Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TAFIYAR DARE MAYYUN JINI Na Abdul King Article Ebook created by Shuraih Usman Ebook publish by http://www.hausaebooks.cf TAFIYAR DARE 2 MAYYUN JINI AUTHOR : ABDUL KING ARTICLE EPISODE 1 PAGE 1 Dare mahutar bawa, idan lokacin ka yayi dole a tareka, dare mahutar bawa, idan kazo dolene komi ya samu akasi. Dare mahutar bawa, duk wanda bai zauna wuri daya ba to bayada banbanci da matacce. Wannan magana haka take ba tantama, nasan dolene kayi mamaki yadda na fadi wadannan zantuttuka masu rudani da tafarfasa zuciya. Amma wannan ya farune sanadiyar wani bakin al amari daya taba faruwa a gareni shekaru da yawa, wannan al amari ya farune a cikin dare kuma ya kare a cikin dare. Sanadiyar hakane naga ya kamata in bayyana kadan daga faruwar wannan abu ba don komi ba sai dai domin kaima ka kiyayi dare domin gudun watarana. Sunana anisa, amma akan kirani da baby, a wannan lokaci ba abunda na rasa na jin dadi daga gidanmu domin abbana ya tanadar min duk wani abu na jin dadi da annashuwa, amma kuma duk da hakan ko kadan ban damu ba. Babban abunda ke batamin rai shine abba baya bari na fita ko kofar gida, idan kaga na fita to makaranta zanje domin duk wani abu da ake bukata akwai masu aiki. Saboda haka su ake sawa aikace aikacen gida. Inada waya babba ipone x, sai kuma laptop dita HP, kai in takaicemaka labari harda mota tawa inada amma ko kadan bana moriyarta sanadiyar bana yawo, daga makaranta sai makaranta, kai ko biki idan zan fita sai abba yayi min nasiha cewa in kiyaye, wannan abu na mutukar batamin rai sai dai ba yadda xanyi, a duk lokacin danaga kawayena suna sharholiyarsu abun kan mutukar burgeni, sai naji dama ace inada wannan damar ai da shikenan. Bako shakka uwaye sun cancanci yabo, godiya, karamci, da kuma girmamawa. Duk wanda bai girmama uwayensa ba to yayi asara tun a nan duniya. Duk abunda abbana ke horar dani gaskiyane, ni a tunani na yana cutar dani amma daga baya sai na gano ba haka ba. Bako shakka abba na mutukar sona so na hakika son da duk wata ya mace zataso ace abbanata na mata. Na gano hakan ne sanadiya wata tafiya data kama mu a cikin dare nida kawayena. Saboda haka bari in baka labarin wannan tafiya da kuma makasudinta. PAGE 2 Anisa ce ke zaune cikin wani katafaren falo cikin jin dadi, fuskarata cike take da annashuwa da walwala. Kai da gani kasan diyar masu hali ce tun daganin shigar ta. Dan lemon tane exotic a kusa da ita sai wani cup na glass rike da hannunta, idan tadan kurba lemon sai ta fincike wani cake dake kunshe a cikin wata leda. Idanunta ko kyaftawa basayi sanadiyar ta kurawa tv idanu sai kyalkyatar dariya take kai kace mahaukaciya. " Laaaaa, shegiya baby hala miye kikeci haka kina dariya sai kace aJmaryar da za a kai gobe? " Anan anisa ta daga ido sai tayi arba da kawarta. A guje ta sheko suka rungume juna cikin murna. " Amma zee bakida kirki ko kadan,wai ace kinyi graduating amma ko flashing ba za ayimuna ba." Haka anisa ta fada tare da jawota. " Haba kawata kiyi hakuri mana, ai da kin san abundan ya faru da bakice haka ba." Cewar zee tana murmushi. Anan anisa ta wani karkada idanu tare da yi mata kallon uku saura kwata. " Humm, dama haka kike, ai dama nasan dole ki manta damu tunda kin samu kawaye a can ko. Mutuniyar banza." Anan anisa ta fita falon. Bata jima ba sai gata ta dawo da wani cup. " Yauwa, bari na zuba miki lemon kema kisha ko kyaji gardi." Anan anisa ta zuba mata lemon ta bata. " Saura kuma kice mun bazaki shaba." " Au, har na isa." Inji zee bayan ta karbi lemon. " Kedai kinason exotic, ni kodan bai yimun ba, balantana yanzu fa akwai drinks na yayi amma ke kullum ancient ce. Bakauya kawai." " Iyee, kina nufin ni bakauya ce?" Anisa ta tambaya. " Tab, to ke a tsammaninki yar birni ce? Mai bleaching da garin kwaki irinki." zee ta bata amsa. Dariya sukayi tare da kallon juna suna taba hannu. " Keda ko waya bakida, amma ni kike cema bakauya." Anisa ta fada cikin wasa. " E naji dai, ai waya nice banso samu ba, kema kin san ruwa ba sa an kwando bane, zan iya sa samarina su siya min duk wadda nakeso." Inji zee cikin daga murya. " Samari kuma? Yaushe kika fara bin maza ban sani ba?" Inji anisa. " Au, dama baki sani ba? Ai karuwace kike kawance da ita." Xee ta fada cikin bakar magana. PAGE 3 " A a ni dai kada ki kaini inda yan kuda ke salati, nifa ba haka nake nufi ba. " Anisa ta fada cikin lallashi. " Ko ma me kike nufi ke acciki, nidai nasan duk yadda goma ta lallace tafi biyar albarka. Ke da kike daure sai kace tunkiyar masar. Idan ba tsoro ba mutum ya fita mana, kinzo kin hakince cikin gida bakya ko tunanin aure, ko kina nufin samarin a cikin gida zasu ganki suce sunaso?" " Kema fa kin san ba laifi na bane laifin abba ne." inji anisa. " To cigaba da jira sai abba yace ki fita sannan zaki fita, aiko yarinya inaga zaki tsufa gidanku, domin nan da shekaru kadan zaki yi expiry. Kinga da ganan sai mu kaiki bola tunda kinyi wari." Haka zee ta fada tana hamma. Cikin rashin tsammani ta banko wata tusa mai shegen doyi ji kake buuuuuuuummmmm. " Haba zee bagirman kibane, yanzu fa da ace su al-ameen na nan da sunyi dariya." Cewar anisa bayan ta toshe hancinta. " Wai har kin sa gabana ya fadi, hala ina suka jene?" Zee ta tambaya. " Tare suka fita da abba, inaga harda mumy ta bisu wai zasuje kasuwa." Anisa ta bata amsa. " Kice ke kadaice a gidan yau?" Zee ta fada. To kafin anisa ta bata amsa sai ga wata tusa wadda tafi ta farko kara da wari. Anan zee ta mike da sauri." Wayyo cikina, inaga exotic din nan da kiban ya bata mun ciki. Nifa zawo nakejiiii." Anan zee ta nufi toiltet a guje. Anisa ce ta danyi dariya saboda kallon data yiwa zee a lokacin da take gudun. Wato kayan data sa ne suka matseta sosai yadda gudun take amma ana ganin kome na siffar jikinta. Anan anisa ta kara fanka domin warin yadan rage. To bayan ta zauna ne sai tunanin maganar zee ta taso mata. To cigaba da jira sai abba yace ki fita sannan zaki fita, aiko yarinya inaga zaki tsufa gidanku, domin nan da shekaru kadan zaki yi expiry. Kinga da ganan sai mu kaiki bola tunda kinyi wari. Bako shakka abunda zee ta fada gaskiyane fa, to yanzu idan na cigaba da zama a nan to yaushe zanyi aure, burin kowace ya mace shine tayi aure ta kuma haifafa. To amma ni ko kadan banada wannan gatan. To yanzu yama za ayi samari su ganni suji na burgesu idan ban fita ba? Bako shakka dolene na dauki mataki sosai game da wannan al amari. Anan tunanin anisa ya yanke sanadiyar fitowar zee daga toilet. PAGE 4 " Wai, har naji dan sauki." Cewar zee bayan ta kishingida kan kujera. " Duk kin cika mana wuri da shegen doyi." Inji anisa cikin wasa. " Ai ba laifina bane, ai dana sani da ban sha ba." Inji zee. Anan ta mike ta dauki jakarta." Bari na koma gida magriba ta kusa." " Tun yanzu zaki fita?" Anisa ta tambaya. " Hmmm, ni dai sai anjima kada ki bata min lokaci, gashi ba yawo kikeyi ba balantana nace ki rakani." Haka zee ta fada kafin ta fita. Anisa binta tayi da kallo cikin zurfin tunani na wannan maganar data yi mata. Haka zee ta fita cikin rangwada kai kace jikinta ba jini da tsoka bane. To a wannan lokaci tunanin anisa ya zurfafa har takai ta kashe tv saboda ji take kamar ana damunta. Gaskiya dole na dauki mataki akan wannan al amari, abu har yakai an fara yimin gori akan rashin fita. Gashi kuma na girma amma har yanzu ace banada yancin kaina. Haka dai anisa ta cigaba da tunani daga nan kuma sai ta koma dakinta domin ta dan yi bacci. Kida ne ke tashi mutane sai rawa akeyi kowa ya kama gwaninsa, maza da mata an cankude sai bushasha akeyi. Anisa ce ke tafiya tana waige waige a cikin filin rawan. A haka ne tayi kicibis da wata budurwa tsaye. " Yauwa, dama ke nake jira." Haka yarinyar ta fada kafin daga bisani ta dauko yuka da zimmar yanka ta. Anisa ce ta kwala uban ihu daga nan ta farka firgigit. Ashe mafarki ne takeyi. To a wannan lokaci mumy ce ta shigo taga lafiya. Anan anisa ta fada jikinta tsorace. " Me ya faru haka kike wannan ihu sai kace mahaukaciya, to fa kada ince dai mafarkin ne kika karayi?" Mumy ta fada bayan ta rungume ta." " E wallahi mumy, a wannan karon dakyar nasha da ta sokamin yuka." Anisa ta fada a tsorace. " Kinga abunda nake fada miki ko? Idan akayi la asar ba a bacci amma kinki. Ko yaushe sai kice wai yafi karfinki." Mumy ta fada bayan ta tayar da ita." To yanzu sai kije kiyi salla ga a can ana magrib." PAGE 5 Da misalin karfe 8:30 PM ne su anisa suka nufi dinning table domin daukar dinner. A wannan lokaci kowanensu yayi sallar isha i. Al ameen ne da husna suka fara zaunawa saman kujerun. Abunka da yara basa ko bari sauran jama ar su karaso domin aci abincin tare. Cikin gaggawa suka fara tura loma suna kyakkyatar dariya. To bayan kowa ya zauna ne sai aka fara cin abincin tare. " Nifa wannan mafarki na anisa kan mutukar ban mamaki domin ban taba jin wanda ya taba yin irinsa ba. Kuma ace abu ya kici yaki cinyewa." Haka daddy ya fada yana kallonsu daya bayan daya. " Hmm, kai dai bari, ai abu ya tsananta yanzu. Tunda har da fizge fizge take yi idan tana bacci." Haka mumy ta fada tana kallon anisa. " Haba mumy fizge fizge fa kikace." Anisa ta fada cikin rashin jin dadi. " E to zan miki karyane?" Mumy ta tambayeta. " Yanzu dai ya isa sai ku saurara muci abinci." Daddy ya tsawatar. A haka dai suka cigaba da cin abincin, to bayan sun kammala ne kowa ya nufi dakinsa domin ya sarara. Haka anisa ta shiga dakin cikin rashin jin dadi. A yau dai jikinta ba karfi sai kace wadda aka zane. Laptop da dauko da nufin kallo kuma saita ajiyeta gefe saboda tunanin daya dameta. Tana cikin hakane sai ga husna ta shigo aguje rike da littafinta na islamiya ( MUKARRAT TAUHID) " Shegiya har kin ban tsoro, wai uban me ya kawoki dakin nan?" Anisa ta fada cikin jin haushi. " Wayyo sorry baby, wani fa assignment ne aka bamu kuma gobe akeso mu bayar." Husna ta fada cikin tausayawa. " Ina fatan dai english ne?" Anisa ta tambaya. " A a, amma duba ki gani." Anan husna ta miko littafin. Anisa na kallon littafin gabanta ya fafi. " Kwal uba." Ta fada da karfi tana kallon husna. Anan ta fara tunani yadda zata bulloma al amarin domin ko kur ani daga shekara sai shekata take karatunsa a lokacin azumi. Gashi kuma bataso ace bata iya ba. PAGE 6 " Baby ya naga kinyi shiru?" husna ta tambaya cikin natsuwa. " E ina dan tunani ne ai kema kin san cewa wannan littafi na dade da kammala shi. Yanzu bari na biya miki." Anan anisa ta rika mukarrat tauhid ba tare da sanin abun cewa ba. Ita kuwa husna kallonta take tana saurare taji me zatace. " An karbo daga.... Ummm......" Muryar anisa ta fara rawa. " Laaaaaa, bafa hadisi bane ji yadda take....." Husna ta fada cikin dariya. " Ke ubanwa kikewa dariya?" Anisa tasha toka. Anan husna tasha jinin jikinta domin tasan data motsa zataji masga. " Wane wurine za a biya miki?" Anisa ta tambaya. Anan husna ta buda mata dai dai shafin da takeso ta karanta mata. Cikin rashin tsammani sai sukaji an banko kofar da karfi. Juyawa sukayi da nufin ganin ko waye. Ai kuwa ba kowa ceba in banda halina wato kawar anisa. " Me kuke karatu haka?" Ta fada tana taku dai dai. Basu amsa mata iyaka dai sun bita da murmushi har ta karaso wurinsa. To anan suka taba hannu cikin jin dadi. Batayi wata wata ba ta fizge littafin tana dubansa. " Anisa, yaushe kika zama ta kwarai, wai kece da wanan littafi kuwa?" Halina ta tambaya cikin mamaki. " Hmm, ai kema kin sani ba saina fadaba. Nifa rabona da arabic tun..... " Anan anisa tayi shiru bata iyar ba don kada husna ta gane halin da ake ciki na cewa bata iya karatun ba. " To yanzu tun da Allah ya kawoki ai shi kenan kin hutar dani sai ki fada mata." Cewar anisa cikin murmushi. Kasancewar halina mai ilimin addini ce, cikin kankanin lokaci ta karbi littafin ta fashema husna shi har saida ta fahimci abunda ake magana akai. Daga nan kuma ta taimaka mata wurin amsa assignment din da aka bata. Anan husna ta karbi littafinta ta nufi waje bayan tayi godiya. Wannan abu da halina tayi ya mutukar burge anisa domin tasan cewa idan da bata zoba. Tofa yau da kunya ta kasheta. PAGE 7 " Amma fa kawata kin ceceni, yau inaga da baki zoba da sunana gawa." Anisa ta fada cikin dariya. " Au wai kina nufin bazaki iya karanta wannan littafin na yara ba?" Inji halina. " Wai na yara! Kajita da wata magana." Anisa ta fada tana kallonta. " Wai ya akayi kikasan ina nan?" Anisa ta tambaya. " Daga shigowata na iske su mumy a falo, to bayan mun gaisa ne saita fadamin cewa kina nan daki." Halina ta amsa. " Gaskiya ilimin addini yayi, yanzu ke halina bakida matsala ko kadan." " Haba wa? Ni har ilimi gareni, ai idan kikaga wasu sai kin rike baki." Anan su anisa sukayi tadi har saida dare ya raba sannan sukayi sallama halina ta koma gida. Tunda kulu kulun safiya anisa ta farka domin yau akwai al amurran da takeso ta gabatar, a haka ta shirya jikinta tsaf, daga nan ta dauko wayarta ta fara wasa. Da misalin karfe 8:30 AM, sai ta farajin ana kwankwasa kofar dakinta. Bai jira an budeba kai tsaye ya shigo. " Anisa, wai kece a farke?" " E mana daddy tun dazu fa na tashi." " Tab, kina nufin har kinyi sallah?" " E mana tun dazu." " Mamaki, Keda bakya asuba sai karfe goma sha biyu na rana amma yau har kin samu asuba. To Allah yayi miki abarka yata." Anan ya juya ya fita. Da misalin karfe 11:30 AM, anisa ta fito da makullin motarta, a yau fa cikin jin dadi take saboda tafiyar da zatayi. Rabonta data fito waje har ta manta. Gate man ne ya mayar da kofar bayan ta fita da motar. To anan ta nausa aguje ba sassauci. A haka ta miki hanya duma na tashi a hankali yadda ita kadai keji. Bayan tayi tafiya mai dan nisa sai ta cimma wani makeken gida. Sau biyu kawai tayi oda aka bude mata gate din. Ciki ta nausa kai da gani kasan cewa ba bakuwar gidan bace. " Hajiya sannuki da zuwa." Anan mai gadi ya sheko a guje wurinta. " Yauwa barka, ina fatan dai tana ciki.?" Anisa ta tambaya. " Gaskiya batanan, amma taban wannan takardar cewa idan kinzo in baki." PAGE 8 Anan anisa ta karbi takardar tana karantawa, " Ai kuwa daka fadamin da bazan shigo ciki ba, kaga yanzu aiki ya sameni wai ba a nan zamu hadu ba." Haka anisa ta fada cikin rashin jin dadi domin ji take kamar duk ta wahala. " Hajiya ayi hakuri, anan na tafka babban kuskure." Haka mai gadi ya bata hakuri. Daga nan kuma ya bude gate din ta fita. To bayan ta fita ne saita nufi inda zata hadu da kawarta. Anan taci taya sai banka wuta take. Bata tsaya koina ba sai kusa ga wani restaurant. Aiko tsayawarta keda wuya sai taji an shigo cikin motar. Tana dubawa sai tayi arba da zee. Wato kawarta. " Tun dazu fa nake jiranki amma sai yanzu." Zee ta fada cikin murmushi " Yanxu dai ba wannan ba, muje muci abinci nifa yunwa nakeji." Anisa ta fada bayan ta fito daga motar. Daga nan sai zee ta biyota. Bayan sun zauna ne aka kawo musu abincin da sukeso. Daga nan sai suka faraci suna tadi. To cikin hakane anisa ta lura da wani zane ( Tattoo) dake a hannun zee, hoton maciji ne akayi a hannun nata. Anan anisa ta kurawa wannan zane idanu cikin mamakin ko me yake nufi. To da zee ta lura da kallon da takewa zanen, sai tayi sauri ta juyar da hannunta. Anisa tayi mamaki sosai domin bata saba ganin irin wannan zaneba. Tayi niyar ta tambayi zee game dashi amma kuma sai wani abu ya tauke mata hankali har ta manta. To bayan sun kammala cin abinci sai zee ta karbi makullin motar domin ta tukasu zuwa wurin da zasu. " Kikace walimar aurece zamu ko?" Anisa ta tambaya. " Koma dai miye ai zaki gani." Zee ta bata amsa. A haka suka yita shiga lungu lungu sako sako wasu unguwanni anisa bata masan dasuba. Sai wazajen la asar sannan suka kawo wani gida shi kadai a rabe. Anan zee ta mata umarni dasu shiga ciki. To bayan sun shigo ne sai anisa taga ba abunda ake in banda casu. Katon filine wangameme mutane maza da mata sai sharholiya akeyi. Daga shigowar anisa aka tsura mata ido, anan kowa ya bita da kallo wasu ko kyaftawa basayi. PAGE 9 " Wai dama ba walima ce mukazo ba?" Anisa ta tambaya. " Hmm, wai walima. Kada ki damu kawata na fadi hakane yadda idan kika fadawa su mumy kai tsaye zasu yarda kije. Domin idan ba walima kikace zakiba nasan bazasu bari ki fita ba." Xee ta bata amsa. Anan sukayi dariya, " Lalle kin cika yar duniya. Wato har kin san halin da gidanmu yake ciki kenan." Inji anisa. Anan suka zauna suna kallon yan rawa, to abunda yaba anisa mamaki shine mafi yawancin mutanen dake wannan wuri suna dauke da irin zanen zee akan hannunsu, katon macijine baki kirin aka zana musu. Wannan abu yaba anisa mamaki, to anan ta fara ganin cewa duk yadda akayi wannan zane na maciji akwai abunda yake magana akai, kuma bako shakka dole abokan juna ne domin bazai yiwuba ace duk daukakin mutanen dake gidan sunada zane iri daya a hannunsu. " To amma wai me yasa kika kawoni wannan wuri?" Anisa ta tambaya. " Saboda inaso in taimake ki, nasan da cewa gida ba a bari kiyi yawo, amma yanzu wannan yawo da mukayi don Allah bakiji dadi ba?" Zee ta fada cikin fara a. " E kwarai kuwa, kamar kin san abun na yimin zafi wai ace banda ikon fita, kenan fa ko yanxu da ace banyi wannan karyar ba da bazasu bari na fita ba." Inji anisa. " Kada ki damu kawata, ai daga yau kukanki ya bushe, wannan wuri fa dana kawoki nan za a share miki hawayenki. Kuma za a baki yanci na kiyi duk abunda kikeso a lokacin da kikaga dama." Xee ta fada cikin harzukawa. " Allah ko kawata? To amma wannan wane wurine kuma ya za ayi ku sharemin hawaye?" Anisa ta tambaya. " Ki kwantar da hankalinki kawata. Yanzu zan gabatar dake ga sauran members namu. Amma fa duk abunda sukace kiyi zakiyi." Inji zee. Daga nan saita tashi ta nufi wani lungu. To anan ne anisa ta kalli wurin taga yadda aka kawata gidan abun gwanin ban shawa. Ga mutane iri iri kowa sai sha a nin gabansa yake. Kowane saurayi yaja tasa budurwa sun fake a gefe daya. Abun ya mutukar burge anisa duk da cewa batada saurayi. PAGE 10 A wannan lokaci duhu ya farayi amma kuma mutane sai tudadowa sukeyi sai kace yanxu aka fara cin kasuwa. Tana cikin wannan hali sai taji an shafi kanta. Da karfi ta juyo domin taga ko waye. To anan tayi arba da wani saurayi dan shala. Anan suka hada ido da anisa. Gabanta ne ya fadi duuuumm. " Yan mata ko kinada karas ne? " Anan anisa ta kalle sa ba tare da cewa komi ba sanadiyar rashin sanin abunda yake magana akai. " Ya ina magana kin yi shiru. To idan bakida ni zan baki." Anan ya fada yana dubanta daga sama har kasa. Can sai ga zee ta dawo. To a wannan lokaci shi kuwa ya mike hannunsa da nufin ya kara shafa kanta. Caraf yaji an cafke masa hannu. " Haba zalo kawata cefa!" Zee ta fada cikin laushi. " Iyeee, dama kawarki ce, to nifa koma wace na siya. Saboda haka yanzu sai ki fada mata." " Kai kuma kana wannan magana kofa register ba a yi mata. Yanzu dai kayi hakuri idan ta zama yar gari zan tuntunbeka. " Tab wai ke nufinki bata taba haduwa da karas ba. Amma fa tayi girman banxa. Ga kyau amma ko kadan bata more masa." Anan ya fada yana mai tafiyarsa. Daga nan sai zee ta jawo hannunta suka nufi wani lungu. " Wai me yake nufi da karas? Ko yana nufin carrot wanda na sani?" Anisa ta tambaya. Anan zee ta kyalkyace dariya. " Ke sabuwar zuwace bakisan kome ba. Ga kuma shegen ustazanci da kike fama dashi. Yanzu dai muyi sauri suna jira." Saida sukayi tafiya mai dan nisa kafin su shigo wani katon daki cike da mutane kowa sai sha anin gabansa yake. Ai kuwa mutanen na ganin sai suka fara tabi da shewa suna kallon anisa. Ita kuwa batason abunda akeyi ba iyaka dai ta kura musu idanu. A haka suka cigaba da tafiya ana musu tabi har suka kawo wurin wani dogon table mai fadi an lullubeshi da carpet. PAGE 11 To anan wani mutum yama anisa umarni data tube kayanta ta kwanta saman teburin. Da farko taki yarda sai da kyar zee ta shawo kanta sannan ta yarda ta debe dan kwali shi kadai. Amma sauran kaya taki cirewa. Daga nan sai mutumin ya kura mata idanu. Sai da ya kallace surar jikinta tsaf sannan sai ya kyalkyace da dariya. Can kuma sai ya taba hannunsa sau uku. Ai kuwa saiga wani kato ya fito daga shi daga shi sai dan guntun wando duk ana ganin kome nasa. Ai kuwa mutanen na ganinsa sai suka fara ihu suna masa jinjina ka da gani kasan sananne ne a wurin. A haka ya cigaba da tafiya yana taku dai dai su kuwa yan matan gurin sai kallonsa suke suna kyalkyatar dariya. A haka wannan katon ya nufo wurin anisa. Daga zuwansa sai ya dauko wata kwarya dake jicce a wurin. Wata katanyar fanteka ya bude ya debo wani abu jawur. Daga nan sai ya mikowa zee domin ta ba anisa. " Wannna zobo ne ko meye jawur?" Anisa ta tambaya. " Kedai sha kawai." Xee ta fada. Ai kuwa anisa na kafa baki mutanen suka dau ihu. Bata wani jimawa ba ta amayar da abun tana tari sai da zee ta kwantar da ita. Daga nan sai mutumin ya kusance ta. Ai kuwa sai kaji wurin yayi tsit sai kace anyi mutuwa. To anan kowa ya kuro musu idanu yana kallonsu. Da farko mutumin sai ya fara shafa gashin kanta. Ai kuwa nan take jikin anisa ya mutu. Daga nan sai ya sauko da hannunsa ga dukkanin jikinta koina shafawa yake. To anan anisa ta fara girgiza sai kace marar lafiya. Can kuma sai

Chapter 1 of 6