata amsa. " Tun daxu nakejin tsoro,akan hakan yasa nace dole naxo na duba ko lafiya." Umma ta fada bayan sun fara tafiya tare. A haka suka cigaba da tafiya suna fira su uku, sai da suka kawo wata mararraba sannan suka rabu. Dije da mamarta suka nufi hanyarsu daban itama mairo haka. A haka mairo ta cigaba da tafiya ita kadai, kasancewar tun da safene ba kowa kake gani a hanya ba. To anan hanya tabi da ita ta wannan rafin da dije ta fada jiya. Ai kuwa tana kaiwa wurin sai ta tarar da wata mota. Bayan ta kusa cimma motar ne sai taga wata mata ta fito daga cikin motar ita kadai. Anan aka fara kallon kallo. Can sai matar tayi magana ta kirata. Bayan mairo tazo wurin sai matar ta fara

Chapter 4 of 6