Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  HALIN RAYUWA 1 NA 07035586299 HAJ. HAFSAT C. SODANGI (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) 1 Hakkin Mallaka [m] Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat C. Sodangi ne GODIYA Godiyata har kullum ga Allah take Subhanahu ta'ala mai kowa mai komai, Makadaici, Mahalicci wanda a ke nufa da dukkan bukatu gwani mai hikima wanda yayi halittarsa bisa tsari na aure wato mace da namiji. Tsira da aminci su kara tabbata ga cikamakin Annabawa, shugaban Manzanni Annabin karshe Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe, wato ranar rarrabewa tsakanin karya da gaskiya (AIkiyama), Ubangiji yasa mu dace. Har wayau ina mika godiyata ta musamman ga daukacin makaranta littattafaee cikin kasa da waje, Ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karfafa zumuncin da ke tsakaninmu. Na gode, Haj. Hafsat C. Sodangi 6/7/1434 2 GODIYA Godiya mai dumbin yawa gare ki. Rabi'atu Faruk Jauro (Ministry of Commerce and Industry Yola, Adamawa State) Da Zainab Sunusi Kofar Gabas Danbatta Zainab Abarshi Yawuri GAISUWA Gaisuwar littafin naka ne Muh'd. Kabir Sodangi (A.T.B.U BAUCH) 3 LITTATTAFAN SODANGI: Uwar Miji Naga Ta Kaina Rabon Kwado... Cikar AIkawari Wayyo Duniya Yi wa Wani... Abu Naka... Mata Ma su Duniya Nufin Allah Kifi Na Ganinka.. Daga Kin Gaskiya.. Da Kamar Wuya.. Mai Uwa. Duk Daya.. Mata Da Kicin Dinsu Wacece Ni? Wata Fuskar.. Mijin Ta ce Garin Banza... Ga ni Gare ka Biyan Bukatar Rai Shamaki Hattara Mata Masu Duniya Kyautata Ayi Dai Mu Gani. Tabbataccen Al'amari 4 HALIN RAYUWA 2 Washegari da safe gaba daya mutanen gidan kowa a cikin natsuwarsbi yake, in ban da Babah Lantana da ke ta faman zirga-zirga tana fadin maganganu kamar yanda dama al' adarta take in har wani abu ya 6ata mata rai. Haka kawai a cizan mun yarinya sannan wani Rato ya shigo har cikin gida ya dakar min yaro, to wane irin rashin yanci ne wannan? Ai kayi hukuncin da za ka yikawai in gani. Lalle ne kuma kayi hukunci me tsanani don in ba haka ba kam... Sai tayi kwafa tare da fadin "Hanya ratatata nuna alamar abinda zai farun ba karamin al'amari ba ne. Koda Babah Lantana bata furta irin wadannan kalaman ba zan kasance ne a cikin natsuwata sosai don na saba jinta tana bada umarnin a rama cizo ko da kuwa bayan shekara guda ne, to balle ni da nayi cizo jiya, cizon kuma ya haifar da sakamako mai tsanani don daga Asabe har SaHau babu wanda bai samu kanshi cikin wani hali ba matsananci. Asabe dai tana kwance tana fama da matsanancin zazzabi, Sallau kuwa bai iya rufa bakinshi ya daina kurma ihun da yake kurmawa ba, sai da aka kira Mallam Bahago yazo ya gyara mishi targaden da aka yi mishia kafada. Don haka sanin a nayi Babana yana cikin gidan nan dai shi ne abinda ya zaunar dani a cikinsh da 5 kuma ganin Asabe a kwance tana fama da kanta nasan a haka ba za ta ce zata rarume ni don ta rama cizon da nayi matan ba, amma duk da haka ina ganin Babana ya dauki kwandon tumatirinshi da nufin fita. Nima zan yunkura in bar musu gidan don ba zai viFu in 2auna tare da su ba tunda nasan zama da su din ba zai haifar min da da mai ido ba. Ina cikin wannai tunanin ne na bango Babana tsaye a tsakar gida rike da kwandon tumatirinshi a hannu alamar zai fita kenan nayi maza na jawo gyalena kusa da ni, don yana fita in bi bayanshi sai kawai naji ya ce ing Yaacuwuna take? Nayi maza na ce Gani nan Baba, na fadi daidai lokacin da na tsuguna a gebanshi, karki sake li fita daga gidan nan. Gabana yayi mummunan faduwa, "Kin ji na gaya miki ko ba kiji ba?" cikin sanyin jiki na ce mishi naji Baba. Na mike tsaye jikina a sanyaye na koma dakin na Zuna na jawo littafina ns karatu ina dubawa sai dai gaba daya hankalina ba a kan shi ya ke ba. "Kai Sallau!" Sallau ya yunkura ya fito gani Baba, shirya ka bar min gida ka koma inda dama ka ke, tunda ka zo kana yi min fada a gida shima wancan din na aika a gayawa Babanshi ya gaya mishi kar ya sake shigo min cikin gidana." gama fadin hakan yasa kai ya wuce zai tafi. 6 Babah Lantana ta bishi da kallo irin na takaici tare da fadin "A hau, ahau wannan shi ne hukuncin naka? Taja wani mummunan tsaki ta juya taga Sallau da ke tafiya da kyar yana rike da ledar kayanshi a hannu zai bar gidan don cika umarnin da maigidan ya ba shi. Sai kawai naji ta daka mishi tsawa "Ina za ka da wannan jikin naka? Maza maida ledar nan kayi kwanciyarka ka huta, ai ko za ka bar gidan nan sai bayan kun rama abinda a ka yi muku tukuna. Cikina ya badasautin kulululuu! Don nasan me maganar tata ta ke nufi Sallau ya koma daki yayi kwanciyarshi yayinda lia ma ta koma kan hidimominta da maganganun da take ta yi. Ana cikin haka ne naji wata irin murya tayi sallama a bakin kofar shigowa tsakar gidanmu. Muryar ta mata amma abin mamakın shi ne da sunan maza naji Babah Lantana ta kira bakuwar. "Nalami ne kuma har cikin gida ba za ka tsaya daga waje ka ce ayi maka iso ba? yayi 'yar shewa tare da 'yar dariya kafin ya ce "In ba kiyi min haka ba ai ba ai ba ki cika 'yar halak ba, ai ba zan ce kin amsa sunanki na Butulu' ba ko ba sunan da dama yan gidanku suke kiranki ke nan ba? Butulu ai dama kazo ne har gidan mijina ka ci mutuncina? 7 Yayi maza ya ce "A'a ko kadan ai darajar aure ya shige haka komai iya shegenka in har ka samu ka shiga karkashin inuwarshi to ka zama mai mutunci sai a mutuntaka saboda darajar shi, don haka ba zan ci mutuncinki a gidan mijinki ba. To tunda ka fadi haka da bakinka muje daga waje, ya ce a'a nan kuma daya a nan din nan zaan zauna bau ce zan shiga dakinki ba balle kiyi tunanin zan hau kan gadonki in kina tsoron kar mijinki ya shigo ya ganin ne babu komai yana shigowa sai in gyara zama in maida kaina kanin Babanki in kuma ki ka ce za kiyi min iya shege to kema kin san ni babanki ne a nan ma. Ina iya zuwa har wurin 7aman nasu in yi koma1, ai ta can na biyo an nuna min shi,don haka dauko tabarma kawai ki shimfida min." Ta kawo tabarmar tana shimiidawa yayinda ni kuma zuciyata ke ta faman kai-kawo a tambayata wane irin mutum ne wannan? Na yunkura na matsa na kebe ta matsin kyauren dakin namu mutum har mutum yasha babbar riga har da hula zanna sai dai kalamanshi. "Ashe har mazaunai ne da ke haka? yayi tambayar daidai ya kaiwa mazaunan nata duka gabana ya sake faduwa, tayi maza ta kars daure fuska kafin Nalami ba ka da mutunci ya gyad zama 8 kan tabarmar ya ce, Eh komai ma kina iya gaya min ni na zo. Ta ce to ka tafi mana ko ni na kira ka? Ya kalleta a'a ba ke ba ce ai kin samu wurin zama sai cin mutuncin Jama'a ki ke yi ja' ira kawai mara tuna baya, kai bebi baki da tuna alheri. "Dakata ka ji Nalami, na daina amsa wannan sunan duk wani abu makaman cin wannan da ka sani na daina shi, mijina mai mutunci ne. " Yayi maza ya ce "Gaskiya kam gaskiya kam ai na ganshi ruan Malamai ne da shi inda tambayar take dai na yanda aka yi ya iya zama da ke ne." Ta zuba mishi ido cikin takaici ai ba za ka bari muyi magana ta gaskiya ba ke nan? Ya tsura mata nashi idanuwan da suka fi kama da gauta saboda kaduwarsu kafin ya ce ai ba ki da ita ne, gaskiyar balle ayi maganarta da ke. Ta gyada kai tare da fadin to shi ke nan naji me ya kawo ka? A haka zan fara magana ina zuba tun ban ci komai ba? Ai sai ki kawo min da na shar kajin da a ka bani labarin kullum a ka zo' gidanki sai an ci. Yana cin naman da ta kawo mishi yana magana zuwa nayi in dangwali arzikinki tunda kin shigo cikin inuwarshi don kuwa nima babu irin taimakon da ban yi miki ba, sanda su sarka suke wulakantaki, ko sanda ki ka haifiyaran nan..." Tayi maza ta katse shi "Ba fa tarihi ka zo karanta min ba, arziki ka ce ka zo ci." Yayi maza ya ce, "Eh 9 haka na ce, to kai duk abinda ka ke da shi bai ishe ka ba sai ka zo wurina ni da nake zaune a dakina ko sana' a bana yi? To ai ku ne masu rufin asirin amma na wajen nan menene ne a cikin abin? Kin san fa shari'ar nan da a ke ta kafawa ta karya darajar al'amuran namu kana gaba daya ke dai ayi shiru kawai tunda kana Musulmi ba zai yiwu ka buda baki ka ce ba ka ji dadin abin ba. Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta mika mishi to ungo rike wannan ko sigari ka sha, lokacin ne na tuna farkon zuwan Babah Lantana na gidanmu har sigari sha take ji amma yanzu kam ta daina don na ma manta in ban da yanzu da naji ta ambata da bakinta. Maimakon ya karba yayi godiya kamar yanda al'adar wanda a ka yi wa kyauta take sai kawai naga ya harari abinda ta ba shin ya ce kyautar matsiyata za ki yi min? ko da na ce miki ba ni da harka ai kin san nafi Rarfin irin wannan kyautar don kin san kont waye? To in tsaya daga waje mana in yi bara ki bai wa yara su kawo min sadaka, ai a sauwake abinda za ki bani in bar gidannan bakina alaikum jaka guda ne. Da sauri ta ce mishi a'a buhu guda ba jaka guda ba gaka guda lafiya ce da za ka ce in baka ita ina na ganta? Kai barawo ne? A'a to sai in gyara zama ai 10 sai kin samu, to sai in gyara zama ai sai kin samu to ma me za ki kira ni kuma oho ni dai kin san ba Delu ba ce da ta taimake ki ta rinka yi mii zirga-zirgar gidajen Malamai da 'yantsubbu bayan irin wahalar da tai tayi miki da 'ya'yanki Sai da ki ka samu kan miji ki ka mallake shi taf ya zama bai da katabus sai naki sannan ki ka yi mata irin tukuicin da ki ka saba yi wa wadanda suka saba taimakonki wanda yayi dalilin da suka rada miki sunanki na ainihi 'Butulu' ki ka koreta ki ka ce kar ta sake zuwa miki gidą don ba ki yarda da, ita ba." "Ita taje ta turo ka ke nan? " kan ya bata amsa sai naji yaro yana magana a tsakar gida wai Maryan ana kiranta a waje." Da sauri Nalami ya kalli Babah Lantana cikin yanayin rage murya dama ba mu biyu ba ne a gidan shi ne ba ki gaya min mun yi maganar a hankali ba? Ba ki kyaufa ba Lantäna, ai wata kusar tafi wata. Ai in da ná sani ba zan yi îrin wadannan kalaman wani ya ji ba, na fito zan wuce in je'kiran da a ke yi min ban sani ba ko zaman Nalamin ne ya hanata tuna min da dokar da Babana ya. kafa mini ko kuma don taga ita ma bata bi dokar ba ne oho, tunda nasan tafi kowa jin an ce ana kirana a waje. Ina fitowa muka hada ido da Nalami barin komai yayi ya shiga bina da kallo, wani irin kallo da yafi 11 kama da na kidima, uh' uh uhhh, wacece wannan Lantana? Tambayar da naji shi yana yi mata kenan yayin da ni kuma na shige cikin zaure na bar su a nan ban jiwo amsar da ta ba shi ba' lna daga cikin zaure na hango Mubarak a tsaye daga waje yayi kwalliya sosai. Karo na farko da ya taka yazo kofar gidanmu tunda ya dawo daga Ibadan, sai ko jiya wannan kuwa naji an ce wai Babah Sumaye ce da taji ihun da nake yi ta aiki Almajirinta da gudu yaje ya gaya mishi abinda ke faruwa. Daga cikin zauren naja na tsaya ban ce mishi komai ba, shi ya matso bakin kofar zauren ya tsaya kina da wata matsala ne? yayi tambayar yana kallona, na girgiza kai a hankali nuna alamar babu. Ya miko min ledar da ke hannunshi cikin zauren na mika nawa bhannun na karba ya juya ya tafi ba tare da na ce mishi komai ba. Na koma baya ta cikin lungun zauren saboda jin ledar da nauyi ga kuma sai da na nemi wuri mai dan kyau sannan na zauna na fito da abinda ke ciki, gasasshiyar kaza ce katuwa tayi matukar gasuwa gashin injin ga yaji a wata takardar ga kuma ruwan lemo na kwali mai sanyi. Lokacin ne na kara tuna har a wannan lokacin da agogo ya kai kan sha biyu da rabi ban sa komai a 12 bakina ba, da bai zo ya kawo min wannan kazar ba kuma to da ban san lokacin da zan samu abinda zan ci ba, ko a haka kuma Babana yake ganin zan iya tsare dokar da ya kafa min ta kar in tafi ko'ina? Oho! Ci nayi sai da naga na koshi sannan na dora ruwan lemon nan a kai sannan na mike na dauki saura na nade na adana shi a cikin gyalena, na shiga cikin gida har lokacin Babah Lantana magana take yi da bakon nata, sai dai a yanzu maganar tasu ta dan sauya da alamar sun dan samu daidaituwa. Yana ganina ya saki wani lallausan murmushi har hakoran Makkanshi suka fito guda biyu, kuma jajaye yana ganin mun hada ido da shi yayi maża ya sakar min signal da idanuwanshi. Nima nayi maza na galla mishi wata irin matsiyaciyar harara na wuce na shiga dakina. Wasu sabbin kwanukan abincin na gani wurin Asabe da alamun fitan da nayi ya kara bada damar da aka sake kawo mata wani abin. "Yanzu dai kin gani Hajiýa bani kawai abinda ki ka ga za ki ba ni tunda ga bayanin da ki ka yi min na halin da kike ciki in an kwana biyu ai zan dawo." Da sauri ta ce, "A'a-a'a ni kar ka dawo min gida in ba so ka ke ka kara min wata matsalar ba." "A aha, ai ke halinki ke nan ki ka sani ko zuwan nawa na alheri ne? To ta ina zuwanka zai zame min alheri ni kuwa?" ya yi murmushi "Uhum, Babah 13 Lantana kenan, ai na daina kiran sunan naki gatsau sai na sakaya miki shi da Baba ko kuma Hajiya. Ai kin san shi sunan Hajiya ma mai niyya yake nufi." "Kai dai karbi amma ni kar ka dawo min gida." Ya karba yana kirgawa, ai tunda na ce zan dawo zan dawo din ne kiyi fatan kawai dawowan nawa ya zame miki alheri." Ya tashi ya tafi. Ina zaune a gida Babana dokarshi a kaina ni kadai take aiki, Babah Lantana da 'ya'yanta babu abinda ya shafe su da ya dawo yazo ya samu Sallau a gidan ma bai ce mishi kala ba, sannan da zai kafa min dokar daina fita daga gidan sai ya manta bai sanya ta bani abinda zan ci dole ba. Duk da haka na bi umarnin da ya banin na in daina fita saboda magnar da Yaya Dijah take yawan gaya min in bi duk wani abinda zai sanya ni komai wuyarshi, kar in ki yi mishi yayya a kai kar kuma in lura da cewar wasa ba su yi mishi ba ni ce ya zama wajibi a kaina in bishi ba su ba. Ina zaune a haka cikin wani irin matsanancin hali in ba Mubarak ne ya kawo min abinda zan ci ba babu mai bani a hakan kuma ga barazana gami da wulakanci da neman tsokana Kowane lokaci a cikin maganar ake haka kawai sai ka ci Babah Lantana ta ce ah cizo? Ai sai kin rama a natse za ki rama kara warkewa dai kawai karfinki ya kara dawowa jikinki." 14 Ina kallo Asabe take fitowa daga wanka ta shafa maina tayi kwalliya da kayan kwalliyata in ta gama ta jawo akwatin kayana ta zabi wanda yayi mata ta daura, bana cewa komai saboda ina tsoron kar maganar da zan yin ya zama sanadin da zamu yi fadan da zata rama cizon. Sannan in ta gama abinda take yin sai ta mike ta bar komai a hakanshi sai na gyara wanda ni shi ne ma yafi bata min rai. Rannan da hantsi Mubarak yazo muna tsaye muna magana sai ga Sallau yazo ya wuce mu yana taku dai-dai, ya bishi da kallo kafin ya dawo da kallon nashi gare ni wannan ya bai tafi ba ne? na ce mishi ch, ya dan yi shiru jimawa kadan ya ce uhun, wato shi Baba ke kadai yake iya hukuntawa? Ban ce mishi komai ba sai ya sake kallona "Ba suyi miki wani abu ba ko? Har na ce mishi Eh, sai kuma naga to in ban gaya mishi ba wa zan gayawa? Don haka na kwashe bayanin komai nayi mishi, ya ce To babu laifi." Hirarmu muke yi sosai ina daga cikin zaure yana waje sai ga Asabe tazo zata shiga cikin gida, cikin dace zanina ne a jikinta kuma shi ya saya min shi, wani lalataccen kallo tayi mishi ta wuce da nufin shiga gida, ba karamar kiyayya Asabe ke yi wa Mubarak ba. 15 Duk sanda ta bude baki zata yi magana akanshi munanan kalamai take yi. Ina wuni Asabe? A lalace ta ce mishi lafiya, dan saurare ni mana minti bivu Ta waiwayo tana yi mishi kallo na sama da kasa. lafiya? Ta ce, bani da lokaci. Ya ce To je ki zan aiko agogo yazo ya gaya miki ama kafin ki ji sakon daga wurinshi kina shiga gida ki cire wannan zanin da ke jikinki ki wanke shi ki goge shi ki maida shi inda ki ka same shi ki ajiye. Ta ce ai ka san don ku kadai Bature yayi iinshi, bai tanka mata ba sai kawai ya kira wani yaro mai kimanin shekaru sha biyar da ke can gefe. Zo nan Isiyaku, maza haura can saman layi ko bayan layi kaje ka kira min agogo ka ce mishi ina nan na jiranshi yazo yanzu. Hankalina yayi matukat daurewa saboda ganin yanda jikin Asabe yayi matukar yin sanyi da jin an tura a kira agogo. Me ke tsakaninta da agogo? Kuma wancne ma agogo? Wadannan sune tambayoyin da suka tsaya a raina. Ga ni! Ta fadi tana mai kallonshi cikin natsuwa ya buda baki ya ce mata, in kin shiga ki gayawa Mamanku saboda nasan uwa ta gar tana karbar shawara wurin danta in dai tasan shi din mai hankali ne. Ki bata shawarar kar ta sake saki ke ko wani ku bugi Maryamu, kai ko da ita kanta ne kar ta sake? 16 Ku barta ta zauna lafiya a gidan ubanta don ta samu tayi ta bin dokokin da yake saka mata." A lalace ta kalle shi ta ce, in ba haka ba fa? Bai kau da ido daga gare ta ba ya ce in ba haka ba ranku ne zai fi na kowa baci, don ke da ni zan shiga cikin lamurranki ba kadan ba, kin san babu abinda ban sani ba a kanki zan sa a gayawa Agogo labarin Dangana kin kuma san abinda hakan ke nufi. Zan sa shi Agogon-ya kula min da lamarin gaba daya, ina yi muku wannan kashedin ne saboda kiyaye hakkin makwabtaka tunda akwai iyayenmu a tsakani, in kuma ba ki ji ba to kuje kuyi. Ke Maryam kar ki tsokani kowa a cikin su, amma mugun kallo idan suka yi miki ki gaya min, na ce to. Ya kau da kai daga garcta alamar maganar ta kare ta gane hakan don kanta ta wuce ta shiga gida ba a dauki lokaci mai tsawo bayan nan ba nima na shiga cikin gidan. Daga shigan da nayi na gane akwai wani canji a tare da Asabe don ban samu kayana a jikinta ba, Babah Lantana ce dai na same ta tana huci tana fadin, Aikin banza aikin wofi, ni kam ai rashin jini rashin tsagawa. Abinda zai hana ni dukan mutum bai tabo ni ba ne kawai, amma duka ai har da na tsiya zan yi mata 17 ko ma don in ga abinda za ayi min, sai nayi na wuce daki na barta tana maganganunta. Asabe dai na gane ta dan ji abinda Mubarak ya gaya mata, ana cikin haka sai ga Sallau ya shigo gidan "Mama ina so muyi magana da ke." Ta bar abinda take yi ta tsaya tana kallonshi, yayinda shima yaja ya tsaya Kerere a gabanta suna kallon juna, "Menene ya faru? tayi mishi tambayar tare da sauraron abinda zai gaya mata. "Wannan yarinyar ce nake so in ce miki ki fita hanyarta, ki bar kowa ya zauna lafiya, abinda kawai zan gaya miki ke nan." Da sauri ta tambaye shi, "Wacce yarinyar?" "Mero." Ya fadi sunan cikin wani yanayi. Kan ya gama karasa sunan ya ji saukar mari a gefen fuskarshi tau! Da iyakacin karfinta tayi mishi marin, a kan wannan shegiyar yarinyar ka ke yi min wannan maganar, in ce ko dan tumurmusan da yayi maka ne yasa ka tsorata da shi haka har yake aiko ka da irin wadannan maganganun ka gaya min? To na rantse sai nayi mata duka har cizon da ta yi wa Asabe sai na sata ta rama ko in rama mata da kaina, aikin banza aikin wofi, barazanar banza da wofi. Ni za a kawowa iya shege? 18 Ni fa nan da ka ke ganina ni ba matsoraciya ba ce, bana tsoron kowa duk iya shegen mutumn kallonshi kawai nake yi, yauwa! Ya'yan Babah Lantana sun dan shiga natsuwarsu kadan saboda ta ki yarda suyi aiki sosai da kashedin da aka yi musu wanda ya tsorata su, amma duk da haka Asabe ta fita hanyar kayana ta kuma kiyaye yi mun wulakanci. na kai tsaye. Illa iyaka dai ba ma magana da juna. Ina zaune a cikin gidan babu mai magana da ni in ba Mubarak ne yazo ya kira ni ba, shi kanshi Baban nawa gaisuwa ce kawai take hada ni da shi, amnma bayan nan babu wani abu. Tsananin kewa da kunci suka tarar min cikin zuciyata, na gane babu abinda yafi mu'amalla tsakanin mutum da mutum dadi, wanda ya rasa abokin mu'amallah kuma to ba karamar wahala ce ta same shi ba. Ana cikin wannan haki na kamu da wani irin matsanancin rashin lafiya, zazzabi mai zafi gami da mura ga matsanancin ciwon ciki saboda lokacin al'adata ya gabato, babu wani taimako da nake samu daga gidan, sai dai in Babah Lantana taga ina rarumen abinda za ayi ko zan ci, saboda yunwar da ke yawan damuna, sai ta rinka fadin ba dai kin ce da ni za ki yi ba? Ai mun sa kafar wando daya ke nan ni da ke, naga wanda zai fara zare kafarshi. 19 Mubarak yazo duba ni da yamma yana daga waje ina cikin zaure, yanzu ke kin rinka zama da ciwo ke nan? An ce ki fito a kai ki asibiti kin ki, shi Baban ba ya ganin irin ramar da ki ka yi ne ya bar ki a haka? Ban ce mishi komai ba na juya na shiga gida ina rike da ledar sayayyar da yazo min da ita. Ina shiga daki na zauna na bude ledar na jawo robar nono zan sha don kuwa nasan barin da jikina ke yi bana ciwo ba ne har da na yunwar da nake ji. na gama shan nonon na dawo-dashi gaba daya ta hanyar yin amai mai wani irin yawa da wari,

Chapter 1 of 7