Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
bayan daya an san lura da halin da dan shi ke ciki yasa shi yin hakan duk wanda yaje ya dawo kuma maganar guda daya ce ita ce ta ya riga yayi alkawari don haka ba zai saba ba. Daga gidansu Mansur ma an turo suma ba su yi nasara ba. Yaya Dijah da mijinta ma sun zo suma duk a banza, haka Yakumbo Halima wacce ita kam kaca-kaca suka sake yi da Babah Lantana, a wannan lokacin bana iya zaman gida ko da na mintuna ne, Babah Lantana da Asabe ba su da wata hira sai ta bukin nawa suna lissafin irin kwalliyar da za su yi. Don haka ina idar da sallar Asuba in na mike gidan Yaya Dijah nake tafiya a hanya nake gama lazimin da nake yi da addu'o'ina a gidan Yaya Dijah ba ma komai sai kuka ko kuma muyi shiru amma duk da halin da muke ciki na bacin rai taja ta tsaya kan bata yarda in tafi ko ina ba. To ki tafi ina Maryam? Kuma ki tafi ki bar ni da wa? Ki bar ni ni kadai? Tambayoyin da ta jero min kenan lokacin da na gaya mata niyyata ta barin gida in yi tafiyata in shiga duniya ya fiye min auren Nalami sauki. 99 Tana maganar tana kallona, yanzu nan za ki iya tafiya ki bar ni ni kadai? To ni kuma in zauna in yi me? Ba a karbarwa mutum ne Maryam da na karbar miki wadannan fitintinun da ki ke rayuwa a cikinsu, tana fadan hakan ta kama kuka, kuka Auwa mai tsanani. Hakan yasa shi kawar da wannan tunanin saboda sanin da nayi gaskiyar magana ta gaya min da ana karbarwa dan uwa wani al'amarin na kaddarar rayuwarshi na yarda da Yaya Dijah zata iya karbar min don ban taba shiga wata fitina ta bar ni na shigeta ni kadai ba. Gaba daya na bijirewa Mubarak na daina sauraronshi na daina shiga gidansu gani nake tanfar har da sakacinshi ya kara jawo min abinda Babah Lantana tayi min na hada ni da Nalami. Kina nufin ke kin fini shiga fitina ne yasa ki ke nema ki hada min da wulakancinki Kan halin da nake ciki? Tambayar da yayi min kenan a ranar da ya biyo ni gidan Yaya Dijah na ki fita ia ba shi umarnin shigowa har cikin falonta in da nake kwance tunda har falon mijinta da ya fara shiga na ce ba za ni ba. Niyyata yayi maganarshi ya gama ban ce mishi uffan ba amma ban san yanda aka yi ba hakan ya 100 gagare ni, na' samu kaina da tambayar menene fitinarka ba abinda kake so aka yi ba? Zuba min ido yayi yana kallona cikin matsananciyar kaduwa me yasa ki ka gaya min wannan maganar? Na kawar da kaina gefe don kar in ga kallon da yake yi min. A hankali na ce ai ba yau ka ke ganina ba. Yayi maza ya ce kuyo Maryam kwadayi ne da ni a kan karatunki ganin badi kamar yanzu kina shirin fita ne yasa yin hakuri na danne zuciyata. Dago ido nayi na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi 'Boko?; ya ce eh, na ce to na daina yin shi daga yau har abada kuma ba zan yi ba tunda dai saboda shi ne kayi sakacin da kaja min wannan musibar. Don haka kara kina kawai ka daina wahalar da kake yi a kaina tunda bokon da zai sa ka aure ni ban yi shi ba, ba kuma zaih yi shi ba. Cire ni kawai cikin matan da za ka aura, koda yake ma ni ban taba sanin kana son aurena ba in ban da wannan karon ban taba jin ka ce kana sona ba na soma kuka. Ka kyale ni kawai ka fita hanyata bana sonka bana kuma son komai naka, daga yau kuma kar ka sake yi min wani aike ba na so ka daina jin tausayina. 101 Mikewa yayi ya fita daga falon ya tafi ba tare da ya tsaya yiwa Yaya Dijah sallama ba. Yaya Dijah ta shigo bayan tafiyar tashi, da kin daina yiwa Mubarak irin wannan abinda ki ke yi mishi da wanne zai ji ne? ni dai ban taba jin Lausayinshi irin na yau ba kinga irin zubewan da yayi? Bakin ciki ai baida kyau, ni kuma ban tabbatar ma za ayi aurenki da Nalami ba don jikina da Zuciyata ba su yarda da hakan ba nafi zaton wata hanya zata bullo da zata zame mana wata mafita ta warwarewar al'amuran kałamanta suka sanya ni na samu natsuwa har na yarda nayi wanka na shafa min na sanya daya daga cikin kayanta. Muje kicin muyi girki ka utanen gida su ji yunwa ba mu ba su abinci ba, na kalli agogo na ce ga su Inna ma sun kusa dawowa daga Makaranta, muna cikin girkin Isiyaku ya sake shigowa ya gaida Yaya Dijah kafin ya gaishe ni ya kuma shaida min tare da Mubarak suke. Yaya Dijah tayi maza ta kalle ni ya dawo, to kar ki yarda ki sake 6ata mishi rai na ce to na tashi na fita na same shi gaba daya idanuwanshi sun kada sun yi jazur. Ki ka ce ba ki tab6a sanin ina sonki ba saboda ban taba gaya miki ba? Shiru nayi ban ce mishi 102 komai ba, ya sake yi min wata tambayar shi yasa ki ka nemi wulakanta ni saboda. wasu suna gaya miki su suna sonki? Wani shirun na sake yi ban tanka mishi ba, to tunda ban taba cewa ina sonki ba, yanzu a wane matsayi ki ka ajiye ni ke nan? Ban kalle shi ba na ce mishi kayi hakuri, ina gaya mishi hakan fushin da yazo da shi ya gushe. Rannan ina kwance a dakina cikin dare idona biyu bacci ne ya gagare ni, in ban da sakar zuci babu abinda nake yi, in saka wannan in kwance, in saka wancan. Aurena da Nalami da kullum Yaya Dijah ke cewa bata tabbatar za'ayi shi ba saboda jikinta da zuciyarta ba su ji kamar za'ayi shi ba. Kullum kara matsowa yake yi, Babah Lantana da kawayenta tare da 'yarta sai shirye-shirycnshi suke tayi ko a ina take samun kudin a take ta kashewa oho. Ni kam cikin zuciyata ban tabbatar da maganar ta Yaya Dijah ba tunda ban hango wani juyi da zai zo ya hana aukuwar auren ba, in dai ba wata kaddara ta Ubangiji ba ne tunda dai komai na auren Babah Lantana ta sayo irin wanda taga yayi mata daidai. To haka zan zauna in yi ta zuba ido ina kallo har ranar auren yazo a daura a kai mishi ni? In har 103 aka yi haka kuma to me zai faru? Me zai biyo bayan hakan? Wanne hali zan shiga? Wacce irin rayuwa zan yi a gidan Alhaji Nalami? Rayuwar aure da Alhaji Nalami to a ya ya zata kasance ke nan? Wadannan sune jerin tambayoyin da suka addabi zuciyata, da na zurfafa cikin tunani mai tsanani sai naga aurena da Nalami kamar baya cikin jerin biyayyar da ya kamata in yi wa Babana, domin shima sa shi aka yi ba ra'ayin kanshi ba ne yin shi. Ita kuma wacce ta hada din da ta hango wani alheri a ciki komai kankantarshi to da bani ta tura ba tunda ni kam ai bata nufina da wani alheri, to haka zan zauna in yi ta yarda kullum Babah Lantana sai ta cuce ni ta cuci Babana? Ina kawowa nan na mike na sauko daga kan gadon na tsallake shimfidar Asabe da ke kwance a kasa na bude kofa nayi waje ko ban tafi na bar gida ba a yau ina son ganin yanda duhun dare yake in da hali ma kuwa ina ganin tafiyata kawai zan yi in yaso bayan wucewar ranar auren na dawo. Sannu a hankali cikin sanda na nufi kofar gidanmu, zare sakatar na sake jawo kofar a hankali na rufe don kar in bar musu kofa a buda bayan kuma dare ne kasancewar dama kudina a kulle suke a bakin zanina yasa ban tsaya tunanin komai 104 ba na kama hanya, hanyar baya na yi nufin bi don kar wani tsautsayi yasa in gamu da wani don in yi nisa da gida kafin gari ya waye in san in da na nufa. Ban yi wata tafiya mai yawa ba naja na tsaya cak saboda muryar da na jiwo a bayana tana tambayata ina za ki cikin daren nan? Kadan ya rago in karta da gudu saboda tsananin kaduwar da nayi in ban da kawai a kowane hali na kasance ko na samu kaina muryar da na jin ba za ta taba bace min ba, in dai ba Mubarak ba ne wannan to Aljani ne abinda naji uciyata tana gaya min ke nan, to shi kuma me zai fito da shi waje a cikin duhun daren nan a kuma daidai wannan lokacin na karfe biyu da rabin dare, in ban manta ba abinda na gani ke nan a dakinmu kafin fitowàta. Ina kike nufin zuwa a wannan lokacin? Kina nufin tana da asara in ki ka aikata wani abu makamancin wannan da kike shirin aikatawa? Ai bata da asara, watakila ma abinda tafi son gani ke nan. Kalaman nashi suka sanya zuciyata ta sakankance cewa lalle shi ne ba wani aljani ba, don haka na juyo muka fuskanci juna, hasken farin 105 wata yayi dalilin haduwar idanuwanmu nan take na soma kuka. Kawo hannunki kiji, kawo hannunki kiji irin abinda kirjina ke gaya min, kawo hannunki ki taba nan din nan ban ba shi hannun nawa ba sai dai na dcga idona na kalli nan din da ya ke nuna min, mazaunin zuciyarshi ne. Kwana nake yi ina zaune Maryam ban samu mutsuwar da na iya dora kafadata a kan shimfidata ba shi yasa nake barin dakin in fito waje in yi ta zirga-zirga tsakanin gidanmu da naku, tsoro nake kar su fake ni su sace min ke suyi sanadin shigata cikin halin da yafi wanda nake ciki. Tunda na gane abin da suke son ganinn nayi kenan to amma yanzu da ki ka fito din nan za ki tafi ban sani ba yar uwarki bata sani ba, me ki ke nufi da yin hakan'? Kina nufin za ki iya bada kanki ga wani ne? Kin san abinda barin gida ke nufi kuwa musamman wurin 'ya mace? Kina nufin za ki iya tafiya inda za ki rayu ba tare da ni ba yar uwarki ba? Kina nufin in akwai alheri a cikin tafiyar taki ni ba zan baki wannan shawarar ba? Don me ki ka shirya tafiya ba tare da kin nemi mu tafi ni da ke ba? Ke ce ba kya sona ki k: cewa ni ne saboda kawai ban ta6a buda baki na gaya 106 miki ba, ban taba zaton sai na furta miki da fatar baki ba, baki ai yana furta karya Maryamu, zuciya kuwa takan tilasta gabobi suyi bayanin abinda ke cikinta. Ban iya cewa Mubarak komai ba saboda kukan da nake tayi. Yi min alkawari a yau a in da muke tsayen nan a cikin sararin nan na Ubangiji cewar ba za ki taba fita ki tafi wani wuri ba tare da kin gaya min ko kin gayawa 'yar uwarki ba. Ki kuma yi min alkawarin ba za ki ta6a auren wannan mutumin ba ke ba shi kadai ba Maryamu yi min alkawari na wani ba zai taba taba min ke ba. Nayi maza na gyada kaina tare da furta kalmar nayi da bakina, duk kuwa da ban san yanda zan yi in cika alkawarin da yake tasa ni ina yi mishin ba, to muje in maida ke gida ki kwanta. Nayi maza na girgiza kai nuna alamar a'a, cikin nutsuwa ya dago idonshi sama na tsawon lokaci kafin ya dawo da kallon nashi gare ni, kina ganin zai yiwu muyi ta tsayuwa a nan har gari ya waye? Da sauri na ce mishi eh, ya girgiza kai a hankali nuna alamar a'a mutane za su yi mana mummunan fahinmta marasa tunani daga cikinsu su zarge mu da abinda bai kamata zargin zai fi tsanani a kanki ba zan so ayi hakan ba, don zai iya 107 zamowa bata suna zai iya zamowa dalilin da Baba zai yi fushi da ke, ba zan ji dadin hakan ba, ina so ki rabu da shi ne lafiya kin gane? Na gyada kaina nuna alamar na yarda. Muje in kai ki gida, ban sake yin musu da shi ba ya tasa ni a gaba sai da yaga shigana cikin gidanmu har sai da na maida kofar na kulle sannan ya juya ya tafi. Na sake yin wata sandar a hankali zan shiga dakinmu, sai kawai naji kofar dakin a kulle, abinda ya tabbatar min da cewar Asabe tana kallon fitana daga dakin bata dai yi min magana ba ne, kawai sai da taji na fita na bar gidan ta mike ta rufe kofa ta koma tayi kwanciyarta. Yaya zan yi? Abinda na tambayi kaina lokacin da na taba naji kofar dakin a kulle, fita zan yi in koma inda na baro Mubarak ko kuwa zama zan yi a nan in jira gari ya waye ta tashi ta bude in shiga? Ko kuwa sa hannu zan yi in buga kofar don taji na dawo ta tashi ta bude min in shiga? In yaso kowa ma yasan na fita da daddaren. Har na matsa jikin kofar da nufin fara bugawa sai kuma naga kai to in Babana ya fito ya tambaye ni ina naje a cikin tsohon daren nan in ce mishi me? In yi sanadin da zai yi bakin ciki? Kai ba zan iya ba da in yi haka gara kawai in kwana a tsakar 108 gidan in jira gari ya waye a bude in shiga in yaso ko don in kaucewa 6ata mishi sai in ce fita fitsari nayi Asaben ta kulle kofar. Don haka na shiga kicin na hau kujera na zauna ina kallon irin berayen da ke zirga-zirga daga kicin din zuwa tsakar gida da wurin wanke-wanke wanda yawan ta'adin abinci ya kara haddasawa. Wajen Asuba naga fitowar Babana zai wuce ban dakin gidan, nayi maza na kauce daga inda nake zaune na koma lungu sosai ya gamå abinda zai yi ya fita ya tafi Masallaci, sai ga Babah Lantana ta fito daga ita sai zani a kirji tana ganin kicin dinta a bude ta leko cikinshi tana haskawa. Satar min naman miya za ki yi? Kamar in tambayeta ko ta taba ganin inda da ya zamaa 6arawo a gidan ubanshi? Sai kawai naga to a na me zan tsaya ina irin wannan cacar bakin da ita, bayan ta riga ta buge ni tayi nasara a kaina tasa Babana ya dauke ni ya baiwa mutumin da babu wanda yasan me ke tsakaninsu sai su biyun suka san abinsu. Ba fa satan miki naman miya taje yi ba, iskancinta ta tafi shi ne ni kuma na maida kofar na kulle ta dawo ta same ta a kulle shi ne ta shiga kicin din ta zauna don kar ta buga kofar a ji ta a 109 tambayeta daga ina take? Iskanci kamar ya ya? Ta bukaci sani. Asabe ta tsaya tana yi mata bayani, ai dama rana dai-dai ne bata bude kofa cikin dare ta tafi can wajenshi sai sunyi abinda za su yi sannan ta dawo ta shigo ta kwanta gajiya nayi jiyan na rufe mata kofar. Babah Lantana ta tabe baki ta ce, ki ka sani ma da ba ki rufe mata ba kin barta ta shiga tayi kwanciyarta ta huta ni kam yanzu ai bani da sauran matsala da ita balle har in je ina kai kararta wajenshi a kan tana zuwa kwanan gida, to a na me? Kwanaki tara ne fa kacal suka ragewa zaman nata a cikin gidan nan, gidan da kullum sai ta yi wa mutane gorinshi sai kuma ta koma gidan Nalami, Nalami kuwa wannan matar tashi in dai tana nan a yanda nasan ta tooo ta dan yi murmushin iya shege ta wuce ta shiga bayan gidan tana fadin, dama in mutum ya ce ba zai yi sharar Masallaci ba ai zai yi na kasuwa. Duk abinda suke fada ina jin su shiru kawai nayi saboda ba ni da wani abinda zance musu huce bakin cikin da suka sanya ni a ciki. A haka muka kasance a çikin gidan nan har a ka wayi gari ana cewa saura kwana biyu ne daurin 110 auren nawa abinda yayi dalilin da na zama tanfar mara hankali saboda tsananin kidima da gigicewa, babu abinda bai zo ya roki Babana ba amma yayi shiru bai ce komai ba. Babah Lantana sai hidimarta take yi, babu abinda yafi komai. daga min hankali irin tsananin farin cikin da take ciki, wuni take yi tana dariya bata gaji ba, kan abinda bai taka kara ya karya ba ma sai ta kyalkyale da dariya ta bugi cinya tare da shewa kafin ta ce sai ni Lantana 'yar Babanta, mata a gidan Mallam Habu mai timatir, kowa yaci tuwo tare da ni miya yasha. In rasa in da zan tsoma raina in dan ji dadi nayi kuka a wannan lokacin har na fige na fita cikin hayyacina, ga shi bana ci ba na sha nayi mummunar ramar da na zama tanfar majinyaciya, wai a irin wannan halin da nake cikin kuma sai manya su rinka zaunar da ni suna cewa wai in yi hakuri wata rana sai labari. Ba don dai kar in yi wata magana na ce na fadi ba daidai ba ga shi ni kuma a' yanzu nema nake in rabu da kowa lafiya don gani nake tanfar ba zan wuce wannan lokacin ba, bakin cikin da ke addabar zuciyuata zai kashe ni kowa ya huta, da na tambaye su ni yaushe ne wata ranar nan da kullum a ke gaya min amma ban taba ganin tazo kan 111 al'amarina ta mayar min da shi abin bada labarin ba? A wannan lokacin ko gidan Yaya Dijah bana iya zuwa saboda rashin kuzari na wuni nake yi a kwance kamar yanda nake kwana a kwance don haka ban san abinda take ciki ba amma dai itama na gaya mata na gaji da jin zancenta na bata tabbatar za'ayi aurena da Nalami ba saboda wai jikinta da zuciyarta ba su yardan mata za'ayi hakan ba. Na ce to sai yaushe za su yarda? Sai sun ganni a dakinshi? Daina gaya min haka Yaya Dijah, bar ni kawai in fuskanci abinda yake gabana, ina fadin hakan ta kama kuka nima ban tsaya bata hakuri ba nasa kai na fita na bar gidan, ban sake komawa ba. Mubarak kuwa sai yazo kofar gidanmu sau biyu sau uku ban iya tashi na fita ba saboda bani da jarumtakar yin irin wadannan abubuwan kuma a wannan lokacin sai nafi sha'awar a ce kowa ya fita harkata a bar ni kawai ni kadai in yi ta kwanciyata ina tunanin Innata da sauran abubuwan da sukai saura. Bikin nawa ba wani biki ne da Babah Lantana tayi wa wani sayayya na abin arziki ba, amma ta shirya kawatashi ta hanyar tara tsofaffin kawayenta da suka yi gwagwarmayar rayuwarsu 112 tare har ma da Dafau Mai kalangu naji tana cewa zata kira. A al'ada ranar sakun lalle rana ce da Amarya tare da kawaycnta kan tafi yawon ban kwana, sai cikin dare take dawowa in an je an kamo ta a kawo ta gida a sa mata lalle, a irin wannan ranar ni na wayi gari ne a kan gadona ina kwance babu wata kawa a tare da ni ba a kira min ita ba nima kuma ban nemarwa kaina ita ba. Ina daki a kwance ina kallo Asabe ta sha kwalliya ta fita itama Babah Lantanar hidima sosai take yi tare da 'yan bukin da suka fara zuwa mata. Ina daki ni kadai in saka wannan in warware in saka wancan wai Nalami Babana ya yarda zai bada aurena gare shi in zama mallakinshi? To zai yi hakan a dalilin ya daina sona ne ko kuwa dai da gaske abin yafi karfin nashi ne? wannan shi ne abinda yake ta kai kawo a cikin Zuciyata. Da daddare kawar Babah Lantana ta sani a lalle saboda babu wanda ya tako cikin gidan, cikin dangin Innata da Yaya Dijah don sun ce babu ruwansu da bikin. Ni da mai sakun lallen kallon juna muke yi da ido zuru-zuru ta juya tana fadin oh'oh amaren 113 yanzu suna da abin mamaki babu ruwansu da duka don an saka musu lalle. Babah Lantana ta taso daga inda take tana fadin ai bata yi kukan sakun lallen ba, ita wannan ai tata rashin kunyar ta daban ce, ni kuma ba a wannan abinda ni bari ka gani, in na zo na sharara mata mari ai zata yi mai dalili. Ta zabura ta taho cikin saurinta da nufin shararan min marin, wasu cikin kawayenta masu dan hankali suka tare ta tare da fadin a'a haba mai shararawa Amaryar tana cikin lalle ki sharara mata mari me yayi zafi haka? Ina ruwana ni da lalleta tunda dai bata da mutunci a sa mata lalle ta ki yin kuka saboda ta matsu a kaita gidan mijin ko me? A haka dai ana wasa ana dariya a ka cimma burinta na dukana a cikin taron kawayenta da ta tara a gidanmu. Wata daga cikin kawayen nata da naji suna kira da sunan Lari baby duk da kokkodewarta wai baby take amsawa, ta matso kusa da ni cikin natsuwa ta ce min kin gani ko Amarya " yanmata ke yarinya ce don haka zan gaya miki lamarin duniyar nan sai a hankali, kar ki yarda kiyi abinda za ki cuci kanki. Zauna wuri daya kawai ki nutsu kar kiyi abinda zai je yazo ya dame ki shi lallen nan da ki ke gani ba karamin al'amari ba ne, wasa da hakkokinshi 114 wurin amarya al'amari ne babba. Shi ke sawa ki ga wasu amaren sun zama wasu, kar ki yarda ki ce za ki fita daga dakin nan ki fita waje kin ji ko? Amarya mai fita da lalle haukacewa take yi kin ji ko? Na ce mata to, saboda tsoratar da nayi da irin bayanin da tayi min din. To ina ruwanki ne da ki ke rattabo mata wannan bayanin? Tayi tambayar tare da galla mata harara kai ke daima da dogon baki ki ke, taja tsaki ta juya ta fita. Uh'uh Anti Lantana gara in gaya mata ta sani shi da ai na kowa ne, ai sai kiyi ta fita ta fita. Duk da bayanin da matar nan tayi min zuciyata bata hakura ta bar ni na zauna lafiya ba, kai-kawon da take yi yayi tsanani ko mikewa a gadona gagarata yayi ina zaune ne kawai ina sauraron abubuwan da take gaya min. Daren nan na yau shi kadai ne yai saura min gari na wayewa za a daura min aure tunda daurin auren ma na safe a ka ce za'ayi kenan daga nan zuwa wayewar gari ne yai saura min, to haka zan zauna shi ke nan magana ta kare ko kuwa ya ya zan yi? Shi ke nan sai in zauna a daura min aure da mutumin da Babah Lantana ta kawo min? da Babana ne don ra'ayin kanshi yaga zai bada ni 115 gare shi da ba zan yi jayayya da auren ba tunda ni din mallakinshi ne, to amma Babah Lantana, in zauna in karasa waycwan gari a Cikin gidan nan yana nufin na yarda da auren da za'a daura min. In sa kai in fita kuma ina tsoro saboda bayanin dakawar Babah Lantana tayi min, ina cikin wannan kai-kaWon sai kawai na tsoro matsayar da ta sanya ni mikewa tsaye ita ce ta da in zauna a daura min aure a kaiwa Alhaji Nalami ni gara kawai in fita in bar gidan in yaso duk abinda zai faru da ni ya faru dani a can gaba. Da wannan tunanin cikin zuciyata nasa kai na fita daga gidanmu sai dai ban san yanda aka yi ba ganina kawai nayi na kama hanyar zuwa gidan su Mubarak. Ina dosar gidan na hango shi zaune a kan dakalin kofar gidansu yayi zaman dirshan a kasa kanshi a sunkuye, har na isa kanshi bai ji motsi ba saboda ya riga ya shagala kan abinda yake yi. Na kasa ce mishi komai don ban san me zan ce mishi ba, kusan mintoci biyu zuwa uku kafin ya dago kai daga sunkuyon nashi yana ganina ya dan kadu bai ji isowar tawa ba da sauri ya shiga goggoge fuskarshi da tafukan hannayenshi duka biyu. 116 Me ya fito da ke a cikin daren nan? Tambaya yayi min cikin wani irin yanayi na nuna karfin hali da jarumtaka ban tsaya ba shi amsa ba sai kawai nasa kai na nufi cikin gidansu, maimakon in wuce can ciki kamar yanda na saba kofar wurinshi na tura na shiga nasa kai na wuce falon na shiga har can cikin dakin nashi abinda bai taba faruwa ba a rayuwata hasalima yau ne shigana wurin Mubarak na biyu. Can cikin dakin nashi a kayace yake matuka ga Ramshinshi da na saba ji a tare da shi katuwar katifa a yashe a kasa tasha shimfida mai daraja ga tarkacen takardu tare da laptop a gefe sai wardrope wacce na tabbatar kayanshi a ciki. Gabana sai faduwa yake yi yana harbawa da sauri da sauri, me ke shirin faruwa ne? me ya shigo da ni nan wurin? Abinda ke ta kai-kawo cikin raina ke nan. Mubarak ya biyo ni har can cikin dakin yaja ya tsaya a bayana cikin wani irin yanayi na sanyin jiki da tsorata da abinda yaga nayin me ki ke so a kawo miki Maryam? Ban tanka ba ban kuma waiwaya na kalle shi ba, na kai guiwowina duka biyu kasa na durkusa a kansu, ya sake biyo ni kasan yayi yanda yaga nayi muka fuskanci Juna. A hankali cikin nutsuwa cikin wata irin murya mai laushi da taushi a dalilin karaya da tsoratar da 117 tayi na soma yi mishi magana, zuwa nayi a yau don in yi maka godiya bisa dawainiyoyinka da alhairorinka a garce ni. A sanina ban taba sanin wani mutumin da ya kai ka yawan alhairi ba ka taimaki maraicina ta hanyoyi daban-daban da ba zai yiwu in fade su ba. To me ya kawo wadannan maganganun Maryam? Yayi min tambayar a sanyaye idanuwanshi kuma suna kafe a kaina. Na kawar da kaina daga kallon da yake yi min kafin na soma ce mishi Babana yayi nufin aurar da ni ga wanda yayi niyyar bada ni gare shi bana zaton akwai wani dalili da zai hana shi yin abinda ya shiryan in dai ba wata kudura ba ce ta Ubangiji. Ban ki auren don raina maganarshi ko bijirewa umarninshi ba, naki auren ne a dalilin sanin dalilin kulla shi da aka yi a yanzu ina cikin wani hali da ba zai fadu ba, don haka nazo wurinka in roke ka kayi min wani alheri tunda

Chapter 6 of 7