Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
a kai ba "Hodar Iblis!" ta tambayi kanta . Ta sake daukar daya wasikar ta fara karantawa, ga mamakinta sai taga a ashe amsar waccan wasikar ce da ta gama karantawa yanzu. Na ga sakonka Alhaji, na kuma dawo gida lafiya zan zo jibi, tare da bayanin yarinyar da za mu sa ta yi aikin, tuni har na sa babban yarona binciken wacce ya ga kanta ya waye da bariki... "Kamar ni ke nan!" Surayya ta yi dariya, sannan ta aje wasikar ta fice daga dakin. Ba'a fi mintuna biyar da faruwar hakan ba sai ga Surayya ta shiga dakin saukar bakin dauke da jakun-kunanta guda biyu ta sami mutumin da ta sa aikin zaune yana karanta mujalla, tana zuwa sai ta mika masa dan mukullin, "Na gode.." Ta ce da shi, "...ni zan tafi sai kuma wani lokacin." Ya bude baki yana kallon ta cikin mamaki. "Hajiya me ya sa zaki tafi tun yanzu, ko dan..." Irin kallon da ta yi masa shi ya sa shi ya yi shiru. "Sai an jima" Tace da shi. Kafin ya sake buda baki ta fice daga otal din, tana fitowa ta sami mota ta ɗaga mata hannu ta tsaya "Falmanda otal" ta ce da direban motar . Falmanda otal ita ma katuwar otal ce a nan garin banasariyya, tana ɗaya daga cikin kayatattun otal dake garin Ko babu komai a kalla dai tana da manya-manyan dakunan kwana, wanda mutum biyar za su kwanta ba tare da wani ya shaƙi numfashin wani ba. Fulawowi da yan kyawawan dukus-dukus din bishiyoyin dake Falmanda otal su ma abin kallo ne, in ka dauke inda motoci ke bi, da kuma inda aka yi shuke-shuke ko ina tayil ne a otal din. Lokacin da ta iso otal din, sai ta fara tunanin ko mafarki ta ke yi? . A zaune a farfajiyar otal din akan kujera, bakin tabarau a idonsa sigari a bakinsa, mujallar kwallon kafa a hannunsa, daya daga cikin samarin nan ne, wanda suka jefar da ita a bakin kogi, abu daya ta tabbata shi ne ba zai taba gane ta ba, saboda daman ganin dare ya yi ma ta, bai kuma taba ganin ta ba, sai ranar da Rayyanu yasa su dake ta. Farin ciki ya lullube ta, hakika sa'a a bangarenta take. Ta kasa gaba ta kasa baya, zuciyarta cike da tunanin abin da ya kamata ta yi, tuni ta fara tunanin cewa wannan ita ce damar da take jira ta rama abin da Rayyanu ya yi mata. Duk da yake dai da farko ba ta yi niyyar farawa takan Rayyanu ba, abin da ta yi niyya shi ne ta fara ta kan Haidar, wanda shi ne musababbin faruwar komai. Sai kuma ga shi hannun agogo ya dawo baya. "Tabbas wannan dama ce a gare ni mai girma." Ta ce cikin zuciyarta. Mintuna biyu suka shude tana tsaye, daga karshe ta yanke shawarar abin da ya kamata ta yi, sannan sai ta nufi cikin otal din, ta yi wa kujerar da saurayin ke zaune kallo daya sannan ta dauke kanta. Ta na tafiya kamar dawisu, ta nufi inda sauran jama'a ke zaune suna shakatawarsu, tun kafin ta karasa gurin da samari da yammata ke juyawa, zuwa ga kallon ta, zuciyar samarin cike da yabo na kyaun cikar halittar Surayya, zuciyar magidantan wajen su kuma cike da takaicin ganin yarinya kyakkyawa ta shiga yawon bariki. Ba ta ko lura da abin da suke ba, sai ta wuce kai tsaye gurin mai saukar baki na otal din, yana zaune a wani dan karamin daki, wanda aka kirkire shi a tsakiyar wani dakin, ta hanyar yin amfani da bangon gilashi, mai saukar bakin ya karbe ta, tare da faffadan murmushi, manya-manyan farare hakoransa suka bayyana a fili kamar jerin luwadu. Saurayin bai yi aune ba yana karatun mujallarsa sai ya ji kamshin turare ya bugi hancinsa, ya dago kai lokaci guda da sauran mutanen dake otal din, kamar dai sauran shi ma ya yaba da kyawun Surayya, fiye da kowa kuma dake gurin, tsigar jikinsa ta yi yar!!! Shi kansa sai da abin ya razana shi, ya kuma ba shi mamaki, domin karo na farko tun lokacin da ya fara yawon duniya sai yau ne ya hadu da macen da ya ji kaunarta ta mamaye masa zuciya. A da can wani zamani da ya wuce bai san menene so ba, sau da yawa ya kan yi dariya ga wadanda ya ji suna cewa, wai ina son wane, ko ina son wance Hakika yau ya gane kuskurensa. Kallo daya ya yi wa Surayya, ya tabbatar masa da cewa yar bariki ce, irin suturar da tasa, da kuma yadda take tafiya, kanta a dage fuskarta a hade, shi ya tabbatar masa da hakan. Tunanin farko da ya fara fadowa zuciyarsa shi ne "Shin Surayya za ta dace da aikinsu kuwa?" Shin zai iya yarda da ita kuwa? Ya sake tambayar kansa, bai sami amsar tambayar sa ba, sai ga Surayya ta sake fitowa daga cikin dakunan otal din. A wannan karon ba shi ba, hatta mai saukar baki, sai da ya nuna alamar rikicewa da irin kyawun Surayya. Tana sanye da bakar riga ta siliki wacce ta kama jikinta tsam-tsam, zanen rigar shi ma irin silikin rigar ne, kusan iya gwiwa ta daura shi, kanta babu dankwali, sai gashin kanta ke kyalli kamar madubi, kafarta sanye cikin takalmi baki mai gashin robar, sarkokin da Grace matar malam Jackson ta bata su suka kara fito da kwalliyarta, fuskarta a boye a bayan bakin tabarau, babu alamar murmushi a fuskarta, ta tsaya kerere tana duban mutanen da ke farfajiyar otal din daida, a daidai lokacin ne saurayin ya yi karfin hali ya daga mata hannu, ta dube shi a yatsine sannan ta dauke kai, daga karshe sai ya ninke mujallar da yake karantawa, sannan ya nufo inda take tsaye. "Dake fa nake yan mata." "Jin ka nake dan samari." Ta ce da shi "Ya kamata mu sami guri mu zauna, ko kuwa me ki ka gani yan mata?" Ya tambaya. "Haka ne fa dan samari." A karo na farko, sai tausasan lebbanta suka fadada izuwa murmushi, saurayin ya yi kokarin ganin kwayar idonta ta cikin bakin tabaran, amma maimakon haka, sai ya yi nasarar hango hoton mummunar fuskarsa, ta cikin tabaranta. Sun yi kimanin mintuna arba'in suna hirarsu, irin ta yan bariki, hirar da duk mai mutunci ba zai so ya ji irin ta ba, duk da yake kuwa Surayya na yin ta ne kawai don ganin ta ribta shi ya yarda da ita, duk abin da ake Surayya na da masaniyar cewa, zaman da saurayin nan yake zama ne na zaben yarinyar da za ta fitar da hodar Iblis din uban gidansa Rayyanu. Surayya ta yi mutukar sakin jikinta wanda daga karshe saurayin ya fara tunanin ko ita ma wai ta fara kaunarsa ne. . "Mene ne aikinka?" ta tambaye shi. Saurayin ya yi dariya, duk da yake kuwa dariyar na iya firgita kananan yara, "Aikina yan mata ki ke son ki sani?" Surayya ta gyada kanta. "Aikina shi ne CI A SAUKAKE." Surayya ta yi dariya "Ashe dai hanyar mu guda dan samari, ni ma abin da ya fito da ni kenan yawon duniya, yau shekarata biyu kenan, amma har yanzu ba bayani, ban sami abin bukata ba, "Mene ne abin bukatarki yan mata?" "Kudin gaggawa." ta ce da shi cikin murmushin yaudara. Saurayin ya yi jim, zuciyarsa ta kasa yanke shawara kwakkwara, shin zai iya amince mata kuwa? Sannan ya dubeta cikin zargi ya ce, "Da za ki iya wani aiki da kin sami abin bukatarki kudin gaggawa amma da hadari fa. Idan kuma na fada miki aikin babu zancen janyewa dole ne sai kin yi ko kuma..." Surayya ta yi murmushi, ta ce "Na fahimta ba sai ka fada ba, na gane ka san fa ba yau na fara bariki ba." "Da kyau yanmata, ashe kina ganewa." Sannan ne ya saki jiki ya fara labarta mata, abin da za ta yi. . ********** ******** ********* . A dakin Surayya wanda ke Almanda Otal aka shirya taron, tuni samarin sun hallara, Rayyanu kawai ake jira, wanda kuma shi ne zai zo da hodar Iblis din, samarin biyu suna zaune a cikin biyu daga cikin kujerun dake dakin, dukkansu suna shan taba, kowannensu ya boye mummunar fuskarsa a bakin tabarau. Ko kadan yanzu Surayya ba tajin tsoronsu, ramuwar gayyar da ke zuciyarta su suka kashe duk wani tsoro, zuciyarta a bushe take kamar dutsen da ke tsakiyar sahara. "Yau ne zan fara ganin cikar burina" ta ce cikin zuciyarta. Kwana biyu kenan tun haduwarsu da saurayin nan, "Sakaran banza." Ta ce a cikin zuciyarta, ta yi mamakin ganin yadda ya fada cikin tarkon da ta kulla masa haka da gaggawa, kamar wasa sai saurayin nan ya zayyane mata bukatarsa a fili, "Ina tsoron fa kar a kama ni" Surayya kenan ke fadi lokacin da take kokarin kara rifta shi a rami gaɓa dubu. "Babu mai kama ki..." Ya ce da ita, "...in dai kin yi yadda na sanar da ke, to babu abin da zai faru. Kedai kawai ki yi kokarin ganin kin yaudari mai binciken kome ya nema a gunki kar ki ki yarda ki hana shi, abin da nake son ki gane shi ne yadda kike da kyawun halittar nan ba dukkan ɗa namiji ne zai ganki ya kyale ba, to balle kuma lalataccen mutum irinsa." Saura kadan dariya ta kubucewa Surayya "Yau ga lalatacce yana cewa kuma wani wai lalatacce. "Duk ranar da za a yi tafiyar sai ya sami yarinyar da zai tafi da ita, kin gane ko?" Ya ci gaba da cewa, "Su kansu matuka jirgin ruwan sun san da haka, kin ga kuwa kina cusa kanki zai yarda da ke, idan kuwa ya amince miki to babu bincike a kanki domin tare za ku shige jirgin, ke bari ma na fada miki, ba za ku shiga jirgin ba sai bayan an gama duk bincike- binciken da za'a yi, kuma shi mutumin da nake baki labari shi ne babban jami'in tsaro mai bincike na gabar kogin garin nan, kuma duk lokacin da babban jirgi ya zo, da shi yake tafiya, saboda idan za'a sauke kayan ma sai ya sake bincike na musamman, ina fatan kin gane manufata? Ya tambaya, Surayya ta gyada kai, "Saboda haka jibi za mu zo da komai da komai nan otal din, zamu zo tare da babban Ubangidanmu, shine kuma zai zo da hodar Iblis din, saura kuma dame? Za mu same ki a can kasar masar din idan kun sauka, mu zamu bi ta jirgin sama, kina isa zamu hadu da ke a can." Duk wannan tunanin ta na yin sa ne lokacin da take tsaye a bakin tagar dakin tana leke, awa biyu kenan suna jiran Rayyanu, har yanzu bai zo ba. . "Yau Rayyanu zai yi kaduwar da bai taba yi ba a rayuwarsa..." ta ce cikin zuciyarta. Tunaninta ya katse a daidai lokacin da hancin wata zungureriyar mota ya danno kai cikin otal din, kofar motar ta bude Rayyanu ya fito dauke da bakar jaka, mai dishi-dishin fari, bata tatsaya bata lokaci ba, sai ta juyo ta ce da samarin da suke zaune "Ina zuwa." Sai kawai ta shige bandakin dake fuskantar dakin, babu wanda ke da masaniyar abin da ta shiga yi, dukkan samarin kuma babu wanda ya san da zuwan Rayyanu, kofar dakin ta bude a hankali, Rayyanu ya shigo dakin kamar fatalwa, ba su san ya shigo dakin ba sai da ya yi gyaran murya sannan ne suka yi firgit. "Sannu da Zuwa" Suka ce da shi, bai amsa ba, yana tsaye ne a tsakiyar dakin idonsa akan kofar bandakin, yana dube-dube, kamar kullum hannunsa na hagun a cikin aljihun kwat dinsa, hannunsa kuma na dama rike da kyakkyawar akwatin nan, babu yadda za'a yi idan ba an gaya maka ba ka yi imani da cewa miliyan arba'in ne a ciki, kamar sauran shi ma Rayyanu idonsa a boye a cikin bakin tabaron, sai dai nasa daga samansa an rubuta "Colombo" Zungureren karan sigari a bakinsa hayaki na fita ta hanci, gwani ne wajen iya shan taba, bai ko damu da zaro hannunsa daga aljihun ba, don rike sigarin, har yanzu yana duba cikin zargi da rashin yarda, duk da yake samarin na da taurin zuciya, sai da zuciyarsu ta yi laushi tubus, tsoro kuma ya kama su, domin sun san idan ran Rayyanu ya baci, yafi kumurcin maciji hadari. Rayyanu ya yi taku biyu gaba sannan ya juyo bayansa na fuskantar bandakin, ya fuskanci samarin a lokaci guda kuma ya zuke sigarin dake bakinsa ya fitar da hayakin ta hanci daya, sannan ya saki sigarin ta fado, ya sa kafa ya take ta, "Ina yarinyar take?" Ya tambayi samarin cikin kakkausar murya. Kafin su amsa, sai muryar Surayya ta ratsa sararin dakin, yadda sassanyar iska ke ratsa jiki, "Gani nan!" Rayyanu ya juya firgigit, sannan ya yi mutuwar tsaye, Surayya na tsaye a bakin dakin, hancin yar karamar bindigar da Grace ta ba ta na barazanar sakin harsashi zuwa cikin Rayyanu, gaba daya samarin sun yi mutuwar tsaye babu mai motsi. Da ka gansu sai ka dauka gumaka ne, bakin tabaran dake idon Rayyanu ya fado kasa kar, sukayi ido hudu da Surayya, babu alamar tausayi ko imani a fuskarta, wani abu ya taho ya tokare makogwaron Rayyanu saboda kaduwa da tsoro, da kyar yake numfashi, tunda yake bai taba ganin fatalwa ba sai yau, sai dai kuma fatalwarsa ta fi ta kowa haɗari. "Fatalwa da bindiga! Dana san za ta yi fatalwa da ban kashe ta ba. . "Kada ka yi tsammanin fatalwa ka ke gani" Muryarta ta sake ratsa shirun dake dakin, kada kuma ka yi tsammanin ba zan harbe ka ba, daidai nake da na harbe ku ku duka, ka san an ce rama cuta ga macuci ibada ce, ina son jakar da ke hannunka. Rabin minti na baka ka yanke shawara da ranka da Naira miliyan arba'in wanne ka fi so? Sannan ta kalle shi ta yi dariya, "Kowa ya kwana lafiya shi ya so Rayyanu, amma kai ba ka so zaman lafiya ba, arzikin da kake tunanin za ka yi ba za ka yi shi ba, sai kuma na ga karshen ka." Dakin ya yi tsit ba ka jin komai sai bugun zuciyar su Rayyanu, "Ki yi hakuri" "Hakuri?" ta kyalkyale da dariya " Ashe taurin kanku na banza ne dan samari, ka tuna lokacin da kake duka na, ko hakuri ban baka ba fa, amma kai gashi har ka karaya!" Ta ba da baya kunamar bindigar ta yi kara kur, sannan ta ce da samarin da suke zaune, kamar gumaka, "Ku ce da shi ya aje akwatin a kasa, idan kuma ba haka ba, to ta kanku zan fara sai kun fara mutuwa kafin shi" Jikin samarin ya dauki rawa, dogon cikinsu ya ce da Rayyanu "Aje mata Rayyanu in har kana son mu tsira da ranmu" "Me kake nufi kenan?" Rayyanu ya tambaye shi. "Abin da nake nufi shi ne idan baka aje ba za mu hadu mu karya wuyanka muba ta jakar, domin mu rayuwar mu tafi kudi, ina amfanin badi babu rai" "Ka fadi gaskiya abokina" daya saurayin ya ce. Surayya na jin su ba ta ce komai ba, har yanzu bindigar na saitin kirjin Rayyanu. Rayyanu ya dubi samarin, sai ya ga idan har bai bada jakar ba, to ba abin da zai hana su kashe shi su ba ta jakar. "Yanzu muna ji muna gani naira miliyan arba'in zatabi ruwa?" "To mene ne?" daya saurayin ya ce "Gara rayuwar mu da duk arzikin duniyar nan, "Lokacin ka ya cika Rayyanu" muryar Surayya ce mai dauke da tsananin barazana ta sake ratsa dakin. Rayyanu ya saki jakar ta fado a kasa tim, sannan ya juya ya kalli samarin a fusace, ya ce "Banzaye matsorata, yanzu kuna nufin ku ce min mun yi sallama da kudin kenan. Miliyan Arba'in! Miliyar Arba'in!! Miliyan Arba'in!! Sannan ya kwalla kara yafadi a tsakar dakin, miliyan arba'in. "TA LEƘO TA KOMA" Muna ji muna gani" Surayya ta matso da sauri kusa da inda ya fadi ta daki kansa da gindin bindigar dake hannunta nan take ya sume, samarin suka motsa da niyyar su rufo mata, kafin su tashi tuni ta ja da baya ta sake rufe su da hancin bindigar, "Kada ku zolayi kanku, domin kuwa daidai nake da na hallaka ku gaba daya, ku shiga bandaki ku rufe kanku!" ta buga musu tsawa gaba dayansu, kowannen su hannayensa a sama suka shige bandakin. Surayya ta yi sauri ta kulle su a ciki ta zare kubar mintuna kadan da faruwar haka, sai ga ta a cikin jirgin ruwa, ta nufi gidan Malam Jackson, gudun hijira kenan koda jirgin ya harba a cikin ruwa sai Surayya ta yi murmushi. "BAZAN AURI KARUWA BA" Ta Tuna kalaman Haidar. . ********* ********* ********** . "Karya kake munafukin banza, kai ma wato yanzu ka koyi munafurci ko? Tunda muke da kai Rayyanu na taba zaluntarka? Tab! Ai wannan zancen banza ne ka ce min wai mace ta kwace maka abin da zai kai darajar miliyan arba'in, mace fa ka ce, kai Rayyanu hankalinka kuwa daya kake fada min wannan zancen banzan?" ALHAJI D. BANASARE ya yi shiru yana kallon Rayyanu cikin takaici fuskar Rayyanu kamar madubin da aka kwarawa ruwa sai kyalli takeyi. Ta jike sharkaf da gumi. "Alhaji Wallahi ba laifina ba ne, na fada ma ritsa mu ta yi da bindiga, ta doke ni akai, ta kulle kuma yarana a bandaki, ka san kuma idan har ban bata ba kashe ni za ta yi. Yanzu Alhaji duk iya zaman da muka yi da kai na tsawon shekaru muna wannan sana'a ba ka yarda da ni ba? Ka tuna fa irin hadarin da na sha jefa kaina wajen ganin hodar iblis dinka ta samu shiga." Rayyanu ya yi shiru na dan lokaci, sannan ya ce "Na yi mamakin ganin cewa kafi damuwa da kudi fiye da ni, duk da yake kuwa duk son kudin ka baka samunsu sai da taimakona, ai kamata ya yi tunda ka yi wa kudi mugun sabo, to ka fitar da hodar iblis din da kanka, kuma kai kanka ka san baka da wanda ya fi ni. Kai na daina rokonka da ka yi hakuri, idan baka yarda da abin da na fada ba, to kasa hukuma ta kama ni, a matsayin wanda ya sace maka hodar iblis" Rayyanu ya yi dariya ganin fuskar Alhaji D. Banasare ta koma toka-toka. "Ya isa haka." Alhaji Banasare ya ce da shi, "Da na dauka da gaske maganarka haka take, duk fadan da nake yi ina yin sane domin kada ka sake yarda a yaudareka nan gaba, amma maganar da ka yi yanzun nan ita ta tabbatar min karya kake, wato kai dabararka ita ce idan ka rike hodar iblis din bani da ikon yin komai, saboda kana ganin a matsayina na mai aikata babban laifi ba zan tunkari HUKUMA BA. "Ka yi kuskure Rayyanu, wannan kuma ya nuna min kai karamin dan fasa-kwaurin miyagun kwayoyi ne, tunda baka san alakar dake tsakaninmu da jami'an tsaro ba" Alhaji Banasare yace. "Amma kada ka manta na yi alkawari duk inda hodar Iblis dina take sai ta dawo, za'a dauki lokaci babu mamaki mako guda, wata daya, ko ma shekara amma na san za ta dawo. "Sau da yawa Rayyan, mutane irinka masu hadama sun sha cuta ta, ta hanya dabam-dan suna ganin kamar za su tsira, to hakika sun ga kuskurensu daga karshe. Duk wanda ya cuce ni dole ne na rama, babu wanda ya taba cuta ta, ya kai labari, yau shekara arba'in da tara 49 kenan ina safarar miyagu kwayoyi. Kasancewa tun kafin a haifeka kenan, ban taba samun wanda ya kawo mun karyar rainun hankali kamarka ba" Alhaji Banasare ya yi shiru yana kallon Rayyanu, ko ido baya kiftawa, sannan ya ci gaba da cewa "Yau da ace yarinyar nan da ta ritsa ku da bindiga ba bahaushiya bace zan iya kusan yarda, amma bahaushiya fa, zai yi wuya na yarda, na San al'adar matan turawa ce rike bindiga tare da sauran matan wasu kabilun Nigeria, amma matan mu sun cika tsoro, bindigar ma ba sa son gani fa, amma sai ga shi kana kokarin shayar da ni karyar wai yarinyar yar bahaushe ce ta ritsa ku, ku uku da bindiga ta kwace muku abin da zai kai darajar naira milyan arba'in, haba Rayyanu, yanzu kana nufin kace min famfamfam kenan da milyan arba'in, yau shekara goma sha daya kenan ina shirin samun wannan hodar iblis ɗin baka san irin wahalar dana sha ba, wajen samunta, tun da na ke ban taba samun mai yawanta ba, sai ga shi cikin sa'a guda ka salwantar min da ita? Lallai a gaishe ka ɗan samari. Kana nufin ka ce min "TA LEƘO TA KOMA" kenan? Zai yi wuya dan samari. Dole ne sai hodar iblis dina ta dawo, duk tsiyarka" Sannan YA daga Dan yatsansa yana nuna goshin Rayyanu yace, "Ba kuma za ka kai labari ba, kamar sauran na can, kuma zan shawarce ka, abin nufi shi ne ka sayi likkafani dan samari babu mamaki kwanakinka aduniya ba su fi haka ba.." ya daga yan yatsu biyar a fuskar Rayyanu, "Tashi fice munafuki!" ya buga masa tsawa mai kama da aradu. . *********** ********* ************ . In ka dauke Alhaji Banasare dake sanye da farare kaya riga da wando na shadda duk dakin kowa sanye yake da bakaken kaya, su goma sha biyu ne banda Alhaji Banasare. Kujerun dakin kowacce na dauke da mai bakin kaya da gashin baki guda daya, dakin kamar majalisar dinkin duniya, ba don masu damara sun yi yawa ba. Za ka yi mamaki idan aka ce ma wannan taron anyi shine akan yadda za'a nemo hodar iblis din da Rayyanu ya salwantar. Abin mamakin da ya fi kowanne kuma shi ne yau ga masu hanawa ayi za kuma su yi, babban jagorar tawagar shi ne mataikakin kwamishinan yansanda M.K. AGANANI MU-SHA-GARA wanda ke zaune kusa da Alhaji Banasare, yana zazzare idanu, dankareran mutum ne, mai kwarjinin gaske yanada fadin kirji, kansa mai kama da kankana na dauke da kananan idanu irin na maciji, gashin bakinsa wanda sai ya turar da shi gefe guda yake samun damar shan iska, shi zaka fara gani idan ka hango shi daga nesa, sau da yawa mutane su kan tuna da zamanin su Lamarudu, aduk lokacin da suka dubi gashin bakin M.K Aganani Mu-sha-gara, dogo ne na innanaha, idan ya fara mikewa tsaye sai ka fara tunanin kamar ba zai kare ba, akwai jita-jita dake cewa shi ne ma'aikacin dansanda da ya fi kowa tsayi da ban tsoro. Idonsa kamar gauta yana da faffadan hanci, mai kama da usir, abin mamaki kyeyarsa ce kadai ke da gashi, amma idan ka dawo sauran bangaren kansa kamar kwai yana kyalli kamar bakin kuturun tawada. . M.K. Aganani Musha-gara ya dade yana cin amanar gwamnati da kuma kungiyar yansanda, amma a boye, ba kuma sanin kwamishinan yan sanda na Banasariyya. In ka dauke shi kansa tare da mutane goma sha daya da ke goya masu baya, wadanda su ma yake lasa musu zuma, a duk lokacin da aka dace, babu wanda ya san aika-aikar da yake aikatawa. Babu wanda ya san takamaiman yarensa. Wasu sun ce gara ne. Wasu sun ce Bakatafe ne. Allah ne dai masani. Yau shekaru ashirin da tara yana taimakawa Alhaji Banasare wajen safarar miyagun kwayoyinsa, ko da yake ko ba'a fada ba, kasan cewa ba karamar zuma ake lasa masa ba Albashin da Alhaji Banasare yake biyan sa, ya rubanya wanda yake samu a gurin aikinsa sau shida da wani abu. Karatun yaransa zuwa kasar waje da kuma kayan abinci irin na alatu dake kwarara a gidansa duk wata Alhaji Banasare ne ke daukan nauyin. Kamar yarda aka saba yau ma sai ga shi an taru a babban falon Alhaji D. Banasare, ana tattaunawa. . "Kana nufin ka ce min yaron ne ya yi sama da fadin KOKEN din ne?" Aganani ya tambaya cikin muryar da za ka iya kira ta jami'in tsaro mai aiki tukuru. "Kwarai kuwa" Banasare ya ce "Ka ji fa zancen nan wai mace bahaushiya ta ritsa maza karti guda uku ta kwace abu a hannunsu, zai yi wuya Aganani. Abin da nake so da kai shi ne ku tattausa min Yaron nan sai ya yi Aman gaskiya. Ba sai na bata lokaci ba wajen fada ma abin da ya dace ku yi, amma ina so daga karshe ku zo min da labarin inda ya boye hodar iblis din...... . Aganani ya daga kai ya dube shi, sannan ya ce. "An gama" A zahiri Aganani Mu-sha-gara samsam bai ji ko rabin abin da Alhaji Banasare ke fadi ba, abin da kawai ya ji sosai shi ne wani yaro ya salwantar masa da koken din naira milyan arba'in. . "To da na bar aikin dansanda kenan, wannan damar ba za ta wuce ni ba!" Ya ce cikin zuciyarsa. "A yi niyya!!! Ya buga wa yansanda tsawa. Suka mike duka lokaci guda suna rawar jiki kamar sun ga mala'ikan mutuwa. Aganani ya mike daga kan kujera gaba daya yan sandan sai suka zama kamar mota agaban jirgi, tsakanin kansa da silin din rufin ɗakin bai kai kamun tafin hannu ba. Sannan ya dubi Alhaji Banasare ya buda baki zai ce bai sani ba, su nema da kansu, sai talfon din ya dau kara, Banasare ya yi sauri ya dauka yansandan na kallon sa. . "Wa ke magana?" Ya tambaya. "Saurara da kyau!" Aka ce da shi, "Da ni ne kai to da sai na nemi Rayyanu a sariyana Otal idan kuma ba ka gaggauta ba, ka yi sallama da hodar iblis dinka kenan." . "Wace ce ke magana? Mene ne sunanki?" Alhaji Banasare ya tambaya bakinsa na rawa "Sunana kake son ka ji? Ban sani ba." Aka ce da shi, a lokaci guda kuma wayar telfon din ta katse. . ********** ********* ********** . Surayya ta yi murmushi, sannan ta aje kan talfon din, ta duba agogonta, karfe shida da rabi na yamma agogon ya nuna "Bari na basu mintuna biyar." ta ce cikin zuciyarta, "na san kafin nan sun kusan isa Otal din. Ba'a dade ba sai ta sake daukar talfon din, ta sake buga daya daga cikin jerin lambobin da ta samu a gurin wani ma'aikacin "NITEL" A can daya bangaren Rayyanu ya dubi agogon dake manne a jikin bangon dakinsa dake Sariyana Otal karfe shida da mintuna talatin da shida. Ya kai kimanin sa'o'i uku kenan yana zaune, yana ta zulumin saɓanin da ya shiga tsakaninsa da Ubangidansa Alhaji Banasare. Zuciyarsa kuma cike da tunanin abin da Surayya ta jefa shi a ciki, "Haka Surayya ta yi min?" Ya ce cikin raɗa "Sai na nuna mata iyakarta, daga yau ta sake yi wa wani. Duk ran da na kama ta sai na karya wuyanta." Ya ce cikin fushi, "Sai dai kuma ina zan fara nemanta yanzu, a ina take? Ya tambayi kansa kamar amsar tambayarsa, sai talfon dinsa ta dau kara, da farko da ba zai dauka ba domin ya dauka

Chapter 3 of 9