Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
yau tak'i sanar dasu komai. Guri ta samu gefen gadon ta zauna tana sauraran yanda Jaleela ke rere karatu. Tunawa tayi ita yaushe rabon da ma ta d'auki Qur'ani ta karanta?. Kai ko sallah idan zatayi Falak'i da Nas kawai take karantawa don tasan idan tace zata d'auko doguwar surata to tabbas zatayi kwaba, saboda babu karatun. Dama shi Qur'ani idan ka barshi ne da kwana d'aya ya barka da shekara guda. Tana jin Jaleela ta kai aya ta k'arshe tana 'Subhanakallahumma ashhadu an la'ilah illa'ant. Ashtagfurullahi wa'a tubu ilai'. Tace "Yauwa kin idar?. Ke nake ta jira tun d'azu. Na samo miki babbar harka...." Saurin katseta Jaleela tayi ta hanyar girgiza mata kai. Shiru Kainat tayi tana kallon Jaleela data nuna mata Qur'anin dake hannun ta. Miƙewa tayi ta fara ajiye Qur'anin a gefa cikin nutsuwa, ta cire dogon hijabin dake jikinta ta ninke shi ta ajiye cikin kwaba, sannan ta juyo inda Kainat ke zaune tana kallonta cike da mamaki. Saida ta nannade daddumar da tayi sallan a kai, sannan ta sami guri kusa da Kainat ta juyo tana kallonta tace "Yanzu ya dace kiyimin wannan maganan amma muje falo ,Anees tana barci" Baki Kainat ta buɗe amma babu abunda ya fito. Tsananin mamaki ya saka ta saki bakin tana kallon Jaleela. Wai Jaleela nada irin wannan addini take wannan mummunan dabi'u?. Ita kuwa wane irin mummunan iftila'i ne ya sameta haka take irin wannan rayuwar?. Duk abunda take haka, baisa ta manta da ibada ba. Falo suka fito Kainat ta wuce kitchen ta deb'o musu drinks da gashin kaza . Bayan sun nutsu take gaya mata kamun da tayi mata. DUBAI /ABU DHABI. THE PALACE. Katuwar masarautace da aka zuba mata dukiya kace baza'a mutu ba. Komai na masarautar tun daga wajen sa har cikin sa anyi sa da zenare da crystal stones. B'arin KING LK kuwa da daimons aka kerashi kace ruwan su ake. Kowa yasan Abu Dhabi shine b'angaren da dukkanin wani hamshakin mai kuɗi na duniya ke yada zango a Dubai ,wasu ma suna da gidaje na kansu a can, saboda Abhu Dhabi shine k'arshen gari na masu kuɗi. Kyakkyawar macece da bazata haura shekara 40 ba cikin wani tankamememen falo da aka k'awata da abubuwan more rayuwa. Tana zaune ne cikin wata lallausar kujerar mai tsananin taushi da akayi wa ado da zinare. Gefenta a tsaye,kuyangi ne wasu na mata firfita duk da cewa akwai Ac ta ko wane lungu da tsako na falon da girman sa ya yi wani k'aramin flat house d'in. Falon cike yake da bayi da suke tayi mata bauta. Gefenta yarinyace da bata wuce shekara 20 ba zaune k'asan lallausar kafet wajen kafar ta. Kaman yanda wannan babbar mata ke sanye cikin alkyabba ta sarauta data sha ado da zinare, haka itama yarinya. Daga gefen matar wasu manyan dattijai ne guda biyu zaune cikin kujeru dake fuskantar ta. Numfashi ta sauke mai k'arfi tana k'ara bin dattijan da kallo, kafin ta mayar da ido kan yarinyar dake zaune wajen gefen k'afar ta. Numfasawa ta k'arayi ta buɗe baki tana magana da muryar ta mai sanyi da dad'in sauraro da harcen larabci. "Anya kuwa wannan abu mai yiwu wane?. Kar ku manta irin kalubale da muke fuskata cikin wannan masarautar duk lokacin da wannan abu ya faru. Mata da yawa, rayuwar su ta salwata saboda wani sirri da mun kasa gane masa. Kuna ganin babu cutarwa cikin wannan LAMARI idan aka sake tafka wannan kuskure a karo na hud'u?" To fa wane sirrine wannan? Wannan tafiyar ta dabance. Kudai ku cigaba da bibiyar alkalamim Ashantylove. Kafin muyi nisa wannan littafin PAID BOOK ne. Zaki iya fara biya tun tafiyar bata fara zafi ba @ 500N kacal. Domin neman k'arin bayani ko tuntu'beni a wannan number 👇 08140754777 𝗚𝗨𝗗𝗨 𝗡𝗔 𝒜𝓀ℯ 𝓎𝒾. 𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮 11/15. Balaraben dattijan daya fi kusa da ita, wanda ke sanye cikin bak'ar alkyabba da rawani kaman yanda malamai suke. Hannun sa carbi ne kato mai d'auke da sunayen Allah. Saida yaja dogon salati da yin istigfari sannan yace da harcen larabci. "Hak'ika kin kasance Malika, sarauniya mai adalci da kuma tausayin talakawan ta. Kin kasance sarauniya dake sauke nauyi da Ubangijin sammai da kassai ya baku, bawai don kunfi sauran bayin sa ba, sai dan hakan yana daga cikin hikima irin tasa. Hak'ika Ubangiji bai hallici ko wane bawa ba ,saida ya rubuta masa kaddarar sa. Wannan kuma na daga cikin jarabawar ku" Shiru ya yi yana d'an jan fasali. Wani bafade dake gefen sa, ya yi maza ya zuba masa ruwa cikin wani irin glass cup mai kyan gaske ya miƙa masa cikin girmawawa. Karb'an ruwan ya yi ya d'an jik'a makogaro sa. Malika dake zaune tana sauraran sa, ta sauke numfashi. Allah kaɗai yasan abunda ke ranta. Juyowa mutumin ya yi sosai yana fuskantar ya cigaba da cewa "Tabbas Abu Sufyan da y'ar sa Aafiya sunsan kalubale da ake fuskanta cikin wannan masarauta. Ba suzo nan ba saida suka tabbatar da dukkanin wani jita-jita da ake yad'awa , walau gaskiya ne ko k'arya . A shirye suke wajen ganin sun tayamu yak'i da wannan b'oyyeyyen sirri da muka kasa gane masa. Sun kasance d'aya daga cikin dubbunnan Al'umma dake da burin ganin wannan masarauta mai Albarka ta had'a zuri'a dasu, du da sanin su na cewa rayuwar ya'yan su, ko su kansu ya'yan na iya salwanta. Yareema mai jiran gado dole yana buk'atar mace da zata taimaka masa kan wannan karaga ta MULKI. Lokaci na ja, lokaci na tafiya. Yanzu ne lokaci daya dace Yareema ya hau Mulki. Shine kad'ai ya cancanta domin shine ya kai wannan munzali ba kannen sa ba. Ya kamata Malika ta huta da dawainiya da dubbunnan Al'umma dake wuyanta. Ta sauka ta bawa Yareema mai jiran gado. Haka zamuyi hak'uri mu cigaba da kawaiwa Allah kukan mu har zuwa lokacin da zai yaye mana wannan musifa. Aafiya a shirye take don zama dashi da jure dukkanin wani kalubale da zata fuskata. InshaAllahu zamu samu nasara nan bada jimawa ba. Mu dage dayi masa Addu'a da yawanta sadaka har Allah ya kawo mana mafita" Shiru falon ya d'auka baka jin komai sai k'arar Ac da saukar numfashin sa. Manyan idanuwanta dake b'oye cikin farin glass Malika ta lumshe. Saida ta d'auki sama da minti biyu a haka tana tunanin da Allah kaɗai ya sani. Cikin nutsuwa ta k'ara gyara maza ta buɗe idan nata a hankali ta watsa su kan Aafiya dake zaune gefen ta. Magana tayi da murya mai taushi. Kai kanajin yanda tayi maganan kasan sarauta an gaje ta ciki da waje. "Aafiya " Ta kira sunanta. A hankali Aafiya ta d'ago kai da girmawawa har tana d'an yunƙurawa. Ido Malika ta zuba mata. Tabbas Aafiya yarinyace kyakkyawa san kowa kin wanda ya rasa. Bazata so ace yarinya k'arama kaman wannan ta had'u da wannan cruel fate ba da saura mtan da suka zo cikin masarautar nan, kaman dai yanda Aafiya sukayi da mahaifin ta. "Kina san ibni?"(D'a na?) Kai Aafiya ta k'ara d'agawa a kunyace. "Zaki iya zama dashi duk da sanin ki na abunda ke faruwa matsawar ki ka aureshi?. Duda da kinsa cewa zaki iya rasa rayuwar ki?" Nan ma dai kai Aafiya ta k'ara d'agawa. Ido Malika ta zuba mata cike da nazari. Hak'ika tana cikin mamakin yanda mata ke sadaukar da rayukan su a kan d'an nata shi kuma sam basa gaban sa. Tana burin d'an nata ya yi aure ya hayayyafa don cigaba da gina wannan masarauta data taso tun kakanni daga zuri'ar su. Kai ta d'an jinjina ta juyo da kanta wajen Abu Sufyan. "Abu Sufyan " "Na'am ya Malika" "Kaji ka aminci kuma kayi Na'am da wannan abu?, idan har kana da ja zaka iya magana. Aafiya y'ar kace babu wanda ya isa da ita kaman kai. Ka yarda ta kasance matsayin matar d'ana LAMEEN KHALELULLAH?. Sarauniya a wannan masarauta?" Da girmawawa sosai yace " Na'am ya Malika " Numfashi ta k'ara saukewa ta mayar da idonya kan Wazir dake gefenta. "Ayi shela da sanarwa cikin satin nan Yareema zai sake aure. Ayi sadaka ta Shanu da rakuma na dubu hamsin, da kuma sauka sau hamsin don samun nasara da kuma kariyar ubangiji" Murmushi ne kwance kan fuskar Wazir da Abu Sufyan har Malika ta miƙe don barin fadar. Kallon Wazir tayi da Abu Sufyan da suka rungume juna bayan sunyi musa baha na taya juna murna kaman yanda Larabawa ke yi. Kai ta d'aga musu ta wuce bayin ta da fadawan ta suka rufa mata baya. Wata had'addiyar lifter dake cikin falon ta glass da aka kawata da gwal ta shiga ita kad'ai sai wata baiwa dake binta duk inda tayi. Sauran suka shiga wata dake jikin wannan. Hannu ta kai a hankali ta dafe goshinta da take ji kaman zai rabe biyu ,sosai take cikin damuwa da tunanin kaman sun k'ara tafka wani kuskuren babba. Tana fargabar abunda ya faru da sauran matan da Yareema ya aura, ya faru ga Aafiya . Duk cikin yaran dake rububin zuwa ,bata san me yasa ba Aafiya tafi kwanta mata a rai. Ko dan hakan yana da nasaba da hankali da kuma tarbiyar da take tunanin yarinya na tare da ita ne?. A hankali ta furta a fili "Ya rabbil samawati, ya ubangijin sammai da kasai. Ya ubangijin dukkanin wata halitta. Mutum ko Aljan. Ya wanda ya halicci ruwa, ya halicci iska, ya halicci wuta da Aljanna. Ya Zuljalalu wal Ikram. Allah ka kawo mana mafita cikin wannan sark'arkiya da bamu da amsar ta. Allah ka kawo mana k'arshen wannan musiba. " Baiwar dake kusa da ita ta amsa da Amin cike da tausayin uwar d'akin nata. Hak'ika tun tasowar ta cikin masarautar nan taga irin gwaggwarmaya da SARKI KHALELULLAH ya yi da matarsa MALIKA, ARWA . Tasan dukkanin wani kalubale da jarumta da sukayi wajen ganin sun gina wannan masarauta mai Albarka. Taga irin jarumta da Malika tayi bayan k'asa ta rufewa SARKI KHALELULLAH ido. Irin dawainiya da take da ya'yan ta da mutane wajen basu kulawa da kariya daga dukkanin wani sharri da kalubale na rayuwa. Na ciki dana waje. To amma Yareema yana tare da wani sark'arken abu da an kasa gano masa. Anyi maganin sammu, anyi na aljanu. Amma an kasa samun nasara. A yanzu kam Addu'a ce kawai ake yi da yawan sadaka Allah ya warware koma menene. Ita kanta tana tausayin Aafiya. ABUJA. To Jaleela dai kam an zama mutanen Abuja. Duda dama Abujan ba bakon ta bane. Sai dai zuwanta yanzu ,Kainat tayi yawo da ita sosai cikin garin Abuja musamman clubs dake ci sosai na manyan yara. Tunda suka zo take ta fad'i tashi wajen ganin ta mayar da Anees makaranta. Yarinya har sukayi kwana biyu ta kasa daina kunci ,sam taki walwala. Abun tun baya damun Jaleela har ya fara damunta. Don haka yau ta d'auke ta suka dinga yawo Park,Parks da mall don ganin tayi walwala. Ai kuwa Anees tafi kowa farin ciki. Rabon da Jaleela taga farin ciki kan fuskar yarinya kaman haka harta manta. Sannu a hankali ta fara warwarewa musamman yanzu data fara zuwa makaranta tayi kawaye sosai. Kowa yana son ganin ya zama abokinta saboda kyau da Allah ya bata ga masifar k'ok'ari. A b'angaren Jaleela itama abun haka ne. Don yanzu dukkanin wani clubs da suke zuwa ita da Kainat tayi suna. Sunanta na clubbing shina LA REINA ,the cold Beauty. Ba ko wane namiji ne yake cire tuta a kanta ba sai ta zaba ta dirje kafin kace me,kuɗi sun fara zamarwa Jaleela tana wadaka dasu sai abunda taga dama. Nanny guda ta d'aukowa Anees dake kulawa da ita idan basa nan, duk da cewa basa fita sai ta tabbatar Anees tayi barci haka nan duk inda take, duk inda hud'u na asuba tayi zata dawo kafin Anees ta farka. Ciki kwana biyun nan ma basu cika had'uwa da Kainat ba saboda tayi busy sosai da wasu alhazawa da suka zo Nigeria. Ita dai Jaleela nata harkan bata bada kanta. Zatayi maka dukkanin abunda ka ke so amma baza ka tab'a ba tare da kasa ko yatsa a jikin ta ba. Wannan shine sharad'in ta. Abunka da mai kyau a guje mazan ke k'arban wannan offer, sudai indai zasu huta ai basu da matsala. Can k'asan zuciyarta tana kyamar wannan abu da take. Kai su mazan ma gaba d'aya ta tsane su , don namiji shine SILAH na fad'awarta cikin wannan halaka. A ganinta wannan abu da take shine kad'ai zai bata damar da zata bawa Anees rayuwa mai kyau. Dukkanin wani abu da zatayi gani take baza ta samu ba kaman yanda take samu haka ,bare har ta gina musu rayuwa mai kyau. (To amma kin manta kuɗi irin wannan basu da Albarka tunda ba ta hanyar mai kyau aka same su ba). Yau asabar daga ita har Kainat suna gida. Gaba d'ayan su suna falo ne. Jaleela na kwace cikin katuwar kujera sanye da riga da wando pink color. Anees na sanye cikin wata y'ar k'arama gown silver mai hoton unicorn a jiki. Kanta an rabashi biyu an kamshi gefe da gefe. Kainat kuwa n kwance kasan kafet tana mafa da waya daga ita sai y'ar doguwar riga mara nauyi. Ihu tasa ta miƙe tana zare ido a waje. A kasalance Jaleela ta kalleta ganin yanda duk ta rude riƙe da waya baki a hangame. Anees tace "Aunty Kainat, menene? Ko kinga dodo ne a wayar?" Dariya Kainat ta saki a hanzarce tace da Anees. "Baby jeki d'aki ki d'aukomin laptop d'ina kinji y'ar Albarka " A guje Anees ta ajiye Teddy da take wasa dashi tayi d'akin a guje. Da azama Kainat ta taso ta zauna kusa da Jaleela dake kallonta. Saida ta nuna mata wayar hannun ta tace "Gaskiya ke ko, ta dabance wlh. Labarin ki kawai yaji yake nemanki ruwa a jallo. Kinsa waye yake nemanki kuwa? Yanzu nan Khairat ta turo min. Kin san waye? ZAIN" Ta fad'i sunan da k'arfi. Tsaki mai k'arfi Jaleela ta yi tace "Waye kuma haka?" Ido Kainat ta waro harda d'aka mata duka "Zain ne baki sani ba?, d'an minister babban likita dake zama a turai. Ance yazo gari yaji labarin ki shine yace yana son had'uwa dake. Ko kinsan irin sa'ar da zaki taka idan ki ka kasance dashi?. Mata da yawa suna mafarki a kansa da burin kasancewa dashi kona rana d'aya ne. To ganin sa ma wahala yakewa mutane bare ka same shi. Kaman yanda ki ke juya mutane shima haka yake dan yaga yana da kyau. Ga kuɗi, ga kyau, ga aji, ga class. Haba wlh kedai kina da sa'a, manyan yarane kawai ke binki, ko da yake kin cancanci hakan ne don duk yanda mutum zai kiyasti ki kin wuce haka" Baki Jaleela ta tab'e cikin ko in kula tace "Bani da lokacin sa" Kainat ta buɗe baki zatace wani abu Anees ta fito a guje da laptop d'in datace ta d'auko mata. Dole ta taune harshe tayi shiru da maganan, amma ta kudurta a ranta dole nema ta had'asu. Itama ta yagi abunda zata yaga Jaleela baza tayi mata bak'in ciki ba. 𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔 𝒜𝓀ℯ. 𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮 16/20. Tsawan kwana biyu Kainat nayin dukkanin iya bakin k'ok'ari wajen ganin ta shawo kan Jaleela sunje club d'in da take tunanin Zain na zuwa, fafur Jaleela tak'i kwana biyu ma babu inda taje ta mak'ale a gida wajen Anees. Duk hanyar da Kainat ta biyo Jaleela zata toshe dole tayi shiru ta zuba mata, amma k'asan ranta tana had'a plan. Saida tasan yanda zatayi ta samu number Zain. Da farko tayi masa kiran duniya yak'i d'agawa saboda isa. Haushi kaman ya kashe Kainat. Batayi k'asa a gwiwaba ta tura masa sak'o cewar ita tasan yarinya da yake nema La REINA, the cold Beauty. Zata had'ashi da ita amma sai ya bata kaso mai tsoka. Lokacin da sak'on ta ya shigo wayarsa yana kwance ne cikin tamfatsetsen d'akin sa da aka kashewa dukiya. Gajeren wando ne a jikinsa da single. Zain kyakkyawan mutum ne irin handsome black beauty d'in nan. Yana da manyan lumsheshshun idanuwa da dogon hanci ,bakin sa irin full d'innan ne dake nan jazur dashi ,kuma very oily kaman wanda ke shafa masa man leb'e. Zain yana daga cikin irin mazannan da za'a kira tsaka-tsaki a fannin tsayi. Yana da murdadden jiki burin ko wace mace. K'irjinsa kuwa cike yake da gashi yala-yala daya kwanta tsam gwanin sha'awa. Haka fuskar sa kewaye take da dan siririn gashi daya zagayo har zuwa bakinsa. Ana kiran irin wannan gyaran fuska da kwata million. Zain kan abun MashaAllah don ya gama had'ewa ta ko wanne fanni. Bak'ar fatarsa da taji hutu da kuɗi sai shek'i take irin ta aje butters. Ga fatar tasa da mugun laushi kaman mace. Bashi da gashi sosai a kansa don gashinsa irin namu ne na malam bahaushe, amma saboda gyara da mai da kan kesha gashin ya kwanta lum kansa, ya nannade kace hula ya d'ura. Hankalin sa da nutsuwar sa gaba d'aya yana kan laptop nashi ne yana duba wani file da aka masa transfer na wata mata da tayi mummunan had'ari a can CALIFORNIA. had'arin ya yi muni da dole ake buk'atar manyan likitoci surgeon's don su dukafa a kanta, wajen hatsarin da tayi ne wani irin rodi mai tsananin k'arfi ya huda ta kasan habarta ya bullu ta saman kanta. Kana ganin kwakwalwarta dake motsi ga jini dake fita ta kan nata yana tsartuwa kaman fanfano. Likitoci sun had'u sosai a kanta wajen ganin an bata taimakon gaggawa, duk da cewa da yawa suna tunanin bazata kai ko ina ba. Sai akayi rashin sa'a Zain baya k'asa lokacin da abun ya faru. Da za'ayi mata aikin sai Zoom call akayi dashi yana ganin yanda abun ke gudana yana bada taimakon da yake ganin ya dace. Cikin ikon Allah kuwa aka cire k'arfen amma saida aka kwana aka wuni sunayin. Yanzu matar tana kan bed rest ne don ta shiga coma. Bayan samun nasara na wannan babban aiki da akayi. Tun dawowar sa bai fita ba sai ranan ya shirya don samun fresh air. Bayan zuwansa club d'in ne yaji maza na magana kan Jaleela, da yanda suke buri ganin sun samu lokacin ta kona awa d'aya ne. Amma ita d'in wuyar samu take sai ka ajiye kwalitis da take so. Yanda yaga mazan na hauka a kanta duk inda ya wuce maganan The Cold Beauty suke. Hakan yaji shima yana da interest a kan wannan yarinya. Baiyi zaton zataki amsar tayinsa ba duba da matsayin sa da yanda mata ke hauka a kansa. Saboda wannan ja masa class da take yaji interest nashi a kanta ya kara picking. Murmushin gefen baki ya yi bayan ya gama karanta sakon Kainat. A take ya bata amsa yace ta turo account nata zai saka mata kuɗi. Yana ajiye wayar aka buga k'ofar d'akin nasa aka shigo. Yarinya ce ta shigo da bata wuce shekara 18 ba. Kyakkyawace ta gaske Black beauty. Kallo d'aya zakayi mata kasan sun had'a alaka da Zain. Manyan idanuwansa ya d'ago ya watsama mata ta shigo rik'e da tray dake d'auke da wani bowl na fruits da shawarma sai zuba kamshi take. A kunyace ta ajiye kayan kan tebir saboda irin kallon da Zain ke jefanta da shi. Kusa da gadon ta samu guri ta zauna tana murmushi tace "Barka da rana Ya Zain. Ga fruits na kawo maka nasan kayi aiki ka gaji" Wani irin killer look ya bata yana murmushin gefen baki ya ajiye laptop din dake cinyarsa. Murya so sexy yace "Thank you my dearest, yaushe ki ka zo?" D'an far tayi da ido a dan shagwaɓe tace " ba tunda ka dawo ka ki zuwa mu gaisa ba?, to ni na biyoka har gida" "Sorry tunda nazo ban zauna bane. How is Uncle?" Tana wasa da yatsun hannun ta tace "Yana nan lfy. Tare muka zo" Kai ya jinjina ya d'auko abincin yana ci . Sosai suke jefin juna da wani shirtaccen kallo kai kana gani kasan ko wanne da matsayin daya ajiye d'an uwansa. Ayush y'ar k'anin babansa ce. Kaf family na mai tangaran. Wato minister an san yanda Ayush da Zain suka shaku da juna tun suna yara. Saboda wannan dalili yasa iyayen suke yanke had'asu aure. To amma daga Zain har Ayush babu wanda yasan da wannan batun. Dukkanin su ,su biyun babu wanda ya furtawa d'an uwansa kalman so. B'angaren Kainat tana ganin sak'on ta daka wani tsalle da ihu. A gaggauce ta tura masa account number nata da kuma ranan da zata kawo masa Jaleelan har inda yake. Kaman yanda Kainat d'in ta shirya Plan nata. Yau rana ta juma'a da safe misalin k'arfe takwas ta fito cikin shiri. Falo ta sami Jaleela da Anees na karyawa. Anees shirye cikin kaya na makaranta. Kaman yanda Jaleela ta koyar da ita yarinya da ladabi ta gaisar da Kainat. Murmushi Kainat tayi ta shafa kanta tana tambayar yanda ta tashi. Zama itama tayi suka karya tare suna gamawa suka fito gaba d'aya don kaita makaranta. Bayan sun sauketa Kainat ta juyo ta kalli Jaleela data maida hankali kan tuki tace "Yau fa ina da wani babban event." "Na me?" Jaleela tace ba tare data juyo ba. Kainat ta cigaba da cewa "Ina wata kwata Cele?. Yau birthday nata za'ayi party a nan club da muke zuwa. Don Allah badan niba ki daure kizo kinga musamman ta gayyace ki" Shiru Jaleela tayi tana tunani. Itama dai tana san ta d'an fita tasha iska. Kwana biyu babu inda ta leke. Ko wayarta kashewa tayi don bata san damuwa. Saida ta d'an tura harshen ta wajen kuncinta kaman wanda ke hura iska tace "Zanje" Ihu Kainat tayi harda d'an rungume ta ta gefe. Tace "Kai amma na gode. Ga Vip card naki idan kinzo kai tsaye zaki shiga " D'an k'aramin card ta mik'awa Jaleela . Karb'a kawai tayi ta ajiye bata duba ba. Ran Kainat fari tas ta ajiye ta hanya inda zata had'u da wani sugar Daddy nata. Itama Jaleela wani had'edd'en restaurant tayi ta kebe guri d'aya tana cigaba da tunanin rayuwarta da iyayen ta. Misalin k'arfe goma na dare ta gama shiryawa cikin wata arniyar doguwar riga mai hannu d'aya. Rigar kaman net take tabi dukkanin wani sassan jikinta ta ta kwanta. Gashin kanta ta sake shi ya zubo gadon bayanta. Dogon takarmi ne a k'afarta mai igiya. Kan rigar ta d'ura wata y'ar jacket mai hula dake da gashi. Sosai tayi bala'in kyau ta fito sak baturiya. D'an k'aramin bak'in daya sa janbaki ta motsa tana k'ara kallon kanta cikin mudubi. Kai ta jinjina kanta ta matsa gadon da Anees ke kwance ta k'ara tofeta da Addu'a kafin ta fito daga d'akin. Zaune falon ta sami LAMI dake kula da Anees idan bata nan. Dattijowar mata ce . Mata tana da kulawa sosai ga tsabta. Bacin haka akwaita da ibada. Murmushi Jaleela tayi ta ciro y'ar k'aramar waya ta mik'a mata kaman yacce take duk ranan da zata fita. "Gashi Mama. Idan kuna buk'atar abu sai ki gaggauta yimin waya koda Anees zata farka" Kai Lami ta d'aga ta karb'i wayar cikin girmawawa. Sallama Jaleela tayi mata ta wuce Lami ta bita da kallo ciki da mamaki da Allah wadai irin wannan rayuwa. Tana mamakin rayuwar da Jaleela ke yi. A haka kana kallonta kallon salihar mace zakayi mata. Don tana da hankali ga nutsuwa da tausayi, bayan haka kuma ga tsananin ibada. Dazu tana jin yanda take rera karatun Qur'ani kaman wata Sudais. Amma yanzu ji irin shirgar da tayi ta fice da wannan tsohon daren. Ita kuwa wane iftila'i ne ya sameta haka harta

Chapter 2 of 7