Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
suna jiran ma su zama cikinsu. Kasan dakin tayal ne wanda aka lilliba masa bargon sitira da lallausan kilishi, bangon dakin launin sararin samaniya ne, daga bangaren kudu kuma wani katon gilashi ne wanda ke kunshe da kyakkyawan hoton wani gida irin ginin mutanen Sin. Sannan daga saman gilashin wani kyakkyawan agogo ne shan kwallon dafa, agogon ya mallake shi ne ranar da aka yi bikin shekarunsa talatin da haihuwa, sannan a tsakiyar fale- falen agogon an rubuta cikin siraran haruffa AGANANI MU-SHA-GARA Karfe goma da rabi na safe agogon ya nuna. Aganani mu- sha-gara ya lalubi gaban aljihun rigarsa, ya dauko abin kunna taba, sannan ya kunnawa karan sigarinsa wuta, ya fesa hayaƙi sama, ya kuma murza gashin bakinsa sannan yaci gaba da cewa. "Abu daya da zai fi ba mu wahala shi ne inda zamu same ta." Ya dan yi shiru sannan ya ce da su. "ina fatan akwai wanda ya san gidan Rayyanu acikinku?" Yansandan suka gyada kai kamar kurame, "Ina tunanin wani abu." Ya ce da su yana zazzare idanu. "Ina son mutum uku daga cikinku, su kaiwa gidan Rayyanu ziyara a daren yau, saboda ina tsammanin Surayya yarinyar sa ce. . "Ranka ya dade, kana tsammanin za ta zauna a can ne?" Wani dogo daga cikin yansandan ya tambaya. "I to, tana iya zama a can, abin da ba ku sani ba shine, ba ta san muna neman ta ba, matsalar kawai a nan daya ce shi ne ba mu san kamanninta ba, amma in dai mun samu hotonta to tazo mana gidan sauki saboda na tabbata za ta fita yawo tunda ba ta zaton komai." Ya dan yi shiru sannan yace, "Ku je gidan ku bincika ina tsammanin ko ba ku same ta ba a can za ku sami hotonta ku bincika sosai, sauran kuma ba sai na fada muku ba, na san kowa a cikinku gwanine wajen iya nazarin hoto kallo daya.. Kun dai gane, ku warwatsu ko ina, ina tsammanin ganinta nan da kwana biyu." Aganani ya yi shiru sannan yayi murmushi. Jikin yansandan ya dauki rawa gaba daya, saboda sun san abin da murmushin ke nufi. "Idan mun kama ta" Aganani ya ce, "Ita ma za ta bi hanyar da Rayyanu ya bi" Sannan ya dada da cewa, "Ba za ta kai labari ba, ita kadai ta rage a hanyarmu, dole ne kuma mu kawar da ita. . ********** ********** ********** . Tun safiyar ranar ake ta lullumi, sau da yawa sai ka ga gajimare ya lillibe rana kamar za ayi ruwa, idan kuma an jima can sai ka nemi gajimaren ka rasa. Haka aka yi ta yi a ranar. Mutane sun ji dadin yanayin tun da a kalla dai ko ba ayi ruwa ba gajimaren ya ceto mutane daga zafin dake addabarsu, ta hanyar lullube hasken rana sannan ya saki iska mai dadi. . Misalin karfe goma da rabi na dare, sai gajimaren ya sake mamaye sararin samaniya, a wannan karon harda rugugin aradu da kuma walkiya mai hasken gaske. Sassanyar iska mai ratsa kashi da bargo ta ci gaba da busawa sannan lokaci guda ba zato ba tsammani sai aka tsuge da ruwa kamar da bakin kwarya, nan da nan mutane suka shiga tsereren kaiwa gida wasu har karo suke da yan uwansu garin gudu, saboda ruwan ya zo musu ne babu gargaɗi. Mintina bakwai da faruwar hakan sai titinan Banasariya suka zama babu kowa kamar an share. A can ma daya daga cikin fitattun titunan da aka fi sani a birnin Banasariya, kowa ya shiga gida babu kowa a waje in ka dauke yan kalilan din motocin da ba su da gata wadanda ke tsaye a cikin ruwan yana dukansu. Abin da ido zai iya gani kenan. Sai dai kuma bayan motocin dake tsaye cikin ruwan akwai wasu kuma daban. Mutanen uku suka fito daga cikin duhun jikakken daren, bakinkirin da su kamar aljanu kowannensu sanye yake da doguwar rigar ruwa ta leda tafi da hularki, sannan kuma sawayensu sanye cikin takalmin roba baki, kowannensu rike yake da cocilan, a gaban aljihun kowacce rigar ledar da suke sanye da ita kuma an rubuta cikin kananan harufa (Banasariyya Police). Dogon cikin su ne ya buda tangamemiyar kofar gidan. Yayin da sauran biyun suka bi shi a baya, dayan dan tsattana ne mai fuskar matsorata, dayan kuma dan gajere ne, mai katon kai kamar murhu, kowanne rike da cocilarsa a hannun dama suna dallara haskenta izuwa cikin gidan. Suka ratsa ta cikin kyawawan furanni da shuke- shuken dake farfajiyar gidan, cikin sanda kamar aljannu, ruwan saman kuma na ta zanar su amma hakan ba ta dame su ba, kokarinsu kawai shi ne sukai ga kofar dakin. Lokacin da suka kusa da kofar dakin sai dogon dake yi musu ja gaba ya daga hannunsa sama, sauran biyun suka tsaya cak, lokaci guda kmar a gurin fareti. Suka yi shiru na dan lokaci, ba su ji motsin komai ba, sai ruwan saman dake tafkar saman kwanukan gidan, sannan kuma babu alamar haske a cikin dakunan gidan. Dogon ya yi mamakin abin da ya sa haka. "Ina tsammanin babu kowa a ciki." Dogon ya ce da sauran cikin rada. "Kar dai mu yi saurin shiga," Dan tattsaman ya ce. "Ina ganin mai yiyuwa tana ciki tana barci, abin da nake ganin ya fi shi ne, mu sai mu zagaya ta baya ko za mu ga budaddiyar taga sai mu shiga ta baya mu dan duba" "Haka ne," dogon ya ce da su. "Ni bari na jira ku anan, idan kun shiga sai na biyo ku a baya" Dogon dansandan ya jingina da bangon dakin ruwan saman yana dukansa, amma shi a lokacin zuciyarsa ta tafi ga tunanin abinda ke iya faruwa a cikin dakin. Idan akwai abin da ya ki jini bai wuce tashin hankali ba, irin wadannan mutane irin su Rayyanu abin tsoro ne, domin su na da matukar hadarin gaske. Tun ranar da Aganani ya zabe su a matsayin wadanda za su zo gidan gabansa yake faduwa, sakamakon wani mummunan tunani da ya darsu a zuciyarsa. Tsayiwar da yake a halin yanzu cikin ruwan saman, tunanin ne a zuciyarsa. "Yanzu idan suka sami irin mutanen su Rayyanu ya zasu yi. Yan safarar miyagun kwayoyi suna da hadarin gaske saboda mafi yawancin su suna da bindigogi ba su kuma da cikakken hankali. Jikinsa ya dauki rawa,duk da ruwan saman da ake shekawa kamar da bakin kwarya hakan bai hana shi gumi ba. Ya lalibi bindigarsa dake kwibinsa na hagu, ga mamakinsa sai ya ji bindigar ba ta kara masa kwarin gwiwar komai ba, kuma bugu da kari ko harba bindigar bai taba yi ba, rabonsa da harba bindiga tun a gurin koyon aikin dansanda. Sannan mafi wayancin aikin da ake sa shi ba su kai wannan hadari ba, jikinsa ya sake daukar rawa a karo na biyu. "Yanzu idan Surayya na tare da wasu cikin dakinfa?" ya tambayi kansa. Saura kadan ya shide gurin don tsoro lokacin da yaji an kwankwasa kofar da yake tsaye kusa da ita. "Babu kowa ciki, kana iya shigowa" wata murya ta ce da shi. Dogon dansandan ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya gane muryar dan gajeren nan ce. Mintuna biyu da faruwar hakan sai gasu a tsakiyar dakin shakatawar. Ba su kunna lantarkin dakin ba, maimakon hakan sai suka yi amfani da cocilarsu domin nazarin dakin binciken gaggawa ya tabbatar musu ba bu komai na karuwa a dakin sun bincika lungu-lungu na dakin amma ba su ci nasarar ganin koda kundin hotuna daya ba. Adaidai lokacin ne tocilar dantsamiririn dan sandan ta hasko tangamemen hoton Surayya dake jikin bangon dakin yansandan uku suka yi ajiyar zuciya daga daya ba bukatar sake dogon bincike, kowa ya san ko hoton wacece hoton Surayya monika ne, hoton yarinyar da suke nema ruwa a jallo. *** Alhaji Banasare ya juyo a firgice sannan kuma cikin mamaki, kafin ya bude baki yansandan sun buga masa agogon maza (Ankwa) Sannan suka tura shi waje suka je cikin motarsu suka yi gaba da shi, shi kansa bai san inda za su kai shi ba. Yan sa'o'i kadan da faruwar hakan, motar asibiti tazo tana jiniya ta dauke gawar Rayyanu daga dakin Alhaji Banasare. Wasu daga cikin mutanen unguwar ba su yi mamakin kama Alhaji Banasare ba, saboda tuni daman tsurku da gulma sun cika gari cewa dan safarar kwayoyi ne, yayin da yan karawa miya gishiri suke cewa wai dan yankan kai ne, haka dai aka yi ta surutai, kadan daga cikin mutanen unguwar ne suka tausaya masa, wanda mafi yawancinsu masu ci ne a gindinsa. Bayan da suka yi tafiyar yan mintina sai Alhaji Banasare ya ji motar ta tsaya, yansandan biyar suka cakumo shi suka yiwo waje da shi yayin da sauran suke tsaye a baya suna muzurai da dogayen bindigogi a hannunsu. "Ban san laifin da na yi muku ba" Alhaji Banasare ne yake cewa da yansandan. Sannan ga mamakinsa sai ya ga ashe bakin ruwa aka zo da shi. Wani dankareren jirgin, ruwa ya yi wa idon Alhaji Banasare sallama launin fari da shudi ne. Sannan a jikin jirgin an rubuta (Banasariyya Police) Yansandan suka tusa keyarsa zuwa cikin jirgin ta hanyar yin amfani da matattakalar da ta gangara har bakin gabar kogin...... . "Yana da kyau na san laifin da na yi.." kafin yakarasa wani katon dansanda mai mukamiki kamar marikin lema ya yi taku biyu gaba ya wanke shi da mari tas!! Jini ya fara zuba daga bakin Alhaji Banasare. "Ba ka ma san abin da ka yi ba?" Dansandan ya buga masa tsawa. "Maraba gasasshe" ya ce sannan ya fashe da dariya. Shi ne babban yaron Aganani Mu-sha-gara, ɗan gajere ne mai katon kai kamar murhu. . ********** ********* *********** . Ma'aikacin ya buda baki kamar zai yi magana amma kalmar da yake son fada ba ta sami fitowa ba. Surayya ta dube shi a daidai lokacin da ta Mike tsaye. "Na gode" Ta ce da shi, tana murmushi. "Sai yaushe kenan?" ta tambaye shi tana lumshe idanu. "In da son samu ne na samu adireshinki ko kuwa me ki ka gani?" Ya tambaye ta. "Sunana Aliyu, ke kuma ga shi ban san naki sunan ba" "Kada ka damu," ta ce da shi, "Sunana Sa'adiyya shi kenan? Bari na baka adireshin nawa" ya yi shiru ya miko mata biro da takarda ta zana masa adireshin iska, shi kuma dadi ya rufe shi azatonsa gaskiya ne. "Zan tafi Aliyu na gode, ina zuba idon ganinka" Suna bude kofar dakin sai ta ji hayaniyar jama'a ta sake cika mata kunne suka nufi kofar fita daga dakin karbar hotunan, Aliyu a gefen ta suna hira kamar da gaske. . Dogon dansandan ya rufe jaridar da yake karantawa, sannan ya yi mika. Shi daman tuni yayi zaton haka, ya san wahalar banza kawai za su sha, idan banda yana jin tsoron Aganani da ba abinda zai sa shi wannan aikin wahala. Ya dubi agogonsa, yayi kimanin sa'o'i biyar kenan yana gurin yana jiran gawon shanu. "Yaushe za'a ce ka yi ta duban yarinya guda cikin dubunnen jama'a" ya ce cikin zuciyarsa. Daga inda yake yana iya hangen mutane suna shiga suna fita daga dakin karbar hotunan. Ya yi mamakin abin da mutane suke yi da hoto har suke wahalar da kansu haka, shi dai indai ta shi ne da ba a dauki hoto ba, domin shi hoto in ba wanda ya shafi aikinsa ba bai damu da shi ba ko kadan domin shi a gurinsa barnar kudi ne. Ya sake duba agogonsa, sannan ya mike tsaye. "Abin kwai da ya fi shi ne, na yi tafiyata gida na huta in ya so da yamma na sake fitowa domin na san wahala ce kawai, tun daga shi.." Numfashinsa ya dauke, lokacin da ya ga yarinyar ta nufi bakin titi, yar bakar jaka a rataye da ita. Duk a cikin yansandan Banasariya babu wanda yafi shi tsoro da lalaci, sai dai kuma idan akwai abin da ya fi kwarancewa akai shi ne gane SIFFAR YAN ADAM. "Ko shakka babu wannan ita ce Surayya. Irin yadda ya ji gabansa ya fadi shi ya kara tabbatar masa da hakan. Ya yi sauri ya nufi inda take. "Hajiya Ji mana" Ya ce da ita. Da farko ba ta yi zaton da ita ake ba, amma jin ya dada kiran sai Surayya ta juyo, gabanta ya fadi lokacin da suka yi ido hudu da dansandan, ita kanta ba ta san dalilin faduwar gaban ba. "Hajiya muna bukatar dan wani jawabi daga gurinki" kafin tayi magana, sai ta ga ya tsaida mota "Police Station" Ya ce da dan-taski din, muryarsa na rawa. . ********** ********** ********* . Alhaji Banasare, ya dulmiya cikin kogin tunanin abin da ke faruwa kamar a mafarki. A duk lokacin da ya hada uku da uku sai ya ga biyar, amma a halin yanzu ya fara ganin shida. Babban abin da ya fi daure masa kai shine, dalilin dayasa ake son dora laifin kisan Rayyyanu akansa. A iya saninsa, babu wani ma'aikacin hukumar da ya san sirrinsa da kuma sana'arsa ta fasakwaurin miyagun kwayoyi. Sai dai kawai jita-jita da ake yi agari. "Jita-jita kuma irin wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya, domin duk sa'ad da jama'a suka fahimci kana samun makudan kudi, kuma ba tare da sun san wata takamaimiyar sana'ar ka ba to dole ne ka ji irin wannan jita-jita. "Aganani Mu-sha-gara ne kawai ya san sirrina" Banasare ya ce cikin zuciyarsa. Gidan ya yi shiru ba ka jin komai sai sautin zubar ruwa a kwanukan gidan tuhumar. Alhaji Banasare ya muskuta a cikin kurkukun dakin da aka kulle shi ciki, hannunsa da kafafunsa a daure tamau da agogon maza (Ankwa). Ko shakka babu yanzu yasan wanda ya kulla masa wannan sharrin. "AGANANI?" Ya tambayi kansa. Uku da uku da sun fara ba shi shida, Aganani Mu-sha-gara ne, abin da ya karawa lamarin launi MA shine, gawar Rayyanu da aka kawo dakinsa. Yau da a ce kama shi kawai aka yi ba tare da an kawo gawar wani dakinsa ba to da sai ya yi tsammanin ko kawai zargi ne ya tsananta a kansa aka kama shi. To amma gawar Rayyanu ita takara tsoratar dashi, yanzu kam ya san kamun da aka yi masa na yan wasu mutane kalilan ne dake son cimma wani burinsu. Ya zargi kansa saboda saurin amincewa Aganani mu-sha- gara da ya yi. Naira miliyan arba'in ba abar amincewa kowa ce ba. Yanzu kam ya gane duk abinda Aganani ke shirin aikatawa. Jikinsa ya dauki rawa saboda wani tunani da ya Fado zuciyarsa. Ko shakka ba ya yi yanzu ya san hodar Iblis din na hannun Aganani, "Wannan shi ne dalilin kashe Rayyanu" Ya ce cikin zuciyarsa. Jikinsa ya sake daukar bari lokacin da ya tuna da shi kadai kenan ya san da maganar hodar Iblis din. Saboda haka shi ma yanzu rayuwarsa na cikin hadari gumi ya rufe shi sharkaf. Ya motsa hannayensa da kafafunsa dake daure tamau. Idan ya motsa su sai ya ji kamar kara daure shi suke. "Ina hanyar tsira?" ya tambayi kansa. A wani zamani da ya huce, Alhaji Banasare ya yi sanadiyyar Mutuwar mutane da dama, in dai za ka kawo cikas ga sana'arsa to sunanka matacce. Amma duk da abin da ya yi a da, ya fi kowa tsoron mutuwa. Idan akwai abin da ya fi tsoro da fargaba bai wuce mutuwa ba, wannan shi ne abin da yasa ko makabarta ba ya son zuwa. Idan an yi rasuwa a makwabtansa, sai dai ya aika likkafani da turare a matsayin sana mai kudi ya sake jijjiga ankwar dake hannunsa, sai ya ji ta sake daure shi tamau kamar hannayensa za su yanke su fadi. Ya rufe idonsa jikinsa na bari lokacin da ya tuna da irin tukwanen da ake jerawa a saman kabarin matacce. Mutuwa!! Hakika yana tsoron mutuwa, duk da yake kuwa shi ma a zamaninsa ya yi sanadiyyar asarar rayukan jama'a da dama. . ************ ******* ********** . "A wane dalili!" Surayya ta ce da dansandan cikin tsawa a daidai lokacin da dan taksi din ya ja ya tsaya a gabansu tuni har yara sun fara taruwa agurin. "Kin ga ba...ba wani dogon surutu na nema da ke ba kawai dai na ce muna son magana da ke ne..." "Ba za ni ba!!" Ta ce da shi cikin karaji, "Me ka dauke ni ne yar iska ko me, na ce ni ba za ni ba! Ba na ra'ayinka!! Bana kaunarka!! Dole ne sai ka takura min na bi ka? To na bika ina..." "Malama dakata, ban gane abin da kike nufi ba." "Ai daman ba za ka gane ba, tun da abin naka babu gaskiya." Kafin kiftawa da bismilla ta tara masa mutane, nan da nan gumi ya fara ketowa daga goshin dansandan. Wasu daga cikin mutanen suna kokarin su tambayi abin da ke faruwa amma fargaba ta hana su, saboda ganin rigimar da dansanda ne ba su sani ba ko wani laifi ta yi yake son kamata. Dan taksi din da dansandan ya tsayar ya ga za'a bata masa lokaci, sai ya sauke gilashin tagar gaba ya leko da kansa yace, "Yallabai ko na yi gaba ne?" "Jira...jira ni minti biyu" dansandan ya ce yana in'ina, sannan ya juyo ga Surayya wacce tuni mutane yan tsurku har sun fara tambayar ta abin da ke faruwa." "Wai kawai don ya nemi ya cusa kansa a gurina nace ba na ra'ayinsa, shi kenan wai na yi laifi." Surayya ce take fadawa jama'ar dake tambayarta. Nan da nan gurin ya dau hayaniya saboda jin abin da Surayya ta fada. "Yallabai gaskiya ba haka ake yi ba." Wasu daga cikin tsagerun samarin da suka taru a gurin ne suke cewa. Mutane da dama a gurin ba su yi ko da shakkar abin da Surayya ta fada ba, saboda al'adar mutane a yanzu sun dauki dansanda a matsayin wanda ya fi kowa iya sharri. "Malama da ke nake fa, gara tun wuri ki zo mu tafi ki amsa tambayoyinki, cikin arziki tun kafin na dauki mataki matsananci akanki." Duk maganar da dansandan nan yake ta karfin hali ce, saboda shi a gurinsa ba don kunyar idon jama'a ba da tuni ya bar ta ta tafi, ba don komai ba kuwa sai don abu guda. Tuni ya fara addu'ar Allah ya sa kar wani dansanda dan uwansa ya zo wucewa ta gurin. Saboda idan suka kai ta ofishin yansanda ya ce da su ya kama ta da me?" Muddin ya fadi dalilin daya sa ya kama Surayya to hakan na nufin ya tona sirrin Aganani, domin kamun da za ayi mata na Aganani Mu-sha-gara ne ba kamun hukumar yansanda ba bakuma sa son kowa ya sani. Jikin dansandan ya dauki rawa da ya tuna da aika-aikar dake shirin faruwa shin yanzu idan hakan ta faru yaya zai yi da Aganani? Ya tambayi kansa cikin fargaba, Aganani na iya kashe shi. "Ba za ni ba, sai dai ka kashe ni!!" Surayya ta ce da dansandan cikin karaji. Wasu samari guda biyu karti, madoka kato kuma bakake, suka diro a gurin kamar an jefo su daga sama, daga su sai yankakken gajeren wando iya gwiwa babu riga, kowannensu rike da galan din fetur, daya daga cikinsu rike yake da galan din fetur guda biyu. Dayan kuma galan din fetur ne daya kawai rike a hannunsa na dama, hannunsa na hagun kuma rike da tsinkakken takalminsa silifa launin rawaya. Tun kafin a karasa sanar da su abin dake faruwa suka ce, "Karya ne!!!" gaba dayansu. "Ba ka isa ka kafi da ita ba, rashin mutuncin naku ya tashi daga kan yan cuwa-cuwa kuma ya koma kan mata?" Sannan dayan ya dubi dayan ya ce, "Kai baba!! Wannan bawon ba shi bane ya yi mana rashin mutunci kwanaki ba, ka gane shi ai? Shi ne wanda rannan ya rike ƊANBA'U ya ce sai ya kai shi. "Ah! Ah!! Ah!!!" Dayan ya ce cikin karaji "Na gane shi ai baba, Wallahi ba za ka tafi da ita ba, sai dai ka tafi da mu. Mu daman mun saba karo da ku." Saurayin daya ya shiga tsakanin dansandan da Surayya. Damar da dansandan ke jira kenan domin tuni daman ya gaji da cacar bakin shi ma so yake Surayya ta bar gurin kar abin da yake tsoro ya faru. Dansandan ya yi wuf ya rike gefen gajeren wandon saurayin da ya shiga tsakaninsu da Surayya. "Rike ni da kyau, ni na isheka...!!" Saurayin ya ce da shi yana ciccije baki. Dayan saurayin ya yi sauri ya tsaida babur sannan ya ce da Surayya: "Hau ki tafi yan mata ki bar mu da karamin ARNE." . Surayya ta dan yi jim amma jin mutanen dake gurin sun kara mata karfin gwiwa sai ta hau dan kabu- kabun ya sa giya sannan ya falla da gudu da Surayya wacce ke bayan babur din wasu daga cikin mutanen dake gurin da kuma yara suka dauki sowa da tafi gabadaya. Sannan kallo ya dawo kan dansandan da samarin wanda tuni sun fara kokawar kwacewa daga hannun dansandan, wannan ba wani sabon al'amari ba ne ga yan cuwa-cuwa. . *********** ********** ********* . Tun zuciyarsa na bugawa gami da mummnan tunanin abin da yake zaton zai faru gare shi, har dai daga karshe tsoron da fargabar suka gushe sannan bakin ciki da fushi da kuma tunanin ramuwar gayya suka maye gurbin. Alhaji Banasare ya fara haure-haure, sannan zazzafan hawayen bakin cikin halin da yake ciki ya fara kwaranya akan kumatunsa. Abin da ya fi bashi haushi fiye da komai shi ne cin amanarsa da Aganani ya yi, ya dubi shekarun da suka wuce tun Aganani mu-sha-gara yana karamin dansanda suke harka tare, amma abin mamaki sai gashi yau ya ci amanarsa... Tunaninsa ya katse lokacin da kofar dakin ta bude sannan yansandan uku suka shigo suna muzurai, kowannensu dauke da zungureriyar bindiga harbi ka ruga. Ba su yi masa magana ba, sai suka cakumi babbar rigarsa, wani kuma ya dauki kafafunsa suka fito da shi daga cikin dakin mai kamar akurki. Suna zuwa sai suka jefar da shi tim!! A tsakar dakin mai kamar akurki. Suna zuwa sai suka ja da baya suna kallonsa, kamar yadda kuraye ke kallon naman da suke shirin fadawa. Mintunansu uku da rabi a gurin tsaye, kamar an dasasu. Kofar dakin ta bude sannan Aganani mu- shagara ya shigo dakin, sankonsa na kyalli kamar an haska madubi da fitila, sannan kansa na barazanar taba saman dakin. Shigowarsa ke da wuya sai duk yansandan dake gabansa suka zama yangajeruna duk da yake kuwa suna da tsayi. Irin yanayin da ya bayar yayi kama da yanayin da zaka gani yayin da rakumi ya tsaya a gaban shanu. Shirun dake dakin da kuma kasancewar Aganani mu-sha-gara su suka sauya yanayin dakin lokaci guda, kamar yadda kalanzir ke sauya ruwa. Yansandan suka kame kamar ruwa ya cinye su fuskokinsu suna duban kasa, sannan zuciyoyinsu na harbawa kamar yadda manunin dakika ke harbawa. "Ku kunce shi." Aganani ya ce da yansandan. Kafin kiftawa da Bismillah sun kunce Alhaji Banasare. Mutanen biyu wadanda yan kwanakin da suka wuce abokaine suka dubi junansu alamun tsana karara suke a fuskokinsu. "Ka ba ni mamaki Aganani" Alhaji Banasare ya ce muryarsa na rawa. "Ba abin mamaki bane idan aka yi la'akari da irin kudin dake cikin harkar." 45,000,000 Miliyan arba'in ba karamin kudi bane da har za'a iya amincewa wani akanta, ina tsammanin ba dukkan zuciya ba ce za ta iya hakurewa miliyan arba'in. Kasa kanka amatsayina za ka gane cewa idan kai ne ni da abinda za ka yi kenan. Ka dade kana jan zaranka yadda kake so, saboda haka ni ma lokaci ya zo daya kamata na ja nawa zaren. Aganani mu-sha-gara ya yi shiru, sannan ya ci gaba da cewa. "Ban ji dadin abin da ya faru ba tsakaninmu da kai Banasare, saboda ka kyautatamin a baya duk da yake dai nasan bautar da nayi ma tafi karfin abin da kake bani, wannan shine dalilin da yasa nayi amfani da wannan dama don ganin nima na gina kaina, Aganani ya yi murmushin mugunta sannan ya ce. "Zan yi maka taimakon karshe Banasare, taimakon da zan yi maka kuwa shi ne na kashe ka domin ina ganin mutuwarka tafi zamanka, kuma hakan shine zai hutar da kai kuma ya hutar da ni. . *********** ********* ************ . Karar wayar talfon din ta cika dakin sannan koriyar danjar dake jikin kan talfon din ta yi haske. Aganani ya nufi talfon din da sauri koriyar danjar na nuni da cewa yaronsa ne ke bugo wayar karfe bakwai da rabi na dare, agogon dake jikin bangon dakin ya nuna, Aganani ya yi mamakin abin dake tattare da waya domin yaransa basu saba bugo masa waya ba a irin wannan lokaci. "Yaf!" Aganani mu-sha-gara yace cikin kan talfon din. "Banasare ya gudu!!" wata murya taceda shi daga can daya bangaren irin yadda sautin muryar me maganar ke fitowa ta cikin talfon din, shi ya sa Aganani tunani cewa kadan ya rage mai maganar ya fashe da kuka saboda fargaba. Fuskarsa ta koma toka-toka, sannan idanunsa suka yi jajur kamar gauta fuskarsa ta yamutse kamar an taka dan tunfafiya, "Me kuke nufi da ya gudu!!!" Aganani ya yi haushi cikin talfon din. "Wal..wallahi...yallabaimuma saida muka sami kanmu sumammu sannan... "Ya isa haka sakaran banza!!" "kuna nufin kace sumar da ku ya yi?" "Haka aka yi yallabai lokacin da ka bar mu ji..jiransa kafin ya gama cin abinci shine... "Yi min shiru shashasha! Saurara da kyau, ina son ku zagaye duk wata kofa da kuke tunanin za ta iya bashi hanyar gudu, nasan ba zai iya guduwa ba, yana nan ku yi kokarin samun sa kafin nazo." "Abin da ka ce shi za'a yi yal..yallabai" mai maganar ya ce cikin in'ina. Aganani ya yi shiru na dan lokaci sannan yace: idan har kuka sake ya gudu baku kama shi ba to ina baku shawarar da kowannenku ya sai wa kansa likkafani kafin na karaso." ya ajje kan talfon din kararaf! Yana huci kamar kumurcin maciji.. . ********** ********* ********* . Alhaji Banasare bai gasgata abin da kunnensa suke jiye masa ba. Ya yi saroro yana sauraran Aganani Kamar wanda yake tsammanin ya tabu. Kamar ya san abinda ke zuciyarsa sai Aganani mu-sha-gara ya ce: "Ko kusa kar ka yi tunanin ba kaina daya ba, da hankalina abin da nace haka ne babu ko shakka aciki, daidai kaji ba wai kunenka ne yake karya ba." Sannan ya ci gaba da cewa. "Bari na maimaita abin da nace babu mamaki lokacin ko gayan tuwo ya toshe ma kunne abin da nace shine, mutuwarka tafi rayuwarka, itace kuma zata hutar da ni ta hutar da kai." Kakkausar sautin muryar Aganani ya daki dodon kunnen Banasare, sannan lokaci guda jikinsa ya dauki bari, abinda ya gani a idon Aganani mu-sha-gara, shi ya tabbatar masa da cewa Aganani na iya aikata abinda ya ce. "Bai kamata ka yi

Chapter 5 of 9