Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
Alhaji Banasare ne, "Dauki Rayyanu" wata zuciyar ta ce da shi. Ya dauki kan talfon din, sannan ya tambaya "Wace ce?" . "Saurara da kyau." Aka ce da shi "Ni ce Surayya Monika, da kuma za ka dauki Shawarata da sai na ce da kai kayi sauri ka hada tsummokaranka ka bar garin nan tun da sauran kwananka, Ubangidanka ya turo yansanda za su kama ka kasan kuwa in suka kama ka to kashinka ya bushe." . "Me kike nufi?" Rayyanu ya tambaya. "Kin ga Surayya Wallahi idan ba so ki ke..." Rayyanu ya yi shiru. Idan har ba kunnensa ne ke fada masa karya ba ya ji kukan jiniyar yansanda. A can daya bangaren talfon din Surayya ta kyalkyale da dariya, sannan ta ce "SUN ISO. Habawa! Dan samari, duk sharrinka kalilan ne akan na mace, sakayyar kisan da ka yi wa Mu'azu ce ka fara gani tun a duniya." . "Idan sun kama ni ba!" Rayyanu ya ce a fusace, "Idan kuma na ƙwace kashinki ya bushe! Yarinya wannan dai kin yi nasara, amma ki tuna fa ba kullum take juma'a ba, . "Mu zuba mu gani dan samari." Surayya ta ce, ko Surayya dake can daya bangaren tana sauraro ta ji kwakkwaran dukan kofar dakin da yansanda suka fara yi ta yi sauri ta aje kan talfon din. . ********** ********** ********** . Rayyanu ya leka tagar dakin, a daidai lokacin da aka ci gaba da dukan kofar da kafa daga inda yake tsaye yana hangen yan doka guda uku suna jiransa a gindin hawan benen, a kofar otal din kuma M.K. Aganani Mu-sha-gara na zaune yana zazzare idanuwa, salula a hannunsa yana ta faman babatu kamar zai amayar da hanjin cikinsa, jajayen idanunsa, hade da kakkauran gashin bakinsa, su suka sa yawun bakin Rayyanu ya kafe, "Hanya mafi sauki na gudu, domin idan na yi musu bayani ma a banza" Rayyanu ya ce a cikin zuciyarsa, yanzu kam ya tabbatar kashinsa ya bushe idan suka kama shi, ya tabbatar yansandan Alhaji Banasare ne suke yiwa aiki don haka duk wani bayani ma a banza, hanya mafi sauki ya gudu. Aka ci gaba da dukan kofar da kafa, tuni har kofar ta fara alamun yin saranda, Rayyanu ya leka tagar dakin, har yanzu yansanda na nan, don haka sai kawai ya ja da baya ya fara tunanin abin yi kofar dakin ta bada kara, sai ta fara budewa kadan- kadan, ko da Rayyanu ya lura sai ya ga ashe yansandan su biyu ne aka turo masa, don haka sai kawai ya nufi karkashin tangamemen gadon dake dakin ya shige ciki, idonsa akan saitin kofar dakin, bai fi dakika goma da shigewa ba, kofar dakin ta balle da wata irin kara marar dadin ji, kofar ta fadi kan kafet din tsakar dakin, yansanda biyu suka bayyana a dakin, suna dube-dube, ba su ga komai ba, Rayyanu yana ganin kafafunsu, don haka sai ya matso gaba-gaba yana jan ciki a daidai lokacin ne yansandan biyu suka matso gaba-gaban gadon suna dube-dube, Rayyanu ya ziro hannayensa biyu ya kama kafar yansandan dai-dai ya fizga da karfi, yansanda suka zube babu shiri daya daga cikin yansandan ya yi ƘARAR RAZANA Rayyanu ya yi sama gaba daya ya ɗago da gadon, ya rufe yansandan, sannan ya nufi kasan benen da gudu, bai dade ba ya zo matattakalar da za ta kai shi kasan benen na karshe don haka sai ya fara tafiya a hankali, ko da ya karaso sai ya leko a nan ne ya ga yansanda biyu, su kuma suna hawowa bene, ya yi wuri-wuri ko zai ga gurin buya babu, ya kama kofar wani daki zai shige sai ya ji a rufe, ya juya kuma zai koma baya da gudu sai ya jiyo wadancan yansandan da ya rufe da gado su kuma suna biyo shi don haka sai kawai ya yi kan wadancan na gabansa da gudu, kafin su farga ya banke su ya wuce idonsa ya rufe ba ya ko tunanin akwai saura a waje bai tsaya ba yana gudu sai ya ji wani abu mai kama da kafar doki ya daki kafarsa ya kwalla kara a lokaci guda kuma ya fadi, ya dago kai suka yi ido hudu da wanda ya yi dukan. Aganani Mu-sha-gara ne. . *********** ********** *********** . Surayya ta aje kan talfon din sannan ta yi murmushi, sannan ta ce cikin zuciyarta "Kadan ma ka gani azzalumi" Tana zaune akan kujerar da Grace ta saba zama ne. Lokacin da Surayya ta yi nasarar kwace hodar iblis din nan daga hannun su Rayyanu sai taga babu wani waje da zata ji dadin buya sai gidan su Malam Jackson, da matarsa Grace, tun da ga shi yanzu tana da kudi, me zai sa ta dami kanta, abin kawai da za ta yi shi ne ta sayo kayan abincin da zai ishe ta, ta yi zamanta a nan gidan tunda ba kowane ya san da gidan ba. Zaman da take a yanzu a cikin babban falon Jackson take, da kuma talfon dinsa take amfani gurin aikata abin da taso. Koda ta aje talfon din sai ta ga ya kamata ta tafi bakin gabar kogin domin ta sha iska, don haka sai ta koma dakin barcin da Grace ta saba amfani da shi kafin ta tafi. Inda kuma a nan ne Surayya ta ke kwanciya a yanzu, a nan ne ta zabo yar karamar singileti fara, sannan ta daura zanen atamfa kore mai adon furanni, launin gwal, bayan ta gama shiri tsaf, sai ta nufi bakin kogi. Tana zuwa sai ta shige cikin jirgin ruwan da ta dauka, haya lokacin da za ta gudo, ta yi zamanta a ciki tana tunanin kuma abin da zai biyo ba ya, abin da take jira ta ji shi ne shin yan sanda sun kama Rayyanu, ko kuwa ba su kama shi ba, idan ba su kama shi ba, ita za ta shiga nemansa har sai ta danka shi a hannunsu, idan kuwa sun kama shi, to burinta ya cika kenan, "Saura da me kuma?" ta tambayi kanta "Saura HAIDAR" zuciyarta ta ba ta amsa. UMMUL ABA'ISI, kenan wanda shi ne salsalar duk abinda yafaru. Tabbas saura shi. "ta ce cikin sassanyar murya, "Sai shi ma ya gane kuskurensa" Ga mamakin Surayya, sai ta ji tana tausayinsa. "Shin har yanzu daman son Haidar na cikin zuciyarta? Ta tambayi kanta?" Sassanyar iskar bakin kogin ta ci gaba da kada gashin kan Surayya, masu santsi da sheki, daya daga cikin mayen karfen da ke jan hankalin duk namijin da suka yi ido hudu da ita kenan "HAIDAR! haba zuciya kar ki zalunce ni mana, bana son Haidar na tsane shi" ta ce a hankali. Ita kanta ba ta yarda da kalamin da ta furta ba, hakika ta san har yanzu akwai soyayyar Haidar a tare da ita "Amma dole ne na nuna masa kuskurensa. "Yadda ya wulakanta ni sai na rama.. Tunaninta ya gushe, adaidai lokacin da ta ji dirin karar injin jirgin ruwa. Ta yi mamakin jin hakan, domin duk iya zamanta da su Jackson bata taba ganin babban jirgi ya wuce ba, amma da taji karar injin wannan jirgin ta san kato ne. Ba'a dade ba sai ga jirgin ya bayyana a fili, ga mamakinta sai taga a hankali yake tafiya, tana kuma iya hango yansanda hudu akan saman jirgin kowannensu rataye da bindiga na biyar din neba tagane ba, wanda shi ta lura kamar a kwance yake, hannayensa a daure a bayansa. Duk ta sami ganin hakan ne sakamakon hasken fitilar cikin jirgin ruwan da ta haskake ko'ina cikinsa, amma babu alamar fitilar waje. Zuciyar Surayya ta fara bugawa tsakanin hakarkarinta, "Kamar Rayyanu" ta ce a hankali, lallai kuwa shi ne. Ta gane hakan ne ta hanyar wani dansanda da ya tashi Rayyanu zaune, ya kwara masa ruwa akai. "Ina za su kai shi" ta tambayi kanta, a daidai lokacin ne to jirgin ya matso kusa da inda take yana tafiya a hankali, nan da nan Surayya ta yi sauri ta fice daga jirgin ta buya a tsakanin sarkakiyar bishiyoyi da ciyayin da suke bakin kogin. Daga inda take boye tana iya hangen fentin jirgin ruwan fari sol, an yi masa layi da fenti launi kore, a tsakiyar koren kuma an rubuta da bakin fenti "Banasariyya Police" Ba'a dade ba, jirgin ya wuce inda take boye bayan ya dan gota ta kadan sai ta yi sauri ta koma cikin gidan da gudu, tana zuwa ta buda wata loka, ta yi sa'a ta sami abin da take nema kyamarar Malam Jackson ce. Ta sha ganinsa yana buda lokar yana daukowa, ga shi cikin sa'a bai tafi da ita ba, ta buda kyamarar babu sauran dodon daukar hoton a ciki, amma akwai sabo wanda ko amfani ba'ayi da shi ba, a kusa da kyamarar a ajje. Ba a dade ba da yin hakan sai ga Surayya cikin jirgin ruwanta ta dafawa su Rayyanu baya abin duka ya faru ne cikin abinda bai Gaza minti goma ba. . Tafkeken gida ne mai dauke da dakunan gana azaba, irin na yan sandan ciki, har guda shida, kowanne daki yana dauke da masu azabtar da mutum guda shida, babban dakin shi aka kai Rayyanu, tuni har an tube shi daga shi sai gajeren wando. A ka'ida yansandan ciki su suka saba irin wannan tuhumar duk wani mai laifin da yaki fadin gaskiya. A yau kuma sabanin sauran lokuta M.K Aganani mu-sha-gara ne ke azabtar da Rayyanu. Wasu karti guda biyu masu kama da ƙwaɗi, suka kama kafafun Rayyanu suka jefa shi sama, suka kauce ya fado sannan suka haushi da duka tun yana kara har ya kasa sannan Aganani ya daga musu hannu suka tsaya sannan ya matso kusa da Rayyanu ya daki bakinsa da kwabdeden takalminsa. Bakinsa ya fashe jini ya fara zuba, "Ina koken din ta ke?!" Aganani ya daka masa tsawa. "Ban dauka ba." Rayyanu ya ce, "Wallahi Surayya ce." "Karya ka ke fadi gaskiya idan ba haka ba kuma yau za ka gwammace dama ba a haife ka ba." Rayyanu ya yi shiru saboda azaba, kirjinsa kamar zai fashe Aganani ya dakawa kartin tsawa, nan da nan daya katon ya yi tsalle ya fado akan kirjin Rayyanu, ya yi wata irin kara mai ban tausayi da razanarwa, hatta Surayya wacce ke make a kofar dakin tana daukar hoton abin dake faruwa sai da ta tsorata da irin azabar da ake ganawa Rayyanu, ita kanta ta san cikin hadari take yar kafar dake jikin dankareriyar kofan dakin azabtarwar ita ta baiwa Surayya damar daukar hoton duk abin da ke faruwa. Rayyanu ya some, kafin ya farko an kawo wani katon diro cike da ruwa, Aganani ya cakumi wuyansa ya daga shi sama da hannu daya kamar yartsana, sannan ya dilmiya kansa cikin ruwan sai daya daga cikin kartin ya taka cikinsa da kafa, ruwan da ya sha ya fara bulbulowa ta baki da hanci, kamar fashewar mitar ruwa, Aganani mu- sha-gara ya daga hannu suka tsaya, sannan ya matso kusa da shi ya ce, "Yaro! Kar ka yi wasa da rayuwarka akan naira miliyan arba'in, ko ka fada min inda ka boye koken din ko kuma na yankaka da ranka." ya ce da shi cikin tsawa. Bakin Rayyanu ya bude, amma ya kasa magana, abin kawai da ya yi nasarar fitarwa shi ne, "Surayya." "Wace ce Surayya?" Bakin Rayyanu ya sake nuna alamar "Monika." Aganani ya yi fushi, domin shi a zatonsa Rayyanu bai sani ba ya ce don haka ya sake dakawa kartin tsawa "A sake dabara!" ya ce da su. Daga saman dakin, kamar tsafi, igiyoyi biyu suka taho a daure a bakin kowacce igiya kugiya ce. Aka yi sama da Rayyanu kamar kara, suka raba kafafunsa biyu, suka daure shi kowacce kafa a daure a jikin kugiya daya. Sannan suka fara lila shi tun Rayyanu na numfashi har ya kasa, su kuwa ba su daina ba, suka ci gaba da tsalala masa bulalar wayar lantarki, duk bayansa ya fashe, yana ta zubar da jini, Aganani mu-sha-gara ya daga hannu suka tsaya, sannan ya matsa gaba, kusa da ina kan Rayyanu ke lilo kafafunsa a sama "Wace ce Surayya?" Bakin Rayyanu ya ce "Monika." Bakin ciki ya sake kama Aganani har yanzu shi ya dauka Rayyanu ban sani ba yake cewa, cikin fushi ya zaro wuka mai kaifi daga aljihunsa ya yanyanke igiyoyin da Rayyanu ke lilo akai, ya fado kasa da wuya, sannan kafarsa ta dama ta dan motsa bai ko kara motsawa ba, Aganani ya daga shi tsaye sai ya ji ya yi nauyi, yana sakinsa sai ya fadi sharkaf. Surayya ta dauki hoton gurin, sannan ta zurare ta tabbata Rayyanu ya mutu. . Aganani ya ja da baya sannan ya zaro farin kyalle daga aljihun rigarsa na gaba ya goge fuskarsa, da kuma sankonsa wanda ke kyalli, "Ya mutu." ya ce da kartin, da kuma sauran yansandan da ke dakin. "Abin da ya rage yanzu shi ne mu nemi yarinyar da ya ke ta fadi Surayya, na tabbata koken din tana wajenta, amma idan har muna son mu sami dukiyar mu cikin ruwan sanyi dole ne mu san yadda za'ayi mu kawar da mutum guda." yansanda suka kalle shi idanuwan su cike da tambayar abin da yake nufi, "Abin nufi a nan shi ne..." ya ci gaba da cewa, "...kun san yanzu babu wanda ya san da hodar Iblis din daga mu sai Alhaji Banasare, sai kuma yarinyar nan Surayya, wacce yanzu na tabbata ta dauki hodar iblis din, saboda haka idan muka kawar da Alhaji Banasare ya rage daga mu sai Surayya kenan, muna kama ta an gama. Kudi ya zo kenan kuma kowannen ku dama dazu na fada muku abin da zai samu naira miliyan daya da rabi, kunga duk sai mu yi ritaya, ko me kuka gani yara?" Ya tambaya yana zazzare idanu. "Haka ne yallabai!" Suka amsa gaba dayansu, dakyau yarana, saboda haka yanzu ga abin da ya kamata mu yi wajen kawar da Alhaji Banasare." Sannan ya fara fada musu shirinsa na makirci. Bayan ya gama sai ya sami mutum hudu, ya ce "ku za ku kai shi." sannan ya nuna dayan ya ce, "kai kuma gobe karfe bakwai na safe zan jira ka a ofishin kwamishina, bakwai daidai ka bugo waya, ka sanar da shi cewa akwai rikici a gidan Alhaji Banasare, ka gane ko, ni kuma zan yi sauran." "Yes Sir" dansandan ya amsa, gaba dayansu suka watse. . *********** ********** ***************** ******** ********* Misalin karfe hudu da rabi na asuba, Alhaji Banasare ya fito zuwa danƙareren masallacin Allah ga nakan da ya gina, a kofar gidan shakatawarsa, wanda kuma wai shi ne babban limamin duk da yake kuwa shi kansa bai san ka'idodin zama liman din ba. Ba'a dade ba ya tada sallah guntun talakawan unguwa wadanda kwadayin abin duniya ya tsone wa ido suka bi shi. Yansandan hudu dake jiransa ya fita tun awowi biyu da suka shude suka shige gidan dauke da gawar Rayyanu suna yi mata cali-cali suka shige cikin gidan da ita ba'a dade ba suka fito. Karfe bakwai na safe daidai M.K Aganani ya shiga shimfideden ofishin kwamishinan yansanda na Banasariyya, kamar jiransa dama talfon din yake ya shigo ya daukara, yana shigowa sai ya kame, ya yi gaisuwa irin ta yansanda sannan ya dau kan talfon din, ya fara magana, kwamishin yansanda SULAIMAN S. BABA yana kallon sa. Dan gajere ne kakkaura, shima yana da dan tarin gashin baki, amma ba can ba, ba don Ƙoshi ya yi masa yawa ba, da kuma tsufa da ya fara kama shi, da sai ka kira shi kyakkyawa, yau shekarunsa talatin da takwas kenan yana aikin dansanda, ita ce kuma ta zo daidai da shekarar sa ta goma sha daya akan kujerar kwamishinan yansanda na Banasariyya. Aganani mu-sha-gara, ya aje talfon din, "Menene?" Suleman ya tambaya, "Ni ma ban gane ba" Aganani ya ce "Peter ne ya bugo waya daga unguwar su Alhaji Banasare, wai ya ji hayaniya a gidan kamar ana fada, sun je gidan kuma an ki a bude, to ka san yadda Alhaji Banasare yake a garin nan don haka suka ji Tsoron haurawa." "Kwarai kuwa sun yi daida da suka sanar da mu." Kwamishinan ya ce "Amma ka ce masa su sake "Try" idan ba'a bude ba to su karya gidan su shiga ni na sa su." "An gama Sir." "Ka kuma tura musu karin yara ko abin zai fi karfinsu," Kwamishina ya ce. "Yes Sir" Aganani ya amsa. . Alhaji Banasare ya shigo tangamemen falon dake da doguwar tasbaha tana jan kasa kamar da gaske, yana zuwa sai ya wuce bangaren falon na bangaren kudu yana zuwa sai ya bude kofar da niyyar ya dauko wasu kudade da ya aje su tun shekaran jiya, kofar lokar ta bude gawar Rayyanu ce ta biyo kofar ta fado kan kafar Alhaji Bansare, wanda ya daka tsalle guri guda, sannan ne ya gane Rayyanu shi kansa duk da taurin kansa sai da abin ya girgiza shi, "Rayyanu!" ya kira sunansa, sannan ya durkusa ya dafa kirjinsa. A daidai lokacin ne babbar kofar falon ta bude yan sanda suka cika falon, su bakwai ne kowanne dauke da bindiga harbi ka ruga, "ku kama shi." Wani jami'i Peter yace, yana zazzare idanuwa ba wasa. . *********** *********** *********** . Surayya monika ta yi murmushi, fararen hakoranta suka bayyana afili, lokacin da ta tunkari ma'aikacin wanda ke fitowa daga cikin dakin na'urorin wanke hotuna hannunsa na dama rike da jakar zuba hotunan. "Barka da aiki." Ta ce da shi a daidai lokacin da mutanen dake cikin dakin suka juyo kusan lokaci guda suka dube ta sannan kuma lokaci guda suka maida hankalinsu gurin karbar hotunan kowa na kokarin shiga gaban dan uwansa don mika rasitinsa. Duk da yake na'urar sanyaya dakin na ta kwararar da sansanyar iska hakan bai hana Jama'ar sharbar gumi ba wanda mafi yawansu maza ne, mata uku ne kawai in ka hada har da Surayya cikin lissafinka. "Sannunki da zuwa." Ma'aikacin ya ce da ita, gami da dan murmushi. Suka yi ido hudu da Surayya, zuciyarsa ta buga sannan ya ji tsigar jikinsa ta yi yar!! Jikinsa ya dauki rawa, Surayya Monika ta dan kara matsawa gaba ta sake haske shi da murmushin Allah kashe ni don dadi. "Ki...na bukatar wani abu...ne...." Ma'aikacin ya tambaya muryarsa na rawa. Rabonsa da ganin kyakkyawar yarinya kamar wannan dake gabansa har ya manta, mata da yawa kuma kyawawa su kan zo gurin domin wankin hotunansu amma mafi yawan su ba kyawawa bane, akwai wasu lokutan da kyawawan suke ziyartar gurin sai dai kuma, ba su fiye shigowa cikin dakin karbar hotunan ba, sai dai su zauna cikin mota a waje, su kuma direbobinsu su zo su karbar musu. To amma duk cikin matan da ya gani a baya ba zai iya tuna wadda ta kama ko da kafar Surayya wajen kyau ba. Sannan kuma akwai wani abu dake tare da ita wannan yarinya dake tsaye agabansa wanda ke jan hankalinsa da kuma duk wata nutsuwarsa kamar yadda mayen karfe ke jan karfe. Surayya ta kanne idonta na dama sannan ta ce cikin muryar da za ka iya kira sarewa. "Kwarai kuwa ina bukatar taimako dan samari" Ma'aikacin ya yi murmushi sannan ya ji farin ciki ya lillibe shi don jin cewa an kira shi dan samari. Wasu mutane guda biyu dogo da dan tsattsama wadanda ke tsaye daga baya-baya suna jiran su sami yar kafar da za su mika rasitinsu don karbar hotunansu, suka dubi junansu, sannan kuma lokaci guda suka dubi Surayya cikin mamaki domin jin cewa ta kira ma'aikacin wai dan samari. Mutanen biyu suka yi murmushi, tsakaninsu da su Surayya bai fi taki uku ba, amma duk da haka sun ji abin da take fadi Dogon mutumin ya kalli dan tattsaman sannan ya matsa kusa da shi ya yi kasa-kasa da muryarsa sannan ya ce. "Ka ji abin da take cewa da shi kuwa? Wai dan samari." Suka tuntsure da dariya sannan suka tafa, dan tsamirmirin ya ce da dogon. "ya kusa sa'an ubanta fa dubeshi ka gani zai kusan shekara arba'in da biyu, kawai don dai yana jin dadi ne don haka bai motse ba, amma ka ji don daurewa karya gindi wai dan samari! Tab!! Agaishe da samari." Suka sake fashewa da dariya, hakan ne ma ya sa har wasu daga cikin mutanen dake turmutsitsin karbar hotunansu suka juyo domin ganin abin da samarin biyu ke yi wa dariya. "Yana da kyau a ce mun dan kebe guri guda, kinga hayaniyar mutane ta yi yawa a nan." Ma'aikacin ya ce da Surayya yana dan murmushin da yake tsammanin shi ne murmushin da ya fi kowanne daukar hankalin mace a gurinsa, ko da yake a can bangaren Surayya ita murmushin nasa ya zo mata ne a matsayin irin kamannin da zaka gani a fuskar wanda aka sokawa allura. "Yana da kyau ace mun kebe din" ta ce da shi tana rangwada a gabansa kamar dawisu. Tuni ta gane cewa ta saye zuciyarsa, farin ciki ya lullube ta saboda ganin ta karya zuciyarsa ta yin amfani da kyakkyawar surarta, ta san kuma a shirye yake da ya mika soyayyarsa a gareta, hakan kuma yana da matukar muhimmanci a gareta. Ma'aikacin ya nufi wata yar siririyar kofar daki dake fuskantar katon dakin karbar hoton daga bangaren kudu sannan ya zaro dan mukulli daga aljihunsa ya bude sannan ya shiga Surayya na biye da shi a baya. Surayya ta dubi dakin lokacin da ma'aikacin ya maida kofar ya rufe sannan ya dawo ya janyo daya daga cikin kujeru biyu dake dakin ya zauna ita ma Surayya ta janyo dayar ta zauna. Dan kankanin daki ne mai kamara akurki in ka dauke kujeru biyu da teburin dake dakin da kuma wasu tarin takardu dake kusurwar dakin yamma maso kudu, babu komai a cikin dakin sai fankar dake juyawa a saman dakin wanda tuni ta sa Surayya fargaba, kar ta fado musu aka, saboda atunanin Surayya fuka-fukan fankar na iya cin karo da bangon dakin yayin da take juyawa, saboda kankantar dakin. "Sai dai ki yi hakuri Hajiya kin ga dan dakin namu kamar roko shi muka yi." "Babu komai." Surayya ta ce da shi tana murmushi sannan ta ci gaba da cewa "Daman wasu yan hotuna ne nake son samunsu da gaggawa yau din nan bana son su kai gobe saboda tafiya zan yi da su idan an jima." Ta dubi agogonta sannan ta yatsine fuska, lokaci guda kuma ta sake haske ma'aikacin da tattausan murmushinta. "Taimakon kenan da nake son ka yi min ka ga (film) din ko dodon ma ba'a fito da shi ba, a fada min ko nawa ne zan biya." Ma'aikacin ya yi murmushi cikin mamaki sannan yace, "Ranki ya dade wannan ai ba wani abu, daman ai muna irin wannan aikin na gaggawa kudin kawai ake riɓanyawa, amma Hajiya tun da ke ce zan iya yi miki a madaidaicin farashin na da." "Na gode." surayya ta ce da shi. Sannan ta dube shi har yanzu tattausan murmushin bai bar fuskarta ba. "Ai har yanzu ba ka bari na karasa fada ma taimakon da nake son ka yi min ba." "Kamar me fa?" Ma'aikacin ya tambaya cikin mamaki. "Za ka iya kuwa?" Surayya ta tambaye shi, a daidai lokacin da ta bude jakarta ta dauko dodon hoton wanda ke nannaɗe a cikin wani dan karfe, sannan ta rufe jakar. "Fadi mana ranki ya dade." Ya ce da ita "Ai babu taimakon da ba zan iya yi miki ba ai darajarki agurina ta fi komai.." ya dan yi shiru, cikin dan jin kunyar abin da ya fada. Shi kansa bai san lokacin da kalmar ta kwace masa ba. Surayya ta dube shi sannan tace da shi, "Ni ma ai fahimtar haka ne ya sa nake neman taimakon agurinka, naji dadi kuma jin cewa ashe wai har ina da wata daraja ta daban a gurinka." Ta dan girgiza kanta sannan ta dan matsa gaba ta dora kyawawan hannayenta a kan teburin ta ce da shi, "Ba na son kowa ya ga hoton sai kai kadai, saboda hoton sirri ne a gareni kai ma kuma ganin irin mutuncin da na ga kana da shi ne ya sa zan amince da kai na baka, na san ba za ka so ka tona sirrina ba." Ta yi murmushi. "Haba Hajiya aikin fi karfin ko..komai a gaurina." yace muryarsa na rawa duk lokacin da ta furta dadadan kalamanta sai ya ji kaunarta ta kara shige masa zuciya irin kalaman kwantar da hankalin da take yi masa magana da su yanzu su suka sa jikinsa rawa numfashinsa kuma sama-sama. "Wannan ba damuwa." ya ce da ita lokacin da ya mike tsaye. Surayya ta mika masa dodon hoton, ya karba. "Dan jira ni ina zuwa." ya fita da sauri ya maida kofar ya rufe. Ba'a dade ba sai ga shi ya dawo dauke da kwalaban lemo guda uku a hannunsa da kuma kofin roba guda daya ya ajiye a kan teburin dake gaban Surayya. "Sai ki dan jira ni." Ya ce da ita, "Nan da yan mintina zan zo miki da hotunan." Sannan har zai fita sai yadawo, ya leka karkashin teburin ya janyo lokar teburin, daga cikinta ne ya zaro wani littafi na Kasar Turai wanda ke dauke da hotunan kyawawan guraren shakatawa da kuma tallace-tallacen finafinan daukar hoto da kyamarori ya ajje a kan teburin a gaban Surayya. "Ga abokin hira nan" Ya ce da ita. "Na gode, har da wannan wahala haka? Ni da ka bar ni ma haka ai babu damuwa. "Ah! Haba Hajiya ai kin wuce wannan." Ya ce da ita a daidai lokacin da ya nufi kofar dakin sannan ya sake juyowa suka hada ido da Surayya. Magidancin mutumin da kuma matashiyar yarinyar suka dubi junansu na dan lokaci. Sannan ya juya ya fice daga dakin zuciyarsa cike da tsabar kaunarta. Mintuna ashirin da daya daidai sai ga shi ya dawo cikin dakin da Surayya ke jiransa hannunsa rike da jakar hotunan. "Har an yi me?!" Surayya ta tambaya cikin mamaki. "Har an gama." Ya ce da ita yana murmushi. Surayya ta ajje littafin dake hannunta, sannan ta karbi jakar hotunan ta zazzage su. Kala uku ne hotunan ko wane kati bibbiyu. Hotunan sun yi kyau matuka, fiye da yadda Surayya take tsammani. Hoton farkon ya nuna Aganani tsaye a kan Rayyanu lokacin da katon nan ya yi tsalle ya fado akan kirjin Rayyanu. Hoto na biyu kuma ya nuna inda Aganani ne ya ɗaga Rayyanu sama ya dulmiya kansa cikin dirom ruwa. Sai kuma hoto na karshe, Aganani Mu-sha-gara ne rike da kwalar rigar Rayyanu lokacin da yake kokarin daga shi amma kuma rai ya yi halinsa. . Surayya ta yi ajiyar zuciya sannan ta maida hotunan cikin jakarsu, ta kuma bude tata jakar ta jefa jakar hoton ciki ta rufe. Ma'aikacin na tsaye a kanta fuskarsa sharkaf da gumi alamun tambaya karara suke kuma abayyane a fuskarsa. . ************* ************ ************ . Yansandan goma sha daya suka yi shiru suna saurarena. Aganani ya ci gaba da cewa, "Idan son samu ne yana da kyau a ce mun kama yarinyar nan cikin kwana biyu." Ya dan yi shiru yana dubansa sannan ya yi nazarin tafkeken falon da suke ciki. Kujeru sama da ashirin sun yi layi a cikin dakin shakatawar

Chapter 4 of 9