Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
na ce Ubangiji na gode maka da kasa uwata ta haife ni tare da ubana da ka jarrabe ni da maraici ma ba ka jarrabe ni da na uban ba sai ka rufa mion asiri ka zaunar da ni tare dashi. Ka kuma sa shi ya so ni bai ta6a yarda da shawarar mugaye na ya bada rikona ga wasu ba, 58 na shafa a fuskata. na gyara zamana a bakin gadona. Da wa ki ke wadannan maganganun? Tayi tambayar a fusace na ce da wanda ya tsargu tunda ni dai ban ambaci sunan kowa ba, ina zaune a gidan ubana kuma to ai babu wanda ya isa ya hana ni 'yancin yin magana, haka kawai in mutum yaga abinda nake yi ban yi mishi ba to kowa yaje gidan ubanshi mana. In da gaskiya cikin lamazin ai cewa aka yi kije a kai ki wurin naki. don ki huta gorin da ake yi miki to sai kuma ki dawo mana yau? An dawo din sai kiyi abinda za ki yi na ce babu abinda zan yi sai gori babu kuma mai hana ni. Muna cikin haka sai ga Isiyaku ya shigo da saurinshi, murmushi yake tayi alamar yana cikin farin ciki, na kalle shi na taya shi murmushin dona in zolaye shi, na ce mishi yaya na gan ka da jallabiya har da bagaruwa da dabino, ko makwabcinku Alhaji Madugu ya dawo ne? Yaja wani mummunan tsaki kafin ya ce na rantse Anti Mero da gangan kike yi, Alhaji Madugu da ko katangar gidanshi bai yarda taba ba shi ne zai dawo Umra ya bimu da tsaraba irin wannan? Yaya Mubarak ne wajen mu goma ya Daiwa ya shiga lissafa min yaran na gidaje daban- 59 daban, na ce Ubangiji ya karba musu badar da suka yiwo, addu'o'in da suka yi mana ya karba mana ya ce amin. Dadi mai yawa ne ya kama ni don kuwa ba karamin kewar Mubarak nayi ba, dan sauki-saukin abin ma shi ne Mansur ya rage min kewar tashi da ba karamar waiala nasha ba. Za ka share zauren nan ne? Isiyaku yayi murmushi cikin yanayin nokewa, gaskiya kiyi hakuri Anti Mero gida zani inyi wanka, in sa kayana zan je in raka Yaya Mubarak sallar Juma'a, na ce to babu laifi sai kun dawo. Na koma daki na zaro tsintsiyar zaburi na nufi zaure don in kara kalelece zauren saboda in yazo ya samu wurin cikin tsabta tunda nasan saukowa daga Masallaci nan zai zo. Ina sharar zauren ina lissafin rabon Mubarak da gida a zuciya, na ce kwana ashirin da uku daidai, kwanakin sun tafi da yawa al'amura masu dama sun faru a bayanshi ga shi dama mun dade babu wata mu'amallah a tsakaninmu tun kafin tafiyarshi hidimar kasa, ko da dai shi ba mai hira ba ne balle in ce zamu baiwa juna labarai masu yawa. Ni kam zan yi kokari in koyi ba shi labarin abubuwan da aka yi baya nan, ina cikin haka sai kawai naga wata gabjejiyar kafa ta tako cikin 60 zauren, in daga ido don ganin mai kafar bakon Babah Lantana na gani yau ma ya dawo, ko me ya kawo shi kuma oho? Wani lallaus an faffadan murmushin da ya sake bayyanar min da hakoran gwal dinshi yayi min, nan da nan kuma ya sake kifta min ido wai signal yake yi min, nai maza na sake banka mishi wata irin uban harara kamar dai yanda muka yi da shi wancan karon. Ya wuce cikin gidan ya bar ni ina tunanin maza suna tafiya Masallaci don yin sallar Juma'a shi kuma ya shigo gidan mata zai zo ya nade kafa yayi ta zuba zance. "Me ya kawo ka gidannan yau kuma? Tayi mishi tambayar bayan ta mike tsaye ta tsura mishi idanuwanta tana kallonsa, "Kai ke kam Hajiya Lantana ba ki iya karbar bako ba, to alheri nazo miki da shi." "Ai ba ka da shi ne ko ka ambace shi an ganshi a farko to sai ka biyo bayanshi da wani sharri." To babu laifi, duk abinda ki ka ga dama ki gaya min ni naga abin ki nasa rai a kai." Ya gyara zama kan tabarmar mishi, na shigo gidan da nufin wucewa in je in yi wanka, idona ya kai kan sunkin kudin da ya tura mata tare da fadin "Ungo wannan rike naki ne ki da ta shimfida 61 Soma taba su, in maganar da na zo miki da ita ta samu karbuwa a wurinki to wannan din ba komai ba ne illa somin-tabin alherin da za ki samu a wurina" Ta zuba mishi ido tana kallonshi ba tare da ta taba kudin ba, ai sai kayi min bayani naji in da zancen naka ya dosa, sannan in naga za su ciwo in taba, ai babu abinda ban sani ba a hali irin naka baka fidda kwabo matukar ba ka hango yanda za' ayi ya jawo maka sisi su zo tare ba." Na shiga wankananabar su suna maganganunsu ban jin abinda suke fadi saboda bayan gidan a lungu ne na kuma rufo kofa, wanka mai kyau sosai na tsaya nayi saboda a yau ina matukar dokin saduwata da Mubarak. A wannan lokacin na riga na zama budurwa na kai munzalin yan matancin sosai nayi sha shida da yawan mutane musamman Mansur sunan da suke kirana kenan yanmata, ban san dalili ba sai pake jin zuciyata ta soma so da begen kalmomi masu dadi tsakanina da wanda nake ganin ya dace yayi min hakan. Ko da dai shi Mubarak bai taba furta min wata magana ko nuna wata alama ta gane na kawo wannan lokacin ba, a wannan lokacin ina ganin zai 62 gane hakan ko daga irin tarbar da nake shirin yi mishi. Kullum a Makaranta kawayena ba su da wata hira wadda ta wuce ta samarinsu da irin kalamansu masu dadin ji da sanyaya zuciya, amma ni ba ni da mai furta min irin wadannan kalaman, dan dama- dama ma Mansur. Ga shi kuma kusan kowa ya ganni zai yaba kyakkyawar halittar da aka yi min gani da tsabta gani da gyara, ga ni da ado daidai gwargwado ga shi kuma a wannan lokacin auren yara kan faro ne daga sha biyu sha uku sha hudu in ta dan yi tsayi sha biyar ko mu abinda yasa muka kai sha shida ba a damu ba don muna Makaranta ne, amma shiru ba ni da kowa. Na fito daga wanka daidai Nalami ya fito da Wasu soyayyun kaji daga cikin wata leda da ya shigo gidan da ita, gashi nan komai dan kankantanshi. Yana ganina sai ya canza maganar yana fadin da hannuna na soya miki ita don dai kiji-kiji dadi ki tuna da girkin maza, ban sake kallonsu ba na wuce na bar Babah Lantana ta fara yagar wata cinya tana ci. Kwalliya sosai nayi na sanya kayana, maimakon ma in zauna a cikin gidan sai kawai na fito zaure na zauna ina sauraron isowarsu, ana 63 cikin haka sai ga Mansur ya shigo da dardumarshi a hannunshi alamar ya dawo ne daga Masallaci. "Barka da Juma'a. na daga ido na kalle shi nayi murmushi har an sauko? Ya taya ni murmushin an sauko ranki ya dade, na sunkuyaar da kaina kasa ban cika son kana kirana da irin wadannan sunayen ba, kana sa ni ina jin wani iri. Yayi maza ya tsuguna a gabana ya zuba min ido yana kallona, me za ki ji don nayi miki addu'ar ranki ya dade? Ai bar ni kawai in ce miki ranki ya daden, ko na dan ji sanyi a raina, kin san yanda ki ke a'wurina kuwa? Ai kallonki nake tamfar wata tauraruwa in ban da kin takura ni kin hana bakina furta miki kalmomin da yake son furta miki da kin sha magana. Tsuke fuskar da nayi yasa shi yin maza ya canza maganar da tambayata, amma dai kwalliyar nan da ki ka yi ba unguwa za ki ba na zo na tsare ki da magana? Nayi maza na ce mishi a'a, cikin zuciyata kuwa fadi nake yi ina son jin irin wadannan kalaman amma ba daga bakinka ba. kwalliyar taki ce na ganta ta zama ta To ai kwalliyar taki ce na ganta ta zama ta musamman ta bambanta da irin kwalliyar da ki ka saba yi kullum wannan din tana da wani abin da take nufi ta kara miki kyau tasa ki kin zama 64 budurwa ta sosai-sosai da ganinki kuma an san ke din babbar yarinya ce mai daraja taimake ni ki gaya min gaskiya kwalliyar nan saboda wa ki ka yi ta? Kalamanshi suka yi dalilin da na ce mishi saboda kai, yayi maza ya ce ke bari zance Maryamu, kar, ki zuga' abin nan da ba a fadan sunanta ta hau kaya donni ki ka yi? Na ce, uhh, don in ganki in ji dadi? Na sake cewa uhh. Sai naji ya ce, To in dai donni ki ka yi da gaske don in gan ki in ji dadi saboda kina tattalin farin cikina to bani izini kawai in je gida in shaidawa Babana don yazo wurin Mahaifinki ya gabatar da zancena a wurinshi. Maganar tashi ta firgita ni ba abinda nayi zaton zai fito-daga bakinshi kenan ba, don haka na dago ido da nufin kallonshi, kafin in san irin amsar da zan ba shi, abin mamaki Mubarak na gani tsaye a bayan nashi cikin wani irin yanayi, ga dai kwalliya ta burgewa' yayi amma kuma fuskarshi takai matuka wajen daurewa alamar bacin rai mai yawa a tare dashi. Gabana yayi matukar faduwa, na firgita da ganin nashi nayi maza na sunkuyar da kaina kasa, ban san yanda a ka yi ya shigo cikin zauren ban ji motsinshi ba. 65 Ban san me Mansur ya gani ba da yayi dalilin da ya waiwaya cikin sauri, ganin Mubarak a tsaye bayan nashi ya sa shi hanzarin mikewa tsaye tare da mika mishi hannu. "Assalamu alaikum, barka da dawowa." Suka vi musabaha bai sake tsayawa ba ya wuce ya tafi Kusan minti biyu zuwa uku Mubarak yana tsaye kallcza kawai yake yi, ba tare da ya ce uffan ba jikina sai rawa yake yi, ji na nake tanfar na aikata wani zunubi. Cikin zuciyata sai tunani nake yi in ya tambaye ni me zan ce mishi? Ina cikin wannan zullumin ne sai kawai naga ya juya ya tafi ba tare da ya ce min komai ba, tafiyar tashi a sani cikin wani irin yanayi da na kasa jin dadin raina, jimawa can dai na wartsake na ce oho. Na mike na nade tabarmata a nufi cikin gida, har lokacin Babah Lantana tana ta da bakonta, sai dai ga alama sallama suke yi saboda na ! shi yana cewa, to sai yanda ta yiwu, ko me a ke ciki zan turo in ji bayani, ko kuma in zo da kaina, ta ce to duk wanda a ka yi. Nayi mamaki a raina yanda a ka yi bhirar tasu ta kasance sabanin ta ranar da ya fara zuwa gidan. Ina kwance a kan gadona zuciyata ta ca takai kawo cikin sake-saken al'amura, naji wani mai 66 sayen kwalla yana tambayar akwai kwalla ko tangaran ko tasoshi? Da sauri naji Babah Lantana tana cewa babu sai gado mai rumfa in kuna saye, yayi maza ya ce muna saye mana, ai mu duk wani abinda zamu samu amfani a kanshi saye muke yi. Nayi maza na mike a tsakiyar gadon don ganin gado mai rumfar da Babah Lantana ke shirin gado mai runfar da Babah Lantana ke shirin sayarwa tunda naji ta ce ya shigo. Ina daga zaunen najiwo ta tana kakkarya gadon Innata, Asabe tana tayata, 'wannan gadon ma ai tuni ya kamata in rabu da shi in canza na bari har wannan shegiyar ta zo tana yiwa mutane goshinshi. Ba ma a yayinshi fa Babah, ta ce ch ai in suka saya kauye suke kaiwa ko kuma su yankę shi su maida shi na familin mai Rarfe. Sai da suka fitar da shi zaure suka soma cinikinshi sannan nabi baya na kalli mai sayen nace mishi, kai Mallam gadon ba na sayarwa ba ne, mai gado ya kalle ni ya kalli Babah Lantana ya dan yi turus alamar rudewa. To ko dai tayin da aka yin ne bai yi miki ba? Babah Lantana ta ce, yau naga fitina, kai Mallam ba ni kudina ka ji na sallama maka. Na ce in ka saya ma banza ka saya gadona ne da na gada a 67 wurin Mahaifiyata, ban saida shi ba kuma ai babu mai sayar da shi ko kuwa? Yayi maza ya gyada kai tare da fadin in dai haka ne kam babu shi na ce a to, na leka na kira wani yaro na ce mishi gudu kaje ka kira min Isiyaku, yaron ya tafi da gudu, ni kuma naja na tsaya a Rofar gida ina kunkuni, to an zo da gado gidanmu ne balle a jawo gado a ce za a sayar ayi canji? To ku sasanta dai sai mai gadon ta gaya mnin kudin gadon in biya, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi amma ai nace maka ba na sayarwa ba ne za ka bar wurin nan ko sai na kira yaran can sun rakaka? Sum-sum ya kama banva ya bar wurin. Babah Lantana tayi kwafa ta kama gado zata mayar ciki na ce a'a ai tunda ya uto ba zai koma ba a zo a sayar da shi bana nan, katifar ma don dai ba zan bar Babana ya kwanta a kasa ba ne da na shiga na fito da ita na hada su. Ai sai ki fito da itan kawai ta ju ya ta shiga gida Isiyaku ya iso na ba shi gadon na ce ya hadu da yara su kaui shi gidan Yaya Dijah. A wannan lokacin ne Babah Lantana ta rasa yanda za ta yi da ni a dake dai ba zai yiwt ba in zagi ne ba zai gamsar da ita ba, tunda nima nayi rikan da bana rama zagin amma ina komawa gefe 68 in yi kunkunan da bata jin abinda nake fada wanda nasan yafi komai bata mata rai. Ga shi ta fito da gado da niyyar sayarwa ta karbi kudin wai-ita zata yi canji na kwace gadon na tura wa Yaya Dijah: shi babu kuma yanda zata yi dani, ina jin ta tana rattabawa Babana bayani na karya da na gaskiya don dai ta samun ya sa baki cikin maganar bai ce mata komai ba. Takaicinshi ya kama ta, ta kalle shi cikin yanayin bacin rai tare.da jan tsaki kai kam ai gaya maka magana ma ba ta da wani. amfani sai ayi a gama kana ji ba za ka ce komai ba, kayi wani gum da baki kamar na mai cin najasa. Bai ce komai ba nima ban ce tha cikin zuciyata dai ccwa nayi in ma kin yi ne don ki:cuci wani to kanki zai koma. Ban sani ba ko takaicin labiane yake yawan damunta ko kuma ta mantá ne:cewar dasa hannunta: cikin shirun na Babaha yasa naji ta tana mita ita kadai' a dakinta, a ce maigida duk abinda aka yi a gidanshi ba zai ce komai ba, sai yayi gum da bakinshi kamar na mai bubu? To ina zance? A hankali na buda baki na ce babu, sai dai nasan bata ji ni ba. Tsaraba mai daraja sosai Mubarak ya aiko min da itya, sai dai hakan bai sa da muka gamu da shi a 69 hanya na daga ido na kalle shi ba, balle in je ina kula shi saboda na gaji da yanda yake tafiyar da ni ba kuma zan lamunci miskilanci da jan aji irin nashi ba. A wannan lokacin mu'amallata da Ahmad Mubarak sai ta kara ja baya sosai mafi yawancin lokaci ko yana dan murmushi ya ganni daure fuska yake yi, ko yayi kamar bai ganni ba, nima bana kallonshi in ba a kan kuskure ba. In na san yana gida ma bana zuwa sai in bari sai baya nan in yi maza in je in gaida Umma in dama abin da zan yi mata ma in yi mata ina ganin ya dawo zan yi maza iu îta in bar gidan. Umma da kanta ta ganc mun yi 'yar tsama ni dashi don sau biyu tana tambayata ni me ke faruwa ne tsakaninki da Ahmad Muuarak Maryamu? Ina jin ta soma irin wadannan tambaycin sai kawai in gudu in barta. Sai dai irin wannan zaman da muke yi da shi bai sa ya canza komai ba na daga abubuwan da ya saba yi min kowane lokaci a cikin yi min aike yake, kayayyakin bukatar rayuwa irin su mai, sabulai, na wanka da wanki, under wears, audugar al 'ada, kudi babu abinda ba ya baiwa Isiyaku ya kawo min. 70 Ana cikin haka watan Azumin Ramadan ya iso, don dama su Mubarak sun yi umrarsu ne a watan Rajab, Isiyaku ya turo yazo ya tambaye ni me da me nake so a kawo min? na ce yaje ya gaya mishi bana bukatar komai har cikin zuciyata ban jina kamar ina bukatar wani abu nashi a wannan lokacin tunda abinda nake so yayi min bai yi ba abinda nake nema a wurinshi ban samu ba. Babu wata alama kuma da take nuna zan samu yanda nake so din a wurinshi, to ana me zai yi ta hidima yana ta dawainiya dani bayan shi ba sona yake yi irin son da nake yi mishi ba, in taimakona wake yi don kyakkyawar mu'amallar da yayi da Innata a shekarunsbi na kuruciya to ya kyautata ya taimake ni a bayanta har na kawo munzalin da nake ciki & yanzu. Don haka na gode ya bari haka, in don tausayi ne ma dai to na gode yanzu nayi girman da shi bai lura ya gane ba, don haka ya bar ni kawai in ci gaba ni kadai in ma wahalar ce in shata kawai. A yanzu abinda nake so ya so ni ne kawai irin son da nake yi mishi, soyayyar da zata rikida ta zama ta 8ure, aroma ba kullum a ji tausayina ba. A duk lokacin da irin wadannan abubuwan suka dawo a cikin raina zama nake yi in yi ta kuka 71 wani irin kukan da sai nayi na gaji kawai nake yin shiru. Ban san dalili ba cikin zuciyata babu abinda nake so irin aure, ban sani ba kowace yarinya ta kevo munzalin da nake abinda take ji ke nan ko kuwa ni don ina tare da Babah Lantana ne? matar da kuliu:burinta ta cutar da ni ne in kaga bata yi min hakan ba to abin ya gagara ne kawai. Sannan kullum hirar kawayena ke nan samarinsu da ranar aurensu, sai na samu kaina nima a irin wannan yanayi da matsayin sai dai kuma na kasa sakin zucivata in so wani ban da jin dadin wata magana in dai a hakin wani ta fito ta in da nake so ta fito din kuma abin ya gagara, to ya fita mana ko zan samu in saba da wasu irin sabon da nayi da shi in so su irin son da uake yi mishi ko na rinka jin dadin kalamansu. Gaya mishin da aka yi bana bukatar komai shi ne yayi dalilin da ya gangaro da kanshi yazo har kofar gidanmu sai dai yau ma cikin rashin sa'a tare da Mansur din yazo ya same ni, sai dai maimakon ya juya ya tafi bayan tafiyar Mansur din kamar yanda yayi wancan karon tsayawa yayi ya tsare ni da ido yana kallona, yayinda ni kuma na sunkuyar da kaina kasa nayi kamar ban san da tsayuwar tashi ba 72 Ni me ke tsakaninki da wannan ne? a hankal1 na ce wa'? Yayi shiru ya ci gaba da kallona ba tare da ya sake cewa komai ba, saboda sanin da yayi nasan wa yake nufi, na mike tsaye a hankali cikin natsuwa tare da karkade jikina a sakamakon zaman dirshan din da nayi a kasa sanda nake hirar. Cikin natsuwa na kalle shi na ce Mubarak, ya ce uhh, ya amsa ba tare da ya buda bakinshi ba watakila bai ji dadin yanayin da na ambaci sunan nashi a ciki ba. Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi yau ne ka ga ya dace ka tambaye ni abinda ke tsakanina da Mansur? Ya sake cewa uhhm, ba tare da na dago ido na kalle shi ba, nace to ai ka makara, na juya na shiga gida na bar shi a wurin yana tsaye. Na hau gadona na zauna a dalilin na kasa kwanciya jikina sai faman bari yake yi, yayinda Zuciyata ke ta faman harbawa a dalilin sanin da nayi na batawa Mubarak rai. Hankalina yayi matukar tashi na kasa jin dadin al'amarina. Tsawon lokacin ina cikin wannan hali kafin naji zuciyata tana rarrashina tana bani hakuri kalamai masu karfi take gaya min, ya zama dole in zama jaruma a kan lamarinshi in har ni kadai ce na 73 ke sonshi shi tausayina yake ji to ya tafi ya bani wuri mana kawai ya gani ko ba zan rayu ba. Ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni tare da masu sona irin son da nake bukatar ayi min a yanzu, ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni in yi harkokin rayuwata menene na tsare ni da tambayoyi? Na mike cikin kuzari saboda jin da nayi zuciyata ta gamsu da abinda na aikatan naje na debi ruwan sanyi nayi wanka na dawo na zauna goge jikina ina shafe shi da man shafawa na 10.0-6 man da Mubarak ya saban min da shafawa. Wani abin takaicin shi ne duk wani abinda ke kewaye dani shi ne don haka na tsayar ma raina da cewar cikin matakan da zan dauka na kamewa daga gare shi har da daina yarda da hidimomin da yake yi min. Ina cikin wannan halin sai ga Isiyaku ya shigo dauke da wani katon kwali shake da kayayyakin amfani na hidimar Azumi, ba zan iya cewa a mayar mishi ba don kuwa yana da girma da kima a wurina. Na karba na ajiye, Mansur ma ya kawo min nashi na sake hadawa daga gidan Yaya Dijah ma ta aiko da sako guda biyu, na Babana da nawa. Ina jin Babah Lantana tana gayawa Baba wai in ban da kar ta ce ya mayar wa Yaya Dijah da kayan kamun 74 AZumin da ta kawo mishi ace bata kyauta ba da ta fada don kuwa ba a kan son ranta ta bada nashin ba, tunda abinda ta bashin bai kai wanda ta ba ni yawa ba. A watan Azumin kullum na kan shiga gidan su Mubarak ne da safe in je in gaida Umma in kuma rike mata Alkur'aninta muje wajen jin Wa'azin Tafsir din da ake yi a babban Masallacin Juma'armu in a ka tashi sai na rakata gida kafin in zo gidanmu in yi alwala in yi sallah, in hau gadona in kwanta in yi bacci. Ba na farkawa sai karfe uku da rabi, sai in yi wanka in yi alwala in yi sallar La'asar in kama shirye-shiryen abin buda bakina wanda nake yi da dan dama don bani kadai ba ce, 'yan Almajiraina guda biyu da muka yi matukar sabo sai Isiyaku da Mansur da kuma Babana da kullum nake daidaitan dawowanshi daga wurin Tafsir tunda na dare yake zuwa in ba shi abinda nayi ya zauna yana ci, ni kuma ina gefe ina jiranshi sai ya gama in karbi kwanon ya wuce ya shiga gida kafin in bi bayanshi. A haka har Azumin yazo karshe muka shiga kwanaki goma mafiya daraja kwanakin neman daren Lailatul Kadri daren da AIkur'ani mai 75 girma ya ba mu labarin cewa darajarshi tafi ta watanni dubu, haka alkairorin da ke cikinshi. Ubangiji yasa mu dace, kullum abinda Umma ke fadi ke nan in taji Mallam yana ta nanata fadin alherin daren 'Lailatul kadri ni kuwa sai in ce mata anmin Umma. A wannan lokacin zan iya cewa ban taba samun kaina cikin hali na kunci da farin ciki lokaci daya ba irin wannan karon, ina cikin farin ciki saboda alkhairori da suke ta zuwa min daga wurare daban-daban. Kusan kullum gari ya waye sai an zo min da sako na kayan sallah daga wani wuri. Yakumbo Halima da ba wani karfi ne da ita ba ma atamfa 'yar Holland ta dinka min a dalilin wai na zama budurwa, Yaya Dijah tsalelen leshi gami da takalmi da Jaka da gyale. Umma atamfa da leshe itama da takalmi da Jaka da gyale mahadin takalmin duk da dai tace wai da kudin bankina ta saya min amma dai nasan alherin Umma bai kwatantuwa a wurina. Mansur yayi min kala biyu masu kyau shima tare da takalmi da Jaka tare da gyale, sai kuma a ka kawo min na Mubarak, Isiyaku ya aiko ya kawo min. Na zauna ina kallonsu suma kala biyun ne sal dai shi komai nashi daban ne da na saura, bai taba 76 mancewa da wani abu ba in dai har aiken zai yi min yadika ne masu kyau masu laushi kala biyu mai ruwan madara da kuma baki na rike su a hannuna ina kallonsu ruwan da suke yi ya kara tabbatar min da darajarsu. An yi musu adon zare a wuyansu kalan zaren ya dace da kalan takalma guda biyu da ya saka a cikin kayan kenan kowanne da mahadinshi gyale biyu sai kayan shafa da under wears ga kuma wani dan karamin akwati mai dauke da wata 'yar sarka mai dan madaidaicin 'yan kunne da zobe a wata yar takarda kuma wasu siraran wararai ne da agogo babu yanda za ayi a kushe hidimar Mubarak in dai zai yi ta matsalarshi guda daya ce ita ce ta ban san in da yasa gaba ba. Kuncin da nake ciki da takura kuma shi ne na tasa ni a gaba da Mansur yayi in bar shi ya tura iyayenshi wajen Babana magana ta wuce tsakanina da shi har yaje ya hada ni da Yakumbo Halima, ita kuma ta kira Yaya Dijah ta gaya mata cewar lalle ne ta gaya min in bar Mansur ya tura iyayenshi wajen Babana ayi maganar aurena in kuma ba shi nake so ba to in turo wanda nake son daga nan zuwa watan Sallah in har ba so mu nuna mata ba ita ta haife mu ba, amma ina amfanin wannan zaman da nake yi a gidanmu? 77 Shi karatun boko ai ba dole ba ne wurin 'ya mace, na Addini kuwa na same shi daidai gwargwado a gidan mijina ma kuma zan iya yi tunda neman sanin addini ne shi aure ai suturar 'ya mace ne. Yanda naga Yaya Dijah ta dauki maganar da karfi na tabbatar zai yi wuya a ce watan Sallah yazo ya wuce ba tare da an titsiye ni na fitar da mijin ba, to ya ya zan yi? Ba da sunan Mansur din zan yi shi da yake son a bada sunan nashi ko kuwa wata hikima zan yi da Mubarak zai san abin da nake ciki? Cikin hanzari na kawar da wannan tunanin saboda sanin da nayi cewar ba zan taba nuna mishi wani abu

Chapter 4 of 7