Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
ya dame ni game da shi ba, ba zan taba karya 'yancina na kasancewata halitta mai daraja da Ubangiji ya karramata da kunya ba, wato halittar da aka yi min na zamowata 'mace Haba, mace ta rasa kunya? Ai kuwa dai tayi rashi mai girma, kalaman Yaya Dijah ke nan kunya ai adon 'ya mace ne, a bakin Umma na saba jin hakan, don haka na kara kudurawa raina babu wani abin da zai sa in nuna mishi wani abu in dai yaga ci gaba da yin shirun nashi yafi mishi to yaje yayi tayin shiru. 78 Aka wayi gari a gidanmu da ma sauran gidajen Musulmi na garuruwa daban-daban, hidimar sallah a ke yi, Jama'a sai kaiwa da kawowa suke yi cikin walwala da farin ciki ga dukkan alamu kuma an yi sallar ne cikin walwala da wadata. Tasa kayan sallar tawa nayi a gabana gaba dayansu ina binsu da kallo daya bayan daya, kafin zuwan sallar niyyata in sanya kayan da Yakumbo Halima tayi min ne ranar sallah don girmamawa a gareta, amma a yau da aka wayi gari ana hidimar sallar ga kuma kayan sallar tawa a gabana sai naji bazan iya kaucewa sanya daya daga cikin kayan sallar da Mubarak yayi min ba duk kuwa da niyyar da nake da ita ta daina mu'amalla da kayanshi. Duk da hakan sai na ce to tunda yanzu hidimar sallah a ke yi bari in bari bayan sallah na dauki wannan matakin amma yanzu bari in yi adon sallah kawai. Bakin yadin na sanya wanda jikinshi yafi kama da voil ko silk tasha ado irin na barnina a gaban rigar dan madaidaicin ado da yayi matukar kawata rigar ta zamo gwanin sha'awa, na sanya takalmi da gyale tare da Jaka da suka dace da kayan. Sannan na dauko 'yar sarkar da 'yan kunnena tana sanya ga kuma warwarai da agogo, in tsaya cewa nayi kyau ma bata baki ne kawai, na tsaya 79 gaban dogon yaron Innata da Babah Lantana ta fitar a dalilin hanata saida gadon da nayi na dauko shi na kawo dakin. Kallon kaina nake yi a cikin shi cikin zuciyata na tabbatar ban taba yin kyau irin na yau din ba, ko ba a gaya min ba kuwa dama nasan ni din mai kyau ce, don kuwa kowa ya ce da Innata nake kama Innata kuwa mata ce da ta rayu mutanen da suka santa suna ba da labarinta. Yau kam duk mishikilancin shi da taurin kanshi in ya ganni ba zai iya kame bakinshi yayi shiru ba, sai ya yabi kyan kwalliyata sai ya furta wata kalma da zata zamo mai karfi a tsakanina da shi. Ina tsaye a wurin ina kara feshe jikina da turare tare da kara kallon kaina a madubin Asabe ta shigo dakin tana zage-zage nayi kamar in tanka mata tunda nasan da ni take yi sai nayi maza na baiwa kaina shawarar kame bakina tare da hanzarta barın gidan don ba zai zamo mata komai ba ta rufe ni da dukan da zai yi dalilin da zata tumurmusa ni ta lalata min kwallioyar sallar tawa ba. Don haka nayi maza na yafa gyalena na kuma shuri takalmana nayi waje, gidan Umma na nufa zanje in yi mata barka da sallah daga nan taga kwalliyata. 80 Nayi maza na yamutsa fuska na ce, a'a Umma ni fa ba don kowa nake yi ba, tayi murmushi, au haka ne Maryamu kai wannan kayan sallah naki da kyau suke kai ji wata sarka kai kai kai, wa ya saya miki wannan sarka Mero? Na shiga dibi-dibi cikin sa'a ta sake tambayata, Dijah ce ko? Nayi maza na ce mata ch, lokacin ne na kara sanin darajar sarkar. Nabi umarnin Umma na shiga nayi wa Baba barka da sallah a falonshi na fito daidai Mubarak yana shigowa gidan ban daga ido na kalle shi ba balle in gane irin kwalliyar da yayi na dai san kawai na shaki kamshin turarenshi. Baba ya bani goron sallah, nayi maganar ina nuna mata kudin da ya banin, tayi godiya. Kai wannan kwalliya taki tayi kyau, bani plate guda biyu Umma zan ba wasu, zuciyata ta soma yin nauyi da na soma tunanin har uwarshi ta gane don shi nake yin abubuwa masu yawa amma shi bai gane ba, ko kuma ya gane ya ki nunawa saboda bai da bukatata. Babu wanda ya ganni bai yabi kwalliyata ba sai shi sai kokarin karbar waina yake yi wai wasu bakin sun kara zuwa mishi. 82 Iko sai Ubangiji, girman 'ya mace babu wuya ai duk in da budurwa takai kin kai Maryamu, kin kuma yi kyau irin wanda ba a zaton miki ba. Nayi murmushi na ce Umma kenan, na juya tare da cewa na tafi, da sauri ya biyo ni wata kila yayi zaton zan tsaya mishi ganin ban nuna alamar hakan ba ya sa shi fara yin magana ina za ki ne haka? Ban tanka mishi ba, da ke fa nake magana, na sake yin kamar ban ji shi ba, tafiyata kawai nake yi to tsaya mana ki ji maganar da zan gaya miki, cak naja na tsaya saboda abinda zuciyata ke raya min, ya biyo ki ne ya gaya miki wata muhimmiyar magana, zai yabi kwalliyarki ne wata kila ma yayi abin da zai fi hakan dadi a gare ki. Naja na tsaya ya iso ya same ni, maimakon in ji ya kama hanyar gaya min wata magana mai dadi sai naji ya fara jero min tambayoyi ina za ki ne haka? A hankali na ce mishi gida, to me za ki je kiyi a gidan da ki ke irin wannan saurin? Nayi shiru saboda ban ga kamar zan iya amsa irin wadannan tambayoyin ba. Muje in kai ki kiyi hoto, ban kalle shi ba na ce na daina yin hoto a daidai lokacin kuma na kama tafiyata cikin zuciyata ina tunanin bai iya komai ba sai sayayyan kaya mai kyau amma bai san yaga 83 kayan jikin wanda ya sayawa ya yaba kwalliyar da aka yi da su din ba, to ko meye amfanin sanya kayan nashi? Ina dosar kofar gidanmu na hango Mansur shi kuma yana fitowa daga zauren gidan namu ga alama nemana yaje yi daga in da ya hango ni ya saita kyamararshi ya soma daukana a hoto, kan mu gamu yayi min hotuna da dama. Muna gamuwa da shi ya soma furta min dadadan kalamanshi masu sanyaya zuciya da sanyata cikin wani hali na natsuwa da farin ciki. Alfarmarki nazo nema, ta me fa? Ya sake kallona cikin wani yanayi tanfar dai tsoro yake kar ya nemi alfarmar bai samu ba. Cikin natsuwa ya ce min gaishe-gaishen yan uwa da abokan arziki nake so in roke ki muje tare. Ba wani tsaya yin wani tunani ba na ce mishi muje, dadi ya kama shi don in kara mishi jin dadin kumá na sake ce mishi, jira ni ina zuwa, na wuce na nufi gidanmu da nufin in canza kayan jikina in sanya wanda yayi min. Cak! Naja na tsaya a cikin zaure ina sauraron maganar da nake ji tana fitowa daga bakin mutumin da zuwanshi gidan namu ya zama ka'ida in bai zo ba wannan satin to sati mai zuwa za ka 84 ganshi ya zo, a yanzu kuma har da tsaraba ya ke zuwa mata da shi Ba dai kin ce kin ba shi wadannan kajin yaci ba, ta ce eh, to ki gaya mishi kawai ba zai yi jayaiya da ke ba, cikin zuciyata na ce oh'oh shi kam Babana ko me a ke nema a wurinshi kumna yanzu oho? Sanin da nayi Mansur yana jirana shi ne abinda ya hana ni tsayawa in ji zancen nasu sOsai, na shiga gida kawai na wuce su na shiga dakina na canza kwalliyata cikin kayan da Mansur yayi min wanda suma suka yi matukar karbata. Na fito na same shi yana tsaye ni yake jira yana ganina ya saki wani lallausan murmushi, kin san kuwa al'amarinki yana bani mamaki, da sauri na tambaye shi mamakin, sai ya kalle ni ya ce min, to komai ki ka yi kyau ki ke yi Maryamu, komai ki ka sa yayi miki kyau ko kin taba sanin ke din daban ce da duk wata budurwa da ki ke gani? Ai ni a wurina da za ki bar ni da na yi wa kaina alfarma na daina kiranki da suna Maryamu in koma kiranki da sunan (Ta fi su) saboda ke din daban ce a cikin 'yanmata duka. Murmushi kawai nayi naje na shiga bayan motar da Mansur ya tanada don zuwa gaishe- gaishen yayin da shi da Isiyaku suke gaba. 85 Babu inda ba mu je ba har gidan Yaya Dijah da Jumare da Yakumbo Halima, shima ta bangarenshi mun je mun gaida tsohuwar Kakarshi ba mu dawo ba sai bayan La'asar. Ina fitowa daga cikin motar na hangi Mubarak a kofar gidansu ta wajen gidanmu yake fuskantowa abinda na tabbatar shi ne dawowana yake son gani. Yana hango nin kuwa na ganshi ya dunfaro gidanmu yana tahowa nayi maza na shige cikin zaure don kar ya same ni a waje. Ina shiga sai gashi ya shigo, sannu da zuwa nayi mishi gaisuwar duk da ba dabi'ata ba ce yinta bai 6ata lokacinshi wajen amsata ba. Me ke tsakaninki da Mansur? Abinda kawai ya bukaci sani kenan, na dan yi shiru saboda nauyinshi da nake ji, sai naji ya ce min kiyi magana mana, gaya min kawai ai gara in sani, me ke tsakaninki da shi? Cikin karfin hali da jarumtaka na bude bakina a hankali cikin natsuwa na ce mishi, saurayina ne, to da kyau! Abinda kawai ya fadi kenan ya juya ya fita. Ya bar ni tsaye a cikin zauren sai dai maimakon in wuce in shiga gida nima kasa motsawa nayi a wurin ban san dalili ba har kusan minti uku da fitan shi ina tsaye a inda ya bar ni. 86 Sunkuyar da kaina kasa nayi ina kallon faratun yatsuna can cikin zuciyata dai ba zan iya cewa ga takamaiman abinda nake tunani ba. Motsin da naji ne ya sani dagowa cikin sauri, Mubarak ne ya sake dawowa gabana yayi mummunan faduwa saboda yanayin da na gani a tare da shi, tsoro ya kama ni nan take naji jikina ya dauki rawa, dukana zai yi ko me? Bacin rai da ke fuskarshi ba mai tsanani ba ne, sai dai da ganin yanayin da ke tare da shi ka san ya shanye wani abu saboda yanda idanuwanshi suka canza launi. Me ki ka ce min yana tsakaninki da Mansur? Shiru nayi ban iya ce mishi komai ba, kiyi magana magana ki sake gaya min irin maganar da ki ka gaya min dazu. Wani shirun na sake yi ban tanka mishi ba. Ai ban san kin iya rashin kunya ba sai yau, kina nufin don kin koyi rashin kunya sai ya zama za ki ya cin fuskata kici mutuncina ki bata min, to ai ban san saurayinki ba ne shi yasa na bar ki kina hidimominki, to anma tunda ke da bakinki ki ka gaya min to ina so in sake ganinki da shi ki ga abinda zai faru. Ina so in sake ganinki da Mansur ko in ji labarin an ganku tare ki ga yanda zamu kare ni da 87 ke, mara kunya kawai, wacce ko wayo bata da shi, yana fadin hakan yayi shiru sai dai bai juya ya fita ba. Sake tsare ni yayi yana kallona wani irin kallo da ba zan iya tantance irinshi ba, saboda kainaa a sunkuye yake hawaye suna ta zubo min, yana kuma kallonsu amma bai sa shi tafiya ya kyale ni ba. Tun kwanaki ki ke nema kiyi min wulakanci me nayi miki? Me nayi miki da ki ke so sai kin bata min rai? Ki gaya min in laifi ne in baki hakuri in kuskure ne in gyara, amma ba zan lamunci, rainin hankali ba daga wurinki. Ya juya ya fita nima na lallaba na shiga gida na hau gadona na kwanta, kuka sosai na kama yi. Asabe tana kallona tun tana shiru har ta soma magana ita kadai, in dai namiji ne matsalarki ai kuwa ba ki yi kukan ba tukuna musamman ma wannan dan iskan da ki ka likewa mai kwashe- kwashen tsiya, ban dai tanka mata bá. Ban sani ba ko kashedin da Mubarak ya yi min ne ya tsorata ni na kasa sake fita tare da Mansur, ban iya sake zuwa ko ina ba sai dai kawai in yi kwalliyata in zauna a gida. A 'yan kwanakin da na zauna a gidan nan ne na gane Babana da Babah Lantana ba karamin 88 dasawa suke yi ba, ji da shi Babah Lantana take yi ba kadan ba, ko abinci zai ci sai ta zauna ta tasa shi a gaba yana ci tana kara mishi tana yi mishi wata hira mai dadi da zata sa shi ya ji natsuwa cikin zuciyarshi. A zuciyata na ce wato itama dai matar nan ta iya komai na kyautatawa raini ne kawai da wulakanci yasa bata yi, ko wanene ta samu yayi mata wa'azin da ta gyara halinta? Oho, tunda ko nima dai wannan sallar sau biyu tana zuba abinci a kwano tana bani, ban karba ba ta sake kawo min soyayyun kaji nan ma naki saboda zuciyata bata kwanta min kan in ci ba, amma duk da haka hakan da tayi yasa al'amura sun dan yi sanyi fiye da da. Kwana bakwai a ka yi Babana ya fara fita, Babah Lantanan ce kuwa ta ce babu in da za shi sai an kwana bakwai, ya zauna shima ya huta a cikin iyalinshi. Rannan ya fita ya dawo naji shi yana ce mata yau dai kasuwar ta dan yi nauyi ga abinda a ka samu, na kasa kunne in ji abinda zata ce mishi tunda kullum ya dawo ya ce mata babu kasuwa fada take kamawa tayi ta sababi tana fadin ya dai 6oye kudinne kawai amma wane irin rashin kasuwa bayan dazu ta wuce ta wurin taga yara sun kewaye shi suna sayen abubuwa? 89 Abin mamaki sai naji yau ta ce inishi to ai yau da gobe kenan, Mallam a ka ce wai kayan Ubangiji in babu kasuwa ai sai ka dawo gidanka ka hau sabon gadonka kayi kwanciyarka ka wataya. Ta soma zuba mishi abinci yana ci yayinda ni kuma can cikin zuciyata nake fadin to da haka ki ke yi mishi wa zai damu da rashin kirkinki balle har aje ana yi miki rashin kunya. Suna cikin hirarsu nima ina sha'anina a daki sai na jiwota tana tambayarshi, to in kirata ne ka gaya mata? Yayi shiru bai amsa ba, in ban da uh'uh din da na ji ya fada, don haka na kara kasa kunne wajen sauraron magana tasa sosai don na gane da ni a cikin zancen nata. To amma ai yau ne kayi alkawarin gaya mata, da safe ka ce a'a yanzu da yamma ka sake cewa uh'uh to me ka ke nufi? Ko za ka saba alkawari ne? Dattijo da saba alkawari? Ya sake yin shiru. Ai fa aikinka ke nan in ana magana da kai kayi gum da baki kamar wani mai cin najasa, taja wani mummunan tsaki alamar dai ranta ya soma 6aci, ko ma ya riga ya bacin, ai dama nasan karya ka ke yi ba za ka iya gaya mata ba ka ce za ka iya, abin bakin ciki wai uba yana tsoron 'yarshi. 90 To in ba za ka iya gaya mata ba ni in gaya mata tunda ni kam ai ba tsoronta nake ji ba yayi maza ya ce mata uh'uh to in kira maka ita? Yayi shiru ba ga ta can a daki ba? Kai Mallam kai kam ba ka da dattaku, kai tir!. Kalaman nata suka sanya ni naji wani iri, ga bakaken maganganun da take ta gayawa Babana ina ji, ban da haka kuma na tabbata ko wace irin magana Babah Lantana take son ya gaya min to ba mai sauki ba ce, kan haka sai naji maganganun nata sun sanya tsigar jikina yana tashi. Ban iya ci gaba da zaman da nake yi ba, mikewa nayi na fito nazo na durkusa a gabanshi cikin natsuwa da girmamawa na ce mish1 gaya min maganar da ta matsu in ji Baba, ko menene gaya min kawai zan iya dauka. Ai kai Mahaifina ne, kai ka rene ni ka kuma yi min duk alherin da uba ke yiwa da, na kuma godewa Ubangiji kana sona ba ka yarda ka bayar da rikona ga kowa ba, don haka babu wani dalili da zai sa ka rinka sa ranar gaya min wata magana kana dagawa tunda dai kasan dole ne zan ji ta to gaya min kawai zan fi jin sauki in na ji ta a bakinka maimakon a ce wani ne zai gaya min. A hankali ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min aure zan yi miki Yaacuwuna, na daga 91 ido na kalle shi, damuwa ce karara a fuskarshi ko ni da ya ce zai aurar ba tare da nasan mijin da yake nufin banin ba babu irin wannan damuwar a tare dani, tunda dai nasan a tsakanin biyu ne za a yi daya, ko a baiwa Mubarak ni ko Mansur, wanda duk aka yi da shi zan zauna tunda su dukansu ina da dalilan da za su sa ni zama da su. Na kawar da wannan tunanin daga zuciyata na daga ido na kalli Babana cikin natsuwa na ce mishi Baba wa ka ke nufin baiwa ni? Na dan sunkuyar da kaina kasa don kunya da girmamawa. Auren ai na zumunci ne, cikin hanzari na dago na kalle shi a zuciyata kuwa dadi ne ya kama ni, wato dama Baba yana sa ne da zumuncinshi da kullum ake yi mishi gori a kai, wato dama yayi niyya a kaina ne zai gyara zumuncin nashi ta hanyar bada aurena gare su? Ai kuwa dai duk wanda ya baiwa ni zan zauna da shi da zuciya daya in kuma yi mishi ladabi da biyayya irin na aure. Amma don in kara samun natsuwa cikin zuciyar tawa sai na tambaye shi cikin 'ya' yan wanka ne ko na kannenka za ka baiwa ni Baba? Sai da yayi gyaran murya saboda yanda ta make take nema kuma tayi rawa kafin ya iya ce min a'a wannan dan uwan uwar taki Lantana ma 92 zuwa gidan nan Mahammadu Nalami shi zan baiwa ke, don kara karfafa musu zumnuncinsu ai kin san abokin wasanta ne? Kadan ya rage in suma a tsugune saboda tsananin kaduwar da nayi. Nalami fa kace Baba? Ya gyada kai tare da cewa eh shi nace, ban san yanda a ka yi ba sai tsintar kaina nayi ina yiwa Babana tambayoyi. Zumuncin Babah Lantana yasa ka baiwa wannan mutumin ni naka zumuncin fa Baba? Shiru yayi yana kallona bakina ya sake yin subuta ya ce mishi, ba zan auri Nalami ba Baba, domin babu abinda ya hada ni da Babah Lantana balle zumuncinsu da har zan je ina auren danginta. Tuni na soma kuka ina fadin me nayi maka Baba? Me nayi maka da ka ke taimakon masu son ganin nayi bakin ciki a kaina? A gabana kayiwa Innata alkawarin ba za ka bada rikona ba ne saboda ba za ka iya rabuwa da ni ba to me yasa za ka bada aurena a inda kasan zan yi bakin ciki. Nan da nan kawai sai naji zuciyata tana raya min babu abinda yasa a ke yi min irin wannan musgunawar illa don uwata ta rasu, Yaya Dijah da aka yi aurenta Innarmu tana raye ai bata irin wannan tozartawar ba nan take na soma kuka da iyakacin karfina. 93 Kan ka ce meye wannan sai ga makwabta suna shigowa tambayar me ya faru? Babah Lantana ta tsaya tana yi musu bayani ai ba komai a ka yi mata ba tunda ga uban nata nan a zaune wai daga yace zai bada aurenta ga wani dan uwana shi ne take wannan borin kar ku dada kar ku rage. Maimakon a gamsu da bayariin nata sai kuma a hau salati dan uwanki? In ta ce eh sai a gyada kai a'a tayi ihu, to wane dadinki taji balle aje ana baiwa wani dan uwanki ita? Wannan ya gayawa wannan mutane sai shigowa suke yi yayinda ni kuma nake kwance a kasa ina ta faman kurma ihu. Gaba daya a wannan lokacin fatana bai wuce dayan biyu ya faru da ni ba, in ma dai Babana ya tausayawa kukan da nake yi ya fasa bada ni ga Nalami ko kuma azabar kukan yayi dalilin da nima zan bi bayan Innata in huta da bakin cikin zama da Babah Lantana. Ban san yanda aka yi ba har Umma taji tazo ba sai jinta nayi ta katse Babah Lantana tana mnai cewa, In ban da 'ya'yan yau ba su san biyayyar yaye ba yaushe za a ce ka tarawa ubanka irin wannan Jama'ar mu da yaushe? Umma tayi maza ta ce mata ke dai kam Lantana ba ki san biyayyar yaye ba da kin santa kuwa da ba haka ba, da ba ki a1kata ma irin abubuwan da ki ka aikata ba. 94 Ke wannan sharrin ma da ba ki kulla shi ba, me yasa baki ba shi tsohuwar yarki da ki ke tashe da ita shekara da shekaru ta rasa mijin aure ba? Wannan ai ba huruminki ba ne ki ka shiga don kuwa ba ki yi mata rikon da za ki zartar mata da irin wannan hukuncin ba. Da sauri Babah Lantana ta shiga fadin ai ni ce ma ni ce na hada? In ke ce in ma ba ke ce ba ce dai duk daya, yi kokari kiyi hakan a kan "yarki da ki ka bari tana tanbada kina kallo in ba nema ki ke sai taja miki irin abinda kema ki ka jawa iyayenki ba. Mero kam ai tayi sa'a tana da uban da za a sa shi yayi mata aure da mijin da aka san ba nata ba ne don a cutar da rayuwarta, sai dai ba tanan take wai an danne buduri a ka yace ai ba nan take ba. In kin yi ne don kin ga duk abinda ki ka yi mata a zaman da ki ka yi da ita bai ishe ki ba ruwanki kema kina da 'ya'ya abinda ka shuka kuma shi ka ke girba, mai rabon ganin badi kumna ko ana dakawa a turmi sai ya gani, haka ana muzuru ana shaho zakaran da Ubangiji ya nufa da cara sai yayi. Don haka tashi mu tafi Mero, ta sunkuyá ta kama hannuna na mike na tashi tsaye tana fadin ke ai kin yi arziki da Ubangiji ya ce yayi miki miji 95 wasu ba gasu nan ba sun tsufa a titi da suna da iyayen na gaske ai da ba su zuba musu ido ba. Ki tafi da ita ina za ki kaita? Ko za kije ne ki kara bijirar da ita? Umma ta waiwayo ta kalleta cikin nutsuwa tace mata ai mu ba mu bijirewa iyayenmu ba balle mu haifi masu bajirewa, ba zan bar miki ita ba ne balle kiji dadin cusa mata wani bakin cikin tunda ke ba Imani ne da ke ba. Babu wata za dai ki kai mishi ita ne yayi abinda ya saba, ta ce eh zan kai mishi ita biyo ni ke kuma ki hana ni ko ki kwace ta. A kofar gida muka samu Mubarak yana tsaye, ganina tare da Umma ya sa shi wucewa gaba ya fara tafiya muna shiga gidan yaja ya tsaya, wacce irin musiba ce wannan Umma? Ta ce, Eh ai rayuwa ta gaji ganin al'amura da dama sai addu'a kawai don haka ba' yana nufin komai ya kare ba ne. To me ya saura Umma? Tayi murmushi tare da fadin da yawa. Ni kam in ban da kuka babu abinda nake yi, duk bayanan da Umma ke yi na zai wuce watarana kuma sai labari jinta kawai nake yi kullum abinda a ke gaya min ke nan wata rana sai labari, har yanzu kuma ban ga alamar abubuwan za su wuce ba tunda kullumn wasu muna nan abubuwan sai kara samuna suke yi, duk wata fitina 96 ko tashin hankali da na gani a rayuwata ban taba ganin abinda ya kai cewan da Babana yayi wai zai ba da aurena ga Nalami ba, in dai ba tashin hankalin rasa uwata da nayi ba ne. Ana cikin haka sai ga Baban Mubarak Albaji Muhammadu ya shigo, menene ne haka a ke ta kuka ke kuma kin tasa ta a gaba kina kallonta? Umma ta shiga rattaba mishi bayanin abinda ya faru. Hankalinshi a kwance ya ce to ba shi kenan ba ina ce yarshi ce? Kowa yayi shiru har da ni din saboda ba zan iya ci gaba da yin kukan a gabanshi ba, jimawa kadan sai kuma yayi tsaki kafin ya sake cewa amma bai kyautawa kanshi ba da ya bari a ka maida shi abinda a ke cewa an maida shi din, bari in je wurin Mallam Sule mu tafi wurin nashi tare muji yanda za a yi. Umma ta ce, To Ubangiji yasa muji alheri, ya ce amin. Nayi kukan bakin ciki a wannan lokacin har sai da na rasa hawayen a idona, na rinka jin tanfar ni din komai nawa ya kare ciki kuwa har da farin cikin rayuwata. A duk lokacin da Mubarak ya zaunar da ni da Dufin rarrashina ko ba ni hakuri kan balin da nake Ciki bana sauraronshi, saboda ni kam can cikin Zuciyata bana jin haushin Babana da mutane ke ta 97 fadin maganganu marasa dadi a kanshi, nafi iin Ciwon Mubarak gani nake tanfar inda yayi wani abu mai karfi da wuri tun lokacin da nayi ta fata da burin yayin watakila da wannan abinda ya farun bai faru ba. To wai sai a yanzu da Babana ya riga ya furta wannan maganar shi ne suke ta faman zirga-zirga aje wurin wannan aje wurin wancan ana kamun kafa wanda bana zaton zai yi wani tasiri don magana daya kawai Babah Lantana zata yi ta birkita komai shi ne kai din ba Dattijo ba ne tunda ga shi kayi alkawari za ka canza. Daga ranar da Alhaji iuhammadu yace bari ya kira Mallam Sule suje wurir Babana zuwa cikar kwana bakwai ya tura wa Bapaia mutane daban daban har sau biyar daga ciki akwai tawagar da Liman ya jagoranta ta Malamai wadanda suka yi mishi nasihohi a kan muhimmancin bayar da aire a inda ya dace wato bin kufu'i don a samu zimatu lafiya fahimtar juna da girmamawar da a ke bukata tsakanin miji da matarshi. Haka nan mai unguwa ya jagoranci mayan unguwa bayanshi Alhaji Muhammadu abokanshi Sun je har sau biyu. Yanda na samu kaina cikin kunci da bak ciki haka Mubarak ba zan ce ya fini ba ne, kawai don 98 ni kadai nasan abinda zuciyata ke ciki, amma ko daga jin irin aiken da Babanshi ke yi daya

Chapter 5 of 7