Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
Rayyannu ya ajje wayar talfon din. Ta fada kan gado ta fara kuka, "Allah ka karbi raina na huta da wannan kunan rai" Abin da ba ta sani ba shi ne guntun daddagin begen Haidar shi ne har yanzu ke addabar zuciyarta. . ******* ****** ****** . "Sai na nuna wa wannan yarinyar matsayina." Rayyanu yace cikin zuciyarsa, a dai-dai lokacin da ya yi kwafa, sannan ya fara danna lombobin talfon a hankali, bayan yan dakiku, aka dauka Bayan yan dakiku, aka dauki wayar acan daya bangaren "Wa kenan?" Aka tambaya a can daya bangaren, "Haji Rayyanu ne" "Oho daman kai ne, yallabai yaushe ka dawo daga (Colombia) din ne?" "Saurara da kyau" Rayyanu ya katse masa tambayoyinsa na kwakwa "Jiya na dawo." Ya ba shi amsar tambayarsa ta farko, sannan ya ce "Ina son ganin ka kai da abokin nan naka wanda kuka yi min aiki kwanakin baya." "Lafiya Oga ka ke son ganinmu?" Aka tambaya a can daya bangaran. "Lafiya kalau." Rayyanu ya ce "Ina son zan nuna wa wata marar kunya matsayinta ne." "Wacece wannan yallabai?" aka tambaya, "yarinyar nan mana dana ke ciyarwa nake shayarwa, na saiwa gida da motocin hawa, na kuma daga rayuwarta daga ajin karshe zuwa ajin farko na rayuwa, amma don rashin godiya, wai ni za ta ci wa mutunci, ka san daman.." "Yallabai mu iso yanzu ne?" Aka katse shi cikin doki. "A'a" Rayyanu ya ce, "Ba na son gaggawa, so nake na bar ta ta sakankance kamar na manta da ita, sai kuma mu dirar mata misalin (2:00) na dare." "An gama" Aka ce cikin ɗoki, daga can daya bangaren. Haji Rayyanu na iya jin sowar wanda yake yi wa talfon din, ya yi sauri ya ajje kan talfon din, don gudun kar dodon kunnensa ya yi dameji, muryar mai dariya acan daya bangaren ita ta tuna masa da kukan dodo . ******* ******* ******** . Mahaukacin dukan kofar da ake yi shi ya farkar da Surayya Monika daga cikin nannauyan barcin da take yi. Da farko ta dauka mai gadinta ne Mu'azu,amma da ta tuna da cewa ko wani abu muhimmi ne ya faru, mu'azu ba ya buga mata kofa haka, sai dai ya danna kararrawa, sanin haka shi ya sa Surayya ta tashi a firgice. Cikin rudanin rashin sanin abin dake faruwa. "Monika!" Taji wata kakkausar murya ta yi kiran sunanta, sunan da aka fi sanin ta da shi a bariki. Ba ta amsa kiran ba, ko da yake kafin ma ta amsa tuni an yi mata zagi ya kai cikin kwando. "Ki bude tun da ba gidan abanki ba ne" Aka ce da ita. "Na ji Rayyanu ba gidan ubana ba ne. Ga ni nan kuma zan bude tun da babu gadona a gidan" Surayya ta amsa, a daidai lokacin ne ta matsa daga bangaren arewa na falon in da tagar dakin take, sannan a hankali ta janyo tagar ta leka, abin da ta gani ya sa ta daukewar numfashi, ya kuma kafar da yawun bakinta. A tsaye a bakin kofar dakin Rayyanu ne tare da wasu samari majiya karfi guda biyu, basu da kyan gani, dayan yana sanye da doguwar riga fara jallabiya har kasa, kafarsa sanye cikin takalmin roba, kansa babu hula, sai nannadadden gashin da a ƙalla ya kai wata biyar bai ga ruwa ba, hannunsa a cikin aljihun jallabiyarsa, daya kuma hannun rike da bulalar kebir. Saurayi na biyun shi ya fi ba ta tsoro, fuskarsa irin wacce ka saba gani ce a duk lokacin daka leka zagayen birirrika a gidan ajje naman daji (Zoo) fuskar mai dauke da sharbeben bulle, da gashin baki irin na kafiran da can, su suka sa hantar cikin Surayya kadawa a take a nan taji gumi ya rufe ta, ta san cewa yau za ta ga rashin mutunci. . An ya kuwa Rayyanu ne da kansa zai sa ayi mata Haka ba taji tsoron bude kofar ba saboda tsabar tsoro da karaya da ta yi kofar ta bude a hankali da farko, sannan daga karshe ta taho da karfi ta hadu da bangon dakin hakan shi ya sa wani bangaren simunti daga jikin shafen dakin fadowa akan sawun Surayya. Surayya ta dubi Rayyanu, sannan shi ma ya dube ta, tana sanye da duguwar riga ta barci, marar wadataccen hannu. Kanta babu dankwali. "marar mutunci nazo na ga iyakar rashin kunyarki" "Ni ba marar kunya ba ce." Ta ce da shi. Abin kamar hadin baki shimma Rayyanu yana daga hannu sai ya talle ta da mari tas!! "Ni ka mara Rayyanu?" ta ce da shi cikin shesshekar kuka, "Sai ka gane kuskuren ka." "Kuskurena?" Rayyanu ya ce yana dariya sannan ya harari daya saurayin mai jallabiya. Bai jira komai ba sai ya daga bulalar dake hannunsa ya fara shararawa Surayya. Ta kwalla kara mai tsanani a daidai lokacin da ruwan bulalar ya yi ta zuba a gadon bayanta har sai da ta kasa kuka abin kawai dake fitowa daga bakinta shi ne "Wayyo Allah Haidar ka zo ka kwace ni dan kai fa ake yi min wannan wulakancin! Wayyo Haidar ka zo ka kwace ni kar ka bari na yi fushi da kai.." Tun tana fadar haka har ta kasa. Bayan da Haji Rayyanu ya ga ta kasa kuka sai ya tsaida saurayin sannan ya kama hannun Surayya da niyyar ya tashe ta, sai ta fadi kasa. "Ku dauko min ita" Ya ce da samarin. Mummunan ya kama kafafunta, shi kuma mamuguncin ya kama hannunta suka yi mata cali- cali suka nufi waje da ita. Haji Rayyanu ya bude but din motarsa ya ce su jefa ta ciki suka jefa ta ciki, sannan suka rufe. Mintuna biyu da yin haka sai can mummunan nan ya nisa ya ce da Rayyanu "Ina jin fa yarinyar nan ta mutu" "Ni ma abin da na ke zato ke nan" Rayyanu ya ce. "Amma abin da za mu yi shi ne mu kai ta can cikin ciyayin nan na bakin kogi mu yarda ita da safe a tsince ta, ni kuma daga nan zan sallame ku zan koma kwalambiya a yau din nan. Daman babu wanda ya san na dawo, ko da yansanda ko wasu sun tsince ta babu wanda zai dora alhakin kisan kanta a kaina tunda bana nan, kuma ku ma ku yi shiru da bakinku." . "An gama Oga." Suka amsa baki daya. Bayan yan mintuna suka isa bakin kogi karfe daya da rabi na dare babu kowa a bakin kogin, suna zuwa suka bude bayan mota suka sake yi mata cali-cali sannan suka zabi inda ya fi ko'ina surkukiyar ciyayi suka jefa ta, ta faɗa amma ba ta motsa ba, Rayyanu ya dube ta, sannan ya taka idon sawunta da kafa bata motsaba. Sannan suka shiga mota suka ware. Ba su fi mintuna biyar da barin wajen ba aka tsinke da ruwan sama kamar da bakin kwarya. . ******* ****** ******** . Sautin kukan da Surayya ta kwalla ya daki dodon kunnen mu'azu maigadi, wanda ke kwance akan dogon bencin dake kofar gidan. Jikinsa na ta makyarkyatar zazzabi, tun safe yake fama da zazzabin, tuni jikinsa ya dauki zafi kamar kwanon tuya. Kukan da ya ji Surayya ta kwalla shi ya sa shi ya manta da zazzabin dake addabarsa, a lokaci guda kuma ya tashi zaune zumbur, jikinsa na rawa kamar mazari, sannan ne kuma ya sake jin Karar mari, Surayya ta yi wani irin kuka mai ban tausayi, kukan kamar sukar kibiya ce a kunnen Mu'azu, "Yarinyar da ta dade tana yi min mutunci, yarinyar arziki wadda ta tsamo ni daga cikin matsananciyar wahalar rashin aiki, ta kuma ke ninka min abinda ya kamata ta biya ni da shi, dole ne na ceci rayuwarta daga hannun marar mutuncin nan." Mu'azu maigadi ya sake cewa cikin zuciyarsa, sannan ya ciji yatsa cikin takaici da ya san cewa Rayyanu dukan ta zai yi to da bai bar shi ya shiga gidan ba duk da cewa kuwa yana fama da zazzabi, domin yaji lokacin da su Rayyanu suka zo amma ya kasa tashi ya bude musu kofa saboda juwa da ciwon kai dake daukarsa, ya ji kuma irin cin mutuncin da zagin da Rayyanu ya yi masa, duk da haka bai tashi ba, amma kukan Surayya ya isa ya tashe shi ko da kuwa a kabari ne. Ya ce cikin zuciyarsa duk da yake kuwa bai yarda da hakan ba. Mu'azu mai gadi ya zare takobinsa tsirara sannan ya nufi kofar dakin da sanda, ta hanyar boye jikinsa a cikin duhuwar fulawowin dake farfajiyar gidan, tun kafin yayi rabin kofar dakin sai ya ji kamar an dabaibaye masa kafa, ya tsaya cak kirjinsa na dukan uku-uku, tsoro ya kama shi hakika ba wani abu ne ya hana shi tafiya ba, sai mummunan tunanin daya fado zuciyarsa kamar daga sama "Rayyanu na iya halaka ka fa!" Zuciyarsa ta ce dashi. Zuciyarsa na da hujjar fadin hakan, domin kuwa a watan da ya wuce ne Mu'azu maigadi ya ga wani abu da ya ba shi tsoro da mamaki, duk da yake kuwa bai fadawa kowa ba, har ita kanta uwar dakinsa Surayya bai bar ta ta sani ba. . Ranar Asabar da safe ne abin ya faru, ba zai manta da ranar ba, kamar kullum, sai ga Rayyanu cikin mota, yana zuwa sai Mu'azu ya bude masa kofa, bayan ya wuce ciki ya yi fakin da motar a kusa da inda rumfar Mu'azu take, sai ya bude kofar kujerar baya ta motar ya dauko wata bakar jaka daga ciki, ya nufi but din motar, abin tsautsayi sai jakar ta kwace daga hannun Rayyanu, ta fado kasa, kallon farko da Mu'azu ya yi wa kayan da suke zube a kar bai shaida komai ba sai wata yar karamar bindiga mai barazana ga wanda ke kallon ta, kallo na biyu kuma da Mu'azu ya yi sai idonsa ya hango masa wasu yan kananan ledodi kunshe da wani gari-gari fari tas a ciki, ya yi kokarin ya fahimci ko mene a cikin ledodin amma bai ci nasara ba, sai dai kuma a can cikin zuciyarsa ya fara tunanin anya kuwa wannan ba ita ce abin da ya sha jin labari a bakin mutane ba, "HODAR IBLIS!" Rayyanu ya tsince kayan ya maida su cikin akwati sannan ya jefa ta a bayan motar ya kulle, ya juya suka yi ido hudu da mu'azu maigadi, A kullum Mu'azu ya tuna da irin kallon da Rayyanu ya yi masa, sai ya ji hantar cikinsa ta kada, kallo ne mai dauke da tsabagen gargadi da barazana. Mu'azu ya yi ajiyar zuciya saboda mummunan tunanin da zuciyarsa ta tuno masa, jikinsa ya yi matukar mutuwa, tuni har ya fara tunanin da wahala kuma ya sake gaba da gaba da Rayyanu, bai karasa tunanin ba saiya ji tim! Kamar an daki buhu, sannan ya ji sharaf, alamar faduwa, gumi ya keto masa, kamar ana zuba masa ruwa, a daidai lokacin ne ya ji su Rayyanu sun nufo wajen da yake boye, nan da nan ya tashi a guje ya koma kan bancin da yake ya sake kwantawa, idonsa rabi a rufe rabi a bude, "Wasu masu kama da birirrika sunyi wa uwar gidansa Surayya cali-cali, suna zuwa suka jefa ta a bayan mota, sannan suka shife cikin motar suka tashe ta. Rayyanu ya fito daga cikin filawoyin shi ma ya shiga motar, suka yi ribas suka fice daga gidan da gudu. Mu'azu mai gadi ya tashi aguje ya nufi kofar gidan a daidai lokacin ne ya hangi danjar motar su Rayyanu, ta nufi bakin kogi, mintuna biyu da faruwar hakan sai ga Mu'azu akan kekensa takobinsa a kafadarsa ya nufi bakin kogin kekensa na waka kurki-kurki. . ******* ***** ****** . Sai an yi kamar za a dauke ruwan, sai a sake kecewa kamar da bakin kwarya, hatta kifayen dake cikin kogin kwara a wannan lokacin sunsan ana tafka ruwan sama duk da yake kuwa su daman a cikin ruwan suke, to ballantana kuma Surayya wacce ke kwance a tsakiyar sarkakiyar ciyayin bakin kogin. Samarin da ke tuka motar suka kalli junansu sannan suka yi dariya. A daidai lokacin ne babban ladanin masallacin Banasariyya ya kwalla kiran sallar farko. . ********** ********* ********* . Rugugin jirgin saman shi ya dawo da masu tarar yan uwa da abokan arziki hankalinsu, sai bayan da rugugin jirgin saman ya lafa ne, sannan suka fahimci cewa ashe jirgin sama ya sauka. Zungureran jirgi ne fari, mai dauke da zanen shudi-shudi a jikinsa, a jelarsa an rubuta "KLM" jirgin Turai ne daya kuma daga cikin fasinjojin da jirgin ya kawo Rayyanu ne, sanye da riga da wando, kwat bakake idonsa a boye a cikin bakin tabarau, a saman tabaran daga sama an rubuta kamar haka (Colombo) hannunsa na hagun sanye cikin aljihun kwat dinsa, hannunsa na dama kuma rike da hannun jakar da ya ratayo a bayansa baka, mai dishi- dishin fari, babu alamar farin ciki ko bakin ciki a fuskarsa, abin kawai da za a iya kwatanta fuskarsa da shi a wannan lokaci shi ne bangon siniman. Ya biyo jerin gwanon mutanen suka nufi kasa ta hanyar matattakar jirgin saman. Bayan sun karaso kasa sai ya wuce kai tsaye ya nufi inda ake tarar baki, yana fitowa farfajiyar filin jigin saman sai ya fara waige-waige, lokaci guda kuma ya duba agogonsa, karfe uku da rabi na rana ya iso gida Najeriya, rabonsa da Najeriya yau wata guda kenan da kwana uku. Wata zungureriyar mota ta ja ta tsaya a gabansa, Rolloyis dinsa ce. Samarin biyu masu kama da birirrika suka fito kowannensu sanye da doguwar jallabiya, kamar da gaske idan ka kalle su daga kafarsu zuwa kirjinsu sai ka dauka mutanen kirki ne, amma lokacin da ku ka yi ido hudu sai ka tabbatar da kuskurenka ka kuma gwammace yin ido hudu da damisa akansu. Suka bude masa kofa, shi kuma Rayyanu ya shiga bayan motar ya kame, sannan su ma suka shiga "Ina muka nufa yallabai?" Dayan ya tambaya. "SARIYANA OTAL" ya ce dasu "An gama kuma za'ayi." Suka amsa gaba daya. . ******* ******* ******* . "Ah!! Lallai Surayya kafa ta yi sauki, har da sauri haka." Surayya ta yi murmushi sannan ta kalli GRACE, doguwar mata ce siririya hancinta kamar biro saboda tsawo, tana da idanu dara-dara launin sararin samaniya, baturiya ce yar kasar Ingila, yawon bude ido ne ya kawo ta Najeriya ita da mijinta JACKSON. "Sannu Surayya" Jackson ya ce da ita daga baya. Ta juya ta kalle shi sannan ta yi murmushi, "Nagode Jackson" Ta ce da shi, sannan ta sake kura masa ido, tana al'ajabin irin taimakon da ya yi mata, yau kimanin watanta daya kenan da kwana uku a gidan lambun Jackson, katon gida ne, wanda ke dauke da tafka-tafkan kyawawan dakunan kwana guda uku, gidan an gina shi ne acan tsallaken gaɓar kogin kwara, misalin kilomita ashirin da uku kenan daga unguwar Banasariyya. Babu ko gida daya a gurin in ka dauke gidan Jackson, wanda shima ya gina shi ne a nan domin ya kadaice kansa daga hayaniyar jama'a. Jackson ya gina wannan gida ne tun kusan shekaru shida kenan da suka shude, ba don komai ba kuwa sai don ya sami damar nazarinsa cikin nutsuwa, ba tare da hayaniyar jama'a ta dame shi ba Malam Jackson, Edita ne na wata mujallar ingila, duk kuma wata uku sai ya zo Najeriya, domin yin nazarce-nazarcensa, a ka'ida kuma baya wuce sati daya a duk zuwan da zai yi, Malam Jackson dogo ne shi ma kamar matarsa, sai dai kuma ya fi matarsa tsawo da kadan, yana da tarin suma, wacce ta zubo masa har kafada, hancinsa ya lankwaso kamar kugiya, yana da siraran lebban baki, jajaye kamar yankan reza. Awannan safiyar malam Jackson yana sanye ne da bakar riga mai gajeren hannu, a kirjinta an rubuta "Sun Flowers." Yana sanye da farin wando da hula hana Sallah fara, agogo "Sorinta" a hannunsa. A irin wannan shigar ne kuma Jackson ya tsinci Surayya kwance male-male a kan gadonsa a kuma cikin dakinsa, wanda idan ya je kamun kifi yake hutawa aciki. Koda Surayya ta kalle shi sai hoton ranar da suka hadu da Malam Jackson da kuma irin taimakon da ya yi mata suka fara bayyana garai-garai a zuciyarta, har yanzu kuma hankalinta a tashe yake saboda rashin sanin halin da Mu'azu mai gadi ke ciki, ta yi mamakin rashin ganin dawowarsa. "Lallai wani abu ya faru" ta ce cikin zuciyarta, hakika lokaci ya yi da ya kamata ta fara ramuwar gayya kwanaki talatin da ukun da suka shude ta yi su ne cikin tunanin yadda za ta rama abin da su Haidar da Rayyanu suka yi mata, amma da farko dai shi ne ta bar wannan gidan lambun, tun da ta sami sauki, wani abu kuma da ta fahimta shi ne Rayyanu ya dauka ta mutu, idan kuwa haka ne to ba zata taba bari ya gan ta ba, har sai lokacin da ta samu cikar burinta "Sai na rama wulakancin da Haidar ya yi min" ta ce cikin zuciyarta. "Rayyanu kuma ya shiga masifa tunda ya yi kokarin kashe ni. Zan kuma nuna musu ni yar halak ce." Kiran sunanta da Jackson ya yi shi ya dawo da Surayya hankalinta, sannan ta fahimci ashe tunani ta ke. "Tunanin me ki ke yi Surayya?" Jackson ya tambaye ta. "Ba komai" ta ce, tana murmushin yake amma zuciyarta a cike take da tsanar HAIDAR DA RAYYANU . "Surayya" Jackson ya ci gaba da cewa cikin harshen turanci "Ki yi hakuri, ki rabu da su, kin ga yanzu ke kadai babu yadda za ki yi da su, musamman shi Rayyanu din. Abin da nake ganin ya fi shi ne, idan kin tashi tafiya sai ki koma gida kai tsaye, ki je ku shirya da iyayenki. . ****** ******* ******** . Misalin karfe tara na safe ne Surayya ta fito dauke da bakar jaka rataye a kafadarta, tufafin sawa ne irin na turawa Grace ta ba ta, da kuma yan kunne da abin hannu na mata masu tsada, tana tafe Jackson a gefenta na hagu, Grace kuma a gefenta na dama, rike da hannunta, tana ta faman kuka hakika ta shaku da Surayya, matukar shakuwa, bakin kogin suka nufa, suna zuwa sai Surayya ta yi ido hudu da wani dan karamin jirgin ruwa irin na turawa. "Sai ki tafi a cikinsa." Jackson ya ce da ita, "Idan kin je tashar jiragen ruwa na Banasariyya, sai ki tambayi Ahmad, idan an nuna miki shi sai ki bashi mukullin jirgin ki ce masa ni na turo ki da shi kice masa sai bayan wata uku zan dawo." Bai jira tace komai ba, sai ya zaro damin kudin ingila daga aljihunsa ya mika mata "Ki canza wannan zuwa kudin nan Najeriya za su ba ki a kalla naira dubu dari shida da hamsin. Allah ya taimake ki ya ce da ita." Sannan ya ja da ba ya domin ya basu damar ganawar karshe ita da matarsa Grace. . "To Surayya." Grace ta ce cikin harshen turanci "Sai wata rana." Sannan ita ma ta buda jakarta ta zaro wani abu, ga mamakin Surayya sai taga wata yar karamar bindiga ce irin wacce matan turawa ke rikewa, "Za ta yi miki amfani" Grace ta ce da ita duk da yake Surayya ba ta ko taba rike bindiga ba balle tayi amfani da ita hakan bai hana ta karba ba, Jackson ya buda baki zai yi magana sai ya yi shiru bai ce komai ba Sannan ita ma Grace sai ta ja da baya ta koma kusa da mijinta ta tsaya tana kallon Surayya idonta cike da kwalla. Surayya ta shiga jirgin sannan ta danna gurin da ake tashin jirgin kamar yadda Jackson ya koya mata, sannan ta juyo ta miko hannayenta a lokaci guda, "Na gode muku" ta ce da su, "Ba zan taba mantawa da ku ba." Sannan ta harba cikin ruwan da gudu, ba ta ko kara waigowa ba, har sai da ta ƙule. Grace na tsaye a bakin kogin tana kuka Jackson ya dafa kafadarta sannan suka juya suka nufi gida, da niyyar su ma su bar Kasar. Misalin karfe goma da rabi su ma jirginsu ya daga sai Ingila, Grace ta leko ta tagar jirgin sannan ta ce "Surayya sai wata rana." Kamar tana gurin. . *********** ********** ********* . In ka dauke bambacin sa'o'i da ake samu duk abin da ya faru ne kusan lokaci guda, sa'o'i biyar da wani abu, bayan tashin su Grace zuwa Ingila Rayyanu ya sauka a gida Najeriya. Sannan sa'o'in Surayya hudu da yan mintuna da zuwa SARIYANA OTAL sai ga zungureriyar motar su Rayyanu shi da yan ta'addansa sun isa. Suna zuwa suka yi fakin da motar sannan suka nufi wajen saukar baki, ba'a dade ba, aka ba su daki mai lamba (10) hawa na biyu. Surayya na zaune akan kujera tana leken tagar dakinta, mai lamba (7) hawa na goma, sai taga zungureriyar motar ta malalo cikin harabar otal din kamar ba za ta kare ba saboda tsayi. Abin ya yi matukar ba ta mamaki, ya kuma kada hantar cikinta, "Rayyanu!!!" ta ce cikin ajiyar zuciya. Sannan ta yi shiru tana tunani "Ya kamata na fara wani abu..." ta ce, "...tunda ga Allah ya kawo min shi har nan." Lokaci guda kuma sai dabara ta Faɗo mata. Ta tashi daga kujerar, sannan ta matsa kusa da ɗan karamin teburin dake tsakar dakin, mai shan kuri, tana zuwa ta ɗau kan talfon din sannan ta buga lambobin da take so. "Sariyana otel." Akace da ita a can daya bangaren "Ina son ganin ka da gaggawa don Allah." ta ce da shi, ...ni ce bakuwar da ta zo sa'o'i hudu da suka wuce, daki mai lamba (7) hawa na goma." "Ga ni nan zuwa ranki ya dade." Tuni Surayya daman ta san zai zo, musamman ma da ta tuna da irin kallon nuna sha'awar da ya yi mata lokacin da ta zo otel din, daɗin daɗawar kuma daga zuwanta har ta fara yi wa masu hidimar otel din watsi da kudi, shi kansa naira dari uku ta bashi. . Aka kwankwasa kofar, "Shigo" Surayya ta ce a sanyaye, kofar ta bude sannan ya shigo, shi ne mai karbar baki, kuma shi ne mai baiwa duk wanda yazo otel din dan mukullin ɗaki, dogo ne fari kakkaura, yana da cin zanzana a fuska, yana da kananan idanu kamar na maciji, fatar bakinsa ta dafe ta yi baki, hakan shi ya sa Surayya ta tuna da tarihin ƘABUSU. A wannan ranar yana sanye da shudayen kaya riga da wando, kafafunsa kuma sanye cikin tsohon takalminsa wanda ke kokarin yin dariya kowane lokaci daga yanzu. "Gani na zo ranki ya dade." Ba ta bar damar ta wuce ba sai ta ce cikin iko "Don Allah wani aiki za ka yi min, dan karamin aiki ne, sai dai kuma ladansa na da yawa." "Wanne irin aiki ne Hajiya?" Ya tambaya cikin mamaki. Ba ta bashi amsar ba sai ta ci gaba da cewa "Aikin zai iya kawo maka ladan Naira dubu biyar." Mutumin ya yi ajiyar zuciya hade da hucin da ke barazanar yage labulan dakin, idonsa ya zazzaro sannan ya hadiyi yawu kut! Kamar ansa giyar mota "Fada min na ji Hajiya zan yi miki ko wanne iri ne." Tuni ya fara tunanin abin da zai yi da kudin. "Za ka iya tunawa da bakin da suka zo yanzu yanzun nan?" "Na tuna su Hajiya." "Nawa ne lambar dakin da ka ba su?" "Lamba (10) hawa na biyu." "Kana da wani dan mukullin ne bayan wanda ka ba su?" Ta tambaye shi. "Eh ina da shi, daman kowane daki makuli biyu ne da shi saboda ɓata, daya muna bada shi ga mai dakin daya kuma mu rike." Ya yi shiru lokacin da ya ga Surayya ta mike ta dauko wata jaka dake kan gadon, sannan ta bude ta, a cike take da masu launin siminti, wazobiya, jikinsa ya fara rawa, "Ina son ka ba ni daya dan makullin na dakinsu, gobe zan dawo maka da su, ina son kuma idan bakin sun fita, ka yi min waya domin na sani." Sannan ta yi masa murmushi. "Idan har ka yi abin da na saka ka ci Naira dubu biyar, yanzun nan kuma zan baka." "Ina zuwa." ya ce da ita, ya fice daga dakin da sauri ba a jima ba ya dawo yana zuwa ya mika mata dan makullin har da durkusawa." Ta karbi dan mukullin, sannan ta jefa masa, damin wazobiya "Naira dubu biyar ne, ina kuma jiran sako da zarar sun fita." "An gama Hajiya." har ya juya zai fita sai ya juyo yace da ita "Sai dai kuma Hajiya ya kamata na san dalilin ki na son shiga dakin." "Rakumi na ne ya bata shi ne nake son na duba shi, ko ya shiga ɗakin." Ba ta kara kallon sa ba sai ta nufi tagar dakin wajen kujerarta ta zauna. Maganar da ta yi ita ta gargade shi, kada ya sake wata tambayar. Mintuna uku da yin haka sai Surayya ta ji talfon din ta ya dau kara, ta dauka ta kai hannunta. "Sun fice" Aka ce da ita. Ta yi sauri ta aje kan talfon din, ta nufi kofar ɗakin da sauri, dan mukullin da ya ba ta a hannunta, tana zuwa sai ta hau abin rage hanya, ya yi kasan benen da ita, zuwa hawa na biyu, mintuna uku sai ga ta a kofar dakin. Ta zura dan mukullin ta bude dakin, tana shiga ta ji kamshin turare ya bugi hancinta. Tangamemen daki ne mai dauke da wangamemen gado mai kama da filin wasan kwallo, dakin ya yi mutukar tsaruwa, ta yi mamakin ganin cewa daga zuwan Rayyanu har ya barbaza kayansa ko'ina cikin dakin, ta fara dube-dube, ita kanta ba ta san abin da take dubawa ba, ta birkita nan ta duba can, ba ta ga komai ba, sai bayan da ta gama ne sannan ta yi ido hudu da wata jakar wasika wacce ke aje akan teburin da ke can bangon dakin. A gefen jakar wasikar kuwa wata wasika ce ajje ko linke ta ba a yi ba. A kan farar takarda aka rubuta ta, ga dukkan alamu ba a dade da gama rubuta ta ba, domin har da biro a kan ta, tana zuwa sai ta fara daukar wasikar da nufin karantawa, a sannan ne to sai ta ga adireshin dake bayan wasikar na wata unguwa ce a can cikin kasar kwalambiya, ta zaro wasikar ta fara karantawa, duka wasikar layi takwas ce an kuma rubuta ta da koren biro. "Rayyyanu ina son ka dawo da gaggawa domin abin nan ya samu, zata kai ta Naira miliyan arba'in, mai kyau ce don haka sai ka sami yarinyar da za ta fitar mana da ita, ka san yanzu yadda abin yake idan ba mace ba babu wanda ya isa ya fita da abin daga Najeriya. Sai ka zo." A.D banasare Gumi ya lullube Surayya lokaci guda, kirjinta ya fara bugawa, damar da take jira ta samu domin ta tabbata abin da ake magana ba wani abu ba ne face... Ta yi tsaye tana tunani, idan banda maigadi Mu'azu ya dan sanar da ita labarin Rayyanu ba to da ba za ta taba gane me ake magana

Chapter 2 of 9