hakan ma alfarma yayi maka saboda wai Company sa yana da ma'aikata da yawa zaka dinga kai yaransa makaranta daza man ban zan da kake yi ka gama karatu ba aikin yi..,
Runtsai idanuwan'sa ZAHID yayi yayin da jijiyoyin kasa suka fito raɗa raɗa kanin mahaifinsa yana da damar da zai kaishi ko ina yayi aiki karatun ma dayaya ya ƙara sa ba inda beje ba neman aiki takardun'sa basu da wasu tangarda da first class ya fita amma ko ina yawa an musu baƙin shafi ba'a daukar sa da yayi wannan aiki gwara ya wuni beci ba ko da miliyan zai bashi akwai ranar da yaga yar tasa ta baɗa mai ƙasa ta wuce shi talauci hauka ne da ya zauna a inda za'a dinga hulakanta shi gwara ya bar gurin cikin son ya fahimtar da mahaifan nasa yace '' malma bawai zanƙi bin umarnin ka bane a'a ina so na tsira da mutunci na kaga nan gurin da nake zuwa ina dan samun abin da zan rufawa kaina asiri ba kyara ba hantara amma can sai abin da na gani kuma ba lallai zuciya ta , iya jurewa ba kaga na bata zumuntar da ke tsakanin mu bana so na zama nini silar rushewar wannan ahali koda zuwa nayi na faɗa muku za kuji ba dad'i ballantana bazan iya faɗa muku laifin dan uwanku ba ni kuma matsayin mahaifi yake a guri na, aiki lokaci ne wata rana sai labari bakowa aiki haifa da arziki ba kowa sai da ya sha gwagwarmayar rayuwa nasan abin da kake hange karfin ka ya kare ga najwa ga joud ga Areej wacce lokacin ba zaka iya yi mata komai ba saboda shekarun girma sun ƙara cim maka yanzu ma insha zamu zame muku katanga ni da dan uwana duk wani abu da ake yi ana samun halak zamu bi musa mo muku dan rayuwar mu ta inganta amma wannan aiki na Alhaji bazan iya ba zato yake yi haka zamu dawwama to insha'Allahu dan zaki zai girma alfarmar annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama wani ma sai ya more mu sai yaji daɗin mu karatun yaran nan insha'Allahu bazan gaza ba zan dauke shi har matsayin da zasu sami ilimin da suma zasu tallafi na kasan su...
Limshe idonsa yayi wani sanyi yana ratsa shi tabbas yasan ZAHID gwarzon namiji ne tsayayye duk abin da ya fadi yana ƙoƙarin cika shi ne Gwauron numfashi ya saki yace '' Allah ya dafa muku ya baku abin da kuke nema ta hanyar halak ya tsare rayuwar ku gaba da baya ya raba ku da fitinar zamani...,
ZAHID yace amin a zuciyarsa nanne ma albarka ta saka musu sannan ya tashi ya fita kai tsaye fita yayi a kofar gida yaci karo da Tahir tafiya cafe su kayi suna hira ganin me rake yayi ya tsaya, ya siya musu Tahir ya fara sha yace '' kuma raken akwai zaki wallahi kagan sa tamkar sugar..,
da alama dai santi kake yi mu samu guri mu zauna anan karka fadar min a hanya na rasa inda zan kai ka..
Tahir yace '' wallahi koma m zaka fadi sai dai ka fadi domin kai baka ji zaƙin raken nan ba..,
Tahir sweet da sauri suka juyo jin muryar juhud tana sanye da hijabi har kasa ga niqab a fuskar'ta murmushin jin dadi ZAHID yayi domin duk wayewar juhud tana burge shi idan zata fita tana rufe jikin tane, ta nuna cewa tasan abin da yake mata ciwo yace '' sweet ina zaki..,
kallon sa tayi me cike da ma'anoni kala kala sannan ta lumshe idonta lokaci ɗaya ta bude su tar akan kyakkyawar fuskar ZAHID yace '' unguwa zani nan soron dinki..,
ZAHID ABUBAKAR ABDALLAH GALADANCI yace '' ko mu tawo rakiya ne...,
maida idanuwanta ƙasa tayi tana wasa da yan yatsunta tace '' a'a Nagode barshi hakan zai zama da takura tunda ba kai kaɗai bane...,
murmushi yayi yana kallon Tahir da ya kasa cewa komai sai Yanzu yace '' juhud barka da dare..,
kan'ta yana ƙasa tace '' barka dai ya harkoki..,
Alhamdulilah yace yana zama a kan wani benchi.
To Allah ya dafa muku ya baku abin da kuke nema.
Amin ya Allah yace
sallama tayi musu, ta tafi dukan kafadar Tahir ZAHID yayi yace '' tashi uban son jiki yawa ba namiji ba..,
dariya yayi yace '' GALADANCI naga kai ka dade da zama soja shi ya saka na bar maka fagen daga..,
dariya yayi ya shafa sumar kan'sa yace '' wallahi ka tuno min da school ina kewar ta kai gabaki ɗaya ma karatun ina kewar sa da ba dan kanne na ba da sai na kara kuru na tafi karatu idan na tafi bansan wazai kula da su ba Nabeel bekai girman da zai dauki ragamar rayuwar su ba..,
Dafa shi yayi yace '' karka damu abokina Allah zai dafa mana insha'Allahu zamu cika burikan mu,
Tashi yayi suka fara tafiya suna hira har suka isa CAFÉ din su tarar da aiki sukai dan haka ko wanne ya zauna a mazaunin sa ZAHID buɗa laptop yayi yace '' Abdul Rahman ka samu kuwa website din nan ya buɗe ni wallahi har tsoron shiga nake yi ina shiga zai wullo ni waje..,
dariya dukkan su sukai wanda aka kira da Abdul Rahman yana zaune yana bushe gyaɗar sa yace '' ina fa kai yanzu da ace ya buɗe da network ai da yau sunana rich man..,
dafe goshi ZAHID yayi yace '' wallahi bansan ya zanyi da mutanen nan ba jibi yadda kowa yake jira kuma kamar sun saka headline din rufewa ko..?,
Wallahi sun saka karka damu yanzu haka jina nake kamar wani attajiri tun da ina cin dawisun talaka..
dariya dukkan su suka saka Asim yace '' shege shi ya saka tun dazu kake susar kunne da mukulli sai kaje kunnen ka ya burme..,
duka yakai mai yace '' dan Allah GALADANCI me ya ragewa takala yanzu ya Nigeria banda yayi susar kunne yaju dad'i idan da hali ka dan hada da yar gyaɗanli kana susar kunne kana tauna gyaɗa..,
kai kurum ZAHID ya girgiza domin in da basu sun saba wannan musum ga kuma mutane ana ganin su da kima karsu fara yar tanki tanka girman su ya zube fara danna laptop din'sa yayi yace '' ni dai wallahi ku cire ni a wannan batu ina da abin yi..,
Dole kace kana da abin yi zai kai wa me idon cin naira cewar Abdul Rahman.
Tahir yace '' la la Abdul Rahman kayi shuru wannan mutumin baya son gaskiya.,
tashi yayi ya leƙa wajen da mutane ke zaune ana ciki wani form na daukan aiki gwamnati ce ta fito dashi zata dibi malaman makaranta masu NCE yace "wanda ya ke kan layi yayi sauri ya zo ya haɗa komai website din ya buɗe..."
Wani ne ya taso ya shigo cikin sauri yake shigar mai da komai ya tura addu'a ya dinga yi Allah ya saka ya shiga kar su rufe portal din sanin kowa ne aiki yana karanci yayin da matasa suka rasa abin yi fitina ce ga al'umma bayan sune kashin bayan al'umma din wata ran sune iyaye me gaba ake so ta haifar ne yana wannan tunani yaga sun dawo mai da shi dafe kansa yayi yace "kawai abdulraman ka bawa sauran hakuri yaƙi yi..."
dariya yayi yace '' ashe bari ba shegiya bace da uban'ta ni yau nasan zamu yi tsalle mu duro da oga haka kurum ina zaman basir yace ko purewater ba zaka iya dauka ka siya ba sai abin da ya baka..,
da sauri Tahir yace '' duk wannan uwar gyadar da kuɗin sa ka siya..,
ɗaga mai gira yayi yana gyara zaman rigar sa da duk ta kode amma akwai guga saita glasses din'sa yayi ya zura yace '' galadanci ya kayi shiru ba zaka shigar min fadan nan bane..?,
Mutumin da ake cike mai portal yace '' ba dole yayi shiru ba ka dauko abin da yafi karfin sa..,
dariya yayi yace '' a'a galadanci baya taɓa gazawa damu mu nan da kake ganin mu tawaga ɗaya ce ko wanne a cikin mu da yan kwanaki ya girmi wani tare mukai kuruciya muka tashi shi ne babban mu duk wani faɗa shike tare mana tsakanin mukwai amana da son juna saboda haɗin kanmu kuma course ɗaya muka dauka muka zo muna aiki a waje ɗaya dan haka saniya bata taɓa gazawa da kawonta ko galadanci...,
kai bana son shirmen banza kayi abin da nace kafin ya dawo ka nemo mai kuɗin sa.
Tashi mutumin yayi yace '' to Allah ya bamu nasara da sa'a mu fita daga cikin wannan matsalar...,
amin ya Allah suka ce bayan abdulraman ya dawo ya zauna yace '' kuyi karo karo ku biya min kudin gyadalli...,
Tahir da takaici ya rufe shi ya ciro totuwar rake yace '' wallahi ko kobo bazan bayar ba raken nan ma ba zaka sha ba dan rainin hankali kamar shi yafi kowa son cin dadi kwadayin ka yayi yawa karfa wata ran ya dauko mana abin da zai samu cikin tashin hankali kai baka taɓa yadda da babu baka taɓa zama a inda Ubangiji ya ajiye ka ...,
yauwa guy's nafa yanke shawara domin zaman nan haka zaman jiran tsammani nagaji dashi gabaki ɗayan mu computer science muka karanta ita kan'ta gwammati tasan bara zana ne mu a gare ta idan har ta barmi ba abin yi..
Asim da zancen ya fara shiga jikin sa yace '' haka ne wallahi ci gaba muna jin ka..,
To yasin bazan ci gaba, ba sai ka bani rake shi wancan yace bazai bani ba kai asim bani nasha..
wullo mai gutsire ɗaya yayi yace '' sai kace maye daman tun da naga kana kallo na , nasan cewa akwai wata a ƙasa..,
daukan sa ,yayi ya tauna bayan ya gama tsotsewa yace '' kan bura ubancan ba dai zaƙi ba yau dukkan mu nan munkai munzalin riƙe mata amma saboda talauci da yayi mana kan'ta mun kasa yin aure gwara ku kuna ma da budurwa ni kuwa saboda yanzu abin da na lura matan yanzu consumer ne ya saka na zama zero tension misalin ƙarfe ukun dare nayi kutsai wata na'ura kuma mallakin gwamnatin tarayya ce na gana makudan kudade da ke cikin account ɗin wanda idan muka cire harta ya'yan ya'yan mu wallahi baza suyi talauci ba wacce shawara kuka yanke mun dade muna cewa a gudu tare a tsira tare bama rabuwa cikin ra'ayi ɗaya kullum muna tare.
ZAHID sai yanzu yaga dacewar yayi magana yace '' abdulraman idan na fahimci zancen ka so kake mu fara yahoo ina tarbiyyar da iyayen mu suka bamu idan mun fara sata imanin mu yayi rauni karka manta me Ubangiji yace a cikin Surat Al-Mā’idah (Sura ta 5), Aya ta 38–39
Aya ta 38:
"وَالسَّارِقُ وَالسَّارِقَةُ فَاقْطَعُوا أَيْدِيَهُمَا جَزَاءًۢ بِمَا كَسَبَا نَكَـٰلًاۭ مِّنَ ٱللَّهِ ۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ"
Aya ta 39:
"فَمَن تَابَ مِنۢ بَعْدِ ظُلْمِهِۦ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌۭ رَّحِيمٌ"
aya ta farko Ubangiji yana cewa “Namiji mai sata da mace mai sata, ku yanke hannayensu a matsayin sakamako bisa abin da suka aikata, azaba daga Allah. Kuma Allah Mai iko ne, Mai hikima.”
ta biyu yana cewa
To, wanda ya tuba bayan zaluncinsa (wato satar da ya yi) kuma ya gyara, to lallai Allah Yana karɓar tubansa. Lallai Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.”
Iillolin da sata ke haifar wa suna da yawa duk wanda zai saka hannu ya dauki abin wani sai an cire mai imanin sa sannan sata tana da ga cikin mayan zunubai ita bin jini take , baka tunanin a ko wanne lokaci Ubangiji zai iya kiran mu, kuma dole mu amsa kiransa idan ya kira mu alokacin da mun saka hannu za mu ɗauki abin wani Ubangiji ya zare ran mu me za mu ce da wanne ido zamu kalle sa karka manta kowa akan abin da ya mutu akan shi za'a tashe shi be kamata dan tunani ya gushe ba hankali shima ya gushe ina ilimin addinin mu yake kaf cikin mu nan ba wanda ba zai iya zama ya rubuta Alkur'ani me girma ba saukar mu nawa Ubangiji fa yana ragawa wanda be sani ba akan wanda ya sani kuma ya take sanin sa karka manta me yace azaba ta tabbata ga wanda yayi ilimi sannan baya aiki dashi to mu yanzu mece ribar mu kaga suci aduniya suci a lahira.
shiru suka yi jikin su yayi sanyi abdulraman yace '' tabbas idanuwana sun rufe na kasa tuno maganar Ubangiji hakika samin aboki kamar ka sai an tona muna godiya da fadakar da mu da kayi insha'Allahu haka zamu gudu tare mu tsira tare sheɗan ko sheɗaniya be iya ya raba tsakanin mu ba mudin jini ƊAYA NE...,
rungume shi sukai suna farim cikin sanar da su da yayi tun kafin suyi nisa gurin aikata babban zunubi abdulraman dauko system ɗin sa yayi ya goge abin tare da fita daga cikin duk abin da zai nuna acewa anyi musu kutsai cikin na'ura..
Tahir yace '' yadda bamu da gata sai na Ubangiji aka kama mu wallahi sai igiya tayi saura a jikin mu domin sai me tsawon rai zai rayuwa kaga mun saka iyayen mu a wata damuwa da sai ranar da mala'ikan mutuwa ya tsaya a kan su zasu manta da ita wasu a cikin mu ta sanadiyar haka iyayen su su mutu wa gare ya waya ko ina talaka ne a ƙasa..,
Wannan haka yake daga haka kowa ya koma akan aikin sa assalamu alaikum da sauri suka amsa tare da gaishe shi amsawa yayi yace '' jiya da yau nawa kuka haɗa..,
kallon kallo aka shiga ZAHID yace '' sakamakon network da yake bamu matsala sannan Portal din shima baya shiga sosai to ba wani abu muka haɗa ba..,
Cire hularsa yayi yace '' oh nayi magana da commissioner yace sun rufe amma wani hanzari ba gudu ba , big man...,
Da yake haka yake cewa ZAHID lokaci zuwa lokaci yace '' na'am oga..,
Yauwa nasan aikin nan sai kai kafi computer ƙwaƙwalwa so nake ka haɗa min link irin na wannan wanda aka rufe din nan muci gaba da amsar kuɗin mu da irin wannan cuwa cuwar ake hayewa lamarin rayuwar nan komai yayi tsanani kuma kuna da buƙatun rayuwa dan haka mu hadu mu rufawa kai asiri muci gaba da amsar kudin mu sannan duk wani me CAFÉ da yazo ku bashi portal code shina kude ne me tsoka..
ran ZAHID ne ya ɓaci irin wannan aiki ba dashi ba dame al'umma za suji 1500 da suke tsira da ita , itama sai an kwace musu wannan wanne irin TSUMMA ne zambo cikin aminci kenan fa yadda da sukai da su shine zasu ha'ince su to wallahi ba dashi ba kauda kai yayi.
Oga nura yace '' big man dakai fa nake kai min shiru ba zakai bane ko yaya na sanka da kawo kabali da ba'adi yawa ba dan zamani ba....?,
*TSUMMA MAKUNSHIN CUTA*
Wolf in sheep's clothing
Ina meson logo ko invitation card
To ga dama ta samu
Werleedert graphics design
ta zo muku da graphic design na ban mamaki
Invatation card
VEDIO invatation
Logo
Banner
Poster
Menu
Acount sticker
Graduation stickers
Business sticker
Save the date
Business flayer
Birthday flayer
Engagement
Event program invatatin
Walimah invatation
Wedding invitation
Vedon invatation
Zaku neme ta a kan wannan number
+234 901 257 6569
Episode 3
ZAHID dauke kan'sa yayi yace '' gaskiya oga bazan boye maka ba bazan iya wannan aiki ba saboda gallazawa al'ummar musulmi ne idan muka mutu mu cewa Ubangiji me da wanne ido zamu kalle sa , ni ko kobo bazan iya ci a ba saboda wannan kudin, kudin haramin ne kuma na zalinci mutane suna ji da yanayin garin nan sannan a ɓullo da wata hanyar cuta su basu sani ba su zo su kawo kudi suna ganin cewa za su samu abin nan ƙarshe kuma ya zo ba riba basu samu ba wallahi Ubangiji ba zai barmu ba zai iya yafe hakkin dake tsakanin mu dashi amma na mutane bazai iya yafewa ba dubban mutane dubu nawa za mu cuta wani kafin lokacin mu yayi shi ya riga mu gidan gaskiya wani har bada baza mu iya sanin inda yake ba balle mu bashi hakuri ya yafe mana, ni ba zan iya cutar rayuwata ba na ginata da haramin ita haramin bin jini take da tsoka nata rusa zuri'a, bazan iya kaiwa iyayena haramun suci ba..,
da hallacan da kata min tun kafin a haife ka nasan wannan jabi zo ka fitar min daga shago na
zuciyar maza fa takai iya wuya ZAHID be yadda da hulakanci ba bayayi kar amai cikin zafin rai ya dauki laptop din sa yace "' da dai nayi maka wannan aiki gwara na bar gurin nan sannan ina me sheda maka barin gurin nan bawai yana nufin nabar rayuwata bane zan ci gaba da rayuwa ina me baka shawara ka tsabtace zuciyarka dan wata ran zata iya kai ka ga halaka da kake cewa kasan wannan tunkafin a haife ni sanin ka be amfana maka da komai ba , ina darajjaka ina mutunta tsofan ka sai dai kai baka gani, na barka lafiya..."
gabaki ɗayan su suka tawo suka dauki kayan su abdulraman yace '' tun da har ka kori ZAHID kamar dukan mu ka kora daga yau mun ajiye maka aikin ka ba me yi sai Allah zamu ci gaba da gwagwarmaya har mu cimma gaci..,
sakar baki yayi ya cire hularsa shaf ya manta shegun kaya ne haka suke yawa kashin awakai lokacin da zai dauke su aiki cewa sukai in har ba zai ɗauke su duka ba sun hakura sanadiyar zuwan su CAFÉN sa ya kafa tarihi me girma, saboda kwarewar su gurin aiki kullum kazo a cike yake dam da mutane wani yawu ya hadiya yace '' wallahi kuka sake kuka bishi duk wanda ya dawo bazan amshe shi ba..,
dariya Asim yayi yace '' oga kenan kamar baka san suwa ye yan kungiyar aminan juna ba to mu idan muka bar guri mun barsa kenan bama begen sa sai dai shi gurin yayi begen mu..,
Tahir yace '' faɗa mai da manyan baki ga tsiyar ka nan mun bar maka ...,
ni kuke faɗawa wannan maganar to wallahi kuyi kuka da kanku zaku gani.
ZAHID yace ''da addu'ar iyaye muke takama dan haka ba abin da za mu gani sai alkairi..,
har ZAHID yaje bakin kofa ya juyo yaga suna binsa girgiza kai yayi zai yi magana Abdul Rahman yace '' karkace komai nasan abin da zaka fadi da mun san da wannan to kamar yadda bamu san da shi ba haka Ubangiji zai budo mana hanyar samu ta inda ba muyi zato ba...,
zuciyar sa ce ta karye saboda alkawarin da yayiwa mahaifansa dafa kan'sa yayi yace '' ya Allah ga salihan bayin ka ya Ubangiji kafi mu sanin abin da ke boye Allah ka tallafi rayuwar mu..,
amin suka ce suka fita daga wajen baki ɗaya har suka iso hanyar gidan su ba me cewa komai kowa ya kasa magana kowa da abin da yake sakawa aran sa da yake al'adar su ce yau su kwana a dakin wannan gobe gidan su wannan za su wanda a cikin su baya iya wannan ZAHID duk dare zai dawo ya kwanta duk da tsakanin su ba nisa..,
yau kwai sai suka yanke shawarar kwana a dakin ZAHID bude musu yayi suka shiga bayan sun ajiye kayan hannun su, suka shiga cikin gidan domin gaishe da su nanne su danyi barkwanci suka dawo dakin sa Tahir jin gina yayi da bango yayin da hasken wutar lantarki ya haske mai fuska da yake kwai wuta Asim ne yace '' guy's ya naga jikin ki duk yayi ba dad'i daman fa ko haka bata faruwa ba ni wallahi ina gab da ajiye wannan aikin wahalar me mutumin nan yake tsinana mana ban da yaron nan da suke hawa sama su doro akan ya daukan hakkin sa..,
Dariya Abdul yayi yace '' sai ya duba yanzu yaga ba dari shidda..,
da sauri Tahir yace '' gyadar har ta dari shidda kaci...?,
gira ya ɗaga musu ba tare da yace komai ba kai ZAHID ya girgiza yace wallahi na tabbatar wannan mutumin bazai barmu haka ba sai yazo ka bashi kudin sa...
be ida rufe bakin sa ba suka ji ana bugu tashi ZAHID yayi ya buɗe turus yayi ganin yan sanda a kofar dakin su suba yan iska ba yace '' barka da dare yallaɓai..,
Kai ne ZAHID ABUBAKAR ABDALLAH GALADANCI..?
dakyar ya iya daga mai kai dan sandan ya fito da ankwa yace '' your ander arrest..,
dakewa yayi yace '' ko zaka iya nuna min ID da dalilin ka mani..?,
jin wannan maganar suka taso da sauri domin suka me ke faruwa Asim yace '' ba inda za shi indan kuma kun matsa sai dai a tafi damu gaba ki ɗaya me yayi muku ZAHID bashi da wani abokin faɗa hayaniya bata dame shi ba...,
naushi dan sandan nan ya kawowa Asim ya kauce yace '' za kuyi bayani ne wallahi sai na saka ku a matsalar da baku isa ku fita daga cikin ta ba maƙiyin ku ma sai ya tausaya muku..,
murmushi ZAHID yayi yace '' rai be isa yayiwa dan uwansa wani abu ba face haka Ubangiji ya tsara dan haka karya kake,kai mana abin da Ubangiji be mana ba muje Ubangiji yana tare da me gaskiyar...,
Dariya yan sanda su kayi Tahir yace muje kar wanda ya sanarwa da su nanne za su shiga damuwa be ida ƙarasa wannan maganar ba sai ga Areej ta fito tana cewa yaya galadanci ga kayan ka ka manta da su nanne tace kar mu kwanta bacci ka tashe mu..
da sauri ta juyo leƙowa tayi ta kalli yan sandan da suke tsaye a gurin agigice ta zubar da kayan hannun ta tare da rushe wa da ihu tsawa ya daka mata sai dai bata dena ba ta kamkame shi ya banta yau sharabon da suyi irin wannan kusanci tun bayan fara girmanta da kuma ƙin karatun ta kasa ko da motsi yayi sai kuka take tana cewa yaya kace su tafi bana son ganin su, su suka zo suka tafi da baffa be ƙara dawowa ba...,
durkusawa yayi ya tallofo habarta yace '' wayan can daban wayan nan daban kiyi shiru ki dauki kayana ki kai min daki na kar wanda kika faɗawa komai kinji..,
Kwantar da kan'ta tayi a kafaɗar sa tace '' yaya ina zaku...?,
murmushi yayi yace '' unguwa..,
da daren nan ita ba'a bari a tafi da rana
eh maza kiyi abin da nace ko kina so na dake ki..?,
kai ta girgiza mai ɗauka tayi ta shiga daki su kuma suka fita har sun fara tafiya ta tsaya ta fito bayan ta fito yace '' to matsa kulle gidan ki shiga gida...,
Duka dan sandan ya kai mai ya riƙe hannun sa yace '' ban ga dokar da ta baka dama ba ka dake ni batare da an tabbatar da laifina ba duk da baka faɗa min laifin da na aikata...,
Tahir yace '' muka dai aikata amma ba mamaki wancan na jadun tsohon ne..,
kullewa tayi ta saka musu sakata ta shiga gida, tana shiga ta tarar da nanne ta jiranta faɗawa jikin'ta tayi tai shiru tana tunani tace '' nanne yau naga irin wa'yanda suka zo rugar su baffa suka ɗauke shi...,
da sauri ta ɗago tace '' Areej bana son karya a ina kika gansu...?,
kwanciyar ta gyara sai kuma hawaye ya fara bin fuskar'ta tace '' wallahi na gansu sun tafi da su yaya galadanci kuma har ƙoƙarin dukan sa suke amma yace nayi shiru zai dake ni idan na faɗa muku dan Allah karki faɗa masa na faɗa miki...,
kasa kwakkwaran motsi tayi yayin da areej bata dena kuka ba iya da take ciki daki ta fito kwankwasa musu kofa tayi dakyar nanne ta tafi ta buɗe kofar iya tace '' maryamu lafiya naji yar nan tana kuka..,
kafin nanne tayi magana Areej tace '' wa'yanda suka zo suka tafi da baffa ne , suka zo suka tafi da ya galadanci..,
La'ilaha'illahu Muhammadun Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama Allahumma ajirni fimasiba