Niba fasikin mutum bane saboda haka bazan auri fasika...."
Kafin ya gama kai zancen Almu ya d'auke shi da wani irin b'arin makauniya. Ai a take dambe mai k'arfi ya kaure tsakanin su. Sosai gurin ya chabe da kyar aka raba Lukman da Almu. Shidai Lukman banda kuka babu abunda yake. Tsananin bak'in ciki da tsanan Aleeyna ya darsu cikin ransa da yake ji kaman ya harbeta. Duk abunda za'ayi ayi amma wlh ya fasa auren. Ran Baffa a b'ace ya kifawa Lukman d'in dake ta muzurai yan maimaita bazaiyi auren ba idan ana dole sai a sashi ya yi ,mari.
"Ni zaka tozarta? Nace ni zaka tozarta? Idan wani abune ya faru ka bari ayi cikin sirri mana. Wato na lura uwarka ta fara maka tasiri wajen ganin ka raba kan zumunci ko?"
A zafafe ya ciro wayarsa ya mikawa Abhie dake tsaye yana kallon Lukman d'in ya kasa cewa komai. Jiki babu kuzari Abhie ya mik'a hannu zai k'arbe Almu ya yi wuff ya kwace wayar. Abunda yaci karo dashi jikin wayar ya yi masifar d'aga masa hankali da jiri ya debeshi ya yi taga-taga zai fad'i. Zubair ya yi saurin tashi.
"Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha"
Almu ya furta da k'arfi. A yanzu kan k'irjin Abhie wani irin matsanancin bugu yake yana kalin Almu daya damke wayar da Baffa ke k'ok'arin kwacewa yaga ko Menene haka a jiki, amma Almu yaki bayarwa. Da wani iri bala'in gudu ya juya a guje ya Zubair ya bishi. Mota ya fad'a jikinsa har wani irin tsuma yake. Ganin haka Abhie da Baffa suka tabbatar lallai koma menene wannan babban abune. A hanzarce suka bi bayan sa Baffa ya saka Lukman a gaba suka shiga mota. Wani wawan fakin Al'mustapha ya yi kofar gida ko motar bai kashe ba ya fito a guje sai Zubair ne ya kashe motar
. Kaman mahaukaci ya shiga yaja kwala kiran Aleeyna. Mata duk akayi cirko-cirko ana kallon Almu daya shigo kaman mahaukaci. Amnah ta fito da sauri tana cewa
"Lfy ya Almu an d'aura auren ne?"
"Ina Auta"
"Tana d'akin Ammi"
A guje ya fad'a d'akin can kuryar gado ya sameta ta nannade cikin bargo Hajjo da wasu mata a kanta suna yi mata sannu. Wani irin fisgota ya yi ya jiki na rawa ya nuna mata fuskar wayar dake hannun sa. Yana tsuma hawaye tab cikin idonsa yace
"Menene wannan? Ki gayamin bake bace a cikin video danan Auta, ki gayamin"
Wani irin dum kanta ya Sara ta kwalao ido tana kallon kanta dake jikin video da Almun ke nuna mata. Gata nan a kwance da wani namiji yana sex da ita haihuwar uwa. Blue film ne sosai. Tsananin kidima da tashin hankali da Aleeyna ta gani ta kasa motsi. Aikuwa Almu ya d'auke da wani irin mari da a take ta sume a guri. Da ihu ya yi kanta zai rufe da duka yana cewa
"Kiyi kun magana"
Dan sam bai lura ta sumen ba. Su Abhie suka riƙe shi da sauri. D'akin duk ya kacame da ihu-ihuce. Wani irin komawa gefe Almu ya yi ya durkusa ya had'a kai da gwiwa yana kuka kaman karamin yaro. HAJJO sai bala'i take kaman zata rufeshi da dukan itama. Ammi kuwa ta kasa ceea komai tsaban mamakin wannan abu. Jikin Abhie a matuk'ar sanyaye ya kai hannu ya kwace wayar dake hannun Almu. Kallo d'aya ya yiwa wayar ya yanke jiki ya fad'i. Ai zo kaga ihu. Hankula suka k'ara dugunzuma. Sai koke-koke da d'akin ya kaure dashi. Cikin tashin hankali aka kwashe su zuwa asibiti. Lukman kuwa babu wanda yasan sanda ya sulale ya bar gurin. Taimakon gaggawa aka basu . Saida Aleeyna tayi awa biyu cur bata farfaɗo ba. Abhie kuwa tun kafin su k'arasa asibitin ya farka yana ta nanata Innalilllahi cikin ransa. Abu dai duk ya dagul an shiga cikin damuwa da tashin hankali. Duk suna zaune jugum jugum Hajjo ta d'ago ta kalli Almu dake tsaye jikin bango duk ya fice hayyacin sa tace
"Wai me yake faruwa ne? Kai Mustapha ka samu a duhu. Ka warware mana abunda yake faruwa gashi ance ba'a d'aura auren ba har yanzu. Ina ma Lukman d'in ne?"
K'irjin Abhie dake wani irin zafi ya taune harshe yana kallon k'asa saboda idan Baffa da yake ji a kansa. Kafin Almu yace wani abu likita ya fito yana cewa su biyoshi office. Abhie, Baffa da Ammi sai Hajjo ne suka shiga. Saida bayan sun zauna yace
"Sakamakon bincike da mukayi ya tabbatar mana da yarinya na d'auke da juna biyu wata d'aya da sati biyu. Ya kamata a dinga kula da Lafiyarta ita da abunda ke cikinta. Saboda early stage na pregnancy babu abunda bazai iya haddasawa ba. A daina bari tana yawan shiga damuwa saboda mun fuskanci tana cikin depression hakan kuma had'ari ne sosai a gareta dan zai iya janyo wa cikin jkinta ya zube. A dinga bata cika mai kyau saboda lfyr ta da kuma abinda ke cikinta."
Wani irin shuuu sukaji gaba d'ayan su kafin suji Tim Ammi ta zube k'asa a sume. Jikin Hajjo na wani irin rawa tace
"Likita wacece take da cikin harna wata guda da sati biyu? Badai jikita ba ko? Yarinya da ko aure batayi ba yau d'innan ne za'a daura auren sai kuma y'ar matsala ta faru. Ka k'ara dubawa da kyau dai ko kayi kuskuren wajen sunan"
Kai ya girgiza " A'a Hajiya. Ita dai wannan yarinya da aka kawo itace nake miki bayani ga file din nata ma ki duba "
Kasa motsi Abhie ya yi sai Baffa ne karb'a jikinsa na rawa. Takardun sukayi ta zubewa yana d'aukowa saida ya yi haka har sau uku sannan ya iya riƙeta a hannun ya buɗe yana karanta report d'in a fili. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Hak'ika wata masiba da tashin hankali ta ratso cikin family nasu kuma babu ta yanda za'ayi su iya guje mata. Wani irin gunjin kuka Hajjo take taba salati da sallami. Shi kuwa Abhie kai ya sunkuyar hawaye na diga daga idansa. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Firgigit Ammi ta farka ta kaman wacce aka mintsila. A guje ta fice daga d'akin tana kuka sosai mai tab'a zuciya. Kai tsaye d'akin da aka kwantar da Aleeyna ta kusa inda ta tarar da duk yan uwan da dangi a ciki saboda farkawarta. Ratsu kawai tayi daidai Amnah da Bagira K'awar Aleeyna na k'ok'arin kamata ta zauna.babu zato ta rufeta da matsanancin duka tana wani irin kuka. A guje aka rike Ammi ana bata hak'uri cewa kawai take
"Ku kyaleni na kasheta na huta da wannan bak'in ciki data jefamu. Ku kyale"
Da kyar aka janye Ammi daha jikin tana kuka sosai. Baffa ya shigo yace kowa da kowa ya fita zaiyi magana da Aleeyna. Saboda yanda Baffa keda kwarjini babu wanda ya musu duk suka fice suka barshi da ita. Wani irin kuka take ta had'a kai da gwiwa abun gwanin tausayi. Numfashi ya fesar mai zafi ya zauna kan kujera yana fuskantar ta ya kira sunanta.
"Aleeyna "
Bata iya amsawa ba sai kai data d'ago ta kalleshi da idanuwan ta da sukayi jazur .
"Ki gayamin tsakani da Allah. Waye ya yi miki ciki?, nasan tarbiyar ki Aleeyna nasan wacece ke. Tarbiyar gidanmu abun alfahari ne a garemu nasan cewa hakan kawai bazaki bari wannan tarbiyar ta lalace ba. Ki gayamin wayene ya lalata miki rayuwa ?.waye sanadin da yaja tarbiyar wannan ahali take k'ok'arin wargajewa?"
Dumdumdum. K'irjin Aleeyna ya wani iri bugawa da saida Baffa yaji. Suman zaune tayi ta kafe Baffan da ido kaman wadda ke ganin kai hud'u a tare dashi. Ita ce take da ciki? Mafarki take ko me? Taya zatayi ciki ita da bata tab'a sanin wani namiji ba? Ko wancan ranan ma tana al'ada kuma bai keta mata haddiba. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Luu ta koma ta k'ara zubewa a sume.
End of free page.
Chakwakwayi da gwaramar yanzu ta fara. Yar uwa kar ki sake ayi wannan tafiyar babu ke.
GUDUNA AKE it just @ 500N.
A turo payment wannan account number
👇
3078293347
Aisha sani danjuma
First Bank.
A turo shedar biya wannan number.
08140754777.
Sai na jiki masoya Ashantylove na kwarai.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels