Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
wannan dajin wata kila ko zamu iya cimma gari idan yaso sai mu kira bakanike yazo ya duba." Inji nabilat. " Wannan tunani ne mai kyau. Inaga sai ku jiramu nan. Ni da namil sai muje." Inji aswad. " Aa, bazaku tafi ku barmu a cikin wannan daji mai ban tsoro ba. To amma me zai hana muje tare.?" Inji saudat. " To yayi ba matsala muje din." Inji aswad. Anan suka raba titi suka shiga cikin dajin mai cike da dogayen itatuwa sai furanni koina. Aswad da saudat su kadaine keda torch-light. Daji ne iya daji mai ban tsoro. Koina ka duba sai itace. A kasa kuwa ciyayi ne masu sarkako. Aswad shine jagoran tafiyar sai namil a gefensa. Su kuwa yan matan sai binsu suke kowace jiki na karkarwa kamar ace kyat su ruga. PAGE 24 " Wai kuna ganin zamu iya cimma gari anan kuwa? Naga tafiya muke amma ko alamar gona babu. Koina sai itace da ramukka." Inji aswad. " Gaskiya nima fa abunda nake gani kenan. Ai yanxu inaga kamar munyi minti talatin muna tafiya ko." Cewar saudat. " Miye minti talatin? Ai munfi. Mun dade fa a wurinnan." Nabilat ta bata amsa. " Ke dubi gabanki." Humairat ta tsawatar. Ita kuwa saudat bata jiba sai firarta take. Ai kuwa kafin kaceme sai tayi tuntube da wani kututturen icce. Sai da tayi yar karamar kara kafin ta juya da nufin faduwa. Shi kuwa namil da jin ihunta sai yayi sauri ya juyo. To kafin ta fadin ne yayi saurin rikota.Anan ya tallabota har saida ta mike tsaye. " Wai,na kuru. Nafa gode dan uwa." Cewar saudat. " Kada ki damu saudat ba kome." Inji namil. Anan saudat ta kalli humairat da nabilat. " Ku kuma da kuke tumaki kuna ganin zan fadi amma a cikinku ba wadda zata iya taimaka min." Injita. " To miye ruwanmu a ciki. Ai naso ace kin fadi kin karkarye muga yadda zakiyi." Cewar humairat. " Iyeee. Ni ko?" Saudat ta tambaya. " To idan akace kedin me zakiyi?" Nabilat ta fadi cikin wasa. " Yanxu dai ya isa ko kuwa sai naci uban mutum ne?" Saudat ta hasko musu fitila. " Ahayye. Rassss." Tare suka fadi nabilat da humairat. Daga nan sai suka taba hannu suna dariya. " Shegiya ke har wani karfi ne dake. Dubarta. Yar ramamma ba jiki sai tsangwama." Cewar humairat bayan ta kulle idonta saboda hasken fitilar da aka hasko mata. " Ji yadda take tafiya burtum burtum sai kace agwagwa. Wai damu zatayi fada." Inji nabilat. Anan dai sukayita tsangwamar saudat tun tana iya ramawa har saida tayi shiru saboda abun yayi yawa. Su kuwa su aswad saurare kawai suke suna dariya. PAGE 25 Saboda wannan fira da suke sai da sukayi tafiya mai nisa ba tare da sun sani ba. Duk da kasancewar dajin mai tsananin duhu ne amma haka suke tafiya sai kace ba mutane ba. To suna cikin tafiyar ne sai fitillun su suka fara billin bilin. Wato su kawo su dauke. A wannan lokaci kuma suka fara jiyo ihun wasu daga can nesa. Ai kuwa daga jin haka sai hankalinsu ya tashi. Anan suka fara gudu domin ganin ko su waye. Sai da sukayi gudu mai dan nisa kafin su kawo inda abun yake. To anan suka labe bayan itatuwa suna ganin abunda ke wakana. Wasu mutane ne masu kirar samudawa sanye da bakaken kaya. Ba a ganin fuskarsu domin sun rufeta da bakin kyalle. Kowanensu ya rike kwari da baka tare da sauran makamai masu ban tsoro na dangin takubba. Wasu mutane ne suka kamo su biyu mace da namiji sai ihu suke. A gaban idonsu wadannan samudawan suka kashe macen da namijin. Daga nan kuma sai suka ja gangar jikinsu suka wuce da ita wani wuri. Bayan wucewar su keda wuya sai su aswad suka fito daga maboyarsu a tsorace. " Bako shakka dole mu bar wannan dajin. Domin wadannan mutane da muka gani na taba jin labarinsu da dadewa. Sai gashi kuma kaddara tasa munxo wurinsu. Kamar yadda naji ance suna...." To kafin nabilat ta iyar sai sukaji ihu a bayansu. To anan sukayi cirko cirko suna tunanin abunyi. Ai kuwa sai ga wata mata a guje tazo wurinsu. " Don Allah ku taimakeni. Kasheni zasuyi. Gasunan tafe." Haka matar ke fadi tana kuka. To anan sukazo wurinta suna lallashinta tare da tambayarta abunda ke faruwa. Amma saboda tsoron daya dabaibayeta sai ta kasa bayani iyaka dai abunda take fadi shine su taimaketa. Wannan abu ya mutukar tayarwa su aswad hankali domin sai suka rasa abunyi. " Gaskiya baxan iya zama a wannan wuri ba. Ni inaga kawai mu koma bakin titi inda motarmu yafi mana sauki." Humairat ta fadi cikin tsoro. Ai kuwa take ta nufi hanyar da suka fito wai ta tafiyarta. Cikin sauri aswad ya jawo hannunta. PAGE 26 " Wai kinada hankali kuwa? Hanyar da muka fito itace wannan matar ta fito kuma tace sun biyota ne don su kasheta. To idan kikaje kika tarar dasu fa. Ni inaga kawai mu manta da komi muyita gudu har mu kure dajin mu gani ko zamu samu taimako." Inji aswad. " To ai ko yanzu bamu tsira ba. Domin hanyar da kakeso mubi itace mukaga sun shiga tare da gawawwakin mace da namijin da suka kashe." Inji Humairat. To anan suka rude suka rasa abunyi. Gaba kura baya hayaki. Wato idan sukaje gaba basu tsira domin zasu iya haduwa dasu haka ma idan suka juya baya inda suka fito shima basu tsira ba. " Ni inaga kawai mubi shawarar humairat cewa mu koma inda muka fito wurin motarmu. Inaga zamu iya bacci a can kafin gobe da safe sai musan abunyi." Inji namil. " Wannan gaskiya ne ina bayanka." Inji nabilat. " Nima haka." Saudat ta fada Daga nan sai suka amince cewa xasu koma ta hanyar da suka fito saboda gudun kada su hadu da wadannn miyagu masu kashe mutane. To anan suka juya tare suna tafiya da sauri cikin tsoro ba mai yarda a barshi baya. Ita kuwa wannan matar da suka gani sai tayi shiru ta cigaba da binsu. Ai kuwa basuyi wani nisa ba suka farajin hargowa. Wasu kibiyoyi ne aka fara sako musu cikin rashin tsammani. Ai kuwa sai kibiya ta shiga wannan matar bakuwa. Anan tayi kara ta fadi. Su kuwa saura suka runtuma baya a guje. Aswad kawaine ya tsaya taimakonta shima da yaga abun yafi karfinsa dole yayi ta kansa. Gudu yake suna binsa sai halbi kakeji ta koina. Yana cikin gudun ne yaji karar matar. Anan yasa a ransa cewa sun kasheta. A haka aswad yayi gudu iya karfinsa. Sai dakyar ya cimma abokansa. To daga nan ne suka tsaya suna haki bayan sunji cewa kamar an daina binsu. " Wai yanzu meye abunyi kenan. Ku a ganinku haka zamu cigaba da gudu da mun gansu kenan? Gaskiya inaga ya kamat muyi fito na fito domin musan abunda suke nema a gunmu." Cewar saudat. " Bama shiba. Ya kamata musan ko su waye, kuma me yasa suke kashe mutane, kuma idan sun kashe to me sukeyi da sauran gangan jiki." Cewar namil. PAGE 27 " Duk kunada gaskiya, amma maganar fito na fito dasu bata tasoba domin sun fimu kome, da farko dai sun fimu yawa, ga kuma makamai, to ya za ayi mu yaki wadannan. Ni a ganina kawai mu cigaba da gudu har zuwa karshen wannan daji wata kila ma samu taimako." Inji aswad. " Da gaskiyarka aswad, wannan itace kawai mafita." Cewar humairat. " To amma yanzu me zai hana mu samu wuri a nan muyi bacci zuwa gobe sai musan tayi." Cewar nabilat. " Hmm, to ke in banda abunki ai yanzu ba wanda zai iya bacci a cikinmu saboda wannan tashin hankali da muke ciki." Inji aswad. " Inaga dai mu daure mu cigaba da gudun kafin su iso nan." Ya kara fada. Duk da kasancewarsu sun gaji, amma haka suka daure suna tafiya da sauri don gudun wadannan mugaye masu farautar mutane. Cikin wannan tafiya ne wani dan reshen bushiya ya fado duum. Ai kuwa nan saudat ta ci taya sai da suka tarota domin ita a zatonta sune suka kawo musu harin ba zata. " Wayyo kafata, ni gaskiya na fara gajiya." Cewar nabilat bayan ta zauna. " Wai me kike nufi ne, ki tashi mana mu cigaba." Inji aswad. " Kai mu hutu zamuyi, idan kana iyawa to ka tafi kai dai." Inji humairta bayan itama ta zauna. Ai kuwa nan suka yi zamansu suna nishi dakyar. Suna cikin hutun ne bacci ya sacesu amma banda aswad domin yana nesa dasu. Saidai duk abunda ke faruwa yana kallo. Kai da ganin fuskarsa kasan yana cikin rashin jin dadi. To anan ya tashi da nufin tayar dasu sai dai abunda ke damunsa shine kishin dake busar da makwogoronsa. To anan ya fara shawara ko ya tayar dasu ko kuwa ya fara samo ruwan da zaisha. Can sai yaji kishin ya damesa. Saboda haka baiyi wata wata ba sai ya fara bincike ko zai samu tafki a wurin. Sai da yayi tafiya mai dan nisa kafin ya cimma magudanar ruwa masu tafiya. Anan ya duka ya kwankwada har saida yayi hamdala. Mikewarsa keda wuya sai ya fara jiyo ihun wasu. Ai kuwa a guje ya juya domin ganin ko su waye. PAGE 28 Cikin kankanin lokaci ya isa wurin daya bar su namil na bacci. A mamakinsa baiga kowa ba. Anan ya tsorata, to kada dai ace wadannan miyagun sun zo sun wuce dasu. Anan ya fara kiran sunayensu daya bayan daya amma ba wanda ya amsa. Can kuma sai ya cigaba da jin ihun. Daga nan ya runtuma a guje a inda yakejin sautin na fitowa. Yana cikin gudun ne sai ya tarar da wasu gungun miyagu sun farauto wasu mutane sai jansu suke da kasa. Anan ya fara tafiya sannu sannu domin ganarma idonsa. Kicibis sai yayi arba dasu namil. Wai ashe wannan ihu da yakeji sune bayan da aka rutsa dasu suna bacci. To anan aswad ya rasa abunda ke masa dadi. A buge dai wadannan miyagu basu buguwa balantana shi ko makami bayada. Cikin bakin ciki da rashin jin dadi ya cigaba da tafiyar sanda yana binsu a hankali domin ganin inda zasu kaisu. Su kuwa su namil sai faman kururuwa suke suna neman taimako. Haka wadannn miyagu suka cigaba da jansu a kasa har saida suka riski wani makeken gidan sama mai ban tsoro. Anan aswad ya labe bayan itace har saida suka gama shiga gidan. Daga nan sai ya lababo domin bude kofar amma gam ya kasa. Ba yadda bai yi ba amma daya tura sai yaji kamar kara rufeta ake. A haka ya hakura ya fara zagayen gidan ko zai samu hanyar shiga. Ai kuwa cikin sa a ya dace domin wata katanyar makwarara ce ya hango manne a kasan gina. Ba abunda ke fitowa ciki in banda wani abu jawur. A haka ya kurawa makwararar idanu yana tunanin ko menene ke fitowa ciki jawur. Daga karshe dai sai ya fara tunanin cewa jini ne domin jan yayi yawa. Cikin makwararar ya shiga bayan ya durkusa. A haka ya cigaba da tafiya a durkushe yana tsallake sassan jikin mutane. Wasu har sun fara wari saboda dadewa. Ai kuwa sai banko jini akeyi a ciki. Kafin kaceme kayansa sun koma jawur. Haka dai aswad ya daure ya cigaba da tafiya har saida ya dau lokaci kafin ya kawo karshen makwararar. PAGE 29 Daga nan sai ya diro a cikin wani wangamemen daki. Ba kome a ciki dakin in banda gawawwaki. Anan ya fara dube dube. Wasu gawawwakin sun bushe. Wasu kuma danyu ne da gani kasan ba a dade da kawasu ba. Wasu kuma a can gefe zigidir ba mai ko kyalle a jiki. An hade maza da mata a wuri daya ba kyaun gani. A haka dai aswad ya cigaba da kallon dakin yana kallon abubuwan ban mamaki. Sai kuma sassan jikin mutane dake sarkafe a gina. Irin su kai, hannaye, kafafuwa kai harda cinyoyi. Sai kuma wani katon gatari a kusa ga makwararar. Kai da gani kasan dashi ake ma mutane kisan gilla. Haka aswad ya karema dakin kallo tsaf daga nan kuma sai ya nufi kofa da nufin fita. Murda ganbun yayi a hankali da nufin budewa amma sai yaga ko alamar girgizawa bai yi ba. Daga nan sai yasa karfinsa amma duk a banza. Da dai yaga ganbun na shirin bata masa lokaci sai ya dauko gatarin dake rataye saman gina. Cikin karfi ya fara dibar ganbun ba sassauci. Ai kuwa yana cikin hakane sai yaji tahowar wasu. Anan yayi jifa da gatarin. Daga nan ya tube kayansa ya koma zindir. Cikin sauri ya shafama kansa jini sannan yayi kwance cikin gawawwaki sai kace matacce. Yana nan kwance ne sai yaga wasu mutum biyu sun shigo mace dana namiji sun ajiye wasu gawawwaki. Daga nan sai suka fara wata magana. To a mamakinsa ba hausa ce sukeba. Wani yarene suke wanda bayaji. Anan ya kurawa namijin idanu kamar ya sansa. Da karfi yayi magana. " Hamir!" Ai kuwa sai namijin ya juyo inda yake kwance. To anan hankalin aswad ya tashi don kada asirinsa ya tonu. Ita kuwa maccen sai ta hanashi domin a ganinta ba kowa a wurin. Saboda haka yaji dai kamar an kirasa ne. Daga nan sai namijin ya fasa zuwa wurin gawawwakin. Iyaka ya bincika makwarara daga nan suka tafiyarsu. Shi kuwa aswad cikin sauri ya fito, anan yasa kayansa ya fita dakin cike da mamaki wannan abu. Bako shakka yasan wannan namijin. Abokinsa ne kuma dan makarantarsu. To amma kuma ya akayi ya shigo wannan kungiya? Wannan itace amsar da aswad ya kasa ba kansa. PAGE 30 Tafiya yakeyi cikin tsoro da fargaba. Sai juye juye yakeyi domin a ganinsa ana iya kawo masa hari ta ko ina. Gidan ya kasance da lunguna masu ban tsoro. Haka dai ya cigaba da tafiya sako sako kwana kwana amma baiga abokansa ba. Wannan abu ya mutukar tayar masa da hankali wanda daga karshe sai ya fara tunanin ko an kashesu. Yana cikin tafiyar ne sai yaji ana magana cikin wani daki. To anan ya labe yana lekon ko su waye a ciki. Idansa ya kafa a huduwar dake ganbun. Anan ya ga abokinsa hamir da wannan matar da suka shigo dakin gawawwaki tare. Wasu bokitayya ne cike da jini. Su kuwa su hamir din sun tube kayansu sai wanka suke da jinin. Yana cikin lekensu ne sai matar ta juyo. Anan sukayi ido hudu da aswad. Ai kuwa bai yi wata wata ba ya watsa a guje. Yana cikin gudun ne yaci karo da wata mata, a nan ya fadi saida kansa ya bugi gina. Da sauri ya mike domin ganin ko wacece. Ai kuwa yana ganinta sai ya ganeta domin itama yar makarantarsu ce tare sukayi jami a. " Laaaa. Zee me kikeyi anan? Kema sun kamoki ne?" Anan ya fadi saboda rashin karfin jiki. " Ki taimake ni zee. Zasu kasheni." Anan ita kuwa zee din ta tallaboshi. " Haba aswad ya kana wannan magana. Kayi shiru kaji ba wanda zai taba min kai." Anan ta rikoshi suka fara tafiya har saida suka iso wani daki. Daga nan ta taimaka masa ta azashi saman wata kujera. A wannan lokaci jikin aswad ba karfi ko kadan saboda wahalar daya sha. Jikinsa duk tambo ne na jimuwar da yayi. Anan zee ta zauna kusa dashi tana tabin fuskarsa. Daga nan kuma saita rungumeshi cikin murmushi. Kasancewar aswad cikin rauni ko kallonta baya iya yi. Hannu tasa da nufin kwance masa bell. Sai dakyar ya samu ya tsayar da ita. " Haba aswad ya kana haka. Nasan kafi kowa son wannan abu da zamuyi." Inji zee. " E amma banda yanzu." Cewar aswad. Daga nan saita mike tsaye. Rigarta ta debe ta koma daga ita sai wata yar shame wadda ta matseta sosai kana ganin kome nata. Anan tayi tafiya ta rangwada domin ya gani. " Ina fatan dai zakaso abunda ka gani. Kome na nan yadda ka barshi ba abunda ya canza." Zee ta fada tana murmushi. PAGE 31 Can sai ga hamir ya shigo dakin shi kadai. Ai kuwa aswad na ganinsa sai ya mike yana tangadi. " Me ya kawoka nan. Macuci azzalumi. Ashe dama kai dan kungiya ne." Haka aswad ke fadi a lokacin daya tunkari hamir cikin fushi. " Haba aswad ya kana fadar haka, ka kwantar da hankalinka ba abunda zai faru." Anan ta jawo aswad saman kujerarsa. Daga nan saita yiwa hamir wani signal da idanu. Ai kuwa yana ganin haka sai ya fita. " Waike in tambayeki, hala me kikeyi a cikin wannan gida na marassa imani? Aswad ya tambaya. " Na marassa imani fa kace?" Cewar zee. " E mana, ai naga abunda na gani. Kuma nasan cewa kema a cikinsu ki...." To kafin ya iyar ne zee ta masa wani mugun bugu fuska. A nan ya zube kasa sumamme. Daga nan saita jawoshi ta kaishi wani karamin daki ta kulle. Bayan kamar minti ashirin, sai ga zee ta dawo tare da hamir. Anan suka bude dakin da aka kulle aswad amma a mamakinsu ba kowa ciki. A nan suka fara dube dube amma ko alamunsa basu gani ba. Juyowa sukayi da nufin su tafi. Ai kuwa juyowarsu keda wuya sukuyi arba dashi a tsaye. Anan ya jawo kawunansu ya buga da juna. Ai kuwa nan suka fadi sumammu jini na fita ta hancinsu. Daga nan sai ya fita dakin a guje. A nan ya nufi wani lungu mai tsananin duhu. Gashi bayada fitila domin ya dade da jifa da ita tun a lokacin da aka biyosu. Saboda haka sai ya fara tafiya a hankali don gudun kada yaci karo da wani abu. Fitillun dake gidan basaci sosai. Wasu kuma sun lalace sai dai su kawo su dauke. Haka dai aswad ya ci gaba da tafiya cikin duhu yana lalube. Can sai ya farajin nishin wani. A nan ya nufi inda yakejin sautin na fitowa. Ai kuwa yana cikin tafiyar ne sai yaji gudun wasu samudawa sun nufo wurin da yake. Cikin sauri ya boye kusa ga ganbun wani daki. To bayan sun wucene sai ya shiga dakin dama a cikine yakejin nishin na fitowa. PAGE 32 Ai kuwa shigarsa keda wuya ya like hancinsa da hannuwa saboda tsananin doyin da yakeji. Anan ya fara dube dube amma baiga kowaba. Kuma baisan ko menene ke wari ba. Can sai ya hango wani daki. To anan ya nufi ciki. Ai kuwa shigarsa keda wuya sai ya tarar da kwarangwal na mutane ( skeleton) tare da wasu gawawwaki duk sun rube. Dakyar ya samu ya shiga har kuryar dakin. Ai kuwa shigarsa keda wuya sai ya tarar da nabilat kwance tana nishi. Sun tube mata kaya ta koma zigidir. Sai kuma bayanta duk an zaneshi da yuka. Anan aswad yazo kusa da ita cikin tausayawa. Tallabota yayi yana tambayarta inda akaje su namil amma bata iya magana. Goyata yayi ya fito da ita dakin. Daga nan sai ya cigaba da gudu yana bincikar inda aka aje sauran abokansa. To yana cikin gudu ne sai ya hango wasu samudawa a gabansa. Kowanensu sanye da bakaken kaya. Bako shakka kai da ganin wadannan mutane dole ka girgiza domin tafiyarsu ma ta daban ce. Anan ya juya baya da nufin tserewa kuma sai yaga wasu irinsu. Sun rike kwari da baka kai da gani kasan basada imani. Aswad a tsorace yake domin yasan dasun iso gunsa to sunansa gawa. Kawai sai ya hango wani daki a kusa dashi. Ai kuwa a guje ya kutsa kai ciki. To kafin ya shiga ne wani daga cikin miyagun ya halbo kibiya. Ai kuwa kai tsaye ta shiga bayan nabilat. Sai da ta danyi wata kara daganan bata kara cewa komi ba. To bayan ya shiga dakin ne sai yaga ashe hanya ce doguwa irin wadda ya baro. Cikin sauri ya kutsa kai ciki sai faman gudu yake. To bayan yayi tafiya mai nisa sai ya tsaya domin yaga halin da nabilat take ciki. Anan yaga ta sandare ko motsi batayi. Girgizata ya farayi amma ina rai yayi halinsa. Anan ya rungumeta yana kuka cikin bakin ciki ya rasa babbar abokiya tun suna yara. Ya dade zaune kusa gareta yana jimami. Bayan wani lokaci kuma sai ya tashi ya nufi hanyarsa yana tafiya dakyar. Haka ya cigaba da tafiya yana tangadi sai kace wanda yasha giya. A wannan lokaci kome nasa ciwo yake. Yana cikin tafiyar ne ya fadi galabaice ba tare da sanin inda yake ba. PAGE 33 A haka aswad ya kasance cikin wannan hali na suma ba tare da sanin inda yakeba. Sai da aka dau lokaci mai tsawo kafin surutun wasu miyagu ya tadashi. Cikin sauri ya tashi firgigit. Labewa yayi cikin wata kwana mai duhu. Bayan sun wuce ne sai ya fito yana bin bayansu domin yaga inda zasu. A haka ya cigaba da tafiya yana binsu. Idan yaga zasu jiyo sai ya boye don kada su ganshi. Sai da sukayi tafiya mai nisa duk a cikin gidan kafin su shigo wani irin makeken daki. Duk mutanen dake cikin dakin a tsaye suke suna sanye da kaya jajjaye masu ban tsoro. Wani mutum ne yayi tsaye a tsakiyarsu sai wata magana yake da wani yare. Kasancewar aswad baya jin abunda suke fadi sai ya boye a cikin labule. Dakin gaba daya an zagayeshi da jan labule ta ko ina. A haka aswad ya natsu yana kallonsu domin yaga abunda ke gudana. Yana cikin kallon ne sai yaga mutumin ya daina magana. Daganan sai wasu mutum biyu suka shigo da wani namiji a daure. Saman wani benchi aka daureshi tamau. Daga nan sai mutumin ya dauko wata yuka. A gaban idonsa aka yanke wannan mutumi. Yukace aka darara masa a wuya kamar yadda ake yankan rago. Cikin kankanin lokaci jini ya kama kwarara kamar fanfo. Anan mutumin wanda da gani kasan shine shugaba ya dauko wata tasa ya tara yadda jinin zai zuba a ciki. Shi kuwa mutumin da aka yanke sai ya kama fizge fizge sai da wasu suka rikeshi. To bayan jinin ya gama zuba ciki sai shugaban ya dauki tasar ya kafa kai. Sai da yasha sannan yaba na kusa gareshi. A haka aka fara zagaye da wannan tasar. Idan wannan yasha yaba wannan har saida kowa yasha. Shi kuwa na karshe dasha sai ya ajiye tasar a kusa ga shugaban. Anan aswad ya lura cewa mutanen maxa da mata ne. Shi kuwa shugaban sai ya nuni tasar da yatsansa. A nan ya fara fadin wasu dalassammai na tsafi. Ba a wani jimawa ba sai yaga innuwar mutumin da aka kashe ta fito cikin tasar. Anan shugaban ya kama innuwar ya turata cikin wata kwalba. Daga nan sai ya rufe ya ajiye ta wani wuri cikin dakin. Can kuma sai aka shigo da wata yarinya zigidir. Anan aka azata saman benchin da aka kashe wannan mutumin na farko. PAGE 34 Bayan an daureta tamau sai shugaban ya tube kayansa ya koma zigidir. Anan ya fuskanceta da nufin keta mata haddi. Shi kuwa aswad da karfi ya dago kansa domin ganin ko wacece wannan yarinyar. Ai kuwa yana dubawa sai yaga ba kowa ceba in banda humairat. Jikinta duk jini ne kai da gani kasan ta galabaita. Anan ya fara tunanin meye abunyi kafin wannan mugun mutumi ya iyar da nufinsa akanta. Wasu samudawa ne sanye da bakaken kaya ko fuskarsu ba a gani saboda sun rufeta da bakkin kyalle. Rike suke da muggan makamai sai kaida komo kawai suke a cikin dakin domin tabbatar da tsaro. Hankalin aswad ya mutukar tashi domin yasan idan suka ganshi to karyarsa ta kare. Haka ya cigaba da wasi wasi sai daga baya dubara ta fado masa. Cikin sauri ya fito daga maboyarsa ya kalli shugaban. " Ni zanyi duk abunda kukeso indai kunyi alkawari bazaku taba wannan yarinyar ba." Anan mutanen dake cikin dakin suka tsura masa ido ko kyaftawa basayi. Daga nan sai shugaban ya fara magana da wani yare yana kallonsa. Haka ya cigaba da maganar har saida aswad yayi zaton cewa kamar bayajin hausa. Mutum biyu daga cikin samudawan ne suka rikoshi. Anan suka gurfanar dashi gaban shugaban. Daga nan sai suka dauko wani benci suka axa shi sama. Basu daureshi ba iyaka dai sunyi tsaye gabansa sai maxurai suke. Bako shakka aswad yayi wautar bayyana kansa ga wadannan miyagu. Sai daga bayane wannan tunani ya shiga kwakwalwsarsa. Shi kuwa shugaban kai tsaye ya nufi wurin humairta da nufin biyan bukatarsa. Aswad yayi kokarin tashi domin ya hanashi amma sai suka rikeshi. Daya ya dafe kafafunsa dayan kuma hannaye. A gaban idonsa wannan mutumi ya taka bencin a inda humairat take. Take ya jawota a jikinsa. Ba yadda aswad bai yiba domin ya hana wannan abu amma ina sunfi karfinsa domin sun rikeshi gam. Yana kallo ana warwasawa amma ba yadda ya iya. A haka ya fara zub da hawaye na bakin ciki domin humairat itace yarinyarsa tun kafin suyi wannan tafiyar. Sai kuma nabilat wadda itace babbar kawarsa tun suna yara. PAGE 35 Saida aka dau lokaci ana warwasawa da humairtat ba kakkautawa. Su kuwa sauran yan kungiya sai kallo suke domin abun gwanin ban shawa ne a wurinsu. Ita kuwa humairat tanaji sai dai bazata iya komeba domin a daure take tamau. Bayan an gama ne sai shugaban ya dauko wata karamar yuka. Anan yasa aka juya masa ita. A saman bayanta ya fara wasu zane zane. Saboda radadin da takeji dole ta fara ihun wuya. Anan aswad ya gane cewa irin wannan zanen da aka yiwa humairat bako shakka shine ya gani ga bayan nabilat kafin ta mutu. To kenan indai hakane itama sai da shugaban yayi amfani da ita kafin ayi mata wadannan zanukkan. Bayan an gama zane bayan humairat da yuka sai aka dauketa aka wuce da ita wani wuri. Shi kuwa aswad sai suka daureshi tamau da kaca aka barshi a nan. Yana kallo kowa ya fita dakin ya barshi a nan. Ba a wani jimawa ba saiga zee ta shigo dakin. Cikin rangwada ta shigo cike da murmushi sai taku take dai dai. " Kai a ganinka ka samu nasara ne ko?" Daga nan saita fara kewayensa tana masa kallon keta. " Kai kyakkyawa ne" Ta fada a lokacin data karo bakinta domin ta sumbaceshi. Ai kuwa da karfi ya tofa mata yawu. A nan taja da baya tare dayin dariya. Halshenta ta janyo tana lashe yawun daya tofa mata. Bata damu ba ko kadan da kazantar dake tattare dasu ba. Wata karamar yuka ta dauko tana lasawa a halshenta. Anan aswad ya kura mata idanu domin yaga ko meye take shirin yi. Kusa ga kafafuwansa ta tsaya. Anan ta fara soka masa yukar a hankali ga ciki. Datasa sai ta fitar, a duk lokacin data fito da yukar sai yayi kara saboda tsananin zogin da yakeji. Kafin kaceme jini ya fara kwararowa

Chapter 3 of 6