Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
ga shi yayi wani irin kala. Amai a -daki? Asabe tayi tambayar cikin wani yanayi na nuna tsananin kyama, to na rantse sai dai ki kwashe ke da kanki, don ni bana taba amai. Ina kwance ina jin ta ko daga ido in kalleta ban yi ba, cikin zuciyata dai fadi nake yi dadin abin ma a kan kayana nayi. Babah Lantana tana jin Asabe tana ambaton sunan amai ta rugo a guje, amai? A nan gidan yau'? Uhum, abinda na gudanwa Mallam ke nan abinda na gudanwa Mallam ke nan, abin da na gudanwa Mallam ke nan, bai gudunwa kan shi ba to tunda bai gudanwa kan shi ba kuwa ga shi nan ya same shi. Ni kuwa babu wanda zai zauna ya renan min cikin shege a gidan nan yauwa, don mu abin kunya 20 gudun shi muke yi saboda ba mu gaje shi ba, su dai ina jin suna da gadonshi shi yasa nake tayi mishi kashedi bai ji ba. Sannan al' amarin Mallam ma ai in ka duba akwai matsala, mutumin da bai da dangi Mallam fa ko sunan garinsu bai kira balle ya ambaci wani dan uwa nashi, wa ya san abin da yayi ya bar gidan? Duk da tsananin ciwon da ke damuna sai da na zubawa Babah Lantana ido ina kallonta. Ta ce, Eh kalle ni da kyau ko. karya nayi muku? Ana barin gida haka kawai ne?. ai yawanci abin kunya a ke yi a tafi in kin ga dama ki gaya mishi kema kin san a tafin hannuna yake. Ta muno min cikin tafin hannun nata, ta juya tana tafiya tana gayawa Asabe tafi can wajen tumatirinshi ki kira min shi yazo ya gani da idonshi kar ya ce karya nayi mishi, daganan kuma sai ya kwashe donni da hannuna ba zan kwashe aman cikin shege ba. Ina kwance ina jin shigowar Babana da irin maganar da Babah Lantana ta tare shi da ita, ai babu abinda ban gaya maka ba kan ciwon da yarinyar nan ke yi ba haka kawai ba ne, ciwo kwana da kwanaki kuma mai zafi haka ai kowa ma yasan menene sai dai a yi shiru. Da sauri Babana ya fadi cikin dakin jikinshi sai rawa yake yi, me ya same ki Yacuuwuna? Me ya 21 same ta ko me ya same ta kai nan sai an gaya maka abinda ya same ta? Yasa hannu ya daga ni a'a har da amai ki ka yi? Yasa hannu ya nade ya fitar ya dawo, Babah Lantana tana fadin ai gara kaga aman da idonka, kar ka ce ko sharri a ka yi mata. Tashi muje in kai ki asibiti, yasa hannu ya daga ni yana rungume da ni a jikinshi muka fito daga dakin za ka kaita a cire ne? ai binka zan yi don ba za ku ce ku dawo kayi min karya ba tunda dai wannan ciwon nata ai kowa ya ganta yasan ciki ne da ita. Ina jin irin lkaduwar da jikin Babana yayi sanda Babah Lantana ta ambata.mishi cikin nan ya dan ja ya tsaya na yan dakiku bai motsa ba, kafin ya ci gaba da tafiya. A asibiti a gaban Babah Lantana da Babang Likita ya gama duba ni ya gaya musu cewar maleriya da yunwa ne suka kama ni. A ka sanya min ruwa saboda ramar da nayi tayi yawa, a ka hada min da magunguna a ka sallame mu, Likita yana dada jaddadawa Babana lalle ne a kula da abincina don na rasa nauyi mai yawa a tare da ni. A gida ina jin Asabe tana tambayar Babah Lantana me Likitan ya ce? Ta tabe baki ta cc bai kai ta wurin wani asibiti na gaske ba, can wurin wani 22 dan iska ya kaita da bai ma iya aikin nashi ba, wai ciwon sauro ne da yunwa. Har yana wahi daura mata ledan ruwa in ma hada baki suka yi ya boye ai shi ciki dan duma ne muna nan sai ki ga ya fito mun gan shi da idonmu. Washegari Babana ya kawo min 'yan abubuwan ciye-ciye da yake ganin za su taimake ni. a gabanshi Babah Lantana ta rabe komai ta bani.abinda take ganin shine daidai a wurinta, tana yi kuma tana fadin "In dai cizon sauro ne lalurarta to wanene mai lafiya ne a cikin gidan nan ba gara ita ba ma tana fita ta sha sharholiyarta a waje, mu kam ai kullum muna ciki muna tare da saurayen. Inda na samu kulawa ta sosai-sosai daga wurin Umma ne da danta sai ko Yaya Dijah da mijinta, kusan kullum sai tayi min aike, kusan kullum din kuma zata ce wa dan aiken ya gaya min in naji sauki in zo tana son ganina in ce mashi to. Na soma jin sauki ke nan Mubarak ya zo yayi min sallama kan za su tafi Umra shi da Babanshi, nayi addu'ar Ubangiji ya dawo da su lafiya,; ya kuma sa suyi aiki karbab6e. Ya ce, To amin. Ban yi miki sayayya ba saboda sanin yanda gidan naku yake da nayi don haka ungo wannan ki rike a wurinki ki adana kar ki bari su gani, balle su kwashe miki duk abinda ki ke so ki saya kar ki yarda ki zauna Cikin damuwa. 23 Na gayawa Isiyaku kullum da safe yazo yaje miki aika ko wankinki ne ya taru ki ba shi zai yi miki, na ce mishi to. Lokaci mai tsawo ya dauka yana yi min kalamai na bada hakuri kan tafiyar da zai yi a cikin dani din ko wadatacciyar lafiya ba ni da itana ce mishi a'a babu komai. Na dawo daki na kirga kudin da ya banin Naira dari ne cif wato fan hamsin ke nan, a wancan lokacin kuwa mafi yawancin sadakin yanmatan unguwarmu da a ke aurarwa ma bai wuce tan goma wato Naira ashirin, in yayi yawa a karbi arba'in ko hamsin da kyar kwarai za ka ji an bada sadaki fan hamsin Naira dari ke nan. Mamaki ya kama ni, na in da Mubarak ya samu irin wadannan kudin ya kuma iya bani su, ganin kimar kudin da yawansu ya sanya ni tunanin in kaiwa Babana su sai naga to ai in na kai mishi ma wurin Babah Lantana zai dawo da su. To ko in kaiwa Umma ta ajiye min? nayi maza na canza saboda tunanin anya ya gaya mata zai ba ni irin wadannan kudin? In bai gaya mata ba ke nan na hada su, don haka na mike da sauri na fita na bar gidan ba tare da na gayawa kowa ba. Na tafi na kaiwa Yaya Dijah kudin da sauri na dawo nazo na boye Naira goman da ta bani ta ce in rike a wurina, saboda bukatuna. 24 Kamar yanda Mubarak ya gaya min cewar Isiyaku zai rinka zuwa min aika hakan a ka yi, da sassafe ya shigo ya gaida Babah Lantana kafin ya zo in da nake na dauko kudi na bashi, na gaya mishi abubuwan da zai kawo min yaje ya kawo ya karbi wankina ya fita da su. Ba a wani dade sosai ba sai gashi ya kawo min su a goge, dadin hakan yasa na mike'da nufin in je in yi wanka don in kara jin dadin jikina. Naje kicin da nufin in sanya ruwan da zan yi wankan da shi a risho don ya dan kore sanyinshi tunda ba gama wartsakewa nayi ba. Babah Lantana tayi maza ta ce min kar ki shigar min wurin nan ba ki da komai a ciki in dai ba tsamar min naman miya za ki yiba. Na dawo da baya nasa hannu na dauki bokitin robar da ake wanka da shi, nufina in tari ruwa a bakin famfo in je in yi wankan a haka, nan ma ta ce a jiye min bokitin nan tunda ba uwarki ce ta saya min shi ba. Na maida shi na ajiye na wuce naje na dauko wani bokitin karfe da ke can gefe na tara shi ina duban ruwan ta bar abinda take yi ta mike ta tsaya tana kallona wai ba nace kar ki taba min wani abina ba ne ko kina nemana ne da magana'? A hankali cikin natsuwa nace mata wannan ai ba naki ba ne kin ga ni? Bokitin Innarmu ne, abinda 25 kawai na fada kenan ta takarkare ta wanke ni da marin da nayi matukar kaduwa. Ba na ce ki daina ambaon min sunan shegiyar matar nan a cikin gidan nan a? ban san lokacin da na buda baki na ce wa Babah Lantana "Gaskiya Innarmu ba shegiya ba ce. Sai kawai ta rufe ni da duka. "Ai dama na gane talke-takenki nema ki ke ki fara zahina kiri-kiri, bayan na bayan idon da kike yi ana gaya min ba ki kuma isa ba don ni nan ko uwar taku ma da tana nan din ba za ta buda baki ta zage ni in kyale ta ba, to balle ke banza a banza. Duka iin wanda Babah Lantana tayi min bai kwatantuwa don kuwa yi tayi sai da ta gaji ta bari don kanta, babu wanda ya shigo gidan don kawo min agaji, duk da irin ihun da nayi ta kurmawa. Asabe ma tana daki a zaune ba ta ce mata komai ba. Ina zaunc a tsakar gida bayan matsanancin dukan da Babah Lantana tayi min ban sake komawa dakin ba saboda abinda nake tsoro wana ke kara sa ni zaman nakin ya faru, don haka ina zaune ne kawai a tsakar gidan amma ban iya daina kuka ba. Ita kuwa Babah Lantana tana ta kai-kawonta tare da fadin "Haba an ce miki ni ina tsoron wani ne? Ni fa da ki ke ganina bana tsoron kowa ina kyaleki ne kawai kina iskancin ina kallonki, amma ba don tsoro ba. 26 Yi ta zama a nan har uban naki ya dawo yazo ya same ki in ji abinda zai ce, ina ce zaman da ki ke yi a wurin ke nan, in kuma shi wancan dan iskan ne ina nan ina zaman jüran dawowarshi in ga abin da zai yi ko ni ma zai zo ya kirba min naushin ne?" Sallau yana shigowa gida ya ganni a zaune yayi turus ya zuba min ido yana kallona, cikin tsananin kaduwa ya juya inda Babah Lantana ke zaune tana sakucen naman da taci da tsinken zaburin shara. "Dukanta ki ka yi Babah, me tayí miki? Ba ta ma fa gama warkewa ba sannan in za ki buge ta ma Babah wannan wane irin duka ne? Da sauri Babah Lantana ta mike ta kifa mishi mari mai tsananin karfi ta sake kifa mishi wani. marin har sau uku da ya tsaya wata kila da abin yafi haka. Juyawa yayi ya fita, ya barta tana fadin, sakarai matsoraci, shashasha kai kam in ba sa'a nayi rakiya kayi wa maza zuwa duniya don duk wata harkarka ta tsoro ce, na bugeta wanda duk ke da abin yi yazo yayi ina nan ina zaman jiranshi, aikin banza aikin wofi, ni za a kawowa iya shege? Ina zaune a daki cikin matsanacin hali don wani zazzabin ne ya sake rufe ni, ga 6acin rai don na fara gajiya da irin wadannan al'amuran naji dawowan Babana da bayanin da Babah Lantana ke yi na nayi 27 mata rashin kunya itama kuma tayi min hukuncin da ya dace da ni. Sau dubu kuma in zan mata to sau dubu itama zata yi min in ina son zama lafiya to in kiyayeta gara tun wuri ya jaddada min in ba haka ba kuwa to ita babu ruwanta bai ce matakomai ba. Washegari da safe tunda na tashi da kyar nayi sallah na koma na kwanta saboda tsamin da jikina yayi ina jin sanda Asabe ta sauko daga kan gado ta take min kafata ban ce mata komai ba. Ta dawo dakin tana sallah na ji Babah Lantana tana ta kwala mata kira, cikin wani yanayi kamar dai wani abu ya faru, da sauri ta:sallame ta fita sai naji tana ce mata yi sauri ki tafi gidansu Delu ki gani ko a can Sallau ya kwana bai dawo gida ba jiya. Gidan su Delu kuma Baba me zai kai shi can bayan duk wannan abinda aka yi? Yanzu haka yana can wajen abokanshi sun sha a bar su suna ta barci. Ke wuce kije ki duba min shi mara mutuncin yarinya mai gardamar tsiya kuma Delun kike kira haka gatsau babu sakayawa babu komai? Asabe ta wuce tana kunkuni haka kawai mutum yaje ya kwana a wurin iskancinshi za a hana ni baccina na safe ace sai na dubo shi sai ka ce wani dan karamin yaro. To ko ni da aka ce Sallau bai kwana a gida ba nayi mamaki don ba mai irin wannan halin ba ne 28 amma sai na maida lamarin kan yayi fushi ne da abinda uwarshi tayi mishi saboda maganar da yayi mata a kaina tunda na saba ganin yana fushin da ita ta bashi hakuri. Abu wasa-wasa sai ya soma neman ya zama gaskiya kusan duk inda ake zaton ganin Sallau sai da aka je nemanshi babu shi babu dalilin shi. A ka wuni ranar babu Sallau, tun ana kokarin danne hankula kar su tashi har dai abin ya gagara a ka shiga tashin hankalin mai tsanani, nena har da Babana a ciki don ko wurin tumatirinshi bai je ba, har wajen yan sanda aka kai riport da kuma asibitoci shiru babu wani motsi. Har wajen taran dare suna zaune jungum- jumgun a tsakar gida, yayinda ni kuma nake kwance a daki sai naji Babah Lantana tayi magana cikin sauri duba Asabe naji kamar an shigo zauren gidan nan. Asabe ta mike tana fadin ke Babah ba za ki bar mutum ya huta ba, dazu ma fa haka ina zaman- zamana ki ka tashe ni wai kin ji kamar an shigo zauren gidan nan to in an shigo menene? Wani irin mummunan ihu Asaben ta kurma a daidai shiganta cikin zauren, abinda yayi dalilin da Babana da Babah Lantana suka karta a guje don ganin dalilin ihun nata. 29 Thun Babah Lantana ya biyo bayan ihun Asabe Babana kuwa sai faman salati yake yi yana karawa alamar abinda ya ganin yayi matukar razana shi. Makwabta ku kawo min agaji da iyakacin karfinta take fadin hakan sai dai babu wanda va shigo duk da ana jin ihun nata da kuma kiran agajin da take yi amma shiru, bata kuma daina ba tanfar dai a ce ta mance da irin zaman da take yi da su nasa mu jinta yayiwa kowa kashedi kan shiga gidanta da ake yi bata so. Bai san yanda aka yi ba naji maganar Baba Baidu cikin zauren yana fadin, a'a bai mutu ba ai ga wannan jijiyar tashi tana harbawa da sauran ran, da alama dai shi Baba Baidu ya amsa kiran neman agajin da take yi ya kawo mata. Ihu Babah Lantana take yi tana karawa bata yi shiru ba har Likitan da Babana yaje ya kira ya iso. Shigo da Sallau tsakar gida da aka yi yasa na koma ta inda nake hangensu, tabbas in dai ba hatsarin mota yayi ba ko wata Rakkarfar dabba ta tattaka shi to wanda duk yayi mishi wannan abin da aka yi mishin ya tabbata mara tausayi. Likita ya fara taba shi shima ya fara fadin na tuba na tuba ku bar ni kar ku kashe ni, kusan awa biyu Likita yana kanshi ana yi ana danne shi saboda zaburar da yake yi. 30 Gaba daya jikin nashi ciwo ne wajen targade shida ne da kuma tsagewan kashi guda biyu, bayanin Likita ke nan. Yayi abinda zai yi ya gama ya mike yana fadin, in hali yayi a kai shi asibiti a kara bincike na sosai amma a yanzu dai wadannan da muka gani mun kula da su. Baba Baidu yayi mishi godiya' yayinda Babana ya bi bayanshi alamar zai je ya sallame shi, ita kuwa Babah Lantaná sai faman kuka take yi tana fyace majina da bakin zaninta itama Asaben da ba wani shiri sosai suke yi ba kuka take tayi. Sannu Sallau, sannu ka ji? Sanu, Ubangiji ya baka lafiya maganar Babana ke nan. A hankali Sallau ya bude baki ya ce "Yauwa Baba, na gode." Da sauri Babah Lantana ta kara matsawa kusa da shi tana tayi mishi magana saboda ganin da tayi ya dawo cikin hayyacinshi. Da kyar ya yarda ya buda baki ya bata amsar tambayar da ta dame shi da ita "Su Agogo ne. gabana yayi mummunan faduwa jin ya ambaci sunan da Mubarak ya ambata a matsayin wanda zai sa yayi mishi maganin abin. Su waye su Agogo? Ta sake bukatar sani, bai ce komai ba sai da ta gaji da tambayar cikin natsuwa ta soma yi cikin karaji da tashin hankali sannan ya bata amsa ki tambayi Asabe tasan shi. 31 Da sauri Asabe ta daka mishi tsawa kai kul kasa sunana a Cikin abin ku da waui ruba66en bakinka. Gaba daya kowa yayi shiru daga inda nake dai ina jiwo mishin Sallau ba kuma san ba dadi ba ne ya kawo hakan can cikin zuciyata kuma ina tunanin Asabe da dan uwanta Sallau babu halin su hadu wuri daya sai sun yi fada na tuna ni da Yaya Dijah na ce to ko don mu ba mu da uwa ne yasa muke son juna oho? Zuwa can Sallau ya sake gajiya da tambayoyin uwar ta shi ya ce, to in na gaya miki abinda yasa Agogo suka yi min haka me za ki yi? Ba kin ce ko sama da kasa zata hadu ba za ki daina dukan Mairo ba, to wannan abinda a ka yi min ai ba komai ba ne kan abin da ki ka ce, don haka gobe ma ki sake dukanta. Shawarar da na baki ba ki dauka ba ne yaja min wannan wahalar gobe ma in kin sake za su sake da har sun je sun kama mijin Babah Delu da ki ke cewa wanki ne suka sake shi saboda ya gaya musu babu abinda ya hada ku in ban da zaman gidan baya, yanzu ma kuma bakwa tare don in sun baki shawara ba kya dauka. In ban da halin da Sallau ke ciki wata Rila da Babah Lantana ta gwabe mishi bakinshi a dalilin 32 wannan bayanin nashi, nmaimakon haka kurma ihu mai tsanani tayi, ta yi kuka irin na fitar hankali bayan ta tambayi Sallau yanzu saboda wannan shegiyar yarinyar a ka yi maka wannan azabar? Bai musa ba bai ce mata uffan ba, to ai kuwa ba zan daina dukantä ba, sai dai... kan ta karasa taji ya ce mata to nuna min kawai inda dangin ubana suke tunda shi kin ce min wai ya mutu in dai da gaske ina da shi ai ba zai rasa dangi ba don ni Babah Delu ta ce min duk abinda ki ke gaya min kar.. Kan ya karasa tayi maza ta tarke shi da mari a kan ciwon nashi, ni dama kashe ni kawai ki ka yi da yafi min tunda dai duk wahalar da nake sha a rayuwata ke ki ke ja min. Wannan din ma ke ce na kuma san za ki sake ja min wani tunda sun ce sau goma ki ka buge ta sau goma za su rama mata a kaina, to ba gara kawai ki nuna min in da ubana yake ba. Ganewan da Babah Lantana tayi cewar Mubarak ne yasa a ka yi wa danta irin wannan matsanancin dukan duka kuma irin na rashin tausayi, a matsayin kashe di mai karfi gareta kan abin da take yi min na azabtarwa yayi matukar tayar mata da hankali. 33 Ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, don bakin ciki ta rasa me zata yi ta dauki fansa kan wannan abinda yayi mata? Tayi kuka tayi kuka har sai da ta kwanta ciwo wanda ban taba ganin ta kwanta da sunan ciwo ba sai a wannan lokacin. Kwana biyu ita ma tana fama da kanta, rannan ta samu sauki ta fito tana zaune a tsakar gida kan turminta ashar take durawa Mubarak tana fadin tana nan tana jiran dawowarshi yayin da ni kuma take ta faman tsine min albarka. Asabe ta gaji ta ce mata, to ya dai tsaya a kan zagin kar kije ki sake jawowa mutane wata fitinar don ke ba kya jin shawara. Wani abin mamaki shi ne, Asabe sai ta kwaso kowacce irin magana ta yabawa Babah Lantana tana kallonta ba za ta ce mata omai ba, amma Sallau duk da kasancewarshi da namiji kuma shi ne babba bata yi mishi lamnunin hakan. Jinya sosai Tanimu ya kwanta yayi kwana da kwanaki yana yi Babana yayi ta dawainiya da shi, amma tun bai gama warkewa ba sai naji Babah Lantana tana cewa Babana wai yana gani ana nema a kashe mata da a kan matsiyaciyar 'yarshi amma ya kame baki yayi gum kamar na mai cin najasa, gum din din dai ya sake yi mata bai ce mata komai ba har tayi ta gaji tayi shiru. 34 Duk da kudin da nakeda su a hannuna rashin Mubarak yasa nayi matukar. takura komai zan eii sai na saya ban saba wannan rayuwar ba, abinda nafi sabawa dashi a kawo min ne don haka kudin da ke hannuna bai hana ni jin yunwa ba, musamman ma da yake wani lokaci ana sayo min in kasa ci, don bai gamsar da ni ba tunda in yana nan ba irin wannan din nake ci ba. Babah Lantana tayi girki ta raba ta baiwa kowa nashi 'ya'yanta guda biyu da Babana yayinda ita kuma take zaune a kicin tana cin nata, na mike naje e same ta na ce Babah a bani nawa abincin. Ta kalle ni a lalace ta ce in ba haka ba fa a kore ni ko a yi ya ya? Shiru nayi na tsaya.ina kallonta, yayinda ita kuma take bayani a nemi kashe min da a kan ki sannan in yi girki in ba ki.ai ba zai yiwu ba. Daga bayana Babana ya ce min to zo ki dauki wannan nawan kici, na juyo da sauri ta biyo ni tazo ta fige kwanukan a hannuna in gadaranka kai ka kawo ai ni na girka, ni baiwarta ce? Bata danye itama ta girkawa kanta ai mace ce babu kuma abinda bata sani ba wani abin ma ta fini sanin shi. Wannan magana da Babah ILantana tayi ta in girkawa kaina shi ne dalilin da yasa da gari ya waye nabi bayan Babana zuwa wurin saida 35 tumatirinshi nace ya bani kayan miya, ya zuba a leda ya miko min. Na kalle shi cikin natsuwa na ce, to abin da zan dafa fa? Akwai a gida, na ce ba za ta ba ni ba, bai ce komai ba ya ciro kudi ya bani na wuce na shiga shago na sayi taliya guda daya na juyo na kama hanyar zuwa gida. Ran 'yanmata ya dade, na jiyo muryar tashi daga bayana na kuma shaidata ta Mansur ce, bàn waiwaya ba na dai ja na tsaya ina jiran isowarshi. Ai rannan na hango ki kina dawowa daga Makaranta nayi ta daga miki hannu ina haba in babu busa babu daga hann ne? sai na lura ma ba ki ganni ba. Nayi murmushi tare da fadin eh, ka kyauta min kwarai da kai da kanka ka gane ganinka ne ban yi ba. A'a haba ai nasan ba ki da irin wannan wulakancin ke dai kawai ganinki ne yana wuya da yake kin riga kin zama budurwa. Na ce, kai Mansur ke nan, barkwancinka yana da yawa, can cikin zuciyata kuwa mamakin dabi'arshi kanbama 'yanmatancina nake yi. Kullum muka gamu sai ya jaddada min ni din budurwa ce ni din mai kyau ce, ni din daba ce da saura, abinda kuma bai taba damun Mubarak ba ke nan. Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin ko 36 Mubarak. sya taba gaya min ifin wadannan kalmomin? Kai bani tuna ba. Kar dai a ce rashin lafiya ki ka yi bai sani ba? Na ce eh amma ba mai tsanani ba ne, ya zuba min ido yana kallona, kina nufin abinda yayi sanadin wannan ramar ba ma tsanani ba ne? nayi murmushi na cé. eh, ya ce to kuwa sai muyi ta addu'a kar mai tsananin yazo, na ce to amin. To mu ba yaran nan ledar cefanen mana don kar mu 6ata muşu lokaci na ce a'a babu komai cefanena ne, kina nufin kece za:ki yi girkin da kanki? Na ce, eh, ya ce a'a to shiga ciki kawai ina zuwa, bari in je in kawo cefane nayi maza na ce a'a ka bari. Ya daure fuska ya ce, to ai ba ke ki ka roke ni ba, na wuce shi da nufin tafiya gida, ya sake biyo ni ran yanmata ya dade, na dan rage takun da nake yi don nasan wata magana yake son gaya min, kina da bukatar wani abu ne? nayi maza na ce mishi a'a na tafi. Ina cikin tafiya sai ga Isiyaku da saurinshi, Anti ai nazo ki ka ce babu aika, na ce eh Isiyaku wurin Babana naje na karbo yasa hannu ya karbi ledar da ke hannuna muna tafiya yana bani labarin wahalar ruwan da ake yin da yanda suma matar Babansu ta 37 sanya dokar sai mutum ya ajiye bokitin ruwa goma kafin ta ba shi abincinshi. Ba ki ga fa inda muke tafiya diban ruwan ba, na ce eb to wata rana ai zai wuce Isiyaku, ya ce haka a ke fada, nayi tunanin shima yana da irin manina kenan, da zuciyata ke yi min a duk lokacin da a ka gaya min haka shi ne na in tambayi kaina to yaushe ne wata ranar zata zo? Cikin gida na shiga shima ya biyo ni duk da yasan Babah Lantana ta tsani shigar da yake yi cikin gidan kullum ta ganshi a ciki sai ta tambaye shi kai baka san nan gidan, gidan matan aure ba ne ba? Sai ya ce ya sani ye uce ta yayi abinda zai yi ya fita. Na shiga cikin kicin, tayi 2za ta biyo ni karki shigar min kicin kar ki taba min komai a wurin nan, don ba zai yiwu ni da ke a ciki ba, in kuma ke ma matar gida ce sai ku zo ke da ubau i ku gaya min." Ban tanka ba nasa hannu na dauko risho tare da tukunya mai murfi, ba na ce kar ki taba min komai ba, na kalle ta na ce, kin gani? Wannan ai na Inna ne, kadan ya rage ta kifa min mari saboda ambaton Inna da nayi a gabanta, ban san yanda a ka yi ba sai kuma naga ta fasa. 38 To juye min kananzir din ciki ko shi ma nata ne? naje na juye mata, ina fitowa Isiyaku da ke biye dani yasa hannu biyu ya karba ya bar ni ina neman wani tsohon galan da na san yana nan a cikin kicin din. Na fito ina kwance bakin zanina da na daure kudina

Chapter 2 of 7