Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
don na daina ajiye su a ko'ina sai a bakin zanin da ke jikina, na zaro abinda zan ba shi ya tafi yaje ya sayo mana. kananzir, na rasa inda zan sa risho din saboda iskar da ke kadawa. Na wuce naje na kai shi dakina da nufin yin girkin, à can nan ma ta biyo ni dakin ai ba naki ba ne ke kadai, don haka ba za ki yi girki a ciki ba, balle kije ki rine mata kayanta da hayakin risho. Don haka ha koma cikin zaure na sa-shi a lungu tunda ni dai nasan kawai zan yi girki ina bukatar cin abincin, ga Isiyaku ma yana bukata, don tunda Mubarak ya hada ni da shi wurina yake zuwa ya karya ya kuma ci na rana, abinda Mubarak din ya gaya mishi ke nan nima ko ban yi niyyar saye ba in yazo sai in ba shi. Shiga wurin Babah Sumaye ka ce wai ta bani wuka da ludayin miya da kuma kwanukan cin abinci, ya ce to. Kai yau ga wani abin dadi, girkin ma a zaure a ke yin shi? Alamar dai ke nan da girkin ba na 39 tsayawa yaci. Na waiwaya cikin murmushi na Darowata ba ae mai wucewa a hanya ma zai iya kalle shi, manya-manyan edoji ne guda biyu a hannunshi a cike da cefane. Na rike baki na ce kai Mansur wacce irin hidima cekwannan? Ya yi maza ya daure fuska alamar bai son maganar tawa, in wanke hannu dai kawai kenan in yi shirin yankan attarugu da albasa tunda nasan zafinsu ai kin ga ba zai yiwu in bar ki ki taba su ba. Nayi murmushi na ce ai an riga an yanka su, sayayya sosaiaMMansur yayi na kayan tea daya ledar kuma kayan ciki ne wanda hanta yafi komai yawa a ciki, ga kuma a gada nono guca mai kyau da ita. Isiyaku yana ganin ledar kayan cikin ya sure shi ya shiga gidan Babah Sumaye yaje ya wanke shi tas ya kawo ya nuna min. ina, dubawa yana yi min magana naga gaushin da Babah Sumaye ta sauke girkinta ko can zan kai wannan? Na ce to kai Isiyaku in babu abinda zata dora a kai. Ko akiwai, ma ai naga wani kurfon buhun gawayi ne kuma da ita zan hura wata wutar, na ce mishi to. A zaure na soya agada na hada mana tea muka sha ni da Isiyaku bayan tafiyar da Mansur yayi a kan zai je gida ya dawo. 40 Sai da muka koshi sannan muka zaune yin girkin dafa dukan taliya mai hade-haden kayan lambu a ciki nayi mana na zubawa Mansur a karamin food flask na zuba mana namu ni da Isiyaku saura na juyewa almajirai da suka zo wucewa su biyu. Farfesun kayan ciki yayi Isiyaku ya shiga ya fito da tukunyar na zuba mana namu ni da shi, na zubawa Mansur da Babah Sumaye na hada baiwa Isiyaku duk yakai musu ya dawo. Muka hadu muka gyara wurin ya kuma yayi mana wanke-wanke ya kife ya dawo. Wai dan girkin nan da nayi naci sai ya haifar min da wata irin natsuwa da na dade ban samu irinta ba, damuwa tayi min sauki naji dadi cikin raina, don haka da na shiga gida ina ajiye kayan tea na' da sauran abubuwan da na shigo da su, sai kawai na wuce na shiga wanka don in kara jin dadi. Na fito daga wanka ina shafa mai na lura naga kamar an taba kayan da na ajiye, na mika hannu don jin ko da gaske ne an taba sai kawai naji an juye babu komai a ciki sai gwangwanayen aka bari. Cikin zuciyata na ce iko sai Ubangiji, na ci gaba da harkokina. 41 Washegari da safe ina kwance kan shimfidata ban motsa na tashi ba saboda nasan ko na tashin bani da wani abinda zan ci na kuma daina aikin Babah Lantana tunda ko nayi bani da rabo cikin abincinta. Jiran shigowar Isiyaku nake yi don in ba shi ya sayo mana abinda zamu karya dashi. Jimawa can sai gashi ya shigo rike da kwano mai shake da waina da wani kwanon kuma, miya ce da kashi da man shanu, cikin fara'a ya ajiye kwanon yana murmushi. ""Yaya Mansur ne ya bani wai in kawo in na gama kuma in je in same shi na ce mishi to." Wajen karfe goma sha daya da rabi na safe sai ga Isiyaku ya dawo dauke da cefane niki-niki har da kaji da kuma busasshen manya-manya. A.zaure rannan ma muka yi komai muka ci na zuba na Babah Sumaye da na Mansur na aiki Isiyaku ya kai musu na zuba mishi na Almajirai yaje suma ya kai musu. Sauran kayan kuwa gaba daya na sa shi ya diba yaje ya kai wa Babah Sumaye ya ce ta ajiye cefane ya zamo mishi wata ka'ida da ya dora wa kanshi kullum sai yayi ko da kuwa na jiyan bai kare ba. Kullum muka yi kuma zan zuba a kai mishi sannu a hankali kuma sai Mansur ya maida zauren gidanmu wurin hirarshi. 42 Rannan iną tare da Mansur a zauren tare da Isiyaku, muna hirar ne ina yi mana girki sai ga Babah Lantana tana ganin Mansur ta soma zagi da fadin lalatattun maganganu irin wadanda ta saba yi wa Mubarak. Nan da nan Mansur ya maida wukar da ke hannunshi wacce yake yanka min albasa, da ita ya daga ido ya kalli Babah Lantana cikin natsuwa ya ce mata ai ki na ambaton sunan 1yayena a cikan maganganun naki za ki gane kin jawa kanki matsala don ba zan bari ki zagan mun su ki kwashe kalau ba, zan gwammace in biyo ki har cikin gidan in sa dorinata in yi miki dukan tsiya. In yaso duk abinda zai faru bayan hakan ya faru zai fiye min sauki a kan kiyi wa iyayena zagin wulakanci irin wanda ki ka saba yi wa mutane suna kyale ki, kin taba ganin na shiga lamarinki? Kin taba ganin na buda bakina na gaya miki wata kalma ko da kuwa ta gaisuwa ce tunda ki ka zo layin nan? Kin taba ganin,na shiga harkokin da ki ke yi? Kin taba ganin na shiga harkar 'ya'yanki? Amma shi ne ki ka zo kina zagina har kina ambaton sunan ubana? To sake fadin kalma guda daya ki ka ga ni? In ma nayi mata ciki sai me? Ina 43 ruwanki ai ba zan barta tayi ta yawo da shi kamar yanda a ka barki kina yawo da naki ba. Ban san yanda a ka yi ba sum-sum naga Babah Lantana ta juya ta shige gida ta bar shi yana fadin haka kawai mata kin zo unguwa kin samu mutane kin tasa su a gaba suna kallonshi sun kyale ki? Ai karyar iya shege ki ke yi. Na shiga gida don taba ruwa sai kawai naji Sallau yana cewa Babah Lantana na rantse miki Mama in ki ka sake jawo wata fitina ta same ni sai kin gaya min inda Babana yake. Tunda na ce zan shiga duniya kin ce namiji don ya shiga duniya ba komai ba ne, ga maigidan nan ma ai shiga duniyar yayi ya bar danginshi da bai samu yanda ya ke so ba. Kuma ya bakura ya yafe su to na fasa shige duniyar tunda don na shiga bai dame ki ba, zama zan yi a inda ki ke iyaka in tara miki Jama'a su rokar min ke ki nuna min in da ubana ya ke, a to. Ya fadi a to din tare da gyada kai nuna alamar da gaske yake yi zai iya aikata abinda ya ce din. Rannan dai jikin Babah Lantana a sanyaye ya wuni saboda rasbhin mutuncin da Mansur yayi mata ga kuma kalaman danta wanda ko gama warkewa bai yi ba, yanda ta wuni jiki a sanyaye haka Sallau ma ya wuni yana mita ba fa gama warkewa nayi 44 ba har yanzu din nan ji nake kamar kasusuwan jikina Agogo ce suke kuma wai kina sake shiga sabgar wani saboda ba ke suke yi wa ba. Ina jin su babu uwana takura ta dai tayi matukar raguwa, gashi abin da nake so shi nake ci na rabu da yunwar da ke yawan damuna a yanzu kuma ina da yann hira ga Isiyaku ga 'yan Almajiraina guda biyu wadanda in ba wani muhimman abu za su yi ba basa barin gidan, sannan ga Mansur abokin hira mai dadi mai fadin kalamai masu dadi mai barkwanci, mai sanya zuciya taji tanfar a kan gajimare take yawo, saboda dadadan kalamanshi, ga shi kuma da yawan alheri. Tun daga ranar da Babah Lantana tayi haka da Mansur nima bata sake shiga harkata da yawa ba balle Mansur din iyaka dai kullum zan ji ta tana cewa Babana wannan yarinyar fa ba a rabu da bukar ba wancan ya tafi ne wani kuma ya mayye gurbinshi. Ta kwashe bayani na karya da gaskiya tayi mishi, rannan har tana yi mishi rantsuwar wai ta ganshi ya matse ni a lungu in banda ta shiga zauren da bata san abinda zai wakana ba. Yana jin ta tayi shiru bai ce mata komai ba, takaici ya kamata ta ce koda yake dai kai dama irin wadannan ba su dame ka ba, ba ka tsoron shege ta 45 kalle shi ta tabe baki tare da mikewa ta nufi dakinta tana tafiyar tana magana a hankali sai dai hakan bai hana a ji ta ba, don rage muryar na iya shege ne. Wa yasan abinda kayi ne ma Mallam kafin ka baro gida nake damun kaina a kan 'yarka? A zuciyata na tabbatarwa kaina raini ya kai duk inda yakai tsakanin Babah Lantana da Babana, tunda har zata iya furta mishi irin wannan maganar a kan idonshi, bai iya ce mata komai ba, na gaji da irin wadannan kalaman na tozartawa da take yi mishi, koda a bayan idonshi ne balle kuma abin ya kawo kan idonshi. Raina ya kai matuka wajen 6aci jikina har yana rawa na gaji da irin wulakancin da a ke yi wa Mahaifina a kan idonshi, a kan idona saboda raini da tozartawa. Ban san yanda aka yi ba sai kawai ji na nayi na bude baki ina cewa Babah Lantana, Babana ko ya baro garinshi da danginshi ai kuma bai yi kama da wanda ya aikata abin kunya ba. Don kuwa bai da wata alama ta rashin mutunci a tare da shi. Tana jin haka ta zabura ta mike da ke nake ko kuwa rashin kunyar taki ta kai ma za ki zage ni nc? ko ba da ni ki ke ba ai cin mutuncin mahaisina kia ke yi a gabana da kuma 'ya'yan da ke da su ya rufa muku asiri. 46 Ta shiga zage-zage tana dura min ashar, ni kuma ina daki ina fadin a'a haka kawai kullum sai kin wulakanta shi yana kallonki don kawai kin ga baya yi miki magana? Ana cin arzikinshi ana kushe shi? Babana in mutumin banza ne zai rike miki 'ya'yanki ne? Asabe tasa kafa ta taka min shimfidata kamar yanda ta saba yi kullum, maimakon .in karkadeta kamar yanda na saba sai na kalleta na ce mata gaskiya wannan wulakancin ya ishe ni haka ke ki taka min shimfida sannan a zagar min ubana ina ji, ya isa haka. Da sauri ta mike ta zauna a tsakiyar gadon, ke yarinya ina ganin fa wani abu yana yi miki yawo a kai, ni sai in sauke miki shi bari kiji in gaya miki na harareta na ce kai haba yarinya ai tana bayan uwarta. Ta zuba min ido, to ba zan daina ba yi abinda za ki yi ta sake tattakawa, na fita naje na tsaya a kofar dakin Babah Lantana don rabon da in shiga dakin har na mance da lissafin tun dai ranar da ta mare ni a kan na taka mata sabuwar ledarta. Naja na tsaya daga waje na ce Baba ya amsa na gaishe shi kafin nayi mishi bayanin abinda ke faruwa na taka min shimfida da Asabe ke yi kullum. 47 Kan ya ce komai sai kawai naji Babah Lantana ta karbe maganar, ai nan karar Asabe ki ka vi wurin ubanki ke nan ga mai uba ko? Aiya sannu mai uba yiwa wacce bata da uba wulakanci. Dadin abin shi kadai gare ki na juya zan koma dakin saboda jin shi Baban nawa bai ce komai ba. Sai naji tana cewa kai ku kam da kuna da wani asali ba a san irin iya shegen da ki ka yi wa mutane ba. Na ce uba ai shi ne asali Babah, ai ni da asalina a ka ganni tunda a gidan ubana aka ganni wanda ya rasa uba ai shi ya rasa asalirishi. Gari na wayewa nayi duk abinda na saba yi na yau da kullum dina, ia jira Babana ya fita sai kawai na leka na kira Isiyaku tare da yan Almajiran nan dama na gaya musu kar suyi nisa. Gaba daya kayan dakina na fitar da nawa da wanda ba nawan ba na share dakin tas na cire cinyayyar ledar da ke ciki na wurgar da ita ina aikin Babah Lantana tana jaddada min in dai hankali da kayan Asabe don ita duk kayanta masu tsada ne. Ban tanka mata ba na dauke yar shimfidata daga kasa na baje ta karkashin katifar da ke kan gadona sannan na maida katifar akai na jawo wani tsohon zanina na shimfida na gyara komai na maida kayan na ajiye kofar dakin ma na sanya 48 mishi sabon labulen da Yaya Dijah ta bani sanda ta gaya.min abinda zan yi ban iya ba, sai yau na kunna turaren tsinke. Nayi wanka nayi kwalliya suma su Isiyaku na ce sujeisuyi wanka su dawo na ba su kudi na ce su sayi sosa da sabulu na mika masu kwalbar Vaseline din da, dama yake boye cikin kayana bana amfani da shi. Daidaddare ina idar da sallar Isha'i na dare kan gadon nayi kwanciyata gabana sai harbawa yake yi, Asabe ta shigo ta ganni kan uba' abinda ta fara fadi ke nan kafin taci gaba da cewa, ai kema kin san ba zai taba yiwuwa ba k ce za ki dawo da kwana a gado. Za ma ki fito da shimfidarki duk inda ki ka kaita ko kuma ki san nayi saboda ba za ki hau gadona ki matse ni ba. A lalace na kalleta na ce mata kuna da gado ne a gidan nan? Ai duk wani gado da yake cikin gidannan in ba ki sani.ba in gaya miki na Innata ne, na sake kallonta na ce ina ce wannan ne ki ke cewa naki? Kan ta bani amsa na ce mata ba ki da kyau ba, don kuwa wannan gadona ne da na gada a wurin mahaifiyata, kin kuma san kayanta ba zai zamo na baitilmal ba, tunda tana da magada. Kace-nacen da muka fara yasa Babah Lantana fitowa tana tambayar Asabe menene? Ta tsaya 49 tana yi mata bayani, nima ina daga kwance ina mita tare da kunkunin da ake iya jiwowa. Haka kawai ni da gidan ubana an zo an takura min, in gaskiya ne abinda ake fadan kowa yaje gidan ubanshi ya zauna mana, wannan gadona ne da uwata ta mutu ta bar min a ka zalunce ni aka kwace min shi a ka maida ni kwanciyar kasa ba kuma zan sake yarda da hakan ba, sai dai duk abinda za ayi ayi amma ba zan sauka a kai ba." To ai sai ki gyara ku kwanta tare ko? Na ce a'a ba mai sake hawa min kai ai bata da gadonta balle ta ce ana ta kason take hawa, Hankalin Babah Lantana yayi matukar tashi, bata saba ganin ina yi mata rashin mutunci irin wannan ba, wata kila kuma bata taba zaton irin wannan ranar zai zo ba. Ni ki ke gayawa wadannan maganganun? Na ce oho, ni dai na gode ina da uba kowa ya san shi dangin uban ne kawai bani da su, yana kuma sona tunda ko unguwa bai barina in je balle yaje ga bada rikona wurin wadan su in je ina zama agola, sai dai a kai mishi karata ya yi min duka amma ba ya tura ni gidan wasu da sunan riko ba. Da sauri Babah Lantana ta juya wurin Babana da ta bari a daki tana yi mishi magana irin wacce ta saba, wato kana jin rashin kunyar da 'yar iskar 50 yar nan taka take yi wa mutane: amma kaja bakinka kayi shiru, kayi wani shememe a kwance kamar gawar sababi ko? To tashi ka bani wuri don a kan ka abin'zai kare tunda kai ne ka rasa abinda zaka haifa a duniya sai tyar iska. Tashi ka gani in sauke katifar inibáiwa Asabe ita kai ka san nayi, don ba zai yiwu,ita tana gado Asabe tana kasa'ba. Ina jin haka nayi maza na yiwo waje don nasan abu ne mai sauki Babana ya sauka a gadou Babah Lantana ta dauki katifar ta baiwa Asabe ita. Dakin na shiga na kara kallon katifar da Baban nawa ke kwance a kai sai da na fito tsakar gida sai na ce mata, Babah in dai wannan katifar ce to ba taki ba ce ta Innata ce, don haka ko kin fito da ita zan karbeta. Shiru tayi bata tanka min ba, ina shiga dakina na gane hikimar da Babah Lantana tayi min saboda ganin Asabe da nayi kan gadon a kwance ta babbake ko'ina. Ki bani gadona na fadi hakan tare da kokarin janye katifar da ke kan gadon ban san yanda a ka yi ba sai ganina kawai nayi muna wani irin dambe ni da Asabe, danbe mai tsanani irin nà kwatar kai. 51 "Dake ta Asabe, bugi ja'ira kar kiyi mata da wasa. Abinda Babah Lantana ke gaya mata ke nan. Sallau ya dogara sandarshi da yake dindingisawa ya fito daga dakinshi kwanaki tara da yin abin har lokacin bai gama warkewa ba. Babah kenan, za ki kara ba Mama? Iyaye suna yiwa ya'ya tattalin abin arziki suna gudarwa ya'yansu fitina amma ke kullum cikinta ki ke jefa su. Babah Lantana tayi maza ta juya gare shi ta kafa mishi wani gigitaccen mari kau! Tanfar ba shi ta gaurawa irin wannan marin ba, bai motsa ba daga yanayin da yake, ni kam ko sau nawa za ki maren ai zan gaya miki gaskiya tunda dai an ce min uwa ta kwarai tana yarda da shawarar ya'yanta matukar su din sun kai munzali na mallakar hankali. Ke Asabe in kin yarda ki bar fadan nan, fada ne fa na rashin gaskiya yarinya tana zaune a gidan ubanta mun zo mun kankane komai ai da gaske ne kowa a nuna mishi gidan ubanshi mu tafi mana. Sallau ne yasa sandarshi ya raba tsakanina da Asabe muka rabu da yake daga ni har ita babu wanda yaji alama na dukanmu muna son rabon da a ka yin sai dai hakan bai sa na yarda da mu kwana 52 mu biyu a kan gadona ba, bałe aje ana fito da katifar Babana a bata shi a bar shi a kan wayar gado. Duk abinda ke.faruwa Babana yana daki yana jin komai amma bai ce uffan ba, har a' ka yi aka gama ina jin ko shi. ne abinda yafi 6atawa Babah Lantana rai ta shiga-daki ta figo gýalenta ta fito tana fadin zo Asabe. fito nan yau, kam in kai ki gidan uban nan naki da kullum:a ke yi min gorinshi. Ta tasa ta a gaba suka fita suka bar gidan, naje na kulle kofar gida nazo na ihau gadon.na/kwanta, tausayin Babana yayi matukar kama ni, babu abinda yafi komai tsayawa a raina irin kifin nan da Babah Lantana ta jefawa laya abaki ta daure: da zaren ilo tasa a ka je aka jefa a rafi, awai yan uwanshi su cinye shi a haka. Zuciyata ta raya min acewar wata kila yi tayi don ta daure bakin Babana komai tayi kar ya ce mata komai, tunda ga skir a yariza ko ne, za'ayi a gabanshi ba zai bude bakinshi ya ce don me ba? To amma yayi ta zama a haka ke nana? Wannan shi ne abinda yafi komai damuna. A haka har gari ya.waye na tashi nayi sallah naje na gaida Babana, na kama hidimomin gida na Byara gidan tsaf lungu-lungu duk inda ya dade ba 53 a gyara ba ma na gyara shi komai yayi tsaf Babana ya fito daga daki yasa hannu ya dauki kwandonshi, kasuwa yake nufin tafiya, nayi maza na' 'ce mishi "Lah, Baba har za ka tafi kasuwar ba ka karya ba?" Cikin' natsuwa ya kalle ni ya ce min da wani abu ne a gidan? Na ce mishi eh Baba, ya ce min to ya nemi wuri ya zauna a kan shimfidar tabarmar shi na kawo mishi lafiyayyan abin karyawa ya karya abinda ya dade bai samu hakan ba don tuni Babah Lantana ta daina ba shi abin karyawa yaron nan ba yana nana a ciki ba? Na ce eh Baba, ya ce to ba shi mana ko babu ne in rage mishi a nan? Na ce akwai na diba naje na kaiwa Sallau na dawo na zauna a gefenshi, gabana ya fadi, ganin yadda wuyan rigarshi tayi dikin- dikin. Baba wannan rigar taka ai tayi datti ka canza wata mana, ya sunkuyar da kanshi ga rigar alamar yana kara dubata, ai duk rigunan nawa masu datti ne, na ce to bani in wake maka su. Ya ce To kafin .ya sake cewa ko ki bari sai gobe saboda sabulu. Na ce bani kawai Baba akwai sabulu, ya ce to. Isiyaku ne ya wanke min kayan ya goge su inaa kallon yanda suka tsufa suka zama 'yan fake-fake saboda jin jiki yayinda zuciyata ke tuna min da 54 dadewan da nayi ban ga Babana da sabon dinki ba ko da kuwa da sallah ne. Komai nashi a hanmun Babah Lantana yake, ita kuma bata da adaloin cewa shima ya yi wa kanshi don a gha mijinta fes ta kanta da 'ya'yanta kawai take yi ko ni ma da zaninshi nake jira in daura to da yanzu ta kai ma ba ni da na daurawa don tun sallar farko da Babah Lastana tayia gidanmu bata sake sawa an yi min sabon dinki ba Rannan a kicin nayi girkina ban je zaure ba, muka zauna tsakar gida muka yi hidimominmu na zuba a kwano na baiwa Ísiyaku ya kai wa Mansur, ni kuma na dauka da sauri naje na kaiwa Babana, na zauna na tsare mishi tumatirinshi ina yi mishi cinikin, yayinda shi kama ya koma dan lungu yaci abincinshi saboda Babana mutum ne mai kunya. A hanya ina rike da kwanon abincin da na kai mishin ina tunanin daga yau in dai zan yi girki to kuwa zan zuba in kai mishi sannan ba zan sake barin Babah Lantana da wankin shi ba, balle yaje yana yawo dikin-dikin. Yana dawowa da yamma naje na wanke bayangida na kai mishi ruwan wanka yayi ya fito na kawo mishi wankakkun kayan shi ya saka yana tayi min addu'a, naji dadi cikin raina har ina 55 tunanin ashe dai in ban da Babah Lantana da Babana bai canza min ba. Kwana uku da tafiyar Babah Lantana sai ga ta ta dawo, tsofaffin kawayenta suka dawo da ita, su Delu da sauran su. Suna kallona ina kallonsu ban ce musu kala ba sai gyada kai suke yi nuna alamar mamaki, in gumu ta gumu kuma su juya suyi kus- kus din su. Wata kila don a kaina suke maganar yasa suke yin kus-kus din don daga baya naji su suna cewa ai dan halal bai manta mafari, to ita Lantana da ta samu fili ta mike kafa sai ta ce babu shegiya sai ni, Ummm in banda dai hannunka bai rubewa yanke shi ka yar kuma Hausawa suka coe wai naka sai naka yaushe zan sake shiga wannan maganar? Ko ni cikin zuciyata na yarda da maganar Delu cewar da sa hannunta Babah Lantana ta samu yin abubuwan da ta yi wa Babana, don haka na kudurawa raina wannan karon ba zan taba yarda in ga za a sake yi mishi wani abin in zuba musu ido ba, sai dai ko suyi a boye amma ba kiri-kiri ba irin na da. Suka fito suka wuce ni a tsakar gida ina jin Delu tana fadin lalle wannan yarinya ta rike, ita kuwa Babah Lantana fadi take yi, ai ta wuce duk yanda ku ke zato, ni kuwa na bisu da kallo a 56 zuciyata na ce duk sun kode sun yamutse babu wata mai kyan gani a cikinsu in banda Babah Lantana saboda ba su sake samun wani mai tsautsayin a ka ba da zai kwashe su a matsayin aure ba. Washegari da safe na shiga kicin na koma can lungu ina aikina na bar wa Babah Lantana nata wurin da na tabbatar zał isheta, tana isowa sai taja ta tsaya daga waje, to fito ki bani wuri ko? Don ba zai yiwu in zauna ni da ke a ciki ba ga kuguna ga naki. Mai wuri yazo sai mai tabarma ya nade, nayi kamar ban ji ta ba, ina ci gaba da aikin da nake yi Ko ba ki ji ni ba ne? na ce ki dauki kayanki ki koma zaure ina ce dama a can ki ke aikinki? Na ce gaskiya ba zan rinka girki a zaure ba, bayan ga kicin a gidanmu, iye? Nayi shiru ko kallon in da take ban sake ba, to ba ri yazo ya raba wannan fitinar don na gaji da rashin kunyar da kike yi min ta ju ya ta tafi ni kuwa nayi girkina na zuba na zuba yanda na saba, naje na kaiwa Babana wurinshi na dawo da kwanukan sannan na zauna naci nawa yara ma suka ci nasu suka watse. Kwana biyu a jere Babah Lantana bata girki . bata baiwa Babana komai sai in ya fita tasan abinda taci ta baiwa Sallau, wai ba za ta sake yin 57 girkin ba sai ya raba rigimar da ya hada ya hana ni shiga kicin don yin komai tunda ai kicin na matar gida ne. Ni kuwa komai nayi in zuba da yawa in kai mishi ko mai fura da nono mai kyau na gani sai na saya na kai mishi ko ta lura ta gane bai samu matsalar da take so ya samu ba ne, tunda in dai don yayi magana tayi hakan ai tasan ba zai yi ba saboda ita tayi mishi wannan sanadin. A karin banza ga koma shiga kicin din tana yin girkin ga kuturin nawa ga natan. Gaba daya al'amura suka cakudewa Babah Lantana saboda ta gane kwata-kwata na daina tsoronta, ya' yanta da take sawa su azabtar da ni kuma ta gane ba zai yiwu ba saboda su dukansu sun tsorata da abinda ya samu Sallau. Rannan ina zaune a dakina sai ga Asabe ta dawo har da Jakarta da dah ta tafi da ita a kan za a kaita gidan ubanta ita ma. Ina ganin ta na daga hannayena duka biyu sama

Chapter 3 of 7