Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
Nagode nanne hakika ke faccala ce ta dabam Allah ya bar mu tare. amin ya Allah tace , tana tashi ta duba targen ta zuba gari ta fara sannan ta mai da tukunya ta rufe lokacin iyamu ta tashi daga bakin kofar dakin ta zama tayi tana jiran dawowar Areej. jin kukan ta asoro da sauri ta tashi ta leƙa tace '' ZAHID wai me yake damun ka da yarinyar nan yanzu daga aiken ta siyan Maggi sai ka dake ta me ta yi maka..?, karaf Areej tace '' ganin sana yi a gidan wannan yar iskar matar me tara mata shi ne nace mai lah daman anan budurwa ka take sai ya dinga dukan baki na har muka ƙara so gidan nan abokin sa ma yaya Tahir sai da ya hana shi., kai nanne ta girgiza tace '' ZAHID ba sai na tsaya ina maka dogon bayani ba ita dai Areej kasan matsayin ta a gurina bazan zuba ido ba naga ɗaya daga cikin ku yana ƙoƙarin takura mata ba ko dan kaddarar da ta same ta be kamata ku tausaya mata ba kuji ƙanta ba amma kai halin ka yafi na kowa, kowa yana nuna mata so da kauna ban da kai Allah ya ganar dakai gaskiya..., har ta gama maganar ta be ce komai ba sai da Areej tabar gurin yace '' nanne kiyi hakuri naga ranki ya ɓaci.., bakomai Allah yayafe mana baki ɗaya , ta faɗa tana barin gurin bude dakin sa yayi yana shigowa tahir ya shigo shiga cikin gida yayi ya durkusa har ƙasa yace '' nanne ina wuni an wuni lafiya.., cikin sakin fuska tace '' lafiya qalau alhamdulilah ya maman taku.., tana lafiya qalau ya su Areej yar lukata.. murmushi nanne tayi tasan ya fadi haka ne dan ya saka Areej kuka ai kuwa ashe tana kusa ta leƙo tace '' na faɗa maka nanne zata kai ni gurin rage tsoka tace tsoka ce tai wa Kamatuna yawa.., dariya yayi ya fita yana cewa da ta kuwa kyauta nanne tace '' ina gama girkin nan kafin su najwa su dawo zan miki kitso..., idanuwanta tane ya ciko da kwallah tace '' nanne dan Allah kiyi hakuri mu bari sai gobe.., haɗe rai tayi tace '' gobe yau she.., tunani ta shiga yi da sauri ta za bura ta shiga cikin daki a guje jakar ta , ta dauko tace '' an bamu assignment Dan Allah ki bawa yaya yayi min ni idan na kai mai yana yi min yana rankwashi na yace min me kan kwakwa ina tsayawa wasa bana karatu kuma nanne duba fa ki gani ...... kalli rubutuna ina yin me kyau haka ma aunty din ajin mu tace.., amsar littafin tayi sosai rubutun Areej ya bata dariya ita kan'ta idan za'a saka mata huka a wuya ta faɗi me ta rubuta ba lallai ta iya fadi ba Areej a kwai wasa da shiririta su, suke hanata fahimtar karatu tace '' Areej zo.., ɗurkwusawa tayi tana kallon littafin nanne tace '' haka malamar ku ta rubuta treesing ne fa amma ga yadda kika sauya musu kamanni kalli tittafin naki yawa ankwato abakin ƙura Areej kefa yanzu kin fara girma kina ECC 3 wata shekarar primary zaki shiga.., idanuwanta tane ya kawo ruwa daman bata da wuyar kuka tasan yau sarai yaya sai ya jibge ta zama tayi tace '' nanne gyara min in dauko pencil ki fiƙe da sharpener domin yayi kyau sosai yauwa harda cleaner.., ke bayan magariba idan su joud suka dawo kuzo na ga littafin ku mu kuma yi karatu sannan wallahi gobe idan baki tafi islamiyya jikin ki zai faɗa miki kin gama cika wa mutane kunne sannan ku zauna haka siddan ba cuta kike ba., shiru tayi tana kallon sa haɗe rai yayi yace '' ina miki magana kin kafe ni da idanuwa zaki bar kallo na ko sai na shigo, dauke kan'ta tayi ta kwantar dashi a cinyar nanne tace '' yaya kai hakuri.., jin maganar nabeel a soro a guje ta tashi ta fita rungume shi tayi tana tsallen murnar dawowar sa , aya ya fito da ita a aljihunsa amsa tayi tana washe hakoranta duk cin zuma tace '' yaya nabeel nagode amma gobe idan ka fita aiki madara nake so.., ɗagata yayi dakyar yace '' yar gidan nanne madara tafi karfina ban miki alkawari ba amma idan na samu hali zan siyo miki ita..., murmushi tayi ta kunce ledar ta watsa kusan goma abakin ta , tace '' to nagode.., Nabeel sauke min ya'karka fasa mata kai naga dakyar kake ɗaukan ta . sauketa yayi yake cewa nanne barka da yamma kin dawo lafiya Lafiya qalau alhamdulilah ya aikin naku da fatan dai komai lafiya ajiyar zuciya ya sauke yace '' alhamdulilah sai godiyar Allah yaya barka da yamma.., to Allah ya temaka ZAHID yace '' barka dai mun wuni lafiya ya aikin naka.., Alhamdulilah yana zama yace '' nanne wannan yar taki ce yawa bata san garin nan ba kullum dada fara shi take yi.., tagumi tayi tace '' wallahi zan ɓatar muku akan yiwa yarinyar nan ba'a sai kun saka ta kamu da cutar gudawa ta zazzage ku barmin kaya ta .., dariya nabeel yayi yace '' an barmiki iya nanne yar gidan nanne ikon Allah.., ya fadi haka yana doko ta komawa kusa da nanne tayi ta zuba mata aya a kan cinyar ta tace '' kema kici..., murmushi nanne tayi ta dauka tana ci. ZAHID yace '' kinde ji menace sauran kice kin manta.., bata fuska tayi zuciyar ta ba dad'i tace '' to.., komawa yayi fitar da da mintina kaɗan sai ga su joud da najwa gaishe da nanne sukai joud tace '' Areej bani ayar take inci naga ta jiƙa.., ɗaya ta dauka ta bantara ta miƙa mata harara ta watsa mata tace '' rike kayar ki aini ba mayya bace ba.., dariya najwa tayi tace '' maganin ki kamar baki san halin ta ba da shegiyar rowa idan kinga ta bada kayanta to nanne ce ko ya nabeel.., munfi kyaurata mata ne shi ya saka ta bamu cewar nabeel ba wacce ta , tanka shi suka shiga ciki cire kayan makaranta sukai suka fito, suka amshi girkin nanne nanne tashi tayi ta dauko kum da kibiya Areej tana yan aya bata san ta tsaya akan ta ba sai ji tayi ta cire inner cap din ta kuka ta saka , zare mata ido nanne tayi ta zauna akan kujera tana taje mata tulin sumar ta , ta usul ba relaxer ko ɗaya ga ƙarfi kuka ta dinga yi har da majiya har aka gama kitson ZAHID da yake cikin ɗaki shi da Tahir suna hira yaja tsaki yafi cikin kwando cikin tsokana Tahir yace '' nifa wallahi kana takurawa kanka me yarinyar nan tayi maka kuruciya ce wata rana ba za tayi ba..., kwafa yayi yace '' idan suka barta ba tare da tsawatarwa ba wallahi haka zata ' shi abin takaici idan kaga hakoran ta to cine shi yasaka kwakwalwar ta , ta zama ta dusa bata iya fahimtar komai kaga saboda da ita na dauko wancan dankon a hanya dazu yau nasan hmmm balallai naga abin arziki a cikin littafin taba ga ƙin makaranta wallahi yarinyar nan ita take jawa kanta nayi mata duk wani abu da banyi niya ba , amma nanne ta dinga faɗa kenan ina jiye mata lokacin da za tai mata Aure ta kasa zaman auren ba shikkenan ba sai ta dawo baya ta gyara kuskuren da tayi..., kwanciya Tahir yayi yace '' to aini ne mijin..kaga kuwa bazan hulakanta ta ba ..., kai dakata wallahi ba zaka jawo min raini ba haka kurum ana zaune kalau ZAHID ya faɗa har cikin zuciyar sa dariya Tahir yayi ganin yadda yayi maganar yace '' kai abokina ina harda su tada jijiyoyin wuya da ina cewa kai zaka fara kafamin gwamnati ..., a'a gwamnatin tarayya zan fara kafa maka wallahi Tahir ka fita a idanuwana da wannan maganar taka me kama da kasha kwaya.., tashi zaune yayi yace '' a'a giya nasha dan rainin hankali ni kuwa ina yar gidan dillaliya...?, dan ya tura masa haushi ya fadi haka ai kuwa ya tura masa a fusace yace '' kaga malam lamarin naka yafara yawa zo ka fita ya za ayi ka dinga cewa mahaifiyar matar da zan aura mutunci ba zai yiwu ba kamata yayi a matsayin ka na amini na ka dinga daraja ta Kana marta bata amma kai kake fara kushe alakar mu.., dole na kushe idanuwanka sun rufe kana shirin aikata babban kuskure a rayuwar ka haba abokina yawa wanda aka jefe ko akai wa sammu da fa kai kake kyamar rayuwar su amma yanzu ka saka kanka a ciki babbar damuwa'ta kar fa ta jaka wata hanya ba me bullewa ba..., toshe kunnuwan'sa yayi yace '' wallahi da ace wani ne ya faɗa min wannan maganar da tuni na dade da shafe shi a cikin rayuwa ta waikai Tahir me ya saka baka so a zauna lafiya ne..., *TSUMMA MAKUNSHIN CUTA* Wolf in sheep's clothing Ina meson logo ko invitation card To ga dama ta samu Werleedert graphics design ta zo muku da graphic design na ban mamaki Invatation card VEDIO invatation Logo Banner Poster Menu Acount sticker Graduation stickers Business sticker Save the date Business flayer Birthday flayer Engagement Event program invatatin Walimah invatation Wedding invitation Vedon invatation Zaku neme ta a kan wannan number +234 901 257 6569 Episode 2 Saboda ina son fahimtar dakai abin da ka manta. tashi yayi ya fita jin ana ƙoƙarin kiran sallar magariba dai-dai lokacin malam ya dawo Tahir shima bin bayan sa yayi daukan kayan da malam ya kawo sukai suka shiga da shi cikin gida shi musu albarka yayi tare da amsa gaisuwar da suke mai. daukan buta yayi da nanne ta ajiye mai ya dauro alwala suma su kayi, suka tafi masallaci a sukwane hafizu ya shigo yana cewa idan na yarda Allah ya tsine min albarka nanne nanne zo ki gani dan Allah yau wallahi wasu zasu bakunci Ingila me tukwane kuttumelesin kan baban ubancan lallai yau fa za ayi ta da dan kamfai idan na yarda nayi yawo tsirara sai da na shigo cikin gidan nan na ƙara tabbatar wa jiki na ya bani a cikin gidan nan aka cinye min kudin naman aska da sauri nanne ta fito tana ƙoƙarin tada sallah tace '' lafiya hafizu me ya faru kake wannan kikirari...?, zaro huka yayi ya soke a kugunsa tare da saka karan sigari da sauri nanne tace '' haba hafizu a cikin gidan namu za ka sha mana sigari kayi hakuri idan ka fita ka sha.., cire ta yayi ya saka a kunnen sa tace '' dan girman Allah duba ki gani duba aska da kyau be rame ba.., da sauri ta kalli karen da yake nuna mata wani irin baki ba kyen gani tace '' ni banda wata rama ba me ya faru.., kina nanne na dade ina so ki an kare ko ba haka ba lamma.. abokin nasa ya cije baki yace ''hakane ka dade kana nuna mata way.., yauwa lamma amma bata ganewa badai zance mata damsil basiratu ba tunda ko ba komai tafi waccan matar da wallahi idan bata sauya halin ta ba kaga dai ban yi wani karatun isilama nayi ba amma dai nasan ae yaneee to idan baya gyara halinta ba naru ce makomar ta kinga nanne ina umara na dinga turo kudi a siya wa aska yaci ya koshi abarshi da ciwon rashin ganina to wannan baiwar Allah sai ita take ci a cikin ta ko baki ga yadda ya rame ba daga zuwa umara na sati uku na dawo shine ya fita daga kamanninsa na tambayi wanda nake bawa kudin ya kawo mata yaci Alkur'an yana kawo mata amma zanyi maganin su dole a fito min da kudi na ko yau mutum yayi kwanan ingila me tukwane Nanne tace "kayi hakuri hafizu nawa ne kudin naka na baka sai ka bar maganar bana son ƙara jin wani tashin hankali.., kama karfen taga yayi yace '' ah wallahi ko karfanfana dattin aljihu bazan karɓa ba wacce dai ta cinye min kudina ta fito min dashi tun kafin nayi alkafura a kan ruwan cikin ta na caccaka mata wuƙa.., toshe kunnuwan'ta tayi domin zancen nasa ba ƙaramin daga masa hankali yayi ba. Kai da sauri suka juyo hamdala tayi ganin ZAHID domin dai-dai yake da shi tsoransa yake jima shiga daki tayi ta barsu fuskar sa ba annuri yace '' me nace maka kwanaki..?, dauke kan'sa yayi daga kallon sa yace '' i get .., kwafa ZAHID yayi yace '' kai kuma karka ƙara shigo mana gida domin gidan nan ba sa'an wasan ka bane .., jan karansa yayi yana cewa albasa batai halin ruwa ba billahilazi ba uban da ya isa ya hanani shugowa da wanda na ga dama cikin gidan nan ni za'a tozarta a gaban abokina.. shiga daki yayi ya zauna yace '' nanne ki dena tsayawa ki saurari wannan yaron kine na sakar mai fuska kamar hakan da kike yi ya ƙara samin damar yin abin da ya ga dama cikin gidan nan ya shigo da wanda ya ga dama kuma kusan abokanan sa ba , mutanen arziki bane kinga su joud mata ne be kamata suna cuɗan ya da irin mutanen nan ba ko dan tarbiyar su.., haka ne wallahi ZAHID abin da ya saka daman nake jan shi ajiki kaga irin su ba'a nuna musu tsana soyayya ake nuna musu ajawo su a jiki sai suyi hankali amma idan ana kyarar su ba za suji da dad'i ba haka iyayen sa kawai sai dai hakuri da addu'a Allah ya shiryar mana da zuri'a baki ɗaya.., amin ya Allah yace najwa ta dauko mai tuwan sa zama yayi yana ci Areej sai matse kwalla take nanne ce ta taɓa jikin ta , taji zafi da sauri tace '' subbanallahi Areej me yake damin ki..? jikin ki zafi raɗau.., kwantar da kan'ta tayi tace '' kaina ke ciwo da kunne na.., joud tace '' nanne ba dole tai cuta ba yarinyar nan wasan ruwa fa take idan ta shiga bayi dan ruwan da muke ajiyewa wallahi tas sai ta karar dashi dan Allah ki siya mata fo ta dinga abin ta muna wanke mata.., da sauri ta tashi ta kalli joud tace '' Allah ya kiyaye tab ni za kiyiwa tsarki wallahi ina neman tsari da wannan ƙaddarar nanne ka wata lukutar magana wai ni za tai wa tsarki sai kace yarinyar goye.., dariya nanne tayi tace '' kyale ta ba wanda zai dinga yi miki tsarki.., kwanciyar ta , ta gyara tace '' ai wannan abin ma salon su ganni ne yara su shigo suyi mini dariya nanne zafi nake ji.., joud tace '' da nafi kowa murna wallahi., Hararar ta tayi tamkar idanuwanta za su fado ƙasa nanne tace '' tashi na cire miki rigar kya sha iska.., satar kallon ZAHID tayi da yake cin abincin sa hankali kwance tamkar baya gurin duk abin da suke yi ko tari be yi ba wayar sa na hannun sa yana daddanawa mai da kallon ta tayi gun nanne a hankali tace '' nanne ba kince ba kyau wani ya ga tsiraicin wani ba kuma Ubangiji yana babbaka mutum lokacin mutuwar sa be ba ya mutu kalli yaya yana gurin ni ba zan cire ba naje na mutu.., Murmushi nanne tayi tace '' haka ne tafi daki ki cire ki saka me dan ƙaramin hannu ta shan iska.., ihu ta saka za ta fara tirje tirje suka haɗa ido da ZAHID yace '' maza ku shirya lokacin karatu yayi..., da sauri ta ɗago tace '' yaya ni zazzaɓi ne a jiki na bani da lafiya ko nanne..?, ko sharafa kike yi sai kinyi karatun nan gobe ma idan zan fita ni zan dauke ki nakai ki ba nabeel ba. wani yawu ta hadiya ta tafi daki kaya ta canza ta dauko jakarta ta fito lokacin har ya fara yiwa su najwa zama tayi ya gama yace '' zo.., zuwa tayi kusa dashi gaban tana faduwa dauko littafin ta yayi ya fara buɗawa zaro ido yayi yace '' Areej me kika rubuta nan.., muci muci ta fara da idanuwanta taja baya dan ƙo hannunta yayi yace "'zaki magana ko sai na kwaɗe ki ..?," Dan Allah yaya kai hakuri aunty namu ce mana tayi botiki botiyun kofi cofiyun kofa kofiyun haka ta karanta mana what a you mad..?, tuni idanuwanta suka cika tab da kwalla still bata dena taunar ayar ta ba ga wata kuma a hannun ta kallon nanne yayi yace '' kinga ko nanne wallahi yarinyar nan nagaji da halin ta wacce malama ce dan Allah zata faɗa mata wannan maganar da munafurci ne da ita ce kan gaba wajen bada labarin abin da ya faru.., Shiru nanne tayi jin maganar iya ta dawo tace '' to bakin mugu wannan yarinyar dai bada ban Allah yayi ta kosasshiya ba wallahi mijina da tuni ka dade da ramar da'ita irin kune ku hana matan ku sakat ka bakar jaraba kullum cikin azumi.., kunya ce ya kama shi ya saki hannun Areej agaban su joud iya ke faɗar haka kai sha'anin iya sai ita nanne tace '' iya sannu da zuwa..?, zama tayi dakyar tana sakar salati tace '' wallahi maryamu bazan amsa gaisuwar ki ba tunda kema kin zama bakar muguwa me hana da ya danƙi hannun ta ki dauki muciya ki buga masa a hannu salon Ya karya min jika ta to yasin kana karya ta hmm ranar caji moshan za mu tafi.., iya kiyi hakuri yanzu nake shirin yi mai magana. nanne ta fada cikin sanyin nan nata Uhmm kyaji dashi ciwon ajali a ɗayan tsa kowa na hango shi na hasko shi da fitila ta Hajara Hajara hajara uwar bakin hali.. da sauri iyamu ta shigo tace '' iya sannu da zuwa.., wani kallo tayi mata tace '' bana bukatar gaisuwar ki naji ance wannan dan neman ya dawo tun a hanya lado sirikina ya faɗa min wanda yake aurar yar gidan kanwata mariya yake min jaje to akul akul karna ji karna gani billahuwar ramanu hajara ranar da dakin ya dauki kayana tofa dole sani ya sake ki agidan ku zaki kwana ina dalili haka kurum me ya nadani da shi ba dai uban sa na haifa ba to bana son zazzagar albarka abarni ma da ciwon hawajan jinin da yake damuna da hasfatatus (hepatitis ) da yake idi me camiris (Chemist) yana namijin kokarin akan wannan ciwo nawa da tuni wani labarin ake ba wannan ba kwanaki maganin dubu biyar na siya har yanzu ina dashi ina watsa uku zuwa hudu na kwanta cikin salama shi ya saka za kuga dakyar nake tashi sallah asubayi.., iya yaushe kika kamu da wannan ciwo likita ne ya gwada ki yace kina dashi juraij ya fadi haka yana kallon ta cikin mamaki tana da wannan ciwo amma lafiyar ta lau to yaushe ma ta kamu dashi.. cire mayafin'ta tayi tace '' mijina hmm daman cuta tana cina ranar nan na kunna gida radio suna wannan shirin da nake ji duk sati na kiwon lafiya ana hira da kwararran likita a Babban Asibiti wallahi kaf abin da ya faɗi ba wanda bana ji shi shine banyi ƙasa a gwuiwa ba na tambayi bukar kudi banma faɗa mai me zanyi da shi ba dan kar na daga mai hankali na tafi gurin idi me Chemist ya bani sauki goma ya haɗa min aunti battatik (anti biotics).., turƙashi iya hannu ta ɗora akan bakin ta tace '' shii bana son jin komai ku kuma da kuke dariya ku ci gaba dayi ku fito kuyi son ran ku masu kan luɗaya ni bani da duhun kai da naje aka bani magani gashi nan ina kan matakin farko haka yace min kuma naga amfanin haka domin bacci ina samun sa ishashshe. shiru suka yi nanne ko matsi ta kasa dole ta saka ZAHID yaje ya jawa idi kunne ko ta kara zuwa ya bata magani karya bata zata zame musu yar kwaya. kusan faduwa tayi da sauri ta ɗafa bango tace '' amma dai Hajara anyi mara kirki wallahi babban burin ki, ki kaini ƙasa to wallahi ubanki ma nafi karfin sa bake ba kurwar sani dai da kika gama shaye ta tas kika rufe sai yadda kikai dashi to wallahi nafi karfin ku duk abin da kuke yi a gidan ku na tsafi yana kunne na tas.., a hankali tace '' iya kiyi hakuri ban san kin tashi ba.., hajara ina kuwa zaki san natashi ta ina zaki sani bakin hali da munafurci ya rufe miki zuciya da ido. shiru tayi ranta na suya ta rasa yadda za tayi da iya wata iriyar jarababbiyar mata ce ita ta iya masifa haka kurum sai ta zauna tana girgiza kafa a tsakar gida tana kallon mutane daddai ba wanda ta kyale a cikin sirikan ta gwara gwara nanne tana raga mata amma itama idan cin mutunci ya biyo ta kanta ranar tas za tai mata ke najwa dauko min mukulli ki bude min kofar nan.. tashi najwa tayi ta fito buɗe kofar tayi tace '' sannu Allah yayi albarka jameela jameela kina ina kina jina kin yi muƙus a daki ga dodo ta dawo nifa bana so na shigo cikin gidan nan ban ganku reras ba yawa yan matan amarya bana son fitina na lura yanzu abin da kika tsira ki dinga ware kanki kina kulle kanki a akurkin dakin ki me kama da shagon dan cirani wallahi ina mamaki ta yaya kike iya numfashi a dakin nan ranar da hamza bashi da Lafiya na shiga hmmm dawowa nayi da ciwon saman kai kwanya ta ciwo ta dinga yi yawa wata jaririya sabuwar haihuwa muɗigata sai harbawa take yi zafin dakin ki ya tada min da muɗigata ta haka na dinga addu'a ta koma ni jikina yana bani gidan nan anyi buso yasin zan kirawo malamai daga maradi abokin malam ne Allah ya jikan rai zai zo yayi addu'a duk dan kutumar uban da yayi min buso a cikin gidan mijina dan ya raba kan zuri'a ta tas zai koma mai kan sa dan haka magana nake muku da babbar murya duk wanda yasan yayi ya cire shi tas.., aunty jameela shigowa tayi da yake kofar ta , tana waje ba'a cikin gidan take ba tace '' sannu da zuwa sallah nake yi lokacin da kika shigo ina idarwa naji kiran ki.., Allah ko ta sallah..? to nayi nisa bana kuma dawowa kim sani yan uwanki suyi miki bayanin duk abin da nace Allah ya isa koda harafin magana kuka boye kunsani sarai ni bana munafurci bakuma nason annamimanci.. shiru su nanne suka yi har ta shiga daki ba wanda ya tofa tashi zama aunty jameela tayi tace '' yaya me ya faru..?, Nanne tace '' gashi nan shi ta shigo tana zai daki Areej shikkenan ta fara faɗa.., murmushi tayi tace '' Areej yar gata .., fadi da wai ki ƙara da ihu Areej yar gata ce dan ta rasa wani gibi na rayuwar ta bawai yana nufin mu ba zamu cike mata shi ba , Iya kiyi hakuri wallahi bada wata manufa na fada ba banza tai mata tashi ga bayi sallama tayi musu ta fita iyamu ta koma ɓangaren ta. da sauri nanne tace '' maza tashi kije ki kwanta karki min bacci anan.., Nanna batai fa sallah ba cewar najwa. Nanne tace '' najwa yaushe rabon ki da kika areej ta saka goshin ta a gabas..?, Joud tace '' to ita dai mutuwa bata sallama wallahi rabona da ganin ta saka goshin ta a ƙasa tun wancan azumin shima saboda fita a sham da yake ta mai da abin kamar zuwa yawo ne shi yasaka take yi. ZAHID yace '' bata sallah kamar ta.., da sauri areej ta hau kan cinyar nanne tana zare idanuwanta. dariya nanne tayi tace '' tashi kije ki kwanta.., Malam ne ya shigo yace '' auta waya taɓa ki naga kina taɓa idon ki zaki tsiyar ki cikawa mutane kunne..?, da hannu tai mai nune da su dariya yayi yace '' dan Allah ku sakarwa yarinyar nan mara tayi futsari wannan wa ce irin rayuwa ce haka.., ZAHID tayi yayi yace'' malam sai da safe.., To Allah yayi albarka yauwa zo.. dawowa yayi ya zauna su kuma su najwa suka shiga dakin su yace '' gani malma.., dan jim yayi sannan yace '' Alhaji yace kaje ka dinga yi mai direba ga

Chapter 2 of 6