Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TA LEKO TA KOMA complet Na Nazir Adam Salih Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) nazir adam Salih La'sar sakaliya mai dauke da lillimin gajimare, tana daya daga cikin lokutan da haidar ya fi so a rayuwarsa. Sau da yawa bai yi niyyar fita yawo ba, idan ya ga irin wannan yanayin sai ya ji ba a bin da yake so kamar ya fita ya dan zaga. Wajen yawon sa bai wuce bakin kogin kwara. Kogin wani dan tattaki ne kadan daga unguwarsu. Hakika yana matukar son kyakkyawan yanayi irin wannan musamman ma a bakin kogin kwara. To a cikin daya daga irin wannan yammacin ne, bayan Haidar ya yi wanka ya shirya sannan ya dauko dan karamin littafinsa na Hausa wanda idan ya je bakin kogin shakatawa zai karanta, sai ya ji dirin mota a kofar gida "Yauwa, shi kenan ma." Ya ce cikin zuciyarsa, a zatonsa abokinsa ne Aliyu ya biyo zai dauke shi. Saboda sau da yawa tare suke fita a duk lokacin da damar hakan ta samu. Nan da nan ya fito tsakar gidan da sauri, a daidai lokacin da suka ci karo da mahaifiyarsa Aishat. "Ina za ka je?" Ta tambaye shi. "Baba ina son za mu fita bakin kogi shakatawa ne" ya ce da ita cikin ladabi. "Ga Aliyu canma a waje yana jirana" "Kada ku sake magariba ta yi muku a can, ka san babanka idan ya dawo da wuri bai gan ka ba zai iya tambayar inda ka shiga." "Ba zan dade ba" yace da ita, a daidai lokacin da ya nufi kofar gidan da sauri cikin kaguwa. Ya yi mutukar kaduwa lokacin da ya isa kofar ya tarar ba Aliyu ne ke jiran sa ba. Mai jiran nasa na tsaye a gaban motar tana kada dan mukullin motar. Tana sanye da duguwar riga baka, kanta lullube da farin gyale fuskarta boye a bayan bakin tabarau irin na mata, wanda ya yi matukar fito da kyakkyawan dogon hancinta mai kama da biro. Duguwa ce fara, mai dara-daran fararen idanu kamar kankara, tana da yawan gashin gira, da kuma dan madaidaicin bakinta mai dauke da kyawawan jerin hakora. A cikinsu akwai wata yar wushirya dake dauke hankalin maza kamar yadda mayen karfe ke jan karfe, surayya kenan, ko kuma kamar yadda suka ce ko kuma suka sake mata suna "Monika" daya daga cikin mata ajin farko, na masu zaman kansu. Zai yi wuya ka gane hakan idan ba an fada maka ba. Abin mamaki idan ka gane cewa a boye a bayan kyakkyawar surar surayya monika, akwai matsanancin halayyar son dukiya, da son rayuwa a duniya, monika tana cin kudi kamar yadda wuta ke cin auguda. Daya daga cikin abubuwan da monika ke kashe kudinta akai shi ne sutura da abin hawa, akwai jita-jitan dake cewa duk wata sai ta sauya mota, an ce kuma wai tana da suturori masu tsadar gaske sama da dari biyu, wan abu muhimmi kuma dake tattare da surayya monika shi ne, ko a cikin yan bariki, ba kowane ke iya harka da ita ba, sai masu dukiyar gaske, sau da yawa surayya tasha karya kananan yan barikin masu kudi. Duk da yake surayya ba ta fi shekara daya da rabi da fitowa yawan bariki ba, hakan bai hana masu hannu da shuni da dama sanin ta ba. Abu daya samar yan bariki suka tabbatarwa kansu, shi ne surayya monika tafi karfinsu, lallai kam tafi karfinsu, in ka dauke mutum daya wato Haidar, so! Wannan kalma ta so tana tattare da abin al'ajabi, haka kawai rana daya duk irin mummunan son abin duniya na monika, sai ga shi ta hakura, tana bin saurayin da bai kai ko yaronta ba wai tana son sa. Wannan ba karamin koma baya ba ne ga surayya, musamman ma idan aka yi la'akari da irin ajinta a gurin alhazan birni, sai ga shi lokaci guda ajin ya zube a gaban dan matashin saurayi Haidar, wanda shi a gurinsa surayya kamar karfen kafa ce, ba wai donba tada kyau ba, a'a, shi dai kawai ba ya kaunar ta ne. Cikin ziyarorin da ta kawo masa a kalla guda ashirin, kullum sai ya gargade ta da ta dauke kafarta daga gidansu, domin tuni mutanen unguwa sun fara maganganu, wanda daga karshe har maganar ta kai kunnen iyayensa. "Haba Haidar" Babarsa ta ce da shi. "Yanzu ace ka rasa wacce za ka aura sai karuwa, marar mutunci? Kada ka sake to abin ya yi nisa ka ji ko? Ko da da kanta ta zo ta same ka, kar ka sake ka kulata shashar banza, ta gaji ta daina zuwa" A cikin yawa-yawan zuwan da surayya ke yi wajen Haidar tuni har mahaifiyar Haidar ta fara fada mata bakaken maganganu. "Kada ki bata min da kin ji ko shi ba dan iska ba ne irinki" Ita kuma Surayya, sai ta sunkuyar da kai kasa sannan ta ce da ita cikin ladabi "Ki yi hakuri baba wallahi dan babu yadda zan yi na daina son sa ne don haka nake zuwa" Kamar kullum yauma sai ga shi ta zo ta ga abin begenta Haidar "Anya kuwa wannan alaka zata ci gaba tsakanin Haidar da Surayya yarinyar da yan bariki suke kira da monika? Abin duk ya fara ne kamar wasa, kuma shi ne ya yi sanadiyyar rikicin da ya shafi jama'a da dama dake unguwar Banasariyya, wacce ke dab da gabar kogin kwara. Gaidar ya dubi Surayya sannan ya ce cikin fushi "Me ya dawo da ke kuma marar zuciya? Ba na ce kar ki kara dawo min nan ba!" "Haba Haidar... Kai yanzu kana ganin ya dace ka yi min irin wannan karbar?" ta ce da shi cikin sassanyar murya mai dauke da tsananin takaici . Har yanzu dan mukullin motar na hannunta, sai dai ta daina kada shi, tana tsaye ne kawai tana kallon sa. . NAZIR ADAM SALIH (NAS) "HAIDAR." Ta yi kiran sunansa. Bai amsa ba, sai ta ce "Haidar so ne ya sa ni zubar da ajina a gabanka, kuma ya sani jure wulakancin da kake yi min kai da mahaifiyarka." . "Shin daman zuwa ki ka yi ki yi min rashin kunya, ko kuwa kin zo ne ki rama wulakancin da babar tawa ta ke yi miki." "ko kusa ba haka ba ne masoyina." Ta ce da shi, "Abin da ya kawo ni shi ne shaukin ganin ka da kuma so da bege da ke addabar zuciyata. Wallahi Haidar duk wulakancin da za ka yi min ban damu ba, in dai har zan saka a idona to burina ya cika." "To ya isa haka uwar dadin baki." Haidar ya ce da ita. "Ni zan tafi, amma ina son na gargade ki da cewa daga yau kar ki sake zuwa nan, wannan shi ne na karshe, in kuma ba so ki ke ranki ya baci ba to ki dauki shawarata. Ke yanzu Surayya ki na ganin ya dace ace dan mutunci kama ta ya aure ki? Kin san fa duk garin nan babu wanda bai san ke yar bariki ba ce, haba!" "Haidar na roke ka don girman Manzo ka daina yi min kallon mutuniyar banza, wallahi da ka san yadda nake masifar begen ka da ba ka fada min wadannan maganganu ba, na san matsayina a gurin mutanen garin nan, amma bai kamata a ce kai wanda nake kauna na ajje komai da komai saboda kai, amma ka ke kira na marar mutunci ba, haba Haidar, don Allah ka daina tunanin abin da ya wuce, ka san cewa kuwa tun lokacin da son ka ya mamaye zuciyata na ji duk na tsani kaina, kuma duk wata sha'awar bariki ta fita daga raina." Ta dan yi shiru sannan ta dan matso ta durkusa a gabansa ta dafa takalmansa, sannan ta ci gaba, "Haidar ka yi min rai ka ceci rayuwata, Haidar ka daina ƙi na, in ma ba za ka so ni ba to ka daina wulakanta ni, in dai ba so kake ciwon zuciya ya kashe ni ba. Na yi ma alkawarin in har za ka aure ni daga yau ba zan sake yawon bariki ba, daman ba nisa na yi ba, son zuciya ne ya kai ni, amma na tuba Haidar na daina, ba don komai ba sai don begen ka da kaunar ka. Wayyo masoyina Haidar ka so ni ka kuma aure ni, kai ma za ka sami lada a wurin Ubangiji," Sannan hawaye ya fara kwarara akan kyawawan kumatunta. Haidar ya dube ta sai ya ji ya dada tsanar ta ba don komai ba sai don shi a wurinsa kamar mayaudariya ce, wacce ke son ta yaudare shi ta kuma hada shi da iyayensa. . "Sai dai ki auri dan iska kamar ki amma ba ni ba, ki je can ki yaudari alhazan birninki masu katon ciki." Sannan ya zare takalminsa daga karkashin hannayenta da ke dafe, bai ko kara duban ta ba sai kawai ya nufi hanyar da za ta kai shi bakin kogi. Surayya ta tashi jiki a sanyaye cikin takaici hawaye na kwarara a idonta, a dai-dai lokacin ne taji kamar motsi a bayanta, ta juya ta fuskanci kofar gidan su Haidar, mahaifiyar Haidar na tsaye a kofar gidan sanye da shudiyar doguwar riga wadda ta dora da zanen atamfa a kanta, "Nan da nan Surayya ta durkusa har kasa da niyyar ta gaida ita "Karma ki durkusa munafuka" mahaifiyar Haidar ta ce, "ni zaki nunawa bariki bace min da gani mutuniyar banza, ni ɗana ba dan iska bane. . ****** ******* ******* . Ya aka yi, yaya kuma aka yi, ita kanta ba ta san yadda aka yi ta tuko kanta zuwa gida ba, tana isowa katon gidan maigadinta Ma'azu, ya bude mata kofa, sannan ya daga hannunsa, cikin girmamawa, bata kalle shi ba, abin ya bashi mamaki, domin ga al'adarta, duk lokacin da ya bude ma ta kofa, sai ta tsaya ta tambaye shi ko akwai wanda ya zo neman ta, in kuma sako ne ma aka ajiye ta karba, sabanin haka sai ga shi yau ba ta ko kalle shi ba. Ta yi fakin da motar a gurin na musamman da aka tanada don ajje motoci, sannan ta fito ta rufe kofar motar da karfi, hakan shi ya tsorata yan tsuntsayen da ke wasa akan fulawowin da ke farfajiyar gidan suka tashi sama far suna rera wakoki cikin yarensu. Surayya, monika ta nufi kyakkyawan farin ginin dake farfajiyar gidan irin ginin mutanen Sin ne (Chaina) yana da rufin ja da kuma farin fenti, wanda aka yi masa ado da fenti ruwan kofi, kofofin da kuma tagogin gidan na mulmulallen jan katako ne, mai sheki, shi ma yana dauke da launin kasa-kasa. Monika, ta nufi kofar dakin tana takawa a hankali, iskar dake kadawa na wasa da gashin kanta mai sheki, wanda ya bayyana a sarari a sakamakon zamewa da lillibin kanta ya yi, ba takuma damu ta maida shi ba. Ta bude dakin sannan ta shiga tangamemen dakin shakatawar mai dauke da hadaddun kujeru sama da ashirin da biyar, kujerun na shudin karen miski ne, hakan shi ya basu damar dacewa da farin fentin dake dakin sun yi wa sararin dakin kuri, sau da yawa idan mutane suka shiga dakin, kujerun kan tuna musu da majalisar dinkin duniya. Tana zuwa ta zarce dakin kwananta kai tsaye ta fada akan makeken gadon rubda ciki, ta fara kuka "Wayyo Allah na tuba." Ta ce cikin shasshekar kuka, "Allah ka cire min son Haidar na huta da azaba, Allah na tuba na daina aikin sabo daga yau, Allah kasa ya so ni ko kuma sonsa ya fita daga zuciyata, sannan ta yi ajiyar zuciya ta kifa kanta akan matashin kan dake kan gadon, sannan ta fara tunani, har saida zuciyarta ta zama tas babu komai sai barci daya maye gurbin wajen............. . Biyar da rabi saura minti daya ta farka daga nannauyan barcin da take yi, tana tashi ta nufi bandaki ta kwarara ruwan sanyi ajikinta, sannan ta sake kwalliya, yadin boyal ruwan hoda ta zaba daga cikin daruruwan kayan da ke cikin akwatinta, sannan ta dubi kanta a cikin tangamemen madubin dake fuskantarta, zane da rigar boyal din sun yi matukar dacewa da ita, komai ya yi in ka dauke idanunta da suka kukkumbura saboda kuka da ta sha, sannan ta fito ta rufe dakin ta nufi wajen motarta, tana tunani, "Allah ka taimake ni." Ta ce cikin zuciyarta. Bata hakura ba, duk da wulakancin da Haidar ya yi mata har yanzu tana da karfin gwiwar cewa mai yiyuwa idan ta yi sauri ta same shi a bakin kogin zai iya kallon ta da idon rahama. Tafiyar minti goma ta kawo ta bakin kogin, samari da yan mata suna ta sheke ayarsu, akwai kuma yan yawon bude ido turawa suna dauke-dauken hotunansu a gabar kogin, Haidar na zaune dab da wasu samari guda uku, su da yan matansu suna hira, rabin kafarsa a ruwa, rabin jikinsa kuma awaje, dukkansu suna zaune ne a bakin gabar kogin, suna wasa da ruwa, da kafafunsu. "Salamu alaikum." Haidar ya shaida muryarta lokaci guda kuma ya hada girar sama da ta kasa, sannan cikin kakkausar murya ya ce da ita "Uwar naci sai da ki ka dawo? Wato baki ji gargadina ba ko? Kai na hadu da jaraba! Ke ba ki da hankali ne, dole ne soyayya ko dole ne sai nayi soyayya da ke? Kin jarabce ni kamar bala'i, don Allah kin ga malama ki daina tsaya min akai gara ki san inda dare ya yi miki tun wuri, tun kafin ma ki sa mutane su fara tunanin ko ni ma lalatacce ne kamar ki." ya dan yi shiru yana maida numfashinsa, sannan yace "Ko ba ki ji ba Monika nacacciya, kin zame min karfen kafa, don Allah ki ba ni sarari na sha iska, ni wallahi abin da nake tsoro ma shi ne kar mutane su ganni da ke suna yi min kallon dan iska kamar ki." . "Ka iya kira na komai ma." SURAYYA monika ta katse shi, "Dama ka samu, don ganin ina son ka shi ya sa kake walakanta ni yadda ka ga dama, amma ka tuna fa, in za ka so mutum ka so shi kaɗan ba can ba, idan ma za ka ki mutum ka kishi kaɗan." Ta dan saurara. "Haidar!" ta sake kiran sunansa, tuni kwalla ta cika idonta, "Na roke ka Haidar don girman mahaifanka ka duba irin son da nake maka, ka daina kirana yar iska." Jin haka shi ya sa Haidar mikewa tsaye, "Ina son ki bace min da gani, ya ce muryarsa na rawa, "Ni na ce bana sonki amma kin nace min har kin sa iyayena sun fara tsana ta, ke yanzu Monika kina ganin ya dace na aure ki a matsayinki na karuwa?" Surayya ta fara kuka, ta durkusa gwiwa biyu a gabansa, bayanta na fuskantar ruwan kogin sannan ta fara rokonsa, "Haba Haidar kai ma abinda za ka ce da ni kenan, ka rasa abin da zaka Kira ni sai karuwa?" . "To na yi miki karya ne?" Ya ce a fusace "Bace min da gani, marar kunyar karya." Sannan ya kama gyalanta ya yi sama da ita ya sharara mata mari, ba tayi ko gezau ba. "Ni ka mara Haidar?" Ta ce da shi, "Sai ka gane kuskuranka, ka kuma rike wannan a zuciyarka bana manta wulakanci da wuri." Haidar ya fashe da dariya marar ma'ana "Haba yarinya sai dai ki ganni ki kyale na fi karfin ki." Sannan ba kunya ba tsoro sai ya hankadata cikin ruwan ta fada da baya, mutanan dake wajen suka fashe da dariya. . ******* ****** ******* . Haji RAYYANU, dogo, siriri wankan tarwaɗa, na kwance akan tattausan gadonsa na alfarma, daga shi sai gajeran wando fari, yana sanye da wata yar fingilgilar riga iya cibiya, baka ce a kirjinta an rubuta cikin harshen turanci (The ocean) "teku" Yana da doguwar fuska irin wacce wasu daga cikin mata ke sha'awa, zungureren karan sigarin (St moritz) a bakinsa. Lokaci-Lokaci, ya kan busa hayaki izuwa saman dakin, hakan shi ya baiwa dan karamin hadarin hayaki haduwa a sararisararin samaniyar dakin. Akan kuma ruwan Cikinsa, mujallar wasanni ce, ta kasar amurka, ya yi kimanin mintuna goma sha biyar kenan yana nazarin mujallar. Jiniyar agogan dake makale a bangon dakin ta dauki kara, karfe tara na safe agogan ya nuna, cikin nutsuwa Rayyanu ya ajiye mujallar akan gadon sannan ya nufi bandaki. Bayan yan mintuna kadan ya gama wanka, sannan ya nufi wata katuwar akwati baka ya bude ta ya zaro bakin wando da farar shet irin ta mutanen (texas) ta kasar amurka ya sanya, ya daura agogansa (mandita) yana sheki kamar madubi. A daidai lokacin ne idonsa ya kai ga bangon dakin, ya yi ido hudu da tangameman hotan Surayya Monika wanda ya dauke ta a gabar kogin NIL na Kasar masar shekaru biyu kenan tun lokacin da suka je yawan bude ido. Ganin hotan shi ya dawo masa da hotan farkon haduwarsu da Surayya, yau shekara biyu da rabi kenan da suka wuce, sun fara haduwa ne a jami'ar G.S.U ta GOMBE a lokacin Surayya take nazarinta a fannin lissafi, shi kuma Rayyanu yakan je lokaci-lokaci su gaisa da abokai, don shi rabonsa da karatu tun yana firamare. Da yamma ne ranar lahadi suka fara haduwa. HAƊUWAR KADDARA. Lokacin da Surayya zata tafi dakin karatu (library) littattafanta a hannu . Kamar wasa, kallo daya surayya ta yi masa ta tabbatar akwai kudi a gurinsa, idan kuwa akwai abin da ya fi komai a rayuwar Surayya to kudi ne, duk da yake iyayanta ba wasu abin ku-zo-ku-gani ba ne, hasali ma babanta ya rasu tun tana shekara biyar a duniya, makarantar ma da take a lokacin mahaifiyarta ce take daukar nauyinta, tare da taimakon samarinta. Hakika tana samun agaji ga samari da dama dake kokarin mallakar ta saboda Allah ya yi mata kirar sace zuciyar mazaje, sai dai kawai a yi rayuwa in dai za ta samu biyan bukatunta na yau da kullum to ita shi kenan. To haka dai kamar wasa sai ta dafewa Haj Rayyanu saurayin da babu wanda ya san takamaiman ta inda ya samo arzikinsa, amma a gaskiyar lamari yana daya daga cikin kwararrun yan fasa kwaurin miyagun kwayoyi da makamantansu, abin kuma ya aure shi, domin babu wanda ya taba ko da zarginsa ballantana ma asirinsa ya tonu. Basu fi wata uku da haduwa ba sai Rayyanu ya canza ma ta rayuwa, zuwa inda take mafarkin shiga. Motocin hawa uku ya sai ma ta na hawa. Jita-jita kuma na cewa a lokacin tana da kayan sawa masu tsadar gaske fiye da kala dari biyar "Ya kamata ki samu canjin rayuwa." Rayyanu ya ce da ita wata rana suna hira a cikin dakinsa, "Ina ganin in har da gaske ne ki na son rayuwa to akwai wajen da nake ganin ya dace da ke, wajen hutu ne amma ba zaki samu damar zuwa ba sai kin yi min alkawarin za ki bar wannan karatun naki marar amfani, sannan zamu tafi, bana kuma so ki sanar da iyayenki domin kin san iyaye wasu lokutan sukan rage mana jin dadin rayuwa." Bayan dan shiru ya dube ta, ya tabbatar shi take sauraro, sai ya ci gaba da cewa "Ina son za mu tafi kasashen waje yawon bude ido daga nan kuma sai mu yi zaman mu a aljannar hutu ta Najeriya duk abin da kike so zan ba ki shi. A karo na farko Surayya ta tambaye shi "Ina ne kuma aljannar hutu ta Najeriya?" Kamar shedan sai kawai ya ci gaba da yi mata huduba "Banasariyya mana, wata sabuwar unguwace ta wanda suka isa, tana yankin gabar tekun kwara ne, akwai rayuwa yarinya!" Ya ce da ita, "Ke dai kawai amincewarki na ke nema." Shi kenan kamar wasa sai ta amince. Duk wannan sai da Rayyanu ya tuna da su lokacin da yake kallon hoton sannan ya yi ajiyar zuciya da ya tuna da cewa a da ya so Surayya kamar ya hadiye ta, amma yanzu ya gaji da ita. Uhm! Lallai yana bukatar canji, ko da yake dai ya san da wahala ya samu kamarta. "Kai shashasha" Wata zuciyar ta ce da shi "Don kawai ka je Colombia ka gano jajayen mata sai ka yarda taka, aiko ban za dami ka tsinta akala. Mai zai hana ku ci gaba da rayuwarku, tunda har yanzu ma ai Surayya yarinya ce wacce samun kamarta sai an tona" Tunanin hakan shi ya sa Haji Rayyanu ya nufi talfon da niyyar ya ji halin da Surayya ke ciki. Yau kwanansa daya kenan da dawowa daga kasar Colombia, sakamakon wata hodar iblis da yake kokarin fitowa da ita daga can. A hankali cikin nutsuwa sai ya buga talfon din, a can daya bangaren talfon din ya dau kara, Surayya Monika wacce ke kwance akan gado rub da ciki tana ta faman kuka, hawayen ta ya kare karaf. Abin da ya faru a jiya ya zame mata kamar wani mummunan mafarki ne, amma ina ba mafarki bane a zahiri ne. Karar talfon din shi ya yi sanadiyyar da ta tabbatar da hakan lokacin da data tashi daga kan gadon da niyyar ta dau talfon din, sai ta lura ashe kayan da Haidar ya turata ruwa da suba tako cire su ba ta kwanta, har yanzu akwai alamar laima a cikinsu. Ta yi ajiyar zuciya data tuna da abin da ya faru, sannan ta dauki kan tarfon din a fusace, dalili kuwa shi ne ita ahalin yanzu ta tsani duk wani da na miji ma, kuma ko ba komai ma ai ya kamata a bar ta ta huta. "Wane?" Ta ce cikin talfon din "Ni ne. Yarinya kin tashi ko kuwa nazo na tashe ki?" Aka ce da ita a can daya bangaren, "Ban tashi ba" ta ce da shi cikin fushi "Kuma bana bukatar a dame ni" Haji Rayyanu ya cika da mamaki sannan kuma ya ji zuciyarsa tana tafarfasa, "Ke don ubanki ni ki ke fadawa wadannan bakaken maganganun? Shin kin gane ma kuwa ko wane ne ke yi miki wayar?" Ya tambaye ta a fusace. "Na gane mana" Ta ce da shi ita ma cikin fushi, "Kaine Rayyanu ko wata tsiya ce kuma daban, wani abu ne kai sakarai!" Ita kanta ba ta san abinda take fada ba, abu daya ta sani shi ne ita ta san dai yanzu tana cikin matsanancin bacin rai, ba ta kuma damu da abinda zai biyo baya ba" Ita yanzu tana tsammanin bayan wulakancin da Haidar ya yi mata babu wani abu kuma da zai zo ya shafe wannan sai dai kuma can cikin zuciyarta ta san ta yi kuskure bai kamata fushin wani ya shafi wani ba. Sauyin karar da taji a kunnenta shi ya tabbatar mata da cewa Haji

Chapter 1 of 9